Categories
L. KID

L. KID 11

Ubangiji zai Ba su Nama

1 Da Ubangiji ya ji gunagunin da mutanen suke yi saboda wahalarsu, sai ya husata ƙwarai, wutarsa ta yi ta ci a cikinsu har ta ƙone wani gefe na zangon.

2 Sai mutanen suka yi ta yi wa Musa kuka, Musa kuwa ya yi addu’a ga Ubangiji, wutar kuwa ta mutu.

3 Aka sa wa wurin suna Tabera, wato matoya, domin wutar Ubangiji ta yi ƙuna a cikinsu.

4 Tattarmukan da suke cikinsu kuwa suka faye kwaɗayin nama, har Isra’ilawa ma da kansu suka fara gunaguni suna cewa, “Wa zai ba mu nama mu ci?

5 Mun tuna da kifin da muka ci kyauta a Masar, da su kakamba, wato wani irin kayan lambu ne mai yaɗuwa, da guna, da sāfa, da albasa, da tafarnuwa.

6 Yanzu ranmu ya yi yaushi, ba wani abu, sai dai wannan manna muke gani.”

7 Manna kuwa kamar tsabar riɗi take, kamanninta kuwa kamar na ƙāro ne.

8 Mutane sukan fita su tattara ta, su niƙa, ko kuwa su daka, su dafa, su yi waina da ita. Dandanar wainar tana kamar wadda aka yi da mai.

9 Manna takan zubo tare da raɓa da dad dare a zangon.

10 Musa ya ji mutanen suna ta gunaguni ko’ina a cikin iyalansu, kowane mutum a ƙofar alfarwarsa. Ubangiji kuwa ya husata ƙwarai.

11 Sai Musa ya ce wa Ubangiji, “Don me ka wahalar da bawanka? Me ya sa ban sami tagomashi a gare ka ba, da ka jibga wahalar dukan mutanen nan a kaina?

12 Ni na ɗauki cikinsu? Ko kuwa ni ne na haife su, har da za ka ce mini, ‘Ka ɗauke su a ƙirjinka, kamar yadda mai reno yake rungume jariri, zuwa ƙasa wadda ka rantse za ka bai wa kakanninsu?’

13 A ina zan samo nama da zan ba wannan jama’a duka? Gama suna ta gunaguni a gabana, suna cewa, ‘Ba mu nama mu ci.’

14 Ba zan iya ɗaukar nawayar mutanen nan ni kaɗai ba, gama nauyin ya fi ƙarfina.

15 Idan haka za ka yi da ni, ina roƙonka ka kashe ni, idan na sami tagomashi a gare ka, don kada in rayu in ga wannan baƙin ciki.”

16 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Tattaro mini mutum saba’in daga cikin dattawan Isra’ila waɗanda aka sani su ne dattawa da shugabannin jama’ar, ka kawo su a alfarwa ta sujada, ka sa su tsaya tare da kai.

17 Ni kuwa zan sauko, in yi magana da kai a can. Zan ɗiba daga cikin ruhun da yake cikinka, in ba su. Su kuma za su ɗauki nawayar jama’ar tare da kai, domin kada ka ɗauki nawayar kai kaɗai.

18 Ka ce wa jama’ar, su tsarkake kansu don gobe, za su ci nama, gama Ubangiji ya ji gunagunin da suka yi, da suka ce, ‘Wa zai ba mu nama mu ci? Ai, zama cikin Masar ya fi mana.’ Domin haka Ubangiji zai ba su nama, za su kuwa ci.

19 Ba ma don kwana ɗaya, ko biyu, ko biyar, ko goma, ko ashirin kaɗai za su ci ba.

20 Amma har wata guda cur. Za su ci har ya gundure su, ya zama musu abin ƙyama saboda sun ƙi Ubangiji wanda yake tare da su, suka yi gunaguni a gabansa , suna cewa, ‘Me ya sa ma, muka fito Masar?’ ”

21 Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “Mutum dubu ɗari shida (600,000) ne suke tafe tare da ni, ga shi kuwa, ka ce za ka ba su nama, za su ci har wata guda cur.

22 Za a yanyanka musu garkunan tumaki, da na awaki, da na shanu, don su ishe su? Ko kuwa za a tattara musu dukan kifayen teku don su ishe su?”

23 Sai Ubangiji ya amsa wa Musa, “Ikon Ubangiji ya gaza ne? Yanzu za ka gani ko maganata gaskiya ce, ko ba gaskiya ba ce.”

Shugabanni sun yi Annabci

24 Musa kuwa ya fita, ya faɗa wa jama’a maganar Ubangiji, ya kuma tattara dattawa saba’in daga cikin jama’ar, ya sa su tsaya kewaye da alfarwar.

25 Sa’an nan Ubangiji ya sauko cikin girgije, ya yi masa magana, ya kuma sa ruhun da yake kansa, ya zama a kan dattawan nan saba’in. Sa’ad da ruhun ya zauna a kansu sai suka yi annabci, amma daga wannan kuma ba su ƙara yi ba.

26 Akwai mutum biyu da suka ragu a zangon, sunan ɗayan Eldad, ɗayan kuwa Medad. Ruhun kuma ya zauna a kansu gama suna cikin dattawan nan da aka lasafta, amma ba su fita zuwa alfarwa ba, sai suka yi annabci a zangon.

27 Sai wani saurayi ya sheƙa a guje ya faɗa wa Musa, ya ce, “Ga Eldad da Medad suna nan suna annabci a cikin zangon.”

28 Joshuwa ɗan Nun, mai yi wa Musa barantaka, ɗaya daga cikin zaɓaɓɓun, ya ce, “Ya shugabana, Musa, ka hana su.”

29 Amma Musa ya ce masa, “Kishi kake yi domina? Da ma jama’ar Ubangiji duka annabawa ne, har ma ya sa Ruhunsa a cikinsu!”

30 Sai Musa da dattawan Isra’ila suka koma zango.

Ubangiji ya Aiko da Makware

31 Sai iska ta huro daga wurin Ubangiji, ta koro makware daga teku, ta bar su birjik kusa da zango, misalin nisan tafiyar yini guda ta kowace fuska. Tsayin tashinsu daga ƙasa misalin kamu biyu ne.

32 Sai mutane suka tashi suka yi ta tattara makware dukan wannan yini, da dukan dare, har kashegari duka. Wanda ya tattara kaɗan, ya tara garwa metan. Suka shanya abinsu kewaye da zangon.

33 Tun suna cikin cin naman, sai Ubangiji ya husata da mutanensa, ya bugi jama’a da annoba mai zafi.

34 Don haka aka sa wa wurin suna Kibrot-hata’awa, wato makabarta, gama a can ne aka binne mutanen nan makwaɗaita.

35 Daga Kibrot-hata’awa mutanen suka yi tafiya zuwa Hazerot, a can suka sauka.

Categories
L. KID

L. KID 12

Aka Hukunta Maryamu

1 Sai Maryamu da Haruna suka zargi Musa saboda mace, Bahabashiya, wadda ya aura.

2 Suka ce, “Da Musa kaɗai ne, Ubangiji ya yi magana, bai yi magana da mu kuma ba?” Ubangiji kuwa ya ji.

3 (Musa dai mai tawali’u ne ƙwarai, fiye da kowane mutum a duniya.)

