Categories
LUK

LUK 1

Gabatarwa

1 Tun da yake mutane da yawa sun ɗauka su tsara labarin waɗannan al’amura da suka tabbata a cikinmu,

2 daidai yadda waɗanda suke shaidu tun farkon al’amari, masu hidimar Maganar, suka rattaba mana,

3 da yake kuma na bi diddigin kowane abu daidai tun farko, ni ma dai na ga ya kyautu in rubuta maka su bi da bi, ya mafifici Tiyofalas,

4 domin kă san ingancin maganar da aka sanar da kai baki da baki.

An Yi Faɗin Haihuwar Yahaya Maibaftisma

5 A zamanin Hirudus, Sarkin Yahudiya, an yi wani firist mai suna Zakariya, na ƙungiyar Abaija. Yana auren wata a cikin zuriyar Haruna, sunanta Alisabatu.

6 Dukansu biyu kuwa masu adalci ne a gaban Allah, suna bin umarnin Ubangiji da farillansa duka da halin rashin zargi.

7 Amma ba su da ɗa, don Alisabatu bakararriya ce, dukansu biyu kuma sun tsufa.

8 Ana nan, wata rana Zakariya na kan hidima tasa ta firist, a sa’ad da hidimar ta kewayo kan ƙungiyarsu,

9 bisa ga al’adar hidimar firistoci, sai kuri’a ta nuna shi ne mai shiga Haikalin Ubangiji, ya ƙona turare.

10 A lokacin ƙona turare kuwa duk taron jama’a suna waje, suna addu’a,

11 sai wani mala’ikan Ubangiji ya bayyana gare shi, yana tsaye a dama da bagadin ƙona turare.

12 Da Zakariya ya gan shi ya firgita, tsoro ya kama shi.

13 Amma mala’ikan ya ce masa, “Kada ka ji tsoro Zakariya, an karɓi addu’arka, matarka Alisabatu za ta haifa maka ɗa, za ka kuma sa masa suna Yahaya.

14 Za ka yi murna da farin ciki,

Mutane da yawa kuma za su yi farin ciki da haihuwa tasa.

15 Domin zai zama mai girma a wurin Ubangiji,

Ba kuwa zai sha ruwan inabi ko wani abu mai sa maye ba.

Za a cika shi da Ruhu Mai Tsarki

Tun yana cikin uwa tasa.

16 Zai kuma juyo da Isra’ilawa da yawa ga Ubangiji Allahnsu.

17 Zai riga shi gaba cikin ruhu da iko irin na Iliya.

Yă mai da hankalin iyaye a kan ‘ya’yansu,

Yă kuma juyo da marasa biyayya su bi hikimar adalai,

Ya tanada wa Ubangiji jama’a, ya same su a shirye.”

18 Sai Zakariya ya ce wa mala’ikan, “Ta ƙaƙa zan san haka? Ga ni tsoho, maiɗakina kuma ta kwana biyu.”

19 Sai mala’ikan ya amsa ya ce, “Ni ne Jibra’ilu da yake tsaye a gaban Allah. An aiko ni ne in yi maka magana, in kuma yi maka wannan albishir.

20 To, ga shi, za ka bebance, ba za ka iya magana ba, sai a ran da al’amuran nan suka auku, don ba ka gaskata maganata ba, za a kuwa cika ta a lokacinta.”

21 Jama’a suna ta jiran Zakariya, suna mamakin jinkirinsa a Haikali.

22 Da ya fito, ya kāsa yi musu magana. Sai suka gane lalle an yi masa wahayi ne a Haikalin. Sai ya riƙa yi musu nuni, amma ba ya magana.

23 Sa’ad da kuma kwanakin hidimarsa suka cika, ya koma gida.

24 Bayan kwanakin nan mata tasa Alisabatu ta yi ciki. Sai ta riƙa ɓuya har wata biyar, tana cewa,

25 “Haka Ubangiji ya yi mini a kwanakin da ya dube ni da rahama, domin yă kawar mini da wulakanci a wurin mutane.”

An Yi Faɗin Haihuwar Yesu

26 A wata na shida Allah ya aiko mala’ika Jibra’ilu zuwa wani gari a ƙasar Galili, wai shi Nazarat,

27 gun wata budurwa da aka ba da ita ga wani mutum mai suna Yusufu, na zuriyar Dawuda, sunan budurwar kuwa Maryamu.

28 Sai mala’ikan ya je wurinta, ya ce, “Salama alaikun, yake zaɓaɓɓiya, Ubangiji yana tare da ke!”

29 Amma ta damu ƙwarai da maganar, ta yi ta tunani ko wannan wace irin gaisuwa ce.

30 Mala’ikan kuma ya ce mata, “Kada ki ji tsoro, Maryamu, kin sami tagomashi a wurin Allah.

31 Ga shi kuma, za ki yi ciki, ki haifi ɗa, ki kuma sa masa suna Yesu.

32 Zai zama mai girma, za a kuma kira shi Ɗan Maɗaukaki.

Ubangiji Allah zai ba shi kursiyin ubansa Dawuda,

33 Zai kuma mallaki zuriyar Yakubu har abada,

Mulkinsa kuwa ba shi da matuƙa.”

34 Sai Maryamu ta ce wa mala’ikan, “Ƙaƙa wannan zai yiwu, tun da yake ba a kai ni ɗaki ba?”

35 Mala’ikan ya amsa mata ya ce,

“Ruhu Mai Tsarki zai sauko miki,

Ikon Maɗaukaki kuma zai lulluɓe ki.

Saboda haka Mai Tsarkin nan da za a haifa, za a kira shi Ɗan Allah.

36 Ga shi kuma, ‘yar’uwarki Alisabatu ma ta yi cikin ɗa namiji da tsufanta, wannan kuwa shi ne watanta na shaida, ita da ake ce wa bakararriya.

37 Ba wata faɗar Allah da za ta kasa cika.”

38 Sai Maryamu ta ce, “To, ga shi, ni baiwar Ubangiji ce, yă zama mini yadda ka faɗa.” Sai mala’ikan ya tashi daga gare ta.

Maryamu ta Ziyarci Alisabatu

39 A kwanakin nan Maryamu ta tashi da hanzari, ta tafi wata ƙasa mai duwatsu, zuwa wani gari na ƙasar Yahuza.

40 Ta shiga gidan Zakariya ta gai da Alisabatu.

41 Sai ya zamana da Alisabatu ta ji gaisuwar Maryamu, jariri ya motsa da ƙarfi a cikinta. Aka kuwa cika Alisabatu da Ruhu Mai Tsarki,

42 har ta tā da murya da ƙarfi, ta ce, “Ke mai albarka ce a cikin mata, ɗan cikinki kuma mai albarka ne!

43 Ta yaya wannan alheri ya same ni, har da uwar Ubangijina za ta zo gare ni?

44 Domin kuwa da jin muryarki ta gaisuwa a kunnena, sai jaririn ya motsa da ƙarfi a cikina domin farin ciki.

45 Albarka tā tabbata ga wadda ta gaskata, domin za a cika abubuwan da Ubangiji ya aiko a faɗa mata.”

Waƙar Maryamu

46 Sai Maryamu ta ce,

“Zuciyata na ɗaukaka shi, Ubangiji,

47 Allah Mai Cetona, da shi ruhuna yake ta farin ciki,

48 Domin fa shi ya dubi ƙasƙancin baiwa tasa.

Ga shi, jama’a ta dukan zamanai,

Za su ce mini mai albarka ce nan gaba.

49 Domin fa shi da yake Mai Iko,

Manyan al’amura ya yi mini,

Sunansa labudda mai tsarki ne.

50 Daga zamanai ya zuwa wani zamani,

Jinƙansa yana ga waɗanda suke tsoronsa.

51 Manyan ayyuka da ya yi,

Masu girmankai, su da dabarbarunsu ya warwatsa.

52 Ya firfitar da sarakuna a sarauta,

Ya ɗaukaka ƙasƙantattu.

53 Mayunwata ya ƙosar da abubuwan alheri,

Mawadata kuwa ya sallame su hannu wofi.

54 Ya taimaka wa baransa Isra’ila,

Domin yana tunawa da jinƙansa.

55 Ya cika faɗarsa ga kakanninmu,

Ga Ibrahim da zuriyarsa, har abada.”

56 Maryamu kuma ta zauna tare da Alisabatu wajen wata uku, sa’an nan ta koma gida.

Haihuwar Yahaya Maibaftisma

57 To, lokacin Alisabatu na haihuwa ya yi, ta kuwa haifi ɗa namiji.

58 Sai maƙwabta da ‘yan’uwanta suka ji yadda Ubangiji ya ji ƙanta ƙwarai, har suka taya ta farin ciki.

59 Sai ya zamana a rana ta takwas suka zo yi wa ɗan yaron kaciya. A dā za su sa masa sunan ubansa, Zakariya,

60 amma uwa tasa ta ce, “A’a, Yahaya za a sa masa.”

61 Sai suka ce mata, “Ai kuwa, ba wani ɗan’uwanku mai suna haka.”

62 Sai suka alamta wa ubansa, suna neman sunan da yake so a sa masa.

63 Sai ya nema a ba shi allo, sa’an nan ya rubuta, “Sunansa Yahaya.” Duka suka yi mamaki.

64 Nan da nan ya sami baki, kwaɗon harshensa ya saku, ya fara magana, yana yabon Allah.

65 Sai tsoro ya kama dukan maƙwabtansu. Aka yi ta baza labarin duk waɗannan al’amura ko’ina a dukan ƙasa mai duwatsu ta Yahudiya.

66 Duk waɗanda suka ji kuwa suka riƙe a zuciyarsu, suna cewa, “Me ke nan ɗan yaron nan zai zama?” Gama ikon Ubangiji yana tare da shi.

Waƙar Zakariya

67 Sai aka cika ubansa Zakariya da Ruhu Mai Tsarki, ya yi annabci, ya ce,

68 “Ubangiji Allahn Isra’ila,

A gare shi ne lalle yabo yake tabbata,

Domin ya kula, ya yi wa jama’a tasa fansa.

69 Ya ta da Mai Ceto mai iko dominmu,

Daga zuriyar baransa Dawuda.

70 Yadda tuntuni ya faɗa ta bakunan

Annabawa nasa tsarkakan nan,

71 Yă cece mu daga abokan gābanmu,

Har ma daga dukan maƙiyanmu.

72 Domin nuna jinƙai ne ga kakanninmu,

Ya tuna da alkawarinsa mai tsarkin nan.

73 Shi ne rantsuwan nan wadda ya yi wa ubanmu Ibrahim,

74 Domin yana cetonmu daga abokan gābanmu,

Mu bauta masa ba da jin tsoro ba,

75 Sai dai da tsarki da adalci a gabansa,

Dukan iyakar kwanakin nan namu.

