Categories
L. FIR

L. FIR 21

Tsarkin Firistoci

1 Ubangiji kuma ya umarce Musa, ya faɗa wa ‘ya’yan Haruna, maza, firistoci cewa, “Kada ko wannensu ya ƙazantar da kansa ta wurin gawar mutanensa,

2 sai dai gawar iyalinsa na kurkusa, wato, gawar mahaifiyarsa, da ta mahaifinsa, da ta ɗansa, da ta ‘yarsa, da ta ɗan’uwansa,

3 da ta ‘yar’uwarsa, budurwa, da take kusa da shi, wadda ba ta yi aure ba tukuna. Saboda su ya iya ƙazantar da kansa.

4 Kada ya ƙazantar da kansa saboda dangantakar aure cikin mutanensa.

5 “Kada su aske kansu ƙwal, ko su kwakkwafe gemunsu, ko su tsattsaga jikinsu.

6 Sai su kasance da tsarki, kada su ƙasƙantar da sunana domin su ne masu kawo hadaya ta ci, masu ƙone hadayu da wuta gare ni, don haka sai su kasance da tsarki.

7 Kada firist ya auri karuwa, ko wadda mijinta ya sake ta, gama shi tsattsarka ne gare ni.

8 Dole jama’a su gan su da tsarki, gama suna miƙa hadaya ta ci gare ni. Ni ne Ubangiji, ni mai tsarki ne, na kuwa tsarkake mutanena.

9 ‘Yar firist wadda ta ɓata kanta da yin aikin karuwanci, ta ƙasƙantar da mahaifinta, sai a ƙone ta da wuta.

10 “Firist wanda yake babba cikin ‘yan’uwansa da aka zuba masa man keɓewa, aka kuma keɓe shi ya riƙa sa tufafin firist, kada ya bar gashin kansa buzu-buzu, ko kuwa ya kyakketa tufafinsa.

11 Kada ya kusaci gawa, ko gawar mahaifinsa, ko ta mahaifiyarsa don kada ya ƙazantu.

12 An keɓe shi domina, kada ya ƙazantar da kansa, kada kuwa ya ɓata alfarwa ta sujada ta wurin shiga gidan da gawa take, ko ta mahaifinsa, ko ta mahaifiyarsa ce.

13 Sai ya auri budurwa.

14 Kada ya auri mace wadda mijinta ya rasu, ko sakakkiya, ko karuwa, amma ya auri budurwa daga cikin kabilarsa,

15 domin kada ya ƙazantar da ‘ya’yansa waɗanda ya kamata su zama tsarkakakku. Ni ne Ubangiji, na kuwa keɓe shi ya zama babban firist.”

16 Sai Ubangiji ya umarce Musa

17 ya faɗa wa Haruna cewa, “Kada ko ɗaya daga cikin zuriyarka, da yake da lahani ya kusato garin ya miƙa hadaya ta ci gare ni har abada.

18 Duk mutumin da yake da lahani na makanta, ko gurguntaka, ko rauni a fuska, ko gaɓar da ta fi wata,

19 ko tauyayye a ƙafa ko a hannu,

20 ko mai ƙusumbi, ko wada, ko mai lahani a ido, ko cuta mai sa ƙaiƙayi, ko kirci, ko dandaƙaƙƙe, ba zai kusato garin ya miƙa hadaya ba.

21 Duk mutumin da yake cikin zuriyar Haruna firist, wanda yake da lahani, ba zai kusato garin ya miƙa hadaya ta ci gare ni ba.

22 Amma zai iya ci daga cikin tsattsarkan abincin da aka miƙa mini, da abinci mafi tsarki.

23 Sai dai ba zai kusaci labulen, ko ya tafi kusa da bagaden ba, domin yana da lahani, don kada ya ɓata wuraren yin sujada, gama ni ne Ubangiji, ni kuwa na tsarkake su.”

24 Haka nan kuwa Musa ya faɗa wa Haruna, da ‘ya’yan Haruna, maza, da dukan Isra’ilawa.

Categories
L. FIR

L. FIR 22

Hadayu suna da Tsarki

1 Ubangiji kuma ya umarci Musa

2 ya faɗa wa Haruna, da shi da ‘ya’yansa cewa, “Ku lura da tsarkakakkun abubuwa waɗanda Isra’ilawa suka keɓe domina, don kada ku ƙasƙantar da sunana mai tsarki. Ni ne Ubangiji.

3 Idan kowanne daga cikin dukan zuriyarku ya kusaci tsarkakakkun abubuwa, waɗanda Isra’ilawa suka keɓe domina, lokacin da yake ƙazantacce, wannan mutum ba zai ƙara kasancewa a gabana ba, wannan kuwa zai zama har dukan lokatai masu zuwa. Ni ne Ubangiji.

4 “Daga cikin zuriyar Haruna wanda yake kuturu, ko mai ɗiga, ba zai ci daga cikin tsarkakakkun abubuwa ba, sai lokacin da ya tsarkaka. Duk wanda ya taɓa wani abu marar tsarki na mamaci, ko wanda maniyyinsa yake ɗiga,

5 da duk kuma wanda ya taɓa wani abu mai rarrafe wanda yake ƙazantarwa, ko kuwa wani mutum mai ƙazanta,

6 duk mutumin da ya taɓa kowane irin abu haka, zai ƙazantu har maraice, ba kuwa zai ci daga cikin tsarkakakkun abubuwan nan ba, sai ya yi wanka da ruwa tukuna.

7 To, sa’ad da rana ta faɗi mutumin zai tsarkaka, bayan wannan ya iya cin tsarkakakkun abubuwan nan, gama ko dā ma abincinsa ne.

8 Kada ya ci abin da ya mutu mushe, ko abin da namomin jeji suka yayyaga, don kada ya ƙazantar da kansa. Ni ne Ubangiji.

9 “Domin haka sai su kiyaye umarnaina don kada su yi zunubi su mutu ta wurin karya tsarkakakkun ka’idodina. Ni ne Ubangiji, ni na sa su tsarkaka.

