Categories
L. KID

L. KID 21

An ci Kan’aniyawa da Yaƙi

1 Da Sarkin Arad, Bakan’ane, wanda yake zaune a Negeb, ya ji Isra’ilawa suna zuwa ta hanyar Atarim, sai ya fita ya yi yaƙi da Isra’ilawa, ya kama waɗansu daga cikinsu.

2 Sai Isra’ilawa suka yi wa’adi ga Ubangiji, suka ce, “In hakika, za ka ba da mutanen nan a hannunmu, lalle za mu hallaka biranensu ƙaƙaf.”

3 Ubangiji kuwa ya ji wa’adin Isra’ilawa, ya kuwa ba su Kan’aniyawa, suka hallaka su da biranensu ƙaƙaf. Don haka aka sa wa wurin suna Horma, wato hallakarwa.

Macijin da aka Yi da Tagulla

4 Isra’ilawa suka kama hanya daga Dutsen Hor zuwa Bahar Maliya don su kauce wa ƙasar Edom. Sai jama’a suka ƙosa da hanyar.

5 Suka yi wa Allah gunaguni, da Musa kuma, suka ce, “Me ya sa kuka fitar da mu daga Masar, kuka kawo mu cikin jeji mu mutu? Gama ba abinci, ba ruwa, mu kuwa mun gundura da wannan abinci marar amfani.”

6 Sai Ubangiji ya aiko macizai masu zafin dafi a cikin jama’a, suka sassari Isra’ilawa, da yawa kuwa suka mutu.

7 Jama’a kuwa suka zo wurin Musa, suka ce, “Mun yi zunubi gama mun yi wa Ubangiji gunaguni, mun kuma yi maka. Ka roƙi Ubangiji ya kawar mana da macizan.” Musa kuwa ya yi roƙo domin jama’ar.

8 Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ƙera maciji da tagulla, ka sarƙafa shi a bisa dirka, duk wanda maciji ya sare shi, idan ya dubi maciji na tagullar, zai rayu.”

9 Musa kuwa ya yi maciji na tagulla, ya sarƙafa shi a bisa dirka, idan kuwa maciji ya sari mutum, in ya dubi macijin tagullar, zai warke.

Tafiya zuwa Kwarin Mowabawa

10 Sai mutanen Isra’ila suka kama hanya, suka yi zango a Obot.

11 Suka kama hanya daga Obot, suka yi zango a kufafen Abarim a cikin jeji daura da Mowab wajen gabas.

12 Daga can suka tashi suka sauka a Kwarin Zered.

13 Daga can kuma suka tashi suka sauka hayin Kogin Arnon, wanda yake cikin jeji wanda ya nausa zuwa iyakar Amoriyawa. Gama Arnon shi ne kan iyakar Mowabawa da Amoriyawa.

14 Saboda haka aka faɗa a Littafin Yaƙoƙi na Ubangiji cewa, “Waheb ta cikin yankin Sufa, da kwaruruka na Kogin Arnon,

15 da gangaren kwaruruka, wanda ya nausa zuwa garin Ar, ya kuma dangana da kan iyakar Mowab.”

16 Daga can suka ci gaba da tafiya zuwa Biyer, wato rijiya wadda Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka tattara mutane wuri ɗaya, zan kuwa ba su ruwa.”

17 Sai Isra’ilawa suka raira waƙa, suka ce,

“Rijiya, ki ɓuɓɓugo da ruwa

Mu kuwa za mu raira waƙa mu gaishe ta!

18 Rijiyar da hakimai suka haƙa,

Shugabannin jama’a suka haƙa,

Da sandan sarauta,

Da kuma sandunansu.”

Daga cikin jejin suka tafi har zuwa Mattana.

19 Daga Mattana suka tafi Nahaliyel suka tafi Bamot.

20 Daga Bamot kuma suka tafi kwarin da yake a ƙasar Mowab wajen ƙwanƙolin Dutsen Fisga wanda yake fuskantar hamada.

Mutanen Isra’ila sun Ci Sihon

21 Mutanen suka aiki manzanni zuwa wurin Sihon, Sarkin Amoriyawa, suka ce masa,

22 “Ka yarda mana mu ratsa ta ƙasarka, ba za mu ratsa ta cikin gonaki, ko cikin gonakin inabi ba, ba kuwa za mu sha ruwan rijiyarka ba, gwadaben sarki za mu bi sosai, har mu fita daga karkararka.”

23 Amma Sihon bai yarda wa Isra’ilawa su ratsa ta karkararsa ba. Sai ya tattara mazajensa, suka fita don su yi yaƙi da Isra’ilawa a jejin. Suka tafi Yahaza suka yi yaƙi da Isra’ilawa.

24 Isra’ilawa kuwa suka karkashe su da takobi, suka mallaki ƙasarsa tun daga Kogin Arnon zuwa Kogin Yabbok, har zuwa kan iyakar Ammonawa, gama Yahaza ita ce kan iyakar Ammonawa.

25 Isra’ilawa kuwa suka ci dukan waɗannan birane, suka zauna a biranen Amoriyawa, wato a Heshbon da ƙauyukanta duka.

26 Gama Heshbon ita ce birnin Sihon,Sarkin Amoriyawa, wanda ya yi yaƙi da Sarkin Mowab na dā. Ya ƙwace ƙasarsa duka daga hannunsa har zuwa Kogin Arnon.

27 Domin haka mawaƙa sukan ce,

“Ku zo Heshbon, bārin sarki Sihon!

Muna so mu ga an sāke gina an kuma fanso shi.

28 Gama sojojin Sihon sun shiga kamar wuta,

A wannan birni na Heshbon,

Sun cinye Ar ta Mowab,

Ta murƙushe tuddan Arnon.

29 Kaitonku, ku mutanen Mowab!

Ku masu sujada ga Kemosh kun lalace!

Gumakanku sun sa mutane su zama ‘yan gudun hijira,

Mata kuwa, Sihon, Sarkin Amoriyawa ya kama su.

30 Amma yanzu an hallaka zuriyarsu,

Tun daga Heshbon har zuwa Dibon,

Har da Nofa kusa da Medeba.”

Isra’ilawa sun Ci Og

31 Haka fa Isra’ilawa suka zauna a ƙasar Amoriyawa.

32 Sai Musa ya aika a leƙo asirin ƙasar Yazar. Suka tafi suka ci ƙauyukanta, suka kori Amoriyawan da suke can.

33 Suka juya suka haura ta hanyar Bashan. Sai Og, Sarkin Bashan, da dukan jama’arsa suka fita, suka yi yaƙi da su a Edirai.

34 Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Kada ka ji tsoronsa, gama na bashe shi a hannunka duk da jama’arsa, da ƙasarsa. Za ka yi masa yadda ka yi wa Sihon, Sarkin Amoriyawa wanda ya zauna a Heshbon.”

