Categories
L. FIR

L. FIR 11

Dabbobin da yake Halal da na Haram

1 Ubangiji ya ba Musa da Haruna waɗannan ka’idodi

2 domin Isra’ilawa. Za ku ci kowace irin dabbar da take a duniya,

3 wadda take da rababben kofato, wadda kuma take yin tuƙa.

4 Ko daga cikin masu tuƙar ko masu rababben kofaton ba za ku ci waɗannan ba. Raƙumi yana tuƙa, amma ba shi da rababben kofato, haram ne a gare ku.

5 Rema tana tuƙa, amma ba ta da rababben kofato, haram ce a gare ku.

6 Zomo yana tuƙa, amma ba shi da rababben kofato, haram ne a gare ku.

7 Alade yana da rababben kofato, amma ba ya tuƙa, haram ne a gare ku.

8 Ba za ku ci namansu ba, ba kuwa za ku taɓa mushensu ba, gama haram ne a gare ku.

9 Kwa iya cin waɗannan abubuwan da suke cikin ruwa, kowane abin da yake da ƙege da kamɓorin da yake cikin tekuna ko koguna.

10 Amma kowace irin halittar da take cikin tekuna da koguna da ba ta da ƙege da kamɓori, abar ƙyama ce a gare ku.

11 Namansu kuma zai zama abin ƙyama a gare ku, ba za ku ci ba. Mushensu kuma abin ƙyama ne.

12 Kowane irin abin da yake cikin ruwa da ba shi da ƙege da kamɓori, abin ƙyama ne a gare ku.

13 Za ku ji ƙyamar waɗannan irin tsuntsaye, ba za ku ci su ba, gama abin ƙyama ne su, wato, gaggafa, da mikiya, da ungulun kwakwa,

14 da shirwa, da buga zabi, da irinsu,

15 da kowane irin hankaka,

16 da jimina, da mujiya, da shaho, da irinsu,

17 da ƙururu, da babba da jaka, da zarɓe,

18 da kazar ruwa, da kwasakwasa, da ungulu,

19 da shamuwa, da jinjimi da irinsa, da burtu, da jemage.

20 Dukan ƙwarin da yake da fikafikai ƙazantattu ne,

21 sai dai waɗanda suke da cinyoyin da suke sa su iya tsalle.

22 Za ku iya cin fara, da gyare, da ƙwanso da irinsu.

23 Amma sauran ƙananan ƙwari duka masu fikafikai, sun a kuma jan ciki, abin ƙyama ne a gare ku.

24 Duk wanda ya taɓa mushen waɗannan dabbobi, zai ƙazantu har faɗuwar rana.

25 Duk wanda kuma ya ɗauki mushensu dole ne ya wanke tufafinsa, amma zai ƙazantu har zuwa maraice.

26 Kowace dabba wadda ba ta da rababben kofato, ba ta kuma tuƙa, haram ce a gare ku. Duk wanda ya taɓa su zai ƙazantu.

27 Duk abin da yake tafiya a kan daginsa daga cikin dabbobin da suke da ƙafa huɗu, haram ne a gare ku. Duk wanda ya taɓa mushensu zai ƙazantu har zuwa maraice.

28 Wanda kuma ya ɗauki mushensu, sai ya wanke tufafinsa, ya zama ƙazantacce har zuwa maraice.

29 Waɗannan ƙananan dabbobin da suke rarrafe a ƙasa haram ne a gare ku, wato, murɗiya, da ɓera, da gafiya da irinsa,

30 da tsaka, da hawainiya, da ƙadangare, da guza, da damo.

31 Duk wanda ya taɓa su ko ya taɓa mushensu, zai zama ƙazantacce har zuwa maraice.

32 Duk abin da mushensu ya fāɗa a kai zai ƙazantu. Ko a kan itace ne, ko a bisa tufafi, ko a fata, ko a buhu, ko cikin kowane irin abu da ake amfani da shi, to, tilas a sa shi cikin ruwa, zai zama ƙazantacce har zuwa maraice, sa’an nan zai tsarkaka.

33 Idan wani daga cikinsu ya fāɗa cikin kasko, to, kaskon da abin da yake cikinsa za su ƙazantu, sai a fasa kaskon.

34 Kowane irin abincin da yake cikinsa kuma da yake da ruwa a cikinsa, zai haramtu. Kowane irin abin sha da yake cikinsa kuma, zai haramtu.

35 Kowane irin abu da mushensu ya fāɗa a kai, zai haramtu, ko randa ce, ko murhu, sai a farfasa, sun ƙazantu, haram ne a gare ku.

36 Duk da haka maɓuɓɓuga, ko tafkin ruwa ba za su haramtu ba, amma duk wanda ya taɓa mushensu ya ƙazantu.

37 Idan kuma kowane ɓangare na mushen ya fāɗa a kan kowane iri da za a shuka, ba zai haramta shi ba.

38 Amma idan an zuba ruwa a kan irin, mushen kuwa ya fāɗa kan irin, zai haramta a gare ku.

39 Idan kuma wata dabbar da kuke ci ta mutu, wanda duk ya taɓa mushenta zai ƙazantu har zuwa maraice.

40 Wanda kuwa ya ci mushen sai ya wanke tufafinsa, ya ƙazantu har zuwa maraice. Haka kuma shi wanda ya ɗauki mushen zai wanke tufafinsa ya kuma ƙazantu har zuwa maraice.

41 Ba za ku ci ƙananan dabbobin da suke motsi a bisa ƙasa ba,

42 duk waɗanda suke jan ciki, da waɗanda suke da ƙafa huɗu, da waɗanda suke da ƙafafu da yawa.

43 Kada ku ƙazantar da kanku da cin waɗannan abubuwa.

44 Ni ne Ubangiji Allahnku, domin haka dole ku tsarkake kanku, ku tsarkaka, gama ni mai tsarki ne.

45 Ni ne Ubangiji wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar domin in zama Allahnku. Sai ku zama tsarkakakku, gama ni mai tsarki ne.

46 Wannan ita ce dokar da ta shafi kowace dabba, da kowane tsuntsu, da kowace irin halitta wadda take tafiya cikin ruwa da kowace irin halitta da take a tudu.

47 Dole ku lura ku bambanta tsakanin masu tsarki, da marasa tsarki, da tsakanin dabbobin da za a ci, da waɗanda ba za a ci ba.

Categories
L. FIR

L. FIR 12

Tsarkakewar Mata bayan Haihuwa

1 Ubangiji ya ba Musa ka’idodin nan domin jama’ar Isra’ila.

2 Idan mace ta yi ciki, ta haifi ɗa namiji, to, za ta zama marar tsarki har kwana bakwai, kamar cikin kwanakin hailarta.

3 A kan rana ta takwas za a yi wa jaririn kaciya.

4 Sa’an nan kuma sai ta ci gaba da zama cikin jinin har kwana talatin da uku. A lokacin ba za ta taɓa kowane tsattsarkan abu ba, ba za ta shiga wurin yin sujada ba, har kwanakin tsarkakewarta su cika.

5 Amma idan ‘ya mace ce ta haifa, za ta zama marar tsarki mako biyu kamar a kwanakin hailarta. Za ta ci gaba da zama cikin jinin har kwana sittin da shida.

6 Sa’ad da kwanakin tsarkakewarta na haihuwar ɗa ko ‘ya suka cika, sai ta kai wa firist ɗan rago bana ɗaya, a ƙofar alfarwa ta sujada don hadaya ta ƙonawa, da ɗan tattabara, ko kurciya na yin hadaya don zunubi.

