Categories
MAT

MAT 21

Mutanen Urushalima Sun Marabci Yesu

1 Da suka kusato Urushalima suka zo Betafaji, wajen Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki almajiransa biyu,

2 ya ce musu, “Ku shiga ƙauyen can da yake gabanku. Da shigarku za ku ga wata jaka a ɗaure, da kuma ɗanta. Ku kwanto su.

3 Kowa ya yi muku magana, ku ce, ‘Ubangiji ne yake bukatarsu,’ zai kuwa aiko da su nan da nan.”

4 An yi wannan kuwa domin a cika faɗar Annabi Zakariya cewa,

5 “Ku ce wa ‘yar Sihiyona,

Ga Sarkinki yana zuwa gare ki,

Mai tawali’u ne,

Yana kan aholaki, wato, ɗan jaki.”

6 Sai almajiran suka tafi suka bi umarnin Yesu.

7 Suka kawo jakar da ɗanta, suka shimfiɗa masu mayafansu, ya hau.

8 Yawancin jama’a suka shisshimfiɗa mayafansu a hanya, waɗansu kuma suka kakkaryo ganye suna bazawa a hanya.

9 Taron jama’a da suke tafiya a gabansa da kuma a bayansa, sai suka ɗauki sowa suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda! Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji! Hosanna ga Allah!”

10 Da ya shiga Urushalima dukkan birnin ya ruɗe, ana ta cewa, “Wane ne wannan?”

11 Sai jama’a suka ce, “Ai, wannan shi ne Annabi Yesu daga Nazarat ta ƙasar Galili.”

Yesu Ya Tsabtace Haikalin

12 Sai Yesu ya shiga Haikalin ya kakkori dukkan masu saye da sayarwa a ciki, ya birkice teburorin ‘yan canjin kuɗi da kujerun masu sayar da tattabarai.

13 Ya ce musu, “A rubuce yake cewa, ‘Za a kira gidana ɗakin addu’a,’ amma ku kun maishe shi kogon ‘yan fashi.”

14 Sai makafi da guragu suka zo wurinsa a Haikalin, ya kuwa warkar da su.

15 Amma manyan firistoci da malaman Attaura suka ga abubuwan al’ajabi da ya yi, har yara suna sowa a Haikalin suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda!” sai suka ji haushi.

16 Suka ce masa, “Kana jin abin da waɗannan suke faɗa?” Yesu kuwa ya ce musu, “I. Amma ba ku taɓa karantawa ba cewa,

‘Kai ne ka shiryar da ‘yan yara da masu shan mama su yabe ka’?”

17 Sai ya bar su, ya fita daga birnin, ya tafi Betanya, ya sauka a can.

La’antar da Itacen Ɓaure

18 Kashegari da sassafe yana komowa birni, sai ya ji yunwa.

19 Da ya ga wani ɓaure a gefen hanya, ya je wurin, amma bai sami kome ba, sai ganye kawai. Sai ya ce wa ɓauren, “Kada ka ƙara yin ‘ya’ya har abada!” Nan take ɓauren ya bushe.

20 Da almajiran suka ga haka, suka yi mamaki suka ce, “Yaya ɓauren nan ya bushe haka nan da nan?”

21 Yesu ya amsa musu ya ce, “Hakika, ina gaya muku, in dai kuna da bangaskiya, ba tare da wata shakka ba, ba abin da aka yi wa ɓauren nan kaɗai za ku yi ba, har ma in kun ce wa dutsen nan, ‘Ka ciru, ka faɗa teku,’ sai kuwa ya auku.

22 Kome kuka roƙa da addu’a, in dai kuna da bangaskiya, za ku samu.”

Ana Shakkar Izinin Yesu

23 Ya shiga Haikali yana cikin koyarwa, sai manyan firistoci da shugabannin jama’a suka zo wurinsa, suka ce, “Da wane izini kake yin abubuwan nan, wa ya ba ka izinin?”

24 Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ni ma zan yi muku wata tambaya. In kun ba ni amsa, ni ma sai in gaya muku ko da wane izini nake yin abubuwan nan.

25 To, baftismar da Yahaya ya yi, daga ina take? Daga Sama take, ko kuwa ta mutum ce?” Sai suka yi ta muhawwara da juna, suna cewa, “In muka ce, ‘Daga Sama take,’ sai ya ce mana, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’

26 In kuwa muka ce, ‘Ta mutum ce,’ ai, muna jin tsoron jama’a, don duk kowa ya ɗauki Yahaya a kan annabi ne.”

27 Sai suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba.” Shi kuma ya ce musu, “Haka ni kuma ba zan faɗa muku ko da wane izini nake yin abubuwan nan ba.”

Misali na Mai ‘Ya’ya Biyu Maza

28 “To, me kuka gani? An yi wani mutun mai ‘ya’ya biyu maza. Ya je wurin na farkon, ya ce, ‘Ɗana, yau je ka ka yi aiki a garkar inabi.’

29 Sai ya ce, ‘Na ƙi.’ Amma daga baya sai ya tuba, ya tafi.

30 Sai ya je gun na biyun ya faɗa masa haka. Shi kuwa ya amsa ya ce, ‘To, za ni, baba,’ amma bai je ba.

31 To, wane ne a cikin su biyun ya yi abin da ubansu yake so?” Sai suka ce, “Na farkon.” Yesu ya ce musu, “Hakika, ina gaya muku, masu karɓar haraji da karuwai suna riga ku shiga Mulkin Allah.

32 Ga shi, Yahaya ya zo ya bayyana muku hanyar adalci, ba ku gaskata shi ba. Amma masu karɓar haraji da karuwai sun gaskata shi, duk da ganin haka kuma, daga baya ba ku tuba kun gaskata shi ba.”

Misali na Manoman da Suka Yi Sufurin Garkar Inabi

33 “To, ga kuma wani misali. An yi wani maigida da ya yi garkar inabi, ya shinge ta, ya haƙa ramin matse inabi a ciki, ya kuma gina wata ‘yar hasumiyar tsaro. Ya ba waɗansu manoma sufurin garkar, sa’an nan ya tafi wata ƙasa.

34 Da kakar inabi ta kusa, sai ya aiki bayinsa wurin manoman nan su karɓo masa gallar garkar.

35 Manoman kuwa suka kama bayinsa, suka yi wa ɗaya dūka, suka kashe ɗaya, suka kuma jajjefi ɗaya.

36 Har wa yau ya sāke aiken waɗansu bayi fiye da na dā, suka kuma yi musu haka.

37 Daga baya sai ya aiki ɗansa gare su, yana cewa, ‘Sā ga girman ɗana.’

38 Amma da manoman suka ga ɗan, suka ce wa juna, ‘Ai, wannan shi ne magajin, ku zo mu kashe shi, gādonsa ya zama namu.’

39 Sai suka kama shi, suka jefa shi bayan shinge, suka kashe shi.

40 To, sa’ad da ubangijin garkar nan ya zo, me zai yi wa manoman nan?”

41 Sai suka ce masa, “Zai yi wa mutanen banzan nan mugun kisa, ya ba waɗansu manoma sufurinta, waɗanda za su riƙa ba shi gallar garkar a lokacin nunanta.”

42 Yesu ya ce musu, “Ashe, ba ku taɓa karantawa a Littattafai ba? cewa,

‘Dutsen da magina suka ƙi,

Shi ne ya zama mafificin dutsen gini.

Wannan aikin Ubangiji ne,

A gare mu kuwa abin al’ajabi ne.’

43 Domin haka ina gaya muku, za a karɓe Mulkin Allah daga gare ku, a bai wa wata al’umma wadda za ta ba da amfani nagari.

