Categories
L. FIR

L. FIR 1

Hadaya ta Ƙonawa

1 Ubangiji ya kirawo Musa, ya yi masa magana daga cikin alfarwa ta sujada, ya ce

2 ya ba Isra’ilawa ka’idodin nan.

Sa’ad da kowane mutum a cikinsu zai kawo sadaka ga Ubangiji, sai ya kawo sadakarsa daga cikin garkunansa na shanu, da na tumaki, da na awaki.

3 Idan sadakarsa ta hadayar ƙonawa ce daga cikin garken shanu, sai ya ba da namiji marar lahani, zai miƙa shi a ƙofar alfarwa ta sujada domin sadakar ta zama abar karɓa a gaban Ubangiji.

4 Sai ya ɗibiya hannunsa a kan kan hadaya ta ƙonawar, za a karɓa masa, a kuwa yi masa gafara.

5 Sa’an nan zai yanka ɗan bijimin a gaban Ubangiji. ‘Ya’yan Haruna maza, firistoci, za su miƙa jinin a bagaden da yake a ƙofar alfarwa ta sujada za su kuma yayyafa jinin a kewaye da shi.

6 Sai mai hadayar ya feɗe dabbar, ya yanyanka ta gunduwa-gunduwa.

7 Sa’an nan ‘ya’yan Haruna maza, firistoci, za su hura wuta a bisa bagaden, su jera itace daidai a wutar.

8 Su ɗibiya gunduwoyin, da kan, da kitsen bisa itacen da yake cikin wutar da take a kan bagaden.

9 Amma mai hadayar zai wanke kayan ciki da ƙafafu da ruwa, sa’an nan firist ya ƙone duka a kan bagaden, hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.

10 Idan hadayarsa ta ƙonawa daga cikin garken tumaki ko kuwa na awaki ne, sai ya ba da namiji marar lahani.

11 Zai yanka shi a arewacin bagaden a gaban Ubangiji. ‘Ya’yan Haruna, firistoci, za su yayyafa jinin a kewaye da bagaden.

12 Mai hadayar kuma zai yanyanka shi gunduwa-gunduwa, da kansa, da kitsensa. Firist zai jera su a bisa itacen da yake cikin wutar da take a bagaden.

13 Amma mai hadayar zai wanke kayan ciki da ƙafafu da ruwa, sa’an nan firist ya miƙa duka, ya ƙone a bisa bagaden, gama hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.

14 Idan kuma hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji daga cikin tsuntsaye ne, sai ya kawo kurciyoyi, ko ‘yan tattabarai.

15 Firist ɗin zai kawo tsuntsun a bagaden, ya murɗe wuyan tsuntsun, sa’an nan ya ƙone kan a bisa bagaden. Za a tsiyaye jini a gefen bagaden.

16 Amma zai ɗauki kururun da gashin ya zubar da su a gefen bagaden a wajen gabas a wurin zuba toka.

17 Zai tsaga shi biyu a tsaka, amma ba zai raba shi ba. Firist ɗin zai ɗibiya shi a bisa itacen da yake bisa bagaden, ya ƙone shi, gama hadaya ta ƙonawa ce mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.

Categories
L. FIR

L. FIR 2

Hadaya ta Gari

1 A sa’ad da mutum ya kawo hadaya ta gari ga Ubangiji, sai ya kawo gari mai laushi, ya zuba masa mai da lubban.

2 Zai kuma kawo hadayarsa a wurin ‘ya’yan Haruna maza, firistoci. Zai ɗibi tāfi guda na lallausan garin da aka zuba wa mai da dukan lubban. Firist kuwa zai ƙona wannan a kan bagaden don tunawa, gama hadaya ta ƙonawa ce mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.

3 Ragowar garin hadayar kuwa, zai zama na Haruna da ‘ya’yansa maza, gama hadaya ce ta ƙonawa mafi tsarki ga Ubangiji.

4 Sa’ad da aka kawo hadaya ta gari da aka toya cikin tanda, sai a yi shi da gari mai laushi marar yisti kwaɓaɓɓe da mai, a shafa masa mai, a toya, ko kuwa a soya ƙosai.

5 Idan kuwa hadayar ta gari ce da aka toya cikin kaskon tuya, sai a yi abinci da gari mai laushi wanda ba a sa masa yisti ba, wanda aka kwaɓa da mai.

6 Za a gutsuttsura shi, a zuba masa mai, hadayar gari ke nan.

7 Idan kuma hadayar ta gari ce wadda aka dafa cikin tukunya, ita kuma, sai a yi ta da gari mai laushi da mai.

8 Za a kawo hadaya ta gari da aka yi da abubuwan nan ga Ubangiji. Sa’ad da aka kai wa firist, sai ya kawo ta a bagaden.

9 Firist zai ɗauki kashi na tunawa daga hadaya ta garin, ya ƙona shi bisa bagaden, hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.

10 Ragowar hadayar garin zai zama na Haruna da ‘ya’yansa maza, gama hadayar ƙonawa ce mafi tsarki ga Ubangiji.

11 A kowace hadaya ta gari da za a kawo wa Ubangiji, ba za a sa yisti ba, gama ba za a yi hadayar ƙonawa ga Ubangiji da yisti, ko da zuma ba.

12 Amma a iya kawo su kamar hadayar nunan fari ga Ubangiji, sai dai ba za a ƙona su a kan bagade ba, kamar hadaya ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi.

13 Sai a sa gishiri a kowace hadaya ta gari, kada a rasa sa gishirin alkawarin Allah a hadaya ta gari. A sa gishiri a dukan hadayu.

14 Idan za a yi hadaya ta gari daga cikin nunan fari ga Ubangiji, sai a miƙa hadaya ta nunan fari da ɗanyen hatsi wanda aka gasa aka ɓarza.

15 Za a zuba masa mai, a barbaɗa masa lubban, gama hadaya ce ta gari.

16 Firist kuwa zai ƙone wani kashi daga cikin ɓarzajjen hatsin a gauraye da man, da dukan lubban don tunawa, gama hadaya ce ta ƙonawa ga Ubangiji.