35 Haka fa suka kashe shi, shi da ‘ya’yansa maza, da dukan jama’arsa, har ba wanda ya tsira, suka kuwa mallaki ƙasarsa.

Categories
L. KID

L. KID 22

Balak ya Sa a Kirawo masa Bal’amu

1 Isra’ilawa suka kama tafiya, suka yi zango a filayen Mowab a hayin Urdun daura da Yariko.

2 Balak ɗan Ziffor ya ga abin da Isra’ilawa suka yi wa Amoriyawa.

3 Sai Mowabawa suka firgita ƙwarai saboda yawan mutanen. Tsoron Isra’ilawa ya kama su.

4 Mowabawa kuwa suka ce wa dattawan Madayanawa, “Yanzun nan wannan taro zai lashe dukan abin da yake kewaye da mu kamar yadda sā yakan lashe ciyawar saura.” Don haka Balak ɗan Ziffor wanda yake sarautar Mowab a lokacin,

5 ya aiki manzanni zuwa wurin Bal’amu ɗan Beyor a Fetor, a ƙasar danginsa, wadda take kusa da kogin, su kirawo shi, su ce, “Ga mutane sun fito daga ƙasar Masar, sun mamaye ƙasar, ga shi, suna zaune daura da ni.

6 Ina roƙonka, ka zo yanzu, ka la’anta mini mutanen nan, gama sun fi ƙarfina, ko ya yiwu in ci su, in kore su daga ƙasar, gama na sani duk wanda ka sa wa albarka zai albarkatu,wanda kuwa ka la’anta, zai la’antu.”

7 Dattawan Mowab da na Madayana suka ɗauki kafin alkalami suka tafi wurin Bal’amu suka faɗa masa saƙon Balak.

8 Ya ce musu, “Ku kwana a nan, ni kuwa zan shaida muku abin da Ubangiji zai faɗa mini.” Sai dattawan Mowab suka zauna wurin Bal’amu.

9 Allah kuwa ya zo wurin Bal’amu ya ce masa, “Suwane ne mutanen da suke tare da kai?”

10 Sai Bal’amu ya ce wa Allah, “Ai, Balak ne ɗan Ziffor, Sarkin Mowab, ya aiko ya ce mini,

11 ‘Ga jama’a sun fito daga Masar, sun mamaye ƙasar, ka zo, ka la’anta mini su, watakila zan iya yin yaƙi da su, in kore su!’ ”

12 Allah kuwa ya ce wa Bal’amu, “Ba za ka tafi tare da su ba, ba kuwa za ka la’anta su ba, gama albarkatattu ne su.”

13 Da safe Bal’amu ya tashi, ya ce wa dattawan Balak, “Ku koma ƙasarku, gama Ubangiji bai yarda mini in tafi tare da ku ba.”

14 Domin haka dattawan Mowab suka tashi, suka koma wurin Balak, suka ce masa, “Bal’amu bai yarda ya biyo mu ba.”

15 Sai Balak ya sāke aiken dattawa da yawa masu daraja fiye da na dā.

16 Suka je wurin Bal’amu, suka ce masa, “Ga abin da Balak ɗan Ziffor ya ce, ‘Kada ka bar wani abu ya hana ka zuwa wurina,

17 gama zan ɗaukaka ka ƙwarai, kome kuwa ka faɗa mini in yi, zan yi, ka zo ka la’anta mini wannan jama’a.’ ”

18 Amma Bal’amu ya amsa ya ce wa barorin Balak, “Ko da a ce Balak zai ba ni gidansa cike da azurfa da zinariya, ba zan yi wani abu ko kaɗan saɓanin umarnin Ubangiji Allahna ba.

19 Amma ina roƙonku ku kwana a nan yau har in san abin da Ubangiji zai faɗa mini.”

20 Sal Allah ya je wurin Bal’amu da dare, ya ce masa, “Idan mutanen nan sun zo kiranka ne, sai ka tashi, ka tafi tare da su, amma abin da na umarce ka kaɗai za ka yi.”

Mala’ika da Jakar Bal’amu

21 Da safe sai Bal’amu ya tashi ya yi wa jakarsa shimfiɗa, ya tafi tare da dattawan Mowab.

22 Allah kuwa ya husata don ya tafi, mala’ikan Ubangiji ya tsaya a hanya ya tarye shi. Shi kuwa yana tafe a bisa jakarsa tare da barorinsa biyu.

23 Da jakar ta ga mala’ikan Ubangiji yana tsaye kan hanya da takobi zare a hannunsa, sai ta kauce daga hanya, ta shiga saura. Bal’amu kuwa ya buge ta don ya komar da ita a hanyar.

24 Sai mala’ikan Ubangiji ya je, ya tsaya a inda hanyar ta yi matsatsi a tsakanin bangayen gonakin inabi.

25 Sa’ad da jakar ta ga mala’ikan Ubangiji, ta matsa a jikin bango, ta goge ƙafar Bal’amu ga bangon, sai ya sāke bugunta.

26 Mala’ikan Ubangiji kuma ya sha kanta, ya tsaya a ƙunƙuntaccen wuri inda ba wurin juyawa zuwa dama ko hagu.

27 Da jakar ta ga mala’ikan Ubangiji, sai ta kwanta a ƙafafun Bal’amu. Sai Bal’amu ya husata, ya bugi jakar da sandansa.

28 Ubangiji kuwa ya buɗe bakin jakar, ta ce wa Bal’amu, “Me na yi maka, da ka buge ni har sau uku?”

29 Bal’amu ya ce mata, “Domin kin shashantar da ni, da a ce ina da takobi a hannuna, da na kashe ki.”

30 Sai jakar ta ce wa Bal’amu, “Ba ni ce jakarka ba wadda kake ta hawa dukan lokacin nan har zuwa yau? Na taɓa yi maka haka?”

Ya ce, “A’a.”

31 Ubangiji kuwa ya buɗe idanun Bal’amu, ya ga mala’ikan Ubangiji yana tsaye a hanya da takobi zāre a hannunsa. Sai ya sunkuyar da kansa, ya fāɗi rubda ciki.

32 Mala’ikan Ubangiji kuwa ya ce masa, “Me ya sa ka bugi jakarka har sau uku? Na fito ne don inhana ka, gama hanyarka ba daidai ba ce a gabana.

33 Jakar ta gan ni, ta kauce mini har sau uku. Da ba ta kakuce mini ba, lalle da na kashe ka, in bar ta da rai.”

34 Sai Bal’amu ya ce wa mala’ikan Ubangiji, “Na yi zunubi, gama ban sa ka tsaya a hanya don ka tarye ni ba. Yanzu fa, idan ka ga mugun abu ne, to, sai in koma.”

35 Ubangiji kuwa ya ce wa Bal’amu, “Tafi tare da mutanen, amma abin da na faɗa maka shi kaɗai za ka faɗa.” Sai Bal’amu ya tafi tare da dattawan Balak.