76 Kai kuma, ɗan yarona, za a ce da kai annabin Maɗaukaki,

Gama za ka riga Ubangiji gaba,

Domin ka shisshirya hanyoyinsa,

77 Kă sanar da ceto ga jama’a tasa,

Wato ta samun gafarar zunubansu,

78 Saboda tsananin jinƙai na Allahnmu,

Daga Sama hasken asubahi zai ɓullo mana,

Daga can Sama ne fa zai keto mana,

79 Domin yă haskaka na zaune cikin duhu,

Da waɗanda suke zaune a bakin mutuwa,

Domin ya bishe mu a hanyar salama.”

80 Sai ɗan yaron ya girma, ya ƙarfafa a ruhu. Ya kuwa zauna a jeji har ranar bayyanarsa ga Isra’ila.

Categories
LUK

LUK 2

Haihuwar Yesu

1 A kwanakin nan Kaisar Augustas ya yi shela, cewa a rubuta dukkan mutanen da suke ƙarƙashin mulkinsa.

2 Wannan shi ne ƙirga na fari da aka yi a zamanin Kiriniyas, mai mulkin ƙasar Suriya.

3 Kowa sai ya tafi garinsu a rubuta shi.

4 Yusufu shi ma ya tashi daga birnin Nazarat, a ƙasar Galili, ya tafi ƙasar Yahudiya, ya je birnin Dawuda, da ake kira Baitalami (domin shi daga gidan Dawuda ne, na cikin zuriyarsa),

5 don a rubuta shi, duk da Maryamu tashinsa, wadda take kuma da ciki.

6 Sa’ad da suke can kuwa, sai lokacin haihuwarta ya yi.

7 Sai ta haifi ɗanta na fari, ta rufi shi da zanen goyo, ta kuma kwantar da shi a wani komi dabbobi, don ba su sami ɗaki a masaukin ba.

Makiyaya da Mala’iku

8 A wannan yankin ƙasa kuwa waɗansu makiyaya suna kwana a filin Allah, suna tsaron garken tumakinsu da dad dare.

9 Sai ga wani mala’ikan Ubangiji tsaye kusa da su, ɗaukakar Ubangiji kuma ta haskaka kewayensu, har suka tsorata gaya,

10 Sai mala’ikan ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ga shi, albishir na kawo muku na farin ciki mai yawa, wanda zai zama na dukan mutane.

11 Domin yau an haifa muku Mai Ceto a birnin Dawuda, wanda yake shi ne Almasihu, Ubangiji.

12 Ga alamar da za ku gani, za ku sami jariri rufe da zanen goyo, kwance a komin dabbobi.”

13 Ba labari sai ga taron rundunar Sama tare da mala’ikan nan, suna yabon Allah, suna cewa,

14 “Ɗaukaka ga Allah ta tabbata, can cikin Sama mafi ɗaukaka.

A duniya salama ta tabbata, ga mutanen da yake murna da su matuƙa.”

15 Da mala’iku suka tafi daga gare su suka koma Sama, sai makiyayan suka ce wa juna, “Mu tafi Baitalami yanzu, mu ga abin nan da ya faru, wanda Ubangiji ya sanar da mu.”

16 Sai suka tafi da hanzari, suka sami Maryamu da Yusufu, da kuma jaririn kwance a komin dabbobi.

17 Da suka gan shi, suka bayyana maganar da aka faɗa musu game da wannan ɗan yaro.

18 Duk waɗanda suka ji kuma, suka yi ta al’ajabin abin da makiyayan nan suka faɗa musu.

19 Maryamu kuwa sai ta riƙe duk abubuwan da aka faɗa, tana biya su a zuci.

20 Makiyayan suka koma, suna ta ɗaukaka Allah, suna yabonsa, saboda duk abin da suka ji, suka kuma gani, yadda aka gaya musu.

Kaciyar Yesu

21 Da rana ta takwas ta kewayo da za a yi masa kaciya, aka sa masa suna Yesu, wato sunan da mala’ika ya faɗa kafin ya zauna a ciki.

Miƙa Yesu a Haikali

22 Da kwanakin tsarkakewarsu suka cika bisa ga Shari’ar Musa, suka kawo shi Urushalima, su miƙa shi ga Ubangiji

23 (kamar dai yadda yake a rubuce a Shari’ar Ubangiji cewa, “Duk ɗan farin da aka haifa, za a ce da shi tsattsarka ne Ubangiji”),

24 su kuma yi hadaya bisa ga abin da aka faɗa a Shari’ar Ubangiji cewa, “Kurciyoyi biyu, ko kuwa ‘yan shila biyu.”

25 To, akwai wani mutum a Urushalima, mai suna Saminu, adali, mai bautar Allah, yana kuma ɗokin ganin ta’aziyyar Isra’ila. Ruhu Mai Tsarki kuwa yana tare da shi.

26 Ruhu Mai Tsarki kuwa ya riga ya bayyana masa, cewa ba zai mutu ba sai ya ga Almasihun Ubangiji.

27 Ruhu na iza shi, sai ya shiga Haikalin. Da iyayen suka shigo da ɗan yaron nan Yesu, su yi masa yadda ka’idar Shari’ar ta ce,

28 sai Saminu ya rungume shi, ya yi wa Allah godiya, ya ce,

29 “Yanzu kam, ya Mamallaki,

Sai ka sallami bawanka lafiya,

Bisa ga abin da ka faɗa,

30 Don na ga cetonka zahiri,

31 Da ka shirya a gaban kabilai duka,

32 Haske mai bayyana wa alummai hanyarka,

Da kuma ɗaukakar jama’arka Isra’ila.”

33 Uwa tasa da ubansa kuwa suna mamakin abin da aka faɗa game da shi,

34 Sai Saminu ya sa musu albarka, ya ce wa Maryamu uwar Yesu,

“Kin ga wannan yaro, shi aka sa ya zama sanadin faɗuwar waɗansu, tashin waɗansu kuma da yawa cikin Isra’ila,

Zai kuma zama alama wadda ake kushenta,

35 Domin tunanin zukata da yawa su bayyana.

I, ke ma, takobi zai tsaga zuciyarki.”

36 Akwai kuma wata annabiya, mai suna Hannatu, ‘yar Fanuyila, na kabilar Ashiru. Ta kuwa tsufa ƙwarai, ta yi zaman aure shekara bakwai bayan ɗaukanta na budurci,

37 da mijinta ya mutu kuma ta yi zaman gwauranci har shekara tamanin da huɗu. Ba ta rabuwa da Haikalin, tana bauta wa Allah dare da rana ta wurin yin addu’a da azumi.

38 Nan take ita ma ta zo, ta yi wa Allah godiya, ta kuma yi maganar ɗan yaron nan ga dukan masu sauraron fansar Urushalima.

Komawa Nazarat

39 Bayan sun ƙare kome da kome bisa ga Shari’ar Ubangiji, sai suka koma ƙasar Galili suka tafi garinsu Nazarat.

40 Ɗan yaron kuwa ya girma, ya kawo ƙarfi, yana mai matuƙar hikima. Alherin Allah kuwa yana tare da shi.

Yesu, Ɗan Saurayi, ya Shiga Haikali

41 To, iyayensa sukan je Urushalima kowace shekara a lokacin Idin Ƙetarewa.

42 Da ya shekara goma sha biyu, sai suka tafi tare da shi bisa ga al’adarsu a lokacin Idi.

43 Da aka gama idin kuma, suna cikin komowa, sai yaron, wato Yesu, ya tsaya a Urushalima, ba da sanin iyayensa ba.

44 Su kuwa suka yi ta tafiya yini guda, suna zaton yana cikin ayari. Sai suka yi ta cigiyarsa cikin ‘yan’uwansu da idon sani.

45 Da ba su same shi ba, suka koma Urushalima, suna ta cigiyarsa.

46 Sai kuma a rana uku suka same shi a Haikalin zaune a tsakiyar malamai, yana sauraronsu, yana kuma yi musu tambayoyi.

47 Duk waɗanda suka ji shi kuwa suka yi al’ajabin irin fahimtarsa da amsoshinsa.

48 Da suka gan shi suka yi mamaki, sai uwa tasa ta ce masa, “Ya kai ɗana, yaya ka yi mana haka? Ga shi nan, ni da babanka muna ta nemanka duk ranmu a ɓace.”

49 Sai ya ce musu, “Me ya sa kuka yi ta nemana? Ashe, ba ku sani wajibi ne in yi sha’anin Ubana ba?”

50 Amma ba su fahimci maganar da ya yi musu ba.

51 Sai ya koma Nazarat tare da su, yana yi musu biyayya. Uwa tasa kuwa na riƙe da dukan abubuwan nan a ranta.

52 Yesu kuwa ya yi ta ƙaruwa da hikima, da girma, da kuma tagomashi wurin Allah da mutane.

Categories
LUK

LUK 3

Wa’azin Yahaya Maibaftisma

1 A shekara ta goma sha biyar ta mulkin Kaisar Tibariyas, Buntus Bilatus yana mulkin Yahudiya, Hirudus yana sarautar Galili, ɗan’uwansa Filibus yana sarauta Ituriya da Tarakunitas, Lisaniyas kuma yana sarautar Abiliya,

2 a zamanin da Hanana da Kayafa suke manyan firistoci, Maganar Allah ta zaike wa Yahaya ɗan Zakariya a jeji.

3 Sai ya zaga duk lardin bakin Kogin Urdun, yana wa’azi, cewa mutane su tuba a yi musu baftisma, domin a gafarta musu zunubansu,

4 yadda yake a rubuce a Littafin Annabi Ishaya cewa,

“Muryar mai kira a jeji tana cewa,

Ku shirya wa Ubangiji tafarki,

Ku miƙe hanyoyinsa,

5 Za a cike kowane kwari,

Kowane dutse da kowane tsauni za a baje su.

Za a miƙe karkatattun wurare,

Za a bi da hanyoyin da ba su biyu ba.

6 Dukkan ‘yan adam kuma za su ga ceton Allah.”

7 Saboda haka, Yahaya ya ce wa taron jama’ar da yake zuwa domin ya yi musu baftisma, “Ku macizai! Wa ya gargaɗe ku ku guje wa fushin nan mai zuwa?

8 Ku yi aikin da zai nuna tubanku, kada ma ku ko fara cewa a ranku Ibrahim ne ubanku. Ina dai gaya muku Allah yana da iko ya halitta wa Ibrahim ‘ya’ya daga duwatsun nan.

9 Ko yanzu ma an ɗora bakin gatari a gindin itatuwa. Saboda haka duk itacen da bai yi ‘ya’ya masu kyau ba, sai a sare shi, a jefa a wuta.”

