Categories
MAT

MAT 1

Asalin Yesu Almasihu

1 Littafin asalin Yesu Almasihu, ɗan Dawuda, zuriyar Ibrahim ke nan.

2 Ibrahim ya haifi Ishaku, Ishaku ya haifi Yakubu, Yakubu ya haifi Yahuza da ‘yan’uwansa,

3 Yahuza kuwa ya haifi Feresa da Zera (uwa tasu Tamar ce), Feresa ya haifi Hesruna, Hesruna ya haifi Aram,

4 Aram ya haifi Amminadab, Amminadab ya haifi Nashon, Nashon ya haifi Salmon,

5 Salmon ya haifi Bo’aza (uwa tasa Rahab ce), Bo’aza ya haifi Obida (mahaifiyarsa Rut ce), Obida ya haifi Yesse,

6 Yesse ya haifi sarki Dawuda.

Dawuda kuma ya haifi Sulemanu (wanda uwa tasa dā matar Uriya ce),

7 Sulemanu ya haifi Rehobowam, Rehobowam ya haifi Abiya, Abiya ya haifi Asa,

8 Asa ya haifi Yehoshafat, Yehoshafat ya haifi Yoram, Yoram ya haifi Azariya,

9 Azariya ya haifi Yotam, Yotam ya haifi Ahaz, Ahaz ya haifi Hezekiya,

10 Hezekiya ya haifi Manassa, Manassa ya haifi Amon, Amon ya haifi Yosiya.

11 Yosiya ya haifi Yekoniya da ‘yan’uwansa, wato, a lokacin da aka ɗebe su zuwa Babila.

12 Bayan an ɗebe su zuwa Babila, sai Yekoniya ya haifi Sheyaltiyel, Shayeltiyel ya haifi Zarubabel,

13 Zarubabel ya haifi Abihudu, Abihudu ya haifi Eliyakim, Eliyakim ya haifi Azuro,

14 Azuro ya haifi Saduƙu, Saduƙu ya haifi Akimu, Akimu ya haifi Aliyudu,

15 Aliyudu ya haifi Ele’azara, Ele’azara ya haifi Matana, Matana ya haifi Yakubu,

16 Yakubu ya haifi Yusufu mijin Maryamu wadda ta haifi Yesu, wanda ake kira Almasihu.

17 Wato, dukkan zuriya daga Ibrahim zuwa kan Dawuda, zuriya goma sha huɗu ce. Daga Dawuda zuwa ga ɗebe su a kai Babila kuwa, zuriya goma sha huɗu. Daga ɗebe su zuwa Babila zuwa kan Almasihu, zuriya goma sha huɗu.

Haihuwar Yesu Almasihu

18 Ga yadda haihuwar Yesu Almasihu take. Sa’ad da Yusufu yake tashin Maryamu mahaifiyar Yesu, tun ba a ɗauke ta ba, sai aka ga tana da juna biyu daga Ruhu Mai Tsarki.

19 Yusufu mijinta kuwa da yake shi mutumin kirki ne, ba ya kuma so ya ba ta kunya a gaban jama’a, sai ya yi niyyar rabuwa da ita a asirce.

20 Amma tun yana cikin wannan tunani, sai ga wani mala’ikan Ubangiji ya bayyana a gare shi a mafarki, ya ce, “Yusufu ɗan Dawuda, kada ka ji tsoron ɗaukar Maryamu matarka, domin cikin nan nata daga Ruhu Mai Tsarki ne.

21 Za ta haifi ɗa, za ka kuma sa masa suna Yesu, domin shi ne zai ceci mutanensa daga zunubansu.”

22 An yi wannan ne duk, don a cika abin da Ubangiji ya faɗa ta bakin annabin cewa,

23 “Ga shi, budurwa za ta yi juna biyu, ta haifi ɗa,

Za a kuma sa masa suna Immanuwel.”

(Ma’anar Immanuwel kuwa itace Allah na tare da mu.)

24 Da Yusufu ya farka daga barci, sai ya bi umarnin mala’ikan Ubangiji, ya ɗauki matarsa,

25 amma bai san ta ba, sai bayan da ta haifi ɗanta, ya kuma sa masa suna Yesu.

Categories
MAT

MAT 2

Ziyarar Masana Taurari daga Gabas

1 Sa’ad da aka haifi Yesu a Baitalami ta ƙasar Yahudiya, a zamanin sarki Hirudus, sai ga waɗansu masana taurari daga gabas suka zo Urushalima, suna cewa,

2 “Ina wanda aka haifa Sarkin Yahudawa? Domin mun ga tauraronsa a gabas, mun kuma zo mu yi masa sujada.”

3 Da sarki Hirudus ya ji haka, sai ya damu ƙwarai, haka kuma dukan mutanen Urushalima.

4 Sai ya tara dukan manyan firistoci da malaman Attaura na jama’a, ya tambaye su inda za a haifi Almasihu.

5 Sai suka ce masa, “A Baitalami ne, ta ƙasar Yahudiya, domin haka annabin ya rubuta cewa,

6 ‘Ke ma Baitalami, ta kasar Yahuza,

Ko kusa ba ke ce mafi ƙanƙanta a cikin manyan garuruwan Yahuza ba,

Domin daga cikinki za a haifi wani mai mulki,

Wanda zai zama makiyayin jama’ata, Isra’ila.’ ”

7 Sai Hirudus ya kira masanan nan a asirce, ya tabbata daga bakinsu ainihin lokacin da tauraron nan ya bayyana.

8 Sa’an nan ya aike su Baitalami, ya ce, “Ku je ku binciko mini ɗan yaron nan sosai. In kun same shi, ku kawo mini labari, don ni ma in je in yi masa sujada.”

9 Su kuwa da suka ji maganar sarki, sai suka yi tafiyarsu. Ga shi kuwa, tauraron da suka gani a gabas yana tafe a gabansu, har ya zo ya tsaya bisa inda ɗan yaron nan yake.

10 Da suka ga tauraron sai suka yi matuƙar farin ciki.

11 Da suka shiga gidan kuwa, sai suka ga ɗan yaron, tare da uwa tasa Maryamu, suka fāɗi gabansa suka yi masa sujada. Sa’an nan suka kwance kayansu, suka miƙa masa gaisuwar zinariya, da lubban, da mur.

12 Amma da aka gargaɗe su a mafarki kada su koma wurin Hirudus, sai suka koma ƙasarsu ta wata hanya dabam.

Gudu zuwa Masar

13 Da suka tashi, sai ga wani mala’ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki, ya ce, “Tashi ka ɗauki ɗan yaron da mahaifiyarsa, ka gudu ƙasar Masar, ka zauna a can sai na faɗa maka, don Hirudus yana shirin binciko ɗan yaron yă hallaka shi.”