7 Sai ya miƙa ga Ubangiji, ya yi kafara dominta, za ta kuwa tsarkaka. Wannan shi ne abin da ya wajaba ga wanda ta haifi ɗa ko ‘ya.

8 Amma idan ɗan rago ya fi ƙarfinta, sai ta kawo kurciyoyi biyu, ko ‘yan tattabarai biyu, ɗaya don hadaya ta ƙonawa, ɗayan kuwa don yin hadaya don zunubi. Firist kuwa zai yi kafara dominta, za ta kuwa tsarkaka.

Categories
L. FIR

L. FIR 13

Dokoki a kan Kuturta

1 Ubangiji ya ba Musa da Haruna waɗannan ka’idodi.

2 Idan mutum yana da kumburi a fatar jikinsa, ko ɓamɓaroki ko tabo, har ya zama kamar cutar kuturta, sai a kai shi wurin Haruna, firist, ko ɗaya daga cikin zuriyarsa, firistoci.

3 Firist ɗin zai dudduba cutar da take a fatar jikin mutumin. Idan gashin da yake wurin cutar ya rikiɗa ya zama fari, zurfin cutar kuma ya zarce fatar jikinsa, wannan cuta kuturta ce. Firist ɗin da ya dudduba shi zai hurta, cewa, mutumin marar tsarki ne.

4 Amma idan tabon fari ne, zurfinsa kuwa bai zarce fatar ba, gashin kuma da yake cikinsa bai rikiɗa ya zama fari ba, sai firist ya kulle mai ciwon har kwana bakwai.

5 A rana ta bakwai firist zai ƙara dudduba shi, in ya ga cutar ba ta yaɗu a fatar jikin mutumin ba, sai ya sāke kulle shi waɗansu kwana bakwai kuma.

6 A rana ta bakwai sai firist ya sāke dubansa, idan ciwon ya dushe, cutar kuma ba ta yaɗuwa a fatar jikin mutumin, firist zai hurta, cewa, mutumin tsattsarka ne, ɓamɓaroki ne kawai, sai ya wanke tufafinsa.

7 Amma idan ɓamɓaroki ya yaɗu a cikin fatar jikin mutumin bayan da ya nuna kansa ga firist don tsarkakewa, sai ya sāke zuwa gaban firist.

8 Firist zai duba shi, idan ɓamɓaroki ya yaɗu a fatar, sai firist ya hurta, cewa, mutumin marar tsarki ne, ba ɓamɓaroki ba ne, kuturta ce.

9 Sa’ad da cutar kuturta ta kama mutum, sai a kai shi wurin firist.

10 Firist kuwa ya dudduba shi, in akwai kumburi a fatar jikin mutum wanda ya rikiɗar da gashin wurin ya zama fari, in kuma akwai sabon miki a kumburin,

11 to, kuturta ce da ta daɗe a fatar jikinsa. Firist kuwa zai hurta, cewa, mutumin marar tsarki ne, ba za a kulle shi ba, gama ya tabbata marar tsarki ne.

12 Idan kuturtar ta faso a fatar jikin mutum har ta rufe fatar jikin mutumin daga kai zuwa ƙafa a iyakar ganin firist,

13 firist ɗin zai duba shi, in kuturtar ta rufe jikin duka, zai hurta, cewa, mutumin tsarkakakke ne daga cutar, gama kuturtar ta rikiɗa, ta yi fari fat, don haka ya tsarkaka.

14 Amma a ranar da aka ga sabon miki a jikinsa zai zama marar tsarki.

15 Sai firist ya dudduba sabon mikin ya hurta, cewa, mutumin marar tsarki ne, sabon miki fa marar tsarki ne, gama kuturta ce.

16 Idan kuma sabon mikin ya juya, ya rikiɗa ya zama fari, zai tafi wurin firist.

17 Firist ɗin zai dudduba shi, idan cutar ta rikiɗa ta zama fara, sai firist ya hurta, cewa, mutumin tsarkakakke ne, gama ya tsarkaka.

18 Amma idan akwai wanda yake da ƙurjin da ya warke,

19 idan kuma akwai tabo jaja-jaja, da fari-farin tabo, sai a nuna wa firist.

20 Firist zai dudduba shi, idan zurfin kumburin ko tabon rikiɗa fari, sai firist ya hurta, cewa, mutumin marar tsarki ne, cutar kuturta ce ta faso a ƙurjin.

21 Amma idan firist ya dudduba shi ya ga gashin wurin bai yi fari ba, zurfin ƙurjin kuma bai zarce fatar ba, amma ya dushe, sai firist ɗin ya kulle shi kwana bakwai.

22 Amma idan ƙurjin ya bazu a fatar jikin, sai firist ya hurta, cewa, shi mutumin marar tsarki ne, kuturta ce.

23 Amma idan tabon ya tsaya wuri ɗaya, bai bazu ba, tabon miki ke nan, sai firist ya hurta, cewa, shi mutumin tsarkakakke ne.

24 Ko kuma idan mutum ya ƙuna a fatar jiki, naman wurin ƙunar kuwa ya yi tabo jaja-jaja, da fari-fari, ko fari,

25 sai firist ya dudduba shi, in gashin wurin tabo ya zarce fatar, to, kuturta ce ta faso a cikin ƙunar, sai firist ya hurta, cewa, shi mutumin marar tsarki ne, cutar kuturta ce.

26 Amma idan firist ya dudduba tabon, ya ga gashin tabon bai zama fari ba, zurfin tabon kuma bai zarce fatar ba, amma ya dushe, firist zai kulle shi kwana bakwai.

27 A kan rana ta bakwai, zai sāke dubansa, idan tabon yana bazuwa cikin fatar, sai firist ya hurta, cewa, shi mutumin marar tsarki ne, kuturta ce.

28 Amma idan tabon ya tsaya a wuri ɗaya, bai bazu a fatar jikin ba, ya kuma dushe, to, kumburi ne na ƙunar, firist zai hurta, cewa, shi mutumin tsarkakakke ne, gama tabon ƙuna ne.

29 Sa’ad da mace ko namiji na da cuta a kai, ko a gemu,

30 sai firist ya dudduba cutar, in ya ga zurfin cutar ya zarce fatar, gashin kuma da yake wurin ya zama rawaya, siriri kuma, firist zai hurta, cewa, shi mutumin marar tsarki ne, miki ne, ciwon da za a iya ɗauka ne.

31 Amma idan firist ya duba mikin, ya ga zurfinsa bai zarce fatar ba, ba kuma baƙin gashi a ciki, sai firist ya kulle mai miki har kwana bakwai.

32 A rana ta bakwai kuma firist zai duba cutar, idan mikin bai bazu ba, babu kuma rawayan gashi a cikinsa, zurfin mikin kuwa bai zarce fatar ba,

33 zai aske kansa, amma ba zai aske mikin ba, sai firist ya sāke kulle mai mikin har waɗansu kwana bakwai.

34 A rana ta bakwai firist zai dudduba mikin, idan mikin bai bazu ba, zurfinsa kuma bai zarce fatar ba, sai firist ya hurta, cewa, shi mutumin tsarkakakke ne, sai mutumin ya wanke tufafinsa, ya tsarkaka ke nan.

35 Amma idan mikin ya bazu bayan tsarkakewarsa,

36 sai firist ya dudduba shi, idan mikin ya bazu a fatar, ba lalle ne ya nemi rawayan gashi ba, shi mutumin marar tsarki ne.

