Categories
M. SH

M. SH 31

Joshuwa zai Gāji Musa

1 Sai Musa ya ci gaba da yi wa dukan Isra’ilawa magana.

2 Ya ce, “Yau shekarata ɗari da ashirin ne, ba na iya kaiwa da komowa. Ubangiji kuwa ya ce mini, ‘Ba za ka haye wannan Urdun ba.’

3 Ubangiji Allahnku shi ne zai yi gaba ya haye, ya hallaka al’umman da take gabanku don ku ci su. Joshuwa ne zai shugabance ku, ya haye kamar yadda Ubangiji ya faɗa.

4 Ubangiji zai yi musu kamar yadda ya yi wa Sihon da Og, sarakunan Amoriyawa, da ƙasarsu, sa’ad da ya hallaka su.

5 Ubangiji zai bashe su a gare ku. Za ku yi musu kamar yadda dā na umarce ku.

6 Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali, kada ku ji tsoro, ko ku firgita saboda su, gama Ubangiji Allahnku yana tare da ku. Ba zai kunyatar da ku ba, ba kuwa zai yashe ku ba.”

7 Sai Musa ya kira Joshuwa, ya yi masa magana a gaban dukan jama’ar Isra’ila, ya ce, “Ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin hali, gama kai ne za ka kai wannan jama’a cikin ƙasar da Ubangiji ya rantse zai ba kakanninsu. Kai ne za ka ba su ita gādo.

8 Ubangiji kansa zai bi da kai, ba zai kunyatar da kai ba, ba kuwa zai yashe ka ba. Kada ka ji tsoro, kada kuma ka karai.”

A Karanta Dokokin Kowace Shekara ta Bakwai

9 Sai Musa ya rubuta waɗannan dokoki, ya ba firistoci, ‘ya’yan Lawiyawa, waɗanda suke ɗaukar akwatin alkawari na Ubangiji, da dukan dattawan Isra’ila.

10 Sai Musa ya umarce su, ya ce, “A ƙarshen kowace shekara bakwai, a lokacin da aka ƙayyade na shekarar yafewa, a lokacin Idin Bukkoki,

11 sa’ad da dukan Isra’ilawa za su hallara a gaban Ubangiji Allahnku a inda zai zaɓa, to, sai ku karanta musu waɗannan dokoki su ji da kunnuwansu.

12 Ku tara dukan jama’a wuri ɗaya, mata da maza, da yara, da baƙin da suke zaune tare da ku a garuruwanku domin su ji, su koyi tsoron Ubangiji Allahnku, su kuma lura su aikata dukan dokokin nan,

13 domin ‘ya’yansu, waɗanda ba su sani ba, su ji, su koyi tsoron Ubangiji Allahnku dukan kwanakinku cikin ƙasar da za ku haye Urdun, ku mallaka.”

Umarnin Ƙarshe da Ubangiji Ya Yi wa Musa

14 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Lokacin rasuwarka ya yi, sai ka kira Joshuwa, ku shigo alfarwa ta sujada, don in ba shi ragamar mulki.” Sai Musa da Joshuwa suka tafi, suka shiga alfarwa ta sujada.

15 Ubangiji kuwa ya bayyana a cikin alfarwar a al’amudin girgije. Al’amudin girgijen kuwa ya tsaya a ƙofar alfarwar.

16 Ubangiji ya ce wa Musa, “Ga shi, za ka rasu ka tarar da kakanninka. Wannan jama’a kuwa za ta fara kaucewa daga hanya, su bi gumakan ƙasar da za su shiga, su zauna. Za su rabu da ni, su ta da alkawarina wanda na yi da su.

17 A wannan rana zan husata da su ƙwarai, in rabu da su, in ɓoye musu fuskata, za a cinye su. Masifu da wahalai za su same su. Za su kuwa ce a ranar, ‘Masifun nan sun same mu domin Allahnmu ba ya tare da mu.’

