Categories
M. SH

M. SH 1

Musa Ya Jaddada wa Isra’ilawa Alkawarin Ubangiji a Horeb

1 Waɗannan su ne zantuttukan da Musa ya faɗa wa dukan Isra’ilawa a hayin Urdun cikin jejin Araba daura da Suf, tsakanin Faran, da Tofel, da Laban, da Hazerot, da Dizahab.

2 Tafiyar kwana goma sha ɗaya ne daga Horeb zuwa Kadesh-barneya, ta hanyar Dutsen Seyir.

3 A shekara ta arba’in, a rana ta fari ga watan goma sha ɗaya, Musa ya faɗa wa Isra’ilawa dukan abin da Ubangiji ya umarce shi ya faɗa musu.

4 A lokacin kuwa ya riga ya ci Sihon, Sarkin Amoriyawa, wanda yake zaune a Heshbon, da Og, Sarkin Bashan, wanda yake zaune a Ashtarot, da Edirai.

5 A hayin Urdun, cikin ƙasar Mowab, Musa ya yi niyya ya fassara waɗannan dokoki.

Ya ce,

6 “Ubangiji Allahnmu ya faɗa mana a Horeb, ya ce, ‘Daɗewarku a wannan dutse ta isa.

7 Ku tashi, ku yi gaba zuwa ƙasar duwatsun Amoriyawa, da dukan maƙwabtansu waɗanda suke a Araba. Ku shiga tuddai, da kwaruruka, da Negeb, da bakin bahar, da ƙasar Kan’aniyawa, da Lebanon, har zuwa babban kogi, wato Kogin Yufiretis.

8 Duba, na sa ƙasar a gabanku, sai ku shiga ku mallake ta, ƙasa wadda na rantse wa kakanninku, wato Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, cewa zan ba su, su da zuriyarsu a bayansu.’ ”

Sa shugabanni

9 “A wancan lokaci ne na yi magana, na ce, ‘Ba zan iya ɗaukar nawayarku ba,

10 gama Ubangiji ya riɓaɓɓanya ku, har yawanku ya kai kamar taurarin sama.

11 Ubangiji Allah na kakanninku ya riɓa yawanku har sau dubu, ya sa muku albarka yadda ya alkawarta muku!

12 Ƙaƙa ni kaɗai zan iya ɗaukar nawayarku da wahalarku da kuma faɗace-faɗacenku?

13 Ku zaɓi masu hikima, da masu ganewa daga cikin kabilanku, waɗanda suka saba da zaman jama’a, ni kuwa in sa su zama shugabanninku!’

14 Kuka amsa mini, kuka ce, ‘I, daidai ne kuwa mu bi shawaran nan da ka kawo mana.’

15 Don haka na ɗauko shugabannin kabilanku masu hikima, waɗanda suka saba da ma’amala da jama’a, na sa su shugabanni a gabanku, waɗansu suka zama shugabanni a kan dubu dubu, waɗansu a kan ɗari ɗari, waɗansu a kan hamsin hamsin, waɗansu kuma a kan goma goma. Na sa su zama shugabanni a kabilanku.

16 “A wannan lokaci kuma na umarci shugabanninku na ce, ‘Ku yi adalci cikin shari’a tsakanin ‘yan’uwanku, tsakanin mutum da ɗan’uwansa, ko kuma da baren da yake zaune tare da shi.

17 Kada ku nuna bambanci cikin shari’a, ko babban mutum ne ko talaka, duka biyu za ku ji su. Kada ku ji tsoron fuskar mutum, gama shari’a ta Allah ce. In kuwa shari’a ta fi ƙarfinku, sai ku kawo ta wurina, ni kuwa zan yanke ta.’

18 A wancan lokaci na umarce ku da dukan abin da ya kamata ku yi.”

An Aiki ‘Yan Leƙen Asirin Ƙasa

19 “Sai muka tashi daga Horeb, muka ratsa babban jejin nan mai bantsoro wanda kuka gani a hanyarmu zuwa ƙasar tuddai ta Amoriyawa, kamar yadda Ubangiji Allahnmu ya umarce mu, muka zo Kadesh-barneya.

20 Sa’an nan na faɗa muku cewa, ‘Kun iso ƙasar tuddai ta Amoriyawa wadda Ubangiji Allahnmu yake ba mu.

21 Ga ƙasar a gabanku wadda Ubangiji Allahnku yake ba ku, sai ku haura ku mallake ta yadda Ubangiji Allah na kakanninku ya faɗa muku. Kada ku ji tsoro ko ku firgita.’

22 “Sa’an nan sai dukanku kuka zo wurina, kuka ce, ‘Bari mu aika da mutane, su je su leƙo mana asirin ƙasar tukuna, domin su shawarce mu ta hanyar da za mu bi, da kuma irin biranen da za mu shiga.’

23 “Na ga al’amarin ya gamshe ni, saboda haka na ɗauki mutum goma sha biyu daga cikinku, mutum guda daga kowace kabila.

24 Mutanen kuwa suka kama hanya, suka tafi tuddai, suka kuma isa kwarin Eshkol, suka leƙo asirin ƙasar.

25 Da hannunsu suka ɗebo daga cikin amfanin ƙasar, suka gangaro mana da shi. Suka kuma faɗa mana cewa ƙasa wadda Ubangiji Allahnmu yake ba mu, mai kyau ce.

26 “Amma kuka ƙi ku haura, kuka ƙi bin umarnin Ubangiji Allahnku.

27 Sai kuka yi ta gunaguni cikin alfarwanku, kuna cewa, ‘Ai, saboda Ubangiji ya ƙi mu, shi ya sa ya fisshe mu daga ƙasar Masar, don ya bashe mu a hannun Amoriyawa, su hallaka mu.

28 Ta ƙaƙa za mu hau? Gama ‘yan’uwanmu sun narkar da zuciyarmu da cewa, mutanen sun fi mu girma, sun kuma fi mu ƙarfi. Biranensu kuma manya manya ne, da gine-gine masu tsayi ƙwarai. Har ma sun ga Anakawa a wurin.’

29 “Sai na ce muku, ‘Kada ku ji tsoronsu ko ku firgita.

30 Ubangiji Allahnku wanda yake tafiya tare da ku, shi kansa zai yi yaƙi dominku kamar yadda ya yi muku a Masar a kan idonku.

31 Kun ma ga yadda Ubangiji ya bi da ku cikin jeji kamar yadda mutum yakan bi da ɗansa, a dukan tafiyarku har zuwa wannan wuri.’

32 Amma ko da yake ya yi muku haka duk da haka ba ku dogara ga Ubangiji Allahnku ba.

33 Shi wanda ya bishe ku, ya nuna muku inda za ku yi zango. Da dare yakan nuna muku hanya da wuta, da rana kuma yakan bi da ku da girgije.”

Hukuncin Allah a kan Isra’ilawa

34 “Ubangiji kuwa ya ji maganganunku, sai ya yi fushi, ya rantse, ya ce,

35 ‘Daga cikin mutanen wannan muguwar tsara ba wanda zai ga ƙasan nan mai albarka wadda na rantse zan ba kakanninku,

36 sai dai Kalibu ɗan Yefunne, shi kaɗai ne zai gan ta. Zan ba shi da ‘ya’yansa ƙasar da ƙafarsa ta taka, gama shi ne ya bi Ubangiji sosai.’

37 Ubangiji ma ya yi fushi da ni sabili da ku, ya ce, ‘Har kai ma ba za ka shiga ba.

38 Baranka, Joshuwa ɗan Nun, shi ne zai shiga. Sai ka ƙarfafa masa zuciya gama shi ne zai bi da Isra’ilawa, har su amshi ƙasar, su gaje ta.’