44 Kowa ya faɗo a kan dutsen nan, sai ya ragargaje. Amma wanda dutsen nan ya faɗa wa, niƙe shi zai yi kamar gari.”

45 Da manyan firistoci da Farisiyawa suka ji misalan nan da ya yi, sai suka gane, ashe, da su yake.

46 Amma da suka nemi kama shi, suka ji tsoron jama’a, don su sun ɗauke shi shi annabi ne.

Categories
MAT

MAT 22

Misali na Bikin Aure

1 Yesu ya sāke yi musu magana da misalai ya ce,

2 “Za a kwatanta Mulkin Sama da wani sarki, wanda ya yi wa ɗansa biki.

3 Sai ya aiki bayinsa su kirawo waɗanda aka gayyata bikin, amma waɗanda aka gayyatar suka ƙi zuwa.

4 Har wa yau ya sāke aiken waɗansu bayi, ya ce, ‘Ku gaya wa waɗanda aka gayyata, “Ga shi, na shisshirya abinci, an yanka shanuna da kiwatattun maruƙana, duk an shirya kome, ku zo bikin mana!” ’

5 Amma suka ƙi kula, suka tafi abinsu, wani ya tafi gona tasa, wani kuma cinikinsa.

6 Sauran kuwa suka kame bayinsa, suka wulaƙanta su, suka kashe su.

7 Sarki ya yi fushi, ya tura sojansa, suka hallaka masu kisankan nan, suka ƙone garinsu ƙurmus.

8 Sa’an nan ya ce wa bayinsa, ‘Bikin fa ya shiryu sosai, amma waɗanda aka gayyata ba su cancanta ba.

9 Saboda haka ku tafi ƙofofin gari, ku gayyato duk waɗanda kuka samu, su zo bikin.’

10 Sai bayin suka yi ta bin titi titi, suka tattaro duk waɗanda suka samu, mugaye da nagargaru duka, har wurin bikin ya cika maƙil da baƙi.

11 “Da sarki ya shigo ganin baƙin sai ya ga wani mutum a can wanda bai sa riga irin ta biki ba.

12 Sai ya ce masa, ‘Malam, ta yaya ka shigo nan ba tare da sa riga irin ta biki ba?’ Mutumin kuwa ya rasa ta cewa.

13 Sai sarki ya ce wa barorinsa, ‘Ku ɗaure shi ƙafa da hannu, ku jefa shi cikin matsanancin duhu. Nan za a yi kuka da cizon baƙi.’

14 Gama da yawa ake kira, amma kaɗan ne zaɓaɓɓu.”

Biyan Haraji ga Kaisar

15 Sai Farisiyawa suka je suka yi shawara yadda za su burma shi cikin maganarsa.

16 Suka aiko almajiransu wurinsa tare da waɗansu mutanen Hirudus, suka ce, “Malam, ai, mun sani kai mai gaskiya ne, sai koyar da tafarkin Allah sosai kake yi, ba ka kuma zaɓen kowa, don ka ɗauki kowa da kowa daidai.

17 To, faɗa mana abin da ka gani. Shin, daidai ne mu biya Kaisar haraji, ko kuwa?”

18 Yesu kuwa domin ya gane muguntarsu, sai ya ce musu, “Don me kuke jarraba ni? Ku munafukai!

19 Ku nuna mini kuɗin harajin.” Sai suka kawo masa dinari.

20 Yesu ya ce musu, “Surar nan da sunan nan na wane ne?”

21 Suka ce, “Na Kaisar ne.” Sa’an nan ya ce musu, “To, sai ku ba Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba Allah abin da yake na Allah.”

22 Da suka ji haka, sai suka yi mamaki, suka rabu da shi, suka yi tafiyarsu.

Tambaya a kan Tashin Matattu

23 A ran nan sai waɗansu Sadukiyawa (su da suke cewa, ba tashin matattu) suka zo wurinsa, suka yi masa tambaya,

24 suka ce, “Malam, Musa dai ya ce, ‘In mutum ya mutu, bai bar na baya ba, sai lalle ɗan’uwansa ya auri matar, ya haifa wa ɗan’uwansa ‘ya’ya.’

25 To, an yi waɗansu ‘yan’uwa maza bakwai a cikinmu. Na farkon ya yi aure, da ya rasu, da yake bai haifu kuma ba, sai ya bar wa ɗan’uwansa matarsa.

26 Haka ya faru ga na biyun da na ukun, har ya kai kan na bakwai ɗin.

27 Bayansu duka sai matar ta rasu.

28 To, a tashin matattu, matar wa za ta zama a cikinsu, su bakwai ɗin? Don duk sun aure ta.”

29 Amma Yesu ya amsa musu ya ce, “Kun ɓăta ne, domin ba ku san Littattafai ba, ba ku kuma san ikon Allah ba.

30 Domin a tashin matattu, ba a aure, ba a aurarwa, sai dai kamar mala’ikun da suke Sama ake.

31 Game da tashin matattu, ashe, ba ku taɓa karanta abin da Allah ya ce muku ba? cewa,

32 ‘Ni ne Allahn Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.’ Ai, waɗanda Allah shi ne Allahnsu rayayyu ne, ba matattu ba.”

33 Da jama’a suka ji haka, sai suka yi mamakin koyarwarsa.

Umarni Mafi Girma

34 Amma da Farisiyawa suka ji ya ƙure Sadukiyawa, suka taru.

35 Ɗaya daga cikinsu, wani masanin Attaura, ya yi masa tambaya, yana gwada shi, ya ce,

36 “Malam, wane umarni ne mafi girma a cikin Attaura?”

37 Ya ce masa, “Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan hankalinka.

38 Wannan shi ne babban umarni na farko.

39 Na biyu kuma kamarsa yake, ‘Ka ƙaunaci ɗan’uwanka kamar kanka.’

40 A kan umarnin nan biyu duk Attaura da koyarwar annabawa suka rataya.”

Tambaya a kan Ɗan Dawuda

41 Tun Farisiyawa suna tare gu ɗaya, sai Yesu ya yi musu tambaya,

42 ya ce, “Yaya kuka ɗauki Almasihu? Shi ɗan wane ne?” Sai suka ce masa, “Ɗan Dawuda ne.”

43 Ya ce musu, “To, yaya kuwa Dawuda, ta ikon Ruhu, ya ce da shi Ubangiji? Har ya ce,

44 ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina,

Zauna a damana,

Sai na ɗora ka a kan maƙiyanka.’

45 Tun da Dawuda ya kira shi Ubangiji ne, to, ƙaƙa zai zama ɗansa?”

46 Ba kuwa wanda ya iya tanka masa. Daga ran nan kuwa ba wanda ya yi ƙarfin halin sāke tambayarsa wani abu.

Categories
MAT

MAT 23

Yesu Ya Fallashi Malaman Attaura da Farisiyawa

1 Sa’an nan Yesu ya yi wa jama’a da almajiransa magana, ya ce,

2 “Malaman Attaura da Farisiyawa suka tsaya a matsayin Musa.

3 Don haka, sai ku kiyaye, ku kuma aikata duk abin da suka gaya muku, amma banda aikinsu. Don suna faɗa ne, ba aikatawa.

4 Sukan ɗaura kaya masu nauyi, masu wuyar ɗauka, su jibga wa mutane a kafaɗa. Amma su kansu ko tallafa musu da ɗan yatsa ba sa yi.

