Categories
L. KID

L. KID 1

Ƙidaya ta Farko a Jejin Sinai

1 A rana ta fari ga wata na biyu a shekara ta biyu bayan da Isra’ilawa suka bar Masar, Ubangiji ya yi magana da Musa a cikin alfarwa ta sujada a jejin Sinai. Ya ce,

2 “Da kai da Haruna ku ƙidaya Isra’ilawa, bisa ga kabilansu da iyalansu. Ku tsara sunayen dukan mazaje

3 daga mai shekara ashirin zuwa sama waɗanda suka isa zuwa yaƙi.

4 Ku roƙi shugaban kowace kabila ya taimake ku.”

5-15 Waɗannan su ne mutanen da aka zaɓa.

Ra’ubainu Elizur ɗan Shedeyur
Saminu Shelumiyel ɗan Zurishaddai
Yahuza Nashon ɗan Amminadab
Issaka Netanel ɗan Zuwar
Zabaluna Eliyab ɗan Helon
Ifraimu Elishama ɗan Ammihud
Manassa Gamaliyel ɗan Fedazur
Biliyaminu Abidan ɗan Gideyoni
Dan Ahiyezer ɗan Ammishaddai
Ashiru Fagiyel ɗan Okran
Gad Eliyasaf ɗan Deyuwel
Naftali Ahira ɗan Enan

16 Waɗannan shugabannin kabilai waɗanda suke manya cikin kabilansu, an zaɓe su daga cikin jama’a domin wannan aiki.

17 Musa da Haruna suka ɗauki waɗannan mutane goma sha biyu,

18 suka kuma kira dukan jama’a wuri ɗaya a ran ɗaya ga watan biyu. Dukan mutanen kuwa aka rubuta su bisa ga kabilansu da iyalansu, da kuma sunayen dukan mazaje masu shekara ashirin ko fi, duk aka ƙidaya su aka rubuta,

19 kamar yadda Ubangiji ya umarta.

Musa ya rubuta jama’a a jeji ta Sinai.

20-46 Mazaje masu shekara ashirin ko fi da suka isa yaƙi aka rubuta su suna suna, bisa ga kabilansu da iyalansu, aka fara da kabilar Ra’ubainu, babban ɗan Yakubu. Ga yadda jimillarsu take.

Ra’ubainu (46,500) Dubu arba’in da shida da ɗari biyar.
Saminu (59,300) Dubu hamsin da tara da ɗari uku.
Gad (45,650) Dubu arba’in da biyar da ɗari shida da hamsin.
Yahuza (74,600) Dubu saba’in da huɗu da ɗari shida.
Issaka (54,400) Dubu hamsin da huɗu da ɗari huɗu.
Zabaluna (57,400) Dubu hamsin da bakwai da ɗari huɗu.
Ifraimu (40,500) Dubu arba’in da ɗari biyar.
Manassa (32,200) Dubu talatin da biyu da ɗari biyu.
Biliyaminu (35,400) Dubu talatin da biyar da ɗari huɗu.
Dan (62,700) Dubu sittin da biyu da ɗari bakwai.
Ashiru (41,500) Dubu arba’in da ɗaya da ɗari biyar.
Naftali (53,400) Dubu hamsin da uku da ɗari huɗu.
Jimilla duka (603,550) dubu ɗari shida da uku da ɗari biyar da hamsin.

An Ba Lawiyawa Ikon Alfarwa

47 Amma ba a rubuta Lawiyawa tare da sauran kabilai ba,

48 gama Ubangiji ya ce wa Musa,

49 “Sa’ad da kake ƙidaya Isra’ilawa, kada ka haɗa da kabilar Lawi.

50 A maimakon haka, sai ka sa Lawiyawa su zama masu lura da alfarwa ta sujada da kayayyakinta. Za su ɗauki alfarwar da kayayyakinta, su yi aikinta, a zango kuma sai su sauka kewaye da ita.

51 Sa’ad da kuka tashi tafiya, Lawiyawa za su kwankwance alfarwar, su ne kuma za su kafa ta, su ɗaɗɗaure, idan suka sauka a sabon wuri. Idan wani dabam ya zo kusa da alfarwar za a kashe shi.

52 Sauran Isra’ilawa za su sauka ƙungiya ƙungiya, kowane mutum a ƙungiyarsa a ƙarƙashin tutarsa.

53 Amma Lawiyawa za su sauka kewaye da alfarwa ta sujada don su yi tsaronta, domin kada wani dabam ya matsa kusa har ya sa in yi fushi in bugi jama’ar Isra’ila.”

54 Sai Isra’ilawa suka aikata kowane abu da Ubangiji ya umarci Musa.

Categories
L. KID

L. KID 2

Zango da Shugabannin Kabilai

1 Ubangiji ya ba Musa da Haruna waɗannan umarnai.

2 Duk sa’ad da Isra’ilawa suka yi zango, kowane mutum zai sauka a inda tutar ƙungiyar kabilarsa take. Zangon zai kasance a kewaye da alfarwa ta sujada.

3-9 Ƙungiyoyin kabilar Yahuza za su sauka su kafa tutarsu a sashin gabas a ƙarƙashin jagorancin shugabanninsu, kamar haka,

Yahuza Nashon ɗan Amminadab 74,600
Issaka Netanel ɗan Zuwar 54,400
Zabaluna Eliyab ɗan Helon 57,400

Jimilla duka,(186,400) dubu ɗari da tamanin da shida da ɗari huɗu.

Ƙungiyoyin kabilar Yahuza su ne za su fara tafiya.

10-16 Ƙungiyoyin kabilar Ra’ubainu za su sauka su kafa tutarsu a sashin kudu a ƙarƙashin jagorancin shugabanninsu, kamar haka,

Ra’ubainu Elizur ɗan Shedeyur 46,500
Saminu Shelumiyel ɗan Zurishaddai 59,300
Gad Eliyasaf ɗan Deyuwel 45,650

Jimilla duka, 151,450) duba ɗari da hamsin da ɗaya, da ɗari huɗu da hamsin.

Ƙungiyoyin kabilar Ra’ubainu za su bi bayan na Yahuza.

17 Sa’an nan Lawiyawa ɗauke da alfarwa ta sujada za su kasance a tsakanin ƙungiyoyi biyu na farko da biyun da suke daga ƙarshe. Kowace ƙungiya za ta yi tafiya kamar yadda aka dokace ta ta zauna a zango, wato kowacce ta yi tafiya a ƙarƙashin tutarta a matsayinta.