10 Sai taron suka tambaye shi suka ce, “Me za mu yi ke nan?”

11 Ya amsa musu ya ce, “Duk mai taguwa biyu, ya raba da marar ita, mai abinci ma haka.”

12 Masu karɓar haraji ma suka zo a yi musu baftisma, suka ce masa, “Malam, me za mu yi?”

13 Ya ce musu, “Kada ku karɓi fiye da abin da aka umarce ku.”

14 Waɗansu soja ma suka tambaye shi, “To, mu fa, me za mu yi?” Sai ya ce musu, “Kada ku yi wa kowa ƙwace ko ƙazafi. Ku dai dangana da albashinku.”

15 Da yake mutane duk sun zaƙu, kowa yana wuswasi a ransa a game da Yahaya, ko watakila shi ne Almasihu,

16 sai Yahaya ya amsa wa dukansu ya ce, “Ni kam, da ruwa nake yi muku baftisma, amma wani yana zuwa wanda ya fi ni girma, wanda ko maɓallin takalminsa ma ban isa in ɓalle ba. Shi ne zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki, da kuma wuta.

17 Ƙwaryar shiƙarsa tana hannunsa, zai kuwa share masussukarsa sarai sarai, ya taro alkama ya sa a rumbunsa, amma ɓuntun sai ya ƙone shi a wuta marar mutuwa.”

18 Ta haka, da waɗansu gargaɗi masu yawa, Yahaya ya yi wa jama’a bishara.

19 Amma sarki Hirudus, wanda Yahaya ya tsawata wa a kan maganar Hirudiya, matar ɗan’uwansa, da kuma dukan mugayen ayyukan da ya yi,

20 sai ya ƙara da kulle Yahaya a kurkuku.

An Yi wa Yesu Baftisma

21 To, da aka yi wa dukan mutane baftisma, Yesu ma aka yi masa baftisma, yana addu’a ke nan, sai sama ta dāre,

22 Ruhu Mai Tsarki ya sauko masa da wata kama, kamar kurciya. Sai aka ji wata murya daga Sama ta ce, “Kai ne Ɗana ƙaunataccena, ina farin ciki da kai ƙwarai,”

Asalin Yesu

23 Yesu kuwa sa’ad da ya fara koyarwa, yana da shekara wajen talatin. An ɗauke shi a kan, wai shi ɗan Yusufu ne, wanda yake ɗan Heli,

24 Heli ɗan Matat, Matat ɗan Lawi, Lawi ɗan Malki, Malki ɗan Yanna, Yanna ɗan Yusufu,

25 Yusufu ɗan Matatiya, Matatiya ɗan Amos, Amos ɗan Nahum, Nahum ɗan Azaliya, Azaliya ɗan Najaya,

26 Najaya ɗan Ma’ata, Ma’ata ɗan Matatiya, Matatiya ɗan Shimeya, Shimeya ɗan Yusufu, Yusufu ɗan Yahuza,

27 Yahuza ɗan Yowana, Yowana ɗan Refaya, Refaya ɗan Zarubabel, Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, Sheyaltiyel ɗan Niri,

28 Niri ɗan Malki, Malki ɗan Addi, Addi ɗan Kosama, Kosama ɗan Almadama, Almadama ɗan Er,

29 Er ɗan Yosi, Yosi ɗan Eliyezer, Eliyezar ɗan Yorima, Yorima ɗan Matat, Matat ɗan Lawi,

30 Lawi ɗan Saminu, Saminu ɗan Yahuza, Yahuza ɗan Yusufu, Yusufu ɗan Yonana, Yonana ɗan Eliyakim,

31 Eliyakim ɗan Malaya, Malaya ɗan Mainana, Mainana ɗan Matata, Matata ɗan Natan, Natan ɗan Dawuda,

32 Dawuda ɗan Yesse, Yesse ɗan Obida, Obida ɗan Bo’aza, Bo’aza ɗan Salmon, Salmon ɗan Nashon,

33 Nashon ɗan Amminadab, Amminadab ɗan Aram, Aram ɗan Hesruna, Hesruna ɗan Feresa, Feresa ɗan Yahuza,

34 Yahuza ɗan Yakubu, Yakubu ɗan Ishaku, Ishaku ɗan Ibrahim, Ibrahim ɗan Tera, Tera ɗan Nahor,

35 Nahor ɗan Serug, Serug ɗan Reyu, Reyu ɗan Feleg, Feleg ɗan Eber, Eber ɗan Shela,

36 Shela ɗan Kenan, Kenan ɗan Arfakshad, Arfakshad ɗan Shem, Shem ɗan Nuhu, Nuhu ɗan Lamek,

37 Lamek ɗan Metusela, Metusela ɗan Anuhu, Anuhu ɗan Yared, Yared ɗan Mahalel, Mahalel ɗan Kenan,

38 Kenan ɗan Enosh, Enosh ɗan Shitu, Shitu ɗan Adamu, Adamu kuma na Allah.

Categories
LUK

LUK 4

Shaiɗan Ya Gwada Yesu

1 Yesu kuma cike da Ruhu Mai Tsarki sai ya dawo daga Kogin Urdun. Ruhu na iza shi zuwa jeji,

2 har kwana arba’in, Iblis yana gwada shi. A kwanakin nan bai ci kome ba. Da suka ƙare kuwa ya ji yunwa.

3 Iblis ya ce masa, “In dai kai Ɗan Allah ne, ka umarci dutsen nan ya zama gurasa,”

4 Yesu ya amsa masa ya ce, “A rubuce yake, ‘Ba da gurasa kaɗai mutum zai rayu ba.’ ”

5 Sai Iblis ya kai shi wani wuri a bisa, ya nunnuna masa dukkan mulkokin duniya a ƙyiftawar ido.

6 Iblis ya ce masa, “Kai zan bai wa ikon duk waɗannan, da ɗaukakarsu, don ni aka danƙa wa, nakan kuma bayar ga duk wanda na ga dama.

7 In kuwa za ka yi mini sujada, duk su zama naka.”

8 Yesu ya amsa masa ya ce, “A rubuce yake cewa,

‘Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada,

Shi kaɗai za ka bauta wa.’ ”

9 Sai kuma ya kai shi Urushalima, ya ɗora shi can kan tsororuwar Haikali, ya ce masa, “In dai kai Ɗan Allah ne, to, dira ƙasa daga nan,

10 don a rubuce yake cewa,

‘Zai yi wa mala’ikunsa umarni game da kai, su kiyaye ka,’

11 da kuma

‘Za su tallafe ka,

Don kada ka yi tuntuɓe da dutse.’ ”

12 Sai Yesu ya amsa masa ya ce, “Ai kuwa an ce, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’ ”

13 Bayan da Iblis ya gama irin dukan gwaje-gwajensa, ya rabu da shi ɗan lokaci tukuna.

Yesu Ya Fara Hidima a Galili

14 Yesu ya koma ƙasar Galili, ikon Ruhu yana tare da shi. Labarinsa ya bazu a dukan kewayen.

15 Ya yi ta koyarwa a majami’unsu, duk ana girmama shi.

An Ƙi Yesu a Nazarat

16 Ya zo Nazarat inda aka rene shi. Ya shiga majami’a a ran Asabar kamar yadda ya saba. Sai ya miƙe domin ya yi karatu.

17 Aka miƙa masa Littafin Annabi Ishaya, ya buɗe littafin, ya sami inda aka rubuta cewa,

18 “Ruhun Ubangiji yana tare da ni,

Domin yā shafe ni in yi wa matalauta bishara.

Ya aiko ni in yi shelar saki ga ɗaurarru,

In kuma buɗe wa makafi ido,

In kuma ‘yanta waɗanda suke a danne,

19 In yi shelar zamanin samun karɓuwa ga Ubangiji.”

20 Ya rufe littafin ya mayar wa mai hidima, ya zauna. Duk waɗanda suke cikin majami’a suka zuba masa ido.

21 Sai ya fara ce musu, “Yau Nassin nan ya cika a kunnenku.”

22 Duk suka yabe shi, suna mamakin maganarsa ta alheri da ya faɗa, har suka ce, “Ashe, wannan ba ɗan Yusufu ba ne?”

23 Yesu ya ce musu, “Lalle za ku faɗa mini karin maganan nan, ‘Likita, warkar da kanka.’ Za ku kuma ce mini, ‘Duk abin da muka ji ka yi a Kafarnahum, ka yi a nan garinku mana.’ ”

24 Ya ce kuma, “Hakika, ina gaya muku, ba annabin da yake yardajje a garinsu.

25 Amma gaskiya nake gaya muku, a zamanin Iliya akwai mata gwauraye da yawa a Isra’ila, wato a lokacin da aka hana ruwan sama har shekara uku da wata shida, sa’ad da babbar yunwa ta game dukan ƙasar.

26 Duk da haka ba a aiki Iliya gun ko ɗaya daga cikinsu ba, sai ga wata mace kaɗai a Zarifat ta ƙasar Sidon wadda mijinta ya mutu.

27 A zamanin Annabi Elisha kuma akwai kutare da yawa a Isra’ila, ba kuwa ɗayansu da aka tsarkake sai Na’aman, mutumin Suriya, kaɗai.”

28 Da suka ji haka, duk waɗanda suke a majami’a suka husata ƙwarai.

29 Sai suka tashi suka fitar da shi bayan gari, har suka kai shi goshin dutsen da aka gina garinsu a kai, don su jefa shi ƙasa.

30 Amma ya ratsa ta tsakiyarsu, ya yi tafiyarsa.

Mai Baƙin Aljan

31 Sai ya tafi Kafarnahum, wani gari a ƙasar Galili, yana koya musu ran Asabar.

32 Suka yi mamakin koyarwarsa domin magana tasa da hakikancewa take.

33 A majami’ar kuwa akwai wani mutum mai baƙin aljan. Sai ya ta da murya da ƙarfi ya ce,

34 “Wayyo! Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne ka hallaka mu? Na san ko wane ne kai, Mai Tsarkin nan ne kai na Allah.”

35 Sai Yesu ya kwaɓe shi ya ce, “Shiru! Rabu da shi!” Bayan da aljanin ya fyaɗa shi ƙasa a tsakiyarsu, ya rabu da shi, bai kuwa cuce shi ba.

36 Sai mamaki ya kama su duka, suna ce wa juna, “Wannan wace irin magana ce? Ga shi, da tabbatarwa, da gabagaɗi kuma yake umartar baƙaƙen aljannu, suna kuwa fita.”

37 Labarinsa duk ya bazu ko’ina a kewayen ƙasar.

Yesu Ya Warkar da Surukar Bitrus

38 Sai ya tashi daga majami’a, ya shiga gidan Bitrus. Surukar Bitrus kuwa tana fama da mugun zazzaɓi, sai suka roƙe shi saboda ita.

