Categories
L. MAH

L. MAH 1

Yahuza da Saminu sun Ci Adoni-bezek

1 Bayan da Joshuwa ya rasu, jama’ar Isra’ila suka tambayi Ubangiji suka ce, “Wane ne daga cikinmu zai fara tafiya don ya yaƙi Kan’aniyawa?”

2 Sai Ubangiji ya ce, “Yahuza ne zai tafi, ga shi, na ba da ƙasar a gare shi.”

3 Yahuza kuwa ya ce wa Saminu ɗan’uwansa, “Ka zo tare da ni a wurin da aka ba ni rabon gādona don mu yaƙi Kan’aniyawa, ni kuma zan tafi tare da kai a wurin da aka ba ka rabon gādonka.” Saminu ya tafi tare da shi.

4 Yahuza ya tafi, Ubangiji kuwa ya ba da Kan’aniyawa da Ferizziyawa a gare su, suka kashe mutum dubu goma daga cikinsu a Bezek.

5 Suka iske Adoni-bezek a can, suka yi yaƙi da shi, suka kuma ci Kan’aniyawa da Ferizziyawa.

6 Sai Adoni-bezek ya gudu, amma suka bi shi, suka kama shi. Suka yanyanke manyan yatsotsinsa na hannu da na ƙafa.

7 Ya kuma ce, “Sarakuna saba’in waɗanda aka yanyanke manyan yatsotsinsu na hannu da na ƙafa, suka kalaci abincinsu a ƙarƙashin teburina. Allah kuwa ya yi mini kamar yadda na yi musu.” Suka kawo shi Urushalima, a nan ya mutu.

Kabilar Yahuza ta Ci Urushalima da Hebron

8 Mutanen Yahuza kuwa suka yaƙi Urushalima, suka ci ta, suka karkashe mutanenta, suka kuma cinna mata wuta.

9 Bayan wannan suka gangara kuma, suka yaƙi Kan’aniyawan da suke zaune a ƙasar tudu, da Negeb, da filayen kwari.

10 Suka kuma tafi su yaƙi Kan’aniyawan da suke zaune a Hebron wadda a dā ake kira Kiriyat-arba. Suka kashe Sheshai, da Ahiman, da Talmai.

Otniyel ya Ci Birnin Debir ya Auri Aksa

11 Daga can suka tafi su yaƙi Debir wadda a dā ake kira Kiriyat-Sefer.

12 Kalibu ya ce, “Duk wanda ya fāɗa wa Kiriyat-Sefer da yaƙi har ya ci ta, zan ba shi ‘yata Aksa aure.”

13 Sai Otniyel ɗan Kenaz, ƙanen Kalibu ya ci birnin da yaƙi, Kalibu kuwa ya ba shi ‘yarsa Aksa aure.

14 Da ta zo wurinsa, ta iza shi ya roƙi mahaifinta saura. Da ta sauka daga kan jakinta, sai Kalibu ya ce mata, “Me kike so?”

15 Sai ta amsa masa, “Ka yi mini alheri, da yake ka tura ni a ƙasar Negeb, ka ba ni maɓuɓɓugan ruwa.” Kalibu kuwa ya ba ta maɓuɓɓugan tuddai da na kwari.

Yawan Wuraren da Yahuza da Biliyaminu Suka Ci

16 Zuriyar Bakene, surukin Musa kuwa suka fita tare da mutanen Yahuza daga birnin dabino, wato Yariko, suka tafi jejin Yahuda da take a Negeb kudu da Arad. A can suka zauna tare da Amalekawa.

17 Yahuza kuwa da ɗan’uwansa, Saminu, suka tafi suka bugi Kan’aniyawan da suke zaune a Zefat. Suka la’anta birnin, suka hallaka shi, suka sāke wa birnin suna Horma, wato hallakarwa.

18 Yahuza kuma ya ci Gaza da karkararta, da Ashkelon da karkararta, da Ekron da karkararta.

19 Ubangiji kuwa yana tare da Yahuza, ya mallaki ƙasar tuddai, amma bai iya korar waɗanda suke zaune a fili ba, domin suna da karusan ƙarfe.

20 Aka ba Kalibu Hebron kamar yadda Musa ya faɗa. Shi kuwa ya kori ‘ya’yan Anak, maza, su uku, a can.

21 Amma mutanen Biliyaminu ba su kori Yebusiyawan da suke zaune a Urushalima ba domin haka Yebusiyawa suka yi zamansu tare da mutanen Biliyaminu a Urushalima har wa yau.

Kabilar Yusufu ta Ci Betel

22 Jama’ar kabilar Yusufu kuwa suka haura don su yaƙi Betel, Ubangiji kuwa yana tare da su.

23 Suka aika a leƙi asirin Betel wadda a dā ake kira Luz.

24 Sai ‘yan leƙen asirin ƙasar suka ga wani mutum yana fitowa daga cikin birnin, suka ce masa, “Muna roƙonka ka nuna mana hanyar shiga birnin, mu kuwa za mu yi maka alheri.”

25 Ya kuwa nuna musu, suka shiga suka kashe dukan mutanen birnin, amma suka bar mutumin da iyalinsa duka.

26 Sai mutumin ya tafi ƙasar Hittiyawa, ya gina birni, ya sa masa suna Luz, haka ake kiran birnin har wa yau.

Yawan Wuraren da Manassa da Ifraimu suka Ci

27 Kabilar Manassa ba su kori waɗanda suke zaune a Bet-sheyan, da Ta’anak, da Dor, da Ibleyam, da Magiddo, da garuruwan da suke kusa da su ba, amma Kan’aniyawa suka yi kanekane cikin ƙasar.

28 Sa’ad da Isra’ilawa suka yi ƙarfi, suka sa Kan’aniyawa su yi aikin gandu, amma ba su kore su ba.

29 Mutanen Ifraimu kuma ba su kori Kan’aniyawan da suke zaune cikin Gezer ba, amma Kan’aniyawa suka yi zamansu a Gezer tare da su.

Yawan Wuraren da sauran Kabilai Suka Ci

30 Mutanen Zabaluna ma ba su kori mazaunan Kattat da na Nahalal ba, amma Kan’aniyawa suka zauna tare da su, suna yi musu aikin gandu.

31 Haka kuma mutanen Ashiru ba su kori mazaunan Akko, da na Sidon, da Alab, da Akzib, da Helba, da Afek, da Rehob ba.

32 Amma Ashirawa suka yi zamansu tare da Kan’aniyawan ƙasar, gama ba su kore su ba.

33 Mutanen Naftali ma ba su kori mazaunan Bet-shemesh, da na Bet-anat ba, amma suka zauna tare da Kan’aniyawan ƙasar, duk da haka mazaunan Bet-shemesh da na Bet-anat suka zama masu yi musu aikin gandu.

34 Amoriyawa suka matsa wa Danawa, suka angaza su cikin ƙasar tuddai, ba su yarda musu su zauna a filayen ba.

35 Amoriyawa kuwa suka nace su zauna a Heres, da Ayalon, da Shalim. Amma mutanen kabilar Yusufu suka mallake su har suka zama masu yi musu aikin gandu.

36 Iyakar Amoriyawa ta nausa ta kan hawan Akrabbim daga Sela zuwa gaba.

Categories
L. MAH

L. MAH 2

Mala’ikan Ubangiji a Bokim

1 Mala’ikan Ubangiji ya haura daga Gilgal zuwa Bokim. Ya ce wa Isra’ilawa, “Ni na kawo ku daga Masar zuwa ƙasar da na rantse zan ba kakanninku. Na kuma ce, ‘Ba zan ta da madawwamin alkawarina da ku ba.

2 Ku kuma ba za ku yi alkawari da mazaunan ƙasar nan ba, amma za ku rurrushe bagadansu.’ Duk da haka ba ku yi biyayya da maganata ba. Me ke nan kuka yi?

3 Don haka na ce, ‘Ba zan kore muku su ba, amma za su zamar muku ƙaya, gumakansu kuwa za su zamar muku tarko.’ ”

4 Da mala’ikan Ubangiji ya faɗa wa Isra’ilawa wannan magana, suka yi kuka mai zafi.

5 Saboda haka suka sa wa wuri suna Bokim, wato waɗanda suke kuka. Suka kuma miƙa sadakoki ga Ubangiji a wurin.

Rasuwar Joshuwa

6 Da Joshuwa ya sallami Isra’ilawa, kowane mutum ya tafi domin ya ɗauki gādonsa, don ya mallaki tasa ƙasa.

7 Isra’ilawa kuwa suka bauta wa Ubangiji dukan kwanakin Joshuwa, bayan rasuwarsa kuma suka bauta wa Ubangiji dukan kwanakin dattawan da suka ga dukan manyan ayyukan da Ubangiji ya yi domin Isra’ilawa.