18-24 Ƙungiyoyin kabilar Ifraimu za su sauka su kafa tutarsu a sashin yamma a ƙarƙashin jagorancin shugabanninsu, kamar haka,

Ifraimu Elishama ɗan Ammihud 40,500
Manassa Gamaliyel ɗan Fedazur 32,200
Biliyaminu Abidan ɗan Gideyoni 35,400

Jimilla duka, (108,100) dubu ɗari da takwas, da ɗari ɗaya daidai.

Ƙungiyoyin Ifraimu za su zama na uku a jerin.

25-31 Ƙungiyoyin kabilar Dan za su sauka su kafa tutarsu a sashin arewa a ƙarƙashin jagorancin shugabanninsu, kamar haka,

Dan Ahiyezer ɗan Ammishaddai 62,700
Ashiru Fagiyel ɗan Okran 41,500
Naftali Ahira ɗan Enan 53,400

Jimilla duka, (157,600) duba ɗari da hamsin da bakwai, da ɗari shida.

Ƙungiyoyin Dan za su bi daga bayan duka.

32 Jimillar yawan Isra’ilawa da aka rubuta su a yadda suke ƙungiya ƙungiya, su dubu ɗari shida da uku da ɗari biyar da hamsin ne (603,550).

33 Amma kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa, ba a rubuta Lawiyawa haɗe da sauran Isra’ilawa ba.

34 Saboda haka Isra’ilawa suka yi dukan abin da Ubangiji ya umarci Musa. Kowa ya yi zango a ƙarƙashin tutarsa, kowa kuma ya yi tafiya cikin jerin kabilarsa.

Categories
L. KID

L. KID 3

Yawan Lawiyawa da Aikinsu

1 Waɗannan su ne zuriyar Haruna da Musa lokacin da Ubangiji ya yi magana da Musa a bisa Dutsen Sinai.

2 Waɗannan su ne sunayen ‘ya’yan Haruna, maza, Nadab ɗan fari, da Abihu, da Ele’azara, da Itamar.

3 Waɗannan su ne sunayen ‘ya’yan Haruna, maza, da aka naɗa firistoci domin su yi aikin firist.

4 Amma Nadab da Abihu sun mutu a gaban Ubangiji a jejin Sinai, a sa’ad da suka ƙona turare da haramtacciyar wuta. Sun mutu, ba su da ‘ya’ya, saboda haka Ele’azara da Itamar suka yi aikin firist su kaɗai a zamanin mahaifinsu Haruna.

5 Ubangiji ya ce wa Musa,

6 “Kawo kabilar Lawiyawa kusa, ka sa su su yi aiki tare da Haruna, firist.

7 Sai su yi wa firistoci da dukan jama’a aiki a gaban alfarwa ta sujada.

8 Su za su lura da kayayyakin alfarwa ta sujada su kuma yi wa Isra’ilawa aiki.

9 Abin da Lawiyawa za su yi, shi ne su yi wa Haruna da ‘ya’yansa aiki.

10 Ka sa Haruna da ‘ya’yansa maza, su kula da aikinsu na firist, idan kuwa wani mutum dabam ya yi ƙoƙarin yin wannan aiki, to, za a kashe shi.”

11 Ubangiji kuma ya ce wa Musa,

12 “Ga shi, na ɗauki Lawiyawa daga cikin Isra’ilawa a maimakon kowane ɗan farin da ya buɗe mahaifa daga cikin mutanen Isra’ila. Lawiyawa za su zama nawa.

13 Gama ‘yan fari duka nawa ne, tun daga ranar da na kashe ‘ya’yan fari na ƙasar Masar, na keɓe wa kaina duk ɗan fari na Isra’ila, na mutum da na dabba. Za su zama nawa, ni ne Ubangiji.”

14 Ubangiji ya yi magana da Musa a jejin Sinai, ya ce masa

15 ya ƙidaya mazaje na kabilar Lawi bisa ga gidajen kakanninsu da iyalansu, tun daga mai wata ɗaya zuwa gaba.

16 Haka Musa ya ƙidaya su bisa ga maganar Ubangiji, kamar yadda ya umarce shi.

17 Waɗannan su ne ‘ya’yan Lawi, maza, bisa ga sunayensu, da Gershon, da Kohat, da Merari.

18 Waɗannan su ne sunayen ‘ya’yan Gershon, maza, bisa ga iyalansu, Libni da Shimai.

19 Ga ‘ya’yan Kohat, maza, bisa ga iyalansu, da Amram, da Izhara, da Hebron, da Uzziyel.

20 Ga kuma ‘ya’yan Merari, maza, bisa ga iyalansu, da Mali da Mushi. Waɗannan su ne iyalan Lawi bisa ga gidajen kakanninsu.

21 Iyalin Libnawa, da na Shimaiyawa su ne iyalan Gershon.

22 Jimillarsa tun daga ɗa namiji mai wata ɗaya zuwa gaba, mutum dubu bakwai ne da ɗari biyar (7,500).

23 Iyalan Gershonawa za su yi zango a bayan alfarwar daga yamma.

24 Eliyasaf, ɗan Layel, shi ne shugaban gidan kakanninsa, Gershonawa.

25 ‘Ya’yan Gershon, maza, su ne da aikin lura da alfarwa ta sujada da murfinta na ciki da na waje, da labulen ƙofar,

26 da labulen farfajiyar da yake kewaye da alfarwar, da bagade, da labulen ƙofar farfajiyar. Su za su lura da dukan aikin da ya shafi waɗannan abubuwa.

27 Iyalan Kohat su ne iyalin Amramawa, da na Izharawa, da na Hebronawa, da na Uzziyelawa. Waɗannan su ne iyalan Kohatawa.

28 Lissafin mazaje duka, tun daga mai wata ɗaya zuwa gaba, su dubu takwas ne da ɗari shida (8,600).

29 Iyalan ‘ya’yan Kohat za su kafa zangonsu a kudancin alfarwar.

30 Elizafan ɗan Uzziyel shi ne shugaban gidan kakanninsa, Kohatawa.

31 Aikinsu shi ne lura da akwatin alkawari, da tebur, da alkuki, da bagadai, da kayayyakin Wuri Mai Tsarki waɗanda firistoci suke aiki da su, da labule, da dukan aikin da ya shafi waɗannan abubuwa.

32 Ele’azara, ɗan Haruna, firist, shi zai shugabanci shugabannin Lawiyawa, shi ne kuma zai lura da waɗanda suke aiki a Wuri Mai Tsarki.

33 Iyalan Merari su ne iyalin Maliyawa, da na Mushiyawa. Waɗannan su ne iyalan Merari.

34 Yawan mazajensu duka da aka ƙidaya tun daga mai wata ɗaya zuwa gaba, mutum dubu shida ne da ɗari biyu (6,200).

35 Shugaban gidan kakannin iyalan Merari kuwa shi ne Zuriyel, ɗan Abihail. Za su kafa zangonsu a arewacin alfarwar.

36 Aikin da aka danƙa wa ‘ya’yan Merari shi ne lura da katakan alfarwar, da sanduna, da dirkoki, da kwasfa, da sauran abubuwa duka, da duk ayyukan da suka shafi waɗannan,

37 da kuma dirkoki na farfajiyar da ta kewaye wurin, da kwasfa da turaku da igiyoyinsu.

