Categories
L. KID

L. KID 31

Yaƙin Jihadi da Madayanawa

1 Ubangiji ya ce wa Musa,

2 “Ka ɗaukar wa Isra’ilawa fansa a kan Madayanawa. Bayan ka yi wannan za ka mutu.”

3 Musa kuwa ya ce wa jama’a, “Ku sa mazajen da suke cikinku su yi shiri, su yi ɗamarar yaƙi, don su tafi su yi yaƙi da Madayanawa, su ɗaukar wa ubangiji fansa a kansu.

4 Sai ku aiki mutum dubu ɗaya daga kowace kabilar Isra’ila zuwa wurin yaƙi.”

5 Aka samo mutum dubu goma sha biyu (12,000) shiryayyu don yaƙi, daga cikin dubban Isra’ilawa, mutum dubu ɗaya daga kowace kabila.

6 Musa ya aike su zuwa yaƙi tare da Finehas, ɗan Ele’azara firist, da akwatin alkawari, da ƙahonin kiran yaƙi a hannun Finehas.

7 Suka yi yaƙi da Madayanawa suka kashe musu kowane namiji, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

8 Suka kashe har da sarakuna biyar na Madayanawa, da Ewi, da Rekem, da Zur, da Hur, da Reba. Suka kuma kashe Bal’amu ɗan Beyor.

9 Isra’ilawa suka kwashi mata da yaran Madayanawa bayi. Suka washe shanunsu, da tumakinsu da dukan dukiyarsu ganima.

10 Suka kuma ƙone dukan biranen zamansu da dukan san saninsu da wuta.

11 Da mutum da dabba sun kwashe su ganima.

12 Suka kawo bayin da ganimar a wurin Musa, da Ele’azara firist, da taron jama’ar Isra’ila a zango a filayen Mowab a Kogin Urdun daura da Yariko.

Sojoji Sun Komo

13 Sai Musa da Ele’azara firist, da shugabannin taron jama’ar Isra’ila suka fita zango su tarye su.

14 Musa kuwa ya husata da shugabannin sojoji waɗanda suke shugabannin dubu dubu da shugabannin ɗari ɗari, waɗanda suka dawo daga wurin yaƙi.

15 Ya tambaye su ya ce, “Don me kuka bar dukan mata da rai?

16 Ku tuna fa, su ne, ta wurin shawarar Bal’amu, suka yaudari Isra’ilawa, suka saɓi Ubangiji cikin maƙidar Feyor, har annoba ta fasu a jama’ar Ubangiji.

17 Yanzu, sai ku kashe dukan yara maza da kowace mace wadda ta san namiji.

18 Amma dukan ‘yan mata da ba su san maza ba, sai ku bar wa kanku.

19 A cikinku duk wanda ya kashe mutum ko ya taɓa gawa, sai ya zauna a bayan zango kwana bakwai don ya tsarkake kansa tare da bayin a rana ta uku da ta bakwai.

20 Za ku tsarkake kowace riga, da kowane abu da aka yi da fata, da kowane kaya da aka yi da gashin awaki, da kowane abu da aka yi da itace.”

21 Ele’azara firist kuwa, ya ce wa sojojin da suka tafi yaƙi, “Waɗannan su ne ka’idodin da Ubangiji ya ba Musa.

22 Zinariya, da azurfa, da tagulla, da baƙin ƙarfe, da kuza, da darma,

23 da dukan abin da wuta ba ta ci ba, su ne za ku tsarkake su da wutar tsarkakewa, duk da haka za a kuma tsarkake shi da ruwa. Amma abin da wuta takan ci, sai a tsarkake shi da ruwa kawai.

24 Ku wanke tufafinku a rana ta bakwai don ku tsarkaka, bayan haka ku shiga zangon.”

Raba Ganima

25 Ubangiji kuma ya ce wa Musa,

26 “Da kai, da Ele’azara firist, da shugabannin gidajen kakannin taron jama’a, ku lasafta yawan mutane, da dabbobin da aka kwaso ganima.