Categories
L. FIR

L. FIR 3

Hadaya ta Salama

1 Idan mutum zai kawo hadayarsa ta salama daga garken shanu, sai ya kawo mace ko namiji marar lahani ga Ubangiji.

2 Zai ɗibiya hannunsa a kan kan hadayarsa, ya yanka a bakin ƙofar alfarwa ta sujada. ‘Ya’yan Haruna maza kuwa, firistoci, za su yayyafa wa bagaden jinin kewaye da shi.

3 Daga hadaya ta salama sai a miƙa waɗannan hadayu na ƙonawa ga Ubangiji, wato, kitsen da yake rufe da kayan ciki, da wanda yake bisansa,

4 da ƙoda biyu, da kitsen da yake bisansu a wajen kwiɓi, da matsarmamar da zai cire tare ƙodojin.

5 ‘Ya’yan Haruna, maza kuwa, za su ƙone su tare da hadayar ƙonawa da take bisa itacen da yake cikin wutar bagade, hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.

6 Idan kuwa hadayarsa ta salama ga Ubangiji daga garken tumaki, ko na awaki ce, sai ya ba da dabbar, mace ko namiji, marar lahani.

7 Idan ɗan rago ne ya bayar don hadaya, sai ya miƙa shi a gaban Ubangiji.

8 Zai ɗibiya hannunsa a kan kan hadayarsa, ya yanka a gaban alfarwa ta sujada. ‘Ya’yan Haruna, maza kuwa, za su yayyafa wa bagaden jinin kewaye da shi.

9 Daga cikin hadaya ta salama sai a miƙa waɗannan hadayu na ƙonawa ga Ubangiji, wato, kitsensa da wutsiyarsa duka mai kitse. Zai yanke ta gab da ƙashin gadon baya, da kitsen da ya rufe kayan ciki kuwa, da wanda yake bisansa,

10 da ƙoda biyu, da kitsen da yake bisansu a wajen kwiɓi, da matsarmamar da zai cire tare da ƙodojin.

11 Firist kuwa zai ƙone su a bisa bagaden kamar hadayar abincin da akan ƙone da wuta ga Ubangiji.

12 Idan ya kawo akuya don hadayarsa, sai ya miƙa ta a gaban Ubangiji.

13 Zai ɗibiya hannunsa a bisa kanta, ya yanka ta a gaban alfarwa ta sujada. ‘Ya’yan Haruna, maza, za su yayyafa wa bagaden jinin kewaye da shi.

14 Sa’an nan mai hadayar zai ba da kitsen da yake rufe da kayan cikin, da wanda yake bisansa,

15 da ƙodoji biyu, da kitsen da yake bisansu wajen kwiɓi, da matsarmama don a miƙa su hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji.

16 Firist kuwa zai ƙone su a bisa bagaden kamar hadayar abincin da akan ƙone don ya yi ƙanshi mai daɗi. Dukan kitse na Ubangiji ne.

17 Ba za a ci kitse ko jinin ba a wuraren zamanku. Wannan doka madawwamiya ce.

Categories
L. FIR

L. FIR 4

Hadayu domin Zunubi

1 Ubangiji ya kuma ce wa Musa,

2 ya faɗa wa mutanen Isra’ila, in wani ya yi zunubi, ba da gangan ba, har ya karya ɗaya daga cikin dokokin Ubangiji, sai ya bi ka’idodin nan.

3 Idan keɓaɓɓen firist ne ya yi zunubi, ya jawo wa jama’a laifi, sai ya ba da ɗan bijimi marar lahani ga Ubangiji don yin hadaya saboda zunubin da ya aikata.

4 Zai kawo ɗan bijimin a ƙofar alfarwa ta sujada a gaban Ubangiji, ya ɗibiya hannunsa a kan kan bijimin, ya yanka shi a gaban Ubangiji.

5 Shi kuma keɓaɓɓen firist ɗin ya ɗibi jinin bijimin ya kai shi a alfarwa ta sujada.

6 Ya tsoma yatsansa cikin jinin, ya yayyafa jinin sau bakwai a gaban Ubangiji a wajen labulen Wuri Mai Tsarki.

7 Zai kuma ɗiba daga cikin jinin, ya sa a bisa zankayen bagaden ƙona turaren da suke cikin alfarwar a gaban Ubangiji. Sauran jinin bijimin kuwa zai zuba shi a gindin bagaden ƙona hadaya wanda yake a ƙofar alfarwa ta sujada.

8 Zai ɗebe dukan kitsen ɗan bijimi na yin hadaya don zunubi, da kitsen da yake rufe da kayan cikin, da wanda yake bisansa,

9 da ƙodoji biyu da kitsen da yake bisansu wajen kwiɓi, da matsarmama.

10 Zai cire su daidai kamar yadda akan cire na bijimin hadaya ta salama. Sai firist ɗin ya ƙone su a kan bagaden ƙona hadaya.

11 Amma fatar ɗan bijimin, da namansa, da kansa, da ƙafafunsa, da kayan cikinsa, da tarosonsa,

12 da sauran bijimin duka zai kai su waje bayan zango a wuri mai tsabta inda ake zubar da toka, nan zai ƙone su da wuta a inda ake zubar da tokar.

13 Idan taron jama’ar Isra’ila sun yi zunubi, ba da gangan ba, har sun aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji ya umarta kada a yi, amma ba su farga da laifinsu ba, duk da haka sun yi laifi.

14 Amma sa’ad da zunubin da suka aikata ya sanu, taron jama’a za su ba da ɗan bijimi na yin hadaya don zunubi. Za a kawo shi a gaban alfarwa ta sujada.

15 Sai dattawan jama’a su ɗibiya hannunsu a kan kan bijimin a gaban Ubangiji, sa’an nan a yanka bijimin a gaban Ubangiji.

