Categories
NEH

NEH 11

Mazaunan Urushalima

1 Shugabannin jama’a kuwa suka zauna a Urushalima. Sauran jama’a kuma suka jefa kuri’a don a sami mutum guda daga cikin goma wanda zai zauna a Urushalima, wato tsattsarkan birni, sauran tara kuwa su yi zamansu a sauran garuruwa.

2 Jama’a suka sa wa dukan waɗanda suka tafi su zauna a Urushalima da yardar ransu albarka.

3 Waɗannan su ne shugabannin lardi waɗanda suka zauna a Urushalima, amma a garuruwan Yahuza kowa ya zauna a mahallinsa a garuruwansu, wato Isra’ila, da firistoci, da Lawiyawa, da ma’aikatan Haikali, da zuriyar barorin Sulemanu.

4 Waɗansu mutanen Yahuza da na Biliyaminu suka zauna a Urushalima.

Daga cikin mutanen Yahuza akwai Ataya ɗan Azariya, wato jīkan Zakariya ɗan Amariya. Sauran kakanninsa su ne Shefatiya, da Mahalalel, zuriyar Feresa ɗan Yahuza.

5 Akwai kuma Ma’aseya ɗan Baruk, jīkan Kolhoze. Sauran kakanninsa su ne Hazaiya, da Adaya, da Yoyarib, da Zakariya, zuriyar Shela ɗan Yahuza.

6 Dukan mutanen Feresa da suka zauna Urushalima su ɗari huɗu da sittin da takwas ne, dukansu kuwa muhimman mutane ne.

7 Waɗannan su ne mutanen Biliyaminu, Sallai ɗan Meshullam, jīkan Yowed. Sauran kakanninsa su ne Fedaiya, da Kolaiya, da Ma’aseya, da Itiyel da Yeshaya.

8 Sa’an nan kuma ga Gabbai da Sallai danginsa, mutum ɗari tara da ashirin da takwas.

9 Yowel ɗan Zikri shi ne shugabansu, Yahuza ɗan Hassenuwa shi ne shugaba na biyu cikin birnin.

10 Na wajen firistoci, su ne Yedaiya ɗan Yoyarib, da Yakin,

11 da Seraiya ɗan Hilkiya, jīkan Shallum. Sauran kakanninsa, su ne Zadok, da Merayot, da Ahitub, mai lura da Haikalin Allah.

12 Tare da ‘yan’uwansu waɗanda suka yi aiki a Haikali, su ɗari takwas da ashirin da biyu ne.

Akwai kuma Adaya ɗan Yeroham, jīkan Felaliya. Sauran kakanninsa su ne Amzi, da Zakariya, da Fashur, da Malkiya.

13 Tare da ‘yan’uwansu shugabannin gidajen kakanni, su ɗari da arba’in da biyu. Sai kuma Amashai ɗan Azarel, jīkan Azai. Sauran kakanninsa su ne Meshillemot, da Immer.

14 Tare da ‘yan’uwansu, su ɗari da ashirin da takwas ne gwarzayen sojoji ne. Shugabansu shi ne Zabdiyel ɗan Haggedolim.

15 Na wajen Lawiyawa kuwa su ne Shemaiya ɗan Hasshub, jīkan Azrikam. Sauran kakanninsa su ne Hashabiya, da Bunni,

16 da Shabbetai, da Yozabad, ɗaya daga cikin manyan shugabanni na Lawiyawa, waɗanda suke lura da kewayen Haikalin Allah.

17 Da kuma Mattaniya ɗan Mika, jīkan Zikri, zuriyar Asaf, shi ne shugaba na farko na mawaƙan addu’a ta godiya. Bakbukiya, shi ne mataimakin Mattaniya. Ga kuma Obadiya ɗan Shemaiya, jīkan zuriyar Galal, zuriyar Yedutun.

18 Dukan Lawiyawa da suke a tsattsarkan birni su ɗari biyu da tamanin da huɗu ne.

19 Masu tsaron ƙofofi kuma su ne Akkub, da Talmon, da ‘yan’uwansu, su ɗari da saba’in da biyu ne.

20 Sauran jama’ar Isra’ila kuwa, da firistoci, da Lawiyawa suka zauna a dukan garuruwan Yahuza, kowa ya zauna a gādonsa.

21 Amma ma’aikatan Haikali suka zauna a Ofel. Ziha da Gishfa, su ne shugabannin ma’aikatan Haikali.

22 Shugaban Lawiyawan da yake a Urushalima, shi ne Uzzi ɗan Bani, jīkan Hashabiya. Sauran kakanninsa su ne Mattaniya, ɗan Mika daga zuriyar Asaf. Su ne mawaƙa a Haikalin Allah.