27 Ku kasa ganima kashi biyu, ku ba sojojin da suka tafi yaƙi kashi ɗaya, kashi ɗayan kuwa ku ba taron jama’ar.

28 Sai ka karɓi na Ubangiji daga cikin kashin ganimar da aka baiwa sojojin da suka tafi yaƙi. Ka ɗauki ɗaya daga cikin mutum ɗari biyar, da shanu ɗari biyar, da jakai ɗari biyar, da tumaki ɗari biyar.

29 Ka ba Ele’azara firist. Wannan hadaya ta ɗagawa ce ga Ubangiji.

30 Daga cikin rabin ganimar da aka ba Isra’ilawa, sai ka ɗauki ɗaya ɗaya daga cikin mutum hamsin, da shanu hamsin,da jakai hamsin, da tumaki hamsin, da dukan dabbobin. Ka ba da su ga Lawiyawa waɗanda suke lura da alfarwar sujada ta Ubangiji.”

31 Musa da Ele’azara firist, suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa.

32 Yawan ganimar da sojoji suka kawo ke nan, tumaki dubu ɗari shida da dubu saba’in da dubu biyar (675,000),

33 shanu dubu saba’in da dubu biyu (72,000),

34 jakai dubu sittin da dubu ɗaya (61,000),

35 ‘yan mata dubu talatin da dubu biyu (32,000) waɗanda ba su san namiji ba.

36 Kashin da aka ba sojoji waɗanda suka tafi yaƙi ne nan, tumaki dubu ɗari uku da talatin da bakwai da ɗari biyar (337,500).

37 Daga ciki aka fitar da tumaki ɗari shida da saba’in da biyar domin Ubangiji.

38 Shanu kuma dubu talatin da dubu shida (36,000), daga ciki aka fitar da shanu saba’in da biyu domin Ubangiji.

39 Jakai dubu talatin da ɗari biyar (30,500), daga ciki aka fitar da jakai sittin da ɗaya domin Ubangiji.

40 ‘Yan mata dubu goma sha shida (16,000), daga ciki aka fitar da ‘yan mata talatin da biyu domin Ubangiji.

41 Sai Musa ya ba Ele’azara firist rabon Ubangiji, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

42 Wannan shi ne kashin da aka ba jama’ar Isra’ila cikin kashin da aka ware daga na waɗanda suka tafi yaƙin.

43 Tumaki dubu ɗari uku da talatin da bakwai da ɗari bayar (337,500),

44 shanu dubu talatin da dubu shida (36,000),

45 jakai dubu talatin da ɗari biyar (30,500),

46 ‘yan mata dubu goma sha shida (16,000).

47 Daga rabin kashi na jama’ar Isra’ila, Musa ya ɗauki ɗaya daga cikin hamsin na ‘yan mata, da na dabbobi, ya ba Lawiyawan da suke lura da alfarwar sujada ta Ubangiji kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

48 Sai shugabannin da suka shugabanci rundunar yaƙin, suka zo wurin Musa.

49 Suka ce masa, “Mu barorinka mun ƙidaya mayaƙan da suke ƙarƙashin ikonmu, ba wanda ya ɓace daga cikinmu.

50 Mun kuwa kawo wa Ubangiji hadaya daga cikin abubuwan da kowannenmu ya samu, kayan ado na zinariya, da mundaye, da ƙawane da ‘yan kunne, da duwatsun wuya, don yi wa kanmu kafara a gaban Ubangiji.”

51 Musa da Ele’azara firist, suka karɓi zinariya da kayan adon duka.

52 Dukan zinariya da shugabanni suka bayar hadaya ga Ubangiji, nauyinta ya kai shekel dubu goma sha shida da ɗari bakwai da hamsin (16,750).

53 Kowane soja ya kwashi ganimarsa.

54 Musa da Ele’azara firist kuwa, suka karɓi zinariya da shugabanni suka bayar, suka kai su cikin alfarwa ta sujada don ta zama abin tunawa da jama’ar Isra’ila a gaban Ubangiji.

Categories
L. KID

L. KID 32

Kabilai a Gabashin Urdun

1 Kabilan Ra’ubainu da Gad suna da dabbobi da yawa ƙwarai. Da suka ga ƙasar Yazar da ta Gileyad wuri ne mai kyau domin shanu,

2 sai suka je wurin Musa da Ele’azara firist, da shugabannin taron jama’ar,

3 suka ce, “Atarot, da Dibon, da Yazar, da Bet-nimra, da Heshbon, da Eleyale, da Simba, da Nebo, da Ba’al-meyon,

4 ƙasar da Ubangiji ya ci da yaƙi a gaban taron jama’a, ƙasa ce mai kyau don dabbobi. Ga shi kuwa, barorinka suna da dabbobi da yawa.