16 Sai keɓaɓɓen firist ya ɗibi jinin bijimin, ya kai cikin alfarwa ta sujada.

17 Sa’an nan ya tsoma yatsansa a cikin jinin ya yayyafa shi sau bakwai a gaban Ubangiji, a gaban labulen.

18 Sai ya ɗiba daga cikin jinin ya shafa wa zankayen bagaden da suke cikin alfarwa ta sujada a gaban Ubangiji, sauran jinin kuwa sai ya zuba a gindin bagaden ƙona hadaya wanda yake a ƙofar alfarwa ta sujada.

19 Zai kwashe kitsensa duka, ya ƙone shi bisa bagaden.

20 Sai ya yi da ɗan bijimin kamar yadda ya yi da ɗan bijimi na hadaya don zunubin firist. Ta haka firist zai yi kafara domin jama’a, za a kuwa gafarta musu.

21 Zai kai bijimin a bayan zango, ya ƙone shi kamar yadda ya yi da na farin, gama hadaya ce don zunubin taron jama’ar.

22 Idan shugaba ya yi zunubi, ba da gangan ba, har ya aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji Allahnsa ya umarta kada a yi, to, ya yi laifi.

23 Idan aka sanar da shi zunubin da ya yi, sai ya kawo bunsuru marar lahani don yin hadaya.

24 Zai ɗibiya hannunsa a kan kan bunsurun, ya yanka a wurin da ake yanka hadaya ta ƙonawa a gaban Ubangiji, gama hadaya ce don zunubi.

25 Sai firist ya ɗibi jinin hadaya don zunubi da yatsansa ya shafa wa zankayen bagaden ƙona hadaya, sa’an nan ya zuba sauran jinin a gindin bagaden.

26 Firist ɗin zai ƙona kitsen duka a bisa bagaden kamar yadda akan yi da kitsen hadaya ta salama, ta haka firist zai yi kafara domin zunubin shugaban, za a kuwa gafarta masa.

27 In wani daga cikin talakawa ya yi zunubi, ba da gangan ba, ya aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji ya umarta kada a yi, to, ya yi laifi.

28 Sa’ad da aka sanar da shi zunubin da ya aikata, sai ya kawo akuya marar lahani don yin hadaya saboda zunubinsa.

29 Zai ɗibiya hannunsa a kan kan hadaya don zunubi, ya yanka hadayar a wurin hadaya ta ƙonawa.

30 Firist zai ɗibi jinin da yatsansa ya shafa wa zankayen bagaden ƙona hadaya, sa’an nan ya zuba sauran jinin a gindin bagaden.

31 Za a ɗebe kitsenta duka kamar yadda akan ɗebe kitsen hadaya ta salama. Firist zai ƙona shi a kan bagaden don ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. Ta haka firist zai yi kafara dominsa, za a kuwa gafarta masa.

32 Idan kuwa daga cikin ‘yan tumaki zai ba da hadayarsa, sai ya kawo ‘yar tunkiya marar lahani.

33 Zai ɗibiya hannunsa a kan kan abin yin hadaya don zunubin, sa’an nan ya yanka a wurin da akan yanka hadaya ta ƙonawa.

34 Sai firist ya ɗibi jinin abin yin hadaya don zunubi da yatsansa ya shafa wa zankayen bagaden ƙona hadaya, sauran jinin kuwa ya zuba a gindin bagaden.

35 Zai kuma ɗebe kitsenta duka kamar yadda a kan ɗebe na ragon hadaya ta salama. Firist zai ƙone shi a bisa bagaden a bisa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Ta haka firist zai yi masa kafara saboda zunubin da ya aikata, za a kuwa gafarta masa.

Categories
L. FIR

L. FIR 5

Hadayu domin Laifi

1 Laifi ne idan mutum ya aikata kowane ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa.

Idan mutum ya ji ana shelar neman mai laifi, amma ya ƙi fitowa ya ba da shaida, ko da yake ya gani, ko kuma ya san abin da ya faru, ya yi laifi, alhaki yana kansa.

2 Ko kuma idan mutum ya taɓa kowane abin da yake haram ko mushen haramtacciyar dabba ta jeji ko ta gida, ko mushen haramtaccen abin da yake rarrafe, zai zama da laifi, ko da bai sani ba.

3 Ko kuma idan ya taɓa kowace irin ƙazantar mutum wadda akan ƙazantu da ita, ba da saninsa ba, amma in daga baya ya sani, to, laifi ya kama shi.

4 Ko kuma idan mutum ya yi rantsuwa da garaje da bakinsa, cewa, zai yi mugunta, ko nagarta, ko kowace irin rantsuwa ta garaje da mutane sukan yi, to, laifi ya kama shi bayan da ya gane da rantsuwarsa.

5 In mutum ya aikata ɗaya daga cikin waɗannan laifofi, sai ya hurta laifin da ya yi.

6 Ya kuma kawo hadaya ga Ubangiji don laifin da ya yi. Sai ya kawo ‘yar tunkiya ko akuya domin hadaya don zunubi. Firist zai yi kafara don laifin mutumin.

7 Amma idan ‘yar tunkiyar ta fi ƙarfinsa, sai ya kawo kurciyoyi biyu ko ‘yan tattabarai biyu don yin hadaya ga Ubangiji saboda laifin da ya yi. Ɗaya za ta zama ta yin hadaya don laifi, ɗayan kuwa don yin hadaya ta ƙonawa.

8 Zai kawo su wurin firist. Da fari firist zai miƙa hadaya don laifi. Zai karye wuyanta, amma ba zai tsinke kan ba.

9 Zai yayyafa jinin hadaya don laifi a gefen bagaden, sauran jinin kuwa zai tsiyaye a gindin bagade, gama hadaya ce don laifi.

10 Sa’an nan zai miƙa ta biyun don hadaya ta ƙonawa bisa ga yadda aka ƙayyade. Firist ɗin zai yi kafara saboda laifin da mutumin ya yi, za a kuwa gafarta masa.