4 Farat ɗaya sai Ubangijiya ce wa Musa, da Haruna, da Maryamu, “Ku uku, ku tafi zuwa alfarwa ta sujada.” Sai su uku suka tafi.

5 Ubangiji kuwa ya zo cikin al’amudin girgije, ya tsaya a ƙofar alfarwar, ya yi kira, “Haruna! Maryamu!” Su biyu fa suka gusa gaba.

6 Ya ce, “Ku ji abin da zan faɗa! Idan akwai annabawa a cikinku, nakan bayyana gare su cikin wahayi, in kuma yi magana da su ta cikin mafarki.

7 Ba haka nake magana da bawana Musa ba, na sa shi ya lura da dukkan jama’ata Isra’ila.

8 Nakan yi magana da shi fuska da fuska a sarari, ba a duhunce ba. Yakan kuma ga zatina. Me ya sa ba ku ji tsoron zargin bawana Musa ba?”

9 Ubangiji kuwa ya husata da su, ya rabu da su.

10 Sa’ad da al’amudin girgijen ya tashi daga kan alfarwar, sai ga Maryamu ta kuturce, fari fat kamar auduga. Da Haruna ya juya wajen Maryamu, ya ga ta zama kuturwa.

11 Sai ya ce wa Musa, “Ya shugabana, ina roƙonka, kada ka hukunta mu saboda wannan zunubi, mun yi aikin wauta.

12 Na roƙe ka kada ka bari ta zama kamar matacce wanda rabin jikinsa ruɓaɓɓe ne a lokacin da aka haife shi.”

13 Sai Musa ya roƙi Ubangiji, ya ce, “Ina roƙonka, ya Allah, ka warkar da ita.”

14 Amma ubangiji ya ce wa Musa, “Da a ce mahaifinta ne ya tofa mata yau a fuskarta, ba za ta ji kunya har kwana bakwai ba? Bari a fitar da ita a bayan zangon kwana bakwai, bayan haka a shigar da ita.”

15 Aka fitar da Maryamu a bayan zangon har kwana bakwai. Jama’ar kuwa ba su ci gaba da tafiya ba, sai da aka shigar da Maryamu a zangon.

16 Bayan wannan jama’a suka tashi daga Hazerot suka sauka a jejin Faran.

Categories
L. KID

L. KID 13

‘Yan Leƙen Asirin Ƙasa

1 Ubangiji kuma ya ce wa Musa,

2 “Ka aiki mutane su leƙi asirin ƙasar Kan’ana wadda nake ba Isra’ilawa. Daga kowace kabila na kakanninsu, ka zaɓi mutum guda wanda yake shugaba a cikinsu.”

3-15 Musa kuwa ya yi biyayya, daga jejin Faran ya aika da waɗannan shugabanni,

Shammuwa ɗan Zakkur, daga kabilar Ra’ubainu.

Shafat ɗan Hori, daga kabilar Saminu.

Kalibu ɗan Yefunne, daga kabilar Yahuza.

Igal ɗan Yusufu, daga kabilar Issaka.

Hosheya ɗan Nun, daga kabilar Ifraimu.

Falti ɗan Rafu, daga kabilar Biliyaminu.

Gaddiyel ɗan Sodi, daga kabilar Zabaluna.

Gaddi ɗan Susi, daga kabilar Manassa.

Ammiyel ɗan Gemalli, daga kabilar Dan.

Setur ɗan Maikel, daga kabilar Ashiru.

Nabi ɗan Wofsi,daga kabilar Naftali.

Geyuwel ɗan Maci,daga kabilar Gad.

16 Waɗannan su ne mutanen da Musa ya aika su leƙo asirin ƙasar. Amma Musa ya ba Hosheya, ɗan Nun, suna Joshuwa.

17 Sa’ad da Musa ya aike su leƙen asirin ƙasar Kan’ana, ya ce musu, “Ku haura, ku bi ta Negeb har zuwa ƙasar tuddai,

18 ku ga yadda ƙasar take, ku ga ko mutanenta ƙarfafa ne, ko raunana ne, ko su kima ne, ko kuwa suna da yawa,

19 ko ƙasa tasu mai ni’ima ce, ko babu, ko biranensu marasa garu ne, ko masu garu ne,

20 ko ƙasar tana da wadata,ko matalauciya ce, ko ƙasar kurmi ce, ko fili. Ku yi jaruntaka, ku ɗebo daga cikin albarkar ƙasar ku kawo.” (Gama lokacin farkon nunan inabi ne.)

21 Sai suka haura, suka leƙo asirin ƙasar tun daga jejin Zin har zuwa Rehob kusa da Hamat.

22 Suka haura ta wajen Negeb, suka isa Hebron inda Ahimaniyawa, da Sheshaiyawa, da Talmaiyawa, zuriyar ƙarfafan mutanen da ake kira Anakawa suke zaune. (An gina Hebron da shekara bakwai kafin a gina Zowan a Masar.)

23 Da suka isa Kwarin Eshkol, sai suka datse reshe guda na nonon inabi da ‘ya’ya cunkus. Suka rataya a sanda, mutum biyu suka ɗauka a kafaɗunsu. Suka kuma kawo rumman da ɓaure.

24 Aka kira wurin Kwarin Eshkol, wato “nonon inabi,” saboda nonon inabi wanda ‘yan leƙen ƙasa suka yanko a wurin.

25 Bayan sun yi kwana arba’in suna leƙen asirin ƙasar, sai suka komo.

26 Suka zo wurin Musa, da Haruna, da dukan taron jama’ar Isra’ila a jejin Faran a Kadesh. Suka faɗa musu labarin tafiyarsu, suka kuma nuna musu amfanin ƙasar da suka kawo.

27 Suka ce wa Musa, “Mun tafi ƙasar da ka aike mu, ƙasar tana da yalwar abinci, ga kuma amfanin ƙasar.

28 Amma mazaunan ƙasar ƙarfafa ne, biranenta kuma manya ne, masu garu, banda wannan kuma, mun ga Anakawa a can.

29 Amalekawa suna zaune a Negeb, Hittiyawa kuwa, da Yebusiyawa, da Amoriyawa suna zaune a ƙasar tuddai, Kan’aniyawa suna zaune kusa da teku, da kuma kusa da Kogin Urdun.”

30 Amma Kalibu ya sa mutane su yi shiru a gaban Musa, ya ce, “Bari mu tafi nan da nan mu mallaki ƙasar, gama za mu iya cinta.”

31 Sai mutanen da suka tafi tare da shi suka amsa suka ce, “Ba za mu iya haurawa, mu kara da mutanen ba, gama sun fi mu ƙarfi.”

32 Haka suka kawo wa ‘yan’uwansu, Isra’ilawa, mugun rahoton ƙasa wadda suka leƙi asirinta, suka ƙara da cewa, “Ƙasar da muka ratsa cikinta domin mu leƙi asirinta, tana cinye waɗanda suke zaune a cikinta, dukan mutane kuma da muka gani a cikinta ƙatti ne.

33 Mun kuma ga manyan mutane a can, wato mutanen Anakawa da suka fito daga Nefilawa. Sai muka ga kanmu kamar fara ne kawai, haka kuwa muke a gare su.”