5 Idan mun sami tagomashi a gare ka, ka ba mu wannan ƙasa ta zama mallakarmu, kada ka kai mu a wancan hayin Urdun.”

6 Amma Musa ya amsa musu ya ce, “Wato sai ‘yan’uwanku su yi ta yaƙi,ku kuwa ku yi zamanku a nan, ko?

7 Don me za ku karya zuciyar jama’ar Isra’ila daga hayewa zuwa ƙasar da Ubangiji ya ba su?

8 Haka iyayenku suka yi sa’ad da na aike su daga Kadesh-barneya don su dubo ƙasar.

9 Gama sa’ad da suka tafi Kwarin Eshkol suka ga ƙasar, suka karya zuciyar jama’a daga shigar ƙasar da Ubangiji ya ba su.

10 Saboda haka Ubangiji ya husata a ranan nan, har ya yi wa’adi ya ce,

11 ‘Hakika ba wani daga cikin mutanen da suka fito daga Masar, tun daga mai shekara ashirin zuwa gaba da zai ga ƙasar da na rantse zan ba Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, domin ba su bi ni sosai ba.

12 Sai dai Kalibu, ɗan Yefunne Bakenizze, da Joshuwa ɗan Nun, domin su ne kaɗai suka bi ni sosai.’

13 Saboda Ubangiji ya husata da isra’ilawa, shi ya sa suka yi ta yawo a jeji har shekara arba’in, wato sai da tsaran nan wadda ta aikata mugunta a gaban Ubangiji ta ƙare.

14 Ga shi, ku kuma da kuke ‘ya’yan mugayen mutanen nan, ku da kuke a matsayin iyayenku, kuna so ku ƙara sa Ubangiji ya husata da Isra’ilawa.

15 Gama idan kun ƙi binsa, zai sāke yashe ku a jeji. Ku ne kuwa za ku zama sanadin hallakar mutanen nan duka.”

16 Sai suka zo kusa da shi, suka ce, “Za mu gina garu na dutse don mu kāre dabbobinmu, da birane don ‘ya’yanmu a nan.

17 ‘Ya’yanmu za su zauna a biranen don gudun mazaunan ƙasar, amma mu za mu ɗauki makamai mu tafi tare da sauran Isra’ilawa, har mu kai su wuraren zamansu.

18 Ba kuwa za mu koma gidajenmu ba, sai lokacin da kowane Ba’isra’ile ya sami gādonsa.

19 Gama ba za mu ci gādo tare da su a wancan hayin Urdun ba, domin mun sami gādonmu a wannan hayi na gabashin Urdun.”

20 Sai Musa ya ce musu, “Idan za ku yi haka, wato ku ɗauki makamai, ku tafi yaƙi a gaban Ubangiji,

21 kowane sojanku ya haye Urdun a gaban Ubangiji, har lokacin da Ubangiji ya kori abokan gābansa daga gabansa,

22 har kuma lokacin da aka ci ƙasar a gaban Ubangiji kafin ku koma, to, za ku kuɓuta daga alhakinku a gaban Ubangiji da jama’ar Isra’ila. Wannan ƙasa kuwa za ta zama mallakarku a gaban Ubangiji.

23 Idan kuwa ba ku yi haka ba, kun yi wa Ubangiji laifi, ku tabbata fa alhakin zunubinku zai kama ku.

24 To, sai ku gina wa ‘ya’yanku birane, ku gina wa garkunanku garu, amma ku aikata abin da kuka faɗa da bakinku.”

25 Sai Gadawa da Ra’ubainawa suka amsa wa Musa, suka ce, “Barorinka za su yi kamar yadda ka umarta.

26 ‘Ya’yanmu, da matanmu, da tumakinmu, da shanunmu za su zauna a birane a nan Gileyad.