8 Bawan Ubangiji, Joshuwa ɗan Nun, ya rasu yana da shekara ɗari da goma.

9 Suka binne shi a Timnat-sera a ƙasar tuddai ta Ifraimu, arewa da dutsen Ga’ash, a ƙasar gādonsa.

10 Dukan tsarar Joshuwa sun rasu, waɗanda suke tasowa kuwa suka manta da Ubangiji da abubuwan da ya yi wa Isra’ila.

Isra’ilawa sun bar Yi wa Ubangiji Sujada

11 Jama’ar Isra’ila kuwa suka yi wa Ubangiji zunubi, wato suka bauta wa gunkin nan mai suna Ba’al.

12 Suka bar yi wa Ubangiji Allah na kakanninsu sujada, wanda ya fisshe su daga ƙasar Masar. Suka fara yi wa allolin mutanen da suke zaune kewaye da su sujada. Suka rusuna wa allolin, da haka suka sa Ubangiji ya yi fushi.

13 Suka bar yi wa Ubangiji sujada suka bauta wa gumakan nan, wato Ba’al da Ashtarot.

14 Ubangiji kuwa ya husata da Isra’ilawa, ya bashe su ga waɗanda za su washe su. Ya sa magabtansu da suke kewaye da su suka sha ƙarfinsu, har ya zama Isra’ilawa ba su iya kāre kansu daga maƙiyansu ba.

15 A duk sa’ad da suka tafi yaƙi sai Ubangiji ya yi gāba da su kamar dai yadda ya faɗa. Saboda haka suka shiga wahala ƙwarai.

16 Sa’an nan Ubangiji ya naɗa musu mahukunta masu ƙarfi da suka cece su daga waɗanda suka washe su.

17 Duk da haka ba su kasa kunne ga mahukuntan ba. Suka yi wa Ubangiji ha’inci, suka yi wa waɗansu alloli sujada. Kakanninsu sun bi umarnin Ubangiji amma wannan tsara nan da nan suka bar yin haka ɗin.

18 Sa’ad da Ubangiji ya naɗa musu mahukunci, yakan taimake shi, ya kuwa cece su daga abokan gāba dukan kwanakin mahukuncin. Gama Ubangiji ya ji ƙansu saboda nishinsu, da zaluncin da ake yi musu.

19 Amma idan mahukuncin ya rasu, sai su sāke kaucewa, su yi zunubi fiye da na kakanninsu. Suna bin gumaka, suna bauta musu, suna kuma yi musu sujada, ba su daina mugayen ayyukansu na rashin aminci da taurin zuciya ba.

20 Ubangiji kuwa ya husata da Isra’ilawa ya ce, “Saboda al’umman nan ta ta da alkawarina wanda na yi da kakanninsu, ba su yi biyayya da maganata ba,

21 don haka daga nan gaba ba zan ƙara kore musu wata al’umma daga cikin al’umman da Joshuwa ya rage kafin rasuwarsa ba.

22 Da haka ne zan jarraba Isra’ilawa, in gani ko za su mai da hankali su yi tafiya cikin hanyata, kamar yadda kakanninsu suka yi, ko kuwa ba za su yi ba.”

23 Don haka Ubangiji ya bar waɗannan al’ummai, bai kore su nan da nan ba, bai kuma ba da su ga Joshuwa ba.

Categories
L. MAH

L. MAH 3

Al’umman da suka Ragu don a Jarraba Isra’ilawa

1 Ubangiji ya bar waɗansu al’ummai a ƙasar domin ya jarraba Isra’ilawan da ba su san yaƙin Kan’ana ba.

2 Ya yi haka ne domin ya koya wa tsararrakin Isra’ila yaƙi, wato waɗanda ba su taɓa yin yaƙi a dā ba.

3 Al’umman da suka ragu a ƙasar su ne, birane biyar na Filistiyawa, da dukan Kan’aniyawa, da Sidoniyawa, da Hiwiyawa da suke zaune a Dutsen Lebanon, tun daga Dutsen Ba’alharmon har zuwa mashigin Hamat,

4 don a jarraba Isra’ilawa da su, a gani ko za su yi biyayya da umarnan Ubangiji da ya ba kakanninsu ta hannun Musa.

5 Saboda haka jama’ar Isra’ila suka zauna tare da Kan’aniyawa, da Hittiyawa, da Amoriyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa.

6 Suka yi aurayya da su, suka kuma yi sujada ga gumakansu.

Otniyel ya Ceci Isra’ilawa

7 Jama’ar Isra’ila kuwa suka manta da Ubangiji Allahnsu, suka yi masa zunubi, suka yi wa gumakan nan Ba’al da Ashtarot sujada.

8 Domin haka Ubangiji ya husata ƙwarai da Isra’ilawa, sai ya bashe su ga Kushan-rishatayim, Sarkin Mesofotamiya. Jama’ar Isra’ila kuwa suka bauta masa shekara takwas.

9 Amma sa’ad da Isra’ilawa suka yi kuka ga Ubangiji, sai Ubangiji ya ta da Otniyel, ɗan Kenaz, ƙanen Kalibu don ya ceci Isra’ilawa.

10 Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko masa domin ya hukunta Isra’ilawa. Ya fita ya yi yaƙi da Kushan-rishatayim, Sarkin Mesofotamiya. Ubangiji kuwa ya ba da sarkin a hannun Otniyel, ya rinjaye shi.

11 Ƙasar ta sami zaman lafiya shekara arba’in sa’an nan Otniyel, ɗan Kenaz ya rasu.

Ehud ya Ceci Isra’ilawa daga Mowabawa

12 Jama’ar Isra’ila kuma suka sāke yin zunubi a gaban Ubangiji, Ubangiji kuwa ya sa Eglon Sarkin Mowab ya yi ƙarfi, domin ya yi gaba da su.

13 Sai ya tattaro Amoriyawa da Amalekawa, ya je ya ci Isra’ilawa, ya mallaki birnin dabino, wato Yariko.

14 Isra’ilawa suka bauta wa Eglon Sarkin Mowab, shekara goma sha takwas.

15 Amma sa’ad da Isra’ilawa suka yi kuka ga Ubangiji, ya ba su wanda zai cece su, wato Ehud, ɗan Gera daga kabilar Biliyaminu, shi kuwa bahago ne. Isra’ilawa suka aika wa Eglon Sarkin Mowab da kyautai ta hannun Ehud.

16 Sai Ehud ya ƙera wa kansa takobi mai kaifi biyu, tsawonsa kamu guda. Ya yi ɗamara da shi wajen cinyarsa ta dama a ƙarƙashin tufafinsa.

17 Sa’an nan ya ɗauki kyautan, ya kai wa Eglon Sarkin Mowab. Eglon kuwa mai ƙiba ne.

18 Da Ehud ya gama ba shi kyautan, sai ya sallami mutanen da suka ɗauko kyautan.

19 Amma Ehud ya juya ya koma daga wajen sassaƙaƙƙun duwatsu kusa da Gilgal, ya ce wa Eglon, “Ranka ya daɗe, na kawo maka saƙo na asiri.”

Sai sarki ya ce wa fādawansa, “Ku ba mu wuri!” Dukansu kuwa suka fita, suka ba da wuri.

20 Ehud kuwa ya je wurinsa, yana zaune shi kaɗai a jinkakken shirayi mai sanyi.

Sai Ehud ya ce, “Ina da saƙo daga wurin Allah zuwa gare ka!” Sarki kuwa ya tashi daga inda yake zaune,

21 Ehud ya sa hannun hagunsa, ya zaro takobin da suke wajen cinyarsa ta dama, ya kirɓa masa a ciki.

22 Takobin ya shiga duk da ƙotar, kitse ya rufe ruwan takobin gama bai zare takobin daga cikin sarkin ba. Ƙazanta kuwa ta fita.