5 Duk ayyukansu suna yi ne don idon mutane, suna yin layunsu fantam-fantam, lafin rigunansu kuma har gwiwa.

6 Suna son mazaunan alfarma a wurin biki, da mafifitan mazaunai a majami’u,

7 a gaishe su a kasuwa, a kuma riƙa ce da su ‘Malam’.

8 Amma ku kam, kada a ce muku ‘Malam’, domin Malaminku ɗaya ne, ku duka kuwa ‘yan’uwa ne.

9 Kada ku kira kowa ‘Uba’ a duniya, domin Uba ɗaya ne yake gare ku, wanda yake cikin Sama.

10 Kada kuma a kira ku ‘Shugabanni’, domin Shugaba ɗaya gare ku, wato, Almasihu.

11 Amma wanda yake babba a cikinku shi zai zama baranku.

12 Duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Mai ƙasƙantar da kansa kuma, ɗaukaka shi za a yi.

13 “Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kun toshe wa mutane ƙofar Mulkin Sama. Ku kanku ba ku shiga ba, kuna kuwa hana masu niyyar shiga shiga. [

14 Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan ci kayan matan da mazansu sun mutu, kukan yi doguwar addu’a don ɓad da sawu. Saboda haka za a yi muku hukunci mafi tsanani.]

15 Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan kewaye ƙasashe da tekuna don samun almajiri ɗaya tak, in kuwa kun samu, kukan mai da shi ɗan wuta fiye da ku, ninkin ba ninkin.

16 “Kaitonku, makafin jagora, ku da kuke cewa, ‘Kowa ya rantse da Haikalin ba kome, amma duk wanda ya rantse da zinariyar Haikalin, sai rantsuwarsa ta kama shi.’

17 Ku makafi, wawaye! Wanne ya fi girma, zinariyar ce ko kuwa Haikalin da yake tsarkake zinariyar?

18 Kukan ce, ‘Kowa ya rantse da bagaden hadaya, ba kome. Amma duk wanda ya rantse da sadakar da aka ɗora a kai, sai rantsuwarsa ta kama shi.’

19 Ku makafi! Wanne ya fi girma, sadakar ko kuwa bagaden hadaya da yake tsarkake sadakar?

20 Don haka kowa ya rantse da bagaden hadaya, ya rantse ke nan da shi, da duk abin da yake a kansa.

21 Duk kuma wanda ya rantse da Haikalin ya rantse da shi, da kuma wanda yake zaune a cikinsa.

22 Kowa kuma ya rantse da Sama, ya rantse da kursiyin Allah, da kuma wanda yake zaune a kansa.

23 “Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan fitar da zakkar na’ana’a, da anise, da lafsur, amma kun yar da muhimman jigajigan Attaura, wato, gaskiya, da jinƙai, da aminci. Waɗannan ne ya kamata ku yi, ba tare da yar da sauran ba.

24 Makafin jagora, kukan tace ƙwaro ɗan mitsil, amma kukan haɗiye raƙumi!

25 “Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan wanke bayan ƙwarya da akushi, amma a ciki cike suke da zalunci da zari.

26 Kai makahon Bafarisiye! Sai ka fara tsarkake cikin ƙwaryar da akushin don bayansu ma ya tsarkaka.

27 “Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kamar kaburburan da aka shafa wa farar ƙasa kuke, masu kyan gani daga waje, daga ciki kuwa sai ƙasusuwan matattu da ƙazanta iri iri.

28 Haka nan a idon mutane ku adalai ne, amma ciki sai munafunci da mugun aiki.

29 “Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan yi gini a kan kaburburan annabawa, kuna ƙawata gubbobin adalai.

30 Kuna cewa, ‘Da mun zauna a zamanin kakanninmu, da ba mu taya su zub da jinin annabawa ba.’

31 Ta haka kuka shaidi kanku ku ne ‘ya’yan masu kisan annabawa.

32 To, sai ku cikasa ayyukan kakanninku!

33 Ku macizai! Yaya za ku tsere wa hukuncin Gidan Wuta?

34 Saboda haka nake aiko muku da annabawa, da masu hikima, da masanan Attaura, za ku kashe waɗansunsu, ku gicciye waɗansu, ku kuma yi wa waɗansu bulala a majami’unku, kuna binsu gari gari kuna gwada musu azaba.

35 Don alhakin jinin dukan adalai da aka zubar a duniya yă komo a kanku, tun daga jinin Habila adali, har ya zuwa na Zakariya ɗan Berikiya, wanda kuka kashe a tsakanin Haikalin da bagaden hadaya.

36 Hakika, ina gaya muku, duk wannan zai auko wa mutanen wannan zamani.”

Yesu Ya Ji Juyayin Urushalima

37 “Ya mutanen Urushalima! Ya mutanen Urushalima! Masu kisan annabawa, masu jifan waɗanda aka aiko a gare ku! Sau nawa ne na so in tattaro ku kamar yadda kaza take tattara ‘yan tsakinta cikin fikafikanta, amma kun ƙi!

38 Ga shi, an bar muku gidanku a yashe!

39 Ina dai gaya muku, ba za ku ƙara ganina ba, sai ran da kuka ce, ‘Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji.’ ”

Categories
MAT

MAT 24

Yesu Ya Faɗi Irin Rushewar da Za ta Sami Haikalin

1 Yesu ya fita Haikalin, yana cikin tafiya, sai almajiransa suka zo suka nuna masa gine-ginen Haikalin.

2 Amma ya amsa musu ya ce, “Kun ga duk waɗannan ko? Hakika, ina gaya muku, ba wani dutsen da za a bari nan a kan ɗan’uwansa ba a baje shi ba.”

Farkon Azaba

3 Yana zaune a kan Dutsen Zaitun sai almajiransa suka zo wurinsa a kaɗaice, suka ce, “Gaya mana, yaushe za a yi waɗannan abubuwa? Mece ce kuma alamar dawowarka, da ta ƙarewar zamani?”

4 Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku kula fa kada kowa ya ɓad da ku,

5 domin mutane da yawa za su zo da sunana, suna cewa, su ne Almasihu, har su ɓad da mutane da yawa.

6 Za ku kuma riƙa jin labarin yaƙe-yaƙe da jitajitarsu. Kada fa hankalinku ya tashi, don lalle ne a yi haka, amma ƙarshen tukuna.

7 Al’umma za ta tasar wa al’umma, mulki ya tasar wa mulki. Za a kuma yi yunwa da raurawar ƙasa a wurare dabam dabam.

8 Amma fa duk wannan masomin azaba ne tukuna.

9 “Sa’an nan za su bashe ku, a ƙuntata muku, su kuma kashe ku. Duk al’ummai za su ƙi ku saboda sunana.

10 A sa’an nan da yawa za su yi tuntuɓe, su ci amanar juna, su kuma ƙi juna.

11 Annabawan ƙarya da yawa za su firfito, su ɓad da mutane da yawa.

12 Saboda kuma yaɗuwar mugun aiki, sai ƙaunar yawancin mutane ta yi sanyi.

13 Amma duk wanda ya jure har ƙarshe, zai cetu.

14 Za a kuma yi bisharar nan ta Mulkin Sama ko’ina a duniya domin shaida ga dukkan al’ummai. Sa’an nan kuma sai ƙarshen ya zo.”

Matsananciyar Wahala

15 “Don haka sa’ad da kuka ga mummunan aikin saɓo mai banƙyama, wanda Annabi Daniyel ya faɗa, an tsai da shi a Wuri Mai Tsarki (mai karatu fa yă fahimta),

16 to, sai waɗanda suke ƙasar Yahudiya su gudu su shiga duwatsu.