27 Amma kowane soja a cikinmu zai haye a gaban Ubangiji zuwa yaƙi kamar yadda shugabanmu ya faɗa.”

28 Sai Musa ya yi wa Ele’azara firist, da Joshuwa ɗan Nun, da shugabannin gidajen kakannin kabilan mutanen Isra’ila kashedi a kansu,

29 ya ce, “Idan kowane soja na Gadawa da Ra’ubainawa zai haye Urdun tare da ku don yaƙi har an ci ƙasar dominku, to, sai ku ba su ƙasar Gileyad ta zama mallakarsu.

30 Amma idan ba su haye tare da ku da shirin yaƙi ba, to, sai ku ba su gādo tare da ku a cikin ƙasar Kan’aniyawa.”

31 Gadawa da Ra’ubainawa kuwa suka ce, “Kamar yadda Ubangiji ya ce wa barorinka, haka za mu yi.

32 Za mu haye da shirin yaƙi a gaban Ubangiji zuwa cikin ƙasar Kan’aniyawa, amma za mu sami gādonmu a wannan hayin Urdun.”

33 Sa’an nan Musa ya ba Gadawa, da Ra’ubainawa, da rabin mutanen Manassa, ɗan Yusufu, mulkin Sihon, Sarkin Amoriyawa, da mulkin Og, Sarkin Bashan, wato ƙasar da biranenta da karkaransu.

34 Sai Gadawa suka gina Dibon, da Atarot, da Arower,

35 da Atarot-shofan, da Yazar, da Yogbeha,

36 da Bet-nimra, da Bet-aram su zama birane masu garu da shinge don dabbobi.

37 Ra’ubainawa kuwa suka gina Heshbon da Eleyale, da Kiriyatayim,

38 da Nebo, da Ba’al-meyon, da Sibma.

39 Mutanen Makir, ɗan Manassa, suka tafi Gileyad, suka ci ta da yaƙi, suka kori Amoriyawan da suke cikinta.

40 Sai Musa ya ba mutanen Makir, ɗan Manassa, Gileyad, suka zauna ciki.

41 Yayir, ɗan Manassa, ya tafi ya ci ƙauyukansu da yaƙi, suka ba su suna Hawot-yayir.

42 Noba kuma ya tafi ya ci Kenat da ƙauyukanta da yaƙi, ya ba ta suna Noba bisa ga sunansa.

Categories
L. KID

L. KID 33

Tafe-tafe daga Masar zuwa Mowab

1 Waɗannan su ne wuraren da Isra’ilawa suka yi zango sa’ad da suka fita runduna runduna daga ƙasar Masar ta hannun Musa da Haruna.

2 Bisa ga faɗar Ubangiji, Musa ya rubuta wuraren tashinsu da wuraren saukarsu. Wuraren saukarsu da na tashinsu ke nan.

3 Sun tashi daga Ramases a rana ta goma sha biyar ga watan fari. A kashegarin Idin Ƙetarewa ne suka fita gabagaɗi a gaban dukan Masarawa.

4 Masarawa suna ta binne gawawwakin ‘ya’yan farinsu da Ubangiji ya karkashe musu. Banda ‘ya’yan farinsu kuma Ubangiji ya hukunta wa allolinsu.

5 Isra’ilawa kuwa suka tashi daga Ramases suka sauka a Sukkot.

6 Suka tashi daga Sukkot suka sauka a Etam wadda take a gefen jejin.

7 Da suka tashi daga Etam, sai suka juya zuwa Fi-hahirot wadda take gaban Ba’al-zefon suka sauka a gaban Migdol.

8 Da suka tashi daga gaban Fi-hahirot sai suka haye teku zuwa cikin jejin. Suka yi tafiya kwana uku a jejin Etam, suka sauka a Mara.

9 Suka tashi daga Mara suka zo Elim inda akwai maɓuɓɓugan ruwa guda goma sha biyu da itacen dabino guda saba’in. Sai suka sauka a can.