39 Sai ya tsaya a kanta, ya tsawata wa zazzaɓin, ya kuwa sake ta. Nan take ta tashi ta yi musu hidima.

Yesu Ya Warkar da Mutane da yawa da Maraice

40 A daidai fāɗuwar rana, duk waɗanda suke da marasa lafiya, masu cuta iri iri, suka kakkawo su wurinsa. Sai ya ɗaɗɗora wa kowannensu hannu, ya warkar da su.

41 Aljannu kuma suka fita daga mutane da yawa, suna ihu suna cewa, “Kai Ɗan Allah ne!” Amma ya tsawata musu, ya hana su magana, don sun sani shi ne Almasihu.

Yesu Ya Tafi Yin Wa’azi

42 Da gari ya waye ya fita, ya tafi wani wurin inda ba kowa. Sai taro masu yawa suka yi ta nemansa, suka je wurinsa. Sonsu ne su tsaishe shi, don kada ya tashi daga gare su,

43 amma ya ce musu, “Lalle ne in yi wa sauran garuruwa bisharar Mulkin Allah, domin saboda wannan nufi ne aka aiko ni.”

44 Sai ya yi ta yin wa’azi a majami’un ƙasar Galili.

Categories
LUK

LUK 5

An Kama Kifi Jingim

1 Wata rana taro suna matsarsa domin su ji Maganar Allah, shi kuwa yana tsaye a bakin Tekun Janisarata,

2 sai ya hangi ƙananan jirage biyu a bakin tekun, masuntan kuwa sun fita daga cikinsu, suna wankin tarunansu.

3 Sai ya shiga ɗaya jirgin, wanda yake na Bitrus, ya roƙe shi ya ɗan zakuɗa da jirgin daga bakin gaci. Sai ya zauna ya yi ta koya wa taro masu yawa daga jirgin.

4 Da ya gama magana, ya ce wa Bitrus, “Zakuɗa da jirgin zuwa wuri mai zurfi, ku saki tarunanku, ku janyo kifi.”

5 Bitrus ya amsa masa ya ce, “Ya Maigida, dare farai muna wahala, ba mu kama kome ba, amma tun da ka yi magana zan saki tarunan.”

6 Da suka yi haka kuwa, suka kamo kifi jingim, har ma tarunansu suka fara kecewa.

7 Sai suka yafato abokan aikinsu a ɗaya jirgin su zo su taimake su. Suka kuwa zo, suka ciccika jiragen nan duka biyu kamar sa nutse.

8 Da Bitrus ya ga haka, sai ya fāɗi a gaban Yesu ya ce. “Ya Ubangiji, wane ni da za ka tsaya kusa da ni, domin ni mutum ne mai zunubi.”

9 Domin shi da waɗanda suke tare da shi duka, mamaki ya kama su saboda kifin nan da suka janyo,

10 haka ma Yakubu da Yahaya ‘ya’yan Zabadi, abokan sabgar Bitrus. Sai Yesu ya ce wa Bitrus, “Kada ka ji tsoro. Nan gaba mutane za ka riƙa kamowa.”

11 Da suka kawo jiragensu gaci, suka bar kome duka suka bi shi.

Yesu Ya Warkar da Kuturu

12 Wata rana Yesu na ɗaya daga cikin garuruwan nan, sai ga wani mutum wanda kuturta ta ci ƙarfinsa ya zo. Da ya ga Yesu ya fāɗi a gabansa, ya roƙe shi ya ce, “Ya Ubangiji, in dai ka yarda kana da ikon tsarkake ni.”

13 Sai Yesu ya miƙa hannu, ya taɓa shi, ya ce, “Na yarda, ka tsarkaka.” Nan take sai kuturtar ta rabu da shi.

14 Yesu ya kwaɓe shi kada ya gaya wa kowa, ya ce, “Sai dai ka je wurin firist ya gan ka, ka kuma yi hadaya saboda tsarkakewarka, domin tabbatarwa a gare su, kamar yadda Musa ya umarta.”

15 Amma duk da haka labarinsa sai ƙara yaɗuwa yake yi, har taro masu yawan gaske suka yi ta zuwa domin su saurare shi, a kuma warkar da su daga rashin lafiyarsu.

16 Amma shi, sai ya riƙa keɓanta a wuraren da ba kowa, yana addu’a.

Yesu ya Warkar da Shanyayye

17 Wata rana na koyarwa, waɗansu Farisiyawa kuwa da masanan Attaura da suka fito daga kowane gari na ƙasar Galili, da na ƙasar Yahudiya, daga kuma Urushalima, suna nan a zaune. Ikon Ubangiji na warkarwa kuwa yana nan.

18 Sai ga waɗansu mutane ɗauke da wani shanyayye a kan shimfiɗa, suna ƙoƙari su shigar da shi su ajiye shi a gaban Yesu.

19 Da suka kasa samun hanyar shigar da shi saboda taro, suka hau a kan soron, suka zura shi ta tsakanin rufin soron duk da shimfiɗarsa, suka ajiye shi a tsakiyar jama’a a gaban Yesu.

20 Da Yesu ya ga bangaskiyarsu sai ya ce, “Malam, an gafarta maka zunubanka.”

21 Sai malaman Attaura da Farisiyawa suka fara wuswasi cewa, “Wane ne wannan da yake maganar saɓo? Wa yake iya gafarta zunubi banda Allah shi kaɗai?”

22 Da Yesu ya gane wuswasinsu, ya amsa musu ya ce, “Don me kuke wuswasi haka a zuciyarku?

23 Wanne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuwa a ce, ‘Tashi, ka yi tafiya’?

24 Amma domin ku sakankance Ɗan Mutum na da ikon gafarta zunubi a duniya”, sai ya ce wa shanyayyen, “Na ce maka, tashi, ka ɗauki shimfiɗarka, ka tafi gida.”

25 Nan take ya tashi a gaban idonsu, ya ɗauki abin kwanciyarsa, ya tafi gida, yana ɗaukaka Allah.

26 Sai suka yi mamaki matuƙa, su duka, suka yi ta ɗaukaka Allah, tsoro kuma ya kama su, suka ce, “Yau mun ga al’ajabai!”

Kiran Lawi

27 Bayan haka ya fita, ya ga wani mai karɓar haraji, mai suna Lawi, a zaune, yana aiki a wurin karɓar haraji. Ya ce masa, “Bi ni.”

28 Sai ya bar kome duka, ya tashi ya bi shi.

29 Sai Lawi ya yi masa ƙasaitacciyar liyafa a gidansa, akwai kuwa taron masu karɓar haraji da waɗansu mutane suna ci tare da su.

30 Sai Farisiyawa da malamansu na Attaura suka yi wa almajiransa gunaguni suka ce, “Don me kuke ci kuke sha tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?”

31 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ai, lafiyayyu ba ruwansu da magani, sai dai marasa lafiya.

32 Ba domin in kira masu adalci na zo ba, sai dai masu zunubi, su tuba.”

Tambaya a kan Azumi

33 Sai suka ce masa, “Almajiran Yahaya suna azumi a kai a kai, suna kuma addu’a, haka kuma almajiran Farisiyawa, amma naka suna ci suna sha.”

34 Sai Yesu ya ce musu, “Wato kwa iya sa abokan ango su yi azumi tun angon yana tare da su?

35 Ai, lokaci na zuwa da za a ɗauke musu angon. A sa’an nan ne fa za su yi azumi.”

36 Ya kuma yi musu misali, ya ce, “Ba mai tsage ƙyalle a jikin sabuwar tufa ya yi maho a tsohuwar tufa da shi. In ma an yi, ai, sai ya kece sabuwar tufar, sabon ƙyallen kuma ba zai dace da tsohuwar tufar ba.

37 Ba kuma mai ɗura sabon ruwan inabi a tsofaffin salkuna. In ma an ɗura, sai sabon ruwan inabin ya fasa salkunan, ya zube, salkunan kuma su lalace.

38 Sabon ruwan inabi, ai, sai sababbin salkuna.

39 Ba wanda zai so shan sabon ruwan inabin bayan ya sha tsohon, don ya ce, ‘Ai, tsohon yana da kyau.’ ”

Categories
LUK

LUK 6

Almajirai suna Zagar Alkama a Ran Asabar

1 Wata rana ran Asabar, yana ratsa gonakin alkama, sai almajiransa suka zāgi alkamar, suna murtsukewa suna ci.

2 Sai waɗansu Farisiyawa suka ce, “Don me kuke yin abin da bai halatta a yi ba a ran Asabar?”

3 Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ashe, ba ku taɓa karanta abin da Dawuda ya yi ba sa’ad da ya ji yunwa, shi da abokan tafiyarsa?

4 Yadda ya shiga masujadar Allah, ya ɗauki keɓaɓɓiyar gurasan nan ya ci, har ma ya ba abokan tafiyarsa, wadda ba ta halatta kowa ya ci ba, sai firistoci kaɗai?”

5 Sai ya ce musu, “Ai, Ɗan Mutum shi ne Ubangijin Asabar.”

Mai Shanyayyen Hannu

6 A wata Asabar kuma ya shiga majami’a, yana koyarwa. Akwai kuwa wani mutum a ciki wanda hannunsa na dama ya shanye.

7 Sai malaman Attaura da Farisiyawa suka yi haƙwansa su ga ko yā warkar a ran Asabar, don su samu su kai ƙararsa.

8 Shi kuwa ya san tunaninsu. Sai ya ce wa mai shanyayyen hannun, “Taso, ka tsaya nan tsakiya.” Sai ya tashi, ya tsaya a wurin.

9 Yesu ya ce musu, “Ina yi muku tambaya. Ya halatta ran Asabar a yi alheri ko mugunta? A ceci rai, ko a hallaka shi?”

10 Sai ya duddube su duke, ya ce wa mutumin, “Miƙo hannunka.” Ya miƙa, hannunsa kuwa sai ya koma lafiyayye.

11 Sai suka husata ƙwarai, suka yi shawarar abin da za su yi wa Yesu.

Yesu Ya Zaɓi Almajirai Sha Biyu

12 A kwanakin nan Yesu ya fita ya hau dutse domin yin addu’a. Dare farai yana addu’a ga Allah.

13 Da gari ya waye ya kira almajiransa, ya zaɓi goma sha biyu a cikinsu, ya ce da su manzanni.

14 Su ne Bitrus, da ɗan’uwansa Andarawas, da Yakubu, da Yahaya, da Filibus, da Bartalamawas,

15 da Matiyu, da Toma, da Yakubu ɗan Halfa, da Saminu, wanda ake ce da shi Zaloti,

16 da Yahuza ɗan Yakubu, da kuma Yahuza Iskariyoti, wanda ya zama maci amana.