Categories
L. KID

L. KID 14

Mutane suka yi Yaji

1 Sai dukan taron jama’a suka yi kuka da babbar murya dukan dare saboda wahala.

2 Dukan Isra’ilawa suka yi gunaguni a kan Musa da Haruna, suke ce, “Da ma mun mutu a ƙasar Masar, ko kuwa a wannan jeji.

3 Me ya sa Ubangiji ya kawo mu a wannan ƙasa, mu mutu da takobi? Matanmu da ƙanananmu za su zama ganima. Ba zai fi mana kyau, mu koma Masar ba?”

4 Sai suka ce wa juna, “Bari mu shugabantar da wani, mu koma Masar.”

5 Sa’an nan Musa da Haruna suka fāɗi rubda ciki a gaban dukan taron jama’ar Isra’ilawa.

6 Sai Joshuwa, ɗan Nun, da Kalibu, ɗan Yefunne waɗanda suke tare da masu leƙo asirin ƙasar, suka yayyage tufafinsu.

7 Suka ce wa dukan taron jama’ar Isra’ilawa, “Ƙasar da muka ratsa ta don mu leƙi asirinta, ƙasa ce mai kyau ƙwarai da gaske.

8 Idan Ubangiji yana jin daɗinmu zai kai mu a wannan ƙasa da take cike da yalwar abinci, ya ba mu ita.

9 Sai dai kada ku tayar wa Ubangiji, kada kuwa ku ji tsoron mutanen ƙasar. Za mu ci su ba wuya, Ubangiji kuma zai lalatar da gumakansu da suke kāre su. Ubangiji kuwa yana tare da mu, kada ku ji tsoronsu.”

10 Amma taron jama’a suka ce za su jajjefe su da duwatsu. Sai ɗaukakar Ubangiji ta bayyana ga dukan mutanen Isra’ila daga cikin alfarwa ta sujada.

11 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Har yaushe mutanen nan za su raina ni? Har yaushe za su ƙi gaskata ni, ko da yake na aikata alamu a tsakiyarsu?

12 Zan kashe su da annoba, in raba su da gādonsu. Zan yi wata al’umma da kai, wadda za ta fi su girma da iko.”

13 Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “Ai, Masarawa za su ji, gama ka fitar da mutanen daga cikinsu da ƙarfin ikonka.

14 Za su kuwa faɗa wa mutanen wannan ƙasa, gama sun riga sun ji, kai, ya Ubangiji, kana cikin tsakiyar jama’ar nan wadda kake bayyana kanka gare ta fuska da fuska. Girgijenka kuma yana tsaye a kansu, kakan kuma yi musu jagora da al’amudin wuta.

15 Idan kuwa ka kashe jama’ar nan gaba ɗaya, sai al’umman da suka ji labarinka, su ce,

16 ‘Domin Ubangiji ya kāsa kai jama’ar nan zuwa cikin ƙasar da ya rantse zai ba su, don haka ya kashe su a cikin jeji.’

17 Yanzu fa, ya Ubangiji, ina roƙonka ka sa ikonka ya zama da girma kamar yadda ka alkawarta cewa,

18 ‘Ubangiji mai jinkirin fushi ne, mai yawan ƙauna, kana gafarta mugunta da laifi, amma ba za ka ƙyale mai laifi ba, gama kakan ɗora wa ‘ya’ya alhakin muguntar iyaye, har tsara ta uku da ta huɗu.’

19 Ina roƙonka ka gafarta muguntar wannan jama’a saboda ƙaunarka mai girma, kamar yadda kake gafarta musu tun daga Masar har zuwa yanzu.”

20 Sai Ubangiji ya ce, “Saboda maganarka na gafarta.

21 Amma, hakika, na rantse da zatina, kamar yadda ɗaukakata za ta cika duniya duka,

22 dukan mutanen da suka ga ɗaukakata da alamuna waɗanda na aikata a Masar, da kuma a jejin, suka kuwa jarraba ni har sau goma, ba su kuma yi biyayya da maganata ba,

23 ba za su ga ƙasar da na rantse zan ba kakanninsu ba. Duk waɗanda suka raina ni, ba za su ga ƙasar ba,

24 sai dai bawana Kalibu da yake ruhunsa dabam ne, gama ya bi ni sosai.

25 Yanzu fa, tun da yake Amalekawa da Kan’aniyawa suna zaune a kwarin, gobe sai ku juya ku nufi wajen jejin ta hanyar Bahar Maliya.”

Ubangiji ya Hukunta Jama’ar saboda Gunaguni

26 Ubangiji kuma ya ce wa Musa da Haruna,

27 “Har yaushe wannan mugun taron jama’a zai yi ta gunaguni a kaina? Na ji gunagunin da Isra’ilawa suka yi a kaina.

28 Sai ka faɗa musu cewa, ‘Ni Ubangiji na rantse da zatina, abin da kuka sanar da ni zan yi muku.

29 Gawawwakin waɗanda suka yi gunaguni a kaina za su fādi cikin jejin nan. Dukan waɗanda aka ƙidaya, tun daga mai shekara ashirin zuwa gaba,

30 ba wanda zai shiga ƙasar da na rantse ta zama wurin zamanku, sai Kalibu, ɗan Yefunne, da Joshuwa ɗan Nun.

31 Amma ‘yan ƙanananku, waɗanda kuka ce za su zama ganima, su ne zan kai su cikin ƙasar, za su san ƙasar da kuka raina.

32 Amma ku, gawawwakinku za su fāɗi a jejin.

33 ‘Ya’yanku za su yi yawo a jeji shekara arba’in, za su sha wahala saboda rashin bangaskiyarku, har mutuminku na ƙarshe ya mutu a jejin.

34 Bisa ga kwanakin nan arba’in da kuka leƙi asirin ƙasar, haka za ku ɗauki alhakin zunubanku shekara arba’in, gama kowane kwana a maimakon shekara yake. Ta haka za ku sani ban ji daɗin abin da kuka yi ba.

35 Ni Ubangiji na faɗa, hakika, haka zan yi da wannan mugun taron jama’ar da suka haɗa kai, suka tayar mini. Za su ƙare ƙaƙaf a wannan jeji, a nan za su mutu.’ ”

36 Mutanen da Musa ya aika su leƙo asirin ƙasar, waɗanda suka komo, suka sa taron jama’a su yi gunaguni a kansa saboda sun kawo rahoto mai banrazana a kan ƙasar,

37 mutanen nan da suka kawo rahoto mai banrazana a kan ƙasar, annoba ta kashe su a gaban Ubangiji.

38 Sai dai Joshuwa, ɗan Nun, da Kalibu, ɗan Yefunne, kaɗai ne ba za su mutu ba daga cikin waɗanda suka tafi leƙen asirin ƙasar.

Ƙoƙarin Cin Ƙasar na Farko ya Kāsa

39 Da Musa ya faɗa wa Isra’ilawa abin da Ubangiji ya ce, sai jama’a suka yi baƙin ciki ƙwarai.

40 Suka tashi da sassafe, suka hau kan tudu, suna cewa, “Ga shi, a shirye muke mu tafi wurin da Ubangiji ya ambata, gama mun yi kuskure.”

