Categories
LUK

LUK 21

Sadaka wadda aka Saka

1 Yesu ya ɗaga kai ya ga waɗansu masu arziki suna saka sadakarsu a baitulmalin Haikali.

2 Sai ya ga wata gajiyayyiya da mijinta ya mutu ta saka rabin kobo biyu a ciki.

3 Sai ya ce, “Hakika, ina gaya muku, abin da gajiyayyiya gwauruwan nan ta saka a ciki, ya fi na sauran duka.

4 Domin duk waɗannan sun bayar daga yalwarsu ne, ita kuwa daga cikin rashinta ta ba da duk kuɗinta na abinci.”

Yesu Ya Faɗi irin Rushewar da za ta Sami Haikali

5 Waɗansu suna zancen Haikali, da yadda aka ƙawata shi da duwatsun alfarma da keɓaɓɓun kayan sadaka, sai ya ce,

6 “In don waɗannan abubuwa da kuke kallo ne, ai, lokaci yana zuwa da ba wani dutsen da za a bari a nan a kan ɗan’uwansa da ba a baje shi ba.”

Alamu da Tsanance-tsanance

7 Sai suka tambaye shi suka ce, “Malam, a yaushe za a yi waɗannan abubuwa? Wace alama kuma za a gani sa’ad da suke shirin aukuwa?”

8 Sai ya ce, “Ku kula fa kada a ɓad da ku. Don mutane da yawa za su zo da sunana, suna cewa su ne ni, suna kuma cewa, ‘Lokaci ya yi kusa.’ To, kada ku bi su.

9 In kuma kun ji labarin yaƙe-yaƙe da hargitsi, kada ku firgita. Lalle ne wannan ya fara aukuwa, amma ƙarshen tukuna.”

10 Sa’an nan ya ce musu, “Al’umma za ta tasar wa al’umma, mulki ya tasar wa mulki.

11 Za a yi raurawar ƙasa manya manya, da kuma yunwa, da annoba a wurare dabam dabam. Za a kuma yi al’amura masu bantsoro da manyan alamu daga sama.

12 Amma kafin wannan duka, za su kama ku, su tsananta muku. Za su miƙa ku ga majami’u da kurkuku, su kuma kai ku a gaban sarakuna da mahukunta saboda sunana.

13 Wannan zai zama muku hanyar ba da shaida.

14 Saboda haka, sai ku ƙudura a ranku, a kan ba za ku damu da yadda za ku mai da jawabi ba.

15 Domin ni ne zan ba ku ikon hurci, da kuma hikima wadda duk abokan adawarku, ba za su iya shanyewa ko musawa ba.

16 Ko da iyayenku ma da ‘yan’uwanku, da danginku, da abokanku, sai sun bāshe ku, su kuma sa a kashe waɗansunku.

17 Kowa kuma zai ƙi ku saboda sunana.

18 Amma ba gashin kanku ko ɗaya da zai yi ciwo.

19 Jurewarku ce za ta fisshe ku.”

Yesu ya Faɗi irin Ribɗewa da za ta Sami Urushalima

20 “Sa’ad da kuka ga rundunonin yaƙi sun kewaye Urushalima, sa’an nan ku tabbata ana kusan ribɗe ta.

21 Sa’an nan waɗanda suke a ƙasar Yahudiya, su gudu su shiga duwatsu, na birni su fice, na ƙauye kuma kada su shiga birni.

22 Saboda lokacin sakamako ne, don a cika duk abin da yake rubuce.

23 Kaiton masu juna biyu da masu goyo a wannan lokaci! Don matsanancin ƙunci zai saukar wa ƙasar, da kuma fushin Allah ga jama’an nan.

24 Za a kashe waɗansu da kaifin takobi, a kuma kakkama waɗansu a kai su bauta zuwa ƙasashen al’ummai duka. Al’ummai kuma za su tattake Urushalima, har ya zuwa cikar zamaninsu.”

Komowar Ɗan Mutum

25 “Za a kuma ga alamu a rana, da wata, da taurari, a duniya kuma al’ummai su matsu ƙwarai, suna shan damuwa saboda ƙugin teku da na raƙuman ruwa.