23 Sarki ya yi wa shugabannin mawaƙa umarni da ƙarfi a kan abin da za su yi kowace rana.

24 Fetahiya ɗan Meshezabel, daga zuriyar Zera na kabilar Yahuza, shi ne wakilin sarki a kan dukan abin da ya shafi jama’a.

Mutanen da Suke a Sauran Garuruwa da Birane

25 Game da ƙauyuka da gonakinsu kuma, waɗansu mutanen Yahuza suka zauna a Kiriyat-arba, da Dibon da ƙauyukanta, da Yekabzeyel da ƙauyukanta,

26 da a biranen Yeshuwa, da Molada, da Bet-felet,

27 da Hazar-shuwal, da Biyer-sheba da ƙauyukanta,

28 da Ziklag, da Mekona da ƙauyukanta,

29 da En-rimmon, da Zora, da Yarmut,

30 da Zanowa, da Adullam da ƙauyukansu, da Lakish da gonakinta, da Azeka da ƙauyukanta. Haka suka yi zango daga Biyer-sheba zuwa kwarin Hinnom.

31 Mutanen kabilar Biliyaminu suka zauna a Geba, da Mikmash, da Ayya, da Betel da sauran ƙauyuka na kewaye,

32 da Anatot, da Nob, da Ananiya,

33 da Hazor, da Rama, da Gittayim,

34 da Hadid, da Zeboyim, da Neballat,

35 da Lod, da Ono, wato kwarin masu sana’a.

36 Waɗansu kashi na Lawiyawan da suke a Yahuza, aka sa su zauna a yankin ƙasar Biliyaminu.

Categories
NEH

NEH 12

Firistoci da Lawiyawa

1 Firistoci da Lawiyawa da suka komo tare da Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, da Yeshuwa, su ne

Seraiya, da Irmiya, da Ezra,

2-7 Amariya, da Malluki, da Hattush,

Shekaniya, da Rehum, da Meremot,

Iddo, da Ginneton, da Abaija,

Miyamin, da Mawadiya, da Bilga,

Shemaiya, da Yoyarib, da Yedaiya,

Sallai, da Amok, da Halkiya, da Yedaiya.

Waɗannan su ne shugabannin firistoci da ‘yan’uwansu a zamanin Yeshuwa.

8-9 Lawiyawa su ne,

Yeshuwa, da Binnuyi, da Kadmiyel,

Sherebiya, da Yahuza, da Mattaniya wanda yake lura da waƙoƙin godiya, da shi da ‘yan’uwansa.

Bukbukiya da Unno, ‘yan’uwansu, suka tsaya daura da su a taron sujada.

Zuriyar Yeshuwa Firist

10 Yeshuwa shi ne ya haifi Yoyakim, Yoyakim ya haifi Eliyashib, Eliyashib ya haifi Yoyada.

11 Yoyada ya haifi Jonatan, Jonatan ya haifi Yadduwa.

Shugabannin Iyalin Firistoci

12-21 A zamanin Yoyakim babban firist, waɗannan su ne shugabannin iyalin firistoci,

na wajen Seraiya, Meraiya ne

na wajen Irmiya, Hananiya ne

na wajen Ezra, Meshullam ne

na wajen Amariya, Yehohanan ne

na wajen Malluki, Jonatan ne

na wajen Shebaniya, Yusufu ne

na wajen Harim, Adana ne

na wajen Merayot, Helkai ne

na wajen Iddo, Zakariya ne

na wajen Ginneton, Meshullam ne

na wajen Abaija, Zikri ne

na wajen Miniyamin da Mowadiya, Filtai ne

na wajen Bilga, Shimeya ne

na wajen Shemaiya, Yehonatan ne

na wajen Yoyarib, Mattenai ne

na wajen Yedaiya, Uzzi ne

na wajen Sallai, Kallai ne

na wajen Amok, Eber ne

na wajen Hilkiya, Hashabiya ne

na wajen Yedaiya, Netanel ne

Lissafin Manya na Iyalin Firistoci da Lawiyawa

22 A zamanin Eliyashib, da Yoyada, da Yohenan, da Yadduwa, Lawiyawa, har zuwa zamanin mulkin Dariyus, mutumin Farisa, aka rubuta shugabannin gidajen kakannin Lawiyawa da firistoci.