39 “Sa’an nan Ubangiji ya ce wa dukanmu, ‘Amma ‘ya’yanku ƙanana waɗanda ba su san mugunta ko nagarta ba, waɗanda kuke tsammani za a kwashe su ganima, su ne za su shiga ƙasar. Ni Ubangiji zan ba su su mallake ta.

40 Amma ku, sai ku koma cikin jeji ta hanyar Bahar Maliya.’ ”

An Ci Isra’ilawa da Yaƙi a Horma

41 “Sa’an nan kuka amsa mini, kuka ce, ‘Mun yi wa Ubangiji Allahnmu zunubi. Za mu tafi mu yi yaƙi bisa ga faɗar Ubangiji Allahnmu.’ Sai kowannenku ya yi ɗamara ya ɗauki makaman yaƙinsa, kuka yi tsammani abu mai sauƙi ne ku shiga ƙasar tuddai.

42 “Amma Ubangiji ya ce mini in faɗa muku, kada ku tafi kada kuma ku yi yaƙi, gama ba ya tare da ku. Maƙiyanku za su kore ku.

43 Haka kuwa na faɗa muku, amma ba ku kasa kunne ba, kuka ƙi yin biyayya da umarnin Ubangiji. Sai kuka yi izgili, kuka hau cikin ƙasar tuddai.

44 Sai Amoriyawa waɗanda suke zaune a ƙasar tuddai suka fito da yawa kamar ƙudan zuma, suka taru a kanku suka bi ku, suka fatattaka ku a Seyir, har zuwa Horma.

45 Sai kuka koma, kuka yi kuka ga Ubangiji, amma Ubangiji bai ji kukanku ba, bai kuma kula da ku ba.

46 Kun kuwa zauna cikin Kadesh kwana da kwanaki, kamar dai yadda kuka yi.”

Categories
M. SH

M. SH 2

Shekarun da suka Yi a Jeji

1 “Muka koma cikin jeji ta hanyar Bahar Maliya kamar yadda Ubangiji ya faɗa mini. Muka daɗe muna ta gewaya ƙasar tuddai ta Seyir.

2 “Sai Ubangiji ya ce mini.

3 ‘Ai, kun daɗe kuna ta gewaya waɗannan tuddai. Ku juya, ku nufi arewa.

4 Ka umarci jama’a, su bi yankin ƙasar zuriyar Isuwa, danginku, waɗanda suke zaune a Seyir. Za su ji tsoronku, sai ku yi hankali,

5 kada ku tsokane su, gama ko wurin sa ƙafa a ƙasarsu ba zan ba ku ba, gama na riga na ba Isuwa ƙasar tuddai ta Seyir.

6 Za ku sayi abincin da za ku ci, da ruwan da za ku sha a wurinsu.

7 Gama Ubangiji Allahnku ya sa albarka a kan dukan ayyukan hannuwanku. Ya kuma san tafiye-tafiyenku cikin babban jejin nan. Ubangiji Allahnku yana tare da ku a shekara arba’in ɗin nan, ba ku rasa kome ba.’

8 “Muka yi gaba, muka bar zuriyar Isuwa ‘yan’uwan nan namu waɗanda suke zaune a ƙasar tuddai ta Seyir, muka bar hanyar Araba, da hanyar Elat da Eziyon-geber. Muka juya, muka nufi wajen jejin Mowab.

9 “Sai Ubangiji ya ce mini, ‘Kada ku dami Mowabawa, ko kuwa ku tsokane su, gama ba zan ba ku ƙasarsu ku mallake ta ba. Na riga na bayar da Ar ta zama mallakar zuriyar Lutu.’ ”

10 (Emawa manya ne, masu yawa, dogaye ne kuma kamar Anakawa. Su ne suke zaune a ƙasar a dā.

11 Su ma akan lasafta su Refayawa tare da Anakawa, amma Mowabawa suka ce da su Emawa.

12 Haka nan kuma a dā Horiyawa ne suke zaune a ƙasar Seyir, amma mutanen zuriyar Isuwa suka zo, suka kore su, suka karkashe su, suka zauna a wurin, daidai kamar yadda Isra’ilawa suka yi da ƙasar mallakarsu, wadda Ubangiji ya ba su.)

13 “ ‘Yanzu, ku tashi ku haye rafin Zered da kanku.’ Sai kuwa muka haye.

14 Lokacin da muka tashi daga Kadesh-barneya zuwa lokacin da muka haye rafin Zered, shekara talatin da takwas ne. Duk wannan lokaci dukan waɗanda suka isa yaƙi suka murmutu kamar yadda Ubangiji ya rantse a kansu.

15 Hakika kuwa ikon Ubangiji ya buge su har suka hallaka ƙaƙaf.

16 “Sa’ad da dukan waɗanda suka isa yaƙi suka mutu,

17 sai Ubangiji ya yi mini magana, ya ce,

18 ‘Yau za ku ratsa kan iyakar ƙasar Mowab a Ar.

19 Sa’ad da ku kuka zo kusa da Ammonawa, kada ku dame su, ko ku tsokane su, gama ba zan ba ku abin mallaka daga yankin ƙasar Ammonawa ba, domin na ba da ita ta zama mallaka ga zuriya Lutu.’ ”

20 (Ita ma aka lasafta ta ƙasar Refayawa ce. Dā Refayawa waɗanda Ammonawa suke kira Zuzawa, su ne suka zauna cikinta.

21 Manyan mutane masu yawa dogaye ne kuma kamar Anakawa, amma Ubangiji ya hallakar da su a gabansu, suka kore su, suka zauna a wurinsu,

22 daidai kamar yadda Ubangiji ya yi wa zuriyar Isuwa waɗanda suka zauna a Seyir, sa’ad da ya hallakar da Horiyawa a gabansu. Su kuma suka kore su suka zauna a wurinsu har wa yau.

23 Haka nan kuma ya faru da Awwiyawa mazaunan ƙauyukan da suke kewaye da Gaza, wato su Kaftorawa waɗanda suka zo daga Kaftor, suka hallakar da su, suka zauna a wurinsu.)

24 “Ubangiji ya ce, ‘Ku tashi, ku kama hanya, ku haye kwarin Arnon. Duba, na ba da Sihon Ba’amore, Sarkin Heshbon, da ƙasarsa a hannunku, ku fara mallakar ƙasar, ku yaƙe shi.

25 A wannan rana ce zan fara sa al’ummai ko’ina a duniya su razana, su ji tsoronku. Sa’ad da za su ji labarinku, za su yi rawar jiki, su damu ƙwarai.’ ”

Isra’ilawa Sun Ci Sihon

26 “Sa’an nan na aiki manzanni daga jejin Kedemot zuwa Sihon, Sarkin Heshbon, ina neman zaman lafiya, na ce,

27 ‘Ka yardar mini in bi ta cikin ƙasarka. Zan bi ta kan babbar hanya sosai, ba zan ratse dama ko hagu ba.

28 Zan sayi abincin da zan ci, da ruwan da zan sha a wurinku.

29 Kai dai ka yardar mini in bi in wuce kamar yadda zuriyar Isuwa, mazaunan Seyir, da Mowabawa, mazaunan Ar, suka yardar mini. Gama ina so in haye Urdun zuwa ƙasa wadda Ubangiji Allahnmu yake ba mu.’

30 “Amma Sihon, Sarkin Heshbon, ya ƙi yarda mu wuce, gama Ubangiji Allahnku ya riga ya taurare hankalinsa da zuciyarsa don ya bashe shi a hannunku, kamar yadda yake a yau.

31 “Sai Ubangiji ya ce mini, ‘Duba, na fara ba da Sihon da ƙasarsa a gare ku. Ku fara fāɗa wa ƙasarsa da yaƙi don ku mallake ta.’