14 Yusufu kuwa ya tashi ya ɗauki ɗan yaron da uwa tasa da daddare, ya tafi Masar,

15 ya zauna a can har mutuwar Hirudus. Wannan kuwa domin a cika abin da Ubangiji ya faɗa ne ta bakin annabin cewa, “Daga Masar na kirawo Ɗana.”

Kisan ‘Yan Yara

16 Da Hirudus ya ga masanan nan sun mai da shi wawa, sai ya hasala ƙwarai, ya aika a karkashe dukan ‘yan yara maza da suke Baitalami da kewayenta, daga masu shekara biyu zuwa ƙasa, gwargwadon lokacin da ya tabbatar a gun masanan nan.

17 A lokacin ne aka cika faɗar Annabi Irmiya cewa,

18 “An ji wata murya a Rama,

Ta kuka da baƙin ciki mai zafi,

Rahila ce take kuka saboda ‘ya’yanta.

Ba za ta ta’azantu ba, don ba su.”

Komowa daga Masar

19 Amma bayan mutuwar Hirudus, sai ga mala’ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki a Masar, ya ce,

20 “Tashi ka ɗauki ɗan yaron da uwa tasa, ka tafi ƙasar Isra’ila, don masu neman ran ɗan yaron sun mutu.”

21 Sai ya tashi, ya ɗauki ɗan yaron da uwa tasa, ya zo ƙasar Isra’ila.

22 Amma da ya ji Arkilayus ya gāji ubansa Hirudus, yana mulkin ƙasar Yahudiya, sai ya ji tsoron isa can. Amma da aka yi masa gargaɗi a mafarki, sai ya ratse zuwa ƙasar Galili.

23 Sai ya je ya zauna a wani gari wai shi Nazarat, domin a cika faɗar annabawa cewa, “Za a kira shi Banazare.”

Categories
MAT

MAT 3

Wa’azin Yahaya Maibaftisma

1 A wannan zamani ne Yahaya Maibaftisma ya zo, yana wa’azi a jejin Yahudiya,

2 yana cewa, “Ku tuba, domin Mulkin Sama ya kusato.”

3 Wannan shi ne wanda Annabi Ishaya ya yi maganarsa, ya ce,

“Muryar mai kira a jeji yana cewa,

‘Ku shirya wa Ubangiji tafarki,

Ku miƙe hanyoyinsa.’ ”

4 Yahaya kuwa yana saye da tufa ta gashin raƙumi, yana kuma ɗaure da ɗamara ta fata, abincinsa kuwa fara ce da ruwan zuma.

5 Sai mutanen Urushalima, da na dukan Yahudiya, da na duk ƙasashen bakin Kogin Urdun, suka yi ta zuwa wurinsa,

6 yana yi musu baftisma a Kogin Urdun, suna bayyana zunubansu.

7 Amma da Yahaya ya ga Farisiyawa da Sadukiyawa da yawa, sun taho domin a yi musu baftisma, sai ya ce musu, “Ku macizai! Wa ya gargaɗe ku, ku guje wa fushin nan mai zuwa?

8 Ku yi aikin da zai nuna tubarku.

9 Kada kuwa ku ɗauka a ranku cewa, Ibrahim ne ubanku, domin ina gaya muku, Allah yana da ikon ya halitta wa Ibrahim ‘ya’ya da duwatsun nan.

10 Koyanzu ma an ɗora bakin gatari a gindin bishiya. Saboda haka duk bishiyar da bata bada ‘ya’ya masu kyau ba, sai a sare ta a jefa a wuta.

11 “Ni dai, da ruwa nake muku baftisma, shaidar tubarku, amma mai zuwa bayana, ya fi ni girma, wanda ko takalmansa ma ban isa in riƙe ba. Shi ne zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki, da kuma wuta.

12 Ƙwaryar shiƙarsa na hannunsa, zai kuwa share masussukarsa sarai sarai, ya taro alkamarsa ya sa a rumbunsa, amma ɓuntun, sai ya ƙone a wutar marar kasuwa.”

An Yi wa Yesu Baftisma

13 A lokacin nan ne Yesu ya zo daga ƙasar Galili, ya je Kogin Urdun wurin Yahaya, domin ya yi masa baftisma.

14 Yahaya kuwa ya so ya hana shi, ya ce, “Ni da nake bukatar kai ka yi mini baftisma, ka zo gare ni?”

15 Amma Yesu ya amsa masa ya ce, “Bari ya zama haka a yanzu, domin haka ne ya dace mu cika dukan adalci.” Sa’an nan Yahaya ya yardar masa.

16 Da aka yi wa Yesu baftisma, nan da nan da ya fito daga ruwan, sai ga sama ta dāre, ya ga Ruhun Allah na saukowa kamar kurciya, har ya sauka kansa.

17 Sai aka ji wata murya daga Sama ta ce, “Wannan shi ne Ɗana ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai.”

Categories
MAT

MAT 4

Shaiɗan Ya Gwada Yesu

1 Sa’an nan sai Ruhu ya kai Yesu cikin jeji, domin Iblis yă gwada shi.

2 Da ya yi azumi kwana arba’in ba dare ba rana, daga baya yunwa ta kama shi.

3 Sai Mai Gwadawar nan ya zo, ya ce masa, “In kai Ɗan Allah ne, ka umarci duwatsun nan su zama gurasa.”

4 Amma Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake cewa,

‘Ba da gurasa kaɗai mutum zai rayu ba,

Sai dai da kowace maganar da yake fitowa daga wurin Allah.’ ”

5 Sa’an nan Iblis ya kai shi tsattsarkan birni, ya ɗora shi can kan tsororuwar Haikali,

6 ya ce masa, “In kai Ɗan Allah ne, to dira ƙasa. Don a rubuce yake cewa,

‘Zai yi wa mala’ikunsa umarni game da kai,’

da kuma

‘Za su tallafe ka,

Don kada ka yi tuntuɓe da dutse.’ ”

7 Sai Yesu ya ce masa, “A rubuce yake kuma cewa, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’ ”

8 Har wa yau dai, sai Iblis ya kai shi kan wani dutse mai tsawo ƙwarai, ya nunnuna masa dukan mulkokin duniya da ɗaukakarsu.