Yesu Ya Hidimta wa Mutane Masu Yawa

17 Sai ya gangaro tare da su, ya tsaya a wani sarari. Ga kuwa babban taro masu binsa, da kuma taro masu yawan gaske daga duk ƙasar Yahudiya da Urushalima, da kuma yankin ƙasar Taya da Sidon da yake bakin bahar, waɗanda suka zo su saurare shi, a kuma warkar da cuce-cucensu.

18 Waɗanda kuma baƙaƙen aljannu suke wahalshe su, aka warkar da su.

19 Duk taron suka nema su taɓa shi, domin iko yana fitowa daga gare shi, ya kuwa warkar da su duka.

Albarka da La’ana

20 Sai ya ɗaga kai, ya dubi almajiransa, ya ce,

“Albarka tā tabbata gare ku, ku matalauta, domin Mulkin Allah naku ne.

21 “Albarka tā tabbata gare ku, ku da kuke mayunwata a yanzu, domin za a ƙosar da kuke.

“Albarka tā tabbata gare ku, ku da kuke kuka a yanzu domin za ku yi dariya.

22 “Albarka tā tabbata a gare ku sa’ad da mutane suka ƙi ku, suka kuma ware ku, suka zage ku, suka yi ƙyamar sunanku saboda Ɗan Mutum.

23 Ku yi farin ciki a wannan rana, ku yi tsalle don murna, domin ga shi, sakamakonku mai yawa ne a Sama. Haka kakanninsu ma suka yi wa annabawa.

24 “Amma kaitonku, ku masu arziki domin kun riga kun sami taku ta’aziyya.

25 “Kaitonku, ku da kuke ƙosassu a yanzu, don za ku ji yunwa. “Kaitonku, ku masu dariya a yanzu, don za ku yi baƙin ciki, ku yi kuka.

26 “Kaitonku in kowa na yabonku. Haka kakanninsu ma suka yi wa annabawan ƙarya.”

Ƙaunar Magabta

27 “Amma ina gaya muku, ku masu sauraro, ku ƙaunaci magabtanku, ku yi wa maƙiyanku alheri.

28 Ku sa wa masu zaginku albarka. Masu wulakanta ku kuma, ku yi musu addu’a.

29 Wanda ya mare ka a kunci ɗaya, juya masa ɗaya kuncin kuma. Wanda ya ƙwace maka mayafi, kada ka hana masa taguwarka ma.

30 Duk wanda ya roƙe ka, ka ba shi. Wanda kuma ya ƙwace maka kaya, kada ka neme shi.

31 Yadda kuke so mutane su yi muku, to, ku yi musu haka.

32 In masoyanku kawai kuke ƙauna wane lada ne da ku? Ai, ko masu zunubi ma suna ƙaunar masoyansu.

33 In kuma sai waɗanda suke muku alheri kawai kuke yi wa alheri, wane lada ne da ku? Ai, ko masu zunubi ma haka suke yi.

34 In kuma sai ga waɗanda kuke tsammani za su biya ku ne kuke ba da rance, wane lada ne da ku? Ai, ko masu zunubi ma, sukan ba masu zunubi rance, don a biya su daidai.

35 Amma ku ƙaunaci magabtanku, kuna yi musu alheri. Ku ba da rance, kada kuwa ku tsammaci biya. Ladanku kuma zai yi yawa, za ku kuma zama ‘ya’yan Maɗaukaki, domin shi mai alheri ne ga masu butulci da kuma mugaye.

36 Ku kasance masu tausayi kamar yadda Ubanku yake mai tausayi.”

Kada ku Ɗora wa Kowa Laifi

37 “Kada ku ɗora wa kowa laifi, ku ma ba za a ɗora muku ba. Kada ku yi wa kowa mugun zato, ku ma ba za a yi muku ba. Ku yafe, ku ma sai a yafe muku.

38 Ku bayar, ku ma sai a ba ku mudu a cike, a danƙare, har ya yi tozo, har yana zuba, za a juye muku a hannun riga. Mudun da kuka auna, da shi za a auna muku.”

39 Ya kuma ba su wani misali ya ce, “Makaho yana iya yi wa makaho jagora? Ashe, dukansu biyu ba sai su fāɗa a rami ba?

40 Almajiri ba ya fin malaminsa. Amma kowa aka karantar da shi sosai, sai ya zama kamar malaminsa.

41 Don me kake duban ɗan hakin da yake a idon ɗan’uwanka, amma gungumen da yake a naka ido ba ka kula ba?

42 Ƙaƙa kuma za ka iya ce wa ɗan’uwanka, ‘Ya ɗan’uwana, bari in cire maka ɗan hakin da yake a idonka,’ alhali kuwa kai kanka ba ka ga gungumen da yake a naka ido ba? Kai munafuki! Sai ka fara cire gungumen da yake a idonka tukuna sa’an nan ka gani sosai yadda za ka cire ɗan hakin da yake a idon ɗan’uwanka.”

Akan Gane Itace ta ‘Ya’yansa

43 “Ba kyakkyawan itace da yake haifar munanan ‘ya’ya, ba kuma mummunan itace da yake haifar kyawawan ‘ya’ya.

44 Domin kowane itace da irin ‘ya’yansa ake saninsa. Ai, ba a ɗiban ɓaure a jikin ƙaya, ko kuwa inabi a jikin sarƙaƙƙiya.

45 Mutumin kirki kam ta kyakkyawar taskar zuciyarsa yakan yi abin kirki, mugu kuwa ta mummunar taskar zuciyarsa yakan yi mugun abu. Ai, abin da ya ci rai, shi mutum yake faɗa.”

Kafa Harsashin Gini Iri Biyu

46 “Don me kuke kirana, ‘Ubangiji, Ubangiji,’ ba kwa kuwa yin abin da na faɗa muku?

47 Duk mai zuwa wurina, yake jin maganata, yake kuma aikata ta, zan nuna muku kwatancinsa.

48 Kamar mutum yake mai gina gida, wanda ya yi haƙa mai zurfi, har ya sa harsashin ginin a kan fā. Da aka yi rigyawa, sai ruwan kogi ya bugi gidan, amma bai iya girgiza shi ba, saboda an gina shi da aminci.

49 Amma wanda ya ji maganata, bai kuwa aikata ba, kamar mutum yake wanda ya gina gida a kan turɓaya, ba harsashi. Ruwan kogi ya buge shi, nan da nan ya rushe. Wannan gida ya yi mummunar ragargajewa!”

Categories
LUK

LUK 7

Yesu Ya Warkar da Bawan Wani Jarumi

1 Bayan da Yesu ya ƙare jawabinsa duka a gaban jama’a, ya shiga Kafarnahum.

2 To, sai bawan wani jarumi, wanda Ubangijinsa yake jin daɗinsa, ya yi rashin lafiya, har ya kai ga bakin mutuwa.

3 Da jarumin ɗin ya ji labarin Yesu, sai ya aiki waɗansu shugabannin Yahudawa wurinsa, su roƙe shi ya zo ya warkar da bawa nasa.

4 Da suka isa wurin Yesu sai suka roƙe shi ƙwarai suka ce, “Ai, ya cancanci a yi masa haka,

5 don yana ƙaunar jama’armu, shi ne ma ya gina mana majami’armu.”

6 Sai Yesu ya tafi tare da su. Da ya matso kusa da gidan, sai jarumin ɗin ya aiki aminansa wurinsa su ce masa, “Ya Ubangiji, kada ka wahalar da kanka. Ban ma isa har ka zo gidana ba.

7 Shi ya sa ban ga ma na isa in zo wurinka ba, amma kă yi magana kawai, yarona kuwa sai ya warke.

8 Don ni ma a hannun wani nake, da kuma soja a hannuna, in ce wa wannan, ‘Je ka,’ sai ya je, wani kuwa in ce masa, ‘Zo,’ sai ya zo, in ce wa bawana, ‘Yi abu kaza,’ sai ya yi.”

9 Da Yesu ya ji haka, ya yi mamakinsa, ya kuma juya ya ce wa taron da suke biye da shi, “Ina gaya muku, ko a cikin Isra’ila ban taɓa samun bangaskiya mai ƙarfi irin wannan ba.”

10 Da waɗanda aka aika suka koma gidan, suka sami bawan garau.

Yesu Ya Tā da Ɗan Mace wadda Mijinta Ya Mutu

11 Ba da daɗewa ba, Yesu ya tafi wani gari, wai shi Nayin, almajiransa da kuma babban taro suka tafi da shi.

12 Ya kusaci ƙofar garin ke nan, sai ga wani mamaci ana ɗauke da shi, shi kaɗai ne wajen uwa tasa, mijinta kuwa ya mutu. Mutanen gari da yawa sun rako ta.

13 Da Ubangiji ya gan ta, ya ji tausayinta, ya kuma ce mata, “Daina kuka.”

14 Sa’an nan ya matso, ya taɓa makarar, masu ɗauka kuma suka tsaya cik. Sai Yesu ya ce, “Samari, na ce maka ka tashi.”

15 Mamacin ya tashi zaune, ya fara magana. Yesu kuwa ya ba da shi ga uwa tasa.

16 Sai tsoro ya kama su duka, suka ɗaukaka Allah suna cewa, “Lalle, wani annabi mai girma ya bayyana a cikinmu,” da kuma, “Allah ya kula da jama’arsa.”

17 Wannan labarin nasa kuwa ya bazu a dukan ƙasar Yahudiya da kewayenta.

‘Yan Saƙo daga Yahaya Maibaftisma

18 Sai almajiran Yahaya suka gaya masa dukan abubuwan nan.

19 Sai Yahaya ya kira almajiransa biyu, ya aike su gun Ubangiji yana tambaya, “Kai ne mai zuwan nan, ko kuwa mu sa ido ga wani?”

20 Da mutanen nan suka isa wurinsa, suka ce, “Yahaya Maibaftisma ne ya aiko mu gare ka, yana tambaya, ‘Kai ne mai zuwan nan, ko kuwa mu sa ido ga wani?’ ”

21 Nan take Yesu ya warkar da mutane da yawa daga rashin lafiyarsu da cuce-cucensu da kuma baƙaƙen aljannu. Makafi da yawa kuma ya yi musu baiwar gani.

22 Sai ya amsa musu ya ce, “Ku je ku gaya wa Yahaya abin da kuka ji da abin da kuka gani. Makafi na samun gani, guragu na tafiya, ana tsarkake kutare, kurame na ji, ana ta da matattu, ana kuma yi wa matalauta bishara.

23 Albarka tā tabbata ga wanda ba ya tuntuɓe sabili da ni.”

24 Baya jakadun Yahaya sun tafi, sai Yesu ya fara yi wa taro maganar Yahaya, ya ce, “Kallon me kuka je yi a jeji? Kyauron da iska take kaɗawa?

