Categories
L. MAH

L. MAH 11

Yefta ya Ceci Isra’ilawa daga Hannun Ammonawa

1 Yefta mutumin Gileyad ne, shi kuwa jarumi ne, amma mahaifiyarsa karuwa ce. Gileyad ne mahaifinsa.

2 Matar Gileyad ta haifa masa ‘ya’ya maza. Sa’ad da suka yi girma, sai suka kori Yefta, suka ce masa, “Ba za ka ci gādo a gidan mahaifinmu ba, gama kai ɗan wata mace ne.”

3 Sai Yefta ya gudu daga wurin ‘yan’uwansa, ya zauna a ƙasar Tob. ‘Yan iska kuwa suka taru wurin Yefta, sukan tafi yawo tare da shi.

4 Ana nan sai Ammonawa suka kai wa Isra’ilawa yaƙi.

5 Da haka ta auku, sai shugabannin Gileyad suka tafi su komo da Yefta daga ƙasar Tob.

6 Suka ce wa Yefta, “Ka zo, ka zama shugabanmu don mu yi yaƙi da Ammonawa.”

7 Amma Yefta ya ce wa dattawan Gileyad, “Ba ku kuka ƙi ni, kuka kore ni daga gidan mahaifina ba? Me ya sa kuka zo wurina a lokacina da kuke shan wahala?”

8 Sai dattawan Gileyad suka amsa masa, “Abin da ya sa muka zo wurinka yanzu, shi ne domin ka tafi tare da mu ne mu yi yaƙi da Ammonawa, ka kuma zama shugaban dukan jama’ar Gileyad.”

9 Yefta kuwa ya ce musu, “Idan kuka koma da ni gida domin in yi yaƙi da Ammonawa, idan Ubangiji ya ba da su a hannuna, to, zan zama shugabanku.”

10 Suka amsa suka ce wa Yefta, “Ubangiji shi ne shaida tsakaninmu, lalle za mu yi maka kamar yadda ka ce.”

11 Yefta kuwa ya tafi tare da dattawa Gileyad. Su kuwa suka naɗa shi shugabansu da sarkin yaƙinsu. Yefta kuwa ya faɗi dukan abin da yake zuciyarsa a gaban Ubangiji a Mizfa.

12 Yefta kuwa ya aiki jakadu wurin Sarkin Ammonawa da cewa, “Me ya haɗa ka da ni, da ka zo ƙasata da yaƙi?”

13 Sarkin Ammonawa ya amsa wa jakadun Yefta cewa, “Domin lokacin da Isra’ilawa suna tahowa daga Masar sun ƙwace mini ƙasa tun daga Kogin Arnon zuwa Kogin Yabbok, har zuwa Kogin Urdun. Yanzu sai ka mayar mini da ita cikin lumana.”

14 Yefta kuma ya sāke aike da jakadu wurin Sarkin Ammonawa,

15 tare da amsa, ya ce, “Isra’ilawa ba su ƙwace ƙasar Mowab ko ta Ammonawa ba.

16 Amma sa’ad da suka baro Masar, sun bi ta jeji zuwa Bahar Maliya, suka zo Kadesh.

17 Sa’an nan suka aike da jakadu wurin Sarkin Edom, su roƙe shi ya bar su su wuce ta ƙasarsa. Amma Sarkin Edom bai yarda ba. Suka kuma aika wa Sarkin Mowab, shi ma bai yarda ba, don haka Isra’ilawa suka zauna a Kadesh.

18 “Sa’an nan suka ci gaba da tafiya ta cikin hamada. Suka zaga ƙasar Edom da ta Mowab. Da suka kai gabashin ƙasar Mowab, sai suka yi zango a bakin Kogin Arnon, amma ba su haye kogin ba, gama shi ne iyakar ƙasar Mowab.

19 Sa’an nan Isra’ilawa suka aike da jakadu wurin Sihon Sarkin Heshbon ta Amoriyawa, suka roƙe shi, suka ce, ‘Ka yarda mana mu wuce ta ƙasarka.’

20 Amma Sihon bai amince wa Isra’ilawa su bi ta ƙasarsa, su wuce ba. Ya kuwa tattara mutanensa, ya kafa sansaninsa a Yahaza, ya yi yaƙi da Isra’ilawa.

21 Ubangiji Allah na Isra’ila kuwa ya ba da Sihon da mutanensa duka ga Isra’ilawa, suka ci su da yaƙi. Suka kuwa mallaki dukan ƙasar Amoriyawa da mazaunan ƙasar.

22 Suka mallaki dukan ƙasar Amoriyawa tun daga Kogin Arnon har zuwa Kogin Yabbok, tun kuma daga jeji zuwa Kogin Urdun.

23 To, ai, ka ga Ubangiji Allah na Isra’ila ne ya kori Amoriyawa saboda jama’ar Isra’ila. To, yanzu so kake ka ƙwace mana?

24 Kai ba za ka mallaki abin da Kemosh, allahnka, ya ba ka mallaka ba? Dukan abin da Ubangiji Allahnmu ya mallakar mana, za mu mallake shi.

25 Kana zaton ka fi Balak, ɗan Ziffor, Sarkin Mowab? Ka ji ya taɓa hamayya da Isra’ilawa? Ko kuwa ka ji ya taɓa yin yaƙi da su?

26 Shekara ɗari uku Isra’ilawa suka yi zamansu a Heshbon da ƙauyukanta, da Arower da ƙauyukanta, da dukan biranen da suke a gefen Kogin Arnon, me ya sa ba ka ƙwace su tun a wancan lokaci ba?

27 Don haka ni ban yi maka laifi ba, kai ne kake yi mini laifi da kake yaƙi da ni. Ubangiji ne alƙali yau, zai shara’anta tsakanin Isra’ilawa da Ammonawa.”

28 Amma Sarkin Ammonawa bai kula da saƙon da Yefta ya aika masa ba.

29 Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko wa Yefta, sai ya tashi ratsa Gileyad da Manassa zuwa Mizfa ta Gileyad, daga can ya haura zuwa wurin Ammonawa.

30 Yefta kuwa ya yi wa’adi ga Ubangiji, ya ce, “Idan dai ka ba da Ammonawa a hannuna,

31 duk abin da ya fara fitowa daga ƙofar gidana don ya tarye ni, sa’ad da na komo daga yaƙin Ammonawa da nasara, zai zama na Ubangiji, zan kuwa miƙa shi hadaya ta ƙonawa.”

32 Yefta ya haye zuwa wurin Ammonawa domin ya yi yaƙi da su. Ubangiji kuwa ya ba da su a hannunsa.

33 Ya karkashe su da mummunan kisa tun daga Arower zuwa yankin Minnit, har zuwa Abel-keramim. Ya cinye biranensu guda ashirin. Da haka Ammonawa suka sha kāshi a hannun Isra’ilawa.

‘Yar Yefta

34 Da Yefta ya koma gidansa a Mizfa, sai ga ‘yarsa, tilo ta fito da kiɗa da rawa don ta tarye shi. Ita ce kaɗai ‘yarsa, banda ita ba shi da ɗa ko ‘ya.

35 Sa’ad da ya gan ta sai ya yayyage tufafinsa, ya ce, “Kaito, ‘yata, kin karya mini gwiwa, kin zamar mini babban dalilin wahala. Na riga na yi wa’adi ga Ubangiji, ba kuwa zan iya warware shi ba.”