41 Amma Musa ya ce, “Me ya sa kuke karya umarnin Ubangiji? Yin haka ba zai kawo nasara ba.

42 Kada ku haura domin kada ku sha ɗibga a gaban maƙiyanku, gama Ubangiji ba ya tare da ku.

43 Gama akwai Amalekawa da Kan’aniyawa a gabanku, za su kashe ku da takobi domin kun bar bin Ubangiji, don haka Ubangiji ba zai kasance tare da ku ba.”

44 Amma sai suka yi izgili, suka haura kan tudun, amma akwatin alkawari da Musa ba su bar zangon ba.

45 Sai Amalekawa da Kan’aniyawa, mazauna a kan tudun, suka gangaro, suka ci su, suka runtume su har Harma, wato hallakarwa.

Categories
L. KID

L. KID 15

Ka’idodin Yin Hadayu

1 Ubangiji ya ba Musa

2 waɗannan ka’idodi domin Isra’ilawa su kiyaye su a ƙasar da zai ba su.

3 Sa’ad da za su yi hadayar da akan yi da wuta ga Ubangiji daga cikin garken shanu, ko na tumaki da awaki, ko hadaya ta ƙonawa ce, ko ta cika wa’adi ce, ko ta yardar rai ce, ko ta ƙayyadaddun idodinsu ce, don a ba da ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji,

4 sai shi wanda ya kawo hadayar ga Ubangiji, ya kuma kawo hadaya ta gari, humushin garwa guda kwaɓaɓɓe da rubu’in moɗa na mai.

5 Ya kuma shirya hadaya ta sha, rubu’in moɗa ta ruwan inabi domin kowane ɗan rago na hadaya ta ƙonawa.

6 Idan kuwa da rago ne, a shirya hadaya ta gari humushi biyu na garwa, a kwaɓa da sulusin moɗa na mai.

7 Za a kuma miƙa hadaya ta sha da sulusin moɗa na ruwan inabi, don a yi ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji.

8 Idan kuwa da bijimi ne za a yi hadaya ta ƙonawar, ko sadaka domin cika wa’adi, ko ta salama ga Ubangiji,

9 sai a miƙa hadaya ta gari tare da bijimin, humushi uku na garwar gari kwaɓaɓɓe da rabin moɗa na mai.

10 Za a kuma miƙa hadaya ta sha da rabin moɗa na ruwan inabi. Hadaya ce da akan yi da wuta, mai yin ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji.

11 Haka za a yi da kowane bijimi, ko rago,ko ɗan rago,ko bunsuru.

12 Bisa ga yawan abin da aka shirya, haka za a yi da kowannensu bisa ga adadinsu.

13 Haka dukan waɗanda suke ‘yan ƙasa za su yi in za su ba da hadayar da akan yi da wuta don yin ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji.

14 Idan baƙon da yake baƙunci a cikinsu ko ko wane ne da yake tare da su a dukan zamanansu, yana so ya ba da hadayar da akan yi da wuta don a yi ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji, sai ya yi kamar yadda suke yi.

15 Ka’ida ɗaya ce domin taron jama’a da kuma baƙin da yake zaune tare da su. Ka’ida ce madawwamiya a dukan zamanansu. Kamar yadda suke a gaban Ubangiji, haka kuma baƙon da yake baƙunci a cikinsu yake.

16 Ka’ida ɗaya ce umarni kuma ɗaya ne domin su da baƙin da yake baƙunci a cikinsu.

17 Ubangiji ya ba Musa

18 waɗannan ka’idodi domin Isra’ilawa su kiyaye a ƙasar da zai ba su.

19 Sa’ad da suke cin amfaninta, sai su miƙa hadaya ta ɗagawa ga Ubangiji.

20 Daga cikin ɓarzajjen hatsinsu na nunan fari sai su yi wainar da za su ɗaga don yin hadaya da amfanin masussuka.

21 Daga cikin ɓarzajjen hatsinsu na nunan fari, sai su miƙa wa Ubangiji hadaya ta ɗagawa a dukan zamanansu.

22 Amma idan sun yi kuskure, ba su kiyaye dukan umarnan nan waɗanda Ubangiji ya faɗa wa Musa ba,

23 wato duk dai abin da ubangiji ya umarta ta bakin Musa tun daga ranar da Ubangiji ya ba da umarnan, har zuwa dukan zamanansu,

24 idan jama’a sun yi kuskure da rashin sani, sai su miƙa maraƙi don yin hadaya ta ƙonawa don a yi ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. Su kuma ba da hadaya ta gari, da hadaya ta sha tare da maraƙin bisa ga ka’idar. Za su kuma miƙa bunsuru ɗaya na yin hadaya don zunubi.

25 Firist kuwa zai yi kafara domin dukan jama’ar Isra’ilawa, za a kuwa gafarta musu kuskuren, domin sun kawo hadaya ta ƙonawa da hadaya don zunubi ga Ubangiji saboda kuskurensu.

26 Za a gafarta wa dukan taron jama’ar Isra’ilawa da baƙon da yake baƙunci a cikinsu, kuskuren da suka yi.

27 Idan bisa ga kuskure wani mutum ya yi zunubi, sai ya ba da ‘yar akuya bana ɗaya ta yin hadaya don zunubi.

28 Firist kuwa zai yi kafara a gaban Ubangiji saboda mutumin da ya yi kuskuren, gama ya yi zunubi ba da saninsa ba, za a kuwa gafarta masa.

29 Ka’idarsu ɗaya ce a kan wanda ya yi kuskure, ko Ba’isra’ile ne, ko baƙon da yake baƙunci a cikinsu.

30 Amma mutumin da ya yi laifi da gangan, ko shi ɗan ƙasa ne, ko kuma baƙo ne, ya sāɓi Ubangiji, sai a kashe shi,

31 gama ya raina maganar Ubangiji, ya karya umarninsa. Hakika za a kashe mutumin nan, alhakin zunubinsa, yana wuyansa.

Jajjefewar Wanda ya Ɓata Ranar Asabar

32 Sa’ad da Isra’ilawa suke jeji, sai aka iske wani yana tattara itace a ranar Asabar.

33 Sai suka kai shi wurin Musa, da Haruna, da dukan taron jama’a.

34 Aka sa shi a gidan waƙafi domin ba a bayyana abin da za a yi da shi ba tukuna.

35 Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “A kashe mutumin, dukan taron jama’a za su jajjefe shi da duwatsu a bayan zangon.”

36 Dukan taron jama’a suka kai shi bayan zangon, suka jajjefe shi da duwatsu har ya mutu, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

Dokoki a kan Tuntayen Riguna

37 Ubangiji ya umarci Musa ya ce,

38 “Ka faɗa wa Isra’ilawa su yi wa shafin rigunansu tuntaye a dukan zamananku. A kan kowane tuntu, su sa shuɗin zare.

39 Tuntu zai zama musu abin dubawa don su riƙa tunawa da dukan umarnan Ubangiji su aikata su, don kada su bi son zuciyarsu, da sha’awar idanunsu yadda suka taɓa yi.