10 Suka tashi daga Elim, suka sauka a gefen Bahar Maliya.

11 Da suka tashi daga Bahar Maliya suka sauka a jejin Sin.

12 Suka tashi daga jejin Sin, suka sauka a Dofka.

13 Daga Dofka suka tafi Alush.

14 Suka tashi daga Alush suka sauka a Refidim inda mutane suka rasa ruwan sha.

15 Suka tashi daga Refidim suka sauka a jejin Sinai.

16 Da suka tashi daga jejin Sinai, sai suka sauka a Kibrot-hata’awa.

17 Suka tashi daga Kibrot-hata’awa suka sauka a Hazerot.

18 Da suka tashi daga Hazerot, sai suka sauka a Ritma.

19 Suka tashi daga Ritma suka sauka a Rimmon-farez.

20 Suka tashi daga Rimmon-farez, suka sauka a Libna.

21 Da suka tashi daga Libna, sai suka sauka a Rissa.

22 Da suka tashi daga Rissa, suka sauka a Kehelata.

23 Suka tashi daga Kehelata suka sauka a Dutsen Shifer.

24 Suka tashi daga Dutsen Shifer suka sauka a Harada.

25 Da suka tashi daga Harada, suka sauka a Makelot.

26 Suka tashi daga Makelot suka sauka a Tahat.

27 Suka tashi daga Tahat suka sauka a Tara.

28 Suka kama hanya daga Tara suka sauka a Mitka.

29 Suka kuma kama hanya daga Mitka suka sauka a Hashmona.

30 Daga Hashmona suka sauka a Moserot.

31 Da suka tashi daga Moserot suka sauka a Bene-ya’akan.

32 Suka tashi daga Bene-ya’akan suka sauka a Hor-hagidgad.

33 Da suka tashi daga Hor-hagidgad suka sauka a Yotbata.

34 Suka kama hanya daga Yotbata suka sauka a Abrona.

35 Da suka tashi daga Abrona, sai suka sauka a Eziyon-geber.

36 Suka tashi daga Eziyon-geber suka sauka a jejin Zin, wato Kadesh.

37 Da suka kama hanya daga Kadesh suka sauka a Dutsen Hor a kan iyakar ƙasar Edom.

38 Bisa ga umarnin Ubangiji, Haruna firist ya hau Dutsen Hor inda ya rasu a rana ta fari ga watan biyar a shekara ta arba’in ta fitowar jama’ar Isra’ila daga ƙasar Masar.

39 Haruna yana da shekara ɗari da ashirin da uku sa’ad da ya rasu a Dutsen Hor.

40 Sai Sarkin Arad, Bakan’ane wanda yake zaune a Negeb, a ƙasar Kan’ana, ya ji zuwan Isra’ilawa.

41 Isra’ilawa kuma suka tashi daga Dutsen Hor, suka sauka a Zalmona.

42 Daga Zalamona suka sauka a Funon.

43 Da suka tashi daga Funon, sai suka sauka a Obot.

44 Suka kuma kama hanya daga Obot suka sauka a Abarim a karkarar Mowab.

45 Suka tashi daga nan suka sauka a Dibon-gad.

46 Suka tashi daga Dibon-gad suka sauka a Almon-diblatayim.

47 Da suka tashi daga Almon-diblatayim, suka sauka a duwatsun Abarim a gaban Nebo.

48 Daga duwatsun Abarim suka sauka a filayen Mowab kusa da Urdun daura da Yariko.

49 Suka sauka kusa da Urdun, suka kakkafa alfarwansu tun daga Betyeshimot har zuwa Abel-shittim, a filayen Mowab.

Umarni kafin su Haye Urdun

50 Sai Ubangiji ya yi magana da Musa a filayen Mowab kusa da Urdun, daura da Yariko, ya ce

51 ya faɗa wa jama’ar Isra’ila, “Sa’ad da kuka haye Urdun zuwa ƙasar Kan’ana,

52 sai ku kori dukan mazaunan ƙasar daga gabanku ku rurrushe sassaƙaƙƙun duwatsunsu, da siffofinsu na zubi, da masujadansu.

53 Sa’an nan ku mallaki ƙasar, ku zauna a ciki,gama na ba ku ƙasar, ku mallake ta.

54 Za ku rarraba wa kanku gādon ƙasar kabila kabila ta hanyar jefar kuri’a. Za ku ba babbar kabila babban rabo, ƙaramar kabila kuwa ku ba ta ƙaramin rabo. Inda duk kuri’a ta fāɗa wa mutum, nan ne zai zama wurinsa. Bisa ga kabilan kakanninku za ku gāji ƙasar.