9 Ya kuma ce masa, “Duk waɗannan zan ba ka in ka faɗi a gabana ka yi mini sujada.”

10 Sai Yesu ya ce masa, “Tafi daga nan, kai Shaiɗan! domin a rubuce yake cewa,

‘Kă yi wa Ubangiji Allahnka sujada,

Shi kaɗai za ka bauta wa.’ ”

11 Sa’an nan Iblis ya rabu da shi. Sai ga mala’iku sun zo suna yi masa hidima.

Yesu Ya Fara Hidima a Galili

12 To, da Yesu ya ji an tsare Yahaya, sai ya tashi zuwa ƙasar Galili.

13 Ya kuma bar Nazarat, ya koma Kafarnahum da zama, can bakin teku, a kan iyakar ƙasar Zabaluna da Naftali,

14 domin a cika faɗar Annabi Ishaya cewa,

15 “Ƙasar Zabaluna da ƙasar Naftali,

Da bakin bahar, da hayin Kogin Urdun,

Da kuma ƙasar Galili ta al’ummai,

16 Mazaunan duhu sun ga babban haske,

Mazaunan bakin mutuwa da fargabarta,

Haske ya keto musu.”

17 Tun daga lokacin nan, Yesu ya fara wa’azi, yana cewa, “Ku tuba domin Mulkin Sama ya kusato.”

Yesu Ya Kira Masunta Huɗu

18 Yana tafiya a bakin Tekun Galili ke nan, sai ya ga waɗansu ‘yan’uwa biyu, Saminu da ake kira Bitrus, da ɗan’uwansa Andarawas, suna jefa taru a teku, don su masunta ne.

19 Sai ya ce musu, “Ku bi ni, zan mai da ku masuntan mutane.”

20 Nan da nan, sai suka watsar da tarunansu, suka bi shi.

21 Da ya ci gaba sai ya ga waɗansu mutum biyu, su kuma ‘yan’uwa ne, Yakubu ɗan Zabadi, da ɗan’uwansa Yahaya, suna cikin jirgi tare da ubansu Zabadi, suna gyaran tarunansu. Sai ya kira su.

22 Nan take suka bar jirgin duk da ubansu, suka bi shi.

Yesu Ya Hidimanta wa Mutane Masu Yawa

23 Sai ya zazzaga duk ƙasar Galili, yana koyarwa a majami’unsu, yana shelar bisharar Mulkin Allah, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiya na mutane.

24 Ta haka ya shahara a cikin duk ƙasar Suriya. Aka kuwa kakkawo masa dukan marasa lafiya, masu fama da cuta iri iri, da masu shan azaba, da kuma masu aljannu, da masu farraɗiya, da shanyayyu, ya kuwa warkar da su.

25 Taro masu yawan gaske suka bi shi daga ƙasar Galili, da Dikafolis, da Urushalima, da ƙasar Yahudiya, har ma daga hayin Kogin Urdun.

Categories
MAT

MAT 5

Wa’azi a kan Dutse

1 Da Yesu ya ga taro masu yawa sai ya hau dutse. Da ya zauna, almajiransa kuma suka zo gunsa.

2 Sai ya buɗe baki ya koya musu.

Albarku

3 “Albarka tā tabbata ga waɗanda suka san talaucinsu na ruhu, domin Mulkin Sama nasu ne.

4 “Albarka tā tabbata ga masu nadāma, domin za a sanyaya musu rai.

5 “Albarka tā tabbata ga masu tawali’u, domin za su gāji duniya.

6 “Albarka tā tabbata ga masu kwaɗaita ga adalci, domin za a biya musu muradi.

7 “Albarka tā tabbata ga majiya tausayi, domin su ma za a ji tausayinsu.

8 “Albarka tā tabbata ga masu tsarkakakkiyar zuciya, domin za su ga Allah.

9 “Albarka tā tabbata ga masu ƙulla zumunci, domin za a ce da su ‘ya’yan Allah.

10 “Albarka tā tabbata ga masu shan tsanani saboda aikata adalci, domin Mulkin Sama nasu ne.

11 “Albarka tā tabbata gare ku sa’ad da mutane suka zage ku, suka tsananta muku, suka kuma ƙaga muku kowace irin mugunta, saboda ni.

12 Ku yi murna da farin ciki matuƙa, domin sakamakonku mai yawa ne a Sama, gama haka aka tsananta wa annabawan da suka riga ku.”

Gishiri da Haske

13 “Ku ne gishirin duniya. Amma in gishiri ya sāne, da me za a daɗaɗa shi? Ba shi da sauran amfani, sai dai a zubar, mutane kuma su tattake.

14 “Ku ne hasken duniya. Ai, birnin da aka gina bisa tudu ba shi ɓoyuwa.

15 Ba a kunna fitila a rufe ta da masaki, sai dai a ɗora ta a kan maɗorinta, sa’an nan ta ba duk mutanen gida haske.

16 To, haskenku yă riƙa haskakawa haka a gaban mutane, domin su ga kyawawan ayyukanku, su kuma ɗaukaka Ubanku da yake cikin Sama.”

Koyarwar Yesu a kan Attaura

17 “Kada ku yi zaton na zo ne in shafe Attaura da koyarwar annabawa. Na zo ne ba domin in shafe su ba, sai dai domin in cika su.

18 Hakika ina gaya muku, kafin sararin sama da ƙasa su shuɗe, ko wasali ko ɗigo na Attaura ba za su shuɗe ba, sai an cika dukan kome.

19 Don haka duk wanda ya yar da umarni ɗaya mafi ƙanƙanta daga cikin umarnan nan, har ya koya wa mutane haka, za a ce da shi mafi ƙanƙanta a Mulkin Sama. Duk wanda ya bi su kuwa, har ya koyar da su, za a ce da shi mai girma a Mulkin Sama.

20 Ina dai gaya muku, in adalcinku bai fi na malaman Attaura da Farisiyawa ba, ba za ku shiga Mulkin Sama ba faufau.”

Koyarwar Yesu a kan Fushi

21 “Kun dai ji an faɗa wa mutanen dā, ‘Kada ka yi kisankai, kowa ya yi kisa kuwa, za a hukunta shi.’

22 Amma ni ina gaya muku, kowa yake fushi da ɗan’uwansa ma, za a hukunta shi. Kowa ya ce da ɗan’uwansa wawa, za a kai shi gaban majalisa. Kowa kuma ya ce, ‘Kai wofi!’ hakkinsa shiga Gidan Wuta.

23 Saboda haka, in kana cikin miƙa sadakarka a kan bagadin hadaya, a nan kuma ka tuna ɗan’uwanka na da wata magana game da kai,

24 sai ka dakatar da sadakarka a gaban bagadin hadaya tukuna, ka je ku shirya da ɗan’uwanka, sa’an nan ka zo ka miƙa sadakarka.