23 Aka kuma rubuta shugabannin gidajen kakannin zuriyar Lawi a tarihi, har zuwa zamanin Yohenan ɗan Eliyashib.

An Rarraba Ayyukan Haikali

24 Shugabannin Lawiyawa kuwa, su ne Hashabiya, da Sherebiya, da Yeshuwa, da Kadmiyel. ‘Yan’uwansu suna tsaye kusa da su daki daki domin su yi yabo, su yi godiya kamar yadda Dawuda mutumin Allah ya umarta.

25 Mattaniya, da Bakbukiya, da Obadiya, da Meshullam, da Talmon, da Akkub su ne masu tsaron ƙofofi, suna tsaron ɗakunan ajiya na wajen ƙofofi.

26 Waɗannan suna nan a zamanin Yoyakim ɗan Yeshuwa, jikan Yehozadak, da zamanin mai mulki Nehemiya, da Ezra, firist da magatakarda.

An Keɓe Garun Birni

27 A lokacin keɓe garun Urushalima, sai aka nemo Lawiyawa a wurarensu duka don a kawo su Urushalima, su yi bikin keɓewa da farin ciki da godiya, da raira waƙoƙi da kuge, da garaya, da molo.

28 Aka tattara mawaƙa daga kewayen Urushalima da ƙauyukan Netofatiyawa.

29 Da kuma daga Betgilgal da karkarar Geba, da Azmawet, gama mawaƙan sun gina wa kansu ƙauyuka kewaye da Urushalima.

30 Sai firistoci da Lawiyawa suka tsarkake kansu, suka kuma tsarkake jama’a, da ƙofofi, da garun.

31 Sai na sa shugabannin Yahuza su hawo garu, sa’an nan na sa manyan ƙungiyoyi biyu waɗanda za su yi godiya, su tafi a jere.

Ƙungiya guda ta bi wajen dama a kan garun zuwa Ƙofar Juji.

32 Hoshaiya da rabin sugabannin Yahuza suka bi bayansu,

33 tare da Azariya, da Ezra, da Meshullam,

34 da Yahuza, da Biliyaminu, da Shemaiya, da Irmiya.

35 Sa’an nan waɗansu ‘ya’yan firistoci, masu busar ƙaho, su ne Zakariya ɗan Jonatan, jīkan Shemaiya. Sauran kakanninsa su ne Mattaniya, da Mikaiya, da Zakkur, daga zuriyar Asaf.

36 Sauran ‘yan’uwansa su ne Shemaiya, da Azarel, da Milalai, da Gilalai, da Ma’ai, da Netanel, da Yahuza, da Hanani. Suna da kayayyakin bushe-bushe da na kaɗekaɗe. Ezra magatakarda ne yake gabansu.

37 A Ƙofar Maɓuɓɓuga kuwa, sai suka yi gaba sosai wajen matakan birnin Dawuda, wajen hawan garu, daga bisa gidan Dawuda, zuwa Ƙofar Ruwa wajen gabas.

38 Ƙungiyar jama’a ta biyu ta masu yin waƙoƙin godiya, ta bi ta wajen hagu. Na bi su tare da rabin jama’a a kan garu, sama da Hasumiyar Tanderu zuwa garu mai fādi,

39 da Kuma sama da Ƙofar, Ifraimu da wajen Tsohuwar Ƙofar, da wajen Ƙofar Kifi, da Hasumiyar Hananel, da Hasumiyar Ɗari zuwa Ƙofar Tumaki, sai suka tsaya a Ƙofar Tsaro.

40 Haka fa ƙungiyoyi biyu ɗin nan masu raira waƙoƙin godiya suka tsaya a Haikalin Allah.

Ni da rabin shugabanni muna tare da su.