25 To, kallon me kuka je yi? Wani mai adon alharini? Ai kuwa, masu adon gaske, masu zaman annashuwa, a fāda suke.

26 To, kallon me kuka je yi? Annabi? Hakika, ina gaya muku, har ya fi annabi nesa.

27 Wannan shi ne wanda labarinsa yake rubuce cewa,

‘Ga shi, na aiko manzona ya riga ka gaba,

Wanda zai shirya maka hanya gabaninka.’

28 Ina gaya muku, a cikin duk waɗanda mata suka haifa, ba wanda ya fi Yahaya girma. Duk da haka wanda ya fi ƙasƙanta a Mulkin Allah ya fi shi.”

29 Da duk jama’a da masu karɓar haraji suka ji haka, suka tabbata Allah mai adalci ne, aka yi musu baftisma da baftismar Yahaya.

30 Amma Farisiyawa da masanan Attaura suka shure abin da Allah yake nufinsu da shi, da yake sun ƙi ya yi musu baftisma.

31 “To, da me zan kwatanta mutanen zamanin nan? Waɗanne iri ne su?

32 Kamar yara suke da suke zaune a bakin kasuwa, suna kiran juna, suna cewa,

‘Mun busa muku sarewa, ba ku yi rawa ba,

Mun yi makoki, ba ku yi kuka ba.’

33 Ga shi, Yahaya Maibaftisma ya zo, ba ya cin gurasa, ba ya shan ruwan inabi, amma kuna cewa, ‘Ai, yana da iska.’

34 Ga Ɗan Mutum ya zo, yana ci yana sha, kuna kuma cewa, ‘Ga mai haɗama, mashayi, abokin masu karɓar haraji da masu zunubi!’

35 Duk da haka hikimar Allah, ta dukkan aikinta ne ake tabbatar da gaskiya tata.”

Yesu a Gidan Saminu Bafarisiye

36 Wani Bafarisiye ya kira shi cin abinci. Sai ya shiga gidan Bafarisiyen, ya ƙishingiɗa wurin cin abincin.

37 Sai ga wata matar garin, mai zunubi, da ta ji Yesu na cin abinci a gidan Bafarisiyen, ta kawo wani ɗan tandu na man ƙanshi,

38 ta tsaya a bayansa a wajen ƙafafunsa, tana kuka. Sai hawayenta ya fara zuba a ƙafafunsa, ta goge su da gashinta, ta yi ta sumbantarsu, ta shafa musu man ƙanshin.

39 To, da Bafarisiyen da ya kira shi ya ga haka, sai ya ce a ransa, “Da mutumin nan annabi ne, da ya san ko wace ce, da kuma ko wace irin mace ce wannan da yake taɓa shi, don mai zunubi ce.”

40 Yesu ya amsa ya ce, “Saminu, ina da magana da kai.” Sai shi kuma ya ce, “Malam, sai ka faɗa.”

41 Yesu ya ce, “Wani yana bin mutum biyu bashi, ɗaya dinari ɗari biyar, ɗayan kuma hamsin.

42 Da suka gagara biya, sai ya yafe musu dukansu biyu. To, a cikinsu wa zai fi ƙaunarsa?”

43 Saminu ya amsa masa ya ce, “A ganina, wanda ya yafe wa mai yawa.” Sai ya ce masa “Ka faɗa daidai.”

44 Da ya waiwaya wajen matar, ya ce wa Saminu. “Ka ga matan nan? Na shigo gidanka, ba ka ba ni ruwan wanke ƙafa ba, amma ita ta zub da hawayenta a ƙafafuna, ta kuma goge su da gashinta.

45 Kai ba ka sumbance ni ba, ita kuwa, tun shigowata nan ba ta daina sumbantar ƙafafuna ba.

46 Ba ka shafa mini mai a ka ba, amma ita ta shafa man ƙanshi a ƙafafuna.

47 Saboda haka ina gaya maka, zunubanta masu yawan nan duk an gafarta mata, domin ta yi ƙauna mai yawa. Wanda aka gafarta wa kaɗan kuwa, ƙauna kaɗan yake yi.”

48 Sai ya ce mata, “An gafarta miki zunubanki.”

49 Masu ci tare da shi kuwa suka fara ce wa juna, “Wannan kuwa wane ne wanda har yake gafarta zunubai?”

50 Sai Yesu ya ce wa matar, “Bangaskiyarki ta cece ki. Ki sauka lafiya.”

Categories
LUK

LUK 8

Waɗansu Mata sun Tafi tare da Yesu

1 Ba da daɗewa ba Yesu ya zazzaga birni da ƙauye yana wa’azi, yana yin bisharar Mulkin Allah. Sha biyun nan kuwa suna tare da shi,

2 da waɗansu mata da aka raba da baƙaƙen aljannu da kuma rashin lafiyarsu. Cikinsu da Maryamu mai suna Magadaliya, wadda aka fitar wa da aljannu bakwai,

3 da Yuwana matar Kuza, wakilin Hirudus, da Suzanatu, da kuma waɗansu da yawa da suka yi musu ɗawainiya da kayansu.

Misali na Mai Shuka

4 Da jama’a masu yawa suka taru, mutane suna ta zuwa gare shi gari da gari, sai ya yi musu misali ya ce.

5 “Wani mai shuka ya tafi shuka. Yana cikin yafa iri sai waɗansu suka fāɗi a hanya, aka tattake su, tsuntsaye suka tsince su.

6 Waɗansu kuma suka fāɗi a dutse. Da suka tsiro sai suka bushe, don ba danshi.

7 Waɗansu kuma suka fāɗi cikin ƙaya, suka tashi tare, har ƙayar ta sarƙe su.

8 Waɗansu kuwa suka fāɗi a ƙasa mai kyau, suka girma, suka yi ƙwaya riɓi ɗari ɗari.” Da ya faɗi haka, sai ya ta da murya ya ce, “Duk mai kunnen ji, yă ji.”

Manufar Misalin

9 Almajiransa suka tambaye shi ma’anar misalin.

10 Sai ya ce, “Ku kam, an yarda muku ku san asiran Mulkin Allah. Amma ga sauran sai da misali, don gani kam, su gani, amma ba za su gane ba. Ji kuma, su ji, amma ba za su fahimta ba.

Yesu Ya Ba da Bayanin Misalin Mai Shuka

11 “To, misalin shi ne, irin Maganar Allah ne.

12 Waɗanda suka fāɗi a hanya su ne kwatancin waɗanda suka ji Maganar Allah, sa’an nan Iblis ya zo ya ɗauke Maganar daga zuciyarsu, don kada su ba da gaskiya su sami ceto.

13 Na kan dutsen kuwa su ne waɗanda da zarar sun ji Maganar, sai su karɓa da farin ciki. Su kam, ba su da tushe. Sukan ba da gaskiya ‘yan kwanaki kaɗan, amma a lokacin gwaji, sai su bauɗe.

14 Waɗanda suka fāɗi cikin ƙaya kuwa su ne waɗanda suka ji Maganar, amma a kwana a tashi, sai yawan taraddadin duniya, da dukiya, da shagalin duniya su sarƙe su, har su kasa yin amfani.

15 Waɗanda aka shuka a ƙasa mai kyau kuwa su ne waɗanda suka ji Maganar, suka riƙe ta kamkam da zuciya ɗaya kyakkyawa, suka jure har suka yi amfani.

Fitila a Rufe da Masaki

16 “Ba mai kunna fitila ya rufe ta da masaki, ko ya ajiye ta a ƙarƙashin gado. A’a, sai dai ya ɗora ta a maɗorinta, don masu shiga su ga hasken.

17 Ba abin da yake a ɓoye da ba za a bayyana ba. Ba kuma asirin da ba zai tonu ya zama bayyananne ba.

18 Ku kula fa, ku iya ji, don mai abu akan ƙara wa. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da yake tsammani yake da shi ma, sai a karɓe masa.”

Uwar Yesu da ‘Yan’uwansa

19 Uwa tasa da ‘yan’uwansa suka zo wurinsa, amma suka kasa isa gunsa saboda taro.

20 Sai aka ce masa, “Tsohuwarka da ‘yan’uwanka suna tsaye a waje, suna son ganinka.”

21 Amma ya amsa musu ya ce, “Masu jin Maganar Allah, suna kuma aikata ta, ai, su ne uwata, su ne kuma ‘yan’uwana.”

Yesu Ya Tsawata wa Hadiri

22 Wata rana ya shiga jirgi tare da almajiransa. Ya ce musu, “Mu haye wancan hayin teku.” Sai suka tashi.

23 Suna cikin tafiya sai barci ya kwashe shi. Hadiri mai iska ya taso a tekun, jirginsu ya tasar wa cika da ruwa, har suna cikin hatsari.

24 Suka je suka tashe shi, suka ce, “Maigida, Maigida, mun hallaka!” Ya farka, ya tsawata wa iskar da kuma haukan ruwa. Sai suka kwanta, wurin ya yi tsit.

25 Ya ce musu, “Ina bangaskiyarku?” Suka kuwa tsorata suka yi mamaki, suna ce wa juna, “Wa ke nan kuma, har iska da ruwa ma yake yi wa umarni, suna kuwa yi masa biyayya?”

Warkar da Mai Aljan na Garasinawa

26 Sai suka iso ƙasar Garasinawa wadda take hannun riga da ƙasar Galili.

27 Da saukarsa a gaci sai wani mai aljannu ya fito daga cikin gari ya tarye shi. Ya daɗe bai sa tufa ba, ba ya zama a gida kuwa, sai a makabarta.

28 Da ganin Yesu sai ya ƙwala ihu, ya faɗi a gabansa, ya ɗaga murya ya ce, “Ina ruwanka da ni, ya Yesu Ɗan Allah Maɗaukaki? Ina roƙonka, kada ka yi mini azaba.”

29 Ya faɗi haka ne domin Yesu ya umarci baƙin aljanin ya rabu da mutumin. Gama sau da yawa aljanin yakan buge shi, akan kuma tsare shi, a ɗaure shi da sarƙa da mari, amma ya tsintsinka ɗaurin, aljanin ya kora shi jeji.

30 Sai Yesu ya tambaye shi, “Yaya sunanka?” Ya ce, “Tuli,” don aljannu da yawa sun shiga cikinsa.

31 Sai suka yi ta roƙansa kada ya umarce su su fāɗa a mahalaka.

32 To, wurin nan kuwa akwai wani babban garkin alade na kiwo a gangaren dutse, suka roƙe shi ya yardar musu su shiga cikinsu. Ya kuwa yardar musu.

33 Sai aljannun suka rabu da mutumin, suka shiga aladun. Garken kuwa suka rungungunta ta gangaren, suka faɗa tekun, suka halaka a ruwa.