25 Ka hanzarta shiryawa da mai ƙararka tun kuna tafiya gaban shari’a, don kada mai kararka ya bashe ka ga alƙali, alƙali kuma ya miƙa ka ga dogari, a kuma jefa ka a kurkuku.

26 Hakika ina gaya maka, ba za ka fita daga nan ba, sai ka biya duk, babu sauran ko anini.”

Koyarwar Yesu a kan Zina

27 “Kun dai ji an faɗa, ‘Kada ka yi zina.’

28 Amma ni ina gaya muku, kowa ya dubi mace duban sha’awa, ya riga ya yi zinar zuci ke nan da ita.

29 In idonka na dama yana sa ka yi laifi, to, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓinka da a jefa duk jikinka ɗungum a Gidan Wuta.

30 In kuma hannunka na dama, yana sa ka yi laifi, to, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓinka da a jefa jikinka ɗungum a Gidan Wuta.”

Koyarwar Yesu a kan Kisan Aure

31 “An kuma ce, ‘Kowa ya saki matarsa, sai ya ba ta takardar saki.’

32 Amma ni ina gaya muku, kowa ya saki matarsa, in ba a kan laifin zina ba, ya sa ta hanyar zina ke nan. Wanda kuma ya auri sakakkiya, ya yi zina.”

Koyarwar Yesu a kan Rantsuwa

33 “Har wa yau dai kun ji an faɗa wa mutanen dā, ‘Kada ka rantse a kan ƙarya, sai dai ka cika wa’adin da ka ɗaukar wa Ubangiji.’

34 Amma ni ina gaya muku, kada ma ku rantse sam, ko da sama, domin ita ce kursiyin Allah,

35 ko da ƙasa, domin ita ce matashin ƙafarsa, ko kuma da Urushalima, domin ita ce birnin Babban Sarki.

36 Kada kuwa ka rantse da kanka, don ba za ka iya mai da ko gashi ɗaya fari ko baƙi ba.

37 Abin da duk za ku faɗa ya tsaya a kan ‘I’ ko ‘A’a’ kawai. In dai ya zarce haka, to, daga Mugun ya fito.”

Koyarwar Yesu a kan Ramawa

38 “Kun dai ji an faɗa, ‘Sakayyar ido, ido ne, sakayyar haƙori kuma haƙori ne.’

39 Amma ni ina gaya muku, kada ku ƙi a cuce ku. Amma ko wani ya mare ka a kuncin dama, to, juya masa ɗayan kuma.

40 In kuwa wani ya yi ƙararka da niyyar karɓe taguwarka, to, ka bar masa mayafinka ma.

41 In kuma wani ya tilasta maka ku yi tafiyar mil guda tare, to, ku yi tafiyar mil biyu ma.

42 Kowa ya roƙe ka, ka ba shi, mai neman rance a wurinka kuwa, kada ka hana shi.”

Ƙaunar Magabta

43 “Kun dai ji an faɗa, ‘Ka so ɗan’uwanka, ka ƙi magabcinka.’

44 Amma ni ina gaya muku, ku ƙaunaci magabtanku, ku yi wa masu tsananta muku addu’a,

45 domin ku zama ‘ya’yan Ubanku wanda yake cikin Sama. Domin yakan sa rana tasa ta fito kan mugaye da kuma nagargaru, ya kuma sako ruwan sama ga masu adalci da marasa adalci.

46 In masoyanku kawai kuke ƙauna, wane lada ne da ku? Ashe, ko masu karɓar haraji ma ba haka suke yi ba?

47 In kuwa ‘yan’uwanku kaɗai kuke gayarwa, me kuka yi fiye da waɗansu? Ashe, ko al’ummai ma ba haka suke yi ba?

48 Saboda haka sai ku zama cikakku, kamar yadda Ubanku na Sama take cikakke.”

Categories
MAT

MAT 6

Koyarwar Yesu a kan Ba Da Sadaka

1 “Ku yi hankali kada ibadarku ta zama ta ganin ido. Domin in kun yi haka, ba za ku sami sakamako wurin Ubanku da yake a Sama ba.

2 “Wato, in za ka yi sadaka, kada ka yi kwakwazo yadda munafukai suke yi a majami’u da kuma kan hanya don dai mutane su yabe su. Gaskiya nake faɗa muku, sun sami iyakar ladarsu ke nan.

3 Amma in kana yin sadaka, kada hannunka na hagu ya san abin da hannunka na dama yake yi,

4 domin sadakarka tă zama a asirce, Ubanku kuwa da yake ganin abin da ake yi a asirce, zai sāka maka.”

Koyarwar Yesu a kan Addu’a

5 “In za ku yi addu’a, kada ku zama kamar munafukai, don sun cika son yin addu’a a tsaye a majami’u da kan hanya, wai mutane su gan su. Gaskiya nake gaya muku, sun sami iyakar ladansu.

6 Amma in za ka yi addu’a, sai ka shiga lollokinka, ka rufe ƙofa, ka yi addu’a ga Ubanku wanda yake ɓoye, Ubanku kuwa da yake ganin abin da ake yi a asirce, zai sāka maka.

7 “In kuwa kuna addu’a, kada ku yi ta maimaitawar banza, kamar yadda al’ummai suke yi, a zatonsu za a saurare su saboda yawan maganarsu.

8 Kada ku zama kamarsu, domin Ubanku ya san bukatarku tun kafin ku roƙe shi.

9 Saboda haka sai ku yi addu’a kamar haka,

‘Ya Ubanmu, wanda yake cikin Sama,

A kiyaye sunanka da tsarki.

10 Mulkinka yă zo,

A aikata nufinka a duniya kamar yadda ake yi a Sama.

11 Ka ba mu abincinmu na yau.

12 Ka gafarta mana laifofinmu,

Kamar yadda mu ma muke gafarta wa waɗanda suke yi mana laifi.

13 Kada ka kai mu wurin jaraba,

Amma ka cece mu daga Mugun.’

14 Domin in kun yafe wa mutane laifofinsu, Ubanku na Sama zai yafe muku.

15 In kuwa ba ku yafe wa mutane laifofinsu ba, Ubanku ma ba zai yafe muku naku ba.”

Koyarwar Yesu a kan Azumi

16 “In kuma kuna yin azumi, kada ku turɓune fuska kamar munafukai, don sukan yanƙwane fuska, wai don mutane su ga suna azumi ne. Hakika, ina gaya muku, sun sami iyakar ladansu ke nan.

17 Amma in kana azumi, ka shafa mai a ka, ka kuma wanke fuska,

18 don kada mutane su ga alama kana azumi, sai dai Ubanku da yake ɓoye ya gani. Ubanku kuma da yake ganin abin da ake yi a asirce, zai sāka maka.”