37 Amma idan a ganinsa mikin bai yaɗu ba, baƙin gashi ya tsiro ya kuma yi tsawo a wurin, mikin ya warke ke nan, mutumin ya tsarkaka, firist kuwa zai hurta, cewa, shi mutumin tsarkakakke ne.

38 Idan a fatar jikin mace ko namiji akwai fararen tabbai,

39 sai firist ya dudduba, idan tabban toka-toka ne, mawanki ne ya faso a fatar, shi tsarkakakke ne.

40 Idan gashin kan mutum ya zube, ya zama mai sanƙo ke nan, amma shi tsattsarka ne.

41 Idan gashin goshin mutum ya zube, ya yi sanƙo ke nan, amma shi tsattsarka ne.

42 Idan a sanƙon ko a gaban goshi akwai tabon cuta jaja-jaja da fari-fari, to, kuturta ce ta faso a sanƙonsa ko gaban goshinsa.

43 Firist kuwa zai dudduba shi, idan an ga kumburin jaja-jaja da fari-fari ne a sanƙon kansa, ko a gabansa kamar alamar kuturta a fata jikinsa,

44 to, kuturu ne shi, marar tsarki. Firist zai hurta, cewa, shi mutumin marar tsarki ne, cutar kuturta tana kansa.

45 Mai kuturta zai sa yagaggun tufafinsa, ya bar gashin kansa ba gyara, sa’an nan ya rufe leɓensa na sama, ya ta da murya, ya riƙa cewa, “Marar tsarki, marar tsarki.”

46 Muddin yana da cutar, zai zama marar tsarki. Zai zauna shi kaɗai a bayan zango.

47 Idan ana tsammani akwai cutar kuturta a rigar ulu ko ta lilin,

48 ko a tariyar zaren, ko a waɗari, ko a lilin, ko a ulu, ko a cikin fata, ko cikin kowane abu da aka yi da fata,

49 idan cutar ta zama kore-kore, ko jaja-jaja a rigar, ko a fatar, ko a tariyar zaren, ko a waɗarin, ko a kan abin da aka yi da fata, wannan cuta kuturta ce, sai a nuna wa firist.

50 Firist zai dudduba cutar, ya ajiye abin da yake da cutar har kwana bakwai.

51 A rana ta bakwai ɗin zai sāke dudduba cutar, idan cutar ta yaɗu a rigar, ko a tariyar zaren, ko a waɗarin, ko a fatar, komene ne za a yi da fata, wannan cuta muguwar kuturta ce, abin zai zama marar tsarki.

52 Zai ƙone rigar, ko tariyar zaren, ko waɗari na ulu ko na lilin, ko abin da dai aka yi da fata wanda yake da cutar, gama muguwar kuturta ce.

53 Amma idan firist ya dudduba ya ga cutar ba ta yaɗu a rigar, ko a tariyar zaren, ko a waɗarin, ko a abin da aka yi da fata ba,

54 sai firist ya umarta a wanke abin da yake da cutar, ya sāke ajiye shi har kwana bakwai kuma.

55 Firist kuma zai sāke duban abin da yake da cutar bayan da aka wanke shi, idan ya ga launin cutar bai sāke ba, ko da cutar ba ta yaɗu ba, abin ya zama marar tsarki ne nan, sai a ƙone shi da wuta, ko tabon cutar yana cikin abin ne, ko a waje.

56 Amma idan firist ɗin ya duba ya ga tabon ya dushe bayan da aka wanke shi, sai ya kece wurin daga fatar, ko tariyar zaren, ko waɗarin.

57 Idan tabon ya sāke bayyana kuma a rigar, ko a tariyar zaren, ko a waɗarin, ko a kan abin da aka yi da fata, ya yaɗu, sai a ƙone abin da yake da kuturtar.

58 Amma da rigar, ko a tariyar zaren, ko a waɗarin, ko kowane abin da aka yi da fata, wanda cutar ta wanku daga shi sa’ad da aka wanke, sai a sāke wanke shi, ya kuwa zama tsarkakakke ke nan.

59 Wannan ita ce dokar da za a bi a kan cutar kuturtar rigar ulu ko ta lilin, ko cutar kuturta ta tariyar zaren, ko ta waɗarin, ko kuma ta kan kowane abu da aka yi da fata, don a tabbatar tsattsarka ne, ko marar tsarki ne.

Categories
L. FIR

L. FIR 14

1 Ubangiji ya ba Musa

2 waɗannan ka’idodi da za a bi a ranar tsarkakewar mai kuturta. Sai a kawo shi ga firist.

3 Firist ɗin zai fita zuwa bayan zango ya dudduba shi. Idan kuturun ya warke daga cutar kuturtar,

4 firist ɗin zai umarta a kawo tsuntsaye biyu masu rai, masu tsabta, da itacen al’ul, da jan alharini, da ɗaɗɗoya domin aikin tsarkakewa.

5 Sai firist ya umarta a yanka tsuntsu ɗaya a kaskon da yake cike da ruwa mai gudu.

6 Ya kuma ɗauki ɗayan tsuntsu, da itacen al’ul, da jan alharini, da ɗaɗɗoya, ya tsoma su cikin jinin tsuntsun da aka yanka a ruwan kaskon.

7 Sai ya yayyafa jinin sau bakwai a kan wanda za a tsarkake daga kuturtar, sa’an nan ya hurta, cewa, mutumin ya tsarkaka, ya kuma saki tsuntsu mai ran ya tafi cikin saura.

8 Shi kuwa wanda za a tsarkake, sai ya wanke tufafinsa, ya aske dukan gashinsa, ya yi wanka da ruwa, zai kuwa tsarkaka. Bayan wannan zai shiga zango, amma kada ya shiga cikin alfarwarsa har kwana bakwai.

9 A kan rana ta bakwai zai aske dukan gashin kansa, da gemunsa, da gashin girarsa, da duk gashin jikinsa. Sai kuma ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai kuwa tsarkaka.

10 A rana ta takwas zai kawo ‘yan raguna biyu bana ɗaya ɗaya marasa lahani da ‘yar tunkiya bana ɗaya marar lahani, da hadaya ta gari rabin garwar gari mai laushi karɓaɓɓe da man zaitun, da rabin moɗa na mai.

11 Firist ɗin da zai tsarkake mutumin zai kawo wanda za a tsarkake da waɗannan abubuwa a gaban Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada.

12 Firist ɗin zai ɗauki ɗan rago ɗaya ya miƙa shi hadaya don diyyar laifi, da rabin moɗa na mai, ya miƙa su don hadaya ta kaɗawa ga Ubangiji.

13 Sa’an nan zai yanka ɗan rago a inda ake yanka hadaya don zunubi da hadaya ta ƙonawa. Tilas ya yi haka domin hadaya ta laifi rabon firist ne kamar hadaya domin zunubi. Hadaya ce mafi tsarki.

14 Firist zai ɗibi jinin hadaya don laifi ya shafa a leɓatun kunnen dama, da bisa babban yatsan hannun dama, da na ƙafar dama na wanda za a tsarkake ɗin.

15 Firist kuwa zai ɗibi man, ya zuba shi a tafin hannunsa na hagu.

16 Ya kuma tsoma yatsan hannunsa na dama a cikin man da yake a tafin hannunsa na hagu, ya yayyafa man da yatsansa sau bakwai a gaban Ubangiji.