26 Mutane za su suma don tsoro, da kuma fargaban al’amuran da suke aukuwa ga duniya, don za a girgiza manyan abubuwan da suke a sararin sama.

27 A sa’an nan ne za su ga Ɗan Mutum yana zuwa a cikin gajimare da iko da ɗaukaka mai yawa.

28 Sa’ad da waɗannan al’amura suka fara aukuwa, sai ku ɗaga kai ku dubi sama, domin fansarku ta yi kusa.”

Aya a kan Itacen Ɓaure

29 Sai ya ba su wani misali, ya ce, “Ku dubi itacen ɓaure da dukan itatuwa,

30 da zarar sun fara toho, kuna gani, ku da kanku kun san damuna ta yi kusa ke nan.

31 Haka kuma sa’ad da kuka ga waɗannan al’amura suna aukuwa, ku sani Mulkin Allah ya gabato.

32 Hakika, ina gaya muku, zamanin nan ba zai shuɗe ba, sai duk abubuwan nan sun auku.

33 Sararin sama da ƙasa za su shuɗe, amma maganata ba za ta shuɗe ba.”

Gargaɗi a Zauna a Faɗake

34 “Ku kula da kanku fa, kada zuciyarku ta zarme da yawan shaye-shaye da buguwa, da kuma taraddadin wannan duniya, har ba labari ranan nan ta mamaye ku kamar tarko.

35 Don haka, za ta auka wa mazaunan duniya duk, kowa da kowa.

36 Koyaushe ku zauna a faɗake, kuna addu’a ku sami ikon tsere wa dukan waɗannan al’amura da za su auku, ku kuma tsaya a gaban Ɗan Mutum.”

37 Kullum da rana yakan koyar a Haikali, da dare kuma yakan fita ya kwana a dutsen da ake ce da shi Dutsen Zaitun.

38 Da sassafe kuma dukan mutane sukan zo wurinsa a Haikali su saurare shi.

Categories
LUK

LUK 22

An Ƙulla Shawara gāba da Yesu

1 To, idin abinci marar yisti, wanda ake ce da shi Idin Ƙetarewa, ya gabato.

2 Sai manyan firistoci da malaman Attaura suka yi ta neman yadda za su kashe shi, amma kuwa suna tsoron jama’a.

3 Sai Shaiɗan ya shiga Yahuza, wanda ake kira Iskariyoti, ɗaya daga cikin sha biyun nan.

4 Sai ya tafi ya yi shawara da manyan firistoci da shugabannin dogaran Haikali a kan yadda zai bāshe shi a gare su.

5 Sai suka yi murna, suka kuma yi alkawarin ba shi kuɗi.

6 Shi kuwa ya yarda, ya kuma nemi hanyar bāshe shi a gare su bayan idon jama’a.

Yesu Ya Ci Jibin Ƙetarewa tare da Almajiransa

7 Sai ranar idin abinci marar yisti ta zo, wato, rana da ake yanka ɗan ragon Idin Ƙetarewa.

8 Sai Yesu ya aiki Bitrus da Yahaya, ya ce musu, “Ku je ku shirya mana Jibin Ƙetarewa mu ci.”

9 Suka ce masa, “Ina kake so mu shirya?”

10 Ya ce musu, “Ga shi, da shigarku gari, za ku gamu da wani mutum ɗauke da tulun ruwa. Ku bi shi har zuwa cikin gidan da ya shiga.

11 Ku ce wa maigidan, ‘Malam ya ce, ina masaukin da zai ci Jibin Ƙetarewa da almajiransa?’

12 Shi kuwa zai nuna muku wani babban soron bene mai kaya a shirye. A nan za ku shirya mana.”

13 Sai suka tafi, suka kuwa tarar kamar yadda ya faɗa musu, suka shirya Jibin Ƙetarewa.

Cin Jibin Ubangiji

14 Da lokaci ya yi, sai ya zauna cin abinci, manzanninsa kuma suna tare da shi.

15 Ya ce musu, “Ina so ƙwarai ko dā ma in ci jibin nan na Ƙetarewa tare da ku, kafin in sha wuya.

16 Gama ina gaya muku ba zan ƙara cin sa ba, sai an cika shi a Mulkin Allah.”

17 Sai ya karɓi ƙoƙo, bayan da ya yi godiya ga Allah, ya ce, “Ungo wannan, ku shassha.

18 Ina gaya muku, daga yanzu, ba zan ƙara shan ruwan inabi ba, sai Mulkin Allah ya bayyana.”

19 Sai ya ɗauki gurasa, bayan da ya yi godiya ga Allah, ya gutsuttsura, ya ba su, ya ce, “Wannan jikina ne da za a bayar dominku. Ku riƙa yin haka, domin tunawa da ni.”