11 Amma idan har kurciyoyi biyu, ko ‘yan tattabarai biyu sun fi ƙarfinsa don yin hadaya saboda laifinsa, sai ya kawo humushin garwar gari mai laushi don yin hadaya saboda laifinsa. Ba zai zuba mai ko lubban a garin ba, gama hadaya ce don laifi.

12 Zai kai wa firist garin, firist zai ɗibi garin cike da tafin hannunsa, wannan shi ne kashi na tunawa. Zai ƙone shi bisa bagaden kamar hadaya na ƙonawa ga Ubangiji, gama hadaya ce don laifi.

13 Ta haka firist zai yi kafara don laifin da mutumin ya aikata daga cikin abubuwan nan, za a kuwa gafarta masa. Sauran garin zai zama na firist kamar yadda yakan zama nasa a hadaya ta gari.

14 Sai Ubangiji ya ba Musa ka’idodin nan.

15 Idan mutum ya ci amana, ya kuwa yi laifi ba da gangan ba, a kan tsarkakakkun abubuwa na Ubangiji, sai ya kawo rago marar lahani daga garken tumaki ga Ubangiji saboda yin hadaya don laifinsa. Za a kimanta ragon da tamanin kuɗi bisa ga ma’aunin azurfar da ake aiki da shi.

16 Zai kuma biya diyya saboda abu mai tsarki da ya yi laifi a kansa. Zai kuma ƙara humushi a kai, sa’an nan ya ba firist. Firist kuwa zai yi kafara dominsa da ragon hadaya don laifi. Za a kuwa gafarta masa.

17 Idan wani ya yi laifi, ya aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji ya umarta kada a yi, to, laifi ya kama shi ko da bai sani ba. Alhakin laifin yana kansa.

18 Sai ya kai wa firist rago marar lahani daga cikin garke. Za a kimanta tamanin rago daidai da tamanin hadaya don laifi. Firist kuwa zai yi kafara don kuskuren da mutumin ya yi ba da saninsa ba, za a gafarta masa.

19 Hadaya ce don laifi, gama ya yi wa Ubangiji laifi.

Categories
L. FIR

L. FIR 6

1 Ubangiji kuma ya ba Musa ka’idodin nan.

2 Idan wani mutum ya yi laifi na cin amana gāba da Ubangiji, wato, ya yaudari maƙwabcinsa a kan ajiya, ko jingina, ko ƙwace, ko ya zalunce shi,

3 ko ya yi tsintuwa, amma ya yi mūsu har ya rantse da ƙarya, duk dai irin abubuwan da akan aikata na laifi,

4 sa’ad da mutum ya yi laifi, ya kuwa tabbata mai laifi ne, sai ya mayar da abin da ya ƙwace, ko abin da ya samu ta hanyar zalunci, ko abin da aka ba shi ajiya, ko abin da ya tsinta,

5 ko kowane abin da ya rantse a kansa da ƙarya. Zai mayar wa mai abin da abinsa a yadda yake, har ya ƙara da humushin tamanin abin. A ranar da zai yi hadaya don laifinsa, a ranar ce zai mayar wa mai abin da abinsa.

6 Zai kuwa kai wa firist rago marar lahani daga garken tumaki don yin hadaya ga Ubangiji saboda laifinsa. Za a kimanta tamanin ragon daidai da tamanin hadaya don laifi.

7 Firist kuwa zai yi kafara dominsa a gaban Ubangiji, za a kuwa gafarta masa irin laifin da ya yi.

Hadayun da Za A Ƙone Ƙurmus

8 Ubangiji kuma ya umarci Musa,

9 ya ba Haruna da ‘ya’yansa maza ka’idodin hadayu na ƙonawa. Hadaya ta ƙonawa za ta kwana bisa bagaden, wutar bagaden kuma ta kwana tana ci har safe.

10 Firist zai sa rigarsa ta lilin, ya ɗaura mukurunsa na lilin, sa’an nan ya kwashe tokar hadaya ta ƙonawa daga bagaden, ya zuba a gefensa.

11 Firist ɗin kuma zai tuɓe rigunansa, ya sa waɗansu, sa’an nan ya kwashe tokar ya kai bayan zango ya zuba a wani wuri mai tsabta.

12 Sai a bar wutar bagaden ta yi ta ci, kada a kashe ta. Firist ɗin ya yi ta iza wutar kowace safiya, ya shimfiɗa hadaya ta ƙonawa a jere a bisa wutar, ya kuma ƙone kitsen hadaya ta salama a bisanta.

13 Sai wuta ta yi ta ci a bisa bagaden kullum, kada ta mutu.

Hadaya ta Gari

14 Wannan ita ce dokar hadaya ta gari. ‘Ya’yan Haruna, maza, za su miƙata a gaban Ubangiji daga gaban bagaden.

15 Ɗaya daga cikinsu zai ɗibi lallausan garin hadayar wanda aka zuba masa mai da lubban cike da tafin hannunsa. Zai ƙona wannan a bisa bagaden, hadaya ce mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji don tunawa.

16 Haruna da ‘ya’yansa maza za su ci ragowar garin. Za a ci shi ba tare da yisti ba a wuri mai tsarki na farfajiyar alfarwa ta sujada.

17 Ba za a sa masa yisti a toya shi ba. Wannan Ubangiji ne ya ba su ya zama rabonsu daga cikin hadayun da ake ƙonawa da wuta, abu ne mafi tsarki, kamar hadaya don zunubi da laifi.

18 Kowane ɗa namiji cikin ‘ya’yan Haruna zai iya ci daga cikin hadayun Ubangiji waɗanda akan yi da wuta. Wannan madawwamiyar doka ce cikin zamananku duka. Duk wanda ya taɓa hadayu zai tsarkaka.

19 Sai Ubangiji ya ba Musa waɗannan ka’idodi,

20 domin keɓe firist, wato, zuriyar Haruna. A ranar da za a keɓe shi zai kawo humushin garwar gari mai laushi (kamar yadda akan kawo na hadaya ta gari), za a miƙa rabinsa da safe, rabin kuma da maraice.