38 Waɗanda za su yi zango a gaban alfarwa ta sujada daga gabas, su ne Musa, da Haruna da ‘ya’yansa maza, waɗanda aka danƙa musu tafiyar da aikin Wuri Mai Tsarki, da dukan aikin da za a yi wa Isra’ilawa. Banda su, duk wanda ya je kusa da wurin sai a kashe shi.

39 Dukan Lawiyawa waɗanda Musa da Haruna suka ƙidaya bisa ga iyalansu, bisa ga umarnin Ubangiji, tun daga mai wata ɗaya zuwa gaba, mazaje dubu ashirin da dubu biyu ne (22,000).

An Fanshi ‘Ya’yan Fari Maza

40 Sai kuma Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ƙidaya dukan ‘ya’yan fari maza na Isra’ilawa, tun daga wata ɗaya zuwa mai gaba, ka rubuta sunayensu.

41 Za ka keɓe mini Lawiyawa a maimakon ‘ya’yan fari maza na Isra’ilawa. Dabbobin Lawiyawa za su zama nawa a maimakon dukan ‘ya’yan farin dabbobin Isra’ilawa. Ni ne Ubangiji.”

42 Sai Musa ya ƙidaya ‘ya’yan fari maza na Isra’ilawa, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

43 Jimillar ‘ya’yan fari maza da aka ƙidaya bisa ga sunayensu tun daga mai wata ɗaya zuwa gaba, mutum dubu ashirin da biyu, da ɗari biyu da saba’in da uku ne (22,273).

44 Ubangiji kuma ya yi magana da Musa, ya ce,

45 “Ka keɓe Lawiyawa a maimakon dukan ‘ya’yan fari na Isra’ilawa. Dabbobin Lawiyawa kuma za su zama a maimakon ‘ya’yan farin dabbobin Isra’ilawa. Lawiyawa kuwa za su zama nawa. Ni ne Ubangiji.

46 ‘Ya’yan fari maza na Isra’ilawa sun fi Lawiyawa da mutum ɗari biyu da saba’in da uku. Sai a fanshi wannan ragowa.

47 Ka karɓi shekel biyar a kan kowane mutum, bisa ga ma’aunin kuɗin da ake aiki da shi.

48 Sai ka ba da kuɗin fansar ga Haruna da ‘ya’yansa maza.”

49 Musa kuwa ya karɓi kuɗin fansar waɗanda suka haura yawan Lawiyawa.

50 Kuɗin da ya karɓa daga ‘ya’yan fari na Isra’ilawa da suka haura yawan Lawiyawa shekel dubu ɗaya da ɗari uku da sittin da biyar (1,365) bisa ga ma’aunin kuɗin da ake aiki da shi.

51 Musa kuwa ya ba Haruna da ‘ya’yansa maza kuɗin fansa bisa ga maganar Ubangiji, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

Categories
L. KID

L. KID 4

Ayyukan da aka Danƙa wa Iyalin Kohat

1 Ubangiji ya faɗa wa Musa da Haruna,

2 su ƙidaya ‘ya’yan Kohat, maza, daga cikin ‘ya’yan Lawi bisa ga iyalansu da gidajen kakanninsu,

3 su ƙidaya daga mai shekara talatin zuwa hamsin, wato waɗanda suka isa su yi aiki a alfarwa ta sujada.

4 Wannan shi ne aikin ‘ya’yan Kohat, maza, a cikin alfarwa ta sujada a kan abubuwa mafi tsarki.

5 Sa’ad da za a tashi daga zango, sai Haruna, tare da ‘ya’yansa maza, su shiga cikin alfarwa, su kwance labulen kāriya, su rufe akwatin alkawari da shi.

6 Sa’an nan kuma su rufe shi da fatun awaki, su kuma shimfiɗa shuɗin zane a bisansa, su zura masa sandunansa.

7 Sai su shimfiɗa shuɗin zane a kan tebur na gurasar ajiyewa, sa’an nan su dībiya farantai, da cokula, da kwanonin, da butocin hadaya ta sha, da gurasar ajiyewa.

8 Sa’an nan su rufe su da jan zane, a kuma rufe su da fatun awaki, sa’an nan su zura masa sandunansa.

9 Su kuma ɗauki shuɗin zane su rufe alkuki, da fitilunsa, da hantsukansa, da farantansa, da dukan kwanonin man da akan zuba masa.

10 Sai su sa alkukin da dukan kayayyakinsa a cikin fatar awaki su naɗe, su sarƙafa shi asandan ɗaukarsa.

11 A rufe bagaden zinariya da shuɗin zane, a kuma rufe shi da fatun awaki, sa’an nan a zura sandunan ɗaukarsa.

12 Su ɗauki dukan kwanonin da ake amfani da su a Wuri Mai Tsarki, su sa su cikin shuɗin zane, sa’an nan su rufe su da fatun awaki, a sarƙafa su a sanda don a ɗauka.

13 Za su kwashe tokar da take cikin bagaden, su rufe bagaden da shunayyan zane.

14 Sa’an nan su sa dukan kayayyakin bagaden a kansa waɗanda ake aiki da su a wurin, wato su farantai don wuta, da cokula masu yatsotsi, da manyan cokula, da daruna da dai dukan kayayyakin bagaden. Su kuma rufe bagaden da fatun awaki, sa’an nan su zura sandunan ɗaukarsa.

15 Sa’ad da Haruna da ‘ya’yansa maza suka gama kintsa Wuri Mai Tsarki da kayayyakinsa duka a lokacin tashi, sai ‘ya’yan Kohat, maza, su zo su ɗauke kayayyakin, amma kada su taɓa abubuwan nan masu tsarki domin kada su mutu.

Waɗannan su ne ayyukan ‘ya’yan Kohat a duk lokacin da za a naɗe alfarwa ta sujada.

16 Ele’azara kuwa, ɗan Haruna, firist, shi ne zai lura da man fitila, da turare, da hadayar gari ta kullum, da man keɓewa, ya kuma kula da dukan alfarwar, da duk abin da yake cikinta, da Wuri Mai Tsarki, da kayayyakinsa.

17 Sai Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,

18 “Kada ku bar zuriyar Kohat

19 ta hallaka ta wurin kusatar waɗannan tsarkakakkun abubuwa. Maganin abin, shi ne sai Haruna da ‘ya’yansa maza, su shiga, su nuna wa kowannensu irin aikin da zai yi, da kayan da zai ɗauka.