55 Amma idan ba ku kori mazaunan ƙasar daga gabanku ba, to, waɗannan da kuka bari cikinta za su zama haki a idanunku, da ƙayayuwa a kwiyaɓunku. Za su yi ta wahalshe ku da yaƙi.

56 Idan ba ku kore su ba, zan lalatar daku kamar yadda na shirya lalatar da su.”

Categories
L. KID

L. KID 34

Iyakokin Ƙasar

1 Ubangiji ya ba Musa

2 waɗannan umarnai domin jama’ar Isra’ila. Sa’ad da suka shiga ƙasar Kan’ana ga yadda iyakokin ƙasashensu za su zama.

3 Iyakar ƙasarsu daga wajen kudu ta miƙa tun daga wajen jejin Zin, har zuwa iyakar Edom. Iyakarsu kuwa ta wajen kudu za ta fara daga ƙarshen Tekun Gishiri wajen gabas.

4 Sa’an nan kuma za ta nausa ta nufin hawan Akrabbim, ta ƙetare zuwa Zin, ta dangana da kudancin Kadesh-barneya, sa’an nan ta miƙa zuwa Hazar’addar, ta zarce ta bi ta Azemon.

5 Iyakar za ta nausa daga Azemon zuwa rafin Masar, ta fāɗa bahar.

6 Bahar Rum ita ce iyakarsu ta wajen yamma.

7 Iyakarsu a wajen arewa kuwa ita ce tun daga Bahar Rum zuwa Dutsen Hor.

8 Daga Dutsen Hor iyakar za ta bi zuwa Hamat ta tsaya a Zedad.

9 Iyakar za ta miƙa har zuwa Zifron, ta tsaya a Hazar-enan, wannan ita ce iyakarsu a wajen arewa.

10 Iyakarsu a wajen gabas za ta tashi tun daga Haza-enan har zuwa Shefam.

11 Sa’an nan za ta gangara daga Shefam zuwa Ribla wajen gabashin Ayin. Za ta kuma gangara har ta kai Tekun Galili a wajen gabas.

12 Iyakar kuma za ta gangara har zuwa Urdun, ta tsaya a Tekun Gishiri. Wannan ita ce ƙasarsu da iyakokinta kewaye da ita.

13 Sai Musa ya ce wa Isra’ilawa, “Wannan ita ce ƙasar da za ku gāda ta hanyar jefa kuri’a. Ƙasar da Ubangiji ya umarta a ba kabilai tara da rabi.

14 Gama kabilar Ra’ubainu da ta Gad da kuma rabin kabilar Manassa sun riga sun karɓi nasu gādo.

15 Kabilan nan biyu da rabi sun karɓi nasu gādo a wancan hayin Urdun a gabashin Yariko.”

Shugabannin da za su Rarraba Kasa

16 Ubangiji kuma ya ce wa Musa,

17 “Ga sunayen mutanen da za su taimake ka raba gādon ƙasar, Ele’azara firist, da Joshuwa ɗan Nun.

18 Za ka kuma ɗauki shugaba ɗaya daga kowace kabila don su raba gādon ƙasar.

19 Waɗannan su ne sunayen mutanen, Kalibu ɗan Yefunne daga kabilar Yahuza.

20 Shemuyel ɗan Ammihud daga kabilar Saminu.

21 Elidad ɗan Kislon daga kabilar Biliyaminu.

22 Bukki ɗan Yogli daga kabilar Dan.

23 Na wajen Yusufu, Haniyel ɗan Efod daga kabilar Manassa,

24 da Kemuwel ɗan Shiftan daga kabilar Ifraimu.

25 Elizafan ɗan Farnak daga kabilar Zabaluna.

26 Faltiyel ɗan Azzan daga kabilar Issaka.

27 Ahihud ɗan Shelomi daga kabilar Ashiru.

28 Fedahel ɗan Ammihud daga kabilar Naftali.”

29 Waɗannan su ne mutanen da Ubangiji ya umarta su raba wa jama’ar Isra’ila gādon ƙasar Kan’ana.

Categories
L. KID

L. KID 35

Biranen Lawiyawa

1 A filayen Mowab a wajen Urdun daura da Yariko, Ubangiji ya yi magana da Musa, ya ce,

2 “Ka umarci jama’ar Isra’ila, ka ce su ba Lawiyawa biranen da za su zauna a ciki daga cikin gādonsu, za su kuma ba Lawiyawa hurumi kewaye da biranen.