21 Za a shirya shi da mai a kwanon tuya. A kwaɓa shi sosai, a toya shi dunƙule dunƙule kamar hadaya ta gari, sa’an nan a kawo shi a miƙa shi don ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji.

22 Wanda aka keɓe daga zuriyar Haruna, shi ne zai miƙa wannan hadaya ga Ubangiji. Za a ƙone ta duka. Wannan farilla ce har abada.

23 Kowace hadaya ta gari ta firist, za a ƙone ta ɗungum, ba za a ci ba.

Hadayu domin Zunubi

24 Sai Ubangiji ya umarci Musa

25 ya ba Haruna da ‘ya’yansa maza waɗannan ka’idodi domin hadaya don zunubi. A inda ake yanka hadaya ta ƙonawa, a nan ne za a yanka hadaya don zunubi a gaban Ubangiji, hadaya ce mai tsarki.

26 Firist wanda ya miƙa hadaya don zunubi zai ci daga ciki a wuri mai tsarki a cikin farfajiyar alfarwa ta sujada.

27 Duk wanda ya taɓa naman zai tsarkaka, in kuma jinin ya ɗiga a riga, sai a wanke rigar a wuri mai tsarki.

28 Sai a fasa tukunyar ƙasa wadda aka dafa naman a ciki, amma in a cikin tukunyar tagulla aka dafa, sai a kankare ta a ɗauraye da ruwa.

29 Kowane namiji a cikin firistoci zai iya cin naman, gama abu ne mafi tsarki.

30 Amma ba za a ci naman hadaya don zunubi ba wanda aka shigar da jininsa a alfarwa ta sujada domin yin kafara a Wuri Mai Tsarki. Sai a ƙone shi da wuta.

Categories
L. FIR

L. FIR 7

Hadaya domin Laifi

1 Waɗannan su ne ka’idodin hadaya don ramuwa, hadaya ce tsattsarka.

2 Za a yanka dabbar hadayar a arewa da bagaden inda akan yanka hadaya don ƙonawa. Sai a yayyafa jinin a kan bagaden da kewayensa.

3 Za a miƙa kitsen abin hadaya duka, da wutsiya mai kitse, da kitsen da yake rufe da kayan ciki,

4 da ƙodoji biyu da kitsen da yake bisansu wajen kwiɓi, da matsarmama wadda za a cire tare da ƙodojin.

5 Firist zai ƙone su a bisa bagaden, gama hadaya ce da akan ƙone da wuta ga Ubangiji, hadaya ce don laifi.

6 Kowane namiji a cikin firistoci zai iya ci. Sai a wuri mai tsarki za a ci, gama tsattsarkan abu ne.

7 Hadaya don laifi kamar hadaya don zunubi take, saboda haka ka’idar yinsu iri ɗaya ce. Firist wanda ya yi kafarar, zai ɗauki abin da ya ragu.

8 Firist kuma wanda ya miƙa hadaya ta ƙonawa ta wani mutum, zai ɗauki fatar abin da aka yi hadayar da shi.

9 Kowace hadaya ta gari da aka toya cikin tanda, da duk wadda aka yi a tukunya ko a kaskon tuya, za su zama na firist wanda ya miƙa hadaya.

10 Kowace hadaya ta gari kuma wadda aka kwaɓa da mai, ko wadda ba a kwaɓa ba, za ta zama rabon ‘ya’yan Haruna, maza duka, kowa da kowa.

Hadaya domin Zumunci

11 Waɗannan su ne ka’idodin hadaya ta salama wadda za a miƙa wa Ubangiji.

12 Idan domin godiya mutum ya miƙa hadaya, sai ya miƙa ta tare da abinci marar yisti, wadda aka kwaɓa da mai, da wadda aka shafa wa mai, da kuma ƙosai.

13 Tare da hadayarsa ta salama don godiya, sai ya kawo dunƙulen abincin da aka sa masa yisti.

14 Daga cikin wannan zai miƙa waina ɗaya daga kowace hadaya don hadaya ta ɗagawa ga Ubangiji. Wannan zai zama na firist wanda ya yayyafa jinin hadaya ta salama.

15 Za a ci naman hadayarsa ta salama da aka miƙa don godiya a ranar da aka miƙa ta. Kada a bar naman ya kai safe.

16 Amma idan hadayarsa ta cika wa’adi ce, ko ta yardar rai ce, sai a ci ta a ranar da aka miƙa ta, kashegari kuma a ci abin da ya ragu.

17 Amma idan ba a cinye naman hadayar ba har ya kai kwana uku, kada a ci, sai a ƙone shi da wuta.

18 Idan aka ci naman hadayarsa ta salama a rana ta uku, ba za a karɓi wanda ya ba da hadayar har ya sami fa’idar hadayar ba, naman zai zama abin ƙyama, duk wanda ya ci ya yi laifi.

19 Kada a ci naman da ya taɓa wani abu marar tsarki, sai a ƙone shi da wuta.

Duk wanda yake da tsarki zai iya cin nama.

20 Amma wanda ya ci naman hadaya ta salama ga Ubangiji lokacin da ba shi da tsarki, za a raba shi da mutenensa.

21 Idan wani mutum ya taɓa abu marar tsarki, ko mutum ne, ko dabba ce, ko wani abu na banƙyama, ya kuma ci naman hadaya ta salama ga Ubangiji, za a raba wannan mutum da mutanensa.

22 Ubangiji kuma ya ce wa Musa,

23 ya faɗa wa mutanen Isra’ila cewa, kada su ci kitsen sa, ko na tunkiya, ko na akuya.

24 Kitsen dabbar da ta mutu mushe, da kitsen dabbar da namomin jeji suka yayyaga, za a iya yin wani amfani da shi, amma kada a kuskura a ci.

25 Duk mutumin da ya ci kitsen dabbar da aka miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji, za a raba shi da mutanensa.