20 Amma idan Kohatawa suka shiga alfarwar suka tarar firistoci suna shisshirya tsarkakakkun abubuwa don tashi, har dai in sun gani, to za su mutu.”

Ayyukan Gershonawa

21 Ubangiji ya kuma faɗa wa Musa,

22 ya ƙidaya ‘ya’yan Gershon, maza, bisa ga iyalansu da gidajen kakanninsu

23 ya rubuta su tun daga mai shekara talatin, har zuwa mai shekara hamsin, duk wanda ya isa yin aikin da zai yi a alfarwa ta sujada.

24 Wannan shi ne aikin da iyalan Gershonawa za su yi wajen ɗaukar kaya.

25 Za su ɗauki alfarwa ta sujada, da labule na ciki da na waje, da murfi na fatun tumaki wanda yake a bisa alfarwar, da kuma labulen ƙofar alfarwa ta sujada,

26 da labulen farfajiya, da labulen ƙofar farfajiya wadda ta kewaye alfarwar da bagaden, da igiyoyinsu, da duk kayayyakinsu na yin aiki. Sai su yi dukan abin da ya kamata a yi da su.

27 Haruna ne da ‘ya’yansa maza za su nuna wa ‘ya’yan Gershonawa irin aikin da za su yi, da kayayyakin da za su ɗauka. Sai a faɗa musu dukan abin da za su yi, da dukan abinda za su ɗauka.

28 Wannan shi ne aikin da iyalan Gershonawa za su yi a alfarwa ta sujada. Itamar ɗan Haruna, firist, shi zai shugabance su cikin aikin da za su yi.

Ayyukan Merariyawa

29 Ubangiji kuma ya faɗa wa Musa ya ƙidaya Merariyawa bisa ga iyalansu da gidajen kakanninsu,

30 ya rubuta su tun daga mai shekara talatin, har zuwa mai shekara hamsin, duk wanda ya isa yin aikin da zai yi a alfarwa ta sujada.

31 Wannan shi ne abin da aka umarce su su riƙa ɗauka na wajen aikinsu a alfarwa ta sujada, katakan alfarwar, da sandunanta, da dirkokinta, da kwasfanta,

32 da dirkokin farfajiya wadda take kewaye da alfarwar, da kwasfansu, da turakunsu, da igiyoyi, da dukan kayayyakinsu. Sai ya faɗa wa kowa kayan da zai ɗauka.

33 Wannan shi ne aikin iyalan ‘ya’yan Merari, maza. Aikinsu ke nan duka a alfarwa ta sujada. Itamar ɗan Haruna, firist, shi ne zai shugabance su.

Yawan Lawiyawa

34-48 Musa da Haruna da shugabannin taron jama’a kuwa suka ƙidaya iyalan Lawiyawa uku, wato Kohatawa, da Gershonawa da Merariyawa bisa ga iyalansu da gidajen kakanninsu, aka rubuta dukan mazaje daga mai shekara talatin zuwa mai shekara hamsin, waɗanda za su iya aiki a alfarwa ta sujada, kamar haka,

Kohat dubu biyu da ɗari bakwai da hamsin (2,750),
Gershon dubu biyu da ɗari shida da talatin (2,630),
Merari dubu uku da ɗari biyu (3,200),
Jimilla duka, dubu takwas da ɗari biyar da tamanin (8,580).

49 Aka ba kowannensu aikinsa da ɗaukar kaya bisa ga umarnin da Ubangiji ya yi wa Musa. Haka kuwa aka ƙidaya su kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

Categories
L. KID

L. KID 5

Ƙazantattun Mutane

1 Sai Ubangiji ya ce wa Musa,

2 “Ka umarci Isra’ilawa su fitar da kuturu, da mai ɗiga, da wanda ya ƙazantu ta wurin taɓa gawa, daga cikin zango.

3 Su fitar da mace ko namiji daga cikin zango, don kada su ƙazantar da zangonku inda nake zaune.”

4 Sai Isra’ilawa suka fitar da su daga cikin zango kamar yadda Ubangiji ya faɗa wa Musa. Haka mutanen Isra’ila suka yi.

Biyan Diyya saboda Ɓarna

5 Ubangiji kuma ya ba Musa

6 waɗannan ka’idodi domin Isra’ilawa. Idan wani ya aikata rashin gaskiya ga Ubangiji, ta wurin saɓa wa wani,

7 sai ya hurta zunubinsa, sa’an nan ya biya cikakkiyar diyyar abin da ƙarin humushin abin, ya ba mutumin da ya yi wa laifin.

8 Idan wanda ya yi wa laifin ya rasu, ba shi kuma da wani dangi na kusa wanda za a ba diyyar, sai a kai diyyar gaban Ubangiji domin firist, tare da ragon hadaya, don yin kafarar da za a yi masa.

9 Dukan sadakoki na tsarkakakkun abubuwa na Isra’ilawa waɗanda sukan kawo wa firist, za su zama nasa.

10 Kowane firist zai adana sadakokin da aka ba shi.

Matsalar Miji mai Kishi

11 Ubangiji kuma ya umarci Musa

12-14 ya faɗa wa Isra’ilawa waɗannan ka’idodi. Idan mutum yana shayin matarsa kan tana yi masa rashin aminci, har ta ƙazantar da kanta ta wurin kwana da wani mutum, amma mijin bai tabbatar ba, domin ta yi abin a asirce, ba kuwa mai shaida, ba a kuma kama ta tana cikin yi ba, ko kuma mijin ya yi shayinta ko da ba ta aikata irin wannan laifi ba,

15 duk da haka sai mutum ya kawo matarsa a gaban firist, ya kawo kuma hadayar da ake bukata, wato humushin garwar garin sha’ir, amma kada ya zuba mai ko kayan ƙanshi, gama hadaya ce domin kishi, domin a bayyana gaskiya a fili.

16 Sai firist ya kawo ta kusa, ya tsai da ita a gaban Ubangiji.

17 Ya ɗebo ruwa mai tsarki a cikin kasko, ya kuma ɗauki ƙurar ƙasar da take a alfarwa ta alkawari ya zuba a ruwan.

18 Sa’an nan firist zai kwance gashin kanta, ya sa hadaya ta gari don tunawa a hannuwanta, hadayar gari ce ta kishi. Ya riƙe ruwan nan mai ɗaci da yake kawo la’ana a hannunsa.

19 Sa’an nan zai sa ta ta yi rantsuwa, ya ce mata, “Idan wani mutum bai kwana da ke ba, to, bari ki kuɓuta daga la’anar da ruwan nan mai ɗaci zai kawo.