Tara Dukiya a Sama

19 “Kada ku tara wa kanku dukiya a duniya, inda asu da tsatsa suke ɓatawa, inda ɓarayi kuma suke karyawa su yi sata.

20 Sai dai ku tara wa kanku dukiya a Sama, inda ba asu da tsatsa da za su ɓata, inda kuma ba ɓarayin da za su karya su yi sata.

21 Domin kuwa inda dukiyarka take, a nan zuciyarka ma take.”

Fitilar Jiki

22 “Ido shi ne fitilar jiki. In idonka lafiyayye ne, duk jikinka ma sai ya cika da haske.

23 In kuwa idonka da lahani, duk jikinka sai ya cika da duhu. To, in hasken da yake gare ka duhu ne, ina misalin yawan duhun!”

Bauta wa Allah ko Dukiya

24 “Ba mai iya bauta wa iyayengiji biyu; ko dai ya ƙi ɗaya, ya so ɗaya, ko kuwa ya amince wa ɗayan, ya raina ɗayan. Ba dama ku bauta wa Allah da dukiya gaba ɗaya.”

Damuwa da Alhini

25 “Saboda haka ina gaya muku, kada ku damu a kan rayuwarku game da abin da za ku ci, da abin da za ku sha, ko kuwa jikinku, abin da za ku yi sutura. Ashe, rai bai fi abinci ba? Jiki kuma bai fi tufafi ba?

26 Ku dubi dai tsuntsaye. Ai, ba sa shuka, ba sa girbi, ba sa kuma tarawa a rumbuna, amma kuwa Ubanku na Sama na ci da su. Ashe, ko ba ku fi martaba nesa ba?

27 Wane ne a cikinku, don damuwarsa, zai iya ƙara ko da taƙi ga tsawon rayuwarsa?

28 To, don me kuke damuwa a kan tufafi? Ku dubi dai furannin jeji, yadda suke girma, ba sa aikin fari, ba sa na baƙi,

29 duk da haka ina gaya muku, ko Sulemanu ma, shi da adonsa duk, bai taɓa yin adon da ya fi na ɗayansu ba.

30 To, ga shi, Allah yana ƙawata tsire-tsiren jeji ma haka, waɗanda yau suke raye, gobe kuwa a jefa su a murhu, balle ku? Ya ku masu ƙarancin bangaskiya!

31 Don haka kada ku damu, kuna cewa, ‘Me za mu ci?’ ko, ‘Me za mu sha?’ ko kuwa, ‘Me za mu sa?’

32 Ai, al’ummai ma suna ta neman duk irin waɗannan abubuwa, Ubanku na Sama kuwa ya san kuna bukatarsu duka.

33 Muhimmin abu na farko, sai ku ƙwallafa rai ga al’amuran Mulkin Allah, da kuma adalcinsa, har ma za a ƙara muku dukan waɗannan abubuwa.

34 “Saboda haka kada ku damu don gobe, ai, gobe ta Allah ce. Wahalce-wahalcen yau ma sun isa wahala.”

Categories
MAT

MAT 7

Kada Ku Ɗora wa Kowa Laifi

1 “Kada ku ɗora wa kowa laifi, don kada a ɗora muku.

2 Don da irin hukuncin da kuka zartar, da shi za a zartar muku. Mudun da kuka auna, da shi za a auna muku.

3 Don me kake duban ɗan hakin da yake idon ɗan’uwanka, amma gungumen da yake a naka ido ba ka kula ba?

4 Ko kuwa yaya za ka iya ce wa ɗan’wanka, ‘Bari in cire maka ɗan hakin daga idonka,’ alhali kuwa da gungume a naka ido?

5 Kai munafuki! Sai ka fara cire gungumen da yake idonka tukuna, sa’an nan ka gani sosai yadda za ka cire ɗan hakin daga idon ɗan’uwanka.

6 “Kada ku ba karnuka abin da yake tsattsarka. Kada kuma ku jefa wa alhanzir lu’ulu’unku, don kada su tattake su, su juyo su kyakketa ku.”

Ku Roƙa, Ku Nema, Ku Ƙwanƙwasa

7 “Ku yi ta roƙo, za a ba ku. Ku yi ta nema, za ku samu. Ku yi ta ƙwanƙwasawa, za a kuwa buɗe muku.

8 Duk wanda ya roƙa, akan ba shi, mai nema yana tare da samu. Wanda ya ƙwanƙwasa kuma za a buɗe masa.

9 To, wane ne a cikinku, ɗansa zai roƙe shi gurasa, ya ba shi dutse?

10 Ko kuwa ya roƙe shi kifi, ya ba shi maciji?

11 To, ku da kuke mugaye ma, kuka san yadda za ku ba ‘ya’yanku kyautar kyawawan abubuwa, balle Ubanku na Sama da zai ba da abubuwan alheri ga masu roƙonsa?

12 Saboda haka duk abin da kuke so mutane su yi muku, ku ma sai ku yi musu, domin wannan shi ne Attaura da koyarwar annabawa.”

Ƙunƙuntar Ƙofa

13 “Ku shiga ta ƙunƙuntar ƙofa, gama ƙofa zuwa hallaka faffaɗa ce, hanyarta mai sauƙin bi ce, masu shiga ta cikinta suna da yawa.

14 Domin kuwa ƙofar zuwa rai ƙunƙunta ce, hanyarta mai wuyar bi ce, masu samunta kuwa kaɗan ne.”

Akan Gane Itace ta ‘Ya’yansa

15 “Ku kula da annabawan ƙarya, waɗanda sukan zo muku da siffar tumaki, amma a zuci kyarketai ne masu ƙāwa.

16 Za ku gane su ta irin aikinsu. A iya ciran inabi a jikin ƙaya, ko kuwa ɓaure a jikin sarƙaƙƙiya?

17 Haka kowane itacen kirki yakan haifi kyawawan ‘ya’ya. Mummunan itace kuwa yakan haifi munanan ‘ya’ya.

18 Kyakkyawan itace ba dama ya haifi munanan ‘ya’ya. Haka kuma mummunan itace ba dama ya haifi kyawawan ‘ya’ya.

19 Duk itacen da ba ya ‘ya’ya masu kyau, sai a sare shi a jefa a wuta.

20 Don haka, da irin aikinsu za a gane su.”

Ban Taɓa Saninku ba

21 “Ba duk mai ce mini, ‘Ya Ubangiji, ya Ubangiji,’ ne zai shiga Mulkin Sama ba, sai dai wanda ya yi abin da Ubana da yake cikin Sama yake so.