3 Biranen za su zama nasu, inda za su zauna, hurumi kuwa domin shanunsu da sauran dukan dabbobinsu.

4 Girman hurumin da za su ba Lawiyawa kewaye da biranen zai zama mai fāɗin kamu dubu kewaye da garun birnin.

5 A bayan birnin za a auna kamu dubu biyu a wajen gabas, kamu dubu biyu a wajen kudu, kamu dubu biyu a wajen yamma, kamu dubu biyu a wajen arewa. Wannan zai zama hurumin mutanen birnin. Birnin kuwa zai kasance a tsakiya.

6 A cikin biranen da za a ba Lawiyawa, shida su zama na mafaka, inda za a yarda wa mai kisankai ya gudu zuwa can. Banda biranen mafaka guda shida, za a kuma ba su birane arba’in da biyu.

7 Wato dukan biranen da za a ba Lawiyawa guda arba’in da takwas ne tare da huruminsu.

8 Isra’ilawa za su ba Lawiyawa biranen nan bisa ga girman mallakarsu. Manyan kabilai za su ba su birane da yawa, amma ƙananan kabilai za su ba su birane kaɗan.”

Biranen Mafaka

9 Ubangiji kuwa ya faɗa wa Musa,

10 ya ce wa jama’ar Isra’ila, “Sa’ad da kuka haye Urdun zuwa cikin ƙasar Kan’ana,

11 sai ku keɓe wa kanku biranen mafaka domin wanda ya yi kisankai da kuskure, ba da niyya ba, ya gudu zuwa can.

12 Biranen za su zamar muku mafaka daga hannun mai bin hakkin jini, don kada a kashe mai kisankai tun bai riga ya tsaya a gaban shari’a ba.

13 Sai ku zaɓi birane shida.

14 Biranen mafaka uku a hayin gabashin Urdun, birane uku kuma a ƙasar Kan’ana.

15 Waɗannan birane shida za su zama wuraren mafaka ga jama’ar Isra’ila, da baƙi, da baren da yake zaune tare da su, domin duk wanda ya kashe wani ba da niyya ba, ya tsere zuwa can.

16 “Amma idan wani ya bugi wani da makami na ƙarfe har ya mutu, ya yi kisankai, sai a kashe shi.

17 Idan kuwa ya jefe shi da dutsen da ya isa a yi kisankai da shi, har ya mutu, ya yi kisankai ke nan, to, sai a kashe shi.

18 Idan kuwa ya buge shi da makami na itace da ya isa a yi kisankai da shi, har kuwa ya mutu, ya yi kisankai ka nan, sai a kashe shi.

19 Sai mai bin hakkin jinin ya kashe mai kisankan sa’ad da ya iske shi.

20 “Idan saboda ƙiyayya ya laɓe, ya soke shi, ko ya jefe shi har ya mutu,

21 ko kuma saboda ƙiyayya ya naushe shi da hannu har ya mutu, sai a kashe shi, gama ya yi kisankai ke nan. Wanda yake bin hakkin jinin, zai kashe wanda ya yi kisankai sa’ad da ya iske shi.

22 “Amma idan bisa ga tsautsayi ya soke shi, ba don ƙiyayya ba, ko kuwa idan ya jefe shi da kowane abu, ba a laɓe ba,

23 ko ya jefe shi da dutsen da ya isa a kashe mutum da shi, ba da saninsa ba, shi kuwa ba maƙiyinsa ba ne, bai kuwa yi niyya ya cuce shi ba, amma ga shi kuwa, ya kashe shi,

24 to, sai taron jama’a su hukunta tsakanin mai kisankan da mai bin hakkin jinin bisa ga waɗannan ka’idodi.

25 Taron jama’a za su ceci mai kisankan daga hannun mai bin hakkin jinin. Su komar da shi a birnin mafaka inda ya je neman mafaka. Zai zauna can sai lokacin da babban firist da aka keɓe da tsattsarkan mai ya rasu.