17 Wanda yake soro, kada ya sauko garin ɗaukar wanda yake a gidansa.

18 Wanda yake a gona kuma, kada ya koma garin ɗaukar mayafinsa.

19 Kaiton masu juna biyu da masu goyo a wannan lokaci!

20 Ku yi addu’a kada gudunku ya zo da damuna, ko ran Asabar.

21 A lokacin nan za a yi wata matsananciyar wahala, irin wadda ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har ya zuwa yanzu, ba kuwa za a ƙara yi ba har abada.

22 Ba don an taƙaita kwanakin nan ba, da ba ɗan adam ɗin da zai tsira. Amma sabili da zaɓaɓɓun nan za a taƙaita kwanakin.

23 A sa’an nan kowa ya ce muku, ‘Kun ga, ga Almasihu nan!’ ko, ‘Ga shi can!’ kada ku yarda.

24 Don almasihan ƙarya da annabawan ƙarya za su firfito, su nuna manyan alamu da abubuwan al’ajabi, don su ɓad da ko da zaɓaɓɓu ma in dai zai yiwu.

25 To, na dai gaya muku tun da wuri.

26 Saboda haka in sun ce da ku, ‘Ga shi can a jeji,’ kada ku fita. In kuwa sun ce, ‘Yana can cikin lolloki,’ kada ku yarda.

27 Kamar yadda walƙiya take wulgawa walai daga gabas zuwa yamma, haka komowar Ɗan Mutum za ta zama.

28 Inda mushe yake, ai, a nan ungulai sukan taru.

Komowar Ɗan Mutum

29 “Bayan tsabar wahalar nan, nan da nan sai a duhunta rana, wata kuma ba zai yi haske ba. Taurari kuma za su farfaɗo daga sararin sama, za a kuma girgiza manyan abubuwan da suke sararin sama.

30 A sa’an nan ne alamar Ɗan Mutum za ta bayyana a sararin sama, duk kabilan duniya kuma za su yi kuka, za su ga Ɗan Mutum yana zuwa kan gajimare, da iko da ɗaukaka mai yawa.

31 Zai kuwa aiko mala’ikunsa su busa ƙaho mai tsananin ƙara, su kuma tattaro zaɓaɓɓunsa daga gabas da yamma, kudu da arewa, wato, daga wannan bangon duniya zuwa wancan.”

Aya a kan Itacen Ɓaure

32 “Ku yi koyi da itacen ɓaure. Da zarar rassansa sun fara sakuwa, suna toho, kun san damuna ta yi kusa ke nan.

33 Haka kuma in kun ga duk waɗannan abubuwa, ku sani ya kusato, a bakin ƙofa ma yake.

34 Hakika, ina gaya muku, zamanin nan ba zai shuɗe ba sai duk abubuwan nan sun auku.

35 Sararin sama da kasa za su shuɗe, amma maganata ba za ta shuɗe ba.”

Ba Wanda Ya San Ranar ko Sa’ar

36 “Amma fa wannan rana da wannan sa’a ba wanda ya sani, ko mala’ikun da yake Sama, ko Ɗan, sai dai Uban kaɗai.

37 Kamar yadda aka yi a zamanin Nuhu, haka dawowar Ɗan Mutum za ta zama.

38 Kamar a kwanakin nan ne gabannin Ruwan Tsufana, ana ci, ana sha, ana aure, ana aurarwa, har ya zuwa ranar da Nuhu ya shiga jirgi,

39 ba su farga ba har Ruwan Tsufana ya zo ya share su. Haka komowar Ɗan Mutum za ta zama.

40 A sa’an nan za a ga mutum biyu a gona, a ɗau ɗaya, a bar ɗaya.

41 Za a ga mata biyu suna niƙa, a ɗau ɗaya, a bar ɗaya.

42 To, ku zauna a faɗake fa, don ba ku san ranar da Ubangijinku zai dawo ba.

43 Amma dai ku sani, da maigida zai san ko a wane lokaci ne da dare ɓarawo zai zo, da ya zauna a faɗake ya hana a shigar masa gida.

44 Don haka ku ma sai ku zauna a kan shiri, domin a lokacin da ba ku zata ba, Ɗan Mutum zai zo.”

Amintaccen Bawa ko Marar Aminci

45 “Wane ne amintaccen bawan nan mai hikima, da ubangidansa ya ba shi riƙon gidansa, yă riƙa ba su abincinsu a kan kari?

46 Albarka tā tabbata ga bawan da in ubangidansa ya dawo zai samu yana yin haka.

47 Hakika, ina gaya muku, sai ya ɗora shi a kan dukan mallakarsa.

48 Amma in bawan nan mugu ne, ya kuma ce a ransa, ‘Ubangidana ya jinkirta zuwansa,’

49 sa’an nan ya soma dūkan abokan bautarsa, yana ci yana sha tare da mashaya,

50 ai, ubangidan wannan bawa zai zo a ranar da bai zata ba, a kuma lokacin da bai sani ba,

51 yă farfasa masa jiki da bulala, ya ba shi rabonsa tare da munafukai. Nan za a yi kuka da cizon baki.”

Categories
MAT

MAT 25

Misali na Budurwai Goma

1 “Sa’an nan za a kwatanta Mulkin Sama da ‘yan mata goma da suka ɗauki fitilunsu suka tafi taryen ango.

2 Biyar daga cikinsu wawaye ne, biyar kuwa masu hikima.

3 Don kuwa a lokacin da wawayen nan suka ɗauki fitilunsu, ashe, ba su riƙo mai ba.

4 Masu hikimar nan kuwa sun riƙo kwalaben mai da fitilunsu.

5 Da yake angon ya yi jinkiri, duk sai suka yi gyangyaɗi, har barci ya share su.

6 Can tsakar dare sai aka ji kira, ana cewa, ‘Ga ango nan! Ku fito ku tarye shi!’

7 Duk ‘yan matan nan suka tashi suka gyaggyara fitilunsu.

8 Sai wawayen nan suka ce wa masu hikimar, ‘Ku sa mana ɗan manku kaɗan mana, fitilunmu na mutuwa!’

9 Amma masu hikimar suka amsa suka ce, ‘Ai, watakila ba zai ishe mu mu da ku ba. Gara ku je wurin masu sayarwa ku sayo.’

10 Tun suna wajen sayen, sai angon ya iso, waɗanda suke shirye suka shiga wurin biki tare da shi, aka kuma rufe ƙofa.

11 Daga baya sai waɗancan ‘yan matan ma suka iso, suka ce, ‘Ya Ubangiji, ya Ubangiji, ka buɗe mana!’

12 Sai ya amsa ya ce, ‘Hakika, ina gaya muku, ni ban san ku ba.’

13 Don haka, sai ku zauna a faɗake, don ba ku san ranar ba, ko kuwa sa’ar.”

Misali na Talanti

14 “Kamar mutum ne da zai yi tafiya, ya kira bayinsa, ya danƙa musu dukiyarsa.

15 Ya ba ɗaya talanti biyar, ɗaya talanti biyu, wani kuma ya ba shi ɗaya, kowa dai gwargwadon ƙarfinsa. Sa’an nan ya tafi.

16 Shi wanda ya karɓi talanti biyar ɗin nan, nan da nan sai ya je ya yi ta jujjuya su, har wuri ya bugi wuri.

17 Haka kuma wanda ya karɓi talanti biyu, shi ma sai wuri ya bugi wuri.

18 Amma wannan da ya karɓi talanti ɗaya ɗin, sai ya je ya tona rami ya ɓoye kuɗin ubangijinsa.

19 To, da aka daɗe sai ubangijin bayin nan ya dawo ya daidaita lissafi da su.

20 Shi wannan da ya karɓi talanti biyar sai ya matso ya kawo waɗansu talanti biyar, ya ce, ‘Ya ubangiji, kā ba ni talanti biyar, ga shi kuma, na ci ribar biyar.’