34 Da ‘yan kiwon aladen nan suka ga abin da ya faru, suka gudu, suka ba da labari a birni da ƙauye.

35 Sai jama’a suka firfito su ga abin da ya auku. Suka zo wurin Yesu, suka tarar da mutumin da aljannun suka rabu da shi, zaune gaban Yesu, saye da tufa, yana cikin hankalinsa. Sai suka tsorata.

36 Waɗanda aka yi abin a idonsu kuwa, suka gaya musu yadda aka warkar da mai aljannun nan.

37 Dukan mutanen kewayen ƙasar Garasinawa suka roƙi Yesu ya rabu da su, don tsoro mai yawa ya kama su. Sai ya shiga jirgi ya koma.

38 Mutumin da aljannun suka rabu da shi kuwa, ya roƙe shi izinin tafiya tare da shi. Amma ya sallame shi ya ce,

39 “Koma gida, ka faɗi irin manyan abubuwan da Allah ya yi maka.” Sai ya tafi ko’ina a cikin birnin yana sanar da manyan abubuwan da Yesu ya yi masa.

Warkar da ‘Yar Yayirus da Matar da ta Taɓa Gezar Mayafin Yesu

40 To, da Yesu ya komo, taron suka yi masa maraba domin ko a dā ma duk suna jiransa ne.

41 Sai ga wani mutum mai suna Yayirus, wani shugaban majami’a, ya zo ya fāɗi a gaban Yesu, ya roƙe shi ya je gidansa.

42 Yana da ‘ya ɗaya tilo, mai shekara misalin goma sha biyu, tana kuma bakin mutuwa.

Yana tafiya, taro masu yawa na matsa tasa,

43 sai ga wata mace wadda ta shekara goma sha biyu tana zub da jini, ta kuma ɓad da duk abin hannunta wajen masu magani, ba wanda ya iya warkar da ita.

44 Ta raɓo ta bayansa, ta taɓa gezar mayafinsa. Nan take zubar jininta ta tsaya.

45 Sai Yesu ya ce, “Wa ya taɓa ni?” Da kowa ya yi mūsū, Bitrus da waɗanda suke tare da shi suka ce, “Maigida, ai, taro masu yawa ne suke tutturarka, suna matsarka.”

46 Amma Yesu ya ce, “An dai taɓa ni, domin na ji iko ya fita daga gare ni.”

47 Da matar ta ga ba dama ta ɓuya, sai ta matso tana rawar jiki, ta fāɗi a gabansa, ta bayyana a gaban duk jama’a dalilin da ya sa ta taɓa shi, da kuma yadda ta warke nan take.

48 Sai ya ce mata, “’Yata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya.”

49 Yana cikin magana, sai ga wani ya zo daga gidan shugaban majami’ar, ya ce, “Ai, ‘yarka ta rasu. Kada ka ƙara wahalar da Malamin.”

50 Amma da Yesu ya ji haka, ya amsa ya ce wa shugaban majami’ar, “Kada ka ji tsoro. Ka ba da gaskiya kawai, za ta kuwa warke.”

51 Da ya isa gidan bai yarda kowa ya shiga tare da shi ba, sai Bitrus, da Yahaya, da Yakubu, da kuma uban yarinyar da uwa tata,

52 Duk kuwa ana ta kuka da kururuwa saboda ita. Amma Yesu ya ce, “Ku daina kuka. Ai, ba matacciya take ba, barci take yi.”

53 Sai suka yi masa dariyar raini, don sun sani ta mutu.

54 Shi kuwa sai ya riƙe hannunta, ya ta da murya ya ce, “Yarinya, ki tashi.”

55 Ruhunta kuwa ya dawo, nan take ta tashi. Sai ya yi umarni a ba ta abinci.

56 Iyayenta suka yi mamaki. Amma ya kwaɓe su kada su gaya wa kowa abin da ya faru.

Categories
LUK

LUK 9

Yesu ya Aiki Goma Sha Biyu ɗin Nan

1 Sai ya tara goma sha biyun nan ya ba su iko da izini kan dukan aljannu, su kuma warkar da cuce-cuce,

2 ya kuma aike su su yi wa’azin Mulkin Allah, su kuma warkar da marasa lafiya.

3 Ya kuma ce musu, “Kada ku ɗauki wani guzuri a tafiyarku, ko sanda, ko burgami, ko gurasa, ko kuɗi. Kada kuma ku ɗauki taguwa biyu.

4 Duk gidan da kuka sauka, ku zauna a nan har ku tashi.

5 Duk waɗanda ba su yi na’am da ku ba, in za ku bar garin, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku don shaida a kansu.”

6 Sai suka tashi suka zazzaga ƙauyuka suna yin bishara, suna warkarwa a ko’ina.

Mutuwar Yahaya Maibaftisma

7 To, sarki Hirudus ya ji duk abin da ake yi, ya kuwa damu ƙwarai, don waɗansu suna cewa Yahaya ne aka tasa daga matattu.

8 Waɗansu kuwa suka ce wai Iliya ne ya bayyana. Waɗansu kuma suka ce ɗaya daga annabawan dā ne ya tashi.

9 Sai Hirudus ya ce, “Yahaya kam na fille masa kai. Wa ke nan kuma da nake jin irin waɗannan abubuwa game da shi?” Sai ya nemi ganinsa.

Ciyar da Mutum Dubu Biyar

10 Da manzanni suka dawo, suka gaya wa Yesu abin da suka yi. Sai ya tafi da su a keɓe zuwa wani gari wai shi Betsaida.

11 Ganin haka sai taro masu yawa suka bi shi. Ya kuwa yi musu maraba, ya yi musu maganar Mulkin Allah, ya kuma warkar da masu bukatar warkewa.

12 Da rana ta fara sunkuyawa, sha biyun suka matso, suka ce masa, “Sai ka sallami taron, su shiga ƙauyuka da karkara na kurkusa, su sauka, su nemi abinci, don inda muke ba mutane.”

13 Amma ya ce musu, “Ku ku ba su abinci mana.” Suka ce, “Ai, abin da muke da shi bai fi gurasa biyar da kifi biyu ba, sai dai in za mu je mu sayo wa dukkan jama’an nan abinci ne.”

14 Maza sun yi wajen dubu biyar. Sai ya ce wa almajiransa, “Ku ce musu su zazzauna ƙungiya ƙungiya, kowace ƙungiya misali hamsin hamsin.”

15 Haka kuwa suka yi, suka sa dukkansu su zazzauna.

16 Da ya ɗauki gurasa biyar ɗin da kifi biyu, sai ya ɗaga kai sama, ya yi wa Allah godiya, ya gutsuttsura su, ya yi ta ba almajiran, suna kai wa jama’a.

17 Duka kuwa suka ci suka ƙoshi, har aka kwashe ragowar gutsattsarin, kwando goma sha biyu.

Hurcin Bitrus a kan Yesu

18 Wata rana yana addu’a shi kaɗai, almajiransa kuwa suka zo wurinsa. Sai ya tambaye su, ya ce, “Wa mutane suke cewa nake?”

19 Suka amsa suka ce, “Yahaya Maibaftisma, waɗansu kuwa, Iliya, waɗansu kuma, ɗaya daga cikin annabawan dā ne ya tashi.”

20 Ya ce musu, “Amma ku fa, wa kuke cewa nake?” Sai Bitrus ya amsa ya ce, “Almasihu na Allah.”

Yesu Ya Faɗi irin Mutuwar da zai Yi

21 Sai ya kwaɓe su gaya matuƙa kada su gaya wa kowa wannan magana.

22 Ya ce, “Lalle ne Ɗan mutum yă sha wuya iri iri, shugabanni da manyan firistoci da malaman Attaura su ƙi shi, har a kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.”

23 Sai ya ce wa dukansu, “Duk mai son bina, sai ya ƙi kansa, ya ɗauki gicciyensa kowace rana, yă bi ni.

24 Duk mai son tattalin ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa saboda ni, tattalinsa ya yi.

25 Me mutum ya amfana in ya sami duniya duka a kan hasarar ransa, ko a bakin ransa?

26 Duk wanda sai ya ji kunyar shaida ni da maganata, Ɗan Mutum ma zai ji kunyar shaida shi sa’ad da ya zo da ɗaukaka tasa, da kuma ɗaukakar Uba, da ta mala’iku tsarkaka.

27 Amma hakika ina gaya muku, akwai waɗansu tsaitsaye a nan da ba za su mutu ba sai sun ga Mulkin Allah.”

Sākewar Kamanninsa

28 Bayan misalin kwana takwas da yin maganan nan, Yesu ya ɗauki Bitrus, da Yahaya, da Yakubu, ya hau wani dutse domin yin addu’a.

29 Yana yin addu’a, sai kama tasa ta sāke, tufafinsa kuma suka yi fari fat, har suna ɗaukar ido.

30 Sai ga mutum biyu na magana da shi, wato Musa da Iliya.

31 Sun bayyana da ɗaukaka, suna zancen ƙaura tasa ne, wadda yake gabannin yi a Urushalima.

32 Sai kuma Bitrus da waɗanda suke tare da shi, barci ya cika musu ido, amma da suka farka suka ga ɗaukakarsa, da kuma mutum biyun nan tsaye tare da shi.

33 Mutanen nan na rabuwa da shi ke nan, sai Bitrus ya ce wa Yesu, “Maigida, ya kyautu da muke nan wurin. Mu kafa bukkoki uku, ɗaya taka, ɗaya ta Musa, ɗaya kuma ta Iliya.” Bai ma san abin da yake faɗa ba.

34 Yana faɗar haka sai wani gajimare ya zo ya rufe su. Da kuma gajimaren ya lulluɓe su suka tsorata.

35 Sai aka ji wata murya daga cikin gajimaren, tana cewa, “Wannan shi ne Ɗana zaɓanɓɓena. Ku saurare shi!”

36 Bayan muryar ta yi magana, aka ga Yesu shi kaɗai. Suka yi shiru. A kwanakin nan kuwa ba su gaya wa kowa abin da suka gani ba.

Yesu Ya Warkar da Yaro Mai Farfadiya

37 Kashegari da suka gangaro daga kan dutsen, wani babban taro ya tarye shi.

38 Sai ga wani daga cikin taron ya yi kira, ya ce, “Malam, ina roƙonka ka dubi ɗana da idon rahama, shi ne ke nan gare ni.

39 Ga shi, aljani yakan hau shi, yakan yi ihu ba zato ba tsammani. Aljanin yakan buge shi, jikinsa yana rawa, har bakinsa yana kumfa. Ba ya barinsa sai ya kukkuje shi ƙwarai.

40 Na kuwa roƙi almajiranka su fitar da shi, amma sun kasa.”

41 Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ya ku tsara marasa bangaskiya, kangararru! Har yaushe zan zama da ku, ina jure muku? Kawo ɗa naka nan.”