10 “Duk wanda ba daga cikin iyalin firistoci ba, ko da yake zama tare da su ne, ko kuwa an ɗauke shi yana yi musu aiki, ba zai ci daga cikin tsarkakakkun hadayun ba.

11 Amma idan firist ya sayi bawa da kuɗinsa, bawan ya zama dukiyarsa, bawan zai iya ci, haifaffun gidansa kuma za su iya cin tsattsarkan abincin.

12 Idan kuwa ‘yar firist ta auri wani wanda ba firist ba, to, kada ta ci daga cikin tsarkakakkun hadayu.

13 Amma idan ‘yar firist ɗin gwauruwa ce, ko sakakkiya, ba ta kuma da ɗa, ta kuwa koma gidan mahaifinta, sai ta ci daga cikin abincin mahaifinta kamar cikin kwanakin ƙuruciyarta. Amma wani dabam ba zai ci ba.

14 “Idan kuwa har wani mutum dabam ya ci daga cikin tsarkakakken abin ba da saninsa ba, to, sai ya maido abin ga firist, da ƙarin humushin tamanin abin.

15 Firist ba zai ƙasƙantar da tsarkakakkun abubuwan nan da jama’ar Isra’ila suke miƙawa ba,

16 da zai bar mutumin da bai cancanta ya ci ba, wannan zai jawo masa hukunci. Ni ne Ubangiji. Ni na tsarkake hadayun.”

17 Sai Ubangiji ya ce wa Musa,

18 ya yi magana da Haruna da ‘ya’yansa maza, da dukan Isra’ilawa ya ce musu, “Sa’ad da duk Ba’isra’ile ko baƙon da yake zaune a Isra’ila, ya kawo hadaya ta ƙonawa, ko ta wa’adi ce, ko ta yardar rai, dole ne dabbar ta zama marar lahani.

19 Dabbar ta kasance namiji marar lahani idan ana so ta karɓu.

20 Kada ku yi hadaya da abin da yake da lahani, gama Ubangiji ba zai karɓa ba.

21 Idan kuwa wani ya kawo hadaya ta salama ga Ubangiji don cika wa’adi, ko don hadaya ta yardar rai, daga cikin garken shanu, ko na tumaki, da na awaki, sai ya zama cikakke, marar lahani, don ya karɓu.

22 Dabbobi makafi, ko naƙasassu, ko mai gundumi, ko mai ɗiga, ko mai susa, ko mai kirci, kada ku miƙa wa Ubangiji, kada kuma ku yi hadaya ta ƙonawa a bagaden Ubangiji da su.

23 Kwa iya ba da dabba, marar cikakkiyar halitta don hadaya ta yardar rai, amma ba za ku bayar don hadaya ta cika wa’adi ba, ba za a karɓa ba.

24 Kowace dabba kuma da lunsayinta yake da ƙujewa, ko dandaƙewa, ko yagewa, ko yankewa, ba za ku miƙa ta hadaya ga Ubangiji ba, ba kuwa za ku yi hadaya da ita a ƙasarku ba.

25 “Ba kuma za ku karɓi irin dabbobin nan daga hannun baƙo don ku miƙa su hadaya ga Ubangiji ba, marasa tsarki ne tun da yake suna da lahani, ba za a karɓa ba.”

26 Ubangiji ya yi magana da Musa, ya ce,

27 “Sa’ad da kuma aka haifi ɗan maraƙi, ko ɗan rago, ko ɗan akuya, zai yi kwana bakwai tare da uwarsa. A rana ta takwas zuwa gaba, sai a karɓe shi don yin hadaya ta ƙonewa ga Ubangiji.

28 Ba za ku yanka uwar dabbar tare da ɗanta rana ɗaya ba, ko uwar saniya ce, ko ta tunkiya ce.

29 Sa’ad da za ku miƙa hadaya ta godiya ga Ubangiji, sai ku miƙa ta yadda za a karɓa.

30 A ranar ce za a cinye, kada a bar kome ya kai gobe. Ni ne Ubangiji.

31 “Ku yi biyayya da umarnina. Ni ne Ubangiji.

32 Kada ku jawo wa sunana mai tsarki ƙasƙanci, amma sai mutanen Isra’ila su gane, ni mai tsarki ne. Ni ne Ubangiji na kuwa tsarkake ku,

33 na kuma fisshe ku daga ƙasar Masar domin in zama Allahnku. Ni ne Ubangiji.”

Categories
L. FIR

L. FIR 23

Ƙayyadaddun Idodi

1 Ubangiji ya ba Musa

2 waɗannan ka’idodi domin ƙayyadaddun idodi sa’a da Isra’ilawa za su taru domin yin sujada.

3 Cikin kwanaki shida za a yi aiki, amma a rana ta bakwai za a huta ɗungum, gama ranar Asabar ce, tsattsarka. Ko kaɗan ba za a yi aiki a ranar ba a duk inda suke, amma ku yi taruwa ta sujada gama ranar Asabar ta Ubangiji ce.

4 Su yi waɗannan idodi a ƙayyadaddun lokatai.

Idin Ƙetarewa da na Abinci Marar Yisti

5 Da maraice a rana ta goma sha huɗu ga watan fari, ita ce ranar Idin Ƙetarewa ta Ubangiji.

6 Sa’an nan kuma sha biyar ga watan za a yi bikin idin abinci marar yisti na Ubangiji. Za su ci abinci marar yisti har kwana bakwai.

7 Za su yi muhimmin taro a rana ta fari. Ba za su yi aiki mai wuya a ranar ba.

8 A kwana bakwai ɗin za su riƙa miƙa hadaya ta ƙonawa kowace rana ga Ubangiji. Za su kuma yi muhimmin taro a rana ta bakwai ɗin. Ba za su yi aiki mai wuya ba.