17 Sauran man da ya ragu a tafin hannunsa, sai ya shafa shi a leɓatun kunnen dama na wanda za a tsarkake, da bisa babban yatsan hannunsa na dama, da na ƙafar dama. Wato, za a shafa man a inda aka shafa jinin hadaya don laifin.

18 Sauran man kuma da ya ragu cikin tafin hannunsa, firist ɗin zai shafa a kan wanda za a tsarkake. Firist zai yi kafara dominsa gaban Ubangiji.

19 Sai firist ya miƙa hadaya don zunubi domin ya yi kafara, don rashin tsarkin mutumin. Daga baya ya yanka hadaya ta ƙonawa.

20 Firist kuma zai miƙa hadaya ta ƙonawa da hadaya ta gari a bisa bagaden. Da haka zai yi kafara dominsa, shi kuwa zai tsarkaka.

21 Amma idan matalauci ne, har ba zai iya samun waɗannan abubuwa ba, sai ya kawo ɗan rago ɗaya domin hadaya don laifi, a yi hadaya ta kaɗawa, a yi kafara dominsa. Ya kuma kawo humushin garwa na gari mai laushi kwaɓaɓɓe da man zaitun don yin hadaya ta gari, da rabin moɗa na mai,

22 da kuma kurciyoyi biyu, ko ‘yan tattabarai biyu yadda dai ya iya. Ɗayan domin hadaya don zunubi, ɗayan kuma don hadaya ta ƙonawa.

23 A rana ta takwas zai kawo su wurin firist don tsarkakewarsa a ƙofar alfarwa ta sujada a gaban Ubangiji.

24 Sai firist ya ɗauki ɗan rago da man zaitun, ya miƙa su hadaya ta kaɗawa ga Ubangiji.

25 Sa’an nan ya yanka ɗan ragon don laifi, ya ɗibi jinin hadaya don laifin, ya shafa a leɓatun kunnen dama na mutumin da za a tsarkake, da a babban yatsan hannunsa na dama, da ƙafarsa ta dama.

26 Firist ɗin kuma zai ɗibi man ya zuba cikin tafin hannunsa na hagu.

27 Sai ya yayyafa man da yake cikin tafin hannunsa na hagu sau bakwai a gaban Ubangiji da yatsansa na hannun dama.

28 Ya kuma shafa man da ya ragu cikin hannunsa a leɓatun kunnen dama na wanda za a tsarkake, da a babban yatsan hannun damansa, da kuma a babban yatsan ƙafar damansa, a inda aka shafa jinin hadaya don laifin.

29 Sauran man da yake cikin tafin hannunsa zai zuba a bisa wanda ake tsarkakewar, ya yi kafara dominsa a gaban Ubangiji.

30 Sai mutumin ya ba da kurciyoyi, ko ‘yan tattabarai yadda ya iya,

31 ɗaya domin hadaya don zunubi, ɗaya kuma don hadaya ta ƙonawa tare da hadaya ta gari. Firist ɗin kuma zai yi kafara a gaban Ubangiji domin wanda ake tsarkakewar.

32 Wannan ita ce doka a kan mai ciwon kuturta wanda ba shi da isasshen abin bayarwa don yin hadayun tsarkakewarsa.

33 Sai kuma Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,

34 “Sa’ad da kuka shiga ƙasar Kan’ana wadda nake ba ku ku mallaka, zan sa kuturta ta yaɗu a gidajenku.” Sa’an nan Ubangiji ya ba su waɗannan ka’idodi.

35 Mutumin da ya ga kuturta a gidansa, tilas ya je ya faɗa wa firist.

36 Firist kuwa ya umarta a fitar da dukan abin da yake cikin gidan kafin ya tafi ya dudduba tabo, domin kada kome da yake cikin gidan ya ƙazantu. Bayan haka sai firist ya shiga, ya duba gidan.

37 Zai dudduba tabon, idan akwai alamar tabon a bangayen gida kore-kore, ko jaja-jaja, idan an ga tabon ya yi zurfi cikin bangon,

38 sai firist ɗin ya fita daga cikin gidan zuwa ƙofa, ya rufe gidan har kwana bakwai.

39 A kan rana ta bakwai, sai firist ɗin ya komo, ya duba. Idan tabon ya yaɗu a jikin bangayen gidan,

40 sai ya umarta a ciccire duwatsun da suke da cutar, a zuba a wuri marar tsarki can bayan birnin,

41 ya sa a kankare jikin gidan duka. Shafen da suka kankare kuwa, sai su zubar da shi a wuri marar tsarki can bayan birnin.

42 Sa’an nan sai su kwaso waɗansu duwatsu, su sa su a wuraren da suka ciccire waɗancan. Sai a kawo laka a shafe gidan.

43 Idan cutar ta sāke ɓulla a cikin gidan bayan da aka ciccire duwatsun, aka kuma kankare gidan, aka yi masa shafe,

44 sai firist ya je ya duba, idan cutar ya yaɗu a gidan, to, muguwar kuturta ce, gidan marar tsarki ne.

45 Sai a rushe gidan, a kwashe duwatsun gidan, da katakansa, da shafensa duka a zubar bayan birni a wuri marar tsarki.

46 Duk wanda ya shiga gidan bayan da an rufe shi, zai ƙazantu har maraice.

47 Wanda kuma ya kwana cikin gidan, sai ya wanke tufafinsa, haka kuma wanda ya ci abinci cikin gidan, zai wanke tufafinsa.

48 Amma idan firist ɗin ya zo, ya dudduba, ya ga tabon bai yaɗu a gidan ba, bayan da an yi wa gidan shafe, sai firist ya hurta, cewa, gidan tsattsarka ne domin tabon ya warke.

49 Don tsarkakewar gidan, sai maigida ya kawo ‘yan tsuntsaye biyu, da itacen al’ul, da jan alharini, da ɗaɗɗoya.

50 Sai a yanka tsuntsu ɗaya a kasko cike da ruwa mai gudu.

51 Zai ɗauki itacen al’ul, da ɗaɗɗoya, da jan alharini, da ɗayan tsuntsu mai ran, ya tsoma su cikin jinin tsuntsun da aka yanka a ruwan kaskon, ya yayyafa wa gidan sau bakwai.

52 Da haka zai tsarkake gidan da jini tsuntsun, da ruwa mai gudu, da tsuntsu mai ran, da itacen al’ul, da ɗaɗɗoya, da jan alharini.

53 Sa’an nan ya saki tsuntsu mai ran daga birni ya tafi saura. Ta haka zai yi kafara domin gidan, gidan kuwa zai tsarkaka.

54 Waɗannan su ne dokoki a kan cuce-cucen da akan ɗauka, da

55 kuturta a tufafi ko a jikin gida,

56 da kumburi, da ɓamɓaroki, ko tabo,

57 don a tabbatar lokacin da suke tsarkakakku da lokacin da ba su da tsarki.

Categories
L. FIR

L. FIR 15

Ƙazanturwar Namiji ko Mace

1 Ubangiji ya ba Musa da Haruna waɗannan ka’idodi

2 domin jama’ar Isra’ila. Duk lokacin da wani namiji yake ɗiga daga al’aurarsa, ƙazantacce ne.