20 Haka kuma, bayan jibi, ya ɗauki ƙoƙon, ya ce, “Ƙoƙon nan sabon alkawari ne, da aka tabbatar da jinina da za a bayar dominku.

21 Amma ga shi, mai bashe ni ɗin nan yana ci a akushi ɗaya da ni.

22 Lalle Ɗan Mutum zai ƙaura kamar yadda aka ƙaddara, duk da haka, kaiton mutumin nan da yake ba da shi!”

23 Sai suka fara tambayar juna ko wane ne a cikinsu zai yi haka.

Mūsū a kan Ko wane ne Babba

24 Sai musu ya tashi a tsakaninsu, a kan ko wane ne babbansu.

25 Sai ya ce musu, “Sarakunan al’ummai sukan nuna musu iko, mahukuntansu kuma sukan nema a ce da su, ‘Mataimakan jama’a.’

26 Amma ku kam ba haka ba. Sai dai wanda yake babba a cikinku yă zama kamar ƙarami, shugaba kuwa yă zama kamar mai hidima.

27 Wa ya fi girma? Wanda ya zauna cin abinci, ko kuwa mai hidimar? Ashe, ba wanda ya zauna cin abinci ba ne? Ga shi kuwa, ina a cikinku kamar mai hidima.

28 “Ku ne kuka tsaya gare ni a gwaje-gwajen da na sha.

29 Kamar yadda Ubana ya ba ni mulki, haka, ni ma nake ba ku iko,

30 ku ci ku sha tare da ni a mulkina, ku kuma zauna a kursiyai, kuna hukunta kabilan nan goma sha biyu na Isra’ila.

Bitrus zai yi Mūsun Sanin Yesu

31 “Bitrus, ya Bitrus, Shaiɗan ya nemi izinin sheƙe ku kamar alkama, ya kuwa samu.

32 Ni kuwa na yi maka addu’a, kada bangaskiyarka ta kāsa. Kai kuma, bayan da ka juyo, sai ka ƙarfafa ‘yan’uwanka.”

33 Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, a shirye nake in bi ka har cikin kurkuku, ko kuma Lahira.”

34 Yesu ya ce, “Ina dai gaya maka Bitrus, a yau ma, kafin carar zakara, za ka yi musun sanina sau uku.”

Jakar Kuɗi, Burgami da Takobi

35 Ya kuma ce musu, “Sa’ad da na aike ku ba kuɗi a ɗamararku, ba burgami, ba takalma, akwai abin da kuka rasa?” Suka ce, “Babu.”

36 Ya ce musu, “Amma a yanzu duk mai jakar kuɗi yă ɗauka, haka kuma mai burgami. Wanda kuwa ba shi da takobi, ya sayar da mayafinsa ya saya.

37 Ina dai gaya muku, lalle ne a cika wannan Nassi a kaina cewa, ‘An lasafta shi a cikin masu laifi.’ Gama abin da aka faɗa a kaina, tabbatarsa ta zo.”

38 Sai suka ce, “Ya Ubangiji, ai, ga takuba biyu.” Ya ce musu, “Ya isa.”

Yesu Ya Yi Addu’a a Gatsemani

39 Sai ya fita ya tafi Dutsen Zaitun, kamar yadda ya saba. Almajiransa kuwa suka bi shi.

40 Da ya iso wurin, ya ce musu, “Ku yi addu’a, kada ku faɗa ga gwaji.”

41 Sai ya ɗan rabu da su misalin nisan jifa, ya durƙusa, ya yi addu’a.

42 Ya ce, “Ya Uba, in dai ka yarda, ka ɗauke mini ƙoƙon wahalan nan. Duk da haka dai, ba nufina ba, sai naka za a bi” [

43 Sai wani mala’ika ya bayyana a gare shi daga Sama, yana ƙarfafa shi.

44 Domin kuma yana shan wahala gaya, sai ya ƙara himmar addu’a, har jiɓinsa yana ɗiɗɗiga ƙasa kamar manyan ɗarsashin jini.]