9 Ubangiji ya yi magana da Musa, cewa,

10 lokacin da suka shiga ƙasar da Ubangiji yake ba su, sai su kawo wa firist dami na fari na amfanin gonakinsu.

11 Firist ɗin zai kaɗa damin hadaya ta kaɗawa a gaban Ubangiji, don a karɓe su. Firist zai kaɗa hadayar a kashegarin Asabar.

12 A ranar da suka miƙa hadaya ta kaɗawa, za su kuma miƙa wa Ubangiji hadaya ta ƙonawa da ɗan rago bana ɗaya marar lahani.

13 Tare da wannan hadaya kuma, za su miƙa hadaya ta gari, humushi biyu na garwar gari mai laushi kwaɓaɓɓe da man zaitun. Za a miƙa shi hadaya ta ƙonawa don ya ba da ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. Za su kuma miƙa hadaya ta sha da ruwan inabi kwalaba ɗaya.

14 Kada su ci sabon hatsin, wanda aka tuma, ko ɗanyensa, ko wanda aka yi gurasa da shi sai sun kawo hadayarsu ta sabon hatsi ga Allah. Za su kiyaye wannan ka’ida, da su da dukan zuriyarsu, har dukan zamanai masu zuwa.

Idin Girbi

15 Za su ƙidaya mako bakwai daga kashegarin Asabar da suka kawo damin hadaya ta kaɗawa domin miƙa wa Ubangiji.

16 Kwana hamsin za su ƙirga zuwa kashegarin Asabar ta bakwai ɗin. Sa’an nan sai su kawo hadaya ta sabon hatsi ga Ubangiji.

17 Za su kawo malmala biyu na abinci da za a kaɗa daga inda suke domin a miƙa su ga Ubangiji. Za a yi malmalan da rabin garwar gari mai laushi. Za a sa wa garin yisti, sa’an nan a toya. Hadaya ta ‘ya’yan fari ke nan ga Ubangiji.

18 Za su kuma miƙa ‘yan raguna bakwai bana ɗaya ɗaya marasa lahani, da bijimi ɗaya, da raguna biyu tare da abincin. Za a yi hadaya ta ƙonawa da su ga Ubangiji, tare da hadayarsu ta gari, da hadayarsu ta sha, wato, hadaya ta ƙonawa da wuta, hadaya ce mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.

19 Za su miƙa hadaya ta zunubi da bunsuru ɗaya, da ‘yan raguna biyu bana ɗaya ɗaya don hadaya ta salama.

20 Firist zai kaɗa su tare da abinci na nunan fari domin hadaya ta kaɗawa, da ‘yan ragunan nan biyu a gaban Ubangiji. Za su zama tsarkakakku ga Ubangiji domin a ba firist.

21 A ranar fa za su yi shela don a yi muhimmin taro. Ba za su yi aiki mai wuya ba. Wannan doka ce gare su har abada a inda suke duka.

22 Sa’ad da suka girbe amfanin gonakinsu, ba za su girbe har da gyaffan gonakinsu ba, ba kuma za su yi kalar amfanin gonakinsu ba. Za su bar wa matalauta da baƙi. Shi ne Ubangiji Allahnsu.

Idin Sabuwar Shekara

23 Ubangiji ya yi magana da Musa, cewa,

24 ya ce wa Isra’ilawa su mai da rana ta fari ga wata na bakwai ta zama ranar hutu musamman, sa’ad da za su ji busar ƙaho, sai su taru domin yin sujada.

25 Ba za su yi aiki mai wuya ba. Za su miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji.

Ranar Kafara

26 Ubangiji ya yi magana da Musa, cewa,

27 rana ta goma ga watan bakwai za ta zama rana ta yin kafara da lokacin yin muhimmin taro. Kada su ci abinci a ranar, su taru su yi sujada, su miƙa hadaya taƙonawa ga Ubangiji.

28 Ba za su yi aiki a wannan rana ba, gama rana ce ta yin kafara dominsu.

29 Duk wanda ya ci abinci a wannan rana ba za a lasafta shi ɗaya daga cikin jama’ar Allah ba.

30 Duk kuma wanda ya yi aiki a wannan rana, Ubangiji kansa zai kashe shi.

31 Wannan ka’ida ta shafi dukan zuriyarsu a duk inda suke.

32 Daga faɗuwar ranar tara ga watan, har zuwa faɗuwar ranar goma ga watan, su kiyaye wannan ta zama ranar hutu musamman. A wannan lokaci ba wanda zai ci abinci.

Idin Bukkoki

33 Ubangiji kuma ya yi magana da Musa, ya ce ya faɗa wa Isra’ilawa, cewa,

34 a rana ta goma sha biyar ga watan bakwai za a yi Idin Bukkoki kwana bakwai saboda Ubangiji.

35 Za a yi muhimmin taro na sujada a rana ta fari. Ba za su yi aiki ba.

36 A kwana bakwai ɗin za su riƙa miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. A rana ta takwas kuma sai su yi muhimmin taro na sujada, su miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Rana ce ta yin sujada, kada su yi aiki.

37 Waɗannan su ne ƙayyadaddun idodi na Ubangiji da za su riƙa yi domin sujada. Za su miƙa hadayu ga Ubangiji, wato, hadaya ta ƙonawa, da hadaya ta gari, da ta sadakoki, da hadayu na sha. Za a miƙa kowace hadaya a ranarta.

38 Waɗannan idodi ƙari ne a kan lokatan sujada da aka saba, hadayun kuma ƙari ne a kan kyautan da aka saba bayarwa, kamar su hadaya don cika wa’adi, da hadaya ta yardar rai da suke bayarwa ga Ubangiji.