3 Ko al’aurar tana ɗiga ko ta daina shi dai ƙazantacce ne.

4 Kowane gado da mai ɗigan ya kwanta a kai ya ƙazantu, da kowane abu da ya zauna a kai ya ƙazantu.

5 Duk wanda ya taɓa gadonsa, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

6 Duk wanda kuma ya zauna a kan kowane abin da mai ɗigar ya zauna a kai, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

7 Wanda kuma ya taɓa jikin mai ɗigar, sai ya wanke tufafinsa ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

8 Idan mai ɗigar ya tofar da yau a kan wanda yake da tsabta, sai mutumin ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

9 Kowane sirdi da mai ɗigar ya zauna a kai zai ƙazantu.

10 Duk wanda ya taɓa kowane abin da yake ƙarƙashin sirdin zai ƙazantu har maraice, duk kuma wanda ya ɗauki wannan abu, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

11 Duk wanda kuma mai ɗigar ya taɓa da hannunsa da bai wanke ba, sai wanda aka taɓa ɗin ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

12 Kaskon da mai ɗigar ya taɓa, sai a fasa shi, amma idan akushi ne sai a wanke shi da ruwa.

13 Sa’ad da mai ɗigar ya warke, sai ya ƙidaya ranaku bakwai don tsarkakewarsa, ya wanke tufafinsa, ya yi wanka a ruwa mai gudu, zai tsarkaka.

14 A kan rana ta takwas zai kawo kurciyoyi biyu, ko ‘yan tattabarai biyu a gaban Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada, ya ba firist.

15 Sai firist ya yi hadaya da su, ɗaya don hadayar zunubi, ɗaya kuma don hadaya ta ƙonawa. Firist ɗin zai yi kafara dominsa a gaban Ubangiji domin ɗigarsa.

16 Idan maniyyin mutum ya zubo, sai ya wanke jikinsa duka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

17 Kowace riga ko fatar da maniyyin ya taɓa, sai a wanke da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

18 Idan mutum ya kwana da mace, sai su yi wanka da ruwa, sun ƙazantu har maraice.

19 Sa’ad da mace take haila irin ta ka’ida, za ta ƙazantu har kwana bakwai, duk wanda ya taɓa ta kuwa zai ƙazantu har maraice.

20 Duk abin da ta kwana a kai a lokacin rashin tsarkinta zai ƙazantu, haka kuma abin da ta zauna a kai zai ƙazantu.

21 Wanda kuma ya taɓa gadonta, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

22 Haka kuma duk wanda ya taɓa kowane abin da ta zauna a kai, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

23 Ko gado ne, ko kuma kowane abin da ta zauna a kai, sa’ad da wani ya taɓa shi zai ƙazantu har maraice.

24 Idan kuma wani ya kwana da ita, rashin tsarkinta zai shafe shi. Zai zama marar tsarki har kwana bakwai. Kowane gado da ya kwanta a kai zai ƙazantu.

25 Idan zubar jinin hailar macen ya yi kwanaki da yawa, ko kuwa kwanakin hailarta sun zarce ka’ida, a duk kwanakin zubar jininta za ta lizima cikin rashin tsarki daidai kamar lokacin hailarta.

26 Kowane gado da ta kwanta a kai a kwanakin zubar jininta, zai zama ƙazantacce, daidai kamar lokacin hailarta. Kowane abin da ta zauna a kai zai ƙazantu kamar a lokacin hailarta.

27 Wanda duk ya taɓa waɗannan abubuwa zai ƙazantu, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.

28 Bayan da hailarta ta tsaya, za ta ƙidaya kwanaki bakwai, bayan haka za ta tsarkaka.

29 A rana ta takwas sai ta kawo ‘yan kurciyoyi biyu, ko ‘yan tattabarai, a wurin firist a ƙofar alfarwa ta sujada.

30 Firist ɗin zai miƙa ɗaya hadaya don zunubi, ɗayan kuma don hadaya ta ƙonawa. Firist zai yi kafara dominta a gaban Ubangiji saboda rashin tsarkinta.

31 Ta haka za ka tsarkake jama’ar Isra’ila daga rashin tsarkinsu, domin kada su mutu saboda rashin tsarkinsu ta wurin ƙazantar da alfarwata wadda take tsakiyarsu.

32 Waɗannan su ne ka’idodi a kan wanda yake ɗiga, da wanda yake zubar da maniyyi, ƙazantacce ne.

33 Haka kuma wadda take haila, da kowane namiji ko mace, da yake ɗiga, da namijin da ya kwana da mace marar tsarki.

Categories
L. FIR

L. FIR 16

Ranar Kafara

1 Sai Ubangiji ya yi magana da Musa bayan rasuwar ‘ya’yan Haruna, maza biyu, sa’ad da suka hura wuta marar tsarki a gaban Ubangiji, suka mutu.

2 Ubangiji kuma ya ce wa Musa, “Faɗa wa ɗan’uwanka Haruna kada ya riƙa shiga Wuri Mafi Tsarki bayan labule ko yaushe, wato, a gaban murfi wanda yake bisa akwatin alkawari, domin kada ya mutu, gama zan bayyana a cikin girgije a kan murfin.

3 Amma sai Haruna ya shiga Wuri Mafi Tsarki bayan da ya kawo ɗan bijimi domin yin hadaya don zunubi, da rago don yin hadaya ta ƙonawa.”

4 Sa’an nan Ubangiji ya ba Musa ka’idodin nan. Sai Haruna ya sa zilaika ta lilin tsattsarka, ya ɗaura mukuru na lilin, ya yi ɗamara da abin ɗamara na lilin, ya naɗa rawani na lilin, waɗannan su ne tsattsarkar sutura. Zai yi wanka da ruwa, sa’an nan ya sa su.

5 Zai karɓi bunsuru biyu daga taron jama’ar Isra’ila domin yin hadaya don zunubi, da rago ɗaya don yin hadaya ta ƙonawa.

6 Haruna zai miƙa bijimi na yin hadaya don zunubi saboda kansa. Zai yi kafara don kansa da gidansa.

7 Zai kuma kawo bunsuran nan biyu a gaban Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada.

8 Sa’an nan ya jefa kuri’a kan bunsuran nan biyu. Kuri’a ɗaya don Ubangiji, ɗaya kuma domin Azazel.

9 A wanda kuri’ar Ubangiji ta faɗa a kansa, sai Haruna ya miƙa shi hadaya don zunubi ga Ubangiji.

10 Amma a wanda kuri’ar Azazel ta faɗa a kansa, sai a miƙa shi da rai a gaban Ubangiji, a yi kafara da shi, a kora shi can cikin jeji domin Azazel.

11 Haruna kuma zai miƙa bijimi na yin hadaya don zunubin kansa, ya yi kafara don kansa da gidansa. Zai yanka bijimi na yin hadaya don zunubin kansa.

12 Zai ɗauki faranti cike da garwashin wuta daga bagaden da yake a gaban Ubangiji, ya kuma cika hannunsa biyu da turare mai ƙanshi, ya shigar da shi bayan labulen.

13 Zai zuba turaren a wuta a gaban Ubangiji, domin hayaƙi ya tunnuke ya rufe murfi wanda yake a kan akwatin alkawari, don kada ya mutu.

14 Sai ya ɗibi jinin bijimin, ya yayyafa da yatsansa a gefen gabas na murfin, zai kuma yayyafa jinin a gaban murfin sau bakwai.

15 Sai kuma ya yanka bunsuru na yin hadaya don zunubin jama’ar ya shigar da jinin bayan labulen. Zai sa jinin kamar yadda ya yi da jinin bijimin, ya yayyafa shi a kan murfin, da gaban murfin.