32 Sai Sihon da mutanensa suka fita su gabza yaƙi da mu a Yahaza.

33 Ubangiji Allahnmu ya bashe shi a hannunmu, muka ci nasara a kansa, da ‘ya’yansa, da dukan mutanensa.

34 Muka ci dukan garuruwansa, muka hallaka kowane gari, da mata, da maza, da yara, ko ɗaya bai ragu ba.

35 Sai dabbobi ne kaɗai da dukiyar garuruwan da muka ci, su ne muka kwashe ganima.

36 Daga Arower wadda take gefen kwarin kogin Arnon, zuwa Gileyad har ma da garin da yake cikin kwarin, Ubangiji Allahnmu ya ba da dukan kome a gare mu. Ba birnin da ya gagare mu.

37 Amma ba ku kusaci ƙasar Ammonawa ba, wato ƙasar da take a kwarin kogin Yabbok, da garuruwan ƙasar tuddai, da wuraren da Ubangiji Allahnmu ya hana mu.”

Categories
M. SH

M. SH 3

Isra’ilawa Sun Ci Og na Bashan

1 “Muka ci gaba da tafiyarmu muka nufi Bashan. Sai Og, Sarkin Bashan, tare da dukan jama’arsa suka fito su yi yaƙi da mu a Edirai.

2 Sai Ubangiji ya ce mini, ‘Kada ka ji tsoronsu, gama da shi, da jama’arsa duka, da ƙasarsa, zan bashe su a hannunka. Sai ka yi masa kamar yadda ka yi wa Sihon, Sarkin Amoriyawa, wanda yake zaune a Heshbon.’

3 “Haka fa Ubangiji Allahnmu ya ba da Og, Sarkin Bashan, da dukan jama’arsa a hannunmu. Muka karkashe su duka, ba wanda muka bari da rai.

4 Muka ƙwace dukan garuruwansa a wannan lokaci. Ko gari guda ɗaya, ba mu bar musu ba, garuruwa sittin, da dukan yankin Argob, da mulkin Og a Bashan.

5 Dukan garuruwan nan masu dogo garu ne, da ƙofofi masu ƙyamaren ƙarfe. Banda waɗannan kuma akwai garuruwa da yawa marasa garu.

6 Muka hallaka su ƙaƙaf kamar yadda muka yi da Sihon, Sarkin Heshbon. Muka hallaka kowane gari, da mata da maza, da yara.

7 Amma muka riƙe dabbobi da dukiyar da muka kwaso daga garuruwan, ganima.

8 “A lokacin ne fa muka ƙwace wannan ƙasa daga hannun sarakunan nan biyu na Amoriyawa, wato ƙasa wadda take a hayin Urdun, daga kwarin kogin Arnon zuwa Dutsen Harmon.”

9 (Sidoniyawa suka kira Harmon, Siriyon, amma Amoriyawa suna ce da shi Senir.)

10 “Wato dukan garuruwa na ƙasar tudu, da dukan ƙasar Gileyad, da ta Bashan har zuwa Salka da Edirai, garuruwa na mulkin Og ke nan cikin ƙasar Bashan.”

11 (Sai Og, Sarkin Bashan, ne kaɗai ya ragu daga cikin Refayawa. Gadonsa na ƙarfe ne. Gadon yana nan a Rabbah ta Ammonawa. Tsawonsa kamu tara, faɗinsa kuma kamu huɗu ne.)

Ra’ubainu, da Gad, da Rabin Kabilar Manassa Sun Zauna a Gabashin Urdun

12 “Sa’ad da muka mallaki ƙasar a wannan lokaci, sai na ba Ra’ubainawa da Gadawa yankin ƙasar daga Arower wadda take gefen kwarin kogin Arnon, da rabin ƙasar tuddai ta Gileyad tare da garuruwanta.

13 Sauran ƙasar Gileyad, da dukan ƙasar Bashan wadda take ƙarƙashin mulkin Og, wato dukan yankin ƙasar Argob.”

(Duk dai yankin ƙasan nan wadda ake kira ƙasar Refayawa.) “Na ba da ita ga rabin kabilar Manassa.”

14 (Yayir na zuriyar Manassa ya karɓi dukan yankin ƙasar Argob a Bashan har zuwa iyakar Geshurawa da Ma’akatiyawa. Sai ya kira ƙauyukan wurin da sunansa, Hawot-yayir.)

15 “Na ba Makir Gileyad.

16 Na ba Ra’ubainawa da Gadawa yankin ƙasar da ta tashi daga Gileyad har zuwa kwarin Arnon, tsakiyar kwarin shi ne iyakar har zuwa kwarin kogin Yabbok wanda ya yi iyaka da Ammonawa.

17 Na kuma ba su Araba, Urdun shi ne iyaka daga Kinneret, har zuwa Tekun Araba, wato Tekun Gishiri, a gangaren gindin Dutsen Fisga wajen gabas.

18 “A wancan lokaci ne na yi muku umarni, na ce, ‘Ubangiji Allahnku ya ba ku wannan ƙasa, ku mallake ta. Dukan mayaƙanku za su haye da shirin yaƙi a gaban ‘yan’uwanku, Isra’ilawa.

19 Amma matanku, da ‘ya’yanku, da dabbobinku, na sani kuna da dabbobi da yawa, su ne za ku bari a garuruwan da na ba ku,

20 har lokacin da Ubangiji ya zaunar da ‘yan’uwanku kamar yadda ya zamshe ku, su ma su mallaki ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba su a hayin Urdun, sa’an nan kowa zai koma ga mallakarsa.’

21 “A lokacin kuwa na umarci Joshuwa na ce, ‘Ai, da idonka ka ga dukan abin da Ubangiji Allahnku ya yi wa waɗannan sarakuna biyu. Haka nan kuwa Ubangiji zai yi wa mulkoki waɗanda za ku haye zuwa wurinsu.

22 Kada kuwa ku ji tsoronsu, gama Ubangiji Allahnku ne zai yi yaƙi dominku.’ ”

Ba a Yarda wa Musa Ya Shiga Kan’ana Ba

23 “Sa’an nan kuma na roƙi Ubangiji, na ce,

24 ‘Ya Ubangiji Allah, kai ne ka fara nuna wa baranka ɗaukakarka da ikonka. Ba wani Allah a Sama ko a duniya da zai aikata ayyuka na banmamaki irin naka.

25 Ka yarje mini, ina roƙonka in haye in ga wannan kyakkyawar ƙasa a hayin Urdun, ƙasan nan mai kyau ta tuddai, da Lebanon.’

26 “Amma Ubangiji ya yi fushi da ni saboda ku, don haka bai ji ni ba. Ya ce mini, ‘Ya isa. Kada ma ka sāke yi mini magana a kan wannan al’amari.

27 Ka hau kan ƙwanƙolin Dutsen Fisga, ka dubi gabas, da yamma, da kudu, da arewa. Ka dubi ƙasar da idanunka, gama ba za ka haye Urdun ba.

28 Amma ka umarci Joshuwa, ka ƙarfafa shi. Shi ne zai jagorar jama’ar nan, su haye, shi ne kuma wanda zai rarraba musu gādon ƙasar da za ka gani.’

29 “Sai muka zauna a kwari daura da Bet-feyor.”

Categories
M. SH

M. SH 4

Musa Ya Gargaɗi Isra’ilawa Su Yi Biyayya

1 “Yanzu, ya Isra’ilawa, sai ku kiyaye dokoki da farillai da nake koya muku don ku rayu, ku shiga ku kuma mallaki ƙasar da Ubangiji Allah na kakanninku suke ba ku.

2 Kada ku ƙara, ko ku rage kome daga cikin abin da na umarce ku, amma ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, waɗanda nake umartarku da su.

3 Idanunku sun ga abin da Ubangiji ya yi a Ba’al-feyor, yadda Ubangiji Allahnku ya hallaka dukan mutane daga cikinku da suka bauta wa Ba’al-feyor.