39 A rana ta goma sha biyar ga watan bakwai, bayan da sun gama tattara amfanin gonakinsu, sai su yi idi ga Ubangiji har kwana bakwai. Rana ta fari, da rana ta takwas za su zama muhimman ranakun hutawa.

40 A ranar sai su ɗibi ‘ya’yan itatuwa masu kyau, da rassan dabino, da kauraran rassan itatuwa masu ganye, da itacen wardi na rafi, sa’an nan su nuna bangirma gaban Ubangiji Allahnsu har kwana bakwai.

41 Za su yi idin nan ga Ubangiji har kwana bakwai. Wannan ka’ida ce a gare su har abada.

42 Za su zauna cikin bukkoki har kwana bakwai. Duk ‘yan ƙasa waɗanda suke Isra’ilawa za su zauna cikin bukkoki.

43 Don zuriyarsu ta sani Ubangiji ya sa Isra’ilawa su zauna cikin bukkoki, sa’ad da ya fito da su daga ƙasar Masar. Shi ne Ubangiji Allahnsu.

44 Haka kuwa Musa ya sanar wa mutanen Isra’ila da ƙayyadaddun idodin Ubangiji.

Categories
L. FIR

L. FIR 24

Kulawa da Fitila

1 Ubangiji kuma ya ce wa Musa

2 ya umarce Isra’ilawa, su kawo masa tsabtataccen man zaitun da aka matse domin fitilar. Fitilar za ta riƙa ci kullum.

3 Za a ajiye ta a gaban labulen shaida a alfarwa ta sujada. Kullum Haruna zai riƙa lura da ita daga maraice har safiya a gaban Ubangiji. Wannan zai zama muku farilla har abada a dukan zamananku.

4 Kullum sai ya shirya fitilun a bisa alkuki na zinariya tsantsa a gaban Ubangiji.

Gurasar da aka Miƙa ga Allah

5 Ɗauki lallausan gari a toya gurasa goma sha biyu. A ki kowace gurasa da humushi biyu na garwar gari.

6 A ajiye su bisa tebur na zinariya tsantsa jeri biyu, shida a kowane jeri.

7 Sai a sa lubban tsantsa a kowane jeri don a haɗa da abincin da za a ƙone domin hadaya ta tunawa ga Ubangiji.

8 Kullum a kowace ranar Asabar, Haruna zai kintsa su a gaban Ubangiji domin Isra’ilawa saboda madawwamin alkawarin.

9 Wannan abinci zai zama rabon Haruna da na ‘ya’yansa maza, za su ci a wuri mai tsarki, tun da yake a gare shi rabo ne mai tsarki daga cikin hadayun da akan ƙone da wuta ga Ubangiji. Wannan farilla ce har abada.

Hukunci a kan Saɓo da Biyan Diyya

10 Ɗan wata mace Ba’isra’iliya wanda mahaifinsa Bamasare ne, ya fita, ya yi faɗa da wani Ba’isra’ile a cikin zangon.

11 Sai ɗan Ba’isra’iliyar ya saɓi sunan Allah. Aka kai shi wurin Musa. Sunan mahaifiyar kuwa Shelomit ‘yar Dibri na kabilar Dan.

12 Musa kuwa ya kulle shi a gidan tsaro kafin Ubangiji ya faɗa musu abin da za su yi da shi.

13 Sai Ubangiji ya ce wa Musa,

14 “Fito da wanda ya yi saɓon nan daga cikin zangon. Ka kuma sa dukan waɗanda suka ji shi su sa hannuwansu a bisa kansa. Taron jama’ar kuwa su jajjefe shi da duwatsu.

15 Sa’an nan ka faɗa wa Isra’ilawa, cewa, duk wanda ya saɓi Allah zai ɗauki alhakin zunubinsa,

16 za a kuwa kashe shi. Duk Ba’isra’ile ko baƙon da yake zaune cikin Isra’ilawa wanda ya saɓi Allah, sai taron jama’a su jajjefe shi da duwatsu ya mutu.

17 “Duk wanda ya kashe mutum, shi ma sai a kashe shi.

18 Wanda ya kashe dabba kuma ya yi ramuwa, rai maimakon rai.

19 “Idan mutum ya yi wa wani rauni, kowane irin rauni ne ya yi masa, shi kuma haka za a yi masa.

20 Idan ya karya masa ƙashi ne, sai a karya nasa ƙashin, idan ya cire wa wani ido, sai a ƙwaƙule nasa, idan haƙori ya ɓalle, sai a ɓalle nasa. Duk irin raunin da ya ji wa wani haka za a yi masa.

21 Wanda ya kashe dabba ya yi ramuwa, wanda kuwa ya kashe mutum sai a kashe shi.

22 Irin shari’ar da za a yi wa baƙo, ita za a yi wa ɗan gari, gama ni ne Ubangiji Allahnku.”

23 Sai Musa ya yi magana da Isra’ilawa, suka kuwa fito masa da mutumin da ya yi saɓon a bayan zangon. Suka jajjefe shi da duwatsu. Haka Isra’ilawa suka aikata yadda Ubangiji ya umarci Musa.

Categories
L. FIR

L. FIR 25

Bikin Kewayowar Shekaru

1 Ubangiji kuwa ya yi wa Musa magana a kan Dutsen Sina’i, ya ce

2 ya faɗa wa Isra’ilawa ka’idodin nan. Sa’ad da suka shiga ƙasar da Ubangiji yake ba su, ƙasar za ta kiyaye shekara ta bakwai ga Ubangiji.

3 Shekara shida za su yi, suna ta noman gonakinsu, suna kuma ta aske gonakin inabinsu, suna tattara amfaninsu.

4 Amma shekara ta bakwai ta Ubangiji ce, sh ekara ce ta hutawa ga ƙasar. Kada su nomi gonakinsu, ko kuwa su aske inabinsu.