36 Sai ta ce masa, “Baba, idan ka riga ka yi wa’adi ga Ubangiji, sai ka yi da ni bisa ga wa’adinka, da yake Ubangiji ya ɗau maka fansa a kan Ammonawa, abokan gābanka.”

37 Ta kuma ce masa, “Ina so ka yardar mini in tafi kan duwatsu ni da ƙawayena in yi makokin budurcina har wata biyu.”

38 Sai ya ce mata, “Tafi.” Ya sallame ta, ta tafi har wata biyu ɗin. Ita da ƙawayenta kuwa suka yi makokin budurcinta a kan duwatsu.

39 Bayan wata biyu, sai ta koma wurin mahaifinta, shi kuwa ya yi abin da ya yi wa Ubangiji wa’adi. Ta rasu ba ta taɓa sanin namiji ba. Wannan kuwa ya zama al’ada a cikin Isra’ila,

40 wato matan Isra’ilawa sukan fita kowace shekara su yi makoki kwana huɗu don ‘yar Yefta, mutumin Gileyad.

Categories
L. MAH

L. MAH 12

Yefta da Mutanen Ifraimu

1 Mutanen Ifraimu suka yi gangami suka haye zuwa Zafon da shirin yaƙi. Suka ce wa Yefta, “Me ya sa ka haye zuwa yaƙi da Ammonawa, amma ba ka kira mu mu tafi tare da kai ba? To, yanzu za mu ƙone ka da gidanka.”

2 Amma Yefta ya amsa musu, ya ce, “Ni da mutanena mun yi ta jayayya da Ammonawa, na kira ku don ku cece ni, amma ba ku cece ni daga hannunsu ba.

3 Sa’ad da na ga ba ku cece ni ba, sai na yi kasai da raina, na haye don in yi karo da Ammonawa. Ubangiji kuwa ya ba da su a hannuna. Me ya sa kuka zo yau don ku yi yaƙi da ni?”

4 Sa’an nan Yefta ya tara dukan mutanen Gileyad, suka yi yaƙi da mutanen Ifraimu, suka ci su.

Mutanen Ifraimu suka ce musu, “Ku mutanen Gileyad masu neman mafaka ne a cikin Ifraimu da Manassa!”

5 Mutanen Gileyad suka hana mutanen Ifraimu hayewa ta mashigan Kogin Urdun. Idan wani mutumin Ifraimu gujajje ya ce, “Ku bar ni in haye.”

Sai mutanen Gileyad su tambaye shi, “Kai mutumin Ifraimu ne?”

Idan ya ce, “A’a,”

6 sai su ce masa, to, ka ce, “Shibbolet,” sai mutum ya ce, “Sibbolet,” gama ba ya iya faɗa daidai. Sai su kama shi su kashe a mashigan Urdun. Mutanen Ifraimu da aka kashe a lokacin su dubu arba’in da dubu biyu (42,000) ne.

7 Yefta mutumin Gileyad ya shugabanci Isra’ilawa shekara shida, sa’an nan ya rasu. Aka binne shi a garinsu, wato Gileyad.

Ibzan, da Elon, da Abdon Sun Shugabanci Isra’ilawa

8 Bayan Yefta, sai Ibzan, mutumin Baitalami ya shugabanci Isra’ilawa.

9 Yana da ‘ya’ya maza talatin, da ‘ya’ya mata talatin. Ya aurar da ‘ya’yansa mata ga wata kabila, ya kuma auro wa ‘ya’yansa maza ‘yan mata daga wata kabila. Ya shugabanci Isra’ilawa shekara bakwai.

10 Sa’an nan ya rasu, aka binne shi a Baitalami.

11 Bayansa kuma, sai Elon mutumin Zabaluna ya shugabanci Isra’ilawa shekara goma.

12 Sa’an nan ya rasu, aka binne shi a Ayalon a ƙasar Zabaluna.

13 Bayan Elon kuma, sai Abdon, ɗan Hillel, mutumin Firaton, ya shugabanci Isra’ilawa.

14 Yana da ‘ya’ya maza arba’in, da jikoki maza talatin, suna hawan jakai saba’in. Abdon ya shugabanci Isra’ilawa shekara takwas.

15 Sa’an nan ya rasu, aka binne shi a Firaton ta ƙasar Ifraimu a tudun Amalekawa.

Categories
L. MAH

L. MAH 13

Haihuwar Samson

1 Isra’ilawa kuma suka sāke yi wa Ubangiji zunubi, sai Ubangiji ya ba da su a hannun Filistiyawa shekara arba’in.

2 Akwai wani mutumin Zora daga kabilar Dan, sunansa Manowa, matarsa bakarariya ce, ba ta haihuwa.

3 Ga mala’ikan Ubangiji ya bayyana gare ta, ya ce mata, “Ga shi, ke bakarariya ce, ba ki haihuwa, amma yanzu za ki yi ciki, za ki kuwa haifi ɗa.

4 Yanzu sai ki lura, kada ki sha ruwan inabi, ko abin sha mai gāfi, kada kuma ki ci haramtaccen abu,

5 gama za ki yi juna biyu, ki haifi ɗa. Ba za ki taɓa aske kansa ba Zai zama keɓaɓɓe ga Allah tun daga cikin ciki. Shi ne zai ceci Isra’ilawa daga hannun Filistiyawa.”

6 Macen kuwa ta tafi ta faɗa wa mijinta cewa, “Mutumin Allah ya zo wurina, fuskarsa tana da bantsoro kamar fuskar mala’ikan Ubangiji. Ni kuwa ban tambaye shi inda yake ba, shi kuma bai faɗa mini sunansa ba.

7 Amma ya ce mini, zan yi juna biyu, in haifi ɗa, don haka kada in sha ruwan inabi, ko abin sa maye, kada kuma in ci haramtaccen abu, gama yaron zai zama keɓaɓɓe ga Allah tun daga cikin ciki har zuwa ranar da zai rasu.”

8 Sa’an nan Manowa ya yi roƙo ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangijina, ina roƙonka ka bar mutumin Allah wanda ka aiko, ya sāke zuwa wurinmu, ya faɗa mana abin da za mu yi wa yaron da za a haifa.”

9 Allah kuwa ya ji roƙon Manowa, ya sāke aiko da mala’ikansa wurin matar, sa’ad da take a saura, mijinta kuwa ba ya tare da ita.

10 Don haka sai ta sheƙa a guje zuwa wurin mijinta, ta faɗa masa, “Ga mutumin da ya zo wurina ran nan, ya sāke zuwa.”

11 Manowa fa ya tashi ya tafi tare da ita. Da ya zo wurin mutumin, sai ya tambaye shi, “Kai ne mutumin da ya yi magana da macen nan?”

Sai ya amsa ya ce, “Ni ne.”

12 Manowa kuma ya ce, “Lokacin da maganarka ta cika, wane irin yaro ne zai zama, me kuma za mu yi?”

13 Mala’ikan Ubangiji ya amsa, ya ce wa Manowa, “Sai matarka ta kiyaye dukan abin da na faɗa mata.

14 Kada ta ci kowane irin abu da aka yi da inabi, kada kuma ta sha ruwan inabi ko abin sa maye. Kada ta ci haramtaccen abu, amma ta kiyaye dukan abin da na umarce ta.”