45 Da ya tashi daga addu’a, ya koma wurin almajiran, ya tarar suna barci saboda baƙin ciki.

46 Sai ya ce musu, “Don me kuke barci? Ku tashi, ku yi addu’a, kada ku faɗa ga gwaji.”

An Ba da Yesu, an Kama Shi

47 Kafin ya rufe baki, sai ga taron jama’a suka zo, mutumin da ake kira Yahuza, ɗaya daga cikin sha biyun nan, yake musu jagaba. Sai ya matso kusa da Yesu, don ya sumbace shi.

48 Amma Yesu ya ce masa, “Yahuza, ashe, da sumba za ka ba da Ɗan Mutum?”

49 Da na kusa da shi suka ga abin da za a yi, suka ce, “Ya Ubangiji, mu yi sara da takuba ne?”

50 Sai ɗayansu ya kai wa bawan babban firist sara, ya ɗauke masa kunnensa na dama.

51 Yesu ya amsa ya ce, “Ku ƙyale su haka.” Sai ya taɓa kunnen bawan, ya warkar da shi.

52 Yesu kuma ya ce wa waɗanda suka tasar masa, wato, manyan firistoci da shugabannin dogaran Haikali da shugabannin jama’a, “Kun fito ne da takuba da kulake, kamar masu kama ɗan fashi?

53 Sa’ad da nake tare da ku kowace rana a cikin Haikali, ba ku miƙa hannu garin ku kama ni ba. Amma wannan lokacinku ne da na ikon duhu.”

Bitrus Ya Yi Musun Sanin Yesu

54 Sai suka kama shi, suka tafi da shi, suka kai shi cikin gidan babban firist. Bitrus kuwa yana biye daga nesa nesa.

55 Da suka hura wuta a tsakar gida suka zazzauna, Bitrus ma ya zauna a cikinsu.

56 Sai wata baranya ta gan shi zaune a hasken wuta, ta zura masa ido, ta ce, “Ai, mutumin nan ma, tare da shi yake.”

57 Amma ya musa ya ce, “Ke, ban ma san shi ba.”

58 Bayan ɗan lokaci kaɗan kuma, sai wani ya gan shi, ya ce, “Kai ma, ai, ɗayansu ne.” Amma Bitrus ya ce, “Ya mutum, ba haka ba ne.”

59 Bayan wajen sa’a guda sai wani ya nace, ya ce, “Ba shakka mutumin nan ma tare da shi yake, don Bagalile ne.”

60 Amma Bitrus ya ce, “Haba, ban ma san abin da kake faɗa ba.” Nan take, kafin ya rufe baki, sai zakara ya yi cara.

61 Sai Ubangiji ya juya ya dubi Bitrus. Bitrus kuwa ya tuna da maganar da Ubangiji ya faɗa masa cewa, “A yau ma kafin carar zakara, za ka yi musun sanina sau uku.”

62 Sai ya fita waje, ya yi ta rusa kuka.

An Yi wa Yesu Ba’a, an Dūke Shi

63 Sai mutanen da suke riƙe da Yesu suka yi ta masa ba’a, suna dūkansa.

64 Suka ɗaure masa idanu, suka tambaye shi, suka ce, “Yi annabci! Wa ya buge ka?”

65 Suka kuma yi ta masa baƙaƙen maganganu masu yawa, suna zaginsa.

Yesu a gaban ‘Yan Majalisa

66 Da gari ya waye sai majalisar shugabannin jama’a ta haɗu, da manyan firistoci da kuma malaman Attaura. Suka kai shi ɗakin majalisarsu suka ce,

67 “To, in kai ne Almasihu, gaya mana.” Amma ya ce musu, “Ko na gaya muku, ba za ku gaskata ba.