21 Sai ubangijinsa ya ce masa, ‘Madalla, bawan kirki, mai aminci. Kā yi gaskiya a kan ƙaramin abu, zan ɗora ka a kan mai yawa. Ka zo ku yi farin ciki tare da ubangidanka.’

22 Sai mai talanti biyun nan kuma ya matso, ya ce, ‘Ya ubangiji, kā ba ni talanti biyu, ga shi kuma, na ci ribar biyu.’

23 Sai ubangijinsa ya ce masa, ‘Madalla, bawan kirki, mai aminci. Kā yi gaskiya a kan ƙaramin abu, zan ɗora ka a kan mai yawa. Ka zo ku yi farin ciki tare da ubangijinka.’

24 Shi kuma wanda ya karɓi talanti guda ɗin, sai ya matso, ya ce, ‘Ya ubangiji, na sani kai mutum ne mai tsanani, kana son girbi inda ba kai ka shuka ba, mai son banza ne.

25 Shi ya sa na ji tsoro, har na je na yi tono na ɓoye talantinka. To, ga kayanka nan!’

26 Sai ubangijinsa ya amsa masa ya ce, ‘Kai mugun bawa, malalaci! Ashe, ka sani ina girbi inda ba ni na shuka ba, ni kuma mai son banza ne?

27 Ya kamata ka sa kuɗina a ma’aji, da na dawo kuma da sai in karɓi abina har da riba!

28 Don haka sai ku karɓe talantin daga gunsa, ku bai wa mai goman nan.

29 Don duk mai abu a kan ƙara wa, har ya yalwata. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da yake da shi ma, sai an karɓe masa.

30 Ku kuma jefa banzan bawan nan a baƙin duhu. Nan za a yi kuka da cizon baki.’ ”

Shara’anta wa Al’ummai

31 “Sa’ad da Ɗan Mutum ya zo cikin ɗaukakarsa tare da mala’iku duka, sa’an nan ne zai zauna a maɗaukakin kursiyinsa.

32 Za a tara dukan al’ummai a gabansa, zai kuma ware su dabam dabam, kamar yadda makiyayi yake ware tumaki da awaki.

33 Zai sa tumaki a damansa, awaki kuwa a hagunsa.

34 Sa’an nan ne Sarki zai ce wa waɗanda suke dama da shi, ‘Ku zo, ya ku da Ubana ya yi wa albarka, sai ku gāji mulkin da aka tanadar muku tun daga farkon duniya.

35 Domin na ji yunwa, kun ba ni abinci. Na ji ƙishirwa, kun ba ni na sha. Na yi baƙunci, kun saukar da ni.

36 Na yi huntanci, kun tufasar da ni. Na yi rashin lafiya, kun ziyarce ni. Ina kurkuku, kun kula da ni.’

37 Sa’an nan ne masu adalci za su amsa masa su ce, ‘Ya Ubangiji, a yaushe muka gan ka da yunwa muka cishe ka, ko kuwa da ƙishirwa muka shayar da kai?

38 A yaushe kuma muka gan ka baƙo muka sauke ka, ko kuwa huntu muka tufasar da kai?

39 Ko kuma a yaushe muka gan ka da rashin lafiya, ko a kurkuku muka kula da kai?’

40 Sai Sarkin zai amsa musu ya ce, ‘Hakika, ina gaya muku, tun da yake kun yi wa ɗaya daga cikin waɗannan ‘yan’uwana mafi ƙanƙanta, ai, ni kuka yi wa.’

41 Sa’an nan zai ce wa waɗanda suke na hagun, ‘Ku rabu da ni, la’anannu, ku shiga madawwamiyar wuta, wadda aka tanadar wa Iblis da mala’ikunsa.

42 Don na ji yunwa, ba ku ba ni abinci ba. Na ji ƙishirwa, ba ku ba ni abin sha ba.

43 Na yi baƙunci, ba ku sauke ni ba. Na yi huntanci, ba ku tufasar da ni ba. Na yi rashin lafiya, ina kuma kurkuku, ba ku kula da ni ba.’

44 Sa’an nan su ma za su amsa su ce, ‘Ya Ubangiji, a yaushe muka gan ka da yunwa, ko da ƙishirwa, ko da baƙunci, ko da huntanci, ko da rashin lafiya, ko a kurkuku, ba mu kula da kai ba?’

45 Sa’an nan zai amsa musu ya ce, ‘Hakika, ina gaya muku, tun da yake ba ku yi wa ɗaya daga cikin waɗannan mafi ƙanƙanta ba, ai, ni ne ba ku yi mini ba.’

46 Waɗannan ne za su shiga madawwamiyar azaba, masu adalci kuwa rai madawwami.”

Categories
MAT

MAT 26

Shugabanni Sun Ƙulla Shawara Gaba da Yesu

1 Da Yesu ya gama duk wannan magana, sai ya ce wa almajiransa,

2 “Kun san Idin Ƙetarewa saura kwana biyu, za a kuma ba da Ɗan Mutum a gicciye shi.”

3 Sai manyan firistoci da shugabannin jama’a suka taru a gidan babban firist, mai suna Kayafa.

4 Suka ƙulla shawara su kama Yesu da makirci su kashe shi.

5 Amma suka ce, “Ba dai a lokacin idi ba, don kada jama’a su yi hargitsi.”

An Shafi Yesu da Man Ƙanshi a Betanya

6 To, sa’ad da Yesu yake Betanya a gidan Saminu kuturu,

7 sai wata mace ta zo wurinsa da wani ɗan tandu na man ƙanshi mai tsadar gaske, ta tsiyaye masa a kā, a lokacin da yake cin abinci.

8 Amma da almajiran suka ga haka, sai suka ji haushi suka ce, “Wannan almubazzaranci fa!

9 Da ma an sayar da man nan kuɗi mai yawa, an ba gajiyayyu!”

10 Yesu kuwa da ya lura da haka, sai ya ce musu, “Don me kuke damun matar nan? Ai, alheri ta yi mini, na gaske kuwa.

11 Kullum kuna tare da talakawa, amma ba kullum ne kuke tare da ni ba.

12 Zuba man nan da ta yi a jikina, ta yi shi ne domin tanadin jana’izata.

13 Hakika, ina gaya muku, duk inda za a yi bisharar nan a duniya duka, abin da matar nan ta yi za a riƙa faɗarsa don tunawa da ita.”

Yahuza Ya Yarda Ya Ba Da Yesu

14 Sai ɗaya daga cikin sha biyun nan, mai suna Yahuza Iskariyoti, ya je wurin manyan firistoci,

15 ya ce, “Me za ku ba ni, in na bashe shi a gare ku?” Sai suka ƙirga kuɗi azurfa talatin, suka ba shi.

16 Tun daga lokacin nan ne ya riƙa neman hanyar da zai bashe shi.

Yesu Ya Ci Idin Ƙetarewa tare da Almajiransa

17 To, a ranar farko ta idin abinci marar yisti sai almajiran suka zo wurin Yesu suka ce, “Ina kake so mu shirya maka cin Idin Ƙetarewa?”