4 Amma ku da kuka dogara ga Ubangiji Allahnku, a raye kuke har yau.

5 “Ga shi, na koya muku dokoki da farillai, yadda Ubangiji Allah ya umarce ni, don ku kiyaye su a ƙasa wadda kuke shiga ku mallake ta.

6 Ku kiyaye su, ku aikata su, gama yin haka zai tabbatar wa sauran al’ummai, kuna da hikima da ganewa. Sa’ad da al’ummai za su ji waɗannan dokoki, za su ce, ‘Ba shakka, wannan babbar al’umma tana da hikima da ganewa.’

7 “Gama babu wata babbar al’umma wadda allahnta yake kusa da ita kamar yadda Ubangiji Allahnmu yake kusa da mu sa’ad da muka kira gare shi.

8 Ko kuwa, da akwai wata babbar al’umma wadda take da dokoki da farillai na adalci kamar waɗannan dokoki da na sa a gabanku yau?”

An Tuna wa Isra’ilawa abin da ya Same su a Horeb

9 “Sai ku lura, ku kiyaye kanku sosai, don kada ku manta da abubuwan da kuka gani da idonku kada kuma su fita a ranku dukan kwanakinku. Ku sanar wa ‘ya’yanku da jikokinku da su,

10 da yadda kuma a waccan rana kuka tsaya a gaban Ubangiji Allahnku a Horeb, sa’ad da Ubangiji ya ce mini, ‘Ka tattara mini jama’a domin su ji maganata, su koyi tsorona dukan kwanakinsu a duniya, su kuma koya wa ‘ya’yansu.’

11 “Sai kuka matso kusa, kuka tsaya a gindin dutsen sa’ad da dutsten yake cin wuta har zuwa sararin sama, ga kuma girgije baƙi ƙirin yana rufe da dutsen.

12 Ubangiji kuwa ya yi magana da ku ta tsakiyar wuta. Kuka ji hurcin kalmomin, amma ba ku ga siffar kome ba, sai dai murya kaɗai kuka ji.

13 Shi ne ya hurta muku shari’ar da ya umarce ku ku kiyaye, wato dokokin nan goma. Ya rubuta su a allunan dutse guda biyu.

14 Duk da haka Ubangiji ya umarce ni in koya muku dokokin da farillan don ku aikata su a ƙasar da kuke hayewa zuwa ciki don ku mallake ta.”

Faɗakarwa a kan Gumaka

15 “Domin haka, sai ku kula da kanku sosai, gama ba ku ga siffar kome ba sa’ad da Ubangiji Allahnku ya yi magana da ku a Horeb ta tsakiyar wuta.

16 don kada ku yi mugunta, ku sassaƙa wa kanku wata siffar kowane abu, ko siffar mace ko ta namiji,

17 ko siffar dabbar da take a duniya, ko siffar tsuntsun da yake tashi a sararin sama,

18 ko siffar kowane abu mai jan ciki bisa ƙasa, ko siffar kifin da yake cikin ruwa ƙarƙashin ƙasa.

19 Ku lura fa, sa’ad da kuka dubi sama, kuka ga rana, da wata, da taurari, da dai dukan rundunar sama, don kada fa ku jarabtu, ku yi musu sujada, ko ku bauta musu. Ubangiji Allahnku ya sa waɗannan saboda dukan al’ummai.

20 Amma ku, Ubangiji ya fisshe ku daga gidan bauta mai zafi, wato Masar, don ku zama jama’arsa ta musamman kamar yadda kuke a yau.

21 Amma Ubangiji ya yi fushi da ni sabili da ku, har ya rantse, cewa ba zan haye Urdun in shiga kyakkyawar ƙasan nan wadda yake ba ku abar gādo ba.

22 Gama a nan ƙasar zan mutu, ba zan haye Urdun ba, amma ku za ku haye, ku mallaki wannan kyakkyawar ƙasa.

23 Saboda haka, ku lura fa, kada ku manta da alkawarin da Ubangiji Allahnku ya yi da ku, don haka kada ku sassaƙa wa kanku wata siffar kowane irin kamanni wanda Ubangiji Allahnku ya hana ku.

24 Gama Ubangiji Allahnku wuta ne mai cinyewa, shi kuma mai kishi ne.

25 “Sa’ad da kuka haifi ‘ya’ya, kuka sami jikoki, kuka kuma daɗe cikin ƙasar, idan kuka yi abin da yake haram, wato kuka yi gunki na sassaƙa na kowace irin siffa, kuka kuma aikata mugunta a gaban Ubangiji Allahnku har kuka tsokane shi ya yi fushi,

26 to, yau na kira sama da duniya su shaida a kanku, cewa lalle za ku hallaka nan da nan cikin ƙasar da za ku haye Urdun zuwa cikinta don ku mallake ta. Ba za ku daɗe cikinta ba, amma za a shafe ku ƙaƙaf.

27 Ubangiji zai warwatsa ku cikin al’ummai. Za ku ragu kaɗan daga cikin al’ummai inda Ubangiji ya warwatsa ku.

28 Can za ku bauta wa gumaka na itace, da na duwatsu, aikin hannuwan mutum, waɗanda ba su gani, ko ji, ko ci, ko sansana.

29 Amma idan kun nemi Ubangiji Allahnku a can inda kuke, za ku same shi muddin kun neme shi da zuciya ɗaya, da dukan ranku.

30 Sa’ad da wahala ta same ku, waɗannan abubuwa kuma suka auko muku nan gaba, za ku juyo wurin Ubangiji Allahnku, ku yi masa biyayya.

31 Ubangiji Allahnku, Allah mai jinƙai ne. Faufau, ba zai kunyata ku ba, ba kuwa zai hallaka ku ba, ba kuma zai manta da alkawarin da ya rantse wa kakanninku ba.

32 “Ku tambaya mana, ko a kwanakin dā kafin zamaninku, tun ma daga lokacin da Allah ya yi mutum a duniya, ku tantambaya daga wannan kusurwa ta samaniya zuwa waccan, ko wani babban abu irin wannan ya taɓa faruwa, ko kuma an taɓa jin labarin irinsa?

33 Akwai wata jama’a da ta taɓa jin muryar wani allah tana magana ta tsakiyar wuta kamar yadda kuka ji, har suka rayu?

34 Ko kuma, da akwai wani allah wanda ya taɓa ƙoƙarin fitar da al’umma saboda kansa daga cikin tsakiyar wata al’umma ta wurin wahalai, da alamu, da mu’ujizai, da yaƙi, da nuna iko, da babbar razana kamar yadda Ubangiji Allahnku ya yi dominku a ƙasar Masar a kan idonku duka?

35 An nuna muku wannan don ku sani Ubangiji shi ne Allah, banda shi, ba wani kuma.

36 Ya sa ku ji muryarsa daga Sama don ya horar da ku. Ya kuma sa ku ga babbar wutarsa a duniya, kuka kuma ji muryarsa daga cikin wutar.

37 Saboda ya ƙaunaci kakanninku shi ya sa ya zaɓi zuriyarsu a bayansu, shi kansa kuma ya fisshe ku daga Masar da ikonsa mai girma.

38 Ya kori al’ummai a gabanku waɗanda suka fi ku girma da iko, ya kawo ku a ƙasarsu, ya ba ku ita abar gādo kamar yadda yake a yau.

39 Domin haka, yau sai ku sani, ku kuma riƙe a zuciyarku, cewa Ubangiji shi kaɗai ne Allah a sama da duniya. Banda shi, ba wani kuma.

40 Sai ku kiyaye dokokinsa da umarnansa waɗanda na umarce ku da su yau, don zaman lafiyarku da na ‘ya’yanku a bayanku, domin kuma ku yi tsawon rai a ƙasa wadda Ubangiji Allahnku yake ba ku har abada.”