18 Hakika kuwa, zan ɓoye musu fuskata sabili da muguntar da suka aikata, suka kuma bi gumaka.

19 “Don haka, sai ka rubuta wannan waƙa, ka koya wa Isra’ilawa. Ka sa ta a bakinsu don waƙan nan ta zama shaida a gare ni game da Isra’ilawa.

20 Sa’ad da na kawo su a ƙasar da take da yalwar abinci, wadda na rantse zan ba kakanninsu, har suka ci, suka ƙoshi, suka yi ƙiba, za su juya, su bi gumaka, su bauta musu. Za su raina ni, su tā da alkawarina.

21 Sa’ad da yawan masifun nan da wahalan nan suka same su, to, waƙar nan za ta ba da shaida a kansu, gama zuriyarsu ba za ta manta da wannan waƙa ba, gama na san ƙudurin da suke yi kafin in kawo su ƙasar da na rantse zan bayar.”

22 Saboda wannan sai Musa ya rubuta wannan waƙa a ranar, ya koya wa jama’ar Isra’ila.

23 Sai Ubangiji ya umarci Joshuwa ɗan Nun ya ce, “Ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin hali, gama kai ne za ka kai jama’ar Isra’ila a ƙasar da na rantse zan ba su, ni kuma da kaina zan tafi tare da kai.”

24 Sa’ad da Musa ya gama rubuta maganar dokokin nan sarai a littafin,

25 sai ya umarci Lawiyawa waɗanda suke ɗaukar akwatin alkawarin Ubangiji, ya ce,

26 “Ku ɗauki littafin dokokin nan, ku ajiye shi tare da akwatin alkawari na Ubangiji Allahnku domin ya zama shaida a kanku,

27 gama na san tayarwarku da taurinkanku. Tun ma ina da rai ke nan tare da ku kuka tayar wa Ubangiji, balle bayan rasuwata.

28 Ku tattaro mini dattawan kabilanku da manyanku don in faɗa musu wannan magana a kunnensu, in kuma kira sama da duniya su zama shaida a kansu.

29 Gama na sani bayan rasuwata za ku aikata mugunta, ku kauce daga hanyar da na umarce ku. Masifa za ta auko muku a kwanaki masu zuwa saboda za ku aikata mugunta a gaban Ubangiji, za ku tsokani fushinsa da aikin hannuwanku.”

Waƙar Musa

30 Sa’an nan Musa ya hurta kalmomin wannan waƙa a kunnen dukan taron jama’ar Isra’ila har ƙarshensu.

Categories
M. SH

M. SH 32

1 “Ku saurara, ya ku sammai, gama zan yi magana,

Bari duniya ta ji maganar bakina.

2 Bari koyarwata ta zubo kamar ruwan sama,

Maganata ta faɗo kamar raɓa,

Kamar yayyafi a bisa ɗanyar ciyawa,

Kamar ɗiɗɗigar ruwa a bisa ganyaye.

3 Gama zan yi shelar sunan Ubangiji,

In yabi girman Allahnmu!

4 “Shi Dutse ne, aikinsa kuma cikakke ne,

Gama dukan hanyoyinsa masu adalci ne.

Allah mai aminci ne, babu rashin gaskiya a gare shi,

Shi mai adalci ne, nagari ne kuma.

5 Sun aikata mugunta a gabansa,

Su ba ‘ya’yansa ba ne saboda lalacewarsu,

Su muguwar tsara ce, karkatacciya,

6 Haka za ku sāka wa Ubangiji,

Ya ku wawaye, mutane marasa hikima?

Ba shi ne Ubanku, Mahaliccinku ba,

Wanda ya yi ku, ya kuma kafa ku?

7 “Ku fa tuna da kwanakin dā,

Ku yi tunani a kan shekarun tsararraki,

Ku tambayi mahaifanku, su za su faɗa muku,

Ku tambayi dattawanku, su kuma za su faɗa muku,

8 Sa’ad da Maɗaukaki ya ba al’ummai gādonsu,

Sa’ad da ya raba ‘yan adam,

Ya yanka wa mutane wurin zama bisa ga yawan Isra’ilawa.