23 Ehud kuwa ya fita ta shirayin, ya kukkulle ƙofofin ɗakin.

24 Bayan da ya tafi, fādawan suka zo, suka ga ƙofofin ɗakin suna a kulle, sai suka zaci sarkin ya zaga ne ya yi bawali.

25 Suka yi ta jira har suka gaji. Da suka ga dai bai buɗe ba, suka ɗauki mabuɗi, suka buɗe, sai ga ubangijinsu a ƙasa matacce.

26 Sa’ad da suke ta jira, Ehud ya riga ya tsere, ya wuce sassaƙaƙƙun duwatsu zuwa Seyira.

27 Da ya isa can sai ya busa ƙaho a ƙasar tudu ta Ifraimu. Jama’ar Isra’ila kuwa suka gangara tare da shi daga ƙasar tudu. Yana kan gaba.

28 Sai ya ce musu, “Ku biyo ni, gama Ubangiji ya ba da Mowabawa maƙiyanku a gare ku.” Suka gangara, suna biye da shi. Suka ƙwace wa Mowabawa mashigan Urdun, suka hana kowa wucewa.

29 A lokacin ne suka kashe ƙarfafan mutane na Mowabawa mutum wajen dubu goma (10,000), ba wanda ya tsira.

30 A ranar nan Isra’ilawa suka rinjayi Mowabawa. Ƙasar kuwa ta sami zaman lafiya har shekara tamanin.

Shamgar ya Ceci Isra’ilawa daga Filistiyawa

31 Bayan Ehud kuma, sai Shamgar ɗan Anat, wanda ya kashe Filistiyawa ɗari shida da tsinken korar shanun noma, shi ma ya ceci Isra’ilawa.

Categories
L. MAH

L. MAH 4

Debora da Barak sun Ci Sisera

1 Bayan rasuwar Ehud, Isra’ilawa suka sāke yin zunubi a gaban Ubangiji.

2 Ubangiji kuwa ya yarda Yabin Sarkin Kan’ana, wanda yake mulkin Hazor ya ci su da yaƙi. Sisera, wanda yake zaune a Haroshet ta al’ummai, shi ne shugaban sojojin Yabin.

3 Sa’an nan jama’ar Isra’ila suka yi kuka ga Ubangiji suna neman taimako, gama Yabin yana da karusai ɗari tara na ƙarfe, ya kuma tsananta wa Isra’ilawa, ya mugunta musu shekara ashirin. Isra’ilawa kuwa suka yi kuka ga Ubangiji domin ya taimake su.

4 Debora, matar Lafidot, ita ce annabiya. Tana hukuncin Isra’ilawa.

5 Ta zauna a gindin giginyar Debora tsakanin Rama da Betel, a ƙasar tudu ta Ifraimu. Isra’ilawa sukan haura zuwa wurinta don ta yi musu shari’a.

6 Sai ta aika a kirawo Barak, ɗan Abinowam, daga birnin Kedesh a ƙasar Naftali. Ta ce masa, “Ubangiji Allah na Isra’ila ya ba ka wannan umarni, ya ce, ‘Ka tafi ka tara mutanenka a Dutsen Tabor, ka kuma ɗauki mutum dubu goma (10,000), daga kabilar Naftali da ta Zabaluna.

7 Ni kuwa zan jawo Sisera, shugaban sojojin Yabin, da karusansa, da ƙungiyoyin sojojinsa ya yi karo da kai a Kogin Kishon, zan kuwa bashe shi a hannunka.’ ”

8 Barak ya ce mata, “Idan za ki tafi tare da ni, zan tafi, amma idan ba za ki tafi tare da ni ba, ni ma ba zan tafi ba.”

9 Sai ta ce masa, “Hakika zan tafi tare da kai, amma darajar wannan tafiya ba za ta zama taka ba, gama Ubangiji zai ba da Sisera a hannun mace.” Debora kuwa ta tashi, ta tafi tare da Barak zuwa Kedesh.

10 Barak kuwa ya kirawo kabilar Zabaluna da ta Naftali zuwa Kedesh. Mutum dubu goma (10,000) suka rufa masa baya, Debora kuwa ta haura tare da shi.

11 Eber, Bakene kuwa, ya ware daga Keniyawa, zuriyar Hobab, surukin Musa, ya kafa alfarwarsa can nesa wajen oak a Za’anannim wanda yake kusa da Kedesh.

12 Aka faɗa wa Sisera cewa, Barak ɗan Abinowam ya haura zuwa Dutsen Tabor.

13 Sai Sisera ya tattaro karusansa na ƙarfe duka guda ɗari tara, da dukan mutanen da suke tare da shi, tun daga Haroshet ta al’ummai, har zuwa Kogin Kishon.

14 Debora ta ce wa Barak, “Tashi! Gama wannan ita ce ranar da Ubangiji ya ba da Sisera a hannunka, gama Ubangiji yana bi da kai!” Sai Barak ya gangaro daga Dutsen Tabor da mutum dubu goma (10,000) biye da shi.

15 Ubangiji kuwa ya sa Barak ya yi kaca-kaca da Sisera, da karusansa duka, da rundunar mayaƙansa duka da takobi. Sisera kuwa ya sauka daga karusarsa, ya gudu da ƙafa.

16 Amma Barak ya runtumi karusan da rundunar har zuwa Haroshet ta al’ummai. Aka kashe dukan rundunar Sisera da takobi, ba wanda ya tsira.

17 Amma Sisera ya gudu da ƙafa zuwa alfarwar Yayel matar Eber, Bakene, gama akwai jituwa tsakanin Yabin Sarkin Hazor da gidan Eber, Bakene.

18 Sai Yayel ta fito, ta taryi Sisera, ta ce masa, “Shigo nan, ubangijina, kada ka ji tsoro.” Ya kuwa bi ta zuwa cikin alfarwa, ta ɓoye shi bayan labule.

19 Ya ce mata, “Ina roƙonki, ki ba ni ruwa kaɗan in sha, gama ina jin ƙishi.” Ta kuwa buɗe salkar madara, ta ba shi ya sha, ta kuma lulluɓe shi.

20 Ya ce mata, “Ki tsaya a ƙofar alfarwar, idan wani ya zo ya tambaye ki, ‘Ko akwai wani a nan?’ Sai ki ce, ‘Babu.’ ”

21 Amma Yayel, matar Eber, ta ɗauki turken alfarwa da guduma, ta yi sanɗa zuwa wurinsa, ta kafa masa turken a gindin kunne, ya zarce har ƙasa, a sa’ad da yake sharar barcin gajiya. Ya kuwa mutu.

22 Barak kuwa yana bin sawun Sisera. Da Yayel ta gan shi, sai ta fita, ta tarye shi, ta ce masa, “Ka zo, zan nuna maka inda mutumin da kake nema yake.” Ya shiga alfarwarta, sai ga Sisera nan kwance matacce da turke a gindin kunnensa.

23 A wannan rana Allah ya fatattaki Yabin Sarkin Kan’ana, a gaban Isra’ilawa.

24 Isra’ilawa suka yi ta tsananta wa Yabin Sarkin Kan’ana har suka hallaka shi.

Categories
L. MAH

L. MAH 5

Waƙar Debora da Barak

1 A wannan rana Debora da Barak, ɗan Abinowam, suka raira wannan waka,

2 Yabo ya tabbata ga Ubangiji!

Isra’ilawa suka ƙudura su yi yaƙi.

Mutane suka sa kansu da farin ciki.

Alhamdu lillahi!

3 Ku kasa kunnenku ya ku sarakuna,

Ku lura, ya ku hakimai,

Zan raira waƙa in yi kaɗe-kaɗe ga Ubangiji,

Allah na Isra’ila.

4 Ya Ubangiji, sa’ad da ka bar duwatsun Seyir,

Sa’ad da ka fito daga jihar Edom,

Ƙasa ta girgiza,

Ruwan sama ya zubo daga sararin sama,

I, gizagizai suka kwararo da ruwa.

5 Duwatsu suka girgiza a gaban Ubangijin Sina’i,

A gaban Ubangiji, Allah na Isra’ila.

6 A zamanin Shamgar ɗan Anat, a zamanin Yayel,

Ayarori suka daina bi ta ƙasar,

Matafiya suka bi ta ƙananan hanyoyi.

7 Garuruwan Isra’ila, ba kowa ciki,

Ba kowa ciki, sai da na zo.