16 Da haka zai yi kafara domin Wuri Mai Tsarki saboda ƙazantar mutanen Isra’ila, da laifofinsu, da dukan zunubansu. Haka kuma zai yi wa alfarwa ta sujada, wadda take a wurinsu, a tsakiyar ƙazantarsu.

17 Kada kowa ya kasance cikin alfarwar sujada lokacin da Haruna ya shiga Wuri Mafi Tsarki domin ya yi kafara don kansa, da gidansa, da dukan taron jama’ar Isra’ila, sai lokacin da ya fita.

18 Sa’an nan zai fita ya tafi wurin bagade wanda yake gaban Ubangiji don ya yi kafara dominsa. Zai ɗibi jinin bijimin da na bunsurun, ya shafa wa zankayen bagaden a kewaye.

19 Zai kuma yayyafa jinin da yatsansa har sau bakwai a kan bagaden, ya tsabtace shi, ya tsarkake shi daga ƙazantar jama’ar Isra’ila.

20 A sa’ad da ya gama yin kafara don Wuri Mai Tsarki, da alfarwa ta sujada, da bagaden, sai ya miƙa bunsuru ɗin mai rai.

21 Haruna zai ɗibiya hannuwansa duka biyu a kan kan bunsurun mai rai, ya hurta muguntar Isra’ilawa duka a bisa bunsurun, da dukan laifofinsu, da dukan zunubansu. Zai ɗibiya su a kan kan bunsurun, ya kora shi cikin jeji ta hannun wanda aka shirya zai kora shi.

22 Bunsurun zai ɗauki muguntarsu duka a kansa zuwa jeji. Mutumin kuwa zai sake shi can a jeji.

23 Sa’an nan Haruna zai shiga alfarwa ta sujada, ya tuɓe tufafinsa na lilin waɗanda ya sa sa’ad da ya shiga Wuri Mafi Tsarki, ya ajiye su a nan.

24 Zai kuma yi wanka da ruwa a wuri mai tsarki, sa’an nan ya sa tufafinsa, ya je, ya miƙa hadayarsa ta ƙonawa, da hadaya ta ƙonawa don jama’a, domin ya yi kafara don kansa da jama’a.

25 Zai ƙone kitsen hadaya don zunubi a bisa bagaden.

26 Shi wanda ya kore bunsurun Azazel, sai ya wanke tufafinsa ya yi wanka da ruwa, bayan haka yana iya komawa cikin zango.

27 Bijimin da bunsurun da aka yi hadaya don zunubi da su, waɗanda aka yi kafara da jininsu a Wuri Mafi Tsarki, sai a kai su bayan zangon, a ƙone fatunsu, da namansu, da tarosonsu.

28 Shi wanda ya ƙone su, zai wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, bayan haka ya iya komawa zangon.

29 Waɗannan za su zama farillai a gare su har abada. A rana ta goma ga watan bakwai za su ƙasƙantar da kansu, ba za su yi kowane irin aiki ba, ko ɗan ƙasa, ko baƙon da yake cikinsu.

30 Gama a wannan rana za a yi kafara dominsu, domin a tsarkake su daga dukan zunubansu, su zama tsarkakakku a gaban Ubangiji.

31 Wannan rana muhimmiya ce don hutawa a gare su. Za su ƙasƙantar da kansu, wannan farilla ce har abada.

32 Firist kuma da aka naɗa ya zama firist a madadin mahaifinsa, zai yi kafara yana saye da tufafin lilin masu tsarki.

33 Zai yi kafara domin Wuri Mai Tsarki, da alfarwa ta sujada, da bagaden. Sa’an nan kuma ya yi kafara domin firistocin, da dukan taron jama’ar.

34 Wannan zai zama dawwamammiyar farilla a gare su. Za a riƙa yin kafara domin jama’ar Isra’ila saboda zunubansu duka sau ɗaya a shekara.

Sai Musa ya aikata kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

Categories
L. FIR

L. FIR 17

Wuri Ɗaya domin Yin Hadaya

1 Ubangiji ya umarce Musa,

2 ya faɗa wa Haruna da ‘ya’yansa maza, da dukan mutanen Isra’ila waɗannan ka’idodi.

3 Idan Ba’isra’ile ya yanka sa, ko ɗan rago, ko akuya a cikin zango, ko a bayan zango,

4 bai kuwa kawo shi a ƙofar alfarwa ta sujada don ya miƙa shi sadaka ga Ubangiji a gaban alfarwa ta sujada ba, alhakin jinin da ya zubar yana bisa kansa, za a fitar da wannan mutum daga cikin jama’arsa.

5 Manufar wannan umarni ce domin Isra’ilawa su riƙa kawo hadayunsu, waɗanda sukan yi a filin saura ga Ubangiji a wurin firist a ƙofar alfarwa ta sujada. Sai su yanka hadayu na salama ga Ubangiji.

6 Sai firist ya yayyafa jinin a kan bagaden Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada. Zai ƙone kitsen don ya ba da ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji.

7 Kada kuma su ƙara yin hadayunsu ga gumaka masu siffar bunsurai waɗanda suka bauta wa. Wannan doka ce ta har abada a gare su har dukan zamanansu.

8 Kowane Ba’isra’ile, ko baƙon da yake baƙunta a cikinsu, wanda ya miƙa hadaya ta ƙonawa ko sadaka,

9 amma bai kawo ta a ƙofar alfarwa ta sujada, ya miƙa ta ga Ubangiji ba, sai a fitar da wannan mutum daga cikin jama’a.

An Hana Cin Jini

10 Idan wani Ba’isra’ile, ko baƙon da yake baƙunta a cikinsu ya ci jini, Ubangiji zai yi gāba da wannan mutum da ya ci jinin ya fitar da shi daga cikin jama’a.

11 Gama ran nama yana cikin jinin, Ubangiji kuwa ya ba su shi a bisa bagade domin a yi wa rayukansu kafara, gama da jini ake kafara saboda akwai rai a cikinsa.

12 Saboda haka Ubangiji ya faɗa wa mutanen Isra’ila, cewa, kada wani daga cikinsu, ko baƙon da yake baƙunta a cikinsu, ya ci jini.

13 Idan kowane Ba’isra’ile, ko baƙon da yake baƙunta a cikinsu ya tafi farauta, ya kama nama, ko tsuntsu da ake ci, sai ya zub da jininsa, ya rufe da ƙasa.

14 Gama ran dukan nama yana cikin jininsa, saboda haka Ubangiji ya faɗa wa mutanen Isra’ila, cewa, faufau ba za su ci jinin kowace dabba ba, gama ran kowace dabba yana cikin jininta. Duk wanda kuwa ya ci shi, za a raba shi da jama’a.

15 Duk wanda ya ci mushe, ko abin da namomin jeji suka yayyaga, ko shi Ba’isra’ile ne, ko baƙo ne, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, ya ƙazantu har maraice, sa’an nan zai tsarkaka.

16 Amma idan bai wanke su ba, bai kuwa yi wanka ba, alhakinsa yana kansa.

Categories
L. FIR

L. FIR 18

An Haramta yin Lalata

1 Ubangiji kuma ya ce wa Musa

2 ya faɗa wa mutanen Isra’ila cewa, “Ni ne Ubangiji Allahnku.

