Categories
MIKA

MIKA 1

1 Ubangiji ya yi magana da Mika mutumin Moreshet a zamanin Yotam, da na Ahaz, da na Hezekiya, sarakunan Yahuza. Ya yi masa magana a kan Samariya da Urushalima.

Makoki don Samariya da Urushalima

2 Dukanku ku ji, ku al’ummai!

Ki kasa kunne, ya duniya, da dukan

abin da yake cikinki.

Bari Ubangiji Allah

Daga Haikalinsa mai tsarki ya zama

shaida a kanku.

3 Ga shi, Ubangiji yana fitowa daga

wurin zamansa,

Zai sauko, ya taka kan tsawawan

duwatsun duniya.

4 Duwatsu za su narke a

ƙarƙashinsa,

Kwaruruka za su tsattsage kamar

kakin zuma a gaban wuta,

Kamar ruwa yana gangarowa daga

tsauni.

5 Duk wannan kuwa saboda laifin

Yakubu ne,

Da laifin Isra’ila.

Mene ne laifin Yakubu?

Ashe, ba bautar gumaka da zaluncin

da ake yi a Samariya ba?

Mene ne kuma laifin Yahuza?

Ashe, ba bautar gumaka da zaluncin

da ake yi a Urushalima ba?

6 “Domin haka zan mai da Samariya

jujin kufai a karkara,

Wurin dasa kurangar inabi.

Zan zubar da duwatsunta a cikin

kwari,

In tone harsashin gininta.

7 Za a farfashe dukan siffofinta na

zubi,

Za a ƙaƙƙone dukiyarta da wuta,

Zan lalatar da gumakanta duka,

Gama ta wurin karuwanci ta samo

su,

Ga karuwanci kuma za su koma.”

8 Mika ya ce, “Saboda wannan zan yi

baƙin ciki, in yi kuka,

Zan tuɓe, in yi tafiya huntu.

Zan yi kuka kamar diloli,

In yi baƙin ciki kamar jiminai.

9 Gama raunin Samariya, ba ya

warkuwa,

Gama ya kai Yahuza,

Ya kuma kai ƙofar jama’ata a

Urushalima.”

10 Kada a faɗe shi a Gat,

Sam, kada a yi kuka.

Yi birgima cikin ƙura a Bet-leyafra.

11 Ku mazaunan Shafir, ku wuce

abinku da tsiraici da kunya.

Mazaunan Za’anan ba su tsira ba.

Bet-ezel ta yi kururuwa, “Zai

tumɓuke harasashin gininki.”

12 Mutanen Marot sun ƙosa su ga

alheri,

Amma masifa ta zo ƙofar

Urushalima daga wurin Ubangiji.

13 Ku mutanen Lakish, ku ɗaura wa

dawakai karusai,

Gama ku kuka fara yin zunubi a

Sihiyona,

Gama an iske laifofin Isra’ila

cikinku.

14 Domin haka sai ku ba Moreshet-gat

guzuri,

Mutanen Akzib za su yaudari

sarakunan Isra’ila.

15 Ku mazaunan Maresha, Ubangiji zai

kawo wanda zai ci ku da yaƙi,

Darajar Isra’ila za ta shiga

Adullam.

16 Ku aske kanku saboda ƙaunatattun

‘ya’yanku.

Ku yi wa kanku ƙwaƙwal kamar

ungulu,

Gama ‘ya’yanku za su tafi bautar

talala.

Categories
MIKA

MIKA 2

Taku ta Ƙare, Ku Masu Zaluntar Matalauta

1 Taku ta ƙare, ku masu shirya

mugunta,

Masu tsara mugunta a gadajensu!

Sa’ad da gari ya waye, sai su aikata

ta,

Domin ikon aikatawa yana

hannunsu.

2 Sukan yi ƙyashin gonaki da gidaje,

sai su ƙwace.