Na zo kamar uwa ga Isra’ila,

8 Sa’ad da Isra’ilawa suka zaɓi baƙin alloli,

Sai ga yaƙi a ƙasar.

Ba a ga garkuwa ko mashi

A wurin mutum dubu arba’in na Isra’ila ba.

9 Zuciyata tana wajen shugabannin yaƙi na Isra’ila,

Da mutanen da suka ba da kansu da farin ciki.

Yabo ya tabbata ga Ubangiji!

10 Ku ba da labari,

Ku da kuke haye da fararen jakuna,

Kuna zaune a shimfiɗu,

Ku da dole ku tafi da ƙafa duk inda za ku.

11 Ku kasa kunne! Da hayaniya mutane a bakin rijiyoyi

Suna ba da labarin nasarar Ubangiji,

Wato nasarar jama’ar Isra’ila!

Sa’an nan jama’ar Ubangiji

Suna tahowa daga biranensu.

12 Ki ja gaba, ke Debora, ki ja gaba!

Ki ja gaba! Ki raira waƙa, ki ja gaba!

Ka ci gaba, kai Barak,

Ɗan Abinowam, ka tasa kamammunka gaba!

13 Sa’an nan amintattu sun zo wurin shugabanninsu,

Jama’ar Ubangiji suka zo wurina a shirye domin yaƙi.

14 Daga Ifrraimu mutane suka gangaro zuwa kwari,

Bayan kabilar Biliyaminu da mutanenta.

Daga Makir shugabannin sojoji suka zo,

Daga Zabaluna kuma jarumawa suka gangaro.

15 Shugabannin Issaka suna tare da Debora,

Hakika, Issaka ya zo, Barak kuma ya zo,

Suka bi bayansu zuwa kwari.

Amma kabilar Ra’ubainu ta rarrabu,

Ba su shawarta su zo ba.

16 Don me suka tsaya daga baya tare da tumaki?

Don su saurari makiyaya na kiran garkuna?

Hakika kabilar Ra’ubainu ta rarrabu,

Ba su shawarta su zo ba.

17 Kabilar Gad suna tsaya a gabashin Urdun,

Kabilar Dan kuma ta tsaya a wuraren kiwo.

Kabilar Ashiru ta zauna a bakin teku,

Sun zauna a gefen teku.

18 Amma mutanen Zabaluna da na Naftali

Suka kasai da ransu a bakin dāga.

19 Sarakuna suka zo, suka yi yaƙi a Ta’anak,

A rafin Magiddo.

Sarakunan Kan’ana suka yi yaƙi,

Amma ba su kwashe azurfa ba.

20 Daga sama, taurari suka yi yaƙi,

Suna gilmawa a sararin sama

Suka yi yaƙi da Sisera.

21 Ambaliyar Kishon ta kwashe su,

Wato tsohon Kogin Kishon.

Zan yi gaba, in yi gaba da ƙarfi!

22 Sa’an nan dawakai sun yi ta rishi

Suna ƙwaƙular ƙasa da kofatansu.

23 Mala’ikan Ubangiji ya ce,

“Ka la’anta Meroz,

Ka la’anta mazauna cikinta sosai,

Gama ba su kawo wa Ubangiji gudunmawa ba,

Su zo su yi yaƙi kamar sojoji dominsa.”

24 Wadda ta fi kowa sa’a daga cikin mata, sai Yayel,

Matar Eber, Bakene,

Wadda ta fi kowa sa’a daga cikin matan da suke a alfarwai.

25 Sisera ya roƙi ruwan sha,

Sai ta ba shi madara,

Ta kawo masa kindirmo a kyakkyawar ƙwarya.

26 Ta ɗauki turken alfarwa a hannunta,

Ta riƙe guduma a guda hannun,

Ta bugi Sisera, kansa ya fashe,

Ta kwankwatse kansa, ya ragargaje.

27 Ya fāɗi a gwiwoyinta,

Ya fāɗi ƙasa, yana kwance shiru a ƙafafunta.

A ƙafafunta ya sunkuya ya fāɗi,

Ya fāɗi matacce har ƙasa.

28 Mahaifiyar Sisera ta duba ta tagogi,

Ta leƙa ta kariyar taga, ta ce,

“Me ya sa karusarsa ta yi jinkirin zuwa?

Don me dawakansa ba su komo da wuri ba?”

29 ‘Yan matanta mafi hikima suka amsa mata,

Ita kuwa ta yi nanatawa, tana cewa,

30 “Nema suke kurum su sami ganima, su raba,

Yarinya ɗaya ko biyu domin kowane soja,

Tufafi masu tsada domin Sisera,

Rinannun tufafi masu ado domin sarauniya.”

31 Ta haka, ya Ubangiji ka sa maƙiyanka su mutu,

Amma abokanka su haskaka kamar fitowar rana!

Ƙasar kuwa ta zauna lafiya shekara arba’in.

Categories
L. MAH

L. MAH 6

Kiran Gidiyon

1 Jama’ar Isra’ila kuma suka sāke yin zunubi a gaban Ubangiji, sai Ubangiji ya ba da su ga Madayanawa su mallake su shekara bakwai.

2 Madayanawa kuwa sun fi Isra’ilawa ƙarfi, saboda haka Isra’ilawa suka yi ta ɓuya a kogon dutse, da waɗansu wuraren ɓuya a tsaunuka.

3 Duk lokacin da Isra’ilawa suka yi shuka, sai Madayanawa, da Amalekawa, da waɗansu kabilai na hamada su zo su fāɗa musu.

4 Sukan zo su kafa musu sansani, su ɓaɓɓata amfanin ƙasar har zuwa kusa da Gaza. Ba su barin wani abinci a ƙasar Isra’ila, domin Isra’ilawa ko dabbobinsu.

5 Gama sukan zo da dabbobinsu da alfarwansu da yawa, kamar fara. Su da raƙumansu ba su ƙidayuwa, sukan zo, su lalatar da ƙasar.

6 Isra’ilawa suka sha ƙasƙanci ƙwarai a hannun Madayanawa. Sai suka yi kuka ga Ubangiji domin ya taimake su.

7 Da Isra’ilawa suka yi kuka ga Ubangiji saboda wahalar da Madayanawa suke ba su,

8 sai Ubangiji ya aika musu da wanda ya faɗa musu saƙon Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya ce, “Ni ne na fito da ku daga bauta a Masar.

9 Na cece ku daga Masarawa, da kuma waɗanda suka yi yaƙi da ku a nan. Na kore su a gabanku, na ba ku ƙasarsu.

10 Na faɗa muku, ‘Ni ne Ubangiji Allahnku, kada ku bauta wa gumakan Amoriyawa, waɗanda kuke zaune a ƙasarsu.’ Amma ba ku yi biyayya da maganata ba.”

11 Mala’ikan Ubangiji ya zo, ya zauna a gindin itacen oak na Yowash mutumin Abiyezer, a ƙauyen Ofra. Ɗansa Gidiyon kuwa yana susukar alkama daga ɓoye, a wurin da ake matse ruwan inabi, don ya ɓuya daga Madayanawa.

12 Mala’ikan Ubangiji kuwa ya bayyana gare shi, ya ce, “Kai jarumi ne, Ubangiji kuma yana tare da kai.”

13 Sai Gidiyon ya ce masa, “Ya shugabana, idan Ubangiji yana tare da mu, me ya sa abubuwan nan suka same mu? Ina kuma ayyukansa masu ban al’ajabi waɗanda kakanninmu suka faɗa mana cewa, ‘Ai, Ubangiji ne ya fisshe mu daga Masar’? Amma yanzu Ubangiji ya yi watsi da mu, ya ba da mu ga Madayanawa.”

14 Ubangiji ya ce masa, “Tafi da dukan ƙarfinka, ka ceci Isra’ilawa daga Madayanawa. Ni kaina na aike ka.”

15 Gidiyon ya amsa ya ce, “Ubangiji, yaya zan yi in ceci Isra’ilawa? Ga shi, dangina ne mafi ƙanƙanta a kabilar Manassa, ni ne kuma ƙarami a gidanmu.”