18 Sai ya ce, “Ku shiga gari wurin wāne, ku ce masa, ‘Malam ya ce lokacinsa ya yi kusa, zai ci Idin Ƙetarewa a gidanka tare da almajiransa.’ ”

19 Almajiran kuwa suka yi yadda Yesu ya umarce su, suka shirya Idin Ƙetarewa.

20 Da magariba ta yi, sai ya zauna cin abinci tare da almajiran nan goma sha biyu.

21 Suna cikin cin abinci, sai ya ce, “Hakika, ina gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.”

22 Sai suka yi baƙin ciki gaya, suka fara ce masa da ɗaya ɗaya, “Ni ne, ya Ubangiji?”

23 Sai ya amsa ya ce, “Wanda muke ci a ƙwarya ɗaya, shi ne zai bashe ni.

24 Ɗan Mutum zai tafi ne, yadda labarinsa yake a rubuce, duk da haka kaiton mutumin nan da yake ba da Ɗan Mutum! Da ma ba a haifi mutumin nan ba, da zai fiye masa.”

25 Sai Yahuza da ya bashe shi ya ce, “Ko ni ne, ya Shugaba?” Yesu ya ce masa, “Ga shi, kai ma ka faɗa.”

Cin Jibin Ubangiji

26 Suna cikin cin abinci, sai Yesu ya ɗauki gurasa, ya yi godiya ga Allah, ya gutsuttsura, ya ba almajiran, ya ce, “Ungo, ku ci. Wannan jikina ne.”

27 Sai ya ɗauki ƙoƙo bayan ya kuma yi godiya ga Allah, sai ya ba su, ya ce, “Dukkanku ku shassha.

28 Wannan jinina ne na tabbatar alkawari, wanda za a zubar saboda mutane da yawa, domin gafarar zunubansu.

29 Ina gaya muku, ba zan ƙara shan ruwan inabi ba, sai dai a ranar nan da za mu sha wani sabo tare da ku a Mulkin Ubana.”

30 Da suka yi waƙar yabon Allah, sai suka fita suka tafi Dutsen Zaitun.

Bitrus Zai Yi Musun Sanin Yesu

31 Sai Yesu ya ce musu, “Duk za ku yi tuntuɓe sabili da ni a wannan dare domin a rubuce yake cewa, ‘Zan bugi makiyayi, tumakin garken kuwa za su fasu.’

32 Amma fa bayan an tashe ni, zan riga ku zuwa ƙasar Galili.”

33 Bitrus ya ce masa, “Ko duk sun yi tuntuɓe sabili da kai, ni kam ba zan yi tuntuɓe ba faufau.”

34 Yesu ya ce masa, “Hakika, ina gaya maka, ko a wannan dare, kafin carar zakara, za ka yi musun sanina sau uku.”

35 Bitrus ya ce masa, “Ko za a kashe ni tare da kai, ba zan yi musun saninka ba.” Haka ma duk almajiran suka ce.

Yesu ya Yi Addu’a a Gatsemani

36 Sa’an nan Yesu ya zo da su wani wuri da ake kira Gatsemani. Ya ce wa almajiransa, “Ku zauna a nan, Ni kuwa zan je can in yi addu’a.”

37 Sai ya ɗauki Bitrus da ‘ya’yan nan na Zabadi biyu, ya fara baƙin ciki da damuwa ƙwarai.

38 Sai ya ce musu, “Raina yana shan wahala matuƙa, har ma kamar in mutu. Ku dakata a nan, ku zauna a faɗake tare da ni.”

39 Da ya ci gaba kaɗan, sai ya fāɗi a ƙasa, ya yi addu’a ya ce, “Ya Ubana, in mai yiwuwa ne, ka ɗauke mini ƙoƙon wahalar nan. Duk da haka dai ba nufina ba, sai naka.”

40 Ya komo wurin almajiran, ya ga suna barci, sai ya ce wa Bitrus, “Ashe, ba za ku iya zama a faɗake tare da ni ko da na sa’a ɗaya ba?

41 Ku zauna a faɗake, ku yi addu’a, kada ku faɗa ga gwaji. Lalle ruhu ya ɗauka, amma jiki rarrauna ne.”

42 Har wa yau a komawa ta biyu, sai ya je ya yi addu’a, ya ce, “Ya Ubana, in wannan ba zai wuce ba sai na sha shi, to, a aikata nufinka.”

43 Har yanzu dai ya dawo ya ga suna barci, don duk barci ya cika musu ido.

44 Har wa yau ya sāke barinsu, ya koma ya yi addu’a ta uku, yana maimaita maganar dā.

45 Sai ya komo wurin almajiran, ya ce musu, “Har yanzu barci kuke yi, kuna hutawa? To, ga shi, lokaci ya yi kusa. An ba da Ɗan Mutum ga masu zunubi.

46 Ku tashi mu tafi. Kun ga, ga mai bashe ni nan, ya matso!”

An Ba da Yesu, an Kama Shi

47 Kafin ya rufe baki ga Yahuza, ɗaya daga cikin sha biyun nan, da babban taron mutane riƙe da takuba da kulake, manyan firistoci da shugabanni ne suka turo su.

48 To, mai bashe shi ɗin ya riga ya ƙulla da su cewa, “Wanda zan yi wa sumba, shi ne mutumin. Ku kama shi.”

49 Nan da nan ya matso wurin Yesu, ya ce, “Salama alaikun, ya Shugaba!” Sai ya yi ta sumbantarsa.

50 Yesu ya ce masa, “Abokina, abin da ya kawo ka ke nan?” Suka matso suka ɗanke Yesu, suka kama shi.

51 Sai ga ɗaya daga cikin waɗanda suke tare da Yesu ya miƙa hannu ya zaro takobinsa, ya kai wa bawan babban firist sara, ya ɗauke masa kunne.

52 Sai Yesu ya ce masa, “Mai da takobinka kube. Duk wanda ya zare takobi, takobi ne ajalinsa.

53 Kuna tsammani ba ni da ikon neman taimako gun Ubana ba, nan da nan kuwa ya aiko mini fiye da rundunar mala’iku goma sha biyu?

54 To, ta yaya ke nan za a cika Littattafai a kan lalle wannan abu ya kasance?”

55 Nan take Yesu ya ce wa taron jama’a, “Kun fito ne da takuba da kulake ku kama ni kamar ɗan fashi? Kowace rana nakan zauna a Haikali ina koyarwa, amma ba ku kama ni ba.

56 Amma duk wannan ya auku ne domin a cika littattafan annabawa.” Daga nan duk almajiran suka yashe shi, suka yi ta kansu.

Yesu a Gaban ‘Yan Majalisa

57 Sai waɗanda suka kama Yesu suka tafi da shi wurin Kayafa, babban firist, inda malaman Attaura da shugabanni suke tare.

58 Amma Bitrus ya bi shi daga nesa, har cikin gidan babban firist. Da ya shiga, sai ya zauna tare da dogaran Haikali, don ya ga ƙarshen abin.

59 To, sai manyan firistoci da ‘yan majalisa duka suka nemi shaidar zur da za a yi wa Yesu don su sami dama su kashe shi.

60 Amma ba su samu ba, ko da yake masu shaidar zur da yawa sun zazzaburo. Daga baya sai waɗansu biyu suka matso,

61 suka ce, “Wannan ya ce, wai zai iya rushe Haikalin nan na Allah, ya kuma gina shi a cikin kwana uku.”

62 Sai babban firist ya miƙe ya ce, “Ba ka da wata amsa? Shaidar da mutanen nan suke yi a kanka fa?”

63 Amma Yesu na shiru. Sai babban firist ya ce masa, “Na gama ka da Allah Rayayye, ka faɗa mana ko kai ne Almasihu, Ɗan Allah.”