Balak ya Marabci Bal’amu

36 Sa’ad da Balak ya ji Bal’amu ya zo, sai ya fito ya tarye shi a Ar, wato wani birni a bakin Kogin Arnon, a kan iyakar Mowab.

37 Sai Balak ya ce wa Bal’amu, “Ashe, ban aika a kirawo ka ba? Me ya sa ba ka zo wurina ba, sai yanzu? Ko ban isa in ɗaukaka ka ba ne?”

38 Bal’amu ya amsa wa Balak ya ce, “To, ai, ga shi, na zo yanzu! Ina da wani ikon yin wata magana ne? Maganar da Allah ya sa a bakina, ita zan faɗa, tilas.”

39 Sai Bal’amu ya tafi tare da Balak suka je Kiriyat-huzot.

40 Can Balak ya yi hadaya da shanu da tumaki, ya kuwa aika wa Bal’amu da dattawan da suke tare da shi.

41 Kashegari, sai Balak ya ɗauki Bal’amu ya kai shi kan Bamotba’al, daga can ya ga rubu’in mutanen.

Categories
L. KID

L. KID 23

1 Sai Bal’amu ya ce wa Balak, “Ka gina mini bagadai guda bakwai a nan, ka kawo mini bijimai bakwai da raguna bakwai.”

2 Balak ya yi yadda Bal’amu ya faɗa masa. Balak da Bal’amu suka miƙa bijimi da rago a kan kowane bagade.

3 Sai Bal’amu ya ce wa Balak, “Tsaya kusa da hadayarka ta ƙonawa, ni kuwa zan tafi can, in ga ko Ubangiji zai sadu da ni. Duk abin da ya bayyana mini, zan faɗa maka.” Ya kuwa tafi wani faƙo a kan tudu.

Bal’amu ya sa wa Isra’ila Albarka

4 Da Ubangiji ya sadu da Bal’amu, sai Bal’amu ya ce wa Ubangiji, “Na riga na shirya bagadai bakwai, na kuwa miƙa bijimi guda da rago guda a kan kowane bagade.”

5 Ubangiji kuwa ya sa magana a bakin Bal’amu ya ce, “Koma wurin Balak, ka faɗa masa abin da na faɗa maka.”

6 Sai ya koma wurin Balak, ya same shi da dukan dattawan Mowab suna tsaye kusa da hadayarsa ta ƙonawa.

7 Bal’amu kuwa ya faɗi jawabinsa, ya ce

“Tun daga Aram Balak ya kawo ni,

Shi Sarkin Mowab ne daga gabashin duwatsu.

‘Zo, la’anta mini Yakubu,

Zo, ka tsine wa Isra’ila!’

8 Ƙaƙa zan iya la’anta wanda Allah bai la’antar ba?

Ƙaƙa zan iya tsine wa wanda Ubangiji bai tsine wa ba?

9 Gama daga kan duwatsu na gan su,

Daga bisa kan tuddai na hange su,

Jama’a ce wadda take zaune ita kaɗai,

Sun sani sun sami albarka fiye da sauran al’ummai.

10 Wa zai iya ƙidaya yawan Isra’ilawa da suke kamar ƙura?

Yawansu ya fi gaban lasaftawa.

Bari ƙarshena ya zama kamar ɗaya daga cikin mutane Allah,

Bari in mutu cikin salama kamar adalai.”

11 Sai Balak ya ce wa Bal’amu, “Me ke nan ka yi mini? Na kawo ka domin ka la’anta abokan gābana, ga shi, sai albarka kake sa musu!”

12 Bal’amu kuwa ya ce, “Ai, ba tilas ne in hurta abin da Ubangiji ya sa a bakina ba?”

13 Sai Balak ya ce masa, “Zo, mu tafi wani wuri inda za ka gan su. Waɗanda suka fi kusa kaɗai ne za ka gani, amma ba za ka iya ganinsu duka ba. Ka la’anta mini su daga can.”

14 Ya kuwa kai shi saurar Zofim a bisa Dutsen Fisga. Sa’an nan ya gina bagadai bakwai, ya miƙa bijimi da rago a kan kowane bagade.

15 Sai Bal’amu ya ce wa Balak, “Tsaya nan kusa da hadayarka ta ƙonawa, ni kuwa in tafi in sadu da Ubangiji a can.”

16 Ubangiji kuwa ya sadu da Bal’amu ya sa masa magana a baka, ya ce, “Koma wurin Balak ka faɗa masa abin da na faɗa maka.”

17 Sai Bal’amu ya koma wurin Balak ya same shi yana tsaye kusa da hadayarsa ta ƙonawa tare da dattawan Mowab. Balak kuwa ya ce masa, “Me Ubangiji ya faɗa?”

18 Sai Bal’amu ya faɗi jawabinsa, ya ce,

“Tashi, Balak, ka ji,

Ka kasa kunne gare ni, ya ɗan Ziffor.

19 Allah ba kamar mutum ba ne, da zai yi ƙarya,

Ba kuwa ɗan mutum ba ne, da zai tuba.

Zai cika dukan abin da ya alkawarta,

Ya hurta, ya kuwa cika.

20 Ga shi, an umarce ni in sa albarka.

Ya sa albarka, ba zan iya janye ta ba.

21 Bai ga mugunta ga Yakubu ba,

Bai kuma ga wahala a Isra’ilawa ba.

Ubangiji Allahnsu yana tare da su,

Suna sowar murna domin shi sarkinsu ne.

22 Allah ne ya fisshe shi daga Masar,

Ya yi yaƙi dominsu kamar kutunkun ɓauna.

23 Ba wata maitar da za ta cuci Yakubu,

Ba kuwa sihirin da zai cuci Isra’ilawa.

Yanzu za a ce, ‘Duba irin abin da Allah ya yi domin Yakubu, wato Isra’ilawa!’

24 Ga shi, jama’ar Isra’ila tana kama da ƙaƙƙarfan zaki,

Ba zai kwanta ba sai ya cinye ganimarsa.

Ya lashe jinin waɗanda ya kashe.”

25 Sai Balak ya ce wa Bal’amu, “Kada ka la’anta su, kada kuma ka sa musu albarka.”

26 Bal’amu kuwa ya amsa wa Balak, ya ce, “Ban faɗa maka ba, duk abin da Ubangiji ya faɗa, shi ne zan yi?”

27 Sai Balak ya ce wa Bal’amu, “In ka yarda ka zo in kai ka wani wuri, watakila Allah zai yarda ka la’anta mini su a can.”

28 Balak kuwa ya kai Bal’amu a ƙwanƙolin Dutsen Feyor wanda yake fuskantar hamada.

29 Sai Bal’amu ya ce wa Balak, “Ka gina mini bagadai bakwai, ka shirya mini bijimai bakwai da raguna bakwai.”

30 Balak ya yi yadda Bal’amu ya faɗa masa. Ya miƙa bijimi da rago a kan kowane bagade.

Categories
L. KID

L. KID 24

1 Da Bal’amu ya gane Ubangiji yana jin daɗin sa wa Isra’ilawa albarka bai tafi neman shawara kamar dā ba, sai ya fuskanci jeji,

2 ya ta da idanunsa ya ga Isra’ilawa sun yi zango kabila kabila. Sai Ruhun Allah kuwa ya sauko masa.