16 Ubangiji kuwa ya ce masa, “Za ka iya, gama zan taimake ka. Za ka muttsuke Madayanawa kamar mutum guda.”

17 Gidiyon kuwa ya ce masa, “Idan ka amince da ni, ka nuna mini alama don in sani kai kake magana da ni.

18 Ina roƙonka, kada ka tashi daga nan, sai na kawo maka hadaya ta abinci.”

Ya amsa cewa, “Zan tsaya har ka kawo.”

19 Gidiyon ya tafi gida, ya yanka ɗan akuya, ya dafa, ya yi waina marar yisti ta gāri mudu guda. Ya sa naman a kwandon, romon kuwa ya zuba a tukunya, ya kawo, ya miƙa masa a gindin itacen oak.

20 Mala’ikan Allah kuma ya ce masa, “Ɗauki naman da wainar marar yisti ka sa a kan dutsen nan, sa’an nan ka zuba romon a kai.” Haka kuwa ya yi.

21 Mala’ikan Ubangiji kuwa ya miƙa kan sandan da yake hannunsa, ya taɓa naman da wainar, sai wuta ta fito daga dutsen ta cinye naman da wainar. Mala’ikan Ubangiji kuwa ya ɓace masa.

22 Da Gidiyon ya gane mala’ikan Ubangiji ne, sai ya ce, “Kaitona, Ubangiji Allah, gama na ga mala’ikan Ubangiji fuska da fuska.”

23 Amma Ubangiji ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, ba za ka mutu ba.”

24 Gidiyon kuwa ya gina wa Ubangiji bagade a wurin, ya sa masa suna, Ubangiji Salama Ne. Har wa yau bagaden yana nan a Ofra, ta iyalin Abiyezer.

25 A wannan dare Ubangiji ya ce masa, “Ka ɗauki bijimin mahaifinka, da wani bijimin bana bakwai. Sa’an nan ka rushe bagaden gunkin nan Ba’al na mahaifinka, ka sare gumakan da suke kusa da shi.

26 Sa’an nan ka gina wa Ubangiji Allahnka bagade mai kyau a kan wannan kagara. Ka ɗauki bijimi na biyu ka miƙa shi hadayar ƙonawa da itacen gumakan da za ka sare.”

27 Gidiyon fa ya ɗauki mutum goma daga cikin barorinsa, ya yi yadda Ubangiji ya faɗa masa. Amma domin yana tsoron, mutanen gidansa da na gari, bai yi wannan da rana ba, sai da dare.

28 Da mutanen garin suka tashi da safe, sai ga bagaden Ba’al a farfashe, gumakan kuma da suke kusa da shi, an sare. Bijimi na biyu kuma, an miƙa shi hadaya a kan bagaden da aka gina.

29 Suka ce wa juna, “Wa ya yi wannan abu?” Da suka binbincika, sai suka tarar Gidiyon ne, ɗan Yowash, ya yi shi.

30 Sai suka ce wa Yowash, “Ka kawo ɗanka a kashe, gama ya rushe bagaden gunkin nan Ba’al, ya kuma sare gumakan da suke kusa da shi.”

31 Yowash kuwa ya ce wa dukan waɗanda suka tasar masa, “Za ku yi hamayya domin gunkin nan Ba’al, ko kuwa za ku goyi bayansa? Duk wanda ya yi hamayya dominsa za a kashe shi da safe. Idan shi allah ne, to, bari ya yi hamayya don kansa, gama an farfashe bagadensa.”

32 A ranar nan aka laƙaba wa Gidiyon suna Yerubba’al, wato “Bari gunki Ba’al ya yi hamayya don kansa, domin an farfashe bagadensa.”

33 Dukan Madayanawa kuwa, da Amalekawa, da mutanen gabas suka tattaru. Suka haye, suke kafa sansaninsu a kwarin Yezreyel.

34 Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko a kan Gidiyon, sai ya busa ƙaho, mutanen Abiyezer suka bi shi.

35 Ya kuma aiki manzanni a ƙasar Manassa duka. Su kuma aka kirawo su su bi shi. Ya kuma aiki manzanni zuwa ga Ashirawa da Zabalunawa, da Naftaliyawa, su kuma suka zo, suka haɗa kai da shi.

36 Sa’an nan Gidiyon ya ce wa Allah, “Ka ce za ka sa ni in ceci Isra’ilawa.

37 To, zan shimfiɗa ulu a masussuka. Idan da safe akwai raɓa a kan ulun kaɗai, ƙasa kuwa a bushe, sa’an nan zan sani za ka ceci Isra’ilawa ta hannuna kamar yadda ka faɗa.”

38 Haka kuwa ya zama Kashegari Gidiyon ya tashi da sassafe, sai ya matse ulun, ruwan raɓa da ya matse daga ulun kuwa, ya cika ƙwarya.

39 Gidiyon kuma ya ce wa Allah, “Ina roƙonka, kada ka yi fushi da ni, bari in ƙara magana sau ɗaya kurum, wato in sāke yin gwaji da ulun. Ina roƙonka ka sa a yi raɓa a ƙasa, amma kada ta taɓa ulun.”

40 Haka kuwa Allah ya yi a daren. Aka yi raɓa a ƙasa, amma ulun yana a bushe.

Categories
L. MAH

L. MAH 7

Gidiyon ya Ci Madayanawa

1 Sai Yerubba’al, wato Gidiyon, da mutanen da suke tare da shi suka yi sammako, suka kafa sansaninsu kusa da maɓuɓɓugan Harod. Madayanawa kuwa suka kafa sansaninsu a arewa da su, kusa da tudun More a kwarin.

2 Ubangiji kuwa ya ce wa Gidiyon, “Mutanen da suke tare da kai sun yi yawa da zan ba da Madayanawa a hannunsu, kada ya zama Isra’ilawa su yi mini fāriya, su ce, ‘Ƙarfinmu ne ya cece mu.’

3 Yanzu sai ka ce wa mutanen, ‘Duk mai jin tsoro da mai rawar jiki, ya koma gida!’ ” Da Gidiyon ya gwada su, mutum dubu ashirin da biyu (22,000) suka koma, dubu goma (10,000) suka tsaya.

4 Ubangiji ya ce wa Gidiyon, “Har yanzu mutanen sun yi yawa. Ka kai su bakin rafi domin in jarraba maka su a can. Wanda na faɗa maka shi zai tafi tare da kai, to, shi ne zai tafi, wanda kuma na faɗa ba zai tafi tare da kai ba, to, ba zai tafi ba.”

5 Gidiyon ya kai mutanen bakin rafi, Ubangiji kuwa ya ce wa Gidiyon, “Duk wanda ya tanɗi ruwa kamar kare, sai ka ware shi waje ɗaya. Wanda kuma ya durƙusa ya sha ruwa, ka ware shi waje ɗaya.”

6 Yawan waɗanda suka tanɗi ruwa su ɗari uku ne. Sauran mutane duka kuwa sun durƙusa ne suka sha ruwan.

7 Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Gidiyon, “Da mutum ɗari uku ɗin nan da suka tanɗi ruwa zan cece ku. Zan ba da Madayanawa a gare ku, ka sallami sauran, kowa ya koma gidansa.”

8 Mutane suka ɗauki guzuri da ƙahoni, Gidiyon kuwa ya sallami sauran mutane, amma ya bar mutum ɗari uku ɗin nan. Sansanin Madayanawa kuwa yana ƙasa da su a kwarin.

9 A wannan dare sai Ubangiji ya ce masa, “Tashi, ka tafi sansanin Madayanawa, gama na ba da su gare ka.

10 Amma idan kana jin tsoro ka tafi kai kaɗai, ka tafi tare da Fura, baranka.

11 Za ka ji abin da suke cewa. Bayan haka za ka sami ƙarfin hali da za ka tafi ka fāda wa sansaninsu.” Gidiyon kuwa ya tafi tare da Fura baransa a gefen sansanin abokan gāba.

12 Madayanawa, da Amalekawa, da mutanen gabas duka suna nan da yawa a shimfiɗe cikin kwarin, kamar fara. Raƙumansu kuma suna da yawa kamar yashi a bakin teku. Ba wanda zai iya ƙidaya su.

13 Sa’ad da Gidiyon ya tafi, sai ya ji wani yana faɗa wa abokinsa mafarkin da ya yi. Ya ce, “Na yi mafarki, na ga wainar sha’ir ta faɗo a tsakiyar sansaninmu. Ta zo ta bugi alfarwa. Alfarwar kuwa ta fāɗi rigingine.”