26 Ko kaɗan, ba za a yi abinci da jini ba, ko na tsuntsu, ko na dabba, a inda suke duka.

27 Duk mutumin da ya karya wannan doka za a raba shi da mutanensa.

28 Ubangiji kuma ya ba Musa waɗannan ka’idodi

29 don mutanen Isra’ila, cewa, wanda zai miƙa hadayarsa ta salama ga Ubangiji, sai ya kawo hadayarsa ga Ubangiji daga cikin hadayu na salama.

30 Sai shi kansa ya kawo hadayar da za a ƙona. Zai kawo kitsen da ƙirjin. Za a yi hadaya ta kaɗawa da ƙirjin a gaban Ubangiji.

31 Firist zai ƙone kitsen a bisa bagaden, amma ƙirjin zai zama rabon Haruna da ‘ya’yansa maza.

32 Za a ba firist cinya ta dama, don hadaya ta ɗagawa daga cikin hadayu na salama.

33 Cinyar ƙafar dama za ta zama rabon ɗan Haruna wanda ya miƙa jinin da kitsen hadaya ta salama.

34 Gama Ubangiji ya ba Haruna da ‘ya’yansa maza, ƙirjin da aka kaɗa da cinyar da aka ɗaga, su zama rabonsu daga cikin hadayu na salama na Isra’ilawa. Ya ba Haruna, firist, da ‘ya’yansa maza, su zama rabonsu har abada daga cikin hadayu na Isra’ilawa.

35 Wannan shi ne rabon da aka keɓe wa Haruna da ‘ya’yansa maza, daga cikin hadayun da ake yi da wuta ga Ubangiji, tun a ranar da aka keɓe su firistoci na Ubangiji.

36 Ubangiji ya umarci Isra’ilawa su ba firistoci wannan a ranar da aka keɓe su. Wannan hakkinsu ne a dukan zamanansu.

37 Waɗannan su ne ka’idodin hadaya ta ƙonawa, da hadaya ta gari, da hadaya don zunubi, da hadaya don laifi, da hadaya don keɓewa, da hadaya ta salama.

38 Waɗannan su ne umarnan da Ubangiji ya ba Musa a Dutsen Sina’i, can cikin hamada, a ranar da ya faɗa wa Isra’ilawa su kawo hadayunsu gare shi.

Categories
L. FIR

L. FIR 8

Keɓewar Haruna da ‘Ya’yansa Maza

1 Ubangiji ya ce wa Musa,

2 “Ɗauki Haruna da ‘ya’yansa maza, da rigunan, da man keɓewa, da bijimi na yin hadaya don zunubi, da raguna biyu, da kwandon abinci marar yisti.

3 Ka kuma tattara jama’a duka a ƙofar alfarwa ta sujada.”

4 Musa kuwa ya yi yadda Ubangiji ya umarce shi. Jama’ar kuwa suka tattaru a ƙofar alfarwa ta sujada.

5 Musa ya faɗa wa taron jama’ar cewa “Wannan shi ne abin da Ubangiji ya umarta a yi.”

6 Sai Musa ya fito da Haruna da ‘ya’yansa maza, ya yi musu wanka.

7 Ya sa wa Haruna zilaika, ya ɗaura masa ɗamara, ya sa masa taguwa, ya kuma sa masa falmaran, ya ɗaura masa ɗamarar falmaran wadda aka yi mata saƙar gwaninta.

8 Ya maƙala masa ƙyallen maƙalawa a ƙirji, sa’an nan ya sa Urim da Tummin, a kan ƙyallen.

9 Sai ya naɗa masa rawani, daga gaban rawanin ya sa allon zinariya, wato, kambi tsattsarka, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

10 Sai Musa ya ɗauki man keɓewa ya shafa wa alfarwa ta sujada da dukan abin da yake cikinta, da haka ya tsarkake su.

11 Ya yayyafa wa bagaden mai sau bakwai, ya kuma shafa wa bagaden da dukan kayayyakinsa, da daron da gammonsa, don ya tsarkake su.

12 Ya zuba man keɓewa a kan Haruna, ya keɓe shi.

13 Sai Musa kuma ya kawo ‘ya’yan Haruna, maza, ya sa musu zilaiku, ya ɗaura musu ɗamaru, ya sa musu huluna kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

14 Sa’an nan ya kawo bijimi na yin hadaya don zunubi, Haruna da ‘ya’yansa maza, suka ɗibiya hannuwansu a kan kan bijimin.

15 Sai Musa ya yanka shi, ya ɗibi jinin a yatsansa ya shafa wa zankayen bagaden a kewaye, ya tsarkake bagaden, ya zuba jinin a gindin bagaden, ya keɓe shi don ya yi kafara dominsa.

16 Sai ya ɗauki dukan kitsen da yake bisa kayan ciki da matsarmama, da ƙodoji biyu da kitsensu, ya ƙone su bisa bagaden.

17 Amma ya ƙone naman bijimin da fatarsa da tarosonsa a bayan zangon kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

18 Sa’an nan ya kawo rago na yin hadaya ta ƙonawa. Haruna da ‘ya’yansa maza suka ɗibiya hannuwansu a kan kan ragon.

19 Sai ya yanka ragon, ya yayyafa jinin a bisa bagaden da kewayensa.

20 Da aka yanyanka ragon gunduwa gunduwa, sai Musa ya ƙone kan, da gunduwoyin, da kitsen.

21 Sa’ad da kuma aka wanke kayan ciki da ƙafafu da ruwa, sai ya ƙone ragon duka a bisa bagaden, hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

22 Musa ya kawo ɗayan ragon keɓewa, sai Haruna da ‘ya’yansa maza suka ɗibiya hannuwansu a kan kan ragon.

23 Musa kuwa ya yanka shi, ya ɗibi jinin, ya sa a leɓatun kunnen dama na Haruna, da bisa babban yatsansa na hannun dama, da babban yatsa na ƙafar dama.

24 Sai aka kawo ‘ya’yan Haruna, maza, Musa kuma ya sa jinin a leɓatun kunnensu na dama, da manyan yatsotsi na hannuwansu na dama, da manyan yatsotsin ƙafafu na dama. Sa’an nan ya yayyafa jinin kewaye da bagaden.