Biranen Mafaka a Hayin Gabashin Urdun

41 Sai Musa ya keɓe birane uku a hayin gabashin Urdun,

42 domin wanda ya yi kisankai ya gudu zuwa can, wato wanda ya kashe mutum ba da niyya ba, babu kuma ƙiyayya tsakaninsu a dā. In ya gudu zuwa ɗaya daga cikin biranen zai tsirar da kansa.

43 Biranen su ne, Bezer cikin jeji a kan tudu domin Ra’ubainawa, da Ramot cikin Gileyad domin Gadawa, da Golan cikin Bashan domin Manassawa.

Gabatarwa a kan Maimaita Dokoki

44 Waɗannan su ne dokokin da Musa ya ba Isra’ilawa,

45 su ne kalmomi, da dokoki, da farillai, waɗanda Musa ya faɗa wa jama’ar Isra’ila, bayan da sun fito Masar,

46 a hayin Urdun a kwari daura da Bet-feyor, a ƙasar Sihon, Sarkin Amoriyawa, mazaunan Heshbon, waɗanda Musa da Isra’ilawa suka ci da yaƙi sa’ad da suka fita daga ƙasar Masar.

47 Suka mallaki ƙasar Sihon, da ƙasar Og, Sarkin Bashan, sarakuna biyu na Amoriyawa waɗanda suke a hayin gabashin Urdun.

48 Ƙasar ta kama daga Arower wanda yake a kwarin kogin Arnon zuwa dutsen Siriyon, wato Harmon,

49 da dukan Araba a hayin gabashin Urdun, har zuwa tekun Araba a gindin gangaren Fisga.

Categories
M. SH

M. SH 5

Dokoki Goma

1 Musa ya kirawo Isra’ilawa duka, ya ce musu, “Ya ku Isra’ilawa, ku ji dokoki da farillai waɗanda nake muku shelarsu a yau! Sai ku koye su, ku aikata su sosai.

2 Ubangiji Allahnmu ya yi alkawari da mu a Horeb.

3 Ba da kakanninmu ne Ubangiji ya yi wannan alkawari ba, amma da mu ne, mu duka waɗanda suke da rai a yau.

4 Ubangiji ya yi muku magana fuska da fuska bisa dutsen ta tsakiyar wuta.

5 Ni ne na tsaya a tsakanin Ubangiji da ku a lokacin don in faɗa muku maganar Ubangiji, gama kun ji tsoro saboda wutar, ba ku kuma hau dutsen ba.

“Ubangiji ya ce,

6 ‘Ni ne Ubangiji Allahnka wanda ya fisshe ka daga ƙasar Masar daga gidan bauta.

7 “ ‘Kada ka kasance da waɗansu gumaka, sai ni.

8 “ ‘Kada ka yi wa kanka gunki, ko wata siffar abin da yake a sama a bisa, ko siffar abin da yake a duniya a ƙasa, ko siffar abin da yake a cikin ruwa a ƙarƙashin ƙasa.

9 Kada ka yi musu sujada, ko ka bauta musu, gama ni Ubangiji Allahnka, Allah mai kishi ne, nakan hukunta ‘ya’ya, da jikoki saboda laifin iyaye waɗanda suka ƙi ni.

10 Amma nakan nuna ƙauna ga dubbai waɗanda suke ƙaunata, suna kiyaye umarnaina.

11 “ ‘Kada ka rantse da sunan Ubangiji Allahnka a kan ƙarya, gama Ubangiji ba zai kuɓutar da wanda yake rantsewa da sunansa a kan ƙarya ba.

12 “ ‘Ka kiyaye ranar Asabar, ka riƙe ta da tsarki yadda Ubangiji Allahnka ya umarce ka.

13 Kwana shida za ka yi aikinka duka.

14 Amma rana ta bakwai ranar hutu ce ta Ubangiji Allahnka. A cikinta ba za ka yi kowane irin aiki ba, kai da ɗanka, da baranka, da baranyarka, da sanka, da jakinka, da kowace dabbar da kake da ita, da baƙon da yake zaune tare da kai, don barorinka mata da maza su ma su huta kamarka.

15 Ka tuna fa, dā kai bawa ne a ƙasar Masar, amma Ubangiji Allahnka ya fisshe ka da dantse mai iko, mai ƙarfi. Domin haka Ubangiji Allahnka ya umarce ka ka kiyaye ranar Asabar.

16 “ ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka yadda Ubangiji Allahnka ya umarce ka domin ka yi tsawon rai, ka sami zaman lafiya a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.

17 “ ‘Kada ka yi kisankai.

18 “ ‘Kada ka yi zina.

19 “ ‘Kada ka yi sata.

20 “ ‘Kada ka yi shaidar zur a kan maƙwabcinka.

21 “ ‘Kada ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka. Kada kuma ka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka, ko gonarsa, ko barorinsa mata ko maza, ko sansa, ko jakinsa, ko kowane abu da yake na maƙwabcinka.’

22 “Ubangiji ya faɗa wa taron jama’arku waɗannan dokoki da murya mai ƙarfi ta tsakiyar wuta, da girgije, da duhu baƙi ƙirin. Ya rubuta su a bisa alluna biyu na dutse, ya ba ni, ba abin da ya ƙara.”

Mutane Suka Ji Tsoro

23 “Sa’ad da kuka ji murya tana fitowa daga duhu, harshen wuta kuma tana ci a bisa dutse, sai shugabannin kabilanku da dattawanku suka zo wurina,

24 suka ce, ‘Ga shi, Ubangiji Allahnmu ya bayyana mana ɗaukakarsa da girmansa, mun kuma ji muryarsa a tsakiyar wutar. Yau mun ga Allah ya yi magana da mutum, duk da haka ya rayu.

25 Don me za mu mutu yanzu? Gama wannan babbar wuta za ta cinye mu. Idan muka ci gaba da jin muryar Ubangiji Allahnmu, za mu mutu.

26 Akwai wani ɗan adam wanda ya taɓa jin muryar Allah, Allah Mai Rai yana magana ta tsakiyar wuta yadda muka ji, har ya rayu?

27 Kai, ka matsa kusa, ka ji dukan abin da Ubangiji Allahnmu zai faɗa, sa’an nan ka mayar mana da dukan abin da Ubangiji Allahnmu ya faɗa maka. Za mu ji, mu kuma aikata.’

28 “Ubangiji kuwa ya ji maganarku wadda kuka yi mini, sai ya ce, ‘Na ji maganar da jama’an nan suka yi maka, abin da suka faɗa daidai ne.

29 Da ma kullum suna da irin wannan zuciya ta tsorona, da za su kiyaye dukan umarnaina, zai zama fa’ida gare su da ‘ya’yansu har abada.

30 Tafi, ka faɗa musu su koma cikin alfarwansu.

31 Amma kai ka tsaya nan a wurina don in faɗa maka dukan umarnai, da dokoki, da farillai, waɗanda za ka koya musu su kiyaye a ƙasar da nake ba su, su mallake ta.’

32 “Sai ku lura ku yi daidai bisa ga abin da Ubangiji Allahnku ya umarce ku, kada ku kauce dama ko hagu.

33 Sai ku bi hanyar da Ubangiji Allahnku ya umarce ku don ku rayu, ku zauna lafiya, ku yi tsawon rai a ƙasar da za ku mallaka.”

Categories
M. SH

M. SH 6

Babban Umarni

1 “Waɗannan su ne umarnai, da dokoki, da farillai waɗanda Ubangiji Allahnku ya umarce ni in koya muku domin ku kiyaye su a ƙasar da kuke hayewa zuwa ciki don ku mallake ta,

2 don ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku da ‘ya’yanku da jikokinku, ku kuma kiyaye dukan dokokinsa da umarnansa, waɗanda nake umartarku dukan kwanakinku don ku yi tsawon rai.