Sukan zalunci mutum, su ƙwace

gidansa da gādonsa.

3 Domin haka Ubangiji ya ce,

Ga shi, yana shirya wa wannan

jama’a masifa,

Wadda ba za ku iya kuɓuta daga

cikinta ba.

Ba kuma za ku yi tafiyar alfarma ba,

Gama mugun lokaci ne.

4 A wannan rana za su yi karin

magana a kanku,

Za su yi kuka da baƙin ciki mai

zafi,

Su ce, “An lalatar da mu sarai!

Ya sāke rabon mutanena,

Ya kawar da shi daga gare ni!

Ya ba da gonakinmu ga waɗanda

suka ci mu da yaƙi.”

5 Don haka ba za ku sami wanda zai sa

muku ma’auni

A taron jama’ar Ubangiji ba.

6 “Kada su yi wa’azi,” amma sun yi

wa’azi.

“Idan ba su yi wa’azi a kan

abubuwan nan ba,

Raini ba zai ƙare ba.

7 Daidai ne a faɗi haka, ya jama’ar

Yakubu?

‘Ruhun Ubangiji ya yi rashin haƙuri

ne?

Waɗannan ayyukansa ne?’ ”

“Ashe, maganata ba takan amfana

wanda yake tafiya daidai ba?”

8 Ubangiji ya amsa ya ce,

“Ba da daɗewa ba mutanena sun

tashi kamar maƙiyi,

Kukan tuɓe rigar masu wucewa da

salama, masu komawa da yaƙi.

9 Kukan kori matan mutanena

Daga gidajensu masu kyau,

Kukan kawar da darajata har abada

daga wurin ‘ya’yansu.

10 Ku tashi, ku tafi,

Gama nan ba wurin hutawa ba ne,

Saboda ƙazantarku wadda take kawo

muguwar hallaka.

11 “Idan mutum ya tashi yana iskanci,

yana faɗar ƙarya, ya ce,

‘Zan yi muku wa’azi game da ruwan

inabi da abin sa maye,’

To, shi ne zai zama mai wa’azin

mutanen nan!

12 “Hakika zan tattara ku duka, ya

Yakubu,

Zan tattara ringin Isra’ila.

Zan haɗa su tare kamar tumaki a

garke,

Kamar garken tumaki a makiyaya

Za su zama taron jama’a mai

hayaniya.

13 “Wanda zai huda garu, shi zai yi musu

jagora,

Za su fita ƙofar, su wuce, su fice ta

cikinta.

Sarkinsu zai wuce gabansu,

Ubangiji kuma yana kan gaba.”

Categories
MIKA

MIKA 3

An Yi wa Shugabannin Isra’ila Faɗa

1 Ni kuwa na ce, “Ku ji, ya ku

shugabannin mutanen Yakubu,

Da ku sarakunan Isra’ila.

Ya kamata ku san shari’a.

2 Amma kuna ƙin nagarta, kuna

ƙaunar mugunta,

Kuna feɗe mutanena,

Kuna kuma fizge naman jikinsu daga

ƙasusuwansu.

3 Kuna cin naman mutanena, kuna

feɗe fatar jikinsu,

Kuna kakkarya ƙasusuwansu,

Kuna yanyanka su gunduwa

gunduwa kamar naman da za a sa

a tukunya.”

4 Sa’an nan za su yi kuka ga Ubangiji,

Amma Ubangiji ba zai amsa musu

ba.

Zai ɓoye musu fuskarsa a wannan

lokaci,

Saboda mugayen ayyukansu.

5 Ga abin da Ubangiji ya ce a kan

annabawan da suka bi da

mutanensa a karkace,

Waɗanda suke cewa, “Salama,”

sa’ad da suke da abinci,

Amma sukan kai yaƙin shahada

Ga wanda bai ba su abin sawa a baka

ba.

6 Saboda haka kome zai zama dare

da duhu, ba wahayi ko duba.