41 Tare da firistoci kuma, wato su Eliyakim, da Ma’aseya, da Miniyamin, da Mikaiya, da Eliyehoyenai, da Zakariya, da Hananiya, suna busa ƙaho,

42 da kuma Ma’aseya, da Shemaiya, da Ele’azara, da Uzzi, da Yehohanan, da Malkiya, da Elam, da Ezer, suna raira waƙoƙi, Yezrahiya kuma shi ne shugabansu.

43 Jama’a suka miƙa hadayu da yawa a wannan rana, suka yi murna, gama Allah ya faranta musu zuciya ƙwarai. Mata da yara kuma suka yi murna. Aka ji muryar murnar mutanen Urushalima daga nesa.

Shiri don Firistoci da Lawiyawa

44 A ran nan aka sa mutanen da za su lura da ɗakunan ajiya, da sadakoki, da nunan fari, da zaka. Su ne za su tara nunan fari daga gonakin da suke kusa da garuruwa, bisa ga yadda doka ta ce, saboda firistoci da Lawiyawa, gama mutanen Yahuza sun yi murna saboda hidimar da firistoci da Lawiyawa suka yi.

45 Sun yi wa Allahnsu sujada, sun yi hidimar tsarkakewa tare da mawaƙa da masu tsaron ƙofofi kamar yadda Dawuda da ɗansa Sulemanu suka umarta.

46 A dā a zamanin Dawuda da Asaf akwai shugaban mawaƙa, akwai kuma waƙoƙin yabo da na godiya ga Allah.

47 A zamanin Zarubabel da zamanin Nehemiya dukan jama’ar Isra’ila suka biya wa mawaƙa da masu tsaron ƙofofi bukatarsu ta kowace rana. Sun kuma ba Lawiyawa sadokoki, su Lawiyawa kuma suka ba zuriyar Haruna nasu rabo.

Categories
NEH

NEH 13

Gyare-gyaren da Nehemiya Ya Yi

1 A wannan rana aka karanta daga littafin Musa a kunnuwan jama’a. A cikinsa aka tarar da inda aka rubuta, cewa kada Ba’ammone, ko mutumin Mowab ya shiga taron jama’ar Allah.

2 Gama ba su taryi jama’ar Isra’ila da abinci da abin sha ba, amma suka yi ijara da Bal’amu ya zo ya la’anta musu su, amma Allahnmu ya juyar da la’anar ta zama albarka.

3 Da mutane suka ji dokokin, sai suka ware dukan waɗanda suke ba Isra’ilawa ba.

4 Kafin wannan lokaci Eliyashib, firist, wanda aka sa shi shugaban ɗakunan ajiya na Haikalin Allahnmu, wanda yake da dangantaka da Tobiya,

5 ya shirya wa Tobiya babban ɗaki inda dā aka ajiye hadaya ta gari, da turare, da tasoshi, da zakar hatsi, da ruwan inabi, da mai, waɗanda aka umarta a ba Lawiyawa, da mawaƙa, da masu tsaron ƙofofi, da inda aka ajiye sadakokin da ake ba firistoci.

6 Ba na nan a Urushalima sa’ad da wannan abu ya faru, gama a shekara ta talatin da biyu ta sarautar Artashate, Sarkin Babila, na tafi wurin sarki. Daga baya sarki ya ba ni izini in koma.

7 Da na komo Urushalima, sai na ga mugun abin da Eliyashib ya yi domin Tobiya, yadda ya shirya masa ɗaki a filin Haikalin Allah.

8 Sai na husata ƙwarai, na fitar da kayan ɗakin Tobiya a waje.

9 Sai na umarta, suka kuwa tsarkake ɗakunan, sa’an nan na mayar da tasoshin Haikalin Allah, da hadaya ta gari, turare a ciki.

10 Na kuma iske ba a ba Lawiyawa rabonsu ba. Saboda wannan Lawiyawa da mawaƙa masu hidima suka watse zuwa gonakinsu.

11 Sai na yi wa shugabanni faɗa, na ce, “Me ya sa aka ƙi kula da Haikalin Allah?” Sa’an nan na tara Lawiyawa da mawaƙa, na sa su a wuraren aikinsu.