5 Kada su girbe gyauron gonakinsu da na inabin da ba su yi wa aski ba. Za ta zama shekarar hutawa ta musamman ga ƙasar.

6 A shekarar nan ɗin ƙasar za ta tanada musu abinci, da su da bayinsu mata, da maza, da barorinsu na ijara, da baƙon da yake zaune tare da su,

7 har da dabbobinsu na gida da na jeji. Duk albarkar da ƙasar za ta bayar, za ta zama abinci.

Murnar Shekara ta Hamsin

8 Sai su ƙidaya shekara bakwai har sau bakwai. Shekarar nan bakwai sau bakwai su ne shekara arba’in da tara a gare su.

9 A ranar kafara, goma ga wata na bakwai za su busa ƙahon rago da ƙarfi cikin ƙasarsu duka.

10 Shekara ta hamsin kuwa za su keɓe ta, su yi shelar ‘yanci cikin ƙasar duka ga dukan mazaunanta. Za ta zama shekarar murna a gare su. Kowa zai koma mahallinsa, ko wannensu kuma wurin danginsa.

11 Shekarar nan ta hamsin za ta zama shekara ta murna a gare su. A cikinta ba za su yi shuka, ko su girbe gyauro ba, ba kuwa za su tattara ‘ya’yan inabin da ba su yi wa aski ba.

12 Shekara ce ta murna, za ta zama keɓaɓɓiya a gare su. Za su ci albarkar da gonakin suka bayar.

13 Ubangiji ya ce, “A wannan shekara ta hamsin ta murna kowa zai koma mahallinsa.

14 In ka sayar, ko ka sayi gona a wurin ɗan’uwanka, Ba’isra’ile, kada ku cuci juna.

15 Idan za ka yi sayayya a wurin maƙwabcinka, sai ka lura da yawan shekarun da za ka mora kafin shekara ta hamsin ta murna ta kewayo.

16 Idan shekarun sun ragu da yawa kafin shekara ta hamsin ta murna ta kewayo, sai ka saya da tsada. Idan kuwa shekarun sun ragu kima ne, sai ka saya da araha, gama yana sayar maka bisa ga yawan shekarun da za ka mora ne.

17 Kada ku cuci juna fa, amma ku ji tsoron Allahnku, gama ni ne Ubangiji Allahnku.”

Matsalolin Shekarar Murna

18 “Domin haka sai ku kiyaye farillaina, da ka’idodina. Ku aikata su domin ku zauna a ƙasar lami lafiya.

19 Ƙasar za ta ba da amfani, za ku ci, ku ƙoshi, ku zauna lafiya.

20 “Idan kuwa kun tambaya abin da za ku ci a shekara ta bakwai, idan ba za ku yi shuka ba, ba kuwa za ku tattara amfanin gona ba,

21 ku sani zan sa muku albarka a shekara ta shida don ta ba da isasshen amfanin da zai kai ku shekara uku.

22 Sa’ad da za ku yi shuka a shekara ta takwas, shi ne za ku yi ta ci, har shekara ta tara lokacin da za ku yi girbi.”

Fansar Mallaka

23 “Kada a sayar da gona din din din, gama ƙasar tawa ce, ku kuwa baƙi na da kuke baƙunci a wurina.

24 “Amma kuna iya jinginar da gonar da kuka mallaka.

25 Idan ɗan’uwanka ya talauce, har ya jinginar maka da mahallinsa, sai danginsa na kusa ya fanshi abin da ɗan’uwansa ya jinginar.

26 Idan mutumin ba shi da wanda zai fansa, idan shi kansa ya arzuta, ya sami abin da ya isa yin fansa,

27 to, sai ya lasafta yawan shekarun da ya jinginar da abin, sa’an nan ya biya jinginar daidai da shekarun da suka haura kafin shekara ta hamsin ta murna ta kewayo, shi ya koma kan mahallinsa.

28 Amma idan ba shi da isasshen abin da zai fanshi abinsa, to, sai wanda ya karɓi jinginar ya ci gaba da riƙon abin da aka jinginar masa ɗin har shekara ta hamsin ta murna, a lokacin ne zai mayar wa mai shi, mai shi ɗin kuwa ya koma a kan mahallinsa.

29 “Haka nan kuma idan mutum ya jinginar da gida a cikin birni mai garu, yana da izini ya fanshi abinsa a ƙarshen shekara guda.

30 Idan kuwa bai fanshi gidan a ƙarshen shekara guda ba, sai gidan nan da yake cikin birni mai garu ya zama mallakar wanda ya karɓi jinginar, da na zuriyarsa duka har abada. Ba za a mayar wa maigidan da gidan a shekara ta hamsin ta murna ba.

31 Amma gidajen da suke cikin ƙauyuka da ba su cikin garu, sai a lasafta su daidai da gonakin da suke cikin ƙasar, ana iya fansarsu, za a kuma mayar wa masu su a shekara ta hamsin ta murna.

32 Amma a kan biranen Lawiyawa, da gidajen da suke cikin biranen da suka mallaka, Lawiyawa suna da izini su fanshe su a kowane lokaci.

33 Amma idan wani daga cikin Lawiyawa bai fanshi gidansa ba, a shekara ta hamsin ta murna sai a mayar masa da gidan nan na cikin birnin da suka mallaka, gama gidajen da suke cikin biranen Lawiyawa su ne nasu rabo a cikin Isra’ilawa.

34 Ba za a jinginar da hurumin biranensu ba, gama wannan shi ne abin mallakarsu har abada.”

Ba da Rance ga Matalauci

35 “Idan ɗan’uwanka, Ba’isra’ile, ya talauce, ya kasa riƙon kansa, sai ka riƙe shi kamar baƙon da yake baƙunci a wurinka.