20 Amma idan kin kwana da wani mutum wanda ba mijinki ba ne,

21 bari Ubangiji ya sa sunanki ya la’antu cikin jama’arki, ya sa cinyarki ta shanye, cikinki kuma ya kumbure.

22 Bari ruwan nan ya shiga cikinki, ya sa cikinki ya kumbure, cinyarki kuma ta shanye.”

Sai matar ta amsa, ta ce, “Amin, amin, Ubangiji ya sa ya zama haka.”

23 Firist ɗin zai rubuta waɗannan la’anoni a cikin littafi sa’an nan ya wanke rubutun da ruwan nan mai ɗaci.

24 Ya sa matar ta shanye ruwa wanda yake kawo la’ana, sai ruwan ya shiga cikinta, ya zama la’ana mai ɗaci.

25 Firist kuma zai karɓi hadaya ta gari don kishi a hannun matar, ya kaɗa ta a gaban Ubangiji. Sa’an nan ya kai wurin bagade.

26 Sai ya ɗibi garin hadaya cike da tafin hannu don yin hadayar tunawa, ya ƙone shi a bisa bagaden, bayan wannan ya sa matar ta sha ruwan.

27 Bayan da ya sa ta ta sha ruwan, idan ta ƙazantar da kanta, ta kuwa ci amanar mijinta, ruwan nan mai kawo la’ana zai shiga cikinta ya zama la’ana mai ɗaci, cikinta zai kumbure, cinyarta ta shanye, matar kuwa za ta zama la’ananniya cikin jama’arta.

28 Amma idan matar ba ta ƙazantar da kanta ba, ita tsattsarka ce, za ta kuɓuta, har ta haifi ‘ya’ya.

29 Wannan ita ce dokar kishi idan mutum yana shayin matarsa, wai wani yana kwana da ita.

30 Matar kuwa za ta tsaya a gaban Ubangiji, firist kuwa zai yi da ita bisa ga wannan doka duka.

31 Mijin zai kuɓuta daga muguntar, amma matar za ta ɗauki muguntarta, idan ta yi laifin.

Categories
L. KID

L. KID 6

Ka’idodin Zama Keɓaɓɓe

1 Ubangiji kuma ya umarci Musa

2 ya faɗa wa Isra’ilawa, cewa idan mace ko namiji ya ɗau wa’adi na musamman na zama keɓaɓɓe domin ya keɓe kansa ga Ubangiji,

3 sai ya keɓe kansa daga ruwan inabin da yake sa maye da ruwan inabi mai tsami. Kada kuma ya sha ruwan inabi mai tsami da yake sa maye da kowane irin abin sha da aka yi da ‘ya’yan inabi mai tsami. Kada kuma ya ci ɗanyu ko busassun ‘ya’yan inabi.

4 A dukan kwanakin nan da ya keɓe kansa, kada ya ci kowane irin abu da aka yi da kurangar inabi, ko da ƙwayar inabi ko da ɓawonsa.

5 A dukan kwanakin wa’adinsa na keɓewa, kada aska ta taɓa kansa, sai kwanakin keɓewar kansa ga Ubangiji sun cika. Zai zama mai tsarki, zai kuma bar sumarsa ta yi tsawo.

6 A dukan kwanakin da ya keɓe kansa ga Ubangiji, kada ya kusaci gawa.

7 Ko ta mahaifinsa ce, ko ta mahaifiyarsa, ko ta ɗan’uwansa, ko ta ‘yar’uwarsa, ba zai ƙazantar da kansa ba, tun da yake ya keɓe kansa ga Allahnsa.

8 Shi tsattsarka ne ga Ubangiji dukan kwanakin da ya keɓe kansa.

9 Idan farat ɗaya wani mutum ya rasu kusa da shi, to, keɓewarsa ta ƙazantu, sai ya aske kansa a ranar tsarkakewarsa a kan rana ta bakwai.

10 A rana ta takwas kuwa zai kawo wa firist ‘yan kurciyoyi biyu, ko ‘yan tattabarai biyu a bakin ƙofar alfarwa ta sujada.

11 Sai firist ya miƙa ɗaya don hadayar zunubi, ɗaya kuma don hadayar ƙonawa, ya yi kafara dominsa, gama ya yi zunubi saboda gawa. A wannan rana zai sāke keɓe kansa.

12 Sai ya sāke keɓe kansa ga Ubangiji daidai da kwanakin da ya ɗauka a dā. Zai kawo ɗan rago bana ɗaya na yin hadaya don laifi. Kwanakin da ya yi a dā ba su cikin lissafi domin keɓewarsa ta dā ta ƙazantu.

13 Wannan ita ce ka’idar zama keɓaɓɓe a ranar da keɓewarsa ta cika. Za a kai shi ƙofar alfarwa ta sujada,

14 ya miƙa wa Ubangiji hadayarsa ta ɗan rago bana ɗaya mara lahani don yin hadaya ta ƙonawa, da ‘yar tunkiya bana ɗaya marar lahani ta yin hadaya don zunubi, da rago marar lahani don yin hadaya ta salama,

15 da kwandon abinci marar yisti da aka yi da lallausan gari kwaɓaɓɓe da mai, da ƙosai wanda aka yayyafa masa mai, da hadaya ta gari, da hadayu na sha.

16 Sai firist ɗin ya kai su gaban Ubangiji, ya miƙa hadaya don zunubi, da hadaya ta ƙonawa.

17 Ya kuma miƙa rago don hadaya ta salama ga Ubangiji tare da kwandon abinci, da ƙosai. Firist ɗin kuma zai miƙa hadaya ta gari, da hadaya ta sha.

18 Sai kuma keɓaɓɓen ya aske sumarsa a ƙofar alfarwa ta sujada, sa’an nan ya kwashe sumar, ya zuba cikin wutar da take ƙarƙashin hadaya ta salama.

19 Firist ɗin zai ɗauki dafaffiyar kafaɗar ragon, da malmala guda marar yisti daga cikin kwando, da ƙosai guda, ya sa su a tafin hannun keɓaɓɓen bayan da keɓaɓɓen ya riga ya aske sumarsa.

20 Firist ɗin zai haɗa su don yin hadayar kaɗawa a gaban Ubangiji. Za su zama rabo mai tsarki na firist tare da ƙirjin da aka kaɗa da cinyar da aka yi hadayar ɗagawa da ita. Bayan haka keɓaɓɓen ya iya shan ruwan inabi.

21 Wannan ita ce ka’ida a kan keɓaɓɓe wanda ya ɗau wa’adi. Hadayarsa ga Ubangiji za ta zama bisa ga keɓewarsa, banda kuma abin da ya iya bayarwa. Sai ya cika wa’adin da ya ɗauka bisa ga ka’idar keɓewarsa.