Rana za ta fāɗi a kan annabawa,

Yini zai zama musu duhu baƙi

ƙirin.

7 Masu gani za su sha kunya,

Masu duba kuwa za su ruɗe,

Dukansu za su rufe bakinsu,

Gama ba amsa daga wurin Allah.

8 Amma ni ina cike da iko,

Da Ruhun Ubangiji,

Da shari’a da ƙarfin hali,

Don in sanar wa Yakubu da laifinsa,

Isra’ila kuma da zunubinsa.

9 Ku ji wannan, ya ku shugabannin

jama’ar Yakubu,

Da ku sarakunan mutanen Isra’ila,

Ku da kuke ƙyamar shari’ar gaskiya,

Kuna karkatar da dukan gaskiya.

10 Kuna gina Sihiyona da jini,

Kuna kuwa gina Urushalima da

zalunci.

11 Shari’ar shugabannin ƙasar ta cin

hanci ce.

Firistocinta suna koyarwa don

neman riba,

Haka kuma annabawa suna annabci

don neman kuɗi.

Duk da haka suna dogara ga

Ubangiji, suna cewa,

“Ai, Ubangiji yana tsakiyarmu,

Ba masifar da za ta same mu.”

12 Saboda ku kuwa za a nome Sihiyona

kamar gona,

Urushalima kuwa za ta zama tsibin

kufai,

Dutse inda Haikali yake zai zama

kurmi.

Categories
MIKA

MIKA 4

Mulkin Salama na Ubangiji

1 Zai zama nan gaba, dutse inda

Haikalin Ubangiji yake

Zai zama shi ne mafi tsawo duka a

cikin duwatsu,

Zai fi tuddai tsayi,

Mutane kuwa za su riƙa ɗunguma

zuwa wurinsa.

2 Al’umman duniya za su zo, su ce,

“Bari mu haura zuwa tudun

Ubangiji,

Zuwa Haikalin Allah na Isra’ila,

Za mu koyi abin da yake so mu yi,

Za mu yi tafiya a hanyar da ya

zaɓa.”

Koyarwar Ubangiji daga Urushalima

take zuwa,

Daga Sihiyona yake magana da

jama’arsa.

3 Zai shara’anta tsakanin al’umman

duniya masu yawa,

Zai sulhunta jayayyar da take tsakanin

manyan al’ummai,

Za su mai da takubansu garemani,

Māsunsu kuma su maishe su

wuƙaƙen aske itace.

Al’umma ba za ta ƙara fita zuwa

yaƙi ba,

Ba za su ƙara koyon yaƙi ba.

4 Kowa zai zauna gindin kurangar

inabinsa da gindin ɓaurensa.

Ba wanda zai tsoratar da shi,

Gama Ubangiji Mai Runduna ne ya

faɗa.

5 Ko da yake al’ummai suna bin

gumakansu,

Amma mu za mu bi Ubangiji

Allahnmu har abada abadin.

Kuɓutar Isra’ila daga Zaman Talala

6 Ubangiji ya ce,

“A waccan rana zan tattara guragu,

Da waɗanda aka kora,

Da waɗanda na wahalshe su.

7 Zan sa guragu su wanzu,

Korarru kuwa su zama al’umma mai

ƙarfi,

Ni, Ubangiji, zan yi mulkinsu a

Sihiyona har abada.

8 “Ke kuma hasumiyar garken tumaki,

tudun Sihiyona,

Mulki na dā zai komo wurinki,

Wato sarautar Urushalima.”

9 Yanzu, me ya sa kike kuka da

ƙarfi?

Ba sarki a cikinki ne?

Mashawarcinki ya hallaka ne,

Da azaba ta auka miki kamar ta

mace mai naƙuda?

10 Ki yi makyarkyata, ki yi nishi, ke

Sihiyona,

Kamar mace mai naƙuda,

Gama yanzu za ki fita daga cikin

birni,

Ki zauna a karkara,

Za ki tafi Babila, daga can za a cece

ki.