22 A ranar nan da yawa za su ce mini, ‘Ya Ubangiji, ya Ubangiji, ashe, ba mu yi annabci da sunanka ba? Ba mu fitar da aljannu da sunanka ba? Ba mu kuma yi ayyukan al’ajabi masu yawa da sunanka ba?’

23 Sa’an nan zan ce musu, ‘Ni ban taɓa saninku ba. Ku rabu da ni, ku masu yin mugun aiki.’ ”

Kafa Harsashin Gini Iri Biyu

24 “Saboda haka, kowa da yake jin maganar nan tawa, yake kuma aikata ta, za a kwatanta shi da mutum mai hikima, wanda ya gina gidansa a kan fā.

25 Da ruwa ya sauko, koguna suka yi cikowa, iska ta taso ta bugi gidan, amma bai faɗi ba, domin an gina shi a kan fā ne.

26 Kowa ya ji maganar nan tawa, bai aikata ta kuma ba, za a misalta shi da wawan mutum, wanda ya gina gidansa a kan rairayi.

27 Da ruwa ya sauko, koguna suka yi cikowa, sai iska ta taso ta bugi gidan har ya rushe, mummunar ragargajewa kuwa!”

Hakikancewar Yesu

28 Da Yesu ya gama duk wannan magana, sai taro suka yi mamakin koyarwarsa,

29 domin yana koya musu da hakikancewa, ba kamar malamansu na Attaura ba.

Categories
MAT

MAT 8

Yesu Ya Warkar da Kuturu

1 Da ya sauko daga dutsen, sai taro masu yawan gaske suka bi shi.

2 Sai ga wani kuturu ya zo gunsa ya yi masa sujada, ya ce, “Ya Ubangiji, in dai ka yarda, kana da iko ka tsarkake ni.”

3 Sai Yesu ya miƙa hannu, ya taɓa shi, ya ce, “Na yarda, ka tsarkaka.” Nan take kuturtarsa ta warke.

4 Sai Yesu ya ce masa, “Ka kula fa, kada ka gaya wa kowa kome. Sai dai ka je wurin firist ya gan ka, ka kuma yi sadaka domin tabbatarwa a gare su, kamar yadda Musa ya umarta.”

Yesu Ya Warkar da Yaron Wani Jarumi

5 Yana shiga Kafarnahum ke nan, sai wani jarumi ya zo gunsa ya roƙe shi,

6 ya ce, “Ya Ubangiji, yarona na kwance a gida, ya zama shanyayye, yana shan azaba ƙwarai.”

7 Yesu ya ce masa, “Zan zo in warkar da shi.”

8 Sai jarumin, ya ce, “Ya Ubangiji, ban isa har ka zo gidana ba, amma sai ka yi magana kawai, yarona kuwa zai warke.

9 Don ni ma a hannun wani nake, da kuma soja a hannuna, sai in ce wa wannan, ‘Je ka,’ sai ya je, wani kuwa in ce masa, ‘Zo,’ sai ya zo, in ce wa bawana, ‘Yi abu kaza,’ sai ya yi.”

10 Da Yesu ya ji haka, sai ya yi mamaki, har ya ce wa mabiyansa, “Gaskiya, ina gaya muku, ko a cikin Isra’ila ban taɓa samun bangaskiya mai ƙarfi irin wannan ba.

11 Ina kuma gaya muku, da yawa za su zo daga gabas da yamma su zauna cin abinci tare da Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu a Mulkin Sama,

12 ‘ya’yan Mulki kuwa sai a jefa su matsanancin duhu. Nan za su yi kuka da cizon haƙora.”

13 Sai Yesu ya ce wa jarumin, “Je ka, ya zama maka gwargwadon bangaskiyar da ka yi.” Nan take yaronsa ya warke.

Yesu Ya Warkar da Surukar Bitrus

14 Da Yesu ya shiga gidan Bitrus, sai ya ga surukar Bitrus tana kwance da zazzaɓi.

15 Sai ya taɓa hannunta, zazzaɓin ya sake ta, ta kuma tashi ta yi masa hidima.

Yesu Ya Warkar da Mutane da Yawa da Maraice

16 Da maraice ya yi, sai suka kakkawo masa masu aljannu da yawa. Da magana kawai ya fitar da aljannun, ya kuma warkar da dukan marasa lafiya.

17 Wannan kuwa domin a cika faɗar Annabi Ishaya ne cewa, “Da kansa ya ɗebe rashin lafiyarmu, ya ɗauke cucecucenmu.”

Masu Cewa, Za Su Bi Yesu

18 To, da Yesu ya ga taro masu yawan gaske sun kewaye shi, sai ya yi umarni a koma wancan hayi.

19 Sai wani malamin Attaura ya zo ya ce masa, “Malam, zan bi ka duk inda za ka je.”

20 Yesu ya ce masa, “Yanyawa da ramummukansu, tsuntsaye kuma da sheƙunan, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin shaƙatawa.”

21 Sai ɗaya daga almajiran ya ce masa, “Ya Ubangiji, ka bar ni tukuna in je in binne tsohona.”

22 Amma Yesu ya ce masa, “Bi ni. Bari matattu su binne ‘yan’uwansu matattu.”

Yesu Ya Tsawata wa Hadiri

23 Da ya shiga jirgi, almajiransa suka bi shi.

24 Sai ga wani babban hadiri ya taso a teku, har raƙuman ruwa suka fara shan kan jirgin, amma yana barci.

25 Sai almajiransa suka je suka tashe shi, suka ce, “Ya Ubangiji, ka cece mu, za mu hallaka!”

26 Ya ce musu, “Don me kuka firgita haka, ya ku masu ƙarancin bangaskiya?” Sa’an nan ya tashi, ya tsawata wa iskar da ruwan. Sai wurin duk ya yi tsit!

27 Mutanen suka yi al’ajabi, suka ce, “Wane irin mutum ne wannan, wanda har iska da ruwan teku ma suke masa biyayya?”

Warkar da Masu Aljannu na Garasinawa

28 Da ya isa wancan hayi a ƙasar Garasinawa, mutum biyu masu aljannu suka fito daga makabarta suka tarye shi. Don kuwa su abin tsoro ne ƙwarai, har ba mai iya bi ta wannan hanya.

29 Sai suka ƙwala ihu suka ce, “Ina ruwanka da mu, kai Ɗan Allah? Ka zo nan ne ka yi mana azaba tun kafin lokaci ya yi?”

30 Nesa kuma kaɗan akwai wani babban garken alade na kiwo.

31 Sai aljannun suka roƙe shi, suka ce, “In ka fitar da mu, tura mu cikin garken aladen nan.”

32 Ya ce musu, “To, ku je.” Sai suka fita, suka shiga aladen. Sai kuwa duk garken suka rugungunta ta gangaren, suka faɗa tekun, suka hallaka a ruwa.