15-16 Manowa dai bai san mala’ikan Ubangiji ne ba, sai ya ce wa mala’ikan, “Ina roƙonka ka jira, mu yanka maka ɗan akuya.”

Amma mala’ikan ya ce masa, “Ko na jira ba zan ci abincinku ba, amma idan kana so ka yanka, sai ka shirya hadayar ƙonawa, ka miƙa ta ga Ubangiji.”

17 Manowa ya ce, “Ka faɗa mana sunanka domin lokacin da maganarka ta cika mu girmama ka.”

18 Mala’ikan Ubangiji ya ce masa, “Don me kake tambayar sunana? Sunana asiri ne.”

19 Manowa kuwa ya yanka ɗan akuya, ya kuma kawo hadayar gāri, ya miƙa a kan dutse ga Ubangiji, mala’ika kuma ya yi al’ajabi. Manowa da matarsa suka yi kallo.

20 Sa’ad da harshen wutar ya hau zuwa samaniya daga bagaden, sai mala’ikan Ubangiji ya hau zuwa sama ta cikin harshen wutar bagaden. Manowa da matarsa sun gani, suka fāɗi a fuskokinsu a ƙasa.

21 Mala’ikan Ubangiji bai sāke bayyana ga Manowa da matarsa ba. Manowa kuma ya gane mala’ikan Ubangiji ne.

22 Manowa ya ce wa matarsa, “Ba shakka za mu mutu gama mun ga Ubangiji!”

23 Amma matarsa ta ce masa, “Da Ubangiji yana so ya kashe mu, ai, da bai karɓi hadayar ƙonawa da hadayar gārinmu ba, da kuma bai nuna mana, ko ya faɗa mana waɗannan abubuwa ba.”

24 Matar kuwa ta haifi ɗa, aka raɗa masa suna Samson. Yaron ya yi girma, Ubangiji ya sa masa albarka.

25 Ruhun Ubangiji ya fara iza shi, sa’ad da yake a zangon Dan, tsakanin Zora da Eshtawol.

Categories
L. MAH

L. MAH 14

Samson da Budurwa a Timna

1 Samson kuwa ya gangara zuwa Timna inda ya ga ɗaya daga cikin ‘yan matan Filistiyawa.

2 Sa’ad da ya hauro zuwa gida sai ya faɗa wa iyayensa, ya ce, “Na ga ɗaya daga cikin ‘yan matan Filistiyawa a Timna, ina so ku auro mini ita.”

3 Amma iyayensa suka ce masa, “Cikin ‘yan’uwanka da mutanenka duka, ba yarinyar da za ka aura daga cikin ‘yan matansu, har ka tafi ka auro mace daga na Filistiyawa marasa kaciya?”

Amma Samson ya ce wa mahaifinsa, “Ita ce wadda nake bukata, ka auro mini ita. Ina sonta.”

4 Iyayensa ba su san al’amarin nan daga wurin Ubangiji ne ba, gama Ubangiji yana so wannan ya zama sanadin yaƙi da Filistiyawa, gama a lokacin nan Filistiyawa ne suke mulkin Isra’ilawa.

5 Samson kuwa ya gangara zuwa Timna, shi da iyayensa. Da ya isa gonakin inabin Timna, sai ga sagarin zaki ya taso masa da ruri.

6 Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko a kansa da iko, sai ya yaga zakin da hannu, kamar yadda akan yayyage ɗan akuya. Amma bai faɗa wa iyayensa abin da ya yi ba.

7 Sa’an nan ya gangara ya yi zance da budurwar, yana kuwa sonta.

8 Bayan ‘yan kwanaki sai ya koma don ya auro ta. Ya ratse don ya duba gawar zakin da ya kashe, sai ya tarar da cincirindon ƙudan zuma, da kuma zuma a cikin gawar zakin, ya yi mamaki.

9 Ya ɗebo zuman a hannunsa, yana tafe yana sha, har ya isa wurin iyayensa, ya ba su, suka sha, amma bai faɗa musu daga cikin gawar zaki ya ɗebo zuman ba.

10 Mahaifinsa ya tafi gidan iyayen yarinyar, Samson kuma ya shirya liyafa a can, gama haka samari sukan yi.

11 Sa’ad da Filistiyawa suka gan shi suka sa samari talatin su zauna tare da shi.

12 Samson kuwa ya ce musu, “Bari in yi muku ka-cici-ka-cici, idan kun faɗa mini amsarsa a kwana bakwai na bikin, to, zan ba ku rigunan lilin talatin da waɗansu riguna talatin na ado.

13 Amma idan kun kāsa ba ni amsar, to, ku ne za ku ba ni rigunan lilin talatin da waɗansu rigunan na ado.”

Sai suka ce, “To, faɗi ka-cici-ka-cicin mu ji.”

14 Sai ya ce musu,

“Daga mai ci, abinci ya fito,

Daga kuma mai ƙarfi, zaƙi ya fito.”

Ba su iya ba da amsar ba har kwana uku.

15 A rana ta huɗu suka ce wa matar Samson, “Ki rarrashi mijinki ya gaya mana amsar ka-cici-ka-cicin, idan kuwa kin ƙi, to, za mu ƙone ki da gidan mahaifinki da wuta. Kun gayyace mu don ku tsiyata mu ne?”

16 Sai matar Samson ta yi kuka a gabansa tana cewa, “Kai dai maƙiyina ne, ba masoyina ba, ka yi wa mutanena ka-cici-ka-cici, amma ba ka gaya mini amsarsa ba.”

Amma ya ce mata, “Ko iyayena ma ban faɗa musu ba, sai in faɗa miki?”

17 Ta kuwa yi ta yi masa kuka har rana ta bakwai ta ƙarewar bikinsu. Amma a rana ta bakwai, ya faɗa mata amsar saboda yawan fitinarta. Ita kuwa ta faɗa wa mutanenta amsar ka-cici-ka-cicin.

18 A rana ta bakwai, kafin rana ta faɗi, mutanen garin suka ce masa,

“Me ya fi zuma zaƙi?

Me kuma ya fi zaki ƙarfi?”

Ya kuwa ce musu,

“Da ba don kun haɗa baki da matata ba,

Da ba ku san amsar ka-cici-ka-cicin ɗin nan ba.”

19 Sa’an nan Ruhun Ubangiji ya sauko a kansa da iko, ya gangara zuwa Ashkelon. Ya kashe mutum talatin a can, ya kwashe ganima, ya ba waɗanda suka faɗa masa amsar ka-cici-ka-cicin riguna. Ya koma gida a husace saboda abin da ya faru.

20 Aka ɗauki matar Samson aka ba wanda ya yi masa abokin ango.

Categories
L. MAH

L. MAH 15

1 Bayan ‘yan kwanaki, sai Samson ya tafi ya ziyarci matarsa, ya kai mata ɗan akuya, a lokacin girbin alkama. Ya ce wa mahaifinta, “Zan shiga wurin matata a ɗakin kwana.”

Amma mahaifinta bai yardar masa ba.

2 Ta ce wa Samson, “Na yi tsammani ba ka sonta ne sam, don haka sai na ba da ita ga wanda ya yi maka abokin ango. Amma ƙanwarta ta fi ta kyau. Ina roƙonka ka ɗauki ƙanwar maimakon matarka.”