14 Abokinsa ya amsa, ya ce, “Ai, ba wani abu ba ne. Wannan takobin Gidiyon ne, ɗan Yowash. Ba’isra’ile! Allah ya ba shi nasara kan Madayanawa da dukan rundunanmu!”

15 Da Gidiyon ya ji mafarkin, har da fassarar, sai ya yi sujada, ya koma a sansaninsu na Isra’ilawa. Da ya isa, sai ya ce, “Ku tashi, gama Ubangiji ya ba da rundunar Madayanawa a gare ku.”

16 Sai ya raba mutum ɗari uku ɗin kashi uku, ya ba kowannensu ƙaho, da tulu, da jiniya a cikin tulun.

17 Sa’an nan ya ce musu, “Sa’ad da muka kai sansani, sai ku dube ni, ku yi duk abin da nake yi. Yadda na yi, ku ma ku yi haka.

18 Sa’ad da ni da dukan waɗanda suke tare da ni muka busa ƙahoni, sai ku kuma ku busa ƙahonin a kowane gefen sansani, sa’an nan ku yi ihu, ku ce, ‘Ubangiji da Gidiyon!’ ”

19 Gidiyon da mutum ɗari da suke tare da shi, suka kai gefen sansanin wajen tsakiyar dare, bayan an sauya matsara. Sai suka busa ƙahonin, suka fasa tulunan da suke a hannuwansu.

20 Ƙungiyoyi uku ɗin nan suka busa ƙahonin, suka fasa tuluna. Suka riƙe jiniyoyi a cikin hannuwansu na hagu, da ƙahonin busawa a hannuwansu na dama. Sai suka yi kuwa, suka ce, “Takobin Ubangiji da na Gidiyon!”

21 Kowannensu ya yi tsaye a inda yake kewaye da sansanin. Dukan rundunar Madayanawa kuwa suka gudu, suna ihu.

22 Da suka busa ƙahonin nan ɗari uku, sai Ubangiji ya sa Madayanawa suka yi ta sassare junansu da takuba. Suka gudu zuwa Zerera har Bet-shitta, har kuma zuwa garin Abel-mehola, kusa da Tabbat.

23 Jama’ar kabilar Naftali, da Ashiru, da Manassa, suka ji kira, suka fito, suka runtumi Madayanawa.

24 Gidiyon kuma ya aika a dukan ƙasar tudu ta Ifraimu, ya ce musu, “Ku gangaro, ku yaƙi Madayanawa, ku tare mashigan Kogin Urdun da rafuffuka, har zuwa Bet-bara.” Aka kuwa kira dukan Ifraimawa, su kuwa suka hana wa Madayanawa mashigan Kogin Urdun da rafuffuka, har zuwa Bet-bara.

25 Suka kama sarakunan Madayanawa biyu, Oreb da Ziyib. Suka kashe Oreb a kan dutsen Oreb, Ziyib kuwa suka kashe shi a wurin matsewar ruwan inabi na Ziyib a lokacin da suke runtumar Madayanawa. Sai suka kawo wa Gidiyon kan Oreb da na Ziyib a inda yake a gabashin Urdun.

Categories
L. MAH

L. MAH 8

1 Mutanen Ifraimu suka ce wa Gidiyon, “Me ke nan ka yi mana, da ba ka kirawo mu lokacin da ka tafi yaƙi da Madayanawa ba?” Suka yi masa gunaguni ƙwarai.

2 Amma ya ce musu, “Yanzu, me na yi fiye da ku? Ai, kalar inabin Ifraimu ta fi dukan girbin Abiyezer, wato ɗan abin da kuka yi ya fi wanda kabilata ta yi nesa.

3 Ga shi, Allah ya ba da Oreb da Ziyib sarakunan Madayanawa a gare ku. To, me na yi wanda ya fi naku?” Da ya faɗi haka, sai suka huce.

Nasara ta Ƙarshe a kan Madayanawa

4 Da Gidiyon ya zo Urdun sai ya haye tare da mutum ɗari uku ɗin nan da suke tare da shi. Ko da yake sun gaji, duk da haka suka yi ta runtumar magabta.

5 Gidiyon ya ce wa mutanen Sukkot, “Ina roƙonku, ku ba mutanen da suke tare da ni abinci, gama sun gaji, ga shi kuwa, ina runtumar Zeba da Zalmunna, sarakunan Madayanawa.”

6 Shugabannin Sukkot kuwa suka ce, “Ba ka riga ka kama Zeba da Zalmunna ba, ta yaya za mu ba sojojinka abinci?”

7 Gidiyon ya ce, “To, sa’ad da Ubangiji ya ba da Zeba da Zalmunna a hannuna, zan tsattsaga jikinku da ƙayayuwan jeji.”

8 Daga can ya tafi Feniyel, ya roƙe su yadda ya roƙi mutanen Sukkot. Mutanen Feniyel kuma suka amsa masa daidai yadda mutanen Sukkot suka amsa masa.

9 Sai Gidiyon ya ce wa mutanen Feniyel, “Sa’ad da na dawo cikin salama, zan rushe wannan hasumiya.”

10 Zeba da Zalmunna kuwa suna Karkor tare da rundunarsu, mutum wajen dubu goma sha biyar (15,000), waɗanda suka ragu daga cikin rundunar mutanen gabas, gama an kashe mutum dubu ɗari da dubu ashirin (120,000), masu takuba.

11 Gidiyon kuwa ya bi ta hanyar gefen hamada wadda take gabas da Noba da Yogbeha, ya faɗa wa rundunar, ta yadda ba su zato.

12 Zeba da Zalmunna, sarakunan nan biyu na Madayana suka gudu, amma ya bi su, ya kamo su. Ya sa dukan rundunarsu ta gigice.

13 Sa’an nan Gidiyon, ɗan Yowash, ya komo daga yaƙin ta hanyar hawan Heres.

14 Gidiyon ya kama wani saurayi na Sukkot, ya yi masa tambayoyi. Shi kuwa ya rubuta masa sunayen sarakuna da na dattawan Sukkot, mutum saba’in da bakwai.

15 Sa’an nan ya zo wurin mutanen Sukkot ya ce musu, “To, ga Zeba da Zalmunna waɗanda kuka yi mini ba’a saboda su, kuna cewa, ‘Ba ka riga ka kama Zeba da Zalmunna ba, ta yaya za mu ba sojojinka da suka gaji abinci?’ To, ga su!”

16 Ya kama dattawan garin Sukkot ya hukunta su da ƙayayuwa.

17 Ya kuma rushe hasumiyar Feniyel, ya karkashe mutanen birnin.

18 Sa’an nan ya ce wa Zeba da Zalmunna, “Waɗanne irin mutane ne kuka kashe a Tabor?”

Suka amsa, “Kamar yadda kake, haka suke. Suna kama da ‘ya’yan sarki.”

19 Gidiyon ya ce musu, “Su ‘yan’uwana ne, mahaifiyarmu ɗaya. Da ba ku kashe su ba, da ba zan kashe ku ba.”

20 Ya ce wa Yeter, ɗan farinsa, “Tashi, ka kashe su.” Amma saurayin bai zare takobinsa ba, gama yana jin tsoro domin shi yaro ne.

21 Sai Zeba da Zalmunna suka ce, “Tashi da kanka, ka kashe mu, gama yadda mutum yake haka kuma ƙarfinsa yake.” Gidiyon kuwa ya tashi ya kashe Zeba da Zalmunna. Ya kwance kayan ado daga wuyan raƙumansu.

Sauran Ayyukan Gidiyon

22 Sa’an nan mutanen Isra’ila suka ce wa Gidiyon, “Ka yi mulkinmu, kai da ‘ya’yanka, da jikokinka, gama ka cece mu daga hannun Madayanawa.”

23 Gidiyon ya ce musu, “Ba zan yi mulkinku ba, ɗana kuma ba zai yi mulkinku ba, Ubangiji ne zai yi mulkinku.”

24 Ya ci gaba ya ce, “Ina roƙon kowannenku ya ba ni ‘yan kunne daga cikin ganimar da ya kwaso.” (Gama Madayanawa suna da ‘yan kunne na zinariya, gama su mutanen hamada ne.)