40 Da haka za su riƙa tunawa, su aikata dukan umarnaina su zama tsarkakakku gare ni.

41 Gama ni ne Ubangiji Allahnku, na fisshe ku daga ƙasar Masar domin in zama Allahnku. Ni ne Ubangiji Allahnku.”

Categories
L. KID

L. KID 16

Tayarwar Kora, da Datan, da Abiram

1-2 Sai Kora, ɗan Izhara, na kabilar Lawi, iyalin Kohat, ya yi ƙarfin hali ya tayar wa Musa. Waɗansu uku kuma daga kabilar Ra’ubainu suka haɗa kai da shi, su ne Datan da Abiram, ‘ya’yan Eliyab, da On,ɗan Felet, da waɗansu Isra’ilawa su ɗari biyu da hamsin, sanannun shugabanni da jama’a suka zaɓa.

3 Suka taru a gaban Musa da Haruna, suka ce musu, “Kun cika izgili, gama dukan taron jama’a na Ubangiji ne, Ubangiji kuwa yana tare da su. Me ya sa kai Musa ka aza kanka shugaba a kan taron jama’ar Ubangiji?”

4 Da Musa ya ji wannan, sai ya fāɗi rubda ciki ya yi addu’a.

5 Sa’an nan ya ce wa Kora da ƙungiyarsa, “Da safe Ubangiji zai nuna mana wanda yake nasa, zai sa wanda yake nasa, wato wanda ya zaɓa, ya sadu da shi a bagade.

6 Kai, Kora da ƙungiyarka duka, gobe, sai ku ɗauki farantan ƙona turare.

7 Ku zuba wuta a ciki, ku kuma zuba musu turaren wuta a gaban Ubangiji. Sa’an nan ne za mu ga wanda Ubangiji ya zaɓa tsakaninmu. Ku Lawiyawa ku ne kuka fi fiffiƙewa!”

8 Musa ya ci gaba da magana da Kora. “Ku Lawiyawa ku kasa kunne!

9 Kuna ganin wannan ƙaramar magana ce, wato cewa Allah na Isra’ila ya keɓe ku daga cikin jama’ar Isra’ila domin ya kawo ku kusa da shi, ku yi aiki a alfarwar sujada ta Ubangiji, ku kuma tsaya a gaban jama’a don ku yi musu aiki?

10 Ya yarda ka zo kusa da shi, kai da dukan ‘yan’uwanka Lawiyawa, a yanzu kuwa sai ƙoƙari kuke ku karɓi aikin firist!

11 Kai da ƙungiyarka kun haɗa kai kuna yi wa Haruna gunaguni, amma wane ne Haruna? A zahiri tawaye ne kuke wa Ubangiji!”

12 Musa kuwa ya aika a kirawo Datan da Abiram, ‘ya’yan Eliyab, amma suka ce, “Ba za mu zo ba!

13 Kana jin ƙaramin abu ne da ka fitar da mu daga cikin ƙasar mai yalwar abinci, don ka kashe mu a jeji? So kake kuma ka mai da kanka sarki a bisanmu?

14 Banda wannan kuma, ga shi, ba ka kai mu zuwa cikin ƙasa mai yalwar abinci ba, ba ka ba mu gonaki da gonakin inabi domin mu gāda ba, yanzu kuwa kana so ka ruɗe mu, to, ba za mu zo ba sam!”

15 Musa kuwa ya husata ƙawarai da gaske, ya ce wa Ubangiji, “Kada ka karɓi hadayarsu. Ban ƙwace ko jakinsu ba, ban kuwa cuce su ba.”

16 Musa ya ce wa Kora, “Kai da ƙungiyarka duka ku hallara a gaban Ubangiji gobe, da kai, da su, da Haruna.

17 Sa’an nan kowane ɗayanku ya ɗauki farantinsa na ƙona turare, ya zuba turaren wuta a ciki, ya kawo a gaban Ubangiji, wato farantan ƙona turare guda ɗari biyu da hamsin ke nan. Kai kuma da Haruna kowannenku ya kawo nasa faranti.”

18 Sai kowannensu ya ɗauki farantinsa, ya zuba wuta a ciki, sa’an nan ya zuba turaren wuta, suka tsaitsaya a bakin ƙofar alfarwa ta sujada tare da Musa da Haruna.

19 Sai Kora ya tara dukan taron jama’a a bakin alfarwa ta sujada, ya zuga su su tayar wa Musa, da Haruna. Sai ɗaukakar Ubangiji ta bayyana ga dukan taron jama’ar.

20 Ubangiji kuwa ya ce wa Musa da Haruna,

21 “Ku ware kanku daga cikin taron jama’ar nan, ni kuwa in hallaka su nan take.”

22 Sai Musa da Haruna suka fāɗi rubda ciki, suka ce, “Ya Allah, Allahn ruhohin ‘yan adam duka, za ka yi fushi da dukan taron jama’a saboda zunubin mutum ɗaya?”

23 Sai Ubangiji ya ce wa Musa,

24 “Ka faɗa wa jama’a su tashi, su nisanci alfarwar Kora, da ta Datan, da ta Abiram.”

25 Musa kuwa ya tashi ya tafi wurin Datan, da Abiram Dattawan Isra’ilawa suka bi Musa.

26 Sai ya ce wa jama’ar, “Ina roƙonku, ku ƙaurace wa alfarwan waɗannan mugayen mutane, kada ku taɓa kowane abu da yake nasu, domin kada a shafe ku saboda zunubansu.”

27 Sai jama’a suka tashi daga inda Kora, da Datan, da Abiram suke zama.

Datan da Abiram kuwa suka fito suka tsaya a ƙofar alfarwansu tare da matansu da ‘ya’yansu, da ‘yan ƙananansu.

28 Sai Musa ya ce, “Da haka za ku sani Ubangiji ne ya aiko ni, in yi waɗannan ayyuka, ba da nufin kaina na yi su ba.

29 Idan mutanen nan sun mutu kamar yadda mutane suke mutuwa, idan abin da yakan sami kowa shi ne ya same su, to, ba Ubangiji ne ya aiko ni ba.

30 Amma idan Ubangiji ya aikata wani abu sabo, ya sa ƙasa ta buɗe bakinta, ta haɗiye su da dukan abin da suke da shi, suka gangara zuwa cikin lahira a raye, sa’an nan za ku sani mutanen nan sun raina Ubangiji.”

31 Musa ya rufe bakinsa ke nan, sai wurin da Datan da Abiram suke tsaye, ƙasar ta dāre

32 ta haɗiye su tare da iyalansu, da dukan mutanen Kora, da dukan mallakarsu.

33 Haka fa, su da dukan abin da yake nasu suka gangara zuwa lahira da rai.

34 Sai Isra’ilawa duka waɗanda suke kewaye da su suka gudu saboda kururuwansu, suka ce. “Mu mā gudu,kada kuma ƙasa ta haɗiye mu.”

35 Wuta kuma ta fito daga wurin Ubangiji ta cinye mutum ɗari biyu da hamsin ɗin nan da suke miƙa hadaya da turare.

36 Ubangiji ya ce wa Musa,

37 “Ka faɗa wa Ele’azara, ɗan Haruna firist, ya kawar da farantan ƙona turare daga wurin da wutar ta cinye, ka watsar da gawayin daga farantan a wani wuri gama farantan tsarkakakku ne.