36 Kada ka ba shi rance da ruwa, amma ka ji tsoron Allah ka bar ɗan’uwanka, Ba’isra’ile, ya zauna tare da kai.

37 Kada ka ranta masa kuɗi da ruwa, kada kuma ka ba shi abinci don samun riba.

38 Ni ne Ubangiji Allahnku wanda ya fanshe ku daga ƙasar Masar don in ba ku ƙasar Kan’ana, in zama Allahnku.”

‘Yantar da Bayi

39 “Idan kuwa ɗan’uwanka, Ba’isra’ile, ya talauce har ya sayar da kansa gare ka, to, kada ka bautar da shi kamar bawa.

40 Amma ya zauna tare da kai kamar bara na ijara, ko kuwa kamar wanda yake baƙunci. Sai ya yi aiki tare da kai har shekara ta hamsin ta murna ta kewayo.

41 Sa’an nan shi da iyalinsa su rabu da kai, ya koma wurin danginsa da mahallin kakanninsa.

42 Gama su bayina ne, waɗanda na fanshe su daga ƙasar Masar, ba za a sayar da su kamar yadda ake sayar da bayi ba.

43 Kada ka mallake shi da tsanani, amma ka ji tsoron Allahnka.

44 Amma a kan bayi mata da maza da kuke so ku samu, kwa iya sayensu daga al’ummar da yake kewaye da ku.

45 Kwa iya sayen bayi daga baƙin da yake baƙunci a wurinku, su da iyalinsu waɗanda aka haifa a ƙasarku. Kwa iya sayensu su zama dukiyarku.

46 Kwa iya barinsu ga ‘ya’yanku maza a bayanku su gāda, su zama abin mallakarsu har abada. Kwa iya bautar da su, amma ‘yan’uwanku, Isra’ilawa, ba za ku mallaki juna da tsanani ba.

47 “Idan baƙo ne ko mai aikin ijara da yake zaune tare da ku ya arzuta, ɗan’uwanku kuwa wanda yake kusa da shi ya talauce, har ya sayar da kansa ga baƙon, ko mai aikin ijarar da yake tare da ku, ko kuwa ga wani daga cikin iyalin baƙon,

48 bayan da ya sayar da kansa ana iya fansarsa. Wani daga cikin ‘yan’uwansa ya iya fansarsa.

49 Ko kawunsa, ko ɗan kawunsa, ko wani daga cikin danginsa na kusa ya iya fansarsa. Idan kuma shi kansa ya arzuta ya iya fansar kansa.

50 Sai ya sa wanda ya saye shi ya lasafta tun daga shekarar da ya sayar da kansa, har zuwa shekara ta hamsin ta murna. Ƙuɗin da za a fanshe shi zai zama daidai da yawan shekarun da suka ragu kafin shekara ta murna. Sai a ɗauke shi kamar bara na ijara.

51 Idan shekarun sun ragu da yawa, sai ya fanshi kansa bisa ga adadin kuɗin da aka saye shi.

52 Amma idan shekarun sun ragu kaɗan kafin shekara ta hamsin ta murna, sai ya lasafta, ya biya don fansarsa bisa ga yawan shekarun.

53 Sai baƙon ya mai da shi kamar bara mai aikin ijara, shekara a kan shekara. Amma kada ya tsananta masa.

54 Idan ba a fanshe shi ta waɗannan hanyoyi ba, sai a shekara ta hamsin ta murna, a sake shi, shi da ‘ya’yansa.

55 Gama a gare ni Isra’ilawa bayi ne waɗanda na fisshe su daga ƙasar Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku.”

Categories
L. FIR

L. FIR 26

Fa’idodin Biyayya

1 Ubangiji ya ce, “Kada ku yi wa kanku gumaka, ko ku kafa sassaƙaƙƙiyar siffa, ko al’amudi. Kada kuma ku kafa wata siffa ta dutse a ƙasarku da za ku durƙusa mata, gama ni ne Ubangiji Allahnku.

2 Sai ku kiyaye lokatan sujadata, ku girmama alfarwa ta sujada. Ni ne Ubangiji.

3 “Idan kun bi dokokina, kun kiyaye umarnaina, kun aikata su,

4 sa’an nan zan ba da ruwan sama a lokacinsa, ƙasar kuwa za ta ba da albarkarta, itatuwan gonaki kuma za su ba da ‘ya’yansu.

5 Za ku yi ta girbi, har lokacin tattara ‘ya’yan inabi, za ku kuma yi ta tattara ‘ya’yan inabi har zuwa lokacin shuka. Za ku ci abincinku, ku ƙoshi, ku yi zamanku a ƙasarku lafiya.

6 “Zan ba da salama cikin ƙasar. Za ku kwanta, ba abin da zai razana ku. Zan kawar da mugayen dabbobi daga ƙasar. Ba za a ƙara yin yaƙi a ƙasarku ba.

7 Za ku runtumi maƙiyanku, za su kuwa fāɗi ta kaifin takobi a gabanku.

8 Mutum biyar ɗinku za su runtumi mutum ɗari, mutum ɗari ɗinku za su runtumi mutum dubu goma. Maƙiyanku kuwa za su fāɗi a gabanku ta kaifin takobi.

9 Zan dube ku da idon rahama, in sa muku albarka, in riɓaɓɓanya ku. Zan tabbatar muku da alkawarina.

10 Za ku girbi amfani mai yawa har kun zubar da sūnā tukuna kafin ku sami wurin ajiye sabo.

11 Zan kafa wurin zamana a tsakiyarku, ba kuwa zan gaji da ku ba.

12 Zan yi tafiya tare daku, in zama Allahnku, ku kuma ku zama mutanena.

13 Ni ne Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar, don kada ku zama bayinsu. Na karya ikonsu da yake danne ku, na bar ku ku yi tafiya a sake.”

Hukuncin Rashin Biyayya

14 “Amma idan ba za ku kasa kunne gare ni ba, to, za ku sha hukunci.