33 Masu kiwon aladen suka gudu, suka shiga gari, suka yi ta ba da labarin kome da kome, da kuma abin da ya auku ga masu aljannun.

34 Sai ga duk jama’ar garin sun firfito su taryi Yesu. Da suka gan shi, sai suka roƙe shi ya bar musu ƙasarsu.

Categories
MAT

MAT 9

Yesu Ya Warkar da Shanyayye

1 Da ya shiga jirgi, ya haye ya je garinsu.

2 Sai aka kawo masa wani shanyayye, kwance a gado. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, “Ɗana, ka yi farin ciki, an gafarta maka zunubanka.”

3 Sai waɗansu malaman Attaura suka ce a ransu, “Wannan mutum, ai, saɓo yake!”

4 Yesu kuwa, da yake ya san tunaninsu, ya ce, “Don me kuke mugun tunani a zuciyarku?

5 Wanne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuwa a ce, ‘Tashi ka yi tafiya’?

6 Amma domin ku sakankance Ɗan Mutum yana da ikon gafarta zunubi a duniya”–sai ya ce wa shanyayyen–“Tashi, ka ɗauki shimfiɗarka ka tafi gida.”

7 Shi kuwa ya tashi ya tafi gida.

8 Da taron suka ga haka, sai tsoro ya kama su, suka ɗaukaka Allah, wanda ya ba mutane iko haka.

Kiran Matiyu

9 Da Yesu ya yi gaba, ya ga wani mutum mai suna Matiyu a zaune, yana aiki a wurin karɓar haraji. Ya ce masa, “Bi ni.” Sai ya tashi ya bi shi.

10 Sa’ad da kuwa Yesu yake cin abinci a gida, sai ga masu karɓar haraji da masu zunubi da yawa sun zo, sun zauna tare da shi da almajiransa.

11 Da Farisiyawa suka ga haka, sai suka ce wa almajiransa, “Don me malaminku yake ci tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?”

12 Amma da Yesu ya ji haka ya ce, “Ai, lafiyayyu ba ruwansu da likita, sai dai marasa lafiya.

13 Sai ku fahimci ma’anar wannan tukuna, ‘Ni kam, zaman jinƙai nake nema a gare ku, ba hadaya ba.’ Ba domin in kira masu adalci na zo ba, sai dai masu zunubi.”

Tambaya a kan Azumi

14 Sai almajiran Yahaya suka zo wurinsa, suka ce, “Don me mu da Farisiyawa mukan yi azumi, amma naka almajiran ba sa yi?”

15 Sai Yesu ya ce musu, “Abokan ango sa yi baƙin ciki tun ango yana tare da su? Ai, lokaci yana zuwa da za a ɗauke musu angon. A sa’an nan ne fa za su yi azumi.

16 Ba mai mahon tsohuwar tufa da sabon ƙyalle, don mahon zai kece tsohuwar tufar, har ma ta fi dā kecewa.

17 Ba kuma mai ɗura sabon ruwan inabi a tsofaffin salkuna. In ma an ɗura, sai salkunan su fashe, ruwan inabin ya zube, salkunan kuma su lalace. Sabon ruwan inabi, ai, sai sababbin salkuna. Ta haka an tserar da duka biyu ke nan.”

‘Yar Shugaban Jama’a da Matar da ta Taɓa Gezar Mayafin Yesu

18 Yana cikin yi musu magana haka, sai ga wani shugaban jama’a ya zo, ya yi masa sujada, ya ce, “Yanzu yanzu ‘yata ta rasu, amma ka zo ka ɗora mata hannu, za ta rayu.”

19 Sai Yesu ya tashi, ya bi shi tare da almajiransa.

20 Ga kuma wata mace wadda ta shekara goma sha biyu tana zub da jini, ta raɓo ta bayansa, ta taɓa gezar mayafinsa,

21 domin ta ce a ranta, “Ko da mayafinsa ma na taɓa, sai in warke.”

22 Sai Yesu ya juya, yă gan ta, ya ce, “’Yata, ki yi farin ciki, bangaskiyarki ta warkar da ke.” Nan take matar ta warke.

23 Da Yesu ya isa gidan shugaban jama’ar, ya kuma ga masu busar sarewa da taro suna ta hayaniya,

24 sai ya ce, “Ku ba da wuri, ai, yarinyar ba matacciya take ba, barci take yi.” Sai suka yi masa dariyar raini.

25 Amma da aka fitar da taron waje, ya shiga ya kama hannunta, sai kuwa yarinyar ta tashi.

26 Wannan labarin kuwa ya bazu a duk ƙasar.

Makafi Biyu Sun Sami Ganin Gari

27 Da Yesu ya yi gaba daga nan, sai waɗansu makafi biyu suka bi shi, suna ɗaga murya suna cewa, “Ya Ɗan Dawuda, ka ji tausayinmu.”

28 Da ya shiga wani gida sai makafin suka zo gare shi. Yesu ya ce musu, “Kun gaskata ina da ikon yin haka?” Sai suka ce masa, “I, ya Ubangiji!”

29 Sa’an nan ya taɓa idanunsu, ya ce, “Yă zama muku gwargwadon bangaskiyarku.”

30 Sai idanunsu suka buɗe. Amma Yesu ya kwaɓe su ƙwarai, ya ce, “Kada fa kowa ya ji labarin.”

31 Amma suka tafi suka yi ta baza labarinsa a duk ƙasar.

Bebe Ya Yi Magana

32 Sun tashi ke nan, sai aka kawo masa wani bebe mai aljan.

33 Bayan an fitar da aljanin, sai beben ya yi magana, taron kuwa suka yi mamaki, suka ce, “Kai! Ba a taɓa ganin irin wannan a cikin Isra’ila ba.”

34 Amma sai Farisiyawa suka ce, “Ai, da ikon sarkin aljannu yake fitar da aljannu.”

Yesu Ya Ji Tausayin Mutane

35 Sai Yesu ya zazzaga dukan garuruwa da ƙauyuka, yana koyarwa a majami’unsu, yana yin bisharar Mulkin Allah, yana kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.

36 Amma da ya ga taro masu yawa sai ya ji tausayinsu, domin suna shan wahala, suna nan a warwatse kamar tumaki da ba makiyayi.