3 Sai ya yi annabcinsa, ya ce.

“Faɗar Bal’amu ɗan Beyor,

Faɗar mutumin da idonsa take a buɗe.

4 Faɗar wanda yake jin faɗar Allah,

Shi wanda yake ganin wahayin Maɗaukaki,

Yana durƙushe, amma idanunsa a buɗe suke.

5 Alfarwan Isra’ilawa suna da kyan gani!

6 Kamar dogon jerin itatuwan dabino,

Kamar gonaki a gefen kogi,

Kamar itatuwan aloyes da Ubangiji ya dasa,

Kamar kuma itatuwan al’ul a gefen ruwaye.

7 Sojojin Isra’ilawa za su sa al’ummai rawar jiki;

Za su yi mulkin jama’a mai yawa

Sarkinsu zai fi Agag girma,

Za a ɗaukaka mulkinsa.

8 Allah ne ya fisshe su daga Masar,

Kamar kutunkun ɓauna yake a gare su,

Yakubu zai cinye maƙiyansa,

Zai kakkarya ƙasusuwansu, ya mummurɗe kibansu.

9 Al’ummar tana kama da ƙaƙƙarfan zaki

Sa’ad da yake barci, ba wanda zai yi ƙarfin hali ya tashe shi.

Duk wanda ya sa muku albarka zai sami albarka,

Duk wanda ya sa muku la’ana zai sami la’ana.”

Annabcin Bal’amu

10 Sai Balak ya husata da Bal’amu, ya tafa hannunsa ya ce wa Bal’amu, “Na kirawo ka don ka la’anta maƙiyana, amma ga shi, har sau uku kana sa musu albarka.

11 Yanzu sai ka tafi abinka. Hakika,na ce zan ɗaukaka ka, amma ga shi, Ubangiji ya hana maka ɗaukakar.”

12 Sai Bal’amu ya ce wa Balak, “Ashe, ban faɗa wa manzanninka waɗanda ka aiko gare ni ba?

13 Na ce, ‘Ko da Balak zai ba ni gidansa cike da azurfa da zinariya, ba zan iya in zarce maganar Ubangiji ba, in aikata nagarta ko mugunta bisa ga nufin kaina.’ Abin da Ubangiji ya faɗa shi ne zan faɗa.”

14 Bal’amu ya ce wa Balak, “Yanzu fa, zan koma wurin mutanena. Ka zo in sanar maka da abinda mutanen nan za su yi wa mutanenka nan gaba.”

15 Sai ya hurta jawabinsa, ya ce,

“Faɗar Bal’amu ɗan Beyor,

Faɗar mutumin da idonsa take buɗe,

16 Faɗar wanda yake jin faɗar Allah,

Wanda ya san hikimar Maɗaukaki,

Wanda yake ganin wahayin Mai Iko Dukka,

Yana durƙurshe, amma idanunsa a buɗe suke.

17 Ina ganinsa, amma ba yanzu ba,

Ina hangensa, amma ba kusa ba.

Tauraro zai fito daga cikin Yakubu,

Kandiri zai fito daga cikin Isra’ila,

Zai ragargaje goshin Mowabawa,

Zai kakkarya ‘ya’yan Shitu duka.

18 Za a mallaki Edom,

Hakka kuma za a mallaki Seyir abokiyar gābanta,

Isra’ila za ta gwada ƙarfi.

19 Yakubu zai yi mulki,

Zai hallaka waɗanda suka ragu cikin birni.”

20 Sai ya dubi Amalek, ya hurta jawabinsa, ya ce,

“Amalek na fari ne cikin al’ummai,

amm ƙarshensa hallaka ne.”

21 Sai kuma ya dubi Keniyawa, ya hurta jawabinsa, ya ce,

“Wurin zamanku mai ƙarƙo ne,

Gidajenku kuma suna cikin duwatsu.

22 Duk da haka za a lalatar da Keniyawa.

Har yaushe za ku zama bayin Assuriyawa?”

23 Sai kuma ya hurta jawabinsa, ya ce,

“Kaito, wa zai rayu sa’ad da Allah ya yi wannan?

24 Jiragen ruwa kuwa za su zo daga Kittim,

Za su wahalar da Assuriya da Eber,

Su kuma da kansu za su lalace.”

25 Sai Bal’amu ya tashi ya koma garinsu, Balak kuma ya yi tafiyarsa.

Categories
L. KID

L. KID 25

Isra’ilawa sun yi Sujada ga Ba’al-feyor

1 Sa’ad da Isra’ilawa suka yi zango a Shittim, maza suka fara yin lalata da matan Mowabawa.

2 Waɗannan mata sukan gayyaci mutanen zuwa wajen shagalin tsafinsu. Isra’ilawa kuwa sukan ci abinci, su kuma yi sujada ga gumaka.

3 Ta haka Isra’ilawa suka shiga bautar gumakan Ba’al na Feyor. Sai Ubangiji ya husata da Isra’ilawa.

4 Ya ce wa Musa, “Ɗauki sugabannin jama’a, ka rataye su a rana a gabana don in huce daga fushin da nake yi da Isra’ilawa.”

5 Musa kuwa ya ce wa alƙalan Isra’ilawa, “Kowa ya kashe mutanensa da suka shiga bautar gumakan Ba’al-feyor.”

6 Sai ga wani Ba’isra’ile ya taho da wata mace, Bamadayaniya, ya kai ta alfarwarsa ƙiriƙiri a gaban Musa da dukan taron jama’ar Isra’ila a sa’ad da suke kuka a ƙofar alfarwa ta sujada.

7 Finehas ɗan Ele’azara, wato jikan Haruna, firist, ya gani, sai ya tashi daga cikin taron, ya ɗauki mashi.

8 Ya bi Ba’isra’ilen, har zuwa ƙuryar alfarwar, ya soke dukansu biyu, Ba’isra’ilen da macen, har ya sha zarar macen. Da haka aka tsai da annoba daga Isra’ilawa.

9 Duk da haka annobar ta kashe mutane dubu ashirin da dubu huɗu (24,000).

10 Sai Ubangiji ya ce wa Musa,

11 “Finehas ɗan Ele’azara, wato jikan Haruna, firist, ya kawar da fushina daga Isra’ilawa saboda ya yi kishi irin nawa a gabansu, don haka ban shafe Isra’ilawa saboda kishina ba.

12 Domin haka ina yi masa alkawarin da ba zai ƙare ba.

13 Alkawarin zai zama nasa da na zuriyarsa, wato alkawarin zama firist din din din, domin ya yi kishi saboda Allahnsa. Ya kuwa yi kafara domin Isra’ilawa.”