3 Don haka, ku ji, ya Isra’ilawa, ku lura, ku kiyaye su domin zaman lafiyarku, domin kuma ku riɓaɓɓanya ƙwarai a ƙasar da take mai yalwar abinci yadda Ubangiji Allah na kakanninku ya alkawarta muku.

4 “Ku ji, ya Isra’ilawa, Ubangiji shi ne Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne.

5 Sai ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku da zuciya ɗaya, da dukan ranku, da dukan ƙarfinku.

6 Waɗannan kalmomi da na umarce ku da su a yau, za su zauna a zuciyarku.

7 Sai ku koya wa ‘ya’yanku su da himma. Za ku haddace su sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya, da sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi.

8 Za ku ɗaura su a hannunku da goshinku don alama.

9 Za ku kuma rubuta su a madogaran ƙofofin gidajenku, da ƙofofinku.”

Faɗakarwa a kan Rashin Biyayya

10 “Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya kai ku ƙasar da ya rantse wa kakanninku Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, zai ba ku manyan birane masu kyau waɗanda ba ku ne kuka gina ba,

11 da gidaje cike da abubuwa masu kyau waɗanda ba ku ne kuka cika su ba, da rijiyoyi waɗanda ba ku ne kuka haƙa ba, da gonakin inabi da itatuwan zaitun waɗanda ba ku ne kuka dasa ba. Sa’ad da kuka ci, kuka ƙoshi,

12 to, kada ku manta da Ubangiji wanda ya fito da ku daga ƙasar Masar, daga gidan bauta.

13 Sai ku ji tsoron Ubangiji Allahnku. Shi ne za ku bauta masa, ku rantse da sunansa.

14 Kada ku bi waɗansu alloli na al’umman da suke kewaye da ku,

15 gama Ubangiji Allahnku wanda yake zaune a tsakiyarku, mai kishi ne, don kada Ubangiji Allahnku ya husata, ya shafe ku daga duniya.

16 “Kada ku gwada Ubangiji Allahnku kamar yadda kuka yi a Masaha.

17 Sai ku himmantu ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, da farillansa, da dokokinsa waɗanda ya umarce ku da su.

18 Sai ku yi abin da yake daidai, da abin da yake mai kyau a gaban Ubangiji saboda lafiyarku, domin kuma ku shiga ku mallaki ƙasa mai kyau wadda Ubangiji ya rantse zai ba kakanninku.

19 Zai kuwa kori maƙiyanku a gabanku kamar yadda ya alkawarta.

20 “Idan nan gaba ‘ya’yanku suka tambaye ku ma’anar maganarsa, da dokoki, da farillai, waɗanda Ubangiji Allahnmu ya umarce ku da su,

21 sai ku amsa wa ‘ya’yanku, ku ce, ‘Dā mu bayin Fir’auna ne a ƙasar Masar, amma Ubangiji ya fisshe mu daga Masar da dantse mai iko.

22 A idonmu Ubangiji ya aikata manyan alamu masu banmamaki, da mu’ujizai gāba da Masarawa, da Fir’auna, da dukan gidansa.

23 Ya fisshe mu daga wurin, ya bi da mu zuwa ƙasar da ya alkawarta wa kakanninmu zai ba mu.

24 Ubangiji kuwa ya umarce mu mu kiyaye dukan waɗannan umarnai, mu kuma ji tsoron Ubangiji Allahnmu domin amfanin kanmu kullum, domin kuma mu wanzu kamar yadda muke a yau.

25 Idan mun lura, muka kiyaye waɗannan umarnai, muka aikata su kamar yadda Ubangiji Allahnmu ya umarce mu, zai zama adalci a gare mu.’ ”

Categories
M. SH

M. SH 7

Tsattsarkar Jama’a ta Ubangiji

1 “Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya kai ku ƙasar da kuke shiga ku mallake ta, zai korar muku da al’ummai da yawa, su Hittiyawa, da Girgashiyawa, da Amoriyawa, da Kan’aniyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa, al’umma bakwai ke nan, waɗanda suka fi ku yawa, da kuma ƙarfi.

2 Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya bashe su a hannunku, kuka kuma ci nasara a kansu, sai ku hallaka su sarai. Kada ku yi alkawari da su, kada kuma ku yi musu jinƙai.

3 Kada ku yi aurayya da su. Kada ku aurar wa ɗansu da ‘yarku, kada kuma ku auro wa ɗanku ‘yarsu.

4 Gama za su sa ‘ya’yanku su bar bina, su bauta wa gumaka. Wannan zai sa Ubangiji ya husata, ya hallaka ku da sauri.

5 Ga yadda za ku yi da su, za ku rurrushe bagadansu, ku ragargaza al’amudansu, ku sassare ginshiƙansu na tsafi, ku ƙaƙƙone sassaƙaƙƙun siffofinsu.

6 Gama ku jama’a ce tsattsarka ta Ubangiji Allahnku. Ubangiji Allahnku ya zaɓe ku daga cikin dukan al’ummai don ku zama jama’arsa, abar mulkinsa.

7 “Ubangiji ya ƙaunace ku, ya zaɓe ku, ba don kun fi sauran al’ummai yawa ba, gama ku ne mafiya ƙanƙanta cikin dukan al’ummai.

8 Amma saboda Ubangiji ya ƙaunace ku, yana kuma so ya cika rantsuwar da ya yi wa kakanninku, shi ya sa ya fisshe ku da dantse mai iko ya fanshe ku kuma daga gidan bauta, wato daga ikon Fir’auna, Sarkin Masar.

9 Domin haka sai ku sani Ubangiji Allahnku shi ne Allah, Allah mai aminci, mai cika alkawari, mai nuna ƙauna ga dubban tsararraki waɗanda suke ƙaunarsa, suna kuma kiyaye umarnansa.

10 Amma a fili Ubangiji yakan yi ramuwa a kan maƙiyansa, yakan hallaka su. Ba zai yi jinkirin yin ramuwa a kan maƙiyinsa ba, zai yi ramuwar a fili.

11 Saboda haka, sai ku kiyaye umarnai, da dokoki, da farillai ku aikata su, wato waɗanda nake umartarku da su yau.”

Albarkun Biyayya

12 “Idan za ku saurari waɗannan farillai, ku kiyaye su, sai Ubangiji Allahnku ya cika alkawarin da ya rantse wa kakanninku, ya kuma ƙaunace ku.

13 Ubangiji zai ƙaunace ku, ya sa muku albarka, ya riɓaɓɓanya ku. Zai sa wa ‘ya’yanku albarka, ya yalwata amfanin gonarku, da hatsinku, da inabinku, da manku, da garken shanunku, da ‘yan ƙananan garkenku a ƙasar da ya rantse wa kakanninku zai ba ku.

14 Za ku fi kowace al’umma samun albarka. Ba za a iske mutum ko mace marar haihuwa a cikinku ba, ko a cikin garkenku.

15 Ubangiji zai kiyaye ku daga dukan cuce-cuce. Ba zai wahalshe ku da mugayen cuce-cuce na Masar ba, waɗanda kuka sani, amma zai wahalar da duk maƙiyanku da waɗannan mugayen cuce-cuce.

16 Sai ku hallaka dukan mutanen da Ubangiji Allahnku ya bashe su a hannunku. Kada ku ji tausayinsu. Kada kuma ku bauta wa gumakansu, don kada su zamar muku tarko.

17 “Ya yiwu ku ce a zuciyarku, ‘Waɗannan al’ummai sun fi mu yawa, ta ƙaƙa za mu iya ƙorarsu?’

18 Kada ku ji tsoronsu. Ku tuna yadda Ubangiji Allahnku ya yi da Fir’auna da dukan Masarawa.

19 Ku tuna kuma da wahalar da kuka gani da idonku, da alamu, da mu’ujizai, da dantse mai iko mai ƙarfi wanda Ubangiji Allahnku ya fito da ku. Haka nan kuma Ubangiji Allahnku zai yi da dukan al’umman nan da kuke jin tsoronsu.