37 Sai ya ce wa almajiransa, “Girbin yana da yawa, amma masu yinsa kaɗan ne.

38 Saboda haka ku roƙi Ubangijin girbin ya turo masu girbi, su yi masa girbi.”

Categories
MAT

MAT 10

Yesu Ya Zaɓi Almajirai Sha Biyu

1 Sai ya kira almajiransa goma sha biyu, ya kuma ba su ikon fitar da baƙaƙen aljannu, su warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.

2 To, ga sunayen manzannin nan goma sha biyu. Da fari, Saminu, wanda ake kira Bitrus, da ɗan’uwansa Andarawas, da Yakubu ɗan Zabadi, da ɗan’uwansa Yahaya,

3 da Filibus, da Bartalamawas, da Toma, da Matiyu mai karɓar haraji, da Yakubu ɗan Halfa, da Yahuza,

4 da Saminu Bakan’ane, da kuma Yahuza Iskariyoti wanda ya bashe shi.

Yesu Ya Aiki Sha Biyu Ɗin

5 Su sha biyun nan ne Yesu ya aika, ya yi musu umarni, ya ce, “Kada ku shiga ƙasar al’ummai, ko kuma kowane garin Samariyawa.

6 Sai dai ku je wurin batattun tumakin jama’ar Isra’ila,Irm

7 kuna tafiya, kuna wa’azi, kuna cewa, ‘Mulkin Sama ya kusato.’

8 Ku warkar da marasa lafiya, ku ta da matattu, ku tsarkake kutare, ku kuma fitar da aljannu. Kyauta kuka samu, ku kuma bayar kyauta.

9 Kada ku riƙi kuɗin zinariya, ko na azurfa, ko na tagulla a ɗamararku,

10 kada kuma ku ɗauki burgami a tafiyarku, ko taguwa biyu, ko takalma, ko sanda, don ma’aikaci ya cancanci hakkinsa.

11 Duk gari ko ƙauyen da kuka shiga, ku nemi mai mutunci a cikinsa, ku kuma baƙunce shi har ku tashi.

12 In za ku shiga gidan ku ce, ‘Salama alaiku.’

13 In gidan na kirki ne, salamarku tă tabbata a gare shi. In kuwa ba na kirki ba ne, to, tă komo muku.

14 Kowa kuma ya ƙi yin na’am da ku, ko kuwa ya ƙi sauraron maganarku, da fitarku gidan ko garin, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku.

15 Hakika, ina gaya muku, a Ranar Shari’a za a fi haƙurce wa ƙasar Saduma da ta Gwamrata a kan garin nan.”

Tsanani Mai Zuwa

16 “Ga shi, na aike ku kamar tumaki a tsakiyar kyarketai. Don haka sai ku zama masu azanci kamar macizai, da kuma marasa ɓarna kamar kurciyoyi.

17 Ku yi hankali da mutane, don za su kai ku gaban majalisa, su kuma yi muku bulala a majami’arsu.

18 Za su kuma ja ku gaban mahukunta da sarakuna saboda ni, domin ku ba da shaida a gabansu, a gaban al’ummai kuma.

19 A lokacin da suka ba da ku, kada ku damu da yadda za ku yi magana, ko kuwa abin da za ku faɗa, domin za a ba ku abin da za ku faɗa a lokacin.

20 Domin ba ku ne kuke magana ba, Ruhun Ubanku ne yake magana ta bakinku.

21 ‘Dan’uwa zai ba da ɗan’uwansa a kashe shi, uba kuwa ɗansa. ‘Ya’ya kuma za su tayar wa iyayensu, har su sa a kashe su.

22 Kowa kuma zai ƙi ku saboda sunana. Amma duk wanda ya jure har ƙarshe, zai cetu.

23 In sun tsananta muku a wannan gari, ku gudu zuwa na gaba. Gaskiya, ina gaya muku, kafin ku gama zazzaga dukan garuruwan Isra’ila, Ɗan Mutum zai zo.

24 “Almajiri ba ya fin malaminsa, bawa kuma ba ya fin ubangijinsa.

25 Ya isa wa almajiri ya zama kamar malaminsa, bawa kuma kamar ubangijinsa. In har sun kira maigida Ba’alzabul, to, mutanen gidansa kuma fa?”

Wanda Za a Ji Tsoro

26 “Don haka kada ku ji tsoronsu, domin ba abin da yake a rufe da ba zai tonu ba, ko kuwa abin da yake ɓoye da ba za a bayyana ba.

27 Abin da nake gaya muku a asirce, ku faɗa a sarari. Abin da kuma kuka ji a raɗe, ku yi shelarsa daga kan soraye.

28 Kada ku ji tsoron masu kisan mutum, amma ba sa iya kashe kurwarsa. Sai dai ku ji tsoron wannan da yake da ikon hallaka kurwar da jikin duka a Gidan Wuta.

29 Ashe, ba gwara biyu ne kobo ba? Ba kuwa ɗayarsu da za ta mutu, ba da yardar Ubanku ba.

30 Ai, ko da gashin kanku ma duk a ƙidaye yake.

31 Kada ku ji tsoro. Ai, martabarku ta fi ta gwara masu yawa.”

Bayyana Yarda da Almasihu gaban Mutane

32 “Kowa ya bayyana yarda a gare ni a gaban mutane, ni ma zan bayyana yarda a gare shi a gaban Ubana da yake cikin Sama.

33 Duk wanda kuwa ya yi musun sanina a gaban mutane, ni ma zan yi musun saninsa a gaban Ubanmu da yake cikin Sama.”

Ban Kawo Salama Ba, Sai Takobi

34 “Kada dai ku zaci na zo ne in kawo salama a duniya. A’a, ban zo domin in kawo salama ba, sai dai takobi.

35 Domin na zo ne in haɗa mutum da ubansa gāba, ‘ya da uwatata, matar ɗa kuma da surukarta.

36 Zai zamana kuma magabtan mutum su ne mutanen gidansa.

37 Wanda duk ya fi son ubansa ko uwarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba. Wanda kuma ya fi son ɗansa ko ‘yarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba.

38 Wanda kuma bai ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, bai cancanci zama nawa ba.

39 Duk mai son adana ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa saboda ni, adana shi yake yi.”

Ayyukan Lada

40 “Wanda ya yi na’am da ku, ya yi na’am da ni ke nan. Wanda ya yi na’am da ni kuwa, to, ya yi na’am da wanda ya aiko ni.

41 Wanda ya yi na’am da wani annabi domin shi annabi ne, zai sami ladar annabi. Wanda kuma ya yi na’am da adali domin shi adali ne, zai sami ladar adali.

42 Kowa ya ba ɗaya daga cikin ‘yan yaran nan, ko da moɗa guda ta baƙin ruwa, kan shi almajirina ne, hakika, ina gaya muku, ba zai rasa ladarsa ba.”