14 Sunan Ba’isra’ilen da aka kashe tare da Bamadayaniyar, Zimri ɗan Salu, shi ne shugaban gidan Saminawa.

15 Sunan Bamadayaniya kuwa, Kozbi, ‘yar Zur. Shi ne shugaban mutanen gidan ubansa a Madayana.

16 Ubangiji kuma ya umarci Musa, ya ce,

17 “Ku fāɗa wa Madayanawa ku hallaka su.

18 Gama sun dame ku da makircinsu da suka yaudare ku a kan al’amarin Feyor da na Kozbi ‘yar’uwarsu, ‘yar shugaban Madayana, wadda aka kashe a ranar da aka yi annoba a Feyor.”

Categories
L. KID

L. KID 26

Ƙidaya ta Biyu

1 Bayan annobar, sai Ubangiji ya ce wa Musa da Ele’azara, ɗan Haruna, firist,

2 “Ku ƙidaya dukan taron jama’ar Isra’ila tun daga mai shekara ashirin zuwa gaba bisa ga gidajen ubanninsu. Ku ƙidaya duk wanda ya isa zuwa yaƙi a cikin Isra’ilawa.”

3 Sai Musa da Ele’azara, firist, suka yi musu magana a filayen Mowab daura da Yariko, suka ce,

4 “A ƙidaya mutane tun daga mai shekara ashirin zuwa gaba kamar yadda Ubangiji ya umarta.”

Isra’ilawa waɗanda suka fita daga ƙasar Masar ke nan.

5 Ra’ubainu shi ne ɗan fari na Yakubu. ‘Ya’yan Ra’ubainu, maza, su ne Hanok, da Fallu,

6 da Hesruna, da Karmi.

7 Waɗannan yawansu ya kai dubu arba’in da uku da ɗari bakwai da talatin (43,730).

8 Fallu ya haifi Eliyab.

9 ‘Ya’yan Eliyab, maza su ne Yemuwel, da Datan, da Abiram. Datan da Abiram ne aka zaɓa daga cikin taron jama’ar, suna cikin ƙungiyar Kora wadda ta tayar wa Musa da Haruna, har ma da Ubangiji.

10 Ƙasa kuwa ta buɗe ta haɗiye su tare da Kora. Wuta kuma ta cinye sauran mutanen ƙungiyar, mutum ɗari biyu da hamsin suka mutu. Suka zama abin faɗakarwa.

11 Amma ‘ya’yan Kora ba su mutu ba.

12 ‘Ya’yan Saminu, maza, bisa ga iyalansu, su ne Yemuwel, da Yamin, da Yakin,

13 da Zohar, da Shawul. Waɗannan su ne iyalan kabilar Saminu.

14 Yawansu ya kai mutum dubu ashirin da biyu da ɗari biyu (22,200).

15 Zuriyar Gad bisa ga iyalansu, su ne Zifiyon, da Haggi, da Shuni,

16 da Ezbon, da Eri,

17 da Arodi, da Areli.

18 Waɗannan su ne iyalan kabilar Gad. Yawan mutanensu ya kai dubu arba’in da ɗari biyar (40,500).

19 Kabilar Yahuza ke nan, (Er, da Onan, ‘ya’yan Yahuza sun mutu a ƙasar Kan’ana).

20 Sauran ‘ya’yansa bisa ga iyalansu su ne, Shela, da Feresa, da Zera,

21 da Hesruna, da Hamul.

22 Waɗannan su ne iyalan kabilar Yahuza. Yawan mutanensu ya kai dubu saba’in da shida da ɗari biyar (76,500).

23 Kabilar Issaka ke nan bisa ga iyalansu, da Tola, da Fuwa,

24 da Yashub, da Shimron.

25 Waɗannan su ne iyalan kabilar Issaka. Yawansu ya kai mutum dubu sittin da huɗu da ɗari uku (64,300).

26 Kabilar Zabaluna ke nan bisa ga iyalansu, Sered, da Elon, da Yaleyel.

27 Waɗannan su ne iyalan kabilar Zabaluna. Yawansu ya kai mutum dubu sittin da ɗari biyar (60,500).

28 Kabilar Yusufu ke nan bisa ga iyalansu, wato Manassa da Ifraimu.

29 Kabilar Manassa, su ne Makir ɗan Manassa. Makir ya haifi Gileyad wanda ya zama tushen zuriyar Gileyad.

30 ‘Ya’yan Gileyad, maza su ne Abiyezer, da Helek,

31 da Asriyel, da Shekem,

32 da Shemida, da Hefer.

33 Zelofehad, ɗan Hefer, ba shi da ‘ya’ya maza, sai dai ‘ya’ya mata. Sunayen ‘ya’yansa mata su ne Mala, da Nowa, da Hogla, da Milka, da Tirza.

34 Waɗannan su ne iyalan kabilar Manassa. Yawansu ya kai mutum dubu hamsin da biyu da ɗari bakwai (52,700).

35 Waɗannan su ne kabilar Ifraimu bisa ga iyalansu, Shutela, da Beker, da Tahat.

36 Iyalin Eran suna lasafta kansu, daga zuriyar Shutela ne.

37 Waɗannan su ne iyalan kabilar Ifraimu. Yawansu ya kai dubu talatin da biyu da ɗari biyar (32,500).

38 Kabilar Biliyaminu ke nan bisa ga iyalansu, Bela, da Ashbel, da Ahiram,

39 da Shuffim, da Huffim.

40 Iyalin Adar da na Na’aman suna lasafta kansu, su daga zuriyar Bela ne.

41 Waɗannan su ne ‘ya’yan Biliyaminu bisa ga iyalansu. Yawansu ya kai mutum dubu arba’in da biyar da ɗari shida (45,600).

42 Waɗannan su ne kabilar Dan bisa ga iyalansu, Hushim. Waɗannan su ne iyalan kabilar Dan.

43 Yawansu ya kai dubu sittin da huɗu da ɗari huɗu (64,400).

44 Kabilar Ashiru ke nan bisa ga iyalansu, Yimna, da Yishwi, da Beriya.

45 Iyalin Beriya kuwa sune Eber, da Malkiyel, suna lasafta kansu a zuriyar Beriya.

46 Sunan ‘yar Ashiru Sera.

47 Waɗannan su ne iyalan kabilar Ashiru. Yawansu ya kai mutum dubu hamsin da uku da ɗari huɗu (53,400).

48 Kabilar Naftali ke nan bisa ga iyalansu, Yezeyel, da Guni,

49 da Yezer, da Shallum.

50 Waɗannan su ne iyalan kabilar Naftali. Yawansu ya kai mutum dubu arba’in da biyar da ɗari huɗu (45,400).

51 Jimillar Isra’ilawa maza waɗanda aka ƙidaya, dubu ɗari shida da dubu ɗaya da ɗari bakwai da talatin (601,730).

An Raba Ƙasa ta Hanyar Kuri’a

52 Sai Ubangiji ya ce wa Musa,

53 “A raba wa waɗannan mutane gādon ƙasar bisa ga yawan kowace kabila.