38 Waɗannan farantan ƙona turaren sun zama tsarkakakku sa’ad da aka miƙa su a bagaden Ubangiji. Sai ka ɗauki farantan mutanen da suka yi zunubin da ya jawo, musu mutuwa, ka ƙera murfin bagade da su, gama an miƙa su a gaban Ubangiji, ta haka za su zama gargaɗi ga jama’ar Isra’ila.”

39 Sai Ele’azara, firist, ya ɗauki farantan tagullar waɗanda mutanen da aka hallaka suka kawo. Aka ƙera murfin bagade da su.

40 Zai zama abin tunawa ga Isra’ilawa domin kada wanda ba firist ba, ba kuwa a cikin zuriyar Haruna ba, ya guso don ya ƙona turare a gaban Ubangiji, domin kada ya zama kamar Kora da ƙungiyarsa. Haka Ubangiji ya faɗa wa Ele’azara ta bakin Musa.

Haruna ya Ceci Jama’a

41 Kashegari dukan taron Isra’ilawa suka yi gunaguni a kan Musa da Haruna, suna cewa, “Ku ne sanadin mutuwar jama’ar Ubangiji.”

42 Da taron jama’ar suka haɗa kai gāba da Musa da Haruna, sai suka fuskanci alfarwa ta sujada. Ga girgije yana rufe da alfarwar, ɗaukakar Ubangiji kuwa ta bayyana.

43 Sai Musa da Haruna suka tafi wajen ƙofar alfarwa ta sujada.

44 Ubangiji kuwa ya yi magana da Musa, ya ce,

45 “Ku nisanci wannan taro, gama yanzun nan zan hallaka su.”

Sai suka fāɗi rubda ciki.

46 Sa’an nan Musa ya ce wa Haruna, “Ɗauki farantin turare, ka cika shi da wuta daga bagade, ka zuba turaren wuta a ciki, ka tafi da sauri wurin taron, ka yi kafara dominsu, gama fushin Ubangiji ya riga ya sauko, an fara annoba.”

47 Sai Haruna ya ɗauko farantin turaren, ya yi yadda Musa ya ce. Ya sheƙa a guje a tsakiyar taron jama’a. Amma an riga an fara annobar a cikin jama’a. Sai ya zuba turare, ya yi kafara domin jama’a.

48 Ya kuwa tsaya a tsakanin matattu da masu rai, annobar kuwa ta tsaya.

49 Waɗanda annoba ta kashe mutum dubu goma sha huɗu ne da ɗari bakwai (14,700), banda waɗanda suka mutu a sanadin Kora.

50 Sai Haruna ya koma wurin Musa a ƙofar alfarwa ta sujada, gama annobar ta ƙare.

Categories
L. KID

L. KID 17

Sandan Haruna

1 Ubangiji ya yi magana da Musa ya ce,

2 “Ka faɗa wa Isra’ilawa su ba ka sanduna, sanda guda daga kowane shugaban gidan kakanninsu, sanduna goma sha biyu ke nan. Ka rubuta sunan kowane mutum a sandansa.

3 Ka rubuta sunan Haruna a kan sandan Lawi, gama akwai sanda guda domin kowane gidan kakanninsu.

4 Sai ka ajiye su a alfarwa ta sujada a gaban akwatin alkawari, inda nakan sadu da kai.

5 Mutumin da sandansa ya yi toho, shi ne na zaɓa, da haka zan sa gunagunin da Isra’ilawa suke yi a kaina ya ƙare.”

6 Musa kuwa ya yi magana da Isra’ilawa. Sai dukan shugabanninsu suka ba shi sanda ɗaya ɗaya, sanda ɗaya daga kowane shugaba bisa ga gidajen kakanninsu, sanduna goma sha biyu ke nan. Sandan Haruna yana cikin sandunan.

7 Sai Musa ya ajiye sandunan a gaban Ubangiji cikin alfarwa ta sujada.

8 Kashegari Musa ya shiga alfarwar, sai ga shi, sandan Haruna na gidan Lawiyawa ya huda, ya yi toho, ya yi furanni, ya kuma yi ‘ya’yan almon nunannu, wato wani irin itace ne mai kama da na yazawa.

9 Musa kuwa ya fito wa Isra’ilawa da dukan sandunan da aka ajiye a gaban Ubangiji. Suka duba, kowanne ya ɗauki sandansa.

10 Ubangiji ya ce wa Musa, “Mayar da sandan Haruna a akwatin alkawari, alama ce ga masu tawaye ta cewa za su mutu idan ba su daina gunaguninsu ba.”

11 Haka kuwa Musa ya yi yadda Ubangiji ya umarce shi.

12 Isra’ilawa suka ce wa Musa, “Ba shakka, mun hallaka. Mun lalace, dukanmu mun lalace.

13 Duk wanda ya kusaci alfarwa ta sujada ta Ubangiji, zai mutu. Ashe, dukanmu za mu mutu ke nan!”

Categories
L. KID

L. KID 18

Ayyukan Lawiyawa da Firistoci

1 Sai Ubangiji ya ce wa Haruna, “Kai da ‘ya’yanka, da gidan mahaifinka za ku ɗauki hakkin abin da ya shafi alfarwa ta sujada. Kai da ‘ya’yanka kuma za ku ɗauki hakkin aikinku wanda ya shafi firistoci.

2 Ka kawo ‘yan’uwanka tare da kai, wato kabilar Lawi, kakanka, don su yi muku aiki sa’ad da kai da ‘ya’yanka kuke gaban alfarwa ta sujada.

3 Za su taimake ku, su kuma yi dukan ayyukan alfarwa. Amma fa, ba za su kusaci kayayyakin Wuri Mai Tsarki, ko bagade ba, don kada su, har da ku, ku mutu.

4 Za su haɗa kai da ku su lura da alfarwa ta sujada da dukan aikace-aikace na cikin alfarwar. Kada wani dabam ya kusace ku.

5 Ku lura da ayyukan Wuri Mai Tsarki da na bagade don kada hasala ta sāke fāɗa wa Isra’ilawa.

6 Ga shi, ni na ɗauki ‘yan’uwanku, Lawiyawa, daga cikin mutanen Isra’ila. Kyauta suke a gare ku, waɗanda aka bayar ga Ubangiji don su lura da alfarwa ta sujada.

7 Da kai, da ‘ya’yanka za ku yi aikin firist da duk abin da ya shafi bagade da aiki na bayan labule. Ku ne za ku yi wannan aiki. Na ba ku aikin firist ya zama naku. Duk wani dabam wanda ya zo kuwa, za a kashe shi.”

Rabon Firistoci

8 Ubangiji ya kuma ce wa Haruna, “Na ba ka aikin lura da hadayuna na ɗagawa, wato sadakokin Isra’ilawa, na ba ka su su zama rabonka da na ‘ya’yanka har abada.

9 Abin da ya ragu daga cikin hadaya mafi tsarki da ake miƙa mini zai zama rabonka da na ‘ya’yanka, wato daga kowace hadaya, da hadaya ta gari, da hadaya don zunubi, da hadaya don laifi.