64 Sai Yesu ya ce masa, “Yadda ka faɗa. Ina kuwa gaya muku a nan gaba za ku ga Ɗan Mutum zaune a dama da Mai Iko, yana kuma zuwa a kan gajimare.”

65 Sai babban firist ya kyakketa tufafinsa, ya ce, “Ya yi saɓo! Wace shaida kuma za mu nema? Yanzu kun ji saɓon da ya yi!

66 Me kuka gani?” Suka amsa suka ce, “Ya cancanci kisa!”

67 Sai suka tattofa masa yau a fuska, suka bubbuge shi, waɗansu kuma suka mammare shi,

68 suna cewa, “Yi mana annabci, kai Almasihu! Faɗi wanda ya buge ka!”

Bitrus Ya Yi Musun Sanin Yesu

69 To, Bitrus kuwa yana zaune a tsakar gida a waje, sai wata baranya ta zo ta tsaya a kansa, ta ce, “Kai ma, ai, tare kake da Yesu Bagalile!”

70 Amma ya musa a gabansu duka ya ce, “Ni ban san abin da kike nufi ba.”

71 Da ya fito zaure, sai wata baranya kuma ta gan shi, ta ce wa waɗanda suke tsaitsaye a wurin, “Ai, mutumin nan tare yake da Yesu Banazare!”

72 Sai ya sāke musawa har da rantsuwa ya ce, “Ban ma san mutumin nan ba.”

73 Jim kaɗan sai na tsaitsayen suka matso, suka ce wa Bitrus, “Lalle kai ma ɗayansu ne, don irin maganarka ta tona ka.”

74 Sai ya fara la’anar kansa, yana ta rantse-rantse, yana cewa, “Ban ma san mutumin nan ba.” Nan da nan sai zakara ya yi cara.

75 Sai Bitrus ya tuna da maganar Yesu cewa, “Kafin carar zakara za ka yi musun sanina sau uku.” Sai ya fita waje, ya yi ta rusa kuka.

Categories
MAT

MAT 27

Yesu a Gaban Bilatus

1 Da gari ya waye sai duk manyan firistoci da shugabannin jama’a suka yi shawara a kan Yesu su kashe shi.

2 Sai suka ɗaure shi, suka tafi da shi, suka ba da shi ga mai mulki Bilatus.

Mutuwar Yahuza

3 Sa’ad da Yahuza mai bashe shi ya ga an yanke masa hukuncin kisa, sai ya yi nadama, ya mayar wa manyan firistoci da shugabanni da kuɗi azurfa talatin ɗin nan,

4 ya ce, “Na yi zunubi da na ba da marar laifi a kashe shi.” Suka ce, “Ina ruwanmu? Kai ka jiyo!”

5 Sai ya watsar da kuɗin azurfan nan a Haikali, ya fita, ya je ya rataye kansa.

6 Amma manyan firistoci suka tsince kuɗin suka ce, “Bai halatta mu zuba su a Baitulmalin Haikali ba, don kuɗin ladan kisankai ne.”

7 Sai suka yi shawara, suka sayi filin maginin tukwane da kuɗin don makabartar baƙi.

8 Don haka, har ya zuwa yau, ana kiran filin nan filin jini.

9 Ta haka aka cika faɗar Annabi Irmiya cewa, “Sun ɗauki kuɗin azurfa talatin ɗin nan, wato, awalajar shi wannan da waɗansu Isra’ilawa suka yi wa kima,

10 suka sayi filin maginin tukwane da su, yadda Ubangiji ya umurce ni.”

Bilatus Ya Tuhumi Yesu

11 To, sai Yesu ya tsaya a gaban mai mulki, mai mulkin kuma ya tambaye shi, “Ashe, kai ɗin nan kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya ce masa, “Yadda ka faɗa.”

12 Amma da manyan firistoci da shugabanni suka kai ƙararrakinsa, bai ce kome ba.

13 Sai Bilatus ya ce masa, “Ba ka ji yawan maganganun da suke ba da shaida a kanka ba?”

14 Amma bai ba shi wata amsa, ko da ta kalma ɗaya ba, har mai mulki ya yi mamaki ƙwarai.

An Hukunta wa Yesu Mutuwa

15 To, a lokacin idi kuwa mai mulki ya saba sakar wa jama’a kowane ɗaurarre guda da suka so.

16 A lokacin kuwa da wani shahararren ɗan sarƙa, mai suna Barabbas.

17 Da suka taru sai Bilatus ya ce musu, “Wa kuke so in sakar muku? Barabbas ko kuwa Yesu da ake kira Almasihu?”

18 Don ya sani saboda hassada ne suka bashe shi.

19 Banda haka kuma, a lokacin da yake zaune a kan gadon shari’a, sai mata tasa ta aiko masa da cewa, “Ka fita daga sha’anin mara laifin nan, don yau na sha wahala ƙwarai a mafarkinsa.”

20 To, sai manyan firistoci da shugabanni suka rarrashi jama’a su zaɓi Barabbas, Yesu kuwa a kashe shi.

21 Sai mai mulki ya sāke ce musu, “Wane ne a cikin biyun nan kuke so in sakar muku?” Sai suka ce, “Barabbas.”

22 Bilatus ya ce musu, “To, ƙaƙa zan yi da Yesu da ake kira Almasihu?” Duk sai suka ce, “A gicciye shi!”

23 Ya ce, “Ta wane halin? Wane mugun abu ya yi?” Amma su sai ƙara ɗaga murya suke ta yi, suna cewa, “A gicciye shi!”

24 Da Bilatus ya ga bai rinjaye su ba, sai dai hargitsi yana shirin tashi, sai ya ɗibi ruwa ya wanke hannunsa a gaban jama’a, ya ce, “Ni kam, na kuɓuta daga alhakin jinin mai adalcin nan. Wannan ruwanku ne.”

25 Sai duk jama’a suka amsa suka ce, “Alhakin jininsa a wuyanmu, mu da ‘ya’yanmu!”

26 Sa’an nan ya sakar musu Barabbas. Bayan ya yi wa Yesu bulala, sai ya ba da shi a gicciye shi.

Sojoji Sun Yi wa Yesu Ba’a

27 Sai sojan mai mulki suka kai Yesu cikin fadar mai mulki, suka tara dukan ƙungiyar soja a kansa.

28 Sai suka tuɓe shi, suka yafa masa wata jar alkyabba.

29 Suka yi wani rawani na ƙaya, suka sa masa a kā, suka danƙa masa sanda a hannunsa na dama, suka kuma durƙusa a gabansa, suna yi masa ba’a suna cewa, “Ranka ya daɗe, Sarkin Yahudawa!”

30 Suka tattofa masa yau, suka karɓe sandan, suka ƙwala masa a ka.

31 Da suka gama yi masa ba’a, sai suka yaye masa alkyabbar, suka sa masa nasa tufafi, suka tafi da shi su gicciye shi.

An Gicciye Yesu

32 Suna tafiya ke nan, sai suka gamu da wani Bakurane, mai suna Saminu. Shi ne suka tilasta wa ya ɗauki gicciyen Yesu.

33 Da suka isa wurin da ake kira Golgota, wato, wurin ƙoƙwan kai,

34 suka miƙa masa ruwan inabi gauraye da wani abu mai ɗaci yă sha, amma da ya ɗanɗana sai ya ƙi sha.