Daga can Ubangiji zai cece ki daga

hannun maƙiyanki.

11 Yanzu al’ummai sun taru suna

gāba da ke, suna cewa,

“Bari a ƙazantar da ita,

Bari mu zura mata ido.”

12 Amma ba su san nufin Ubangiji ba,

Ba su gane shirinsa ba,

Gama ya tara su ne kamar

dammunan da za a kai

masussuka.

13 “Ya Sihiyona, ki tashi, ki tattaka!

Gama zan mai da ƙahonki ƙarfe,

kofatanki kuwa tagulla,

Za ki ragargaje al’ummai da yawa.”

Za ki ba Ubangijin dukan duniya

dukiyarsu da suka tara ta hanyar

zamba,

Wadatarsu kuma ga Ubangijin dukan

duniya.

Categories
MIKA

MIKA 5

1 Ki tattara sojojinki, gama an

kewaye mu da yaƙi.

Za su bugi kumatun Sarkin Isra’ila

da sanda.”

Mulkin Mai Ceto daga Baitalami

2 “Baitalami cikin Efrata,

Wadda kike ‘yar ƙarama a cikin

kabilar Yahuza,

Amma daga cikinki wani zai fito

wanda zai sarauci Isra’ila

Wanda asalinsa tun fil azal ne.”

3 Domin haka zai yashe su,

Sai lokacin da wadda take naƙuda ta

haihu.

Sa’an nan sauran ‘yan’uwansa

Za su komo wurin mutanen Isra’ila.

4 Shi kuwa zai tashi ya ciyar da

garkensa da ƙarfin Ubangiji,

Da ɗaukakar sunan Ubangiji

Allahnsa.

Za su kuwa zauna lafiya,

Gama zai zama mai girma cikin

duniya duka.

5 Zai zama salamarmu.

Ceto da Hukunci

Sa’ad da kuma Assuriyawa za su

kawo mana yaƙi,

Za su tattake kagaranmu,

Za mu sa makiyaya bakwai da

shugabanni takwas su yi gāba da

su.

6 Za su mallaki ƙasar Assuriya da

takobi,

Su shiga ƙofofin ƙasar Nimrod da

zararren takobi,

Zai cece mu daga hannun

Ba’assuriye,

Sa’ad da ya kawo wa ƙasarmu

yaƙi,

Sa’ad da kuma ya tattake ƙasarmu.

7 Sa’an nan ringin Yakubu zai zamar

wa mutane

Kamar raɓa daga wurin Ubangiji,

Kamar kuma yayyafi a kan tsire-

tsire,

Wanda ba ya jinkiri ko ya jira

mutane.

8 Ringin Yakubu kuma zai zamar wa

al’umman duniya,

Kamar yadda zaki yake a tsakanin

namomin jeji,

Kamar kuma yadda zaki yake a

tsakanin garkunan tumaki,

Wanda, sa’ad da ya ratsa, yakan

tattaka,

Ya yi kacakaca da su,

Ba wanda zai cece su.

9 Za a ƙarfafa hannunka a kan

maƙiyanka,

Za a datse maƙiyanka duka.

10 “A wannan rana, ni Ubangiji na ce,

Zan kashe dawakanku, in hallaka

karusanku.

11 Zan shafe biranen ƙasarku,

In rushe garunku.

12 Zan kawar da maita daga ƙasarku,

Ba za ku ƙara samun bokaye ba.

13 Zan sassare siffofinku da

ginshiƙanku,

Ba za ku ƙara sunkuya wa aikin

hannuwanku ba.

14 Zan tumɓuke gumakan nan Ashtarot

daga cikinku,

Zan hallaka biranenku.

15 Da fushi da hasala zan yi sakayya

A kan al’umman da ba su yi biyayya

ba.”