54 Za ka ba babbar kabila babban rabo, ka ba ƙaramar kabila ƙaramin rabo. Kowace kabila za a ba ta gādo bisa ga yawanta.

55 Amma za a rarraba musu gādon ƙasar kabila kabila ta hanyar kuri’a.

56 Za a rarraba gādo tsakanin manya da ƙananan kabilai ta hanyar kuri’a.”

Kabilar Lawi

57 Waɗannan su ne Lawiyawan da aka ƙidaya bisa ga iyalansu, Gershon, da Kohat, da Merari.

58 Sauran iyalin Lawiyawa daga zuriyar Libni ne, da Hebron, da Mali, da Mushi, da Kora. Kohat shi ne mahaifin Amram,

59 wanda ya auri Yokabed ‘yar Lawi wadda aka haifa masa a Masar. Yokabed ta haifa wa Amram, Haruna, da Musa, da Maryamu, ‘yar’uwarsu.

60 Haruna yana da ‘ya’ya huɗu maza, Nadab, da Abihu, da Ele’azara, da Itamar.

61 Amma Nadab da Abihu sun mutu saboda sun miƙa hadaya da haramtacciyar wuta a gaban Ubangiji.

62 Mazan da aka ƙidaya daga mai wata guda zuwa gaba sun kai dubu ashirin da dubu uku (23,000). Ba a haɗa jimillarsu tare da ta sauran Isra’ilawa ba, da yake ba a ba su gādo tare da su ba.

Joshuwa da Kalibu kaɗai suka Ragu

63 Waɗannan su ne Isra’ilawa waɗanda Musa da Ele’azara, firist, suka ƙidaya a filayen Mowab wajen Kogin Urdun daura da Yariko.

64 Amma a cikin waɗannan da aka ƙidaya, ba wanda ya ragu daga Isra’ilawa waɗanda Musa da Haruna, firist, suka ƙidaya a jejin Sinai.

65 Gama Ubangiji ya riga ya yi magana a kansu, cewa lalle za su mutu a jeji. Ba wani mutumin da ya ragu daga cikinsu, sai dai Kalibu ɗan Yefunne, da Joshuwa ɗan Nun.

Categories
L. KID

L. KID 27

Roƙon ‘Ya’yan Zelofehad Mata

1 Sai ‘ya’yan Zelofehad, mata, ɗan Hefer ɗan Gileyad, ɗan Makir, ɗan Manassa, ɗan Yusufu, suka tafi ƙofar alfarwa ta sujada. Sunayen ‘ya’ya, matan ke nan, Mala, da Nowa, da Hogla, da Milka, da Tirza.

2 Da suka tafi, suka tsaya a gaban Musa da Ele’azara, firist, da gaban shugabanni, da dukan taron jama’a, suka ce,

3 “Mahaifinmu ya rasu cikin jeji. Ba ya cikin ƙungiyar Kora wadda ta tayar wa Ubangiji. Ya rasu saboda alhakin zunubinsa. Ga shi, ba shi da ‘ya’ya maza.

4 Don me za a tsame sunan mahaifinmu daga cikin zuriyar iyalinsa saboda ba shi da ɗa? In ka yarda, muna roƙonka ka ba mu gādo tare da ‘yan’uwan mahaifinmu.”

5 Musa ya kai maganarsu a gaban Ubangiji.

6 Ubangiji ya ce wa Musa,

7 “Maganar ‘ya’yan Zelofehad, mata, daidai ce, saika ba su gādo tare da ‘yan’uwan mahaifinsu. Za ka sa gādon mahaifinsu ya zama nasu.

8 Sai kuma ka shaida wa Isra’ilawa, ka ce, ‘Idan mutum ya rasu ba shi da ɗa,sai ‘yarsa ta ci gādonsa.

9 Idan kuwa ba shi da ‘ya, sai a ba ‘yan’uwansa gādonsa.

10 Idan kuma ba shi da ‘yan’uwa, sai a ba ‘yan’uwan mahaifinsa gādonsa.

11 Idan kuma ba shi da su, sai a ba danginsa na kusa su mallaka, wannan zai zama umarni da ka’ida ga Isra’ilawa kamar yadda ni, Ubangiji na umarce ka.’ ”

An Zaɓi Joshuwa ya Gāji Musa

12 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Hau bisa kan Dutsen Abarim, ka dubi ƙasa wadda na ba Isra’ilawa.

13 Bayan da ka gan ta, za ka mutu kamar yadda Haruna ya yi,

14 domin ba ku yi biyayya da umarnina ba a jejin Zin. Lokacin da dukan jama’a suka yi mini gunaguni a Meriba, ba ku nuna ikona mai tsarki a gabansu ba.” (Wannan shi ne ruwan Meriba na Kadesh a jejin Zin.)

15 Musa kuwa ya ce wa Ubangiji,

16 “Bari Ubangiji Allah na ruhohin dukan ‘yan adam ya shugabantar da mutum a kan taron jama’ar,

17 mutumin da zai shugabance su cikin yaƙi, don kada taron jama’ar Ubangiji su zama kamar tumakin da ba su da makiyaya.”

18 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ɗauki Joshuwa, ɗan Nun, mutumin da ya dace, ka ɗibiya masa hannuwanka,

19 ka sa shi ya tsaya a gaban Ele’azara, firist, da gaban dukan taron, sa’an nan ka keɓe shi a gabansu.

20 Ka danƙa masa ikonka don taron jama’ar Isra’ila su yi masa biyayya.

21 Zai dogara ga Ele’azara, firist, don ya san nufina, ta wurin amfani da Urim da Tummin. Ta haka ne Ele’azara zai bi da Joshuwa da dukan taron jama’ar Isra’ila cikin al’amuransu.”

22 Musa kuwa ya yi kamar yadda Ubangiji ya umarce shi. Ya ɗauki Joshuwa, ya sa shi ya tsaya a gaban Ele’azara, firist, da gaban dukan taron.

23 Ya ɗibiya hannuwansa a kansa, ya keɓe shi kamar yadda Ubangiji ya umarta.

Categories
L. KID

L. KID 28

Hadaya na Kullum

1 Sai Ubangiji ya umarce Musa,

2 ya dokaci Isra’ilawa su tabbatar cewa sun miƙa wa Allah hadaya ta abinci tare da hadayun da za a yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji a ƙayyadadden lokaci bisa ga yadda ake bukata.

3 Waɗannan su ne hadayu na abinci da za a miƙa wa Ubangiji, hadaya ta ƙonawa ta kowace rana, raguna biyu ‘yan bana ɗaya ɗaya marasa lahani.

4 A miƙa ɗan rago ɗaya da safe, ɗaya kuma da maraice,

5 da kuma mudun lallausan gari, kwaɓaɓɓe da man zaitun mafi kyau har rubu’in moɗa.