35 Da suka gicciye shi, suka rarraba tufafinsa a junansu ta jefa kuri’a.

36 Suka zauna a nan suna tsaronsa.

37 A daidai kansa aka kafa sanarwar laifinsa cewa, “Wannan shi ne Yesu, Sarkin Yahudawa.”

38 Sai kuma aka gicciye ‘yan fashi biyu tare da shi, ɗaya a dama, ɗaya a hagun.

39 Masu wucewa suka yi ta yi masa baƙar magana, suna kaɗa kai,

40 suna cewa, “Kai da za ka rushe Haikalin, ka kuma gina shi a cikin kwana uku, ceci kanka mana! In kai Ɗan Allah ne, to sauko daga gicciyen mana!”

41 Haka kuma manyan firistoci da malaman Attaura da shugabanni suka riƙa yi masa ba’a, suna cewa,

42 “Ya ceci waɗansu, ya kuwa kasa ceton kansa. Ai, Sarkin Isra’ila ne, yă sauko mana daga gicciyen yanzu, mu kuwa mā gaskata da shi.

43 Yā dogara ga Allah, to, Allah ya cece shi mana yanzu, in dai yana sonsa, don ya ce wai shi Ɗan Allah ne.”

44 Har ‘yan fashin nan da aka gicciye su tare ma, su suka zazzage shi kamar waɗancan.

Mutuwar Yesu

45 To, tun daga tsakar rana, duhu ya rufe ƙasa duka, har zuwa ƙarfe uku na yamma.

46 Wajen ƙarfe uku kuma sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktāni?” Wato, “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?”

47 Da waɗansu na tsaitsayen suka ji haka, sai suka ce, “Mutumin nan na kiran Iliya ne.”

48 Sai nan da nan ɗaya daga cikinsu ya yiwo gudu, ya ɗauko soso ya jiƙa shi da ruwan tsami, ya soka a sanda, ya miƙa masa yă sha.

49 Amma sauran suka ce, “Ku bari mu gani ko Iliya zai zo ya ceci shi.”

50 Sai Yesu ya sāke ɗaga murya da ƙarfi, sa’an nan ya săki ransa.

51 Sai labulen da yake cikin Haikalin ya tsage gida biyu, daga sama har ƙasa. Ƙasa ta yi girgiza, duwatsu kuma suka tsattsage.

52 Aka bubbuɗe kaburbura, tsarkaka da yawa da suke barci kuma suka tashi.

53 Suka firfito daga kaburburan, bayan ya tashi daga matattu, sai suka shiga tsattsarkan birnin, suka bayyana ga mutane da yawa.

54 Sa’ad da jarumin da waɗanda suke tare da shi suna tsaron Yesu suka ga rawar ƙasa da kuma abin da ya auku, sai duk tsoro ya kama su, suka ce, “Hakika wannan Ɗan Allah ne!”

55 Akwai kuma waɗansu mata da yawa a can suna hange daga nesa, waɗanda suka biyo Yesu tun daga ƙasar Galili, suna yi masa hidima.

56 A cikinsu da Maryamu Magadaliya, da Maryamu uwar Yakubu da Yusufu, da kuma uwar ‘ya’yan Zabadi.

Jana’izar Yesu

57 Maraice lis sai wani mai arziki ya zo, mutumin Arimatiya, mai suna Yusufu, shi ma almajirin Yesu ne.

58 Ya je wurin Bilatus ya roƙa a ba shi jikin Yesu. Sai Bilatus ya yi umarni a ba shi.

59 Yusufu ya ɗauki jikin, ya sa shi a likkafanin lilin mai tsabta,

60 ya sa shi a wani sabon kabari da ya tanadar wa kansa, wanda ya fafe a jikin dutse. Sai ya mirgina wani babban dutse a bakin kabarin, ya tafi.

61 Maryamu Magadaliya da ɗaya Maryamun suna nan zaune a gaban kabarin.

Masu Tsaron Kabarin

62 Kashegari, wato, bayan ranar shiri, sai manyan firistoci da Farisiyawa suka taru a gaban Bilatus,

63 suka ce, “Ya mai girma, mun tuna yadda mayaudarin nan, tun yana da rai ya ce bayan kwana uku zai tashi daga matattu.

64 Saboda haka sai ka yi umarni a tsare kabarin nan sosai har rana ta uku, kada almajiransa su sace shi, sa’an nan su ce wa mutane wai ya tashi daga matattu. Yaudarar ƙarshe za ta fi ta farkon muni ke nan.”

65 Sai Bilatus ya ce musu, “Shi ke nan, ku ɗebi soja, ku je ku tsare shi iyakar ƙoƙarinku.

66 Sai suka tafi suka tsare kabarin, suka buga wa dutsen nan hatimi, suka kuma sa sojan tsaro.

Categories
MAT

MAT 28

Tashin Yesu daga Matattu

1 To, bayan Asabar, da asussuba a ranar farko ta mako, sai Maryamu Magadaliya da ɗaya Maryamun, suka je ganin kabarin.

2 Sai kuwa aka yi wata babbar rawar ƙasa, domin wani mala’ikan Ubangiji ne ya sauko daga Sama, ya zo ya mirgine dutsen, ya zauna a kai.

3 Kamanninsa suna haske kamar walƙiya, tufafinsa kuma farare fat kamar dusar ƙanƙara.

4 Saboda tsoronsa sai masu tsaro suka ɗau makyarkyata, har suka yi kamar sun mutu.

5 Amma sai mala’ikan ya ce wa matan, “Kada ku ji tsoro, domin na sani Yesu kuke nema, wanda aka gicciye.

6 Ai, ba ya nan. Ya tashi, yadda ya faɗa. Ku zo ku ga wurin da aka sa shi.

7 Ku tafi maza ku gaya wa almajiransa, cewa, ya tashi daga matattu. Ga shi kuma, zai riga ku zuwa ƙasar Galili, a can ne za ku gan shi. Ga shi, na gaya muku.”

8 Sai suka tashi daga kabarin da gaggawa da tsoro, game da matuƙar farin ciki, suka ruga a guje su kai wa almajiransa labari.

9 Sai kuwa ga Yesu ya tarye su, ya ce, “Salama alaikun!” Suka matso suka rungume ƙafafunsa, suka yi masa sujada.

10 Sai Yesu ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ku je ku gaya wa ‘yan’uwana su tafi ƙasar Galili, a can ne za su gan ni.”

Rahoton Masu Tsaron Kabarin

11 Suna tafiya ke nan, sai waɗansu daga cikin sojan nan suka shiga birni, suka ba manyan firistoci labarin da ya auku.

12 Su kuwa da suka taru da shugabannin jama’a suka yi shawara, sai suka ba sojan kuɗi masu tsoka,

13 suka ce, “Ku faɗa wa mutane almajiransa ne suka zo da daddare suka sace shi kuna barci.

14 In kuwa labarin nan ya kai ga kunnen mai mulki, mā rarrashe shi, mu tsare ku daga wahala.”

15 Sai suka karɓi kuɗin, suka yi yadda aka koya musu. Wannan magana kuwa, ta bazu cikin Yahudawa har ya zuwa yau.

Umarnin Yesu ga Goma Sha Ɗayan

16 To, almajirai goma sha ɗayan nan suka tafi ƙasar Galili, suka je dutsen da Yesu ya umarce su.

17 Da suka gan shi, suka yi masa sujada, amma waɗansu suka yi shakka.

18 Sai Yesu ya matso, ya ce musu, “An mallaka mini dukkan iko a Sama da ƙasa.

19 Don haka sai ku je ku almajirtar da dukkan al’ummai, kuna yi musu baftisma da sunan Uba, da Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki,

20 kuna koya musu su kiyaye duk iyakar abin da na umarce ku. Ga shi, ni kuma kullum ina tare da ku har zuwa matuƙar zamani.”