Albarkar da Firist zai Sa wa Jama’a

22 Ubangiji ya umarci Musa

23 ya faɗa wa Haruna da ‘ya’yansa maza, su sa wa Isra’ilawa albarka haka, su ce musu,

24 “Ubangiji ya sa muku albarka, ya kiyaye ku.

25 “Ubangiji ya sa fuskarsa ta haskaka ku, ya yi muku alheri.

26 “Ubangiji ya dube ku da idon rahama, ya ba ku salama.”

27 Idan suka sa wa jama’a wannan albarka sa’ad da suke addu’a ga Ubangiji domin Isra’ilawa, Ubangiji zai sa musu albarka.

Categories
L. KID

L. KID 7

Hadayun Keɓe Bagade

1 A ranar da Musa ya gama kafa alfarwa ta sujada, ya shafa mata mai, ya tsarkake ta, da dukan kayayyakinta, ya kuma shafa wa bagaden mai, ya tsarkake shi da dukan kayayyakinsa.

2 Sai shugabannin Isra’ila, wato shugabannin gidajen kakanninsu, su ne shugabannin kabilansu, waɗanda suka shugabanci waɗannan da aka ƙidaya,

3 suka kawo hadayarsu a gaban Ubangiji, karusai shida rufaffu, da takarkarai goma sha biyu. Shugabanni biyu suka ba da karusa ɗaya, kowannensu kuwa ya ba da takarkari ɗaya, da suka gama miƙa su,

4 sai Ubangiji ya ce wa Musa,

5 “Karɓi waɗannan daga gare su domin a yi aiki da su a alfarwa ta sujada. Ka ba da su ga Lawiyawa, a ba kowane mutum bisa ga aikinsa.”

6 Musa kuwa ya karɓi karusan, da takarkaran, ya ba Lawiyawa.

7 Ya ba ‘ya’ya maza na Gershon karusai biyu da takarkarai huɗu bisa ga aikinsu.

8 Ya kuwa ba ‘ya’ya maza na Merari karusai huɗu da takarkarai takwas bisa ga aikinsu, a hannun Itamar ɗan Haruna, firist.

9 Amma bai ba ‘ya’ya maza na Kohat kome ba, domin aikinsu shi ne lura da kayayyaki masu tsarki waɗanda ake ɗauka a kafaɗa.

10 Sai shugabanni suka miƙa hadayu domin keɓewar bagade a ranar da aka zuba masa mai. Suka fara miƙa sadakokinsu a bagaden,

11 Ubangiji kuma ya ce wa Musa, “Bari shugabannin su kawo hadayunsa domin keɓewar bagade, har kwana sha biyu, kowa a ranarsa.”

12-83 Suka miƙa hadayunsu bi da bi kamar haka,

Yahuza Nashon ɗan Amminadab
Issaka Netanel ɗan Zuwar
Zabaluna Eliyab ɗan Helon
Ra’ubainu Elizur ɗan Shedeyur
Saminu Shelumiyel ɗan Zurishaddai
Gad Eliyasaf ɗan Deyuwel
Ifraimu Elishama ɗan Ammihud
Manassa Gamaliyel ɗan Fedazur
Biliyaminu Abidan ɗan Gideyoni
Dan Ahiyezer ɗan Ammishaddai
Ashiru Fagiyel ɗan Okran
Naftali Ahira ɗan Enan

Hadayun da kowannensu ya kawo duk daidai da juna suke, farantin azurfa na shekel ɗari da talatin, da kwanon azurfa na shekel saba’in, bisa ga ma’aunin kuɗin da ake aiki da shi, duka suna cike da garin da aka kwaɓa da mai domin hadaya ta gari, cokali na zinariya guda na shekel goma, cike da kayan ƙanshi, da ɗan bijimi guda, da rago ɗaya, da ɗan rago bana ɗaya domin hadaya ta ƙonawa, da akuya guda domin hadaya ta zunubi, da bijimai biyu, da raguna biyar, da awaki biyar, da ‘yan raguna biyar bana ɗaya ɗaya, domin hadaya ta salama.

84-88 Ga jimillar hadayun da shugabanni goma sha biyu suka kawo domin keɓewar bagaden:

farantan azurfa goma sha biyu da kwanonin azurfa goma sha biyu, duka nauyinsu shekel dubu biyu da ɗari huɗu

cokulan zinariya goma sha biyu, nauyinsu duka shekel ɗari da ashirin cike da kayan ƙanshi

bijimai goma sha biyu, da raguna goma sha biyu, da ‘yan raguna goma sha biyu bana ɗaya ɗaya, da kuma hadaya ta gari da za a haɗa da waɗannan domin hadaya ta ƙonawa

awaki goma sha biyu domin hadaya don zunubi

bijimai ashirin da huɗu, da raguna sittin, da awaki sittin, da ‘yan raguna bana ɗaya ɗaya guda sittin domin hadaya ta salama.

89 Duk lokacin da Musa ya shiga alfarwa ta sujada domin ya yi magana da Ubangiji, sai ya ji Ubangiji yana magana da shi daga bisa murfin akwatin alkawari, a tsakanin kerubobi masu fikafikai biyu.

Categories
L. KID

L. KID 8

Haruna ya Kakkafa Fitilu

1 Ubangiji kuwa ya ce wa Musa ya

2 faɗa wa Haruna cewa, “Sa’ad da za ka kakkafa fitilun nan bakwai, sai ka kakkafa su yadda za su haskaka sashin gaba.”

3 Haka kuwa Haruna ya yi. Ya kakkafa fitilun yadda za su haskaka a gaban alkukin, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

4 Da zinariya aka ƙera alkukin tun daga samansa har gindinsa, bisa ga fasalin da Ubangiji ya nuna wa Musa.

Keɓewar Lawiyawa

5 Ubangiji ya kuma ce wa Musa,

6 “Keɓe Lawiyawa daga cikin Isra’ilawa ka tsarkake su.

7 Ga yadda za ka tsarkake su. Ka yayyafa musu ruwan tsarkakewa. Su aske jikunansu duka, su kuma a wanke tufafinsu, sa’an nan za su tsarkaka.

8 Su kuma ɗauki maraƙi tare da lallausan garin hadaya kwaɓaɓɓe da mai. Kai kuma ka ɗauki wani maraƙi na yin hadaya don zunubi.

9 Sa’an nan ka gabatar da Lawiyawa a gaban alfarwa ta sujada, ka kira taron Isra’ilawa duka.

10 Sa’ad da ka gabatar da Lawiyawa a gaban Ubangiji, sai Isra’ilawa su ɗibiya hannuwansu bisa Lawiyawa.

11 Haruna kuma zai gabatar da Lawiyawan a gaban Ubangiji kamar hadaya ta kaɗawa daga Isra’ilawa domin su zama masu yi wa Ubangiji aiki.