15 Idan kuma kuka yi watsi da dokokina, ba ku kuwa kula da ka’idodina ba, har kuka ƙi kiyaye umarnaina, kuka karya alkawarina,

16 to, zan hukunta ku. Zan aukar muku da bala’i, da cuce-cuce da ba su warkuwa, da zazzaɓin da zai lalatar muku da ido, rai zai zama muku da wahala. Za ku yi shuka a banza gama maƙiyanku ne za su ci.

17 Zan yi gāba da ku in sa maƙiyanku su ɗibge ku, waɗanda suke ƙinku za su mallake ku. Za ku yi ta gudu ba mai korarku.

18 “Amma idan duk da haka ba ku kasa kunne gare ni ba, sai in tsananta hukuncinku har sau bakwai saboda zunubanku.

19 Zan karya ikonku wanda kuke fariya da shi, in hana ruwan sama, ƙasa kuma ta zama kamar tagulla.

20 Za ku ɓarnatar da ƙarfinku a banza gama ƙasarku ba za ta ba da amfaninta ba, itatuwan ƙasar kuma ba za su ba da ‘ya’ya ba.

21 “Idan har yanzu kuka tayar mini, ba ku kasa kunne gare ni ba, sai in ƙara yawan hukuncinku har sau bakwai, saboda zunubanku.

22 Zan kuwa turo muku mugayen namomin jeji waɗanda za su kashe ‘ya’yanku, su hallakar da dabbobinku, su sa ku zama kaɗan, har ba mai gilmayya a hanyoyinku.

23 “Idan wannan hukunci bai sa kun juyo gare ni ba, amma kuka ci gaba da tayar mini,

24 sai in hau ku da hukunci, har ya fi na dā riɓi bakwai saboda zunubanku.

25 Zan sa a kawo muku yaƙi saboda karya alkawarina da kuka yi. Idan kuwa kun tattaru a cikin biranenku, sai in aukar muku da masifa, in bashe ku ga maƙiyanku.

26 Zan katse abincinku, mata goma za su dafa abincinku a murhu ɗaya, su rarraba muku shi da ma’auni. Za ku ci, amma ba za ku ƙoshi ba.

27 “Amma idan duk da haka ba ku kasa kunne gare ni ba, amma kuka ci gaba da tayar mini,

28 sai ni ma in tayar muku da fushi, in hukunta ku har riɓi bakwai, saboda zunubanku.

29 Za ku ci naman ‘ya’yanku mata da na ‘ya’yanku maza.

30 Zan lalatar da masujadanku, in rurrushe bagaden ƙona turarenku, in jefar da gawawwakinku a kan gumakanku, raina kuwa zai ji ƙyamarku.

31 Zan sa biranenku su zama kangwaye, in mai da wuraren yin sujada kufai, ba zan shaƙi ƙanshin turarenku ba.

32 Ni zan lalatar da ƙasar har maƙiyanku da suke zaune a ciki za su yi mamaki.

33 Zan sa a kawo muku yaƙi a warwatsa ku a baƙin ƙasashe, ƙasarku za ta zama kufai, biranenku kuwa za su lalace.

34 Sa’an nan ƙasar za ta ji daɗin hutunta muddin tana zaune kango. Sa’ad da kuke a ƙasar maƙiyanku, ƙasar za ta huta, taji daɗin hutunta.

35 Muddin tana zaune kufai za ta sami hutawa, hutawa asabatan da ba ta samu ba a lokacin da kuke zaune cikinta.

36 “Amma ga waɗanda suka ragu, zan sa fargaba a zuciyarsu sa’ad da suke a ƙasar maƙiyansu. Ko motsin ganye kawai ma zai razanar da su su sheƙa a guje kamar waɗanda ake fafara da takobi, ga shi kuwa, ba mai korarsu, za su kuwa fāɗi.

37 Za su yi karo da juna kamar waɗanda suke tsere wa takobi, ko da yake ba wanda yake korarsu. Ba za su sami ikon tsaya wa maƙiyansu ba.

38 Za ku mutu a cikin al’ummai. Ƙasar maƙiyanku za ta haɗiye ku.

39 Sauranku da kuka ragu za ku lalace a ƙasashen maƙiyanku saboda muguntarku da ta kakanninku, za ku lalace kamarsu.

40 “Amma za su hurta muguntarsu da ta kakanninsu, da cin amana da suka yi mini, da kuma tayarwa da suka yi mini,

41 haka kuma ni na tayar musu, na kai su ƙasar maƙiyansu. Amma idan sun ƙasƙantar da kangararriyar zuciyarsu, suka tuba, suka bar muguntarsu,

42 sa’an nan zan tuna da alkawarina wanda na yi wa Yakubu, da Ishaku, da Ibrahim, zan kuwa tuna da ƙasar.

43 Amma za su fita daga ƙasar, ƙasar kuwa za ta ji daɗin hutunta muddin ba su ciki, tana zaman kango. Amma za su tuba saboda sun ƙi kula da ka’idodina, suka yi watsi da dokokina.

44 Duk da haka, sa’ad da suke a ƙasar maƙiyansu ba zan wulakanta su ba, ba kuwa zan ji ƙyamarsu, har da zan karya alkawarina da su ba, gama ni ne Ubangiji Allahnsu.

45 Amma saboda su zan tuna da alkawarin da na yi da kakanninsu waɗanda na fisshe su daga ƙasar Masar a idon al’ummai domin in zama Allahnsu. Ni ne Ubangiji.”

46 Waɗannan su ne dokoki, da ka’idodi, da umarnai waɗanda Ubangiji ya yi tsakaninsa da Isra’ilawa ta hannun Musa a bisa Dutsen Sinai.

Categories
L. FIR

L. FIR 27

Ka’idodin Keɓewa

1 Ubangiji ya ba Musa

2 waɗannan ka’idodi domin Isra’ilawa. Idan an ba da mutum ga Ubangiji don cikar babban wa’adi za a iya fansarsa ta wurin biya waɗannan kuɗi.