25 Ya kuma ɗauki kitsen, da wutsiya mai kitse, da dukan kitsen da yake bisa kayan ciki, da matsarmama da ƙodoji biyu da kitsensu, da cinyar dama.

26 Daga cikin kwandon abinci marar yistin da yake a gaban Ubangiji, ya ɗauki waina guda marar yisti, da waina guda da aka yi da mai, da ƙosai guda. Sai ya ɗibiya su a bisa kitsen da cinyar dama.

27 Ya sa waɗannan abubuwa duka a tafin hannuwan Haruna da na ‘ya’yansa maza, ya miƙa abubuwan nan domin hadayar kaɗawa ga Ubangiji.

28 Sa’an nan ya karɓe su daga tafin hannuwansu, ya ƙone su tare da hadaya ta ƙonawa a bisa bagaden don hadayar keɓewa, hadaya ce da aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.

29 Ya kuma ɗauki ƙirjin, ya kaɗa shi don hadayar kaɗawa ga Ubangiji. Wannan shi ne rabon Musa daga cikin ragon keɓewar, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

30 Sa’an nan Musa ya ɗiba daga cikin man keɓewa da jinin da yake bisa bagaden, ya yayyafa wa Haruna da rigunansa, da ‘ya’yansa maza da rigunansu. Da haka ya tsarkake Haruna da rigunansa, da ‘ya’yansa maza da rigunansu.

31 Sai Musa ya ce wa Haruna da ‘ya’yansa maza, “Ku dafa naman a ƙofar alfarwa ta sujada, ku ci shi a wurin, da abincin da yake a cikin kwandon hadayar keɓewa, kamar yadda Ubangiji ya umarta, cewa, Haruna da ‘ya’yansa maza za su ci shi.

32 Sauran abin da ya ragu daga naman da abincin, sai ku ƙone su.

33 Ba za ku fita daga cikin alfarwa ta sujada ba har kwana bakwai, wato, sai kwanakin keɓewarku sun cika, gama keɓewarku za ta ɗauki kwana bakwai.

34 Abin da aka yi a wannan rana haka Ubangiji ya umarta a yi domin kafararku.

35 A ƙofar alfarwa ta sujada za ku zauna dare da rana har kwana bakwai, kuna kiyaye umarnin Ubangiji don kada ku mutu, gama haka Ubangiji ya umarta.”

36 Sai Haruna da ‘ya’yansa maza suka yi dukan abin da Ubangiji ya umarta ta wurin Musa.

Categories
L. FIR

L. FIR 9

Haruna ya Miƙa Hadayu

1 A kan rana ta takwas, Musa ya kirawo Haruna, da ‘ya’yansa maza, da dattawan Isra’ila.

2 Sai ya ce wa Haruna, “Kawo ɗan maraƙi marar lahani na yin hadaya don zunubi, da rago marar lahani don hadaya ta ƙonawa, ka miƙa su ga Ubangiji.

3 Ka faɗa wa Isra’ilawa su ɗauki bunsuru na yin hadaya don zunubi, da ɗan maraƙi bana ɗaya, da ɗan rago bana ɗaya marasa lahani, don hadaya ta ƙonawa,

4 da bijimi da rago don hadayun salama, a yi hadaya da su ga Ubangiji, da hadaya ta gari da aka kwaɓa da mai, gama yau Ubangiji zai bayyana a gare ku.”

5 Sai suka kawo abin da Musa ya umarce su a gaban alfarwa ta sujada. Dukan taron jama’a suka matso kusa, suka tsaya a gaban Ubangiji.

6 Musa kuma ya ce, “Ubangiji ya umarce ku ku yi dukan wannan, domin ɗaukakar Ubangiji za ta bayyana gare ku.”

7 Sa’an nan Musa ya ce wa Haruna, “Matsa kusa da bagaden, ka miƙa hadayarka don zunubi, da hadayarka ta ƙonawa, ka yi kafara don kanka da kuma don jama’a. Ka kuma kawo hadayar jama’a, ka yi kafara dominsu kamar yadda Ubangiji ya umarta.”

8 Sai Haruna ya matsa kusa da bagaden, ya yanka ɗan maraƙi na yin hadaya don zunubi saboda kansa.

9 ‘Ya’yansa maza kuma suka miƙa masa jinin, sai ya tsoma yatsansa a cikin jinin, ya shafa a zankayen bagaden, ya kuma zuba jinin a gindin bagaden.

10 Amma kitsen, da ƙodojin, da kitsen da yake rufe da hanta na hadaya don zunubi, ya ƙone su a bisa bagaden kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

11 Naman da fatar kuwa ya ƙone su a bayan zangon.

12 Haruna ya yanka hadaya ta ƙonawa, ‘ya’yansa maza kuma suka miƙa masa jinin, sai ya yayyafa a bagaden da kewayensa.

13 Suka kuma miƙa masa hadaya ta ƙonawa gunduwa gunduwa tare da kan, sai ya ƙone su bisa bagaden.

14 Ya kuma wanke kayan ciki, da ƙafafu, sa’an nan ya ƙone su tare da hadaya ta ƙonawa a bisa bagaden.

15 Haruna kuma ya miƙa hadayar jama’a. Ya ɗauki bunsuru na yin hadaya don zunubi jama’ar, ya yanka, ya miƙa shi hadaya don zunubi kamar yadda aka yi da na farin.

16 Ya kuma miƙa hadaya ta ƙonawa, ya yi kamar yadda aka faɗa.

17 Ya kuma kawo hadaya ta gari, ya ɗibi garin cike da tafin hannunsa, ya ƙone shi a bisa bagaden tare da hadaya ta ƙonawa ta safiya.

18 Sai kuma ya yanka bijima da rago don yin hadayun salama domin jama’ar. ‘Ya’yansa maza suka miƙa masa jinin, sai ya yayyafa jinin a bisa bagaden da kewayensa.