3 Sai Samson ya ce musu, “A wannan lokaci, zan zama marar laifi saboda abin da zan yi wa Filistiyawa.”

4 Ya tafi ya kama yanyawa ɗari uku, ya haɗa wutsiyoyinsu, wato wutsiya da wutsiya, sa’an nan ya ɗaura jiniya tsakanin kowaɗanne wutsiya biyu.

5 Da ya sa wa jiniyar wuta, ya sake su zuwa cikin hatsin Filistiyawa. Suka ƙone dammunan hatsi, da hatsin da take a tsaye, da gonakin zaitun.

6 Filistiyawa kuwa suka ce, “Wane ne ya yi mana wannan abu?”

Sai aka ce, “Samson ne, surukin mutumin Timna, domin ya ɗauki matar Samson ya ba wanda ya yi masa abokin ango.” Filistiyawa kuwa suka je suka ƙone matar, ta mutu, suka kuma ƙone gidan mahaifinta.

7 Samson ya ce musu, “Wato haka kuka yi! To, na rantse, ba zan bari ba sai na rama!”

8 Ya kuwa fāɗa musu, ya kashe su da yawa. Sa’an nan ya tafi ya zauna a kogon dutsen Itam.

Samson Ya Ci Nasara a kan Filistiyawa

9 Filistiyawa suka haura, suka kafa sansani a Yahudiya, suka bazu a cikin Lihai.

10 Mutanen Yahuza suka ce, “Me ya sa kuka kawo mana yaƙi?”

Filistiyawa suka ce, “Mun zo ne domin mu kama Samson, mu yi masa kamar yadda ya yi mana.”

11 Sa’an nan mutum dubu uku na Yahuza suka gangara zuwa kogon dutsen Itam. Suka ce wa Samson, “Ba ka sani ba Filistiyawa ne suke mulkinmu? Me ya sa ka yi mana haka?”

Shi kuwa ya amsa musu, ya ce, “Kamar yadda suka yi mini, haka ni kuma na yi musu.”

12 Suka ce masa, “Mun gangara zuwa wurinka don mu ɗaure ka, mu miƙa ka gare su.”

Samson ya ce musu, “Ku rantse mini idan ba ku ne da kanku kuke so ku kashe ni ba.”

13 Suka ce masa, “A’a, ba za mu kashe ka ba, mu dai za mu kama ka, mu miƙa ga Filistiyawa.” Sa’an nan suka ɗaure shi da sababbin igiyoyi biyu, suka sauko da shi daga dutsen.

14 Sa’ad da ya zo Lihai, sai Filistiyawa suka sheƙo a guje suna ihu suka nufo shi. Ruhun Ubangiji ya sauko kansa da iko, sai igiyoyin da suke a ɗaure da shi suka tsintsinke kamar zaren da ya kama wuta.

15 Ya kuwa sami sabon muƙamuƙin jaki, ya ɗauka ya kashe mutum dubu da muƙamuƙin.

16 Sa’an nan Samson ya raira waƙa ya ce.

“Da muƙamuƙin jaki na kashe mutum dubu,

Da muƙamuƙin jaki na tsiba su tsibi-tsibi.”

17 Da ya gama, ya jefar da muƙamuƙin. Sai aka ba wurin suna, Ramat-Lihai, wato tudun muƙamuƙi.

18 Ƙishirwa kuwa ta kama shi ƙwarai, sai ya roƙi Ubangiji ya ce, “Kai ne ka yi wannan babbar nasara ta hannun bawanka, yanzu kuwa ko zan mutu da ƙishirwa, har Filistiyawa marasa kaciya su kama ni?”

19 Allah kuwa ya buɗe wani rami daga ƙasa, sai ruwa ya ɓuɓɓugo daga ciki. Da ya sha, hankalinsa ya komo, ya wartsake. Don haka aka ba wurin suna En-hakkore, wato mai kira. Ramin yana nan a Lihai har wa yau.

20 Samson ya shugabanci Isra’ilawa shekara ashirin a zamanin da Filistiyawa suke mulkinsu.

Categories
L. MAH

L. MAH 16

Samson a Gaza

1 Daga can Samson ya tafi Gaza, inda ya ga wata karuwa, sai ya shiga wurinta.

2 Aka faɗa wa mutanen Gaza, Samson yana nan. Suka kewaye wurin, suka yi fakonsa a ƙofar garin dukan dare. Suka yi shiru dukan dare, suka ce wa junansu, “Za mu jira sai gari ya waye sa’an nan mu kashe shi.”

3 Amma Samson ya yi kwanciyarsa har tsakar dare. Sa’an nan ya tashi ya kama ƙyauren ƙofar birnin, da madogarai biyu na ƙofar, ya tumɓuke su. Ya saɓe su a kafaɗarsa, ya kai su kan dutsen da yake a gaban Hebron.

Samson da Delila

4 Bayan wannan kuma sai ya kama ƙaunar wata mace mai suna Delila a kwarin Sorek.

5 Shugabannin Filistiyawa, su biyar suka je wurinta suka ce mata, “Ki yi masa kirsa, don ki san dalilin irin ƙarfin nan nasa, da kuma yadda za mu yi maganinsa, mu ɗaure shi don mu rinjaye shi. Kowannenmu zai ba ki shekel dubu da ɗari (1,100).”

6 Delila kuwa ta ce wa Samson, “Ina roƙonka ka faɗa mini inda babban ƙarfin nan naka yake, da kuma yadda za a ɗaure ka ka rasa kuzari.”

7 Samson ya ce mata, “Idan an ɗaure ni da sababbin tsarkiyoyi guda bakwai, waɗanda ba su bushe ba, to, sai in rasa ƙarfi, in zama kamar kowa.”

8 Sai shugabannin Filistiyawa suka kawo wa Delila sababbin tsarkiyoyi guda bakwai waɗanda ba su bushe ba. Ta kuwa ɗaure shi da su.

9 Tana kuwa da mutane a laɓe cikin wani ɗaki, sai ta ce masa, “Ga Filistiyawa a kanka, Samson!” Da jin haka, sai ya katse tsarkiyoyi kamar zare idan an sa masa wuta. Asirin ƙarfinsa kuwa bai sanu ba.

10 Delila kuma ta ce wa Samson, “Ga shi, ka yi mini ba’a, ka ruɗe ni. Ina roƙonka, ka faɗa mini yadda za a ɗaure ka.”

11 Ya ce mata, “Idan suka ɗaure ni da sababbin igiyoyi waɗanda ba a yi amfani da su ba, to, zan rasa ƙarfi, in zama kamar kowa.”

12 Sai Delila ta ɗauki sababbin igiyoyi, ta ɗaure shi da su, sa’an nan ta ce masa, “Ga Filistiyawa na zuwa kanka, Samson!” Amma ya katse igiyoyin da ta ɗaure shi da su kamar silin zare. Mutanen kuwa na nan laɓe a wani ɗaki.

13 Delila ta ce wa Samson, “Har yanzu dai, ka maishe ni shashasha, kana ta ruɗina. Ka faɗa mini yadda za a ɗaure ka.”

Ya ce mata, “Idan kin saƙa tukkwayen bakwai waɗanda suke kaina haɗe da zare, kika buga da akwasha sai in rasa ƙarfi, in zama kamar kowa.”

14 Sa’ad da yake barci, Delila ta saƙa tukkwayen nan bakwai da suke kansa haɗe da zare, ta buga da akwasha, sa’an nan ta ce masa, “Ga Filistiyawa a kanka, Samson!” Da ya farka daga barcin, sai ya tumɓuke akwashar, da zaren.