68 In kuma na yi muku tambaya, ba za ku mai da jawabi ba.

69 Amma nan gaba, Ɗan Mutum zai zauna dama na Allah Mai iko.”

70 Duk suka ce, “Ashe, kai ɗin nan Ɗan Allah ne?” Sai ya ce musu, “Yadda kuka faɗa, ni ne.”

71 Sai suka ce, “Wace shaida kuma za mu nema? Ai, mun ji da kanmu daga bakinsa.”

Categories
LUK

LUK 23

Yesu a gaban Bilatus

1 Duk taronsu sai suka tashi, suka kai shi gaban Bilatus.

2 Sai suka fara kai ƙararsa, suna cewa, “Mun sami mutumin nan yana ɓad da jama’armu, yana hana a biya Kaisar haraji, yana cewa, shi ne Almasihu, sarki kuma.”

3 Sai Bilatus ya tambaye shi ya ce, “Ashe, kai ɗin nan, kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya amsa ya ce, “Yadda ka faɗa.”

4 Bilatus ya ce wa manyan firistoci da taro masu yawa, “Ban sami mutumin nan da wani laifi ba.”

5 Sai suka fara matsa masa lamba, suna cewa, “Yana ta da hankalin jama’a, yana koyarwa a dukan ƙasar Yahudiya, tun daga ƙasar Galili har zuwa nan.”

Yesu a gaban Hirudus

6 Da Bilatus ya ji haka, ya tambaya ko mutumin nan Bagalile ne.

7 Da ya ji Yesu a ƙarƙashin mulkin Hirudus yake, sai ya aika da shi wurin Hirudus, don shi ma yana Urushalima a lokacin.

8 Da Hirudus ya ga Yesu, ya yi murna ƙwarai, saboda tun da daɗewa yake son ganinsa, don ya riga ya ji labarinsa, yana kuma fata ya ga wata mu’ujiza da Yesu zai yi.

9 Sai ya yi ta masa tambayoyi da yawa, amma bai amsa masa da kome ba.

10 Manyan firistoci da malaman Attaura na nan a tsaitsaye, suna tsananta kai ƙararrakinsa ainun.

11 Sai Hirudus da sojansa suka wulakanta shi, suka yi masa ba’a, da suka sa masa tufafi masu ƙawa kuma, suka mai da shi wurin Bilatus.

12 A ran nan sai Hirudus da Bilatus suka yi sulhu, don dā abokan gāba ne.

An Hukunta wa Yesu Mutuwa

13 Bilatus ya tara manyan firistoci da shugabanni da kuma jama’a,

14 ya ce masu, “Kun kawo mini mutumin nan a kan, wai yana ɓad da jama’a, na kuwa tuhunce shi a gabanku, amma ban same shi da wani laifi a ƙararrakinsa da kuka kawo ba.

15 Hirudus ma bai samu ba, don ya komo mana da shi. Ga shi kuwa, bai yi wani abu da ya cancanci kisa ba.

16 Saboda haka, zan yi masa bulala in sake shi.”[

17 A lokacin idi kuwa lalle ne ya sakar musu ɗaurarre guda.]

18 Amma duk suka ɗauki ihu gaba ɗaya, suna cewa, “A yi da wannan ɗin, a sakar mana Barabbas!”

19 (Barabbas shi ne wani mutum da aka jefa a kurkuku, saboda wani tawayen da aka yi a birni, da kuma kisankai.)

20 Sai Bilatus ya sāke yi musu magana, don yana so ya saki Yesu.

21 Amma suka yi ta ƙwala ihu, suna cewa, “A gicciye shi! A gicciye shi!”

22 Ya sāke faɗa musu, a faɗa ta uku, “Ta wane hali? Wane mugun abu ya yi? Ai, ban sami dalilin kisa a gare shi ba. Saboda haka, zan yi masa bulala in sake shi.”

23 Amma suka yi ta matsa lamba, suna ɗaga murya, suna cewa a gicciye shi, har surutunsu ya yi rinjaye.

24 Sai Bilatus ya zartar da hukunci a biya musu bukata.

25 Ya kuwa sakar musu wanda suka roƙa, wato, wanda aka jefa a kurkuku a kan laifin tawaye da kuma kisankai. Amma ya ba da Yesu, su yi masa abin da suke so.