25 Suka ce, “Lalle, za mu ba ka su.” Nan da nan suka shimfiɗa mayafi, kowa ya zuba ‘yan kunnen da ya kwaso ganima.

26 Nauyin ‘yan kunnen zinariya da ya roƙa ya kai shekel dubu ɗaya da ɗari bakwai (1,700), banda kayan ado, da na rataye-rataye, da tufafin shunayya waɗanda sarakunan Madayanawa suke sawa, banda ɗan gaba da yake a wuyan raƙumansu.

27 Gidiyon kuwa ya yi gunki da zinariyar, ya ajiye a birninsa, wato Ofra. Isra’ilawa kuma suka bar bin Allah, suka tafi can domin su yi wa gunkin sujada, ya zama tarko ga Gidiyon da iyalinsa.

28 Da haka Isra’ilawa suka mallaki Madayanawa har ba su zamar musu barazana ba. Ƙasar kuwa ta zauna lafiya shekara arba’in a zamanin Gidiyon.

Mutuwar Gidiyon

29 Gidiyon kuwa ya tafi ya zauna a gidansa na kansa.

30 Yana kuma da ‘ya’ya maza saba’in, gama yana da mata da yawa.

31 Yana kuma da ƙwarƙwara wadda take a Shekem, ta haifi masa ɗa, ya sa masa suna Abimelek.

32 Sa’an nan Gidiyon, ɗan Yowash, ya rasu da kyakkyawan tsufa. Aka binne shi a kabarin Yowash mahaifinsa, a Ofra, birnin kabilar Abiyezer.

33 Bayan rasuwar Gidiyon, sai Isra’ilawa suka sāke yin rashin aminci ga Allah, suka yi wa Ba’al sujada. Suka yi Ba’al-berit ya zama allahnsu.

34 Suka daina bauta wa Ubangiji Allahnsu, wanda ya cece su daga magabtan da suke kewaye da su.

35 Ba su kuwa sāka wa iyalin Gidiyon da alheri ba, saboda dukan alherin da ya yi wa Isra’ilawa.

Categories
L. MAH

L. MAH 9

Sarautar Abimelek

1 Abimelek, ɗan Yerubba’al, wato Gidiyon, ya tafi Shekem wurin dukan dangin mahaifiyarsa, ya ce musu,

2 “Ina roƙonku, ku yi magana da shugabannin Shekem, ku ce, ‘Me ya fi muku kyau, ‘ya’yan Yerubba’al, maza saba’in su yi mulkinku, ko kuwa mutum ɗaya ya yi mulkinku?’ Amma ku tuna fa ni jininku ne.”

3 Sai dangin mahaifiyarsa suka yi magana da shugabannin Shekem saboda shi. Zuciyarsu kuwa ta saje da Abimelek, gama suka ce, “Shi ɗan’uwanmu ne.”

4 Suka kuma ba shi azurfa saba’in daga cikin gidan gunkin nan Ba’al-berit. Da wannan azurfa Abimelek ya yi ijarar ‘yan iska waɗanda suka bi shi.

5 Ya tafi gidan mahaifinsa a Ofra, ya kashe ‘yan’uwansa maza, wato ‘ya’yan Yerubba’al, mutum saba’in a kan dutse guda. Amma Yotam ƙaramin ɗan Yerubba’al, shi kaɗai ya ragu domin ya ɓuya.

6 Sai shugabannin Shekem duka da na Betmillo suka taru suka naɗa Abimelek sarki kusa da itacen oak na al’amudin da yake a Shekem.

7 Da Yotam ya ji wannan sai ya tafi, ya tsaya a kan Dutsen Gerizim, da babbar murya, ya ce musu, “Ku kasa kunne gare ni ku mutanen Shekem, domin kuma Allah ya kasa kunne gare ku!

8 Wata rana itatuwa suka taru don su naɗa wa kansu sarki. Suka ce wa itacen zaitun, ‘Kai ka zama sarkinmu.’

9 Amma itacen zaitun ya ce musu, ‘In bar maina wanda da shi ake girmama alloli da mutane, don in tafi in yi ta fama da itatuwa?’

10 Sai kuma itatuwa suka ce wa itacen ɓaure, ‘Ka zo, ka zama sarkinmu.’

11 Amma itacen ɓaure ya ce musu, ‘In bar kyawawan ‘ya’yana masu zaƙi, don in tafi in yi ta fama da itatuwa?’

12 Itatuwa kuma suka ce wa kurangar inabi, ‘Ki zo, ki mallake mu.’

13 Sai kurangar inabi ta ce, ‘In bar ruwan inabina wanda yake faranta zuciyar allolin da ta mutane, don in tafi, in yi ta fama da itatuwa?’

14 Sa’an nan dukan itatuwa suka ce wa itacen ƙaya, ‘Ka zo, ka zama sarkinmu.’

15 Itacen ƙaya kuwa ya ce wa itatuwan, ‘In da gaske kuke, kuna so ku naɗa ni sarkinku, to, sai ku zo, ku fake a inuwata, in ba haka ba kuwa, bari wuta ta fito daga itacen ƙaya ta cinye itacen al’ul na Lebanon.’ ”

16 Yotam ya ci gaba da cewa, “Yanzu kun naɗa Abimelek sarki da zuciya ɗaya ke nan? Kun yi wa Yerubba’al da iyalinsa daidai ke nan? Wannan ne abin da ya cancance shi?

17 Ku tuna fa mahaifina ya yi yaƙi dominku. Ya kasai da ransa domin ya cece ku daga Madayanawa.

18 Amma ga shi, yau kun juya kuna gāba da gidan mahaifina. Kun kashe ‘ya’yansa maza, su saba’in, a dutse guda, kuka naɗa Abimelek, ɗan da baiwa ta haifa, ya zama sarki a Shekem, don dai kawai shi ɗan’uwanku ne.

19 Yanzu dai idan abin da kuka yi wa Yerubba’al da iyalinsa daidai ne, to, sai ku yi farin ciki da Abimelek, ku sa shi kuma ya ji daɗinku.

20 Amma idan ba haka yake ba, Allah ya sa wuta ta fito daga wurin Abimelek ta cinye mutanen Shekem da na Bet-millo. Bari Allah ya sa kuma wuta ta fito daga wurin mutanen Shekem da na Bet-millo ta cinye Abimelek.”

21 Sa’an nan Yotam ya tsere. Ya tafi ya zauna a Biyer, gama yana tsoron ɗan’uwansa Abimelek.

22 Abimelek kuwa ya yi shekara uku, yana mulkin Isra’ila.

23 Ubangiji kuma ya sa husuma ta tashi tsakanin Abimelek da mutanen Shekem. Shugabannin Shekem kuwa suka tayar masa.

24 Wannan ya faru domin a ɗauki fansar jinin, ‘ya’yan Yerubba’al, maza, su saba’in, a kan Abimelek ɗan’uwansu, wanda ya kashe su, da kuma a kan shugabannin Shekem, waɗanda suka taimake shi ya kashe ‘yan’uwansa.

25 Shugabannin Shekem kuwa suka sa mutane su yi kwanto a kan dutwatsu gāba da Abimelek. Suka yi wa duk wanda ya bi ta wannan hanya fashi. Sai aka faɗa wa Abimelek.

26 Ga’al, ɗan Ebed, da ‘yan’uwansa suka yi ƙaura zuwa Shekem. Shugabannin Shekem kuwa suka amince da shi.

27 Suka tafi gona, suka ɗebo inabi, suka matse, suka yi biki a gidan gunkinsu. Suka ci, suka sha, suka zazzagi Abimelek.

28 Ga’al, ɗan Ebed, ya ce, “Wane ne Abimelek har mu mutanen Shekem za mu bauta masa? Ashe, ba Yerubba’al ne mahaifinsa ba, Zebul kuma shugaban yaƙinsa? Don me za mu bauta masa? Ku yi aminci ga kakanku Hamor, tushen kabilarku!

29 Da ma a ce nake shugabancin mutanen nan, da sai in hamɓare Abimelek!” Sai ya ce wa Abimelek, “Ka tara yawan rundunarka ka fito.”

30 Zebul, shugaban birnin ya ji maganganun Ga’al, ɗan Ebed, sai ya husata.

31 Ya aiki jakadu wurin Abimelek a Aruma, ya ce, “Ga fa Ga’al, ɗan Ebed, da ‘yan’uwansa sun zo Shekem, suna kutta garin ya tayar maka.