15 Delila ta ce masa, “Ƙaƙa za ka ce kana ƙaunata, alhali kuwa ba na a zuciyarka? Sau uku ke nan ka maishe ni shashasha, ba ka faɗa mini inda ƙarfin nan naka yake ba.”

16 Sa’ad da ta fitine shi yau da gobe da yawan maganganunta, ta tunzura shi, sai ransa ya ɓaci kamar zai mutu.

17 A ƙarshe ya faɗa mata ainihin gaskiyar, ya ce mata, “Ba a taɓa aske gashin kaina ba, gama ni keɓaɓɓe ga Ubangiji ne tun daga cikin uwata. Idan aka yi mini aski, to, ƙarfina zai rabu da ni, in zama marar ƙarfi kamar kowa.”

18 Sa’ad da Delila ta gane ya faɗa mata ainihin gaskiya, sai ta aika a kirawo shugabannin Filistiyawa tana cewa, “A wannan karo ku zo, domin ya faɗa mini ainihin gaskiyar.” Shugabannin Filistiyawa kuwa suka zo wurinta da kuɗi a hannu.

19 Ta kuwa sa shi ya yi barci a cinyoyinta, sai ta kira wani mutum, ta sa shi ya aske tukkwayen nan bakwai waɗanda suke kansa. Sa’an nan ta yi ƙoƙari ta sa ya harzuƙa, amma ƙarfinsa ya rabu da shi.

20 Ta ce masa, “Ga Filistiyawa a kanka, Samson!”

Sai ya farka daga barcinsa, ya ce, “Zan fita kamar yadda na saba yi koyaushe, in miƙe jikina.” Ashe, bai sani ba, Ubangiji ya rabu da shi.

21 Filistiyawa fa suka kama shi, suka ƙwaƙule idanunsa, suka gangara da shi zuwa Gaza. Suka ɗaure shi da sarƙoƙin tagulla. Ya yi ta niƙa a kurkuku.

22 Amma gashin kansa ya fara tohowa.

Samson ya Mutu

23 Shugabannin Filistiyawa kuwa suka taru domin su miƙa babbar hadaya ga allahnsu, Dagon. Suka raira waƙa, suka ce, “Allahnmu ya ba da Samson, maƙiyinmu a hannunmu!”

24 Da mutane suka gan shi, sai suka raira waƙar yabon allahnsu, suna cewa, “Allahnmu ya ba da maƙiyinmu a hannunmu, wanda ya fallasa ƙasarmu, ya kashe mutanenmu da yawa.”

25 Sa’ad da suke ta farin ciki, sai suka ce, “A kawo Samson ya yi mana wasa.” Sai suka kawo Samson daga kurkuku, ya kuwa yi wasa a gabansu. Suka sa ya tsaya a tsakanin ginshiƙai.

26 Samson kuwa ya ce wa yaron da yake jagoransa, “Bari in taɓa ginshiƙan da suke ɗauke da gidan nan, domin in jingina.”

27 Gidan kuwa yana cike da mutane mata da maza. Shugabannin nan biyar na Filistiyawa suna wurin. Akwai mutum dubu uku mata da maza, a kan benen da suka zo kallon wasan Samson.

28 Sa’an nan Samson ya yi roƙo ga Ubangiji, ya ce, “Ya Ubangiji Allah, ka tuna da ni, ina roƙonka, ka ƙarfafa ni sau ɗayan nan kaɗai, don in ɗauki fansa a kan Filistiyawa saboda idona biyu da suka ƙwaƙule mini.”

29 Sai Samson ya kama ginshiƙai biyu da suke a tsakiya, waɗanda suke ɗauke da gidan. Ya riƙe su da hannunsa biyu, ɗaya a kowane hannu, sa’an nan ya jingina jikinsa a kansu,

30 ya yi kuwwa ya ce, “Bari in mutu tare da Filistiyawa!” Ya sunkuya da iyakar ƙarfinsa. Ɗakin kuwa ya faɗa a kan shugabannin da dukan mutanen da suke a cikin ɗakin. Mutanen da Samson ya kashe a rasuwarsa sun fi waɗanda ya kashe sa’ad da yake da rai.

31 ‘Yan’uwansa da dukan danginsa, suka gangara, suka ɗauki gawarsa, suka binne a kabarin Zora da Eshtawol. Samson ya shugabanci Isra’ilawa shekara ashirin.

Categories
L. MAH

L. MAH 17

Gumakan Mika

1 Akwai wani mutum a ƙasar tudu ta Ifraimu, da ake kira Mika.

2 Shi ne ya ce wa mahaifiyarsa, “Sa’ad da aka sace miki tsabar azurfan nan dubu da ɗari ɗaya (1,100), kin hurta la’ana a kan ɓarayin, na kuwa ji ki. To, ga shi, azurfar na wurina, ni na ɗauka.”

Sai mahaifiyarsa ta ce, “Allah ya sa maka albarka, ɗana.”

3 Ya mayar wa mahaifiyarsa da azurfar dubu da ɗari (1,100). Mahaifiyarsa ta ce, “Domin kada la’anar ta kama ɗana, ina ba da wannan azurfa ga Ubangiji da zuciya ɗaya. Ana iya sassaƙa gunki a kuma yi na zubi saboda haka zan ba ka ita.”

4 Da ya mayar mata da azurfar, ta ɗibi azurfa ɗari biyu ta ba maƙerin azurfa, shi kuwa ya sassaƙa gunki ya kuma yi na zubi. Aka ajiye su a gidan Mika.

5 Mika kuwa yana da ɗakin gumaka. Ya yi gumaka, da falmaransu, da kan gida. Ya keɓe ɗaya daga cikin ‘ya’yansa maza domin ya zama firist nasa.

6 A wannan lokaci ba sarki a Isra’ila, kowa yana ta yin yadda ya ga dama.

7 Akwai wani saurayi Balawen da yake zama a Baitalami ta Yahudiya.

8 Saurayin kuwa ya yi ƙaura daga Baitalami. Sa’ad da yake tafiya sai ya iso gidan Mika, a ƙasar tudu ta Ifraimu.

9 Mika ya tambaye shi, “Daga ina ka zo?”

Ya ce, “Ni Balawe ne na Baitalami ta Yahudiya, ina neman wurin da zan zauna.”

10 Mika ya ce masa, “Ka zauna tare da ni, ka zama mai ba ni shawara, da kuma firist, ni kuwa zan riƙa ba ka azurfa goma, da tufafi, da abin zaman gari kowace shekara.”

11 Balawen kuwa ya yarda ya zauna tare da Mika. Ya kuwa zama kamar ɗa ga Mika.

12 Mika kuma ya naɗa shi ya zama firist ɗinsa. Ya kuwa zauna a gidansa.

13 Sa’an nan Mika ya ce, “Yanzu na sani Ubangiji zai sa mini albarka, da yake na sami Balawe ya zamar mini firist.”

Categories
L. MAH

L. MAH 18

Mika da Kabilar Dan

1 A kwanakin nan ba sarki a Isra’ila. A wannan lokaci kuwa kabilar Dan suna ta neman yankin ƙasar da za su samu, su zauna. Gama har yanzu ba su sami nasu gādon ƙasa tare da sauran kabilar Isra’ila ba.