10 A wuri mai tsarki za ku ci shi, kowane namiji ya iya ci. Abu mai tsarki ne a gare ka.

11 “Har yanzu kuma duk sadakokin da Isra’ilawa suke bayarwa don hadaya ta ɗagawa da ta kaɗawa, na ba ka, kai da ‘ya’yanka mata da maza, a kowane lokaci. Duk wanda yake da tsarki a gidanka zai iya ci.

12 “Duk mai mafi kyau, da ruwan inabi mafi kyau duka, da hatsi mafi kyau duka na nunan fari, waɗanda suke bayarwa ga Ubangiji, na ba ku.

13 Nunan fari na dukan amfanin gonarsu wanda suke kawowa ga Ubangiji, zai zama naka. Duk wanda yake da tsarki a gidanka zai iya cinsa.

14 “Iyakar abin da aka keɓe wa Ubangiji a Isra’ila zai zama naka.

15 “Dukan haihuwar fari, ko ta mutum ko ta dabba da sukan bayar ga Ubangiji zai zama naka. Amma ka fanshi kowace haihuwar fari ta mutum, ko ta dabbar da take haram.

16 Sai ka fanshe su suna ‘yan wata ɗaya a bakin shekel biyar biyar, bisa ga ma’aunin kuɗin da ake aiki da shi.

17 Haihuwar fari ta saniya, ko ta tunkiya, ko ta akuya, ba za ka fanshe su ba, gama su halal ne. Sai kayayyafa jininsu a kan bagade, kitsensu kuma ka ƙone a kan bagaden ƙona hadayu, zai zama turare mai ƙanshi, mai daɗi ga Ubangiji.

18 Naman kuwa zai zama naka, duk da ƙirji na kaɗawa da cinyar dama da aka miƙa su hadaya ta kaɗawa.

19 “Duk hadayu na ɗagawa na tsarkakakkun abubuwan da Isra’ilawa suka miƙa wa Ubangiji, na ba ka, da kai da ‘ya’yanka mata da maza a kowane lokaci. Wannan alkawarin gishiri ne na Ubangiji dominka da zuriyarka.”

20 Ubangiji kuma ya ce wa Haruna, “Ba za ka gāji kome a ƙasar Isra’ilawa ba, ba ka da wani rabo a cikinta. Ni ne rabonka da gādonka a cikin Isra’ilawa.”

Rabon Lawiyawa

21 Ubangiji ya ce, “Na ba Lawiyawa kowace zaka ta Isra’ilawa gādo saboda aikinsu da suke ya a alfarwa ta sujada.

22 Nan gaba kada Isra’ilawa su zo kusa da alfarwa ta sujada don kada su yi zunubi, su mutu.

23 Gama Lawiyawa ne kaɗai za su yi aikin alfarwa ta sujada, wannan alhakinsu ne. Wajibi ne kuma ga zuriyarsu a kowane lokaci. Lawiyawa ba su da gādo tare da Isra’ilawa.

24 Gama ni Ubangiji na ba su zaka da Isra’ilawa suke kawo mini ta hadaya ta ɗagawa ta zama gādonsu. Saboda haka ne, na ce ba su da gādo tare da Isra’ilawa.”

Zaka

25 Ubangiji ya ce wa Musa,

26 “Har yanzu ka faɗa wa Lawiyawa, cewa sa’ad da suka karɓi zaka daga Isra’ilawa wadda na ba su gādo, sai su fitar da zaka daga cikin zakar, su miƙa wa Ubangiji hadaya ta ɗagawa.

27 Za a lasafta hadayarku ta ɗagawa kamar hatsinku ne da kuka sussuka a masussuka, da kuma kamar cikakken amfanin ruwan inabin da kuka samu a wurin matsewar inabinku.

28 Haka za ku miƙa hadaya ta ɗagawa ga Ubangiji daga cikin dukan zakar da kuke karɓa daga wurin Isra’ilawa. Daga ciki za ku ba da hadaya ta ɗagawa ga Ubangiji ta hannun Haruna, firist.

29 Daga dukan kyautar da ake kawo muku, za ku ba Ubangiji hadaya ta ɗagawa daga mafi kyau da kuke samu.

30 Domin haka kuwa sai ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka ɗaga mafi kyau daga cikinta duka, sai ragowar ta zama ta Lawiyawa kamar abin da ya fito daga masussuka, da wurin matsewar inabinsu.

31 Za ku iya cinta ko’ina da kuka ga dama, ku da iyalan gidajenku, gama ladanku ke nan saboda aikin da kuke yi a alfarwa ta sujada.

32 Ba kuwa za ta zama muku sanadin zunubi ba, in dai har kuka ɗaga mafi kyau duka. Ba za ku ɓata tsarkakakkun abubuwa na Isra’ilawa ba, don kada ku mutu.’ ”

Categories
L. KID

L. KID 19

Tsarkakewar Marasa Tsarki

1 Ubangiji ya yi magana da Musa da Haruna, ya ce,

2 “Wannan ita ce ka’ida wadda Ubangiji ya umarta. Ka faɗa wa Isra’ilawa su kawo maka jar karsana, marar lahani, wadda ba ta da wani aibi, wadda ba a taɓa aza mata karkiya ba.

3 Sai ka ba Ele’azara firist ita, sa’an nan a kai ta bayan sansani, a yanka ta gabansa.

4 Ele’azara, firist, kuwa zai ɗibi jininta da yatsansa, ya yayyafa sau bakwai a wajen alfarwar ta sujada.

5 Sai a ƙone karsanar a idonsa, za a ƙone fatarta, da naman, da jinin, tare da tarosonta.

6 Firist zai ɗauki itacen al’ul, da ɗaɗɗoya, da mulufi, ya jefa a wutar da take ƙone karsanar.

7 Sai firist ɗin ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, sa’an nan ya shiga zangon. Firist ɗin zai ƙazantu har zuwa maraice.

8 Shi kuma wanda ya ƙone karsanar, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, shi ma zai ƙazantu har zuwa maraice.

9 Mutumin da yake da tsarki shi zai tara tokar karsanar, ya ajiye a wuri mai tsabta a bayan zangon. Za a adana tokar domin jama’ar Isra’ila, za a riƙa zubawa a ruwa don tsarkakewar zunubi.

10 Shi kuma wanda ya tara tokar karsanar, sai ya wanke tufafinsa zai ƙazantu har maraice. Wannan ka’ida ce ta har abada ga Isra’ilawa da baƙin da yake zama tare da su.”

Taɓa Gawa

11 “Duk wanda ya taɓa gawa zai ƙazantu har kwana bakwai.

12 A rana ta uku da ta bakwai zai tsarkake kansa da ruwa, zai kuwa tsarkaka, amma in a rana ta uku da ta bakwai bai tsarkake kansa ba, to, ba zai tsarkaka ba.

13 Duk wanda ya taɓa gawa, bai kuwa tsarkake kansa ba, ya ƙazantar da alfarwa ta sujada ta Ubangiji, ba za a lasafta shi cikin mutanen Allah ba, domin ba a yayyafa masa ruwan tsarkakewa ba.

14 “Wannan ita ce ka’ida a kan wanda ya rasu a alfarwa, duk wanda ya shiga alfarwar, da duk wanda yake cikin alfarwar zai ƙazantu har kwana bakwai.