3 Kada ku yi kamar yadda suke yi a ƙasar Kan’ana inda nake kai ku. Kada ku kiyaye dokokinsu.

4 Amma ku bi ka’idodina, ku yi tafiya a cikinsu, gama ni ne Ubangiji Allahnku.

5 Domin haka sai ku kiyaye dokokina da ka’idodina waɗanda ta wurin kiyaye su mutum zai rayu. Ni ne Ubangiji.”

6 Ubangiji ya ba da waɗannan ka’idodi kuma. Kada kowane mutum ya kusaci ‘yar’uwarsa don ya kwana da ita. Ya ce, “Ni ne Ubangiji.”

7 Kada ya ƙasƙantar da mahaifinsa, wato, kada ya kwana da mahaifiyarsa, kada ya ƙasƙantar da mahaifiyarsa.

8 Kada ya kwana da matar mahaifinsa, gama ita matar mahaifinsa ce.

9 Kada ya kwana da ‘yar’uwarsa, ‘yar mahaifinsa, ko ‘yar mahaifiyarsa, ko a gida ɗaya aka haife ta da shi, ko a wani gida dabam.

10 Kada ya kwana da jikanyarsa gama zai zama ƙasƙanci a gare shi.

11 Kada ya kwana da ‘yar matar mahaifinsa, wadda mahaifinsa ya haifa, tun da yake ita ‘yar’uwarsa ce.

12 Kada ya kwana da bābarsa gama ‘yar’uwar mahaifinsa ce.

13 Kada ya kwana da innarsa, gama ita ‘yar’uwar mahaifiyarsa ce.

14 Kada ya kwana da matar ɗan’uwan mahaifinsa, gama ita ma bābarsa ce.

15 Kada ya kwana da matar ɗansa, gama ita surukarsa ce.

16 Kada ya kwana da matar ɗan’uwansa, gama ita matar ɗan’uwansa ce.

17 In ya kwana da mace, kada kuma ya kwana da ‘yarta, ko jikanyarta, wannan duk haramun ne, gama su danginsa ne na kusa.

18 Muddin matarsa tana da rai, ba zai auro ƙanwarta ta zama kishiyarta ba.

19 Kada ya kwana da mace a lokacin hailarta, gama ba ta da tsarki.

20 Kada ya kwana da matar maƙwabcinsa don kada ya ƙazantar da kansa.

21 Kada ya ba da ɗaya daga cikin ‘ya’yansa don a miƙa wa Molek, gama yin haka zai ƙasƙantar da sunan Allah. Shi Ubangiji ne.

22 Kada ya yi luɗu, gama Allah yana ƙin wannan.

23 Kada wani ko wata su kwana da dabba don kada su wofintar da kansu.

24 Kada su ƙazantar da kansu da irin waɗannan abubuwa, gama da irin waɗannan abubuwa ne al’umman da Ubangiji yake kora a gabansu suka ƙazantar da kansu.

25 Har ƙasar ma ta ƙazantu, don haka Ubangiji ya hukunta muguntarta, ƙasar kuwa ta amayar da mazaunanta.

26 Amma su sai su kiyaye dokokin Ubangiji da ka’idodinsa. Kada su aikata ko ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa na banƙyama, ko haifaffe na gida, ko baƙon da yake baƙunta a cikinsu.

27 Gama mazaunan ƙasar da suka riga su, sun aikata dukan abubuwa masu banƙyaman nan, don haka ƙasar ta ƙazantu.

28 Kada kuma ƙasar ta amayar da su idan sun ƙazantar da ita, kamar yadda ta amayar da al’ummar da ta riga su zama a cikinta.

29 Duk wanda ya aikata abu ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa masu banƙyaman nan za a raba shi da jama’a.

30 Ubangiji kuma ya ce, “Don haka sai ku kiyaye umarnina, kada ku kiyaye dokoki na banƙyama waɗanda aka kiyaye kafin ku zo, kada ku ƙazantu da su. Ni ne Ubangiji Allahnku.”

Categories
L. FIR

L. FIR 19

Dokoki a kan Tsarki da Yin Adalci

1 Ubangiji ya ce wa Musa

2 ya faɗa wa dukan taron jama’ar Isra’ila cewa, “Ku zama tsarkakakku, gama ni Ubangiji Allahnku mai tsarki ne.

3 Sai ko wannenku ya girmama mahaifiyarsa da mahaifinsa, ya kuma kiyaye lokatan sujada. Ni ne Ubangiji Allahnku.

4 “Kada ku juya ku bi gumaka, ko kuma ku yi wa kanku gumaka na zubi. Ni ne Ubangiji Allahnku.

5 “Sa’ad da za ku miƙa hadaya ta salama ga Ubangiji, ku miƙa ta domin a karɓe ku.

6 A cinye ta a ranar da kuka miƙa ta ko kuwa kashegari. Abin da ya ragu har kwana na uku, sai a ƙone da wuta,

7 gama ta zama abar ƙyama, idan aka ci ta a rana ta uku, ba za ta zama abar karɓa ba.

8 Wanda ya ci ta a rana ta uku ɗin, zai zama da laifi, domin ya tozartar da abu mai tsarki na Ubangiji, sai a raba wannan mutum da jama’a.

9 “Sa’ad da kuke girbin amfanin ƙasarku, kada ku girbe gefen gonakinku, kada kuma ku yi kala bayan da kuka gama girbi.

10 Kada ku girbe kalar gonar inabinku, kada kuma ku tattara ‘ya’yan inabinku da suka kakkaɓe, sai ku bar wa matalauta, da baƙo. Ni ne Ubangiji Allahnku.

11 “Kada ku yi sata, ko ku cuci wani, ko ku yi ƙarya.

12 Kada ku yi alkawari da sunana idan dai ba ku da niyyar cika shi, wannan zai jawo wa sunana ƙasƙanci. Ni ne Ubangiji Allahnku.

13 “Kada ku zalunci kowa ko ku yi masa ƙwace. Kada kuma ku bar lokacin biyan hakkin ma’aikaci ya kai har gobe.

14 Kada ku zagi kurma, kada kuma ku sa wa makaho abin tuntuɓe, amma ku ji tsoron Ubangiji Allahnku. Ni ne Ubangiji.

15 “Ku yi gaskiya da adalci cikin shari’a, kada ku ma ku yi wa matalauci son zuciya, ko ku goyi bayan mawadaci.

16 Kada ku yi ta yaɗa ƙarya game da wani. Sa’ad da wani yake cikin shari’ar kuɓutar da ransa, ku yi magana muddin dai shaidarku za ta taimake shi. Ni ne Ubangiji.

17 “Kada wani ya riƙe ɗan’uwansa da ƙiyayya a zuciyarsa, amma ya daidaita rashin jituwa da shi, don kada ya yi zunubi saboda shi.

18 Kada ya ɗaukar wa kansa fansa a kan wani ko ya yi ta ƙinsa, amma ya ƙaunaci sauran mutane kamar yadda yake ƙaunar kansa. Ni ne Ubangiji.

19 “Sai ku kiyaye dokokina. Kada ku bar dabbobinku su yi barbara da waɗansu iri dabam. Kada ku shuka iri biyu a gonakinku. Kada ku sa tufar da aka yi da ƙyalle iri biyu.

20 “Idan mutum ya kwana da mace wadda take baiwa, wadda kuma wani yake tashinta, tun ba a fanshe ta ba, ko kuwa ba a ‘yanta ta ba, sai a bincike, amma ba za a kashe su ba, domin ita ba ‘yantacciya ba ce.

21 Amma ya kawo rago na yin hadaya don laifinsa ga Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada.

22 Sai firist ya yi kafara da ragon hadaya don laifi saboda laifin mutumin a gaban Ubangiji. Za a kuwa gafarta masa zunubin da ya yi.