12 Sa’an nan Lawiyawa za su ɗibiya hannuwansu a bisa kawunan maruƙan. Za ka yi hadaya domin zunubi da maraƙi ɗaya, ɗaya kuma ka miƙa shi hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji domin ka yi kafara saboda Lawiyawa.

13 “Za ka keɓe Lawiyawa su zama kamar hadaya ta kaɗawa gare ni, ka sa Haruna da ‘ya’yansa maza su lura da su.

14 Da haka za ka keɓe Lawiyawa daga cikin Isra’ilawa su zama nawa.

15 Bayan da ka tsarkake su, ka miƙa su kamar hadaya ta kaɗawa, za su cancanta su yi aiki a alfarwa ta sujada.

16 Gama dukansu an ba ni su daga cikin Isra’ilawa a maimakon dukan waɗanda suka fara buɗe mahaifa, wato dukan ‘ya’yan farin Isra’ilawa. Na karɓi Lawiyawa su zama nawa.

17 A ranar da na kashe ‘ya’yan fari na ƙasar Masar, na keɓe wa kaina dukan ‘ya’yan fari na Isra’ilawa, na mutum, da na dabba.

18 Na kuwa keɓe wa kaina Lawiyawa a maimakon dukan ‘ya’yan fari na Isra’ilawa.

19 Daga cikin Isra’ilawa kuwa na ba da Lawiyawa ga Haruna da ‘ya’yansa maza don su yi wa Isra’ilawa hidima a alfarwa ta sujada, su kuma yi kafara dominsu don kada annoba ta sami Isra’ilawa sa’ad da suka kusaci alfarwa ta sujada.”

20 Musa da Haruna kuwa da dukan taron Isra’ilawa suka yi wa Lawiyawa yadda Ubangiji ya umarce Musa, haka kuwa Isra’ilawa suka yi musu.

21 Lawiyawa suka tsarkake kansu, suka wanke tufafinsu. Haruna kuwa ya keɓe su, suka zama kamar hadaya ta kaɗawa ga Ubangiji, ya kuma yi kafara dominsu don ya tsarkake su.

22 Bayan haka Lawiyawa suka shiga alfarwa ta sujada don su yi aiki a gaban Haruna da ‘ya’yansa maza, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa a kan Lawiyawa, haka kuwa suka yi musu.

Adadin yawan Shekarun Aikin Lawiyawa

23 Ubangiji ya kuma ce wa Musa,

24 “Wannan ita ce ka’idar aikin Lawiyawa, tun daga mai shekara ashirin da biyar zuwa gaba, zai shiga yin aiki a alfarwa ta sujada.

25 Amma daga shekara hamsin, sai su huta daga aiki alfarwa ta sujada.

26 Amma su taimaki ‘yan’uwansu da tafiyar da ayyuka a cikin alfarwa ta sujada, sai dai ba za su ɗauki nauyin gudanar da aikin ba. Haka za ka shirya wa Lawiyawa aikinsu.”

Categories
L. KID

L. KID 9

Idin Ƙetarewa na Biyu

1 Sai Ubangiji ya yi wa Musa magana a jejin Sinai a watan farko na shekara ta biyu bayan fitarsu daga ƙasar Masar, ya ce,

2 “Sai Isra’ilawa su kiyaye Idin Ƙetarewa a ƙayyadadden lokacinsa.

3 A rana ta goma sha huɗu ga wannan wata, da maraice za su kiyaye shi a ƙayyadadden lokacinsa bisa ga dokokinsa da ka’idodinsa duka.”

4 Musa kuwa ya faɗa wa Isra’ilawa su kiyaye Idin Ƙetarewa.

5 Sai suka kiyaye Idin Ƙetarewa a rana ta goma sha huɗu ga watan farko da maraice a cikin jejin Sinai bisa ga dukan abin da Ubangiji ya umarci Musa. Haka kuwa Isra’ilawa suka yi.

6 Akwai waɗansu mutane da suka ƙazantu ta wurin taɓa gawar wani mutum,don haka ba su iya kiyaye Idin Ƙetarewar a ranar ba. Sai suka zo wurin Musa da Haruna a ranar,

7 suka ce masa, “Ai, mun ƙazantu saboda mun taɓa gawa. Me ya sa aka hana mu mu ba da hadaya ga Ubangiji tare da sauran ‘yan’uwanmu a ƙayyadadden lokacin yinta?”

8 Sai Musa ya ce musu, “Dakata, har na ji abin da Ubangiji zai umarta a kanku.”

9 Ubangiji kuwa ya faɗa wa Musa

10 ya faɗa wa Isra’ilawa ya ce, “Idan wani mutum na cikinku, ko na cikin zuriyarku, ya ƙazantu ta wurin taɓa gawa, ko kuwa ya yi tafiya mai nisa, duk da haka zai kiyaye Idin Ƙetarewa ga Ubangiji.

11 Za su kiyaye shi da maraice a watan biyu yana da kwana goma sha huɗu. Za su ci shi da abinci marar yisti da ganyaye masu ɗaci.

12 Kada su bar kome daga cikinsa ya kai gobe, kada kuwa a fasa ƙashinsa, sai su yi shi bisa ga dukan umarnin Idin Ƙetarewa.

13 Amma mutumin da yake da tsarki, bai kuma yi tafiya ba, ya kuwa ƙi kiyaye Idin Ƙetarewa, sai a raba wannan mutum da jama’arsa, gama bai miƙa hadayar Ubangiji a ƙayyadadden lokacin yinta ba. Wannan mutum zai ɗauki alhakin zunubinsa.

14 “Idan baƙo yana zaune a wurinku, shi ma sai ya kiyaye Idin Ƙetarewa ga Ubangiji bisa ga umarnai da ka’idodi na Idin Ƙetarewa. Ka’ida ɗaya ce ga baƙo da ɗan gari.”

Girgijen Wuta

15-16 A ranar da aka kafa alfarwa ta sujada, sai girgije ya sauko ya rufe ta. Da maraice kuwa girgijen yana kamar wuta.

17 A duk lokacin da aka gusar da girgijen, sai Isra’ilawa su kama hanya. A inda girgijen ya tsaya, nan kuma Isra’ilawa za su kafa zango.

18 Da umarnin Ubangiji Isra’ilawa suke tashi, da umarninsa kuma suke sauka. Muddin girgijen yana bisa alfarwar, sukan yi ta zamansu a zangon.