6 Hadaya ce ta ƙonawa kullum, wadda aka kafa a Dutsen Sinai, don daɗin ƙanshi, hadayar da akan yi da wuta ga Ubangiji.

7 Hadaya ta sha za ta zama rubu’in moɗa na ruwan inabi domin kowane ɗan rago. Za a kwarara hadaya ta sha mai gafi ga Ubangiji a bagade.

8 Ɗayan ɗan ragon kuma za a miƙa da maraice, tare da hadaya ta gari kamar ta safe, da hadayarsa ta sha. Za a miƙa shi hadaya ta ƙonawa, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.

Hadayu na Ranar Asabar

9 A rana Asabar kuwa za a miƙa ‘yan raguna biyu bana ɗaya ɗaya marasa lahani da mudu biyu na lallausan gari, kwaɓaɓɓe da mai, domin yin hadaya ta gari tare da hadayarsa ta sha.

10 Wannan ita ce hadaya ta ƙonawa ta kowace ranar Asabar, banda hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadaya ta sha.

Hadayu na Ɗaya ga Wata

11 A farkon kowane wata sai a miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji, da ‘yan bijimai biyu, da rago ɗaya, da kuma ‘yan raguna bakwai bana daya daya; marasa lahani,

12 hadaya ta gari kuma, a kwaɓa gari humushi uku na garwa da man zaitun don kowane bijimi, da gari humushi biyu na garwa don rago,

13 da kuma gari humushin garwa don ɗan rago. Waɗannan su ne hadayu na abinci na ƙonawa, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.

14 Hadaya ta sha kuwa za ta zama rabin moɗa na ruwan inabi don kowane bijimi, sulusin moɗa kuma don kowane rago, rubu’in moɗa don kowane ɗan rago. Wannan ita ce ka’idar hadaya ta ƙonawa don tsayawar kowane wata na shekara.

15 A kuma miƙa bunsuru ɗaya na yin hadaya don zunubi ga Ubangiji tare da hadaya ta ƙonawa, da hadayarta ta sha.

Hadayu na Idin Abinci Marar Yisti

16 Za a yi Idin Ƙetarewa ga Ubangiji a rana ta goma sha huɗu ga watan fari.

17 Kashegari kuwa za a fara idin kwana bakwai. A kwanakin nan, sai a riƙa cin abinci marar yisti.

18 Za ku yi tsarkakakken taro a ranar fari ta idin, ba za a yi aiki ba.

19 Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimai biyu, da rago ɗaya, da ‘yan raguna bakwai bana ɗaya ɗaya ga Ubangiji. Dukansu su zama marasa lahani.

20 Za a kuma miƙa hadaya ta gari tare da dabbobin, da lallausan gari wanda aka kwaɓa da man zaitun, gari humushi uku na garwa tare da kowane bijimi, da gari humushi biyu tare da kowane rago,

21 gari humushi ɗaya tare da kowane ɗan rago.

22 Za a miƙa bunsuru guda don yin hadaya don zunubi, domin yin kafara.

23 Za a miƙa waɗannan hadayu banda hadaya ta ƙonawa wadda akan miƙa kowace safiya.

24 Haka za a miƙa abinci na hadaya ta ƙonawa kowace rana har kwana bakwai, domin daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Za a kuma riƙa miƙa hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta sha.

25 A rana ta bakwai za a yi tsattsarkan taro, ba za a yi aiki ba.

Hadayun Idin Girbi

26 Za a yi tsattsarkan taro a ranar nunan fari, wato idi na mako bakwai lokacin da za a miƙa wa Ubangiji hadaya da sabon hatsi. A ranar ba za a yi aiki ba.

27 Za a miƙa hadaya ta ƙonawa, da ‘yan bijimai biyu, da rago ɗaya, da ‘yan raguna bakwai bana ɗaya ɗaya don daɗin ƙanshi ga Ubangiji.

28 Za a miƙa hadaya ta gāri tare da dabbobin, da lallausan gari wanda aka kwaɓa da mai, gari humushi uku na garwa, za a miƙa tare da kowane bijimi, humushi biyu na garwa don rago,

29 da humushin garwa don kowane ɗan rago.

30 Za a miƙa bunsuru guda saboda yin hadaya don zunubi, domin a yi kafara.

31 Banda hadaya ta ƙonawa ta kullum, sai a miƙa waɗannan tare da hadayarsu ta sha. Dabbobin su zama marasa lahani.

Categories
L. KID

L. KID 29

Hadayu na Idin Watan Bakwai

1 A rana ta fari ga wata na bakwai za a taru domin yin sujada, ba za a yi aiki a ranar ba. A ranar za a busa ƙahoni.

2 Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimi guda, da rago guda, da ‘yan raguna bakwai bana ɗaya ɗaya don daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Dabbobin za su zama marasa lahani.

3 Tare da dabbobin za a kuma miƙa hadaya ta lallausan gāri kwaɓaɓɓe da mai. Za a miƙa gāri humushi uku na garwa tare da bijimin, humushi biyu na garwa kuma tare da ragon.

4 Za a miƙa humushin garwa na gāri tare da kowane ɗan rago.

5 Sai kuma a miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi domin a yi kafara.

6 Banda waɗannan hadayu kuma, sai a miƙa hadaya ta ƙonawa tare da hadayarta ta gari, da akan yi a tsayawar wata, da kuma hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri, da hadayarsu ta sha. Sai a yi su bisa ga ka’idar yinsu. Hadaya ke nan da akan yi da wuta don daɗin ƙanshi ga Ubangiji.

Hadaya a Ranar Kafara

7 Za a yi tsattsarkan taro a rana ta goma ga watan bakwai domin yin sujada. Ba za a ci abinci ba, ba kuwa za a yi aiki ba.

8 Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimi ɗaya, da rago guda, da ‘yan raguna bakwai bana ɗaya ɗaya don daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Dabbobin nan su zama marasa lahani.

9 Tare da dabbobin za a miƙa hadaya ta gāri kwaɓaɓɓe da mai. Za a miƙa gāri humushi uku na garwa tare da bijimi, da gāri humushi biyu na garwa tare da ragon,

10 da humushin garwa kuma tare da kowane ɗan rago.

11 Za a kuma miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, banda hadaya don zunubi saboda yin kafara, da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gāri, da hadayarsu ta sha.

Hadayu na Idin Bukkoki

12 A rana ta goma sha biyar ga watan bakwai za a yi tsattsarkan taro domin yin sujada, ba za a yi aiki ba. Su kiyaye idin da girmama Ubangiji har kwana bakwai.

13 Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da ‘yan bijimai goma sha uku, da raguna biyu, da ‘yan raguna goma sha huɗu bana ɗaya ɗaya don daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Dabbobin nan su zama marasa lahani.