20 Banda wannan kuma Ubangiji Allahnku zai aiko da zirnako a cikinsu su hallaka sauran da suka ragu, suka ɓuya.

21 Kada ku ji tsoronsu, gama Ubangiji Allahnku yana tare da ku, shi Allah ne mai girma, mai banrazana.

22 Ubangiji Allahnku zai kori waɗannan al’ummai a gabanku da kaɗan da kaɗan. Ba za ku hallaka su gaba ɗaya ba, don kada namomin jeji su yaɗu, su dame ku.

23 Ubangiji Allahnku zai bashe su a gare ku, zai firgitar da su har ya hallakar da su.

24 Zai ba da sarakunansu a hannunku, za ku kuwa shafe sunayensu daga duniya. Ba wanda zai iya tasar muku har kun ƙare su.

25 Sai ku ƙone siffofin gumakansu. Kada ku yi ƙyashin azurfa ko zinariya da aka dalaye su da ita. Kada ku kwashe su, don kada su zamar muku tarko, gama Ubangiji Allahnku yana ƙyamarsu.

26 Kada ku kawo abin ƙyama a gidajenku don kada ku zama abin ƙyama kamarsa. Lalle sai ku ƙi shi, ku ji ƙyamarsa, gama haramtacce ne.”

Categories
M. SH

M. SH 8

Ƙasar da za ku Mallaka Mai Albarka Ce

1 “Sai ku lura, ku aikata dukan umarnan da na umarce ku da su don ku rayu, ku riɓaɓɓanya, ku shiga ƙasar da Ubangiji ya rantse zai ba kakanninku.

2 Ku tuna yadda Ubangiji Allahnku ya bishe ku shekarun nan arba’in a jeji don ya koya muku tawali’u. Ya jarraba ku don ya san zuciyarku, ko za ku kiyaye umarnansa ko babu.

3 Ya koya muku tawali’u, ya bar ku da yunwa, ya ciyar da ku da manna wadda ba ku sani ba, kakanninku kuma ba su sani ba, domin ya sa ku sani, ba da abinci kaɗai mutum yake rayuwa ba, amma mutum yana rayuwa da kowane irin abin da yake fitowa daga wurin Ubangiji.

4 A shekarun nan arba’in tufafinku ba su yayyage ba, ƙafafunku kuma ba su kumbura ba.

5 Kun san wannan a zuciyarku, wato kamar yadda mutum yakan yi wa ɗansa tarbiyya, haka kuma Ubangiji Allahnku yake yi muku tarbiyya.

6 Saboda wannan sai ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin hanyoyinsa, ku ji tsoronsa.

7 Ubangiji Allahnku zai kai ku ƙasa mai kyau. Ƙasa mai rafuffukan ruwa da maɓuɓɓugai, da idanun ruwa masu ɓuɓɓugowa daga cikin kwari da tudu.

8 Ƙasa mai alkama, da sha’ir, da inabi, da ɓaure, da rumman. Ƙasa ce mai itatuwan zaitun da zuma.

9 Ƙasa ce inda za ku ci abinci a yalwace, ba za ku rasa kome ba. Ƙasa ce wadda tama ce duwatsunta, ana kuma haƙar tagulla a tuddanta.

10 Sa’ad da kuka ci, kuka ƙoshi, sai ku yabi Ubangiji Allahnku saboda kyakkyawar ƙasa mai albarka da ya ba ku.”

Faɗakarwa Kada a Manta da Ubangiji

11 “Ku kula fa, don kada ku manta da Ubangiji Allahnku, ku ƙi kiyaye umarnansa, da farillansa, da dokokinsa waɗanda na umarce ku da su yau.

12 Sa’ad da kuka ci kuka ƙoshi, kuka gina kyawawan gidaje, kuka zauna ciki,

13 garkunanku na shanu da tumaki suka riɓaɓɓanya, azurfarku, da zinariyarku suka ƙaru, sa’ad da dukan abin da kuke da shi ya haɓaka,

14 to, sai ku lura, kada ku ɗaukaka kanku, har ku manta da Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar, wato inda kuka yi bauta.

15 Ubangiji ya bishe ku cikin babban jejin nan mai bantsoro, ƙasa mai macizai masu zafin dafi, da kunamai, da busasshiyar ƙasa wadda ba ta da ruwa. Ubangiji kuwa ya ba ku ruwa daga dutsen ƙanƙara.

16 Ya ciyar da ku da manna a jeji, abin da kakanninku ba su sani ba, domin ya koya muku tawali’u, ya jarraba ku, don ya yi muku alheri daga baya.

17 Kada ku ce a zuciya, ‘Ai, ikona da ƙarfin hannuwana ne suka kawo mini wannan wadata.’

18 Sai ku tuna da Ubangiji Allahnku, gama shi ne ya ba ku ikon samun wadata domin ya cika alkawarin da ya rantse wa kakanninku kamar yadda yake a yau.

19 Idan kun manta da Ubangiji Allahnku, kuka bi gumaka, kuka bauta musu, kuka yi musu sujada, to, yau ina faɗakar da ku, cewa lalle za ku hallaka

20 kamar al’umman da Ubangiji ya hallakar a gabanku. Haka za ku hallaka domin ba ku kasa kunne ga muryar Ubangiji Allahnku ba.”

Categories
M. SH

M. SH 9

Ubangiji zai Hallaka Al’umman Ƙasar Kan’ana

1 “Ku ji, ya Isra’ilawa, yau kuna kan haye Kogin Urdun, don ku kori al’ummai waɗanda suka fi ku yawa, sun kuwa fi ku ƙarfi. Suna da manyan birane masu dogon garu.

2 Mutane ne ƙarfafa, dogaye, zuriyar Anakawa waɗanda kuka riga kuka ji labarinsu. Ai, kun ji akan ce, ‘Wane ne zai iya tsayayya da ‘ya’yan Anak?’

3 Yau za ku sani Ubangiji Allahnku yake muku ja gaba sa’ad da kuke hayewa. Shi wuta ne mai cinyewa, zai hallaka su, ya rinjayar muku su, domin ku kore su, ku hallaka su nan da nan kamar yadda Ubangiji ya alkawarta muku.

4 “Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya kore su daga gabanku, kada ku ce a ranku, ‘Ai, saboda adalcinmu ne Ubangiji ya kawo mu mu mallaki ƙasar nan.’ Gama saboda muguntar al’umman nan ne Ubangiji ya kore su a gabanku.

5 Ba saboda adalcinku, ko kuma gaskiyarku ne ya sa za ku shiga ƙasar, ku mallake ta ba, amma saboda muguntar waɗannan al’ummai ne, Ubangiji Allahnku ya kore su a gabanku domin kuma ya cika maganar da ya rantse wa kakanninku, wato su Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.

6 Sai ku sani fa, ba saboda adalcinku ne Ubangiji Allahnku yake ba ku kyakkyawar ƙasan nan don ku mallake ta ba, gama ku jama’a ce mai taurinkai.”

Tayarwar Isra’ilawa a Horeb

7 “Tuna fa, kada ku manta da yadda kuka sa Ubangiji Allahnku ya yi fushi a jeji. Tun daga ranar da kuka fita daga Masar har kuka iso wannan wuri kuna ta tayar wa Ubangiji.

8 A Horeb kuka tsokani Ubangiji, Ubangiji kuwa ya yi fushi, har yana so ya hallaka ku.

9 Sa’ad da na hau kan dutsen domin in karɓo allunan dutse, wato allunan alkawarin da Ubangiji ya yi da ku, na zauna a kan dutsen dare arba’in da yini arba’in ban ci ba, ban sha ba.

10 Ubangiji kuwa ya ba ni allunan nan biyu na dutse da shi kansa ya rubuta. A kansu aka rubuta maganar da Ubangiji ya yi muku daga bisa dutsen a tsakiyar wuta a ranar taron.