26 Amma idan a wani lokaci mai kisankan ya fita kan iyakar birnin mafaka inda yake,

27 idan mai bin hakkin jinin ya same shi a bayan iyakar birnin, ya kashe shi, bai yi laifi ba.

28 Gama dole ne mai kisankan ya zauna cikin birnin mafaka inda yake, sai bayan rasuwar babban firist. Bayan rasuwar babban firist, mai kisankan yana iya komawa ƙasarsa.”

Ka’idodin Shaidu da Fansa

29 “Waɗannan ka’idodi sun shafe ku da zuriyarku a duk inda kuke.

30 Duk wanda ya yi kisankai sai a kashe shi bisa ga shaidar shaidu, amma saboda shaidar mutum ɗaya ba za a kashe mutum ba.

31 Kada ku karɓi fansa don ran wanda ya yi kisankai, dole ne a kashe shi.

32 Haka nan kuma kada ku karɓi fansa saboda wanda ya tsere zuwa birnin mafaka don ya koma ya zauna gidansa tun babban firist bai rasu ba.

33 Saboda haka kada ku ƙazantar da ƙasar da kuke zaune a ciki, gama jini yakan ƙazantar da ƙasa. Ba wata kafara da za a yi don ƙasar da aka zubar da jini a cikinta, sai dai da jinin wanda ya zubar da jinin.

34 Kada ku ƙazantar da ƙasar da kuke zaune a ciki, wadda ni kuma nake zaune a ciki, gama ni Ubangiji ina zaune a tsakiyar jama’ar Isra’ila.”

Categories
L. KID

L. KID 36

Gādon Matan Aure

1 Sai shugabannin gidajen iyalan ‘ya’yan Gileyad, ɗan Makir, jikan Manassa, ɗan Yusufu, suka zo suka yi magana da Musa da sauran shugabanni.

2 Suka ce, “Ubangiji ya umarce ka ka raba wa Isra’ilawa gādon ƙasar ta hanyar jefa kuri’a. Ubangiji kuwa ya umarce ka ka ba ‘ya’ya mata na Zelofehad, ɗan’uwanmu, gādo.

3 Amma idan suka auri waɗansu daga waɗansu kabilan jama’ar Isra’ila, wato za a ɗebe gādonsu daga gādon kakanninmu a ƙara wa gādon kabilan mutanen da suka aura, wato ka ga an ɗebe daga cikin namu gādo ke nan.

4 Sa’ad da shekara ta hamsin ta murnar Isra’ilawa ta kewayo, za a haɗa gādonsu da na kabilan mutanen da suka aura, da haka za a ɗebe gādonsu daga gādon kabilar kakanninmu.”

5 Musa kuwa ya umarci Isra’ilawa bisa ga faɗar Ubangiji ya ce, “Abin da mutanen kabilar ‘ya’yan Yusufu suka faɗa daidai ne.

6 Abin da Ubangiji ya umarta a kan ‘ya’ya mata na Zelofehad ke nan, ‘A bar su su auri wanda suka ga dama, amma sai a cikin iyalin kabilar kakansu.

7 Ba za a sāke gādon Isra’ilawa daga wata kabila zuwa wata ba, gama kowane mutum na cikin jama’ar Isra’ila zai riƙe gādonsa na kabilar kakanninsa.

8 Kowace ‘ya mace wadda ta ci gādo a wata kabilar Isra’ila, sai ta yi aure a cikin kabilar kakanta domin kowane Ba’isra’ile ya ci gādon kakanninsa.

9 Ta yin haka ba za a sāke gādo daga wata kabila zuwa wata ba, gama kowace kabilar Isra’ila za ta riƙe gādonta.’ ”

10 Sai ‘ya’yan Zelofehad mata, wato Mala, da Tirza, da Hogla, da Milka, da Nowa suka yi kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

11 Suka auri ‘ya’yan ‘yan’uwan mahaifinsu.

12 Sun yi aure a cikin iyalan ‘ya’yan Manassa, ɗan Yusufu. Gādonsu kuwa bai ɓalle daga cikin kabilar iyalin kakansu ba.

13 Waɗannan su ne umarnai da ka’idodi waɗanda Ubangiji ya ba jama’ar Isra’ila ta wurin Musa a filayen Mowab kusa da Urdun daura da Yariko.