9 Gama rabon Ubangiji shi ne jama’arsa,

Yakubu shi ne rabon gādonsa.

10 “Ya same shi daga cikin hamada,

A jeji marar amfani, inda namomi suke kuka.

Ya kewaye shi, ya lura da shi,

Ya kiyaye shi kamar ƙwayar idonsa.

11 Kamar gaggafar da take kaɗa fikafikanta a kan sheƙarta,

Tana rufe da ‘yan tsakinta,

Ta buɗe fikafikanta, ta kama su,

Ta ɗauke su a bisa kafaɗunta.

12 Ubangiji ne kaɗai ya bishe shi,

Ba wani baƙon allah tare da shi.

13 “Ya sa shi ya hau kan tuddai,

Ya ci amfanin ƙasa,

Ya sa shi ya sha zuma daga dutse,

Ya ba shi mai daga dutsen ƙanƙara.

14 Ya sami kindirmo daga shanu,

Da madara daga garken tumaki da na awaki,

Da kitse daga ‘yan raguna, da raguna,

Da bijimai, da bunsurai daga Bashan,

Da alkama mafi kyau.

Ka sha ruwan inabi jaja wur, mai kyau.

15 “Yeshurun ya yi ƙiba, yana harbin iska,

Ka yi ƙiba, ka yi kauri, ka yi sumul.

Ya rabu da Allahn da ya yi shi,

Ya raina Dutsen Cetonsa.

16 Suka sa shi kishi, saboda gumaka,

Suka tsokani fushinsa da abubuwan banƙyama.

17 Suka miƙa hadayu ga aljannun da ba Allah ba,

Ga gumakan da ba su sani ba,

Sababbin allolin da aka shigo da su daga baya,

Waɗanda kakanninku ba su ji tsoronsu ba.

18 Kun ƙi kula da Dutsen da ya haife ku,

Kun manta da Allahn da ya ba ku rai.

19 “Ubangiji ya gani, ya raina su,

Saboda tsokanar da ‘ya’yansa mata da maza suka yi masa.

20 Ya ce, ‘Zan ɓoye musu fuskata,

Zan ga yadda ƙarshensu zai zama.

Gama su muguwar tsara ce,

‘Ya’ya ne marasa aminci.

21 Suka sa ni kishi da abin da ba Allah ba,

Suka tsokani fushina da gumakansu,

Ni kuma zan sa su su yi kishi da waɗanda suke ba mutane ba.

Zan tsokane su da wawanyar al’umma.

22 Gama fushina ya kama wuta,

Tana ci har ƙurewar zurfin lahira.

Za ta cinye duniya da dukan amfaninta,

Za ta kama tussan duwatsu.

23 “ ‘Zan tula musu masifu,

Zan ƙare kibauna a kansu,

24 Za su lalace saboda yunwa,

Zazzaɓi mai zafi, da muguwar annoba za su cinye su.

Zan aika da haƙoran namomi a kansu,

Da dafin abubuwa masu jan ciki.

25 Waɗanda suke a waje, takobi zai kashe su,

A cikin ɗakuna kuma tsoro,

Zai hallaka saurayi da budurwa,

Da mai shan mama da mai furfura.

26 Na ce, “Zan watsar da su,

In sa a manta da su cikin mutane.”

27 Amma saboda gudun tsokanar maƙiyi,

Kada abokan gābansu su zaci su ne suka ci nasara.

Ai, ni ne na yi wannan.’

28 “Gama su al’umma ce wadda ba ta yin shawara,

Ba su da ganewa.

29 Da suna da hikima, da sun gane wannan,

Da za su gane da yadda ƙarshensu zai zama!

30 Ƙaƙa mutum ɗaya zai runtumi dubu,

Mutum biyu kuma su kori zambar goma,

Sai dai Dutsensu ya sayar da su,

Ubangiji kuma ya bashe su?

31 Gama dutsensu ba kamar Dutsenmu ba ne,

Ko abokan gabanmu ma sun san haka.

32 Kurangar inabinsu daga kurangar inabin Saduma ne

Da gonakin Gwamrata.