23 “Sa’ad da kuka shiga ƙasar, kuka dasa itatuwa iri iri masu ba da ‘ya’ya na ci, ‘ya’yan itatuwan za su zama ƙazantattu a gare ku har shekara uku. A cikin shekarun nan uku ba za ku ci su ba.

24 A shekara ta huɗu ‘ya’yan itatuwan za su tsarkaka. Hadaya ce ta yabo ga Ubangiji.

25 Amma a shekara ta biyar, sai ku ci ‘ya’yan itatuwan domin su ba ku amfani a yalwace. Ni ne Ubangiji Allahnku.

26 “Kada ku ci kowane abu da jininsa, kada kuma ku yi duba, ko sihiri.

27 Kada ku yi wa goshinku da gemunku kwakkwafe saboda matattu,

28 ko ku tsattsaga jikinku, ko kuwa ku yi wa kanku jarfa. Ni ne Ubangiji.

29 “Kada ku ƙasƙantar da ‘ya’yanku mata ta wurin sa su su zama karuwan masujadai, idan kuka yi haka, za ku juya ga gumaka, ƙasar za ta cika da lalata.

30 Sai ku kiyaye lokatan sujada, ku kuma darajanta alfarwata mai tsarki. Ni ne Ubangiji.

31 “Kada ku tafi wurin masu mabiya, kada kuma ku nemi shawarar bokaye, domin kada su sa ku ku ƙazantu. Ni ne Ubangiji Allahnku.

32 “Ku girmama tsofaffi ku darajanta su, gama kuna tsorona. Ni ne Ubangiji.

33 “Idan baƙo ya baƙunce ku a ƙasarku, kada ku cuce shi.

34 Amma ku ɗauke shi tankar ɗan ƙasa, ku ƙaunace shi kamar kanku, gama dā ku ma baƙi ne a ƙasar Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku.

35 “Kada ku cuci wani wajen yin amfani da kowane irin ma’auni na ƙarya, wato, awon tsawo, ko na nauyi, ko na ruwa.

36 Sai ma’auninku na awon nauyi, da mudun awo, da mudun awon abin da yake ruwa ruwa, su zama na gaskiya. Ni ne Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar.

37 Sai ku kiyaye, ku aikata dokokina da umarnaina duka. Ni ne Ubangiji.”

Categories
L. FIR

L. FIR 20

Hukunci a kan Rashin Biyayya

1 Ubangiji ya faɗa wa Musa,

2 ya ce wa mutanen Isra’ila, “Duk Ba’isra’ile da kowane baƙo da yake zaune cikin Isra’ila, wanda ya ba da ɗaya daga cikin ‘ya’yansa ga Molek, lalle ne a kashe shi. Mutanen ƙasar za su jajjefe shi da duwatsu.

3 Ni kaina zan yi gāba da wannan mutum, in raba shi da jama’arsa domin ya ba Molek ɗaya daga cikin ‘ya’yansa, gama ya ƙazantar da alfarwa ta sujada, ya ƙasƙantar da sunana mai tsarki.

4 Idan kuwa mutanen ƙasar ba su kashe mutumin nan, wanda ya ba Molek ɗaya daga cikin ‘ya’yansa ba,

5 ni kaina zan yi gāba da mutumin nan da iyalinsa, da waɗanda suka yarda suka bi Molek tare da shi. Ba zan ƙara ce da su mutanena ba.

6 “Duk wanda yake sha’ani da masu mabiya, ko da bokaye zan yi gāba da wannan mutum, in raba shi da jama’arsa.

7 Sai ku kiyaye kanku da tsarki, gama ni ne Ubangiji Allahnku.

8 Ku kuma kiyaye dokokina, ku aikata su, gama ni ne Ubangiji wanda ya keɓe ku.

9 “Dukan wanda ya zagi mahaifinsa, ko mahaifiyarsa za a kashe shi, gama ya zagi mahaifinsa da mahaifiyarsa. Alhakin jininsa yana wuyansa.

10 “Idan mutum ya yi zina, sai a kashe dukansu biyu, wato, shi da mazinaciyar.

11 Mutumin kuma da ya kwana da matar mahaifinsa, ya ƙasƙantar da mahaifinsa ke nan, su biyu ɗin za a kashe su. Alhakin jininsu yana wuyansu.

12 Duk wanda ya kwana da matar ɗansa, za a kashe su duka biyu ɗin, gama sun yi abin da yake haram. Alhakin jininsu yana wuyansu.

13 Duk mutumin da ya kwana da namiji kamar yadda namiji yake kwana da mace, su biyu ɗin, sun yi aikin ƙazanta, za a kashe su. Alhakin jininsu yana wuyansu.

14 Duk mutumin da ya auri ‘ya tare da mahaifiyarta, wannan mugun abu ne, shi da su biyu ɗin, sai a ƙone su da wuta, don kada mugun abu ya kasance a cikinku.

15 Idan mutum ya kwana da dabba, sai a kashe shi, a kuma kashe dabbar.

16 In kuma mace ta yi ƙoƙari har ta kwana da dabba, sai a kashe matar tare da dabbar, alhakin jininsu yana wuyansu.

17 “Idan mutum ya auri ƙanwarsa ko kuma ‘yar mahaifinsa, sai a ƙasƙantar da su a bainar jama’a, a kuwa kore su daga cikin jama’a. Ya kwana da ƙanwarsa ke nan, tilas su sha hukuncin laifinsu.

18 Idan mutum ya kwana da mace a lokacin hailarta, duka biyunsu za a kore su daga cikin jama’arsu, gama sun karya ka’idodi a kan rashi tsarki.

19 “Idan mutum ya kwana da bābarsa ko innarsa, za a hukunta duka biyunsu saboda abin ƙyama da suka yi.

20 Idan kuma mutum ya kwana da matar kawunsa, ya ƙasƙantar da kawunsa, sai su ɗauki alhakin laifinsu, za su mutu ba haihuwa.

21 Idan mutum ya auri matar ɗan’uwansa, ya yi mugun abu, za su mutu ba haihuwa, gama ya ƙasƙantar da ɗan’uwansa.

22 “Sai fa ku kiyaye dokokina duka, da ka’idodina duka, ku kuma aikata su domin kada ƙasar da nake kai ku ta amayar da ku.

23 Kada ku bi al’adun waɗannan al’ummai, waɗanda nake kora a gabanku, gama sun aikata waɗannan al’amura, don haka nake ƙyamarsu.

24 Amma ni na faɗa muku, za ku gāji ƙasarsu, zan kuwa ba ku ita, ku mallake ta, ƙasar da take da yalwar abinci. Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya keɓe ku daga sauran al’ummai.

25 Domin haka sai ku bambanta tsakanin halattattun dabbobi da haramtattun dabbobi, da tsakanin haramtattun tsuntsaye da halattattun tsuntsaye. Kada ku ƙazantar da kanku da haramtattun dabbobi, ko da tsuntsaye, ko da kowane abu mai rarrafe bisa ƙasa, waɗanda na ware su, su zama haramtattu a gare ku.

26 Sai ku zama tsarkakakku a gare ni, gama ni Ubangiji Mai Tsarki ne, na kuwa keɓe ku daga sauran al’umman duniya don ku zama nawa.

27 “Namiji ko macen da yake da mabiya ko maita, sai a kashe. Za ku jajjefe su da duwatsu, alhakin jininsu yana kansu.”