14 Tare da dabbobin za a miƙa hadaya ta lallausan gāri wanda aka kwaɓa da mai. Za a miƙa gāri humushi uku na garwa tare da kowane bijimi, da gāri humushi biyu na garwa tare da kowane rago,

15 da humushin garwa kuma tare da kowane ɗan rago.

16 Za a kuma miƙa bunsuru guda saboda yin hadaya don zunubi. Banda waɗannan hadayu kuma za a riƙa yin hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri da hadayarta ta sha.

17 A rana ta biyu ta idin za a miƙa bijimai goma sha biyu, da raguna biyu, da ‘yan raguna goma sha huɗu bana ɗaya ɗaya. Dukan dabbobin su zama marasa lahani.

18 Za a kuma miƙa hadaya ta gari da hadayu na sha tare da bijiman, da ragunan, da ‘yan ragunan, bisa ga adadinsu, da kuma bisa ga ka’idar.

19 Za a kuma miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, duk da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gari, da hadayarsu ta sha.

20 A rana ta uku ta idin za a miƙa bijimai goma sha ɗaya, da raguna biyu, da ‘yan raguna goma sha huɗu bana ɗaya ɗaya. Dabbobin su zama marasa lahani.

21 Za a kuma miƙa hadaya ta gari da hadayu na sha tare da bijiman, da ragunan, da ‘yan ragunan, bisa ga adadinsu, da kuma bisa ga ka’idar.

22 Za a miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, duk da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri da hadayarta ta sha.

23 A rana ta huɗu ta idin za a miƙa bijimai goma, da raguna biyu, da ‘yan raguna goma sha huɗu bana ɗaya ɗaya. Dabbobin su zama marasa lahani.

24 Za a kuma miƙa hadaya ta gāri da hadayu na sha tare da bijiman, da ragunan, da ‘yan ragunan, bisa ga adadinsu, da kuma bisa ga ka’idar.

25 Za a miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, duk da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri da hadayarta ta sha.

26 A rana ta biyar ta idin za a miƙa bijimai tara, da raguna biyu, da ‘yan raguna goma sha huɗu bana ɗaya ɗaya. Dabbobin su zama marasa lahani.

27 Za a kuma miƙa hadaya ta gāri da hadayu na sha tare da bijiman, da ragunan, da ‘yan ragunan, bisa ga adadinsu, da kuma bisa ga ka’idar.

28 Za a miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, duk da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri da hadayarta ta sha.

29 A rana ta shida ta idin za a miƙa bijimai takwas, da raguna biyu, da ‘yan raguna goma sha huɗu bana ɗaya ɗaya. Dabbobin su zama marasa lahani.

30 Za a kuma miƙa hadaya ta gāri da hadayu na sha tare da bijiman, da ragunan, da ‘yan ragunan, bisa ga adadinsu, da kuma bisa ga ka’idar.

31 Za a miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, duk da hadaya taƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri da hadayarta ta sha.

32 A rana ta bakwai ta idin za a miƙa bijimai bakwai, da raguna biyu, da ‘yan raguna goma sha huɗu bana ɗaya ɗaya. Dabbobin su zama marasa lahani.

33 Za a kuma miƙa hadaya ta gāri da hadayu na sha tare da bijiman, da ragunan, da ‘yan ragunan bisa ga adadinsu, da kuma bisa ga ka’idar.

34 Za a kuma miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, duk da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri da hadayarta ta sha.

35 A rana ta takwas za a taru domin yin sujada. Ba za a yi aiki ba.

36 Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimi, da rago, da ‘yan raguna bakwai bana ɗaya ɗaya don daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Dabbobin su zama marasa lahani.

37 Za a miƙa hadaya ta gāri da hadaya ta sha tare da bijimin, da ragon, da ‘yan ragunan, bisa ga adadinsu, da kuma bisa ga ka’idar.

38 Za a miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, duk da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri da hadayarta ta sha.

39 Waɗannan su ne hadayun da za a miƙa wa Ubangiji a lokacin idodinsu, duk da hadayunsu na wa’adi, da na yardar rai, da na ƙonawa, da na gāri, da na sha, da na salama.

40 Musa kuwa ya faɗa wa jama’ar Isra’ila kome da kome kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

Categories
L. KID

L. KID 30

Doka a kan Wa’adodin Mata

1 Musa ya kuma ce wa shugabannin kabilan Isra’ilawa, “Ga abin da Ubangiji ya umarta.”

2 Idan mutum ya yi wa’adi ga Ubangiji, ko kuwa ya rantse zai yi wani abu, ko kuwa ba zai yi wani abu ba, to, kada ya warware maganarsa, amma sai ya aikata abin da bakinsa ya hurta.

3 Idan kuma mace ta yi wa’adi ga Ubangiji, ta kuma ɗaure kanta da rantsuwa tun tana yarinya a gidan mahaifinta,

4 idan mahaifinta ya ji wa’adinta da rantsuwarta wadda ta ɗaure kanta da su, bai ce mata kome ba, to, sai wa’adinta da rantsuwarta su tabbata.

5 Amma idan mahaifinta ya ji, ya nuna rashin yarda, to, wa’adinta da rantsuwarta ba za su tsaya ba, Ubangiji kuwa zai gafarce ta domin mahaifinta bai yardar mata ba.

6 Idan kuwa ta yi aure lokacin da take da wa’adi ko kuwa rantsuwar da ta yi da garaje,

7 idan mijinta ya ji wa’adin ko rantsuwar amma bai ce mata kome ba a ranar da ya ji, to, sai wa’adinta da rantsuwarta su tabbata.

8 Amma idan mijinta bai goyi bayanta a ranar da ya ji ba, to, sai wa’adinta da rantsuwarta su warware, Ubangiji kuwa zai gafarce ta.

9 Mace wadda mijinta ya rasu ko sakakkiya, dole ta cika wa’adin da ta yi, da kowane alkawari, za su tabbata.

10 Idan macen aure ta yi wa’adi ko alkawari ba za ta yi wani abu ba,

11 idan mijinta ya ji, amma bai ce mata kome ba, to, sai wa’adinta da kowace irin rantsuwarta su tabbata.

12 Amma idan mijinta ya hana ta a ranar da ya ji, to, sai ta bari. Mijinta ya hana ta ɗaukar wa’adin, Ubangiji kuwa zai gafarce ta.

13 Mijinta yana da iko ya tabbatar, ko kuwa ya rushe kowane wa’adi da kowane irin alkawarin da ta ɗauka.

14 Idan mijinta ya yi shiru, bai ce mata kome ba, to, dole ta cika kowane abu da ta yi wa’adi da wanda kuma ta ɗauki alkawarinsa. Shirun da ya yi ya yardar mata.

15 Amma idan ya ji, sa’an nan daga baya ya hana ta, to, zai sha hukunci a maimakon matar.

16 Waɗannan su ne dokokin da Ubangiji ya ba Musa a kan wa’adodin matar aure da na wadda ba ta yi aure ba, wato matar da take zaune a gidan mahaifinta.