Categories
MIKA

MIKA 6

Ubangiji Yana Gāba da Isra’ila

1 “Ku ji abin da ni Ubangiji

nake cewa,

Tashi ku gabatar da ƙararku a

gaban duwatsu,

Ku bar tuddai su ji muryarku.

2 “Ku duwatsu da madawwaman tussan

duniya,

Ku ji tuhumar da Ubangiji yake yi

muku.

Gama Ubangiji, yana da magana

gāba da mutanensa,

Zai tuhumi Isra’ila.

3 “Ya ku jama’ata, me na yi muku?

Wace irin fitina nake yi muku?

Ku amsa mini!

4 Gama na fito da ku daga ƙasar

Masar,

Na fanshe ku daga gidan bauta.

Na aika muku da Musa, da Haruna,

da Maryamu.

5 Ya ku jama’ata, ku tuna

Da abin da Balak, Sarkin Mowab, ya

ƙulla,

Da yadda Bal’amu ɗan Beyor ya

amsa masa,

Da abin da ya faru daga Shittim, har

zuwa Gilgal,

Don ku san ayyukan adalci na

Ubangiji.”

Abin da Allah Yake So ga Mutane

6 Da me zan zo gaban Ubangiji,

In sunkuyar da kaina a gaban Allah

na Sama?

Ko in zo gabansa da maraƙi bana

ɗaya domin yin hadaya ta

ƙonawa?

7 Ubangiji zai yi murna da raguna

dubbai

Ko kuwa da kogunan mai dubbai?

Zan ba da ɗan farina ne don

laifina?

Ko kuwa zan ba da ‘ya’yana saboda

zunubina?

8 Ya kai mutum, ya riga ya nuna

maka abin da yake mai kyau.

Abin da Ubangiji yake so gare ka,

shi ne

Ka yi adalci, ka ƙaunaci aikata

alheri,

Ka bi Allah da tawali’u.

9 Ubangiji yana kira ga birnin.

Hikima ce ƙwarai a ji tsoron

sunanka.

“Ki ji ya kabila, wa ya sa miki

lokacinki?

10 Ba zan manta da dukiya ta mugunta

a gidan mugu ba,

Ba kuwa zan manta da bugaggen

mudun awo ba.

11 Zan kuɓutar da mutum mai ma’auni

na cuta

Da ma’aunin ƙarya?

12 Attajiran birnin sun cika zalunci,

Mazaunansa kuwa maƙaryata ne,

Harshensu na yaudara ne.

13 Domin haka zan buge ku da ciwo,

In maishe ku kufai saboda

zunubanka.

14 Za ka ci, amma ba za ku ƙoshi ba,

Yunwa za ta kasance a cikinku,

Za ku tanada, amma ba zai tanadu

ba,

Abin da kuma kuka tanada zan bai

wa takobi.

15 Za ku shuka, amma ba za ku girbe ba.

Za ku matse ‘ya’yan zaitun, amma

ba za ku shafa mansa ba,

Za ku kuma matse ‘ya’yan inabi,

amma ba za ku sha ruwansa ba.

16 Domin kun kiyaye dokokin Omri,

Kun bi halin gidan Ahab,

Kun kuma bi shawarwarinsu.

Domin haka zan maishe ku kufai,

In mai da ku abin dariya,

Za ku sha raini a wurin mutanena.”

Categories
MIKA

MIKA 7

Lalacewar Isra’ila

1 Tawa ta ƙare, gama na zama

kamar lokacin da aka gama

tattara amfanin gona,

Kamar lokacin da aka gama kalar

‘ya’yan inabi,

Ba nonon inabi da za a tsinka, a ci,

Ba kuma ‘ya’yan ɓaure da suka

harba wanda raina yake so.

2 Mutanen kirki sun ƙare a duniya,

Ba nagarta a cikin mutane.

Dukansu suna kwanto don su zub da

jini.