2 Sai Danawa suka zaɓi mutum biyar jarumai daga kabilarsu, suka aike su daga Zora da Eshtawol, su tafi leƙen asirin ƙasar, su bincike ta. Suka kuwa tafi zuwa ƙasar tudu ta Ifraimu, suka sauka a gidan Mika.

3 Sa’ad da suke a gidan Mika ɗin, sai suka ji muryar saurayin nan, Balawe, suka tsaya suka tambaye shi, “Wa ya kawo ka nan? Me kuma kake yi a nan?”

4 Ya ce musu, “Mun yi yarjejeniya da Mika, in yi masa aikin firist, shi kuma ya biya ni.”

5 Suka ce masa, “In ka yarda ka roƙar mana Allah ko tafiyarmu na da sa’a.”

6 Firist ɗin ya ce musu, “Kada ku damu, Ubangiji yana tare da ku a tafiyarku.”

7 Saboda haka mutanen nan biyar suka tashi, suka zo Layish, suka ga mutane suna zamansu a huce, kamar Sidoniyawa. Ba su da rigima, natsattsu ne, ba su jayayya da kowa, suna da wadata. Suna nesa da Sidoniyawa, ba su sha’anin kome da kowa.

8 Da mutanen nan biyar suka koma wurin ‘yan’uwansu a Zora da Eshtawol, sai ‘yan’uwan suka tambaye su labarin tafiyarsu.

9 Suka ce, “Ku tashi, mu tafi mu fāɗa musu, gama mun ga ƙasar tana da ni’ima ƙwarai. Kada ku zauna ku ɓata lokaci, ku shiga ku mallake ta!

10 Idan kuka je za ku tarar da mutane suna zama a sake. Ƙasar kuwa babba ce, tana da dukan abin da ɗan adam yake bukata.”

11 Mutum ɗari shida daga kabilar Dan suka yi shirin yaƙi, suka kama hanya daga Zora da Eshtawol.

12 Suka tafi suka kafa sansani a yammacin Kiriyat-yeyarim, birni ne a Yahudiya. Saboda haka ake kiran wurin Mahanedan, wato sansanin Dan, har wa yau.

13 Daga can suka wuce zuwa ƙasar tudu ta Ifraimu, suka zo gidan Mika.

14 Mutum biyar ɗin nan da suka tafi leƙen asirin ƙasar Layish, suka ce wa abokan tafiyarsu, “Ko kun san akwai gunkin itace cikin gidajen nan? Akwai kuma gunki na zubi, da kan gida, da falmaran dominsu. Me ya kamata mu yi musu?”

15 Sai suka juya zuwa gidan Mika, inda saurayin nan Balawe yake, suka gaishe shi.

16 Danawa ɗari shida ɗin da suka yi shirin yaƙi, suka tsaya a bakin ƙofa.

17 Amma mutum biyar ɗin nan da suka tafi leƙen asirin ƙasar suka shiga kai tsaye, suka ɗauki gunkin da aka yi da itace, da falmaran, da kan gida, da gunki na zubi. Firist ɗin kuwa ya tsaya a bakin ƙofa tare da mutum ɗari shida ɗin nan masu shirin yaƙi.

18 Sa’ad da mutum biyar ɗin nan suka shiga gidan Mika suka ɗauki falmaran, da sassaƙaƙƙen gunki, da kan gida, da gunki na zubi, sai firist ɗin ya ce musu, “Me kuke yi?”

19 Suka ce masa, “Yi mana shiru, kame bakinka. Ka biyo mu, ka zama firist namu da mai ba mu shawara. Bai fi kyau ka zama firist na kabilar Isra’ila ba, da a ce ka zama na gidan mutum guda kawai?”

20 Da firist ɗin ya ji haka, sai ya yi murna, ya ɗauki falmaran da kan gida da sassaƙaƙƙen gunki, ya tafi tare da su.

21 Suka juya, suka tafi da ‘ya’yansu da dabbobinsu, da mallakarsu.

22 Sa’ad da suka yi ‘yar tazara daga gidan Mika sai aka kira maƙwabtan Mika, suka je suka ci wa Danawa.

23 Suka yi wa Danawa tsawa. Da suka waiga, sai suka ce wa Mika, “Me ya faru? Me ya kawo waɗannan ‘yan iska?”

24 Mika kuwa ya ce musu, “Kun kwashe allolina da na yi, da firist ɗina, me ya rage mini kuma? Sa’an nan ku ce mini, ‘Me ya faru?’ ”

25 Danawa kuma suka ce masa, “Kada ka kuskura ka ce kome, idan ba haka ba mutanen nan za su harzuƙa, da kai da iyalinka duka ku rasa rayukanku.”

26 Sa’an nan Danawa suka kama hanyarsu. Da Mika ya ga dai sun fi ƙarfinsa, sai ya juya ya koma gida.

27 Da Danawa suka ɗauke gumakan da Mika ya yi, da firist ɗinsa, sai suka je Layish inda suka sami mutane suna zamansu a huce. Suka hallaka su, suka ƙone birnin.

28 Ba wanda zai ceci mutanen Layish, gama suna nesa da Sidon, ba su kuma sha’ani da kowa. A kwari guda ne da Bet-rehob. Danawa kuwa suka sāke gina birnin, suka zauna a ciki.

29 Suka sa wa birnin suna Dan, ɗan Yakubu. Kafin wannan lokaci kuwa ana kiran birnin Layish ne.

30 Danawa fa suka kafa gunkin domin su yi masa sujada. Jonatan, ɗan Gershom, ɗan Musa, shi da ‘ya’yansa maza, suka zama firistocin Danawa, har zuwa ranar da aka kwashe mutanen zuwa bauta.

31 Haka fa suka kafa gunkin Mika har duk lokacin da alfarwar Ubangiji take a Shilo.

Categories
L. MAH

L. MAH 19

Balawe da Ƙwarƙwararsa

1 A lokacin nan ba sarki a Isra’ila. Sai wani Balawen da yake zama a wani lungu na ƙasar tudu ta Ifraimu ya ɗauko wata mace daga Baitalami ta Yahudiya ta zama ƙwarƙwararsa.

2 Ƙwarƙwarar kuwa ta ji haushinsa, ta koma gidan mahaifinta a Baitalami ta Yahudiya. Ta zauna a can har wata huɗu.

3 Sa’an nan mutumin ya tafi ya yi bikonta. Ya tafi da baransa da jaki biyu. Da ya zo gidan mahaifinta, sai ta shigo da shi gidan, mahaifin ya karɓe shi da farin ciki.

4 Mahaifin macen ya i masa ya dakata, sai ya tsaya har kwana uku. Suka ci suka sha tare.

5 A safiyar rana ta huɗun, suka tashi tun da wuri, domin su yi shirin tafiya, amma mahaifin matar ya ce masa, “Ka dakata ka ƙara cin abinci tukuna sa’an nan ka tafi.”

6 Su biyu kuwa suka zauna suka ci suka sha tare. Har yanzu mahaifin mace ya sāke ce masa, “Ina roƙonka ka ƙara kwana, ka saki jikinka ka more.”

7 Sa’ad da mutumin ya tashi zai tafi sai mahaifin macen ya roƙe shi, ya kuma kwana.

8 A rana ta biyar, sai mutumin ya tashi da wuri don ya tafi amma mahaifin macen ya ce masa, “Ka zauna ka ci abinci tukuna har rana ta yi sanyi.” Dukansu biyu suka zauna suka ci tare.