An Gicciye Yesu

26 Suna tafiya da Yesu yake nan, sai suka cafke wani, mai suna Saminu Bakurane, yana zuwa daga ƙauye, suka ɗora masa gicciye, yă ɗauka ya bi Yesu.

27 Sai taron mutane masu yawan gaske suka bi shi, da waɗansu mata da suke kuka, suke kuma gunji saboda shi.

28 Amma Yesu ya juya gare su, ya ce, “Ya ku matan Urushalima, ku bar yi mini kuka, sai dai ku yi wa kanku da kuma ‘ya’yanku,

29 don lokaci na zuwa da za su ce, ‘Albarka tā tabbata ga matan da suke bakararru, waɗanda ba su taɓa haihuwa ba, waɗanda kuma ba a taɓa shan mamansu ba.’

30 Sa’an nan ne za su fara ce wa manyan duwatsu, ‘Ku faɗo a kanmu,’ su kuma ce da tsaunuka, ‘Ku binne mu.’

31 In fa irin abubuwan nan suna faruwa ga ɗanye, yaya zai zama ga ƙeƙasasshe?”

32 Waɗansu mutum biyu kuma masu laifi, aka kai su a kashe su tare da shi.

33 Da suka isa wurin da ake ce da shi Ƙoƙwan Kai, nan suka gicciye shi, da kuma masu laifin nan, ɗaya a damansa, ɗaya a hagun.

34 Sai Yesu ya ce, “Ya Uba, ka yi musu gafara, don ba su san abin da suke yi ba.” Suka rarraba tufafinsa, suna kuri’a a kansu.

35 Mutane da suke tsaitsaye, suna kallo. Shugabanni kuma suka yi masa ba’a, suka ce, “Ya ceci waɗansu, to, ya ceci kansa mana, in shi ne Almasihu na Allah zaɓaɓɓensa!”

36 Soja kuma suka yi masa ba’a, suka matso, suka miƙa masa ruwan tsami,

37 suna cewa, “In kai ne Sarkin Yahudawa, to, ka cece kanka mana!”

38 Sama da shi kuma aka yi wani rubutu cewa, “Wannan shi ne Sarkin Yahudawa.”

39 Sai ɗaya daga cikin masu laifin da aka gicciye ya yi masa baƙar magana ya ce, “Shin, ba kai ne Almasihu ba? To, ceci kanku mana, duk da mu!”

40 Amma ɗayan ya amsa, ya kwaɓe shi, ya ce, “Kai ko tsoron Allah ma ba ka yi, kai, da yake hukuncinka daidai da nasa?

41 Mu kam, daidai aka yi mana, don hakika sakamakon aikinmu muka samu, amma mutumin nan bai yi wani laifi ba.”

42 Ya kuma ce, “Ya Yesu, ka tuna da ni, sa’ad da ka shiga sarautarka.”

43 Yesu ya ce masa, “Hakika, ina gaya maka, yau ma za ka kasance tare da ni a Firdausi.”

Mutuwar Yesu

44 To, wajen tsakar rana ne kuwa, sai duhu ya rufe ƙasa duka, har zuwa ƙarfe uku na yamma.

45 Hasken rana ya dushe. Labulen da yake cikin Haikali ya tsage gida biyu.

46 Sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Ya Uba, na sa ruhuna a ikonka.” Da ya faɗi haka kuwa, sai ya cika.

47 Sa’ad da jarumin ya ga abin da ya gudana, sai ya girmama Allah ya ce, “Hakika mutumin nan marar laifi ne!”

48 Sa’ad da duk taro masu yawa, waɗanda suka zo kallo suka ga abin da ya faru, suka koma, suna bugun ƙirjinsu.

49 Amma duk idon sani, da kuma matan da suka biyo shi, tun daga ƙasar Galili, suka tsaya daga nesa, suna duban waɗannan abubuwa.

Jana’izar Yesu

50 To, akwai wani mutum mai suna Yusufu, mutumin Arimatiya, wani garin Yahudawa, shi ɗan majalisa ne, nagari ne, adali kuma.