42 Yana zuwa, sai aljanin ya buge shi ƙwarai, jikinsa na rawa. Amma Yesu ya tsawata wa baƙin aljanin, ya warkar da yaron, ya kuma mayar wa ubansa da shi.

43 Duk aka yi mamakin girman ikon Allah.

Yesu Ya Sāke Faɗar irin Mutuwar da zai Yi

Tun dukansu suna mamakin duk abubuwan da yake yi, sai ya ce wa almajiransa,

44 “Maganar nan fa tă shiga kunnenku! Za a ba da Ɗan Mutum ga mutane.”

45 Amma ba su fahimci maganan nan ba, an kuwa ɓoye musu ita ne don kada su gane. Su kuwa suna tsoron tambayarsa wannan magana.

Wane ne Mafi Girma?

46 Sai musu ya tashi a tsakaninsu a kan ko wane ne babbansu.

47 Amma da Yesu ya gane tunanin zuciyarsu, ya kama hannun wani ƙaramin yaro ya ajiye shi kusa da shi.

48 Ya ce musu, “Duk wanda ya karɓi ƙanƙane yaro kamar wannan saboda sunana, ni ya karɓa. Wanda kuwa ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ke nan. Ai, wanda yake ƙarami a cikinku shi ne babba.”

Wanda ba ya Gāba da ku, Naku Ne

49 Sai Yahaya ya amsa ya ce, “Maigida, mun ga wani yana fitar da aljannu da sunanka, mun kuwa hana shi, domin ba ya binmu.”

50 Amma Yesu ya ce masa, “Kada ku hana shi. Ai, duk wanda ba ya gāba da ku, naku ne.”

Samariyawan wani Ƙauye sun Ƙi Karɓar Yesu

51 Da lokacin karɓarsa a Sama ya gabato, ya himmantu sosai ga zuwa Urushalima.

52 Sai ya aiki jakadu su riga shi gaba, suka kuwa tafi suka shiga wani ƙauyen Samariyawa su shisshirya masa.

53 Amma Samariyawa suka ƙi karɓarsa, domin niyyarsa duk a kan Urushalima take.

54 Da almajiransa Yakubu da Yahaya suka ga haka suka ce, “Ya Ubangiji, ko kana so mu umarci wuta ta sauko daga sama ta lashe su?”

55 Amma ya juya, ya tsawata musu.

56 Sai suka ci gaba, suka tafi wani ƙauye.

Masu Cewa za su Bi Yesu

57 Suna tafiya a hanya, sai wani mutum ya ce masa, “Zan bi ka duk inda za ka.”

58 Yesu ya ce masa, “Yanyawa da ramummukansu, tsuntsaye kuma da wurin kwanansu, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin shaƙatawa.”

59 Ya kuma ce wa wani, “Bi ni.” Sai ya ce, “Ya Ubangiji, ka bar ni tukuna in je in binne tsohona.”

60 Sai Yesu ya ce masa, “Bari matattu su binne ‘yan’uwansu matattu. Amma kai kuwa, tafi ka sanar da Mulkin Allah.”

61 Wani kuma ya ce, “Ya Ubangiji, zan bi ka, amma ka bar ni tukuna in yi wa mutanen gida bankwana.”

62 Yesu ya ce masa “Wanda ya fara huɗa da keken noma, yana duban baya, bai dace da Mulkin Allah ba.”

Categories
LUK

LUK 10

Yesu Ya Aiki Saba’in Ɗin

1 Bayan wannan Ubangiji ya zaɓi waɗansu mutum saba’in, ya aike su biyu biyu, su riga shi gaba zuwa kowane gari da kowane wuri da shi kansa za shi.

2 Ya ce musu, “Girbin na da yawa, amma masu yinsa kaɗan ne. Saboda haka ku roƙi Ubangijin girbi ya turo masu girbi, su yi masa girbi.

3 To, sai ku tafi. Ga shi na aike ku kamar ‘yan tumaki a tsakiyar kyarketai.

4 Kada ku ɗauki jakar kuɗi, ko burgami, ko takalma. Kada ku yi doguwar gaisuwa da kowa a hanya.

5 Duk gidan da kuka sauka, ku fara da cewa, ‘Salama alaikun mutanen gidan nan!’

6 In akwai da ɗan salama a gidan, to, salamarku za ta tabbata a gare shi. In kuwa babu, za ta komo muku.

7 Ku zauna a gidan, kuna ci kuna shan duk irin abin da suka ba ku, domin ma’aikaci ya cancanci ladansa. Kada ku riƙa sāke masauki.

8 Duk garin da kuka shiga, in an yi na’am da ku, ku ci duk irin abin da aka kawo muku.

9 Ku warkar da marasa lafiya da suke cikinsa, ku kuma ce musu, ‘Mulkin Allah ya kusato ku.’

10 Amma duk garin da kuka shiga ba a yi na’am da ku ba, sai ku zaga kwararo kwararo, kuna cewa,

11 ‘Ko da ƙurar garinku da ta ɗafe a jikin ƙafafunmu ma, mun karkaɗe muku. Amma duk da haka ku sani Mulkin Allah ya kusato.’

12 Ina dai gaya muku, a ran nan, za a fi haƙurce wa Saduma a kan garin nan.”

Tsawata wa Garuruwan da ba su Tuba Ba

13 “Kaitonki, Korasinu! Kaitonki, Betsaida! Da mu’ujizan da aka yi a cikinku, su aka yi a Taya da Sidon, da tuni sun tuba, sun zauna sāye da tsumma, suna hurwa da toka.

14 Amma a Ranar Shari’a, za a fi haƙurce wa Taya da Sidon a kanku.

15 Ke kuma Kafarnahum, ɗaukaka ki sama za a yi? A’a, ƙasƙantar da ke za a yi har Hades.

16 “Duk mai sauraronku, ni yake saurare. Mai ƙinku kuma, ni yake ƙi. Duk mai ƙina kuwa, wanda ya aiko ni ne ya ƙi.”

Komowar Saba’in Ɗin

17 Sai kuma saba’in ɗin nan suka komo da farin ciki, suka ce, “Ya Ubangiji, har aljannu ma suna mana biyayya albarkacin sunanka!”

18 Sai ya ce musu, “Na ga Shaiɗan ya faɗo daga sama kamar walƙiya.

19 Ga shi, na ba ku ikon taka macizai da kunamai, ku kuma rinjaye a kan dukan ikon Maƙiyi, ba kuwa abin da zai cuce ku ko kaɗan.

20 Duk da haka, kada ku yi farin ciki aljannu na yi muku biyayya, sai dai ku yi farin cikin an rubuta sunayenku a Sama.”

Yesu Ya Yi Farin Ciki

21 A wannan lokaci ya yi farin ciki matuƙa ta Ruhu Mai Tsarki, ya ce, “Na gode maka ya Uba, Ubangijin sama da ƙasa, domin ka ɓoye waɗannan al’amura ga masu hikima da masu basira, ka kuma bayyana su ga jahilai. Hakika na gode maka ya Uba, domin wannan shi ne nufinka na alheri.

22 Kowane abu Ubana ne ya mallaka mini. Ba kuwa wanda ya san ko wane ne Ɗan sai dai Uban, ko kuma ya san ko wane ne Uban sai dai Ɗan, da kuma wanda Ɗan yake so ya bayyana wa.”

23 Sai ya juya wajen almajiransa, ya ce musu a keɓance, “Albarka tā tabbata ga idanun da suka ga abin da kuka gani.

24 Ina gaya muku, annabawa da sarakuna da yawa suna son ganin abin da kuke gani, amma ba su gani ba, suna kuma so su ji abin da kuke ji, amma ba su ji ba.”

Basamariyen da Ya Nuna Jinƙai

25 Sai ga wani masanin Attaura ya tashi tsaye yana gwada shi, ya ce, “Malam, me zan yi in gaji rai madawwami?”

26 Yesu ya ce musu, “Me yake rubuce a Attaura? Yaya kake karantawa?”

27 Sai ya amsa ya ce, “Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan ƙarfinka, da dukkan hankalinka. Ka kuma ƙaunaci ɗan’uwanka kamar kanka.”

28 Yesu ya ce masa, “Ka amsa daidai. Ka riƙa yin haka, za ka rayu.”

29 Shi kuwa mutumin, don yana son baratar da kansa, ya ce wa Yesu, “To, wane ne ɗan’uwa nawa?”

30 Sai Yesu ya amsa ya ce, “Wani mutum ne ya tashi daga Urushalima za shi Yariko. Sai ‘yan fashi suka fāɗa shi, suka tuɓe shi, suka yi masa mugun dūka, suka tafi suka bar shi rai ga Allah.

31 Daga nan ya zamana wani firist ya biyo ta wannan hanya. Da ya gan shi sai ya zaga ta ɗaya gefen, ya wuce abinsa.

32 Haka kuma wani Balawe, da ya iso wurin ya gan shi, shi ma ya zaga ta ɗaya gefen, ya wuce abinsa.

33 Ana nan sai hanya ta kawo wani Basamariye inda yake. Da ya gan shi, sai tausayi ya kama shi,

34 ya je wurinsa, ya ɗaɗɗaure masa raunukansa, yana zuba musu mai da ruwan inabi. Sa’an nan ya ɗora shi a kan dabbarsa, ya kai shi masauki, ya yi ta jiyyarsa.

35 Kashegari ya ɗebo dinari biyu ya ba maigidan, ya ce, ‘Ka yi jiyyarsa, duk kuma abin da ka ɓatar bayan wannan, in na dawo sai in biya ka.’

36 To, a cikin ukun nan, wa kake tsammani ya zama ɗan’uwa ga wanda ‘yan fashin suka faɗa wa?”

37 Sai ya ce, “Wanda ya nuna masa jinƙai.” Sai Yesu ya ce masa, “Kai ma, ka je ka riƙa yin haka.”

Yesu Ya Ziyarci Marta da Maryamu

38 Suna tafiya, sai ya shiga wani ƙauye, wata mace kuma mai suna Marta ta sauke da shi a gidanta.

39 Tana kuwa da ‘yar’uwa mai suna Maryamu, wadda ta zauna a gaban Ubangiji tana sauraron magana tasa.

40 Marta kuwa yawan hidimomi ya ɗauke mata hankali, sai ta je gunsa, ta ce, “Ya Ubangiji, ba ka kula ba, ‘yar’uwata ta bar ni ina hidima ni kaɗai? Gaya mata ta taimake ni mana.”

41 Amma Ubangiji ya amsa mata ya ce, “Marta, Marta! Hankalinki a tashe yake, kina kuma damuwa kan abu da yawa.

42 Bukatu kima ne, ta ainihi ɗaya ce. Maryamu ta zaɓi abu mai kyau, ba kuwa za a karɓe mata ba.”