9 Sa’ad da mutumin, da ƙwarƙwararsa, da baransa sun tashi za su tafi, sai mahaifin macen kuma ya ce masa, “Ga shi, rana ta kusan faɗuwa, yamma kuwa ta yi, ina roƙonka, ka sāke kwana ka ji wa ranka da:di, sa’an nan ka yi sammako gobe ka kama hanyarka zuwa gida.”

10 Amma mutumin bai yarda ya sāke kwana ba, sai ya tashi shi da ƙwarƙwararsa suka kama hanya. Ya kai daura da Yebus, wato Urushalima ke nan. Yana tare da jakinsa biyu da ya yi musu shimfiɗa, da ƙwarƙwararsa.

11 Baran kuwa ya ce wa maigidansa, “In ka yarda mu ratse mu kwana a birnin Yebusiyawan nan.”

12 Amma maigidansa ya ce masa, “Ba za mu tsaya a birnin da mutane ba Isra’ilawa ba ne. Za mu wuce zuwa Gibeya,

13 mu ƙara ɗan nisa, mu tafi mu kwana a Gibeya ko a Rama.”

14 Sai suka wuce, suka yi tafiyarsu. Rana ta faɗi sa’ad da suka kai Gibeya, ta yankin ƙasar Biliyaminu.

15 Suka ratse don su kwana a Gibeya. Balawen ya tafi ya zauna a dandalin garin, gama ba wanda ya kai su gidansa su kwana.

16 To, ga wani tsoho yana komowa daga gona da yamma. Tsohon kuwa mutumin ƙasar tudu ta Ifraimu ne, yana zama a Gibeya, amma mutanen Gibeya kabilar Biliyaminu ne.

17 Da dattijon ya duba ya ga matafiyin a dandalin birnin, ya ce masa, “Ina za ka? Daga ina kuma ka fito?”

18 Balawen ya ce masa, “Muna tahowa ne daga Baitalami ta Yahudiya zuwa wani lungun da take ƙasar tudu ta Ifraimu, inda nake. Na je Baitalami ta Yahudiya ne, yanzu kuwa ina komawa gida. Ba wanda ya sauke ni a gidansa.

19 Ina da baro domin jakuna, ina kuma da abinci da ruwa inabi don kaina, da ƙwarƙwarata da barana, ba mu rasa kome ba.”

20 Tsohon nan ya ce, “Ku zo mu je gidana, duk abin da kuke bukata zan ba ku, amma kada ku kwana a dandalin.”

21 Sai ya kai su gidansa, ya ba jakan harawa, aka wanke ƙafafun baƙin, sa’an nan suka ci suka sha.

22 Sa’ad da suke cikin jin daɗin ci da sha, ‘yan iskan da suke birnin suka zo suka kewaye gidan, suka yi ta bubbuga ƙofar, suka ce wa tsohon, “Ka fito mana da mutumin da ya zo gidanka don mu yi luɗu!”

23 Tsohon kuwa ya fito wurinsu, ya ce musu, “A’a, ‘yan’uwana, kada ku yi mugun abu haka, wannan ya sauka a gidana, kada ku yi wannan rashin kunya.

24 Ga ‘yata budurwa da ƙwarƙwararsa, bari in fito muku da su, ku yi abin da kuka ga dama da su, amma kada ku yi wa mutumin nan wannan abin kunya!”

25 Amma ‘yan iskan ba su yarda ba, sai Balawen ya fitar da ƙwarƙwararsa gare su. Suka yi mata faɗe, suka wulakanta ta dukan dare har kusan wayewar gari, sa’an nan suka ƙyale ta.

26 Da gari ya waye, ƙwarƙwarar ta zo ta fāɗi a ƙofar gidan tsohon, inda maigidanta ya sauka, tana nan har hantsi ya cira.

27 Sa’ad da Balawen ya tashi da safe, ya buɗe ƙofa, ya fita domin ya kama hanyarsa, sai ga ƙwarƙwararsa kwance a ƙofar gida, da hannuwanta a dokin ƙofar.

28 Ya ce mata, “Tashi mu tafi.” Amma ba amsa. Sai ya aza gawarta a kan jaki, sa’an nan ya kama hanya zuwa gida.

29 Da ya isa gida, ya ɗauki wuƙa ya yanyanka gawar ƙwarƙwararsa gunduwa gunduwa har goma sha biyu, ya aika a ko’ina cikin dukan ƙasar Isra’ila.

30 Dukan wanda ya ga haka sai ya ce, “Ba mu taɓa ganin irin wannan abu ba, ba a kuwa taɓa yin haka ba tun daga ranar da Isra’ilawa suka fito daga ƙasar Masar sai yau. Ku yi tunani, me za mu yi a kan wannan al’amari?”

Categories
L. MAH

L. MAH 20

Yaƙi da Mutanen Biliyaminu

1 Dukan jama’ar Isra’ila fa suka fito tun daga Dan a arewa har zuwa Biyer-sheba a kudu da kuma Gileyad daga gabas. Suka hallara gaba ɗaya a gaban Ubangiji a Mizfa.

2 Dukan shugabannin kabilar Isra’ila suna cikin wannan taron jama’ar Allah. Sojojin ƙafa yawansu ya kai dubu ɗari huɗu (400,000).

3 Mutanen Biliyaminu kuwa sun ji labari sauran Isra’ilawa sun haura zuwa Mizfa. Isra’ilawa suka tambayi Balawen suka ce, “Ka faɗa mana yadda wannan mugun abu ya auku.”

4 Balawe, mai ƙwarƙwarar da ka kashe, ya amsa ya ce, “Ni da ƙwarƙwarata muna biyo Gibeya ta Biliyaminu mu kwana.

5 Sai mutanen Gibeya suka kewaye gidan da nake da dare, suna neman kashe ni, da ba su same ni ba, sai suka yi wa ƙwarƙwarata faɗe har ya kai ta ga mutuwa.

6 Ni kuwa na ɗauki gawarta na yanyanka gunduwa gunduwa na aika cikin ƙasar gādon Isra’ila duka, gama waɗannan mutane sun aikata abin ƙyama da abin kunya ga dukan Isra’ila.

7 Dukanku nan Isra’ilawa ne, me za mu yi a kan wannan al’amari?”

8 Dukan jama’a kuwa suka tashi gaba ɗaya, suna cewa, “Daga cikinmu ba wanda zai koma alfarwarsa ko kuwa gidansa.

9 Wannan shi ne abin da za mu yi wa Gibeya, mu zaɓi waɗansunmu su fāɗa mata da yaƙi.

10 Kashi ɗaya daga goma na Isra’ilawa su ba da abinci ga sojoji. Sauran jama’a kuwa su je su hukunta Gibeya saboda muguntar da ta aikata cikin Isra’ila.”

11 Saboda haka dukan mutanen Isra’ila suka taru niyya ɗaya domin su fāɗa wa garin da yaƙi.

12 Kabilar Isra’ila kuwa suka aiki manzanni ga kabilar Biliyaminu suka ce, “Wace irin mugunta ce wannan da kuka aikata?

13 Yanzu sai ku ba da mutanen nan ‘yan iska da take cikin Gibeya don mu kashe su, mu kawar da mugunta daga cikin Isra’ila.” Amma mutanen Biliyaminu ba su kula da maganar ‘yan’uwansu, Isra’ilawa ba.