Kowa yana farautar ɗan’uwansa da

tarko.

3 Sun himmantu su aikata abin da yake

mugu da hannuwansu.

Sarki da alƙali suna nema a ba su

hanci,

Babban mutum kuma yana faɗar son

zuciyarsa,

Da haka sukan karkatar da zance.

4 Mutumin kirkinsu kamar ƙaya yake,

Mai gaskiyarsu kuwa kamar shingen

ƙaya yake.

Ranar da kuka sa mai tsaro,

A ran nan za a aukar muku da

hukunci.

Yanzu ruɗewarku ta zo,

5 Kada ka dogara ga maƙwabcinka,

Kada kuma ka amince da abokinka.

Ka kuma kame bakinka daga

matarka

Wadda take kwance tare da kai.

6 Gama ɗa yana raina mahaifi,

‘Ya kuma tana tayar wa

mahaifiyarta,

Matar ɗa kuma tana gāba da

surukarta,

Mutanen gidan mutum su ne

maƙiyansa.

Ubangiji Zai Kawo Haske da Ceto

7 Amma ni zan kafa ido ga Ubangiji,

Zan jira ceton Allahna,

Allahna zai ji ni.

8 Ya maƙiyina, kada ka yi murna a

kaina,

Gama sa’ad da na fāɗi, zan tashi

kuma.

Sa’ad da na zauna cikin duhu,

Ubangiji zai haskaka ni.

9 Zan ɗauka fushin Ubangiji ne,

Gama na yi masa zunubi,

Sai lokacin da ya ji da’awata,

Har ya yanke mini shari’a.

Zai kawo ni zuwa wurin haske,

Zan kuwa ga cetonsa.

10 Sa’an nan maƙiyina wanda suke ce mini,

“Ina Ubangiji Allahnka?”

Zai gani, ya kuma ji kunya.

Idanuna za su gan shi lokacin da aka

tattake shi

Kamar taɓo a titi.

11 Za a faɗaɗa iyakarka

A ranar da za a gina garunka.

12 A waccan rana mutane za su zo

wurinka,

Daga Assuriya har zuwa Masar,

Daga Masar zuwa Kogin Yufiretis,

Daga teku zuwa teku, daga dutse

zuwa dutse.

13 Duniya kuwa za ta zama kufai,

Saboda mazaunan da suke cikinta,

Saboda hakkin ayyukansu.

Juyayin Ubangiji a kan Isra’ila

14 Sai ka yi kiwon mutanenka da

sandanka,

Wato garken mallakarka,

Wanda yake zaune shi kaɗai a kurmi

A tsakiyar ƙasa mai albarka.

Bari su yi kiwo cikin Bashan da

Gileyad

Kamar a kwanakin dā.

15 “Zan nuna muku abubuwa masu

banmamaki,

Kamar a kwanakin da kuka fito

ƙasar Masar.”

16 Al’umman duniya za su gani,

Su kuwa ji kunyar ƙarfinsu duka.

Za su sa hannuwansu a baka,

Kunnuwansu za su kurmance.

17 Za su lashi ƙura kamar maciji da

abubuwa masu rarrafe,

Za su fito da rawar jiki daga wurin

maɓuyarsu,

Da tsoro za su juyo wurin Ubangiji

Allahnmu,

Za su ji tsoronka.

18 Akwai wani Allah kamarka, mai yafe

mugunta,

Mai kawar da laifin ringin

gādonsa?

Ba ya riƙon fushi har abada, gama

shi mai alheri ne.

19 Zai sāke jin juyayinmu,

Ya tattake muguntarmu a ƙarƙashin

ƙafafunsa.

Za ka jefar da zunubanmu a cikin

zurfin teku.

20 Za ka nuna wa Yakubu aminci,

Ga Ibrahim kuma madawwamiyar

ƙauna,

Kamar yadda ka rantse wa

kakanninmu

Tun a zamanin dā.