32 Yanzu sai ka tashi, ka zo da dare tare da mutanen da suke tare da kai, ku yi kwanto a cikin saura.

33 Sa’an nan gobe da safe, da fitowar rana, ku tashi ku fāɗa wa birnin. Idan Ga’al da mutanen da suke tare da shi, suka fito, su kara da kai, ka fatattake su yadda ka iya!”

34 Abimelek da mutanen da suke tare da shi kuwa suka tashi da dare suke yi wa Shekem kwanto da ƙungiya huɗu.

35 Ga’al, ɗan Ebed, kuwa ya fita zuwa ƙofar garin daidai lokacin da Abimelek da mutanensa suka tashi daga wurin kwantonsu.

36 Sa’ad da Ga’al ya ga mutanen, ya ce wa Zebul, “Duba, ga mutane suna zuwa daga kan duwatsu.”

Sai Zebul ya ce masa, “Ai, inuwar duwatsu ce kake gani kamar mutane.”

37 Ga’al kuma ya ƙara yin magana, ya ce, “Duba, mutane suna gangarowa kan hanya, ga kuma wata ƙungiya tana zuwa daga wajen itacen oak na masu duba.”

38 Sa’an nan Zebul ya ce masa, “Ina cika bakin nan naka, kai da ka ce, ‘Wane ne Abimelek da za mu bauta masa?’ Waɗannan su ne mutanen da ka raina. Fita, ka yaƙe su mana.”

39 Ga’al kuwa ya fita ya yi jagorar shugabannin Shekem, suka yi yaƙi da Abimelek.

40 Abimelek kuwa ya runtumi Ga’al, shi kuwa ya gudu. Mutane da yawa suka ji rauni, ya bi su har bakin ƙofar birnin.

41 Sai Abimelek ya zauna a Aruma. Zebul kuwa ya kori Ga’al da ‘yan’uwansa, ya hana su zama a Shekem.

42 Kashegari mutanen Shekem suka tafi saura, sai aka faɗa wa Abimelek.

43 Shi ma ya kwashi mutanensa, ya raba su ƙungiya uku, suka yi kwanto a saura. Da ya duba, ya ga mutane suna fitowa daga cikin birnin. Ya fāɗa musu, ya karkashe su.

44 Abimelek kuma da ƙungiyar da take tare da shi, suka hanzarta, suka tsare ƙofar birnin. Sauran ƙungiya biyu suka ruga, suka faɗa wa dukan waɗanda suke cikin saura, suka karkashe su.

45 Abimelek ya yi yaƙi dukan yini har ya ci birnin, ya kashe mutanen da suke cikinsa. Ya rushe birnin, ya barbaɗe shi da gishiri.

46 Da shugabannin hasumiyar Shekem suka ji labari, suka gudu zuwa hasumiyar gidan Ba’al-berit don su tsira.

47 Abimelek kuwa ya ji dukan mutanen hasumiyar Shekem sun taru wuri ɗaya.

48 Sai ya tafi da mutanen da suke tare da shi suka hau Dutsen Zalmon. Ya ɗauki gatari ya sari reshen itace, ya saɓe a kafaɗa. Ya ce wa mutanen da suke tare da shi, su yi hanzari su yi kamar yadda ya yi.

49 Kowane mutum kuwa ya sari reshen itace, ya bi Abimelek. Suka tara rassan a jikin hasumiyar. Suka sa wa hasumiyar wuta, duk da mutanen da suke cikinta. Ta haka dukan mutanen hasumiyar Shekem suka mutu, mata da maza, wajen mutum dubu.

50 Sa’an nan Abimelek ya tafi Tebez, ya kewaye ta da sansani, ya ci birnin.

51 Akwai wata hasumiya mai ƙarfi a cikin birnin, sai dukan mutanen garin, mata da maza, har da shugabannin, suka gudu zuwa cikinta, suka kulle kansu, suka hau kan rufin hasumiyar.

52 Abimelek kuwa ya zo ya yaƙi hasumiyar. Ya je kusa da ƙofar hasumiyar don ya ƙone ta.

53 Amma wata mace ta jefi Abimelek da ɗan dutsen niƙa a kā, ƙoƙon kansa ya ragargaje.

54 Nan da nan sai Abimelek ya kira saurayin da yake ɗaukar masa makamai, ya ce masa, “Ka zaro takobinka, ka kashe ni domin kada mutane su ce, ‘Mace ta kashe shi.’ ” Sai saurayin ya soki Abimelek, ya mutu.

55 Da Isra’ilawa suka ga Abimelek ya mutu, sai dukansu suka tafi gida.

56 Ta haka Allah ya saƙa wa Abimelek muguntar da ya yi wa mahaifinsa, da ya kashe ‘yan’uwansa maza, su saba’in.

57 Haka kuwa Allah ya sa muguntar mutanen Shekem ta koma kansu. Bakin Yotam, ɗan Yerubba’al, kuma ya kama su.

Categories
L. MAH

L. MAH 10

Tola da Yayir Sun Shugabanci Isra’ilawa

1 Bayan mutuwar Abimelek, sai Tola, ɗan Fuwa, ɗan Dodo, daga kabilar Issaka ya tashi don ya ceci Isra’ilawa. Ya zauna a Shamir, a ƙasar tuddai ta Ifraimu.

2 Ya shugabanci Isra’ilawa shekara ashirin da uku, sa’an nan ya rasu. Aka binne shi a Shamir.

3 Bayansa kuma sai Yayir mutumin Gileyad, ya tashi ya shugabanci Isra’ilawa shekara ashirin da biyu.

4 Yana da ‘ya’ya maza guda talatin, waɗanda suke hawan jakai talatin. Suna kuma da birane talatin a ƙasar Gileyad, waɗanda har yanzu ake kira biranen alfarwai. Ana kiran biranen Hawwot-Yayir, wato na Yayir.

5 Yayir ya rasu aka binne shi a Kamon.

Ammonawa Sun Matsa wa Isra’ilawa

6 Isra’ilawa suka sāke yi wa Ubangiji zunubi. Suka yi sujada ga Ba’al da Ashtarot, allolin Suriyawa, da na Sidon, da na Mowab, da na Ammonawa, da na Filistiyawa. Suka bar bin Ubangiji, suka daina yi masa sujada.

7 Ubangiji kuwa ya husata da Isra’ilawa, ya ba da su ga Filistiyawa, da Ammonawa.

8 Suka murƙushe Isra’ilawa, suka matsa musu. Har shekara goma sha takwas suka yi ta matsa dukan Isra’ilawan da suke a hayin Urdun daga gabas, a cikin Gileyad, inda Amoriyawa suke zaune.

9 Ammonawa kuma suka haye Urdun don su yaƙi mutanen Yahuza, da na Biliyaminu, da na kabilar Ifraimu. Isra’ilawa kuwa suka matsu ƙwarai.

10 Sa’an nan Isra’ilawa suka yi kuka ga Ubangiji, suna cewa, “Mun yi maka zunubi, gama mun bar binka, ya Allahnmu, muka yi wa Ba’al sujada.”

11 Ubangiji ya amsa musu, ya ce, “Ban cece ku daga hannun Masarawa, da Amoriyawa, da Ammonawa, da Filistiyawa,

12 da Sidoniyawa, da Amalekawa, da Mawonawa ba, wato su da suka matsa muku a dā, ku kuma kuka yi kuka gare ni?

13 Amma duk da haka kuka bar bina, kuka yi sujada ga waɗansu alloli, don haka ni kuma ba zan ƙara cetonku ba.

14 Tafi, ku yi wa allolin da kuka zaɓa kuka, don su cece ku a lokacin wahalarku.”

15 Amma Isra’ilawa suka ce wa Ubangiji, “Mun yi zunubi, ka yi mana duk irin abin da ka ga dama, amma in ka yarda ka cece mu yau.”

16 Sa’an nan suka zubar da gumakan da suke wurinsu, suka yi wa Ubangiji sujada. Shi kuwa ya damu saboda azabar da Isra’ilawa suke sha.

17 Sojojin Ammonawa kuwa, suka tattaru, suka kafa sansani a Gileyad. Isra’ilawa kuma suka tattaru, suka kafa nasu sansani a Mizfa.

18 Shugabanni da mutanen Gileyad suka ce wa junansu. “Wa zai fara yaƙi da Ammonawa? Shi zai zama shugaban duk wanda yake Gileyad.”