11 Bayan dare arba’in da yini arba’in ɗin, Ubangiji ya ba ni alluna biyu na dutse, wato alluna na alkawarin.

12 “Sa’an nan ya ce mini, ‘Tashi, ka gangara da sauri, gama jama’arka wadda ka fito da ita daga Masar ta aikata mugunta, ta kauce da sauri daga hanyar da na umarce ta ta bi. Ta yi wa kanta gunki na zubi.’

13 “Ubangiji kuma ya ce mini, ‘Na ga mutanen nan suna da taurinkai.

14 Bari in hallaka su, in shafe sunansu daga duniya, sa’an nan in maishe ka wata al’umma wadda ta fi su iko da kuma yawa.’

15 “Sai na juya, na gangaro daga dutsen da allunan nan biyu na alkawari a hannuwana, dutsen kuma na cin wuta.

16 Da na duba, sai na ga kun yi wa Ubangiji Allahnku zunubi, kun yi wa kanku maraƙi na zubi. Kun kauce da sauri daga hanyar da Ubangiji ya umarce ku ku bi.

17 Sai na ɗauki allunan nan biyu, na jefar da su ƙasa da hannuna, na farfashe su a idonku.

18 Sai na fāɗi ƙasa, na kwanta a gaban Ubangiji dare arba’in da yini arba’in, ban ci ba, ban sha ba, kamar yadda na yi a dā, saboda dukan zunubin da kuka aikata, kuka yi abin da yake mugu ga Ubangiji, kuka tsokane shi.

19 Gama na ji tsoron zafin fushin Ubangiji da ya yi da ku, har ya so ya hallaka ku. Amma Ubangiji ya ji addu’ata a wannan lokaci.

20 Ubangiji kuma ya husata da Haruna, har ya so ya kashe shi, amma na yi roƙo dominsa a lokacin.

21 Sa’an nan na ɗauki abin zunubin nan, wato siffar maraƙin da kuka yi, na ƙone, na farfashe, na niƙe shi lilis, ya zama kamar ƙura mai laushi, na zubar da garin a rafi wanda yake gangarowa daga dutsen.

22 “Kun kuma tsokano Ubangiji ya husata a Tabera, da a Masaha, da a Kibrot-hata’awa.

23 Sa’ad da Ubangiji ya aike ku daga Kadesh-barneya, ya ce, ‘Ku hau ku mallaki ƙasar da nake ba ku,’ sai kuka tayar wa umarnin Ubangiji Allahnku, ba ku gaskata shi ba, ba ku kuwa yi biyayya da muryarsa ba.

24 Tun ran da na san ku, ku masu tayar wa Ubangiji ne.

25 “Sai na fāɗi na kwanta a gaban Ubangiji dare arba’in da yini arba’in saboda Ubangiji ya ce zai hallaka ku.

26 Na roƙi Ubangiji, na ce, ‘Ya Ubangiji Allah, kada ka hallaka jama’arka, abar gādonka wadda ka fanshe ta ta wurin girmanka, waɗanda kuma ka fito da su daga Masar da ikon dantsenka.

27 Ka tuna da bayinka, su Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, kada ka kula da taurinkan jama’ar nan, ko muguntarsu, ko zunubansu

28 Don kada mutanen ƙasar da ka fito da mu su ce, “Ai, saboda Ubangiji ya kāsa ya kai su ƙasar da ya alkawarta musu, saboda kuma ba ya ƙaunarsu, shi ya sa ya fito da su don ya kashe su a jeji.”

29 Amma su mutanenka ne, abin gādonka, waɗanda ka fito da su da ikonka mai girma da dantsenka mai iko.’ ”

Categories
M. SH

M. SH 10

Allunan Dutse na Biyu

1 “A lokacin nan kuwa Ubangiji ya ce mini, ‘Ka sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na farko, ka hau zuwa wurina a bisa dutsen, ka kuma yi akwati na itace.

2 Ni kuma zan rubuta a allunan maganar da take kan alluna na farko waɗanda ka farfashe. Za ka ajiye su cikin akwatin.’

3 “Sai na yi akwati da itacen ƙirya, na kuma sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na farko. Sai na hau dutsen da alluna biyu a hannuna.

4 Ubangiji kuwa ya sāke rubuta dokoki goma a allunan kamar na farko, wato dokoki goma ɗin nan da Ubangiji ya faɗa muku a dutse ta tsakiyar wuta a ranar taron. Sai Ubangiji ya ba ni su.

5 Na sauko daga dutsen, na ajiye allunan cikin akwatin da na yi, a nan suke kamar yadda Ubangiji ya umarce ni.”

6 (Isra’ilawa suka kama tafiya daga rijiyoyin Bene-ya’akan suka zo Mosera. Nan ne Haruna ya rasu, aka binne shi. Sai ɗansa Ele’azara, ya gāje shi a matsayinsa na firist.

7 Daga nan suka tafi Gudgoda, daga Gudgoda kuma suka tafi Yotbata, ƙasa mai rafuffukan ruwa.

8 A wannan lokaci ne Ubangiji ya keɓe kabilar Lawi domin su riƙa ɗaukar akwatin alkawari na Ubangiji, su kuma tsaya a gaban Ubangiji, su riƙa yi masa aiki, su kuma sa albarka da sunan Ubangiji kamar yadda yake a yau.

9 Domin haka kabilar Lawi ba su da rabo ko gādo tare da ‘yan’uwansu, Ubangiji shi ne gādonsu kamar yadda Ubangiji Allahnku ya faɗa musu.)

10 “Na sāke yin dare arba’in da yini arba’in a kan dutsen kamar dā. Ubangiji kuwa ya amsa addu’ata a lokacin kuma, ya janye hallaka ku.

11 Sai Ubangiji ya ce mini, ‘Tashi, ka tafi, ka kama tafiyarka a gaban jama’an nan domin su je, su shiga, su mallaki ƙasar da na rantse wa kakanninsu, zan ba su.’ ”

Abin da Ubangiji Yake So

12 “Yanzu fa, ya Isra’ilawa ga abin da Ubangiji Allahnku yake so a gare ku. Sai ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin hanyoyinsa, ku ƙaunace shi, ku bauta wa Ubangiji Allahnku da zuciya ɗaya da dukan ranku.

13 Ku kiyaye umarnan Ubangiji da dokokinsa waɗanda nake umurtarku da su yau don amfanin kanku.

14 Duba, saman sammai, da duniya, da dukan abin da yake cikinta na Ubangiji Allahnku ne.

15 Duk da haka Ubangiji ya ƙaunaci kakanninku ya zaɓi zuriyarsu a bayansu daga cikin dukan sauran al’umma, kamar yadda yake a yau.

16 Saboda haka sai ku kame zukatanku, kada ku ƙara yin taurinkai.

17 Gama Ubangiji Allahnku, Allahn alloli ne, da Ubangijin iyayengiji. Shi Allah mai girma ne, mai iko, mai bantsoro, wanda ba ya son zuciya, ba ya karɓar hanci.

18 Yakan yi wa marayu da gwauraye na gaske shari’a da adalci. Yana ƙaunar baƙo, yakan ba shi abinci da sutura.

19 Sai ku ƙaunaci baƙo, gama dā ku baƙi ne a ƙasar Masar.

20 Sai kuma ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku bauta masa. Ku manne masa, ku yi rantsuwa da sunansa.

21 Shi ne abin yabonku, shi ne Allahnku, wanda ya yi muku waɗannan al’amura masu girma, masu bantsoro waɗanda kuka gani da idanunku.

22 Kakanninku saba’in ne suka gangara zuwa Masar, amma yanzu Ubangiji Allahnku ya riɓaɓɓanya ku, kuka yi yawa kamar taurarin sama.”