3-7 Abin da aka ƙayyade za su biya bisa ga ma’aunin kuɗin da ake aiki da shi.

Maza masu shekara 20-60 Shekel hamsin
Mata masu shekara 20-60 Shekel talatin
Maza masu shekara 5-20 Shekel ashirin
Mata masu shekara 5-20 Shekel goma sha biyar
Maza masu wata guda zuwa shekara 5 Shekel biyar
Mata masu wata guda zuwa shekara 5 Shekel uku
Tsohon da ya fi shekara 60 Shekel goma sha biyar
Tsohuwar da ta fi shekara 60 Shekel goma

8 Idan mutumin ya cika talauci har ya kasa biyan tamanin da aka kimanta, sai ya kawo mutumin da aka yi wa’adi a kansa a gaban firist, firist ɗin zai kimanta tamaninsa daidai da ƙarfin wanda ya yi wa’adin.

9 Idan kuwa dabba ce irin wadda mutane kan miƙa hadaya ga Ubangiji, dukan irin wannan da mutum yakan bayar ga Ubangiji zai zama tsattsarka.

10 Ba zai musaya shi da wani abu ba, ba zai musaya mai kyau da marar kyau, ko marar kyau da mai kyau ba. Idan kuwa ya musaya dabba da dabba, sai duka biyu, abar da aka musaya, da wadda aka musayar, za su zama tsarkakakku.

11 Idan kuwa dabbar marar tsarki ce, irin wadda ba a miƙa ta hadaya ga Ubangiji, sai mutumin ya kai dabbar a wurin firist.

12 Firist ɗin zai kimanta tamanin dabbar daidai darajarta, kamar yadda firist ya kimanta, haka zai zama.

13 Amma idan mutumin yana so ya fansa, sai ya yi ƙarin humushin tamanin da aka kimanta.

14 Idan mutum ya keɓe gidansa ga Ubangiji, sai firist ya kimanta tamanin gidan daidai darajarsa, ko gidan mai tsada ne, ko mai araha ne. Yadda shi firist ya kimanta tamaninsa, haka zai zama.

15 Idan shi wanda ya keɓe gida nasa yana so ya fansa, sai ya ƙara kashi ɗaya daga cikin biyar na tamanin da aka kimanta, gidan kuwa zai zama nasa.

16 Idan mutum ya keɓe wa Ubangiji wani sashi daga cikin gonarsa ta gādo, sai ka kimanta tamanin gonar daidai da yawan irin da zai rafa. Gonar da za a yafa iri wajen garwa ashirin na sha’ir tamaninta zai zama wajen shekel hamsin.

17 Idan ya keɓe gonarsa daga shekara ta hamsin ta murna, ba za a rage kome daga cikin tamanin gonar da aka kimanta ba.

18 Amma idan ya keɓe ta bayan shekara ta hamsin ta murna, sai firist ya kimanta yawan kuɗin bisa ga yawan shekarun da suka ragu kafin shekara ta hamsin ta murna ta kewayo. Sai a rage kuɗin tamanin gonar.

19 Idan shi wanda ya keɓe gonar yana so ya fanshe ta, to, sai ya ƙara kashi ɗaya daga cikin biyar na tamanin kuɗin gonar, gonar kuwa za ta zama tasa.

20 Amma idan ba ya so ya fanshi gonar, ko kuwa ya riga ya sayar wa wani da gonar, faufau, ba zai sāke fansarta ba.

21 Sa’ad da aka mayar da gonar a shekara ta hamsin ta murna, za ta zama tsattsarka ta ubangiji kamar gonar da aka keɓe. Firist ne zai mallaka ta.

22 Idan kuwa ya keɓe wa Ubangiji gonar da ya saya, wadda ba ta gādo ba,

23 sai firist ya kimanta tamaninta har zuwa shekara ta hamsin ta murna. Shi mutumin zai ba da yawan abin da aka kimanta a ranar, abu mai tsarki ne ga Ubangiji.

24 A cikin shekara ta hamsin ta murna, sai a mayar da gonar ga wanda aka saye ta a hannunsa, wanda gonarsa ce ta gādo.

25 Sai a kimanta tamanin kowane abu bisa ga ma’aunin kuɗin da ake aiki da shi.

26 Kowane ɗan fari na dabba na Ubangiji ne, kada wani ya fanshi sa ko tunkiya, gama na Ubangiji ne.

27 Idan dabbar marar tsarki ce, sai mai ita ya kimanta tamanin kuɗinta, ya ƙara da humushin kuɗin, ya saya. Idan ba a fansa ba, sai a sayar bisa ga tamaninta.

28 Amma iyakar abin da mutum ya ba Ubangiji ɗungum daga cikin abubuwan da yake da su, ko mutum ko dabba, ko gonarsa ta gādo, ba za a sayar ko a fansar ba, gama kowane abu da aka keɓe mafi tsarki ne ga Ubangiji.

29 Ko da mutum ne aka ba Ubangiji ɗungum, ba za a fanshe shi ba, sai a kashe shi.

30 Dukan ushirin amfanin ƙasar, ko na hatsi ne, ko na ‘ya’yan itatuwa ne, na Ubangiji ne, gama tsattsarka ne ga Ubangiji.

31 Idan wani yana so ya fanshi ushiri na kowane iri, sai ya ƙara humushin tamanin ushirin.

32 Dukan ushiri na shanu, da na tumaki da awaki, duk dai dabbar da ta zama ta goma bisa ga ƙirgar makiyayan, keɓaɓɓiya ce, ta Ubangiji ce.

33 Ba ruwan kowa da kyanta ko rashin kyanta. Kada kuma a musaya ta. Idan kuwa an musaya ta, sai dai su zama tsarkakakku ga Ubangiji, ita da abar da aka yi musayar. Ba za a fanshe su ba.

34 Waɗannan su ne umarnan da Ubangiji ya ba Musa a kan Dutsen Sinai saboda isra’ilawa.