51 Shi kuwa dā ma bai yarda da shawararsu, da kuma abin da suka yi ba, yana kuwa sauraron bayyanar Mulkin Allah.

52 Shi ne ya tafi wurin Bilatus, ya roƙa a ba shi jikin Yesu.

53 Sai ya sauko da shi, ya sa shi a likkafanin lilin, ya sa shi a wani kabari da aka fafe dutse aka yi, wanda ba a taɓa sa kowa ba.

54 Ran nan kuwa ranar shiri ce, Asabar kuma ta doso.

55 Matan nan kuwa da suka zo tare da shi daga ƙasar Galili, suka bi baya, suka duba kabarin da yadda kuma aka sa jikinsa.

56 Sai suka koma, suka shirya kayan ƙanshi da man shafawa.

Ran Asabar kuwa, sai suka huta bisa ga umarni.

Categories
LUK

LUK 24

Tashin Yesu daga Matattu

1 A ranar farko ta mako kuwa, da asussuba, suka je wurin kabarin da kayan ƙanshi da suka shirya.

2 Sai suka tarar an mirgine dutsen daga kabarin.

3 Suka shiga ciki, amma ba su sami jikin Ubangiji ba.

4 Tun suna cikin damuwa da abin, sai kawai ga waɗansu mutum biyu a tsaye kusa da su, saye da tufafi masu ƙyalƙyali.

5 Don tsoro, matan suka sunkuyar da kansu ƙasa. Mutanen suka ce musu, “Don me kuke neman rayayye a cikin matattu?

6 Ai, ba ya nan, ya tashi. Ku tuna yadda ya gaya muku tun yana Galili

7 cewa, ‘Lalle ne a ba da Ɗan Mutum ga mutane masu zunubi, a gicciye shi, a rana ta uku kuma ya tashi’.”

8 Sai suka tuna da maganarsa.

9 Da suka dawo daga kabarin suka shaida wa goma sha ɗayan nan, da kuma duk sauransu, dukan waɗannan abubuwa.

10 To, Maryamu Magadaliya, da Yuwana, da Maryamu uwar Yakubu, da kuma sauran matan da suke tare da su, su ne suka gaya wa manzannin waɗannan abubuwa.

11 Su kuwa sai maganan nan ta zama musu kamar zance ne kawai, suka ƙi gaskatawa.

12 Amma Bitrus ya tashi, ya doshi kabarin da gudu. Ya duƙa, ya leƙa a ciki, ya ga likkafanin lilin a ajiye waje ɗaya. Sai ya koma gida yana al’ajabin abin da ya auku.

Almajirai Biyu a Hanyar Imuwasu

13 A ran nan kuma sai ga waɗansu biyu suna tafiya wani ƙauye, mai suna Imuwasu, nisansa daga Urushalima kuwa kusan mil bakwai ne.

14 Suna ta zance da juna a kan dukan al’amuran da suka faru.

15 Ya zamana tun suna magana, suna tunani tare, sai Yesu da kansa ya matso, suka tafi tare.

16 Amma idanunsu a rufe, har ba su gane shi ba.

17 Yesu ya ce musu, “Wace magana ce kuke yi da juna a tafe?” Sai suka tsaya cik, suna baƙin ciki.

18 Sai ɗayansu, mai suna Kiliyobas, ya amsa masa ya ce, “Ashe, kai kaɗai ne baƙo a Urushalima, da ba ka san abubuwan da suka faru a can, ‘yan kwanakin nan ba?”

19 Sai ya ce musu, “Waɗanne abubuwa?” Suka ce masa, “Game da Yesu Banazare ne, wanda yake annabi mai manyan ayyuka da ƙwaƙƙwarar magana a gaban Allah da dukan mutane,

20 da kuma yadda manyan firistoci da shugabanninmu suka ba da shi don a yi masa hukuncin kisa, suka kuwa gicciye shi.

21 Dā kuwa muna bege shi ne zai fanshi Isra’ila. Hakika kuma, bayan wannan duka, yau kwana uku ke nan da aukuwar wannan abu.

22 Har wa yau kuma, waɗansu mata na cikinmu, sun ba mu al’ajabi. Don sun je kabarin da sassafe,

23 da ba su sami jikinsa ba, suka komo, suka ce har ma an yi musu wahayi, sun ga mala’ikun da suka ce yana da rai.