19 Suka cire kitsen bijimin, da na ragon, da wutsiya mai kitse, da kitsen da yake rufe da kayan ciki, da ƙodoji, da matsarmama.

20 Sai Haruna ya aza kitsen a bisa ƙirjin dabbobin ya ƙone kitsen a bisa bagaden.

21 Amma ya yi hadaya ta kaɗawa da ƙirjin da cinyoyi na dama ga Ubangiji, kamar yadda Musa ya umarta.

22 Sai Haruna ya ta da hannuwansa wajen jama’a, ya sa musu albarka sa’an nan ya sauka daga wurin yin hadaya don zunubi, da hadaya ta ƙonawa, da hadayun salama.

23 Musa da Haruna suka shiga alfarwa ta sujada. Da suka fita, sai suka sa wa jama’a albarka. Ɗaukakar Ubangiji kuwa ta bayyana ga jama’a duka.

24 Wuta kuma ta fito daga wurin Ubangiji, ta ƙone hadaya ta ƙonawa da kitsen a bisa bagaden. Da jama’a duka suka gani, suka yi ihu, suka fāɗi rubda ciki suka yi sujada.

Categories
L. FIR

L. FIR 10

Zunubin Nadab da Abihu

1 ‘Ya’yan Haruna, maza, Nadab da Abihu kuwa kowannensu ya ɗauki faranti ya sa wuta, ya zuba turare a kai, ya miƙa haramtacciyar wuta a gaban Ubangiji, ba irin wadda Ubangiji ya umarta ba.

2 Sai wuta ta fito daga wurin Ubangiji ta kashe su, suka mutu a gaban Ubangiji.

3 Musa kuwa ya ce wa Haruna, “Wannan ita ce ma’anar abin da Ubangiji yake cewa, ‘Dukan waɗanda suke bauta mini, dole su nuna ladabi ga tsarkina, zan kuma bayyana ɗaukakata ga jama’ata.’ ” Haruna kuwa ya yi tsit.

4 Musa ya kirawo Mishayel da Elzafan ‘ya’ya maza na Uzziyel, kawun Haruna, ya ce musu, “Ku zo nan, ku ɗauki gawawwakin ‘yan’uwanku daga gaban wuri mai tsarki zuwa bayan zango.”

5 Sai suka zo, suka kama rigunan matattun suka ɗauke su zuwa bayan zango kamar yadda Musa ya faɗa.

Nawayar Aikin Firist

6 Musa kuma ya ce wa Haruna, da ‘ya’yansa maza, wato, Ele’azara da Itamar, “Kada ku bar gashin kanku barkatai, kada kuma ku kyakketa rigunanku don kada ku mutu, don kada Ubangiji ya yi fushi da taron jama’a duka, amma ‘yan’uwanku, wato, dukan Isra’ilawa, suna iya kuka saboda waɗanda Ubangiji ya ƙone.

7 Kada kuwa ku fita daga cikin alfarwa ta sujada don kada ku mutu, gama an shafa muku man keɓewa na Ubangiji.” Sai suka yi yadda Musa ya faɗa.

Dokoki don Firistoci

8 Ubangiji kuma ya yi magana da Haruna ya ce,

9 “Kada kai da ‘ya’yanka maza ku sha ruwan inabi, ko abin sha mai ƙarfi sa’ad da za ku shiga alfarwa ta sujada don kada ku mutu. Wannan doka ce a dukan zamananku.

10 Sai ku bambanta tsakanin abu mai tsarki da marar tsarki, da tsakanin abin da yake halal da abin da yake haram.

11 Ku kuma koya wa mutanen Isra’ila dukan dokokin da Ubangiji ya ba su ta hannun Musa.”

12 Musa kuwa ya ce wa Haruna da ‘ya’yansa maza, waɗanda suka ragu, wato, Ele’azara da Itamar, “Ku ɗauki ragowar hadaya ta gari wadda aka yi hadaya ta ƙonawa da ita ga Ubangiji, ku ci ba tare da yisti ba a gefen bagaden, gama tsattsarka ne.

13 Za ku ci shi a wuri mai tsarki gama naka rabo ke nan da na ‘ya’yanka maza daga cikin hadayun da akan ƙone da wuta ga Ubangiji, gama haka Ubangiji ya umarce ni.

14 Amma ƙirjin da aka yi hadayar ta kaɗawa da shi da cinyar da aka miƙa, za ka ci su a kowane tsabtataccen wuri, da kai da ‘ya’yanka mata da maza, gama wannan ne rabon da aka ba ku, daga hadayun salama na Isra’ilwa.

15 Za su kawo cinyar hadayar ɗagawa da ƙirjin hadayar kaɗawa tare da kitsen hadayun ƙonawa domin a yi hadaya ta kaɗawa ga Ubangiji. Wannan zai zama rabonka da na ‘ya’yanka har abada kamar yadda Ubangiji ya umarta.”

16 Da Musa ya nemi bunsurun hadaya don zunubi sai ya tarar an ƙone shi. Ya kuwa yi fushi da Ele’azara da Itamar, ‘ya’yan Haruna, maza, waɗanda suka ragu, ya ce,

17 “Don me ba ku ci hadaya don zunubi a wuri mai tsarki ba, da yake tsattsarkan abu ne wanda aka ba ku domin ku kawar da laifin taron jama’a, domin kuma ku yi kafara dominsu a gaban Ubangiji?

18 Ga shi, ba a shigar da jinin can cikin Wuri Mai Tsarki ba. Ga shi kuwa, ya kamata ku ci kamar yadda na umarta amma ba ku yi ba.”

19 Sai Haruna ya ce wa Musa, “Ga shi, yau suka miƙa hadayarsu don zunubi, da ta ƙonawa a gaban Ubangiji, ga kuma irin waɗannan abubuwa da suka same ni, da a ce na ci hadaya don zunubi yau, da zai yi kyau ke nan a gaban Ubangiji?”

20 Da Musa ya ji wannan, sai ya yi na’am da shi.