‘Ya’yan inabinsu dafi ne,

Nonnansu masu ɗaci ne.

33 Ruwan inabinsu dafin macizai ne.

Da mugun dafin kumurci.

34 “ ‘Wannan ba a jibge suke a rumbunana ba,

A ƙulle kuma a taskokina?

35 Sakayya da ɗaukar fansa nawa ne,

A lokacin ƙafarsu za ta zame,

Gama ranar masifarsu ta kusa,

Hallakarsu za ta zo da sauri.’

36 Ubangiji zai ɗauka wa jama’arsa fansa,

Zai ji ƙan bayinsa,

Sa’ad da ya ga ƙarfinsu ya kāsa,

Ba kuma wanda ya ragu, bawa ko ɗa.

37 Sa’an nan zai ce, ‘Ina gumakansu,

Dutse wanda suka nemi mafaka gare shi,

38 Waɗanda suka ci kitsen hadayunsu,

Suka sha ruwan inabin hadayarsu ta sha?

Bari su tashi su taimake ku,

Bari su zama mafaka!

39 “ ‘Ku duba fa, ni ne shi,

Ba wani Allah, banda ni,

Nakan kashe, in rayar,

Nakan sa rauni, nakan kuma warkar,

Ba wanda zai cece su daga hannuna.

40 Na ɗaga hannuna sama,

Na rantse da madawwamin raina,

41 Sa’ad da na wasa takobina mai walƙiya,

Na riƙe shi da hannuna don yin hukunci,

Zan ɗauki fansa a kan magabtana

Zan sāka wa maƙiyana.

42 Zan sa kibauna su bugu da jini,

Takobina zai ci nama,

Da jinin kisassu da na kamammu,

Da ƙoƙon kan shugabannin maƙiya.’

43 “Ya ku al’ummai, ku yabi jama’arsa,

Gama zai rama wa bayinsa saboda jininsu,

Zai ɗauki fansa a kan magabtansa,

Zai tsarkake ƙasar jama’arsa.”

Gargaɗin Musa na Ƙarshe

44 Sai Musa da Joshuwa ɗan Nun suka zo, suka hurta dukan kalmomin wannan waƙa a kunnen jama’a.

45 Sa’ad da Musa ya gama hurta waɗannan kalmomi ga Isra’ila,

46 ya ce musu, “Ku riƙe dukan waɗannan kalmomi a zuciyarku, waɗanda nake yi muku kashedi da su a yau don ku umarci ‘ya’yanku su kiyaye dukan maganar dokokin nan sosai.

47 Wannan ba magana kurum ba ce, amma ranku ne. Ta wurin wannan magana ce za ku yi tsawon rai a ƙasar da za ku haye Urdun zuwa ciki don ku mallake ta.”

An Yarda wa Musa Ya Hangi Ƙasar Kan’ana

48 A wannan rana ce Ubangiji ya ce wa Musa,

49 “Ka hau duwatsun Abarim, wato Dutsen Nebo wanda yake a ƙasar Mowab, daura da Yariko, ka duba ƙasar Kan’ana wadda zan ba Isra’ilawa su mallaka.

50 Za ka rasu a kan dutsen da za ka hau, za a kai ka wurin mutanen da suka riga ka gidan gaskiya, kamar yadda ɗan’uwanka, Haruna, ya rasu a Dutsen Hor, aka kai shi wurin mutanensa waɗanda suka riga shi gidan gaskiya.

51 Gama ba ku amince da ni ba a gaban mutanen Isra’ila a wurin ruwan Meriba ta Kadesh a jejin Zin a wannan lokaci, domin ba ku nuna tsarkina a gaban jama’ar Isra’ila ba.

52 Za ka ga ƙasar da nake ba jama’ar Isra’ila, amma ba za ka shiga cikinta ba.”

Categories
M. SH

M. SH 33

Musa Ya Sa wa Kabilan Isra’ila Albarka

1 Wannan ita ce albarkar da Musa, mutumin Allah, ya sa wa Isra’ilawa kafin ya rasu.

2 Ya ce,

“Ubangiji ya taho daga Sina’i,

Daga Dutsen Faran kuma ya haskaka,

Ya taho tare da dubban tsarkakansa,

Da harshen wuta a damansa.