24 Waɗansunsu da suke tare da mu kuma, suka je kabarin, suka tarar kamar yadda matan suka faɗa, amma shi, ba su gan shi ba.”

25 Sai Yesu ya ce musu, “Ya ku mutane marasa fahimta, masu nauyin gaskata duk abin da annabawa suka faɗa!

26 Ashe, ba wajibi ne Almasihu ya sha wuyar waɗannan abubuwa ba, ya kuma shiga ɗaukakarsa?”

27 Sai ya fara ta kan littattafan Musa da na dukan annabawa, ya yi ta bayyana musu abubuwan da suka shafe shi a dukan Littattafai.

28 Sai suka kusato ƙauyen da za su. Ya yi kamar zai ci gaba,

29 suka matsa masa suka ce, “Sauka a wurinmu, ai, magariba ta doso, rana duk ta tafi.” Sai ya sauka a wurinsu.

30 Sa’ad da yake cin abinci tare da su, sai ya ɗauki gurasa, ya yi wa Allah godiya, ya gutsura, ya ba su.

31 Idonsu ya buɗe, suka kuma gane shi. Sai ya ɓace musu.

32 Suka ce wa juna, “Ashe, zuciyarmu ba ta yi annuri ba, sa’ad da yake a hanya, yana bayyana mana Littattafai?”

33 Anan take, suka tashi suka koma Urushalima, suka sami sha ɗayan nan tare gu ɗaya, da kuma waɗanda suke tare da su,

34 suna cewa, “Hakika Ubangiji ya tashi, har ya bayyana ga Bitrus!”

35 Su kuma suka ba da labarin abin da ya faru a hanya, da kuma yadda suka gane shi a wajen gutsura gurasa.

Yesu ya Bayyana ga Almajiransa

36 Suna cikin faɗar waɗannan abubuwa, sai ga Yesu da kansa tsaye a tsakiyarsu, ya ce musu, “Salama alaikun!”

37 Amma suka firgita, tsoro ya kama su, suka zaci fatalwa suke gani.

38 Sai ya ce musu, “Don me kuka firgita, kuke kuma tantama a zuciyarku?

39 Ku dubi hannuwana da ƙafafuna, ai, ni ne da kaina. Ku taɓa ni, ku ji, don fatalwa ba ta da nama da ƙashi, yadda kuke gani nake da su.”

40 Da ya faɗi haka, ya nuna musu hannuwansa da ƙafafunsa.

41 Amma tun suna da sauran shakka saboda tsananin farin ciki da mamaki, sai ya ce musu, “Kuna da wani abinci a nan?”

42 Sai suka ba shi wata tsokar gasasshen kifi.

43 Ya kuwa karɓa, ya ci a gabansu.

44 Ya kuma ce musu, “Wannan ita ce maganata da na gaya muku tun muna tare, cewa lalle ne a cika duk abin da yake rubuce game da ni a Attaura ta Musa, da littattafan annabawa, da kuma Zabura.”

45 Sa’an nan ya wayar da hankalinsu su fahimci Littattafai,

46 ya kuma ce musu, “Haka yake a rubuce, cewa wajibi ne Almasihu ya sha wuya, a rana ta uku kuma ya tashi daga matattu,

47 a kuma yi wa dukan al’ummai wa’azi su tuba, a gafarta musu zunubansu saboda sunansa. Za a kuwa fara daga Urushalima.

48 Ku ne shaidun waɗannan abubuwa.

49 Ga shi, ni zan aiko muku da abin da Ubana ya alkawarta. Amma ku dakata a birni tukuna, har a yi muku baiwar iko daga Sama.”

An Ɗauke Yesu zuwa Sama

50 Sai ya kai su waje har jikin Betanya. Ya ɗaga hannuwansa ya sa musu albarka.

51 Yana sa musu albarka ke nan, sai ya rabu da su, aka ɗauke shi zuwa sama.

52 Su kuwa suka yi masa sujada, suka koma Urushalima, suna matuƙar farin ciki.

53 Ko yaushe kuma suna a Haikali suna yabon Allah.