19 Ko da girgije ya daɗe a bisa alfarwar Isra’ilawa ba sukan tashi ba, sukan bi umarnin Ubangiji.

20 Wani lokaci girgijen yakan yi ‘yan kwanaki ne kawai bisa alfarwar. Tashinsu da zamansu sun danganta ga umarnin Ubangiji.

21 Wani lokaci girgijen yakan zauna a bisa alfarwar daga maraice zuwa safiya ne kawai, sa’an nan ya tashi, su kuma sai su tashi. Amma idan girgijen ya yini, ya kwana, sa’an nan ya tashi, su kuma sai su tashi.

22 Ko kwana biyu ne girgijen ya yi, yana zaune a bisa alfarwar ko wata guda, ko fi, sai Isra’ilawa su yi ta zamansu a zangon, ba za su tashi ba. Amma in ya tashi, sai su kuma su tashi.

23 Da umarnin Ubangiji suke sauka, da umarninsa kuma suke tashi, suna bin faɗarsa, yadda ya umarci Musa.

Categories
L. KID

L. KID 10

Kakaki na Azurfa

1 Ubangiji kuma ya ce wa Musa,

2 “Ka ƙera kakaki biyu na azurfa don ka riƙa kirawo taron jama’a, don kuma ka riƙa sanashe su lokacin tashi daga zangon.

3 Lokacin da aka busa kakaki biyu ɗin gaba ɗaya, sai taron jama’a duka su tattaru a wurinka a ƙofar alfarwa ta sujada.

4 Amma idan ɗaya kaɗai aka busa, sai shugabannin Isra’ila su tattaru a wurinka.

5 Sa’ad da kuka yi busar faɗakarwa, waɗanda suke zaune a gabashin zangon za su tashi.

6 Sa’ad da kuma kuka yi busar faɗakarwa ta biyu, waɗanda suke a kudancin zangon za su tashi. Sai a yi busar faɗakarwa a kowane lokaci da za su tashi.

7 Amma idan za a kira jama’a ne sai a yi busa da ƙarfi amma banda faɗakarwa.

8 ‘Ya’yan Haruna, maza, firistoci, su ne za su busa kakakin.

“Kakakin za su zama muku ka’ida ta din din din cikin dukan zamananku.

9 Sa’ad da kuka tafi yaƙi a ƙasarku gāba da maƙiyanku da suke matsa muku lamba, sai ku yi busar faɗakarwan nan da kakakin, Ubangiji Allahnku zai tuna da ku, ya cece ku daga maƙiyanku.

10 A ranar murnarku, da lokacin ƙayyadaddun idodinku, da tsayawar watanninku, za ku busa kakakin a lokacin yin hadayunku na ƙonawa, da hadayunku na salama. Za su zama sanadin tunawa da ku a gaban Allahnku. Ni ne Ubangiji Allahnku.”

Tashin Isra’ilawa daga Sinai

11 A rana ta ashirin ga watan biyu a shekara ta biyu, sai aka gusar da girgijen daga kan alfarwa ta sujada.

12 Isra’ilawa kuwa suka tashi daki-daki daga jejin Sinai. Girgijen kuma ya tsaya a jejin Faran.

13 Suka fara tafiyarsu bisa ga umarnin da Ubangiji ya yi wa Musa.

14 Tutar zangon kabilar mutanen Yahuza ta fara tashi, ƙungiyoyinsu suna biye. Nashon, ɗan Amminadab, shi ne shugaban rundunarsu.

15 Shugaban rundunar kabilar mutanen Issaka Netanel ne, ɗan Zuwar.

16 Shugaban rundunar kabilar mutanen Zabaluna Eliyab ne, ɗan Helon.

17 Sa’an nan aka kwankwance alfarwar, sai ‘ya’yan Gershon, da ‘ya’yan Merari masu ɗaukar alfarwar suka kama hanya.

18 Tutar zangon kabilar mutanen Ra’ubainu ta tashi, ƙungiyoyinsu suna biye. Shugaban rundunarsu Elizur ne, ɗan Shedeyur.

19 Shugaban rundunar kabilar mutanen Saminu kuwa Shelumiyel ne, ɗan Zurishaddai.

20 Shugaban rundunar kabilar mutanen Gad Eliyasaf ne, ɗan Deyuwel.

21 Daga nan sai Kohatawa masu ɗauke da kayayyaki masu tsarki suka tashi. Kafin su isa masaukin, an riga an kafa alfarwar.

22 Tutar zangon mutanen Ifraimu ta tashi, ƙungiyoyinsu na biye. Shugaban rundunarsu Elishama ne, ɗan Ammihud.

23 Shugaban rundunar kabilar mutanen Manassa Gamaliyel ne, ɗan Fedazur.

24 Shugaban rundunar kabilar mutanen Biliyaminu Abidan ne, ɗan Gideyoni.

25 A ƙarshe sai ƙungiyar mutanen Dan da take bayan dukan zangon, ta tashi, ƙungiyoyinsu suna biye. Shugaban rundunarsu Ahiyezer ne, ɗan Ammishaddai.

26 Shugaban rundunar kabilar mutanen Ashiru Fagiyel ne, ɗan Okran.

27 Shugaban rundunar kabilar mutanen Naftali Ahira ne, ɗan Enan.

28 Wannan shi ne tsarin tafiyar Isra’ilawa bisa ga rundunansu sa’ad da sukan tashi.

29 Sai Musa ya ce wa Hobab ɗan Reyuwel Bamadayane, surukinsa, “Muna kan hanya zuwa wurin da Ubangiji ya ce zai ba mu, ka zo tare da mu, za mu yi maka alheri, gama Ubangiji ya alkawarta zai yi wa Isra’ila alheri.”

30 Amma ya ce masa, “Ba zan tafi ba, zan koma ƙasata da wurin dangina.”

31 Musa kuwa ya ce masa, “Ina roƙonka kada ka rabu da mu, gama ka san jejin da muke zango, kai za ka zama idonmu.

32 Idan ka tafi tare da mu, kowane irin alheri da Ubangiji zai yi mana, mu kuma haka za mu yi maka.”

Mutanen suka Kama Hanya

33 Sai suka tashi daga dutsen Ubangiji, wato Sinai, suka yi tafiya kwana uku. Akwatin alkawarin Ubangiji kuwa ya wuce gabansu don ya nemar musu masauki.

34 A duk lokacin da suka tashi daga zango, sai girgijen Ubangiji ya inuwantar da su da rana.

35 Duk kuma lokacin da akwatin zai tashi, sai Musa ya ce, “Ka tashi, ya Ubangiji, ka sa maƙiyanka su warwatse, ka sa waɗanda suke ƙinka su gudu gabanka.”

36 Sa’ad da akwatin ya sauka kuma, Musa yakan ce, “Ka komo, ya Ubangiji, a wurin dubun dubbai na iyalan Isra’ila.”