3 Hakika, yana ƙaunar jama’arsa,

Dukan tsarkaka suna a ikonka,

Suna biye da kai,

Suna karɓar umarninka.

4 Musa ya ba mu dokoki,

Abin gādo ga taron jama’ar Yakubu.

5 Ubangiji shi ne sarki a Yeshurun,

Sa’ad da shugabanni suka taru,

Dukan kabilan Isra’ila suka taru.

6 “Allah ya sa Ra’ubainu ya rayu, kada ya mutu,

Kada mutanensa su zama kaɗan.”

7 A kan Yahuza ya ce,

“Ka ji muryar Yahuza, ya Ubangiji,

Ka kawo shi wurin jama’arsa.

Ka yi yaƙi da ikonka dominsu,

Ka taimake shi a kan maƙiyansa.”

8 A kan Lawi ya ce,

“Ka ba Mai Tsarki Tumminka da Urim naka,

Shi wanda ka jarraba a Masaha,

Wanda ka yi jayayya da shi a ruwan Meriba,

9 Wanda ya ce wa mahaifinsa da mahaifiyarsa,

‘Ban kula da ku ba.’

Ya ce wa ‘yan’uwansa su ba nasa ba ne.

Ya kuma ƙyale ‘ya’yansa,

Domin sun kiyaye maganarka,

Sun riƙe alkawarinka.

10 Suna koya wa Yakubu farillanka,

Suna koya wa Isra’ila dokokinka.

Suna ƙona turare a gabanka,

Suna ƙona hadaya ta ƙonawa a bagadenka.

11 Ya Ubangiji ka inganta jaruntakarsu,

Ka karɓi aikin hannuwansu,

Ka murƙushe ƙarfin abokan gābansu,

Da waɗanda suke ƙinsu don kada su ƙara tashi.”

12 A kan Biliyaminu, ya ce,

“Shi ƙaunatacce na Ubangiji ne,

Yana zaune lafiya kusa da shi,

Ubangiji yana yi masa garkuwa dukan yini,

Yana zaune a kan kafaɗunsa.”

13 A kan Yusufu, ya ce,

“Ubangiji ya sa wa ƙasarsa albarka,

Da kyawawan kyautai daga sama, da raɓa,

Da ruwan da yake a ƙasa,

14 Da kyawawan kyautan da rana take bayarwa,

Da kyawawan kyautan da watanni suke bayarwa,

15 Da abubuwa mafi kyau na duwatsun dā,

Da kyawawan kyautai na madawwaman tuddai.

16 Da kyautai mafi kyau na duniya da cikarta,

Da alherin wanda yake zaune a jeji.

Bari waɗannan kyautai su sauka a kan Yusufu,

A kan wanda yake keɓaɓɓe daga cikin ‘yan’uwansa.

17 Darajarsa kamar ta ɗan farin bijimi take,

Ƙahoninsa kamar na ɓauna suke,

Da su yake tunkwiyin mutane,

Zai tura su zuwa ƙurewar duniya,

Haka fa rundunan Ifraimu za su zama,

Haka kuma dubban Manassa za su zama.”

18 A kan Zabaluna ya ce,

“Ka yi murna da tafiye-tafiyenka, ya Zabaluna,

Kai kuma Issaka, cikin alfarwanka.

19 Za su kira mutane zuwa dutse,

Can za su miƙa hadayu masu dacewa,

Gama za su ɗebo wadatar tekuna,

Da ɓoyayyun dukiyar yashi.”

20 A kan Gad, ya ce,

“Mai albarka ne wanda ya fāɗaɗa Gad,

Gad yana sanɗa kamar zaki,

Yana yayyage hannu da ƙoƙon kai.

21 Zai zaɓar wa kansa wuri mai kyau,

Gama wurin ne aka keɓe wa shugaba.