12 Sai dukan mutanen Yahuza suka kawo zakar hatsi, da ta ruwan inabi, da ta mai, a ɗakunan ajiya.

13 Sai na sa Shelemiya, firist, da Zadok, magatakarda, da Fedaiya daga cikin Lawiyawa su zama masu lura da ɗakunan ajiya. Na kuma sa Hanan ɗan Zakkur, jikan Mattaniya ya yi aiki tare da su, gama su amintattu ne. Aikinsu shi ne su raba wa ‘yan’uwansu abin da aka kawo.

14 “Ka tuna da ni, ya Allahna, saboda wannan. Kada ka manta da ayyukan kirki da na yi a Haikalin Allah da kuma na hidimarsa.”

15 A kwanakin nan na ga mutane a Yahuza suna matse ruwan inabi, suna labta wa jakunansu buhunan hatsi, da ruwan inabi, da ‘ya’yan inabi, da ɓaure, da kaya iri iri, suna kawo su cikin Urushalima a ran Asabar. Sai na yi musu faɗa a kan sayar da abinci a wannan rana.

16 Mutanen Taya da suke zaune a birnin sukan kawo kifi da kaya iri iri, su sayar wa mutanen Yahuza a Urushalima a ranar Asabar.

17 Sai na tsauta wa manyan mutanen Yahuza, na ce musu, “Wane irin mugun abu ne kuke yi haka, kuna ɓata ranar Asabar?

18 Ashe, ba haka kakanninku suka yi ba, har wannan ya sa Allahnmu ya kawo mana masifa, mu da dukan birnin? Duk da haka kuna ƙara kawo wa Isra’ila hasala saboda kuna ɓata ranar Asabar.”

19 Magariba na yi kafin ranar Asabar, sai na yi umarni a rufe ƙofofin Urushalima, kada a buɗe su sai Asabar ta wuce. Na sa waɗansu barorina a ƙofofin, don kada su bari a shigo da kaya ran Asabar.

20 Sau ɗaya ko sau biyu, ‘yan kasuwa da masu sayar da abubuwa iri iri suka kwana a bayan Urushalima.

21 Amma na tsauta musu, na ce, “Me ya sa kuka kwana a bayan garu? Idan kun ƙara yin haka zan kama ku.” Tun daga wannan lokaci ba su ƙara zuwa a ranar Asabar ba.

22 Sai kuma na umarci Lawiyawa su tsarkake kansu, su yi tsaron ƙofofin don a kiyaye ranar Asabar da tsarki.

“Ya Allahna, ka tuna da wannan aiki nawa, ka rayar da ni saboda girman madawwamiyar ƙaunarka.”

23 A waɗannan kwanaki kuma na ga waɗansu Yahudawa waɗanda suka auro mata daga Ashdod, da Ammon, da Mowab.

24 Rabin ‘ya’yansu suna magana da harshen Ashdod, ko wani harshe dabam, amma ba su iya yin magana da harshen Yahuza ba.

25 Sai na yi musu faɗa na la’ance su, na bugi waɗansu daga cikinsu, na ciccire gashin kansu, na sa su rantse da Allah, cewa ba za su aurar da ‘ya’yansu mata ga ‘ya’yan maza na bare ba, ko kuma su auro wa ‘ya’yansu maza ‘yan matan bare, ko su auro wa kansu.

26 Na faɗa musu cewa, “Ba a kan irin wannan ba ne Sulemanu Sarkin Isra’ila ya yi laifi? A al’ummai, ba sarki kamarsa. Allahnsa ya ƙaunace shi, ya sarautar da shi a Isra’ila, duk da haka baren mata suka sa shi ya yi zunubi.

27 Ba za mu yarda da abin da kuke yi ba, har mu aikata wannan mugunta ta rashin aminci ga Allahnmu, da za mu auro baren mata.”

28 Ɗaya daga cikin ‘ya’yan Yoyada ɗan Eliyashib, babban firist, surukin Sanballat ne, Bahorone, saboda haka sai na kore shi daga wurina.

29 “Ka tuna da su, ya Allahna don sun ƙazantar da aikin firistoci da alkawarin zama firist da Lawiyawa.”

30 Da haka na tsarkake su daga kowane baƙon abu, na sa firistoci da Lawiyawa cikin aiki, kowa ya kama aikinsa.

31 Na kuma shirya yadda za a tara itace domin yin hadaya a kan kari, da kuma lokacin da za a kawo nunan fari.

“Ya Allahna, ka tuna da ni, ka yi mini alheri.”