15 Kowace buɗaɗɗiyarsa kuma wadda ba a rufe ba, za ta ƙazantu.

16 Wanda duk yake cikin saura ya taɓa wanda aka kashe da tokobi, ko gawa, ko ƙashin mutum, ko kabari zai ƙazantu har kwana bakwai.

17 “Don a tsarkake ƙazantar, sai a ɗiba daga cikin tokar hadaya don zunubi a cikinsa, sa’an nan a zuba ruwa mai gudu.

18 Tsarkakakken mutum zai ɗauki ɗaɗɗoya ya tsoma a ruwan, ya yayyafa wa alfarwar, da bisa kan dukan kayayyakin da suke ciki, da a kan mutanen da suke a wurin, da kan wanda ya taɓa ƙashin, ko ya taɓa wanda aka kashe, ko ya taɓa gawa, ko kabari.

19 A kan rana ta uku da ta bakwai kuma, wanda yake da tsarki zai yayyafa wa marar tsarkin ruwa, ya tsarkake shi. Sai mutumin ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, da maraice kuwa zai tsarkaka.

20 “Amma mutumin da ba shi da tsarki, bai kuwa tsarkake kansa ba, ba za a lasafta shi cikin jama’ar Allah ba, tun da yake ya ƙazantar da alfarwa ta sujada ta Ubangiji, gama ba a yayyafa masa ruwan da akan yayyafa wa marasa tsarki ba.

21 Wannan zai zama musu ka’ida har abada. Wanda ya yayyafa ruwan tsarkakewa, sai ya wanke tufafinsa, wanda kuma ya taɓa ruwan tsarkakewa zai zama marar tsarki har maraice.

22 Duk abin da mutumin da ba shi da tsarki ya taɓa zai ƙazantu, duk wanda kuma ya taɓa abin da marar tsarkin ya taɓa zai ƙazantu har maraice.”

Categories
L. KID

L. KID 20

Ruwa daga cikin Dutse

1 Sai dukan taron jama’ar Isra’ilawa suka zo jejin Zin a watan fari, suka sauka a Kadesh. A nan ne Maryamu ta rasu, a nan kuma aka binne ta.

2 Da jama’a suka rasa ruwa, sai suka taru suka tayar wa Musa da Haruna.

3 Suka ce wa Musa, “Da ma mun mutu kamar yadda ‘yan’uwanmu suka mutu a gaban Ubangiji.

4 Don me ka fito da taron jama’ar Ubangiji zuwa cikin wannan jeji don mu mutu a nan, mu da dabbobinmu?

5 Don me kuma ka sa muka fito daga masar, ka kawo mu a wannan mugun wuri inda babu hatsi, ko ɓaure, ko inabi, ko rumman, ko ruwan da za a sha ma?”

6 Sai Musa da Haruna suka bar taron jama’a, suka tafi ƙofar alfarwa ta sujada, suka fāɗi rubda ciki. Ɗaukakar Ubangiji kuwa ta bayyana a gare su.

7 Ubangiji ya ce wa Musa,

8 “Ka ɗauki sandanka, kai da Haruna, ɗan’uwanka, ku tara jama’a, ku yi magana da dutsen a gabansu ya ba da ruwan da yake cikinsa. Za ka sa ruwa ya ɓuɓɓugo musu daga dutsen. Ta haka za ka ba taron jama’a da garkunansu ruwan sha.”

9 Musa kuwa ya ɗauki sanda daga gaban Ubangiji kamar yadda ya umarce shi.

10 Sai Musa da Haruna suka sa jama’a su taru a gaban dutsen, sa’an nan Musa ya ce musu, “Ku kasa kunne, ku ‘yan tawaye, za mu fito muku da ruwa daga cikin dutsen nan?”

11 Musa kuwa ya ɗaga hannu, ya bugi dutsen sau biyu da sandansa, sai ruwa mai yawa ya yi ta kwararowa. Taron jama’a tare da garkunansu suka sha.

12 Ubangiji kuwa ya ce wa Musa da Haruna, “Tun da yake ba ku gaskata ni ba, ba ku kuwa ɗaukaka ni a idon Isra’ilawa ba, to, ba za ku kai taron jama’ar nan a ƙasar da na ba su ba.”

13 Wannan ya faru ne a Meriba inda mutanen Isra’ila suka yi wa Ubangiji gunaguni, inda shi kuma ya nuna musu shi mai tsarki ne.

Sarkin Edom ya Hana Isra’ilawa Wucewa

14 Sai Musa ya aika manzanni daga Kadesh zuwa wurin Sarkin Edom, su ce masa, “In ji ɗan’uwanka, Isra’ila, ka dai san dukan wahalar da ta same mu,

15 yadda kakanninmu suka gangara zuwa Masar, suka zauna a can da daɗewa, da yadda Masarawa suka wahalshe mu, mu da kakanninmu.

16 Sa’ad da muka yi kuka ga Ubangiji, Ubangiji kuwa ya ji kukanmu, ya aiko mala’ikansa, ya fisshe mu daga Masar. Ga mu nan a Kadesh, garin da yake kan iyakar ƙasarka.

17 Ka yarda mana mu ratsa ƙasarka, ba za mu bi ta cikin gona, ko gonar inabi ba, ba kuwa za mu sha ruwan rijiyarka ba. Mu dai za mu bi gwadaben sarki, ba za mu kauce dama ko hagu ba, har mu wuce ƙasarka.”

18 Amma Edomawa suka ce masa, “Ba za ku ratsa ta ƙasarmu ba! Idan kuwa kun ce za ku gwada, za mu fita mu ci ku da yaƙi.”

19 Amma mutanen Isra’ila suka amsa musu suka ce, “Ai, za mu bi gwadabe ne kawai, idan kuwa mu da dabbobinmu mun sha ruwanku, sai mu biya, mu dai, a yardar mana mu wuce kawai.”

20 Amma Edomawa suka sāke cewa, “Ba mu yarda ba.” Sai suka fito da runduna mai yawa su yi yaƙi da su.

21 Da haka Edomawa suka hana Isra’ilawa ratsa ƙasarsu. Sai Isra’ilawa suka kauce musu.

Haruna ya Rasu

22-23 Sai taron jama’ar Isra’ila suka kama tafiya daga Kadesh, suka je Dutsen Hor, a kan iyakar ƙasar Edom. Ubangiji kuwa ya ce wa Musa da Haruna a can,

24 “Haruna ba zai shiga ƙasar da na alkawarta zan ba Isra’ila ba, zai mutu, gama ku biyun nan kuka tayar wa umarnina a Meriba.

25 Ka kawo Haruna da ɗansa, Ele’azara, bisa Dutsen Hor.

26 Ka tuɓe wa Haruna rigunansa na firist, ka sa wa ɗansa, Ele’azara. Haruna zai mutu can.”

27 Musa kuwa ya yi yadda Ubangiji ya umarta. Suka hau bisa Dutsen Hor a idon dukan taron jama’a.

28 Sai Musa ya tuɓe wa Haruna rigunansa na firist ya sa wa Ele’azara ɗan Haruna. Haruna kuwa ya rasu a kan dutsen. Sa’an nan Musa da Ele’azara suka sauko daga kan dutsen.

29 Sa’ad da dukan jama’a suka ga Haruna ya rasu, sai duka suka yi makoki dominsa har kwana talatin.