Ya zo wurin shugabannin mutane,

Tare da Isra’ila, ya aikata adalcin Ubangiji,

Ya kiyaye farillansa.”

22 A kan Dan, ya ce,

“Dan ɗan zaki ne,

Mai tsalle daga Bashan.”

23 A kan Naftali, ya ce,

“Ya Naftali, ƙosasshe kake da alheri,

Cike kake da albarkar Ubangiji.

Sai ka mallaki tafki da wajen kudu.”

24 A kan Ashiru, ya ce,

“Ashiru mai albarka ne fiye da sauran ‘yan’uwansa,

Bari ya zama abin ƙauna ga ‘yan’uwansa,

Ya kuma tsoma ƙafarsa cikin mai.

25 Kurfanka na baƙin ƙarfe ne da tagulla,

Ƙarfinka ba zai rabu da kai ba muddin ranka.”

26 “Babu wani kamar Allahn Yeshurun,

Wanda yakan sauko daga Sama don ya cece ka,

Wanda ya sauko daga bisa da ɗaukakarsa.

27 Allah Madawwami, shi ne wurin zamanka,

Madawwaman damatsansa suna tallafarka,

Yana kore maka maƙiyanka,

Ya ce, ‘Ka hallaka su!’

28 Da haka Isra’ila yana zaune lafiya,

Zuriyar Yakubu tana zaune ita kaɗai

A ƙasa mai hatsi da ruwan inabi,

Wurin da raɓa take zubowa daga sama.

29 Mai farin ciki ne kai, ya Isra’ila!

Wane ne kamarku, mutanen da Ubangiji ya ceta?

Ubangiji ne garkuwarku,

Shi ne kuma takobinku mai daraja.

Magabtanku za su yi muku fādanci,

Amma ku za ku tattake masujadansu.”

Categories
M. SH

M. SH 34

Rasuwar Musa

1 Sai Musa ya tashi daga filayen Mowab zuwa Dutsen Nebo, a ƙwanƙolin Fisga wanda yake daura da Yariko. Sai Ubangiji ya nuna masa dukan ƙasar, tun daga Gileyad har zuwa Dan,

2 da dukan Naftali, da ƙasar Ifraimu, da ta Manassa, da dukan ƙasar Yahuza har zuwa Bahar Rum,

3 da Negeb, da filin kwarin Yariko, birnin itatuwan giginya, har zuwa Zowar.

4 Ubangiji ya ce masa, “Wannan ita ce ƙasar da na rantse wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, zan ba da ita ga zuriyarsu. Na bar ka ka gan ta da idanunka, amma ba za ka haye, ka shiga ba.”

5 Nan fa, a ƙasar Mowab, Musa bawan Ubangiji, ya rasu kamar yadda Ubangiji ya faɗa.

6 Aka binne shi cikin kwarin ƙasar Mowab, kusa da Betfeyor, amma ba wanda ya san inda aka binne shi har yau.

7 Musa ya yi shekara ɗari da ashirin sa’ad da ya rasu. Idanunsa ba su dushe ba, ƙarfinsa kuma bai ragu ba.

8 Isra’ilawa suka yi makoki domin Musa a filayen Mowab har kwana talatin. Sa’an nan kwanakin kuka da makoki domin Musa suka ƙare.

9 Joshuwa ɗan Nun yana cike da ruhun hikima, gama Musa ya ɗibiya masa hannuwansa. Isra’ilawa suka yi masa biyayya, suka aikata bisa ga yadda Ubangiji ya umarci Musa.

10 Tun daga lokacin nan, ba a taɓa yin wani annabi a Isra’ila kamar Musa ba, wanda Ubangiji ya san shi fuska da fuska.

11 Ubangiji ya aike shi ya aikata alamu da mu’ujizai a ƙasar Masar a gaban Fir’auna da dukan barorinsa, da dukan ƙasarsa.

12 Ya kuma aikata ayyuka masu iko, masu bantsoro a gaban dukan Isra’ilawa.