14 Mutanen Biliyaminu kuwa suka fita daga Gibeya gaba ɗaya domin su yi yaƙi da jama’ar Isra’ila.

15 A ran nan mutanen Biliyaminu suka tattaru daga garuruwansu, mutum dubu ashirin da shida (26,000). Banda waɗannan, sai da mazaunan Gibeya suka tara zaɓaɓɓun mutane ɗari bakwai.

16 Daga cikin waɗannan duka akwai zaɓaɓɓun mutane bakwai, bahagwai. Kowannensu yana iya ya baraci gashi guda da majajjawa ba kuskure.

17 Isra’ilawa kuwa banda kabilar Biliyaminu, suka tara mayaƙa dubu ɗari huɗu (400,000) horarru.

Yaƙi da Mutanen Biliyaminu

18 Isra’ilawa suka tashi suka tafi Betel. A can suka yi tambaya ga Allah suka ce, “Wace kabila ce daga cikinmu za ta fara faɗa wa kabilar Biliyaminu?”

Ubangiji ya ce, “Kabilar Yahuza ce za ta fara.”

19 Sa’an nan Isra’ilawa suka tashi da safe suka kafa sansani kusa da Gibeya.

20 Suka kuwa fita su yi yaƙi da mutanen Biliyaminu, suka jā dāgar yaƙi suna fuskantar Gibeya.

21 Mutanen Biliyaminu kuwa suka fito daga birnin suka hallakar da mutum dubu ashirin da biyu (22,000), daga cikin mutanen Isra’ila a ranar.

22-23 Mutanen Isra’ila suka tafi inda ake sujada suka yi makoki a gaban Ubangiji har zuwa dare. Suka tambaye shi suka ce, “Mu sāke zuwa domin mu yi yaƙi da ‘yan’uwanmu mutanen Biliyaminu?”

Ubangiji ya ce musu, “I, ku tafi.”

Saboda haka sai sojojin Isra’ilawa suka ƙarfafa, suka sāke jān dāga a inda suka jā ta dā.

24 Sai mutanen Isra’ila suka tafi su kara da mutanen Biliyaminu a rana ta biyu.

25 Mutanen Biliyaminu kuwa suka fito daga birnin suka hallakar da mutum dubu goma sha takwas (18,000) daga cikin Isra’ilawa. Dukan waɗannan da aka hallaka horarru ne.

26 Dukan rundunan Isra’ilawa suka haura zuwa Betel, suka yi makoki, suka zauna a gaban Ubangiji suka yi azumi har maraice. Sa’an nan suka miƙa wa Ubangiji hadayu na ƙonawa da na salama.

27-28 Suka sāke yin tambaya ga Ubangiji suka ce, “Mu sāke tafiya mu yi yaƙi da ‘yan’uwanmu, mutanen Biliyaminu, ko kuwa mu bari?”

Ubangiji kuwa ya ce musu, “Ku je, gama gobe zan ba da su gare ku.” A lokacin nan akwatin alkawari na Ubangiji yana nan. Finehas ɗan Ele’azara, ɗan Haruna, shi ne mai aiki a gabansa.

29 Isra’ilawa kuwa suka sa ‘yan kwanto kewaye da Gibeya.

30 Sa’an nan suka tafi su kara da mutanen Biliyaminu a rana ta uku. Suka jā dāgar yaƙi gaba da Gibeya kamar dā.

31 Mutanen Biliyaminu kuma suka fito, suka tasar musu. Aka jawo su nesa da birnin. Suka fara kashe Isra’ilawa kamar yadda suka yi a dā, suka kashe wajen mutum talatin a kan karauka wadda ta nufi Betel da wadda ta nufi Gibeya, da filaye.

32 Sai mutanen Biliyaminu suka ce, “Mun fatattake su kamar dā.”

Amma Isra’ilawa suka ce, “Mu gudu don mu jawo su nesa da birnin zuwa karauka.”

33 Isra’ilawa duka suka tashi daga wurin da suke, suka jā dāga a Ba’altamar. Mutanensu da suke kwanto a yammacin Gibeya suka fito.

34 Horarrun sojojin Isra’ila, su dubu goma (10,000), suka faɗa wa Gibeya. Yaƙi kuwa ya yi zafi, amma mutanen Biliyaminu ba su san masifa tana gab da su ba.

35 Ubangiji kuwa ya fatattake mutanen Biliyaminu a gaban Isra’ilawa. Isra’ilawa kuwa suka hallaka mutanen Biliyaminu dubu ashirin da biyar da ɗari ɗaya (25,100) a wannan rana, waɗannan duka kuwa mayaƙa ne.

36 Mutanen Biliyaminu kuwa suka gane an ci su da yaƙi.

Mutanen Isra’ila kuwa suka yi ta ja da baya daga mutanen Biliyaminu domin sun dogara ga mutanensu da suka yi wa Gibeya kwanto.

37 Sai ‘yan kwanto suka gaggauta suka faɗa wa Gibeya, suka kutsa suka kashe dukan waɗanda suke a birnin.

38 Alamar da mayaƙan Isra’ila da na ‘yan kwantonsu suka daidaita a tsakaninsu, ita ce murtukewar hayaƙi a cikin birnin.

39 Idan mutanen Isra’ila sun hangi hayaƙin, sai su juya su fāɗa wa mutanen Biliyaminu da yaƙi. Kafin alamar hayaƙin sai mutanen Biliyaminu suka fara kashe wa Isra’ilawa wajen mutum talatin. Suka ce, “Ai, suna shan ɗibga a hannunmu kamar yadda suka sha da fari.”

40 Amma sa’ad da alamar hayaƙin ta fara murtukewa a cikin birnin, sai mutanen Biliyaminu suka juya, suka duba, suka ga hayaƙi ya murtuke cikin birnin, ya yi sama.

41 Da mutanen Isra’ila suka juyo kansu, sai mutanen Biliyaminu suka tsorata, gama sun ga masifa ta auko musu.

42 Don haka suka juya suka kama gudu suka nufi hamada, amma ba su tsira ba. Aka datse su tsakanin ‘yan kwanto da sauran sojojin Isra’ilawa.

43 Suka yi wa mutanen Biliyaminu tarko, suka runtume su ba tsayawa tun daga Menuha har zuwa daura da Gibeya daga gabas.

44 Aka kashe jarumawan mutanen Biliyaminu mutum dubu goma sha takwas (18,000).

45 Sauran suka juya, suka gudu, suka nufi wajen hamada zuwa Dutsen Rimmon. A kan hanyoyi, aka kashe musu mutum dubu biyar. Aka kuma runtumi sauran da suka ragu har zuwa Gidom inda suka kashe mutum dubu biyu.

46 Mutanen Biliyaminu da aka kashe a ran nan dubu ashirin da biyar (25,000) ne. Dukansu kuwa jarumawa ne.

47 Amma mutum ɗari shida suka juya, suka gudu suka nufi hamada zuwa Dutsen Rimmon inda suka zauna har wata hu:du.

48 Mutanen Isra’ila kuma suka komo, suka fāɗa wa sauran mutanen Biliyaminu. Suka karkashe su, mutane, da dabbobi, da dukan abin da suka iske. Suka ƙone garuruwan wannan yankin ƙasa.