Categories
ROM

ROM 11

Sauran Isra’ila

1 To, ina tambaya. Wato, Allah ya juya wa jama’arsa baya ke nan? A’a, ko kusa! Ai, ni ma da kaina Ba’isra’ile ne, zuriyar Ibrahim, na kabilar Biliyaminu.

2 Ko kaɗan, Allah bai juya wa jama’arsa da ya zaɓa tun dā baya ba. Ko ba ku san abin da Nassi ya faɗa ba ne, a game da Iliya? Yadda ya kai kuka ga Allah, a kan Isra’ila, ya ce,

3 “Ya Ubangiji, sun karkashe annabawanka, sun rurrushe bagadanka na hadaya. Ni kaɗai ne na ragu, suna kuwa neman raina.”

4 Amma me Allah ya amsa masa? Cewa ya yi, “Na keɓe wa kaina mutum dubu bakwai waɗanda ba su taɓa durƙusa wa Ba’al ba.”

5 Haka ma a wannan zamani akwai ragowa, waɗanda aka zaɓa saboda alherinsa.

6 In kuwa na alheri ne, ba sauran cewa ya dogara ga aikin lada ke nan. In ba haka ba, ashe, alheri ba alheri ba ne kuma.

7 To, yaya ke nan? Ashe, abin da Isra’ila take nema, ba su samu ba ke nan, amma zaɓaɓɓun nan sun samu, sauran kuwa sun taurare.

8 Yadda yake a rubuce cewa,

“Allah ya toshe musu basira,

Ya ba su ido, ba na gani ba,

Da kuma kunne, ba na ji ba,

Har ya zuwa yau.”

9 Dawuda kuma ya ce,

“Da ma shagalinsu ya zama musu tarko, abin shammatarsu,

Sanadin faɗuwarsu kuma, har aniyarsu ta koma kansu.

10 Idonsu kuma yă shiga duhu, har su kasa gani,

Ka kuma tanƙwara bayansu har abada.”

Ceton Al’ummai

11 Ina kuma tambaya. Faɗuwar da suka yi, sun faɗi ba tashi ke nan? A’a, ko kusa! Sai ma faɗuwarsu ta zama sanadin ceto ga al’ummai, don a sa Isra’ila kishi.

12 To, in kuwa duniya ta arzuta da hasararsu, wa zai kimanta yawan albarka, in adadinsu masu ɗungumawa ga Allah ya cika?

13 Da ku al’ummai fa nake. Tun da yake ni manzo ne ga al’ummai, ina taƙama da aikina,

14 ko ta wane hali in sa kabilata kishin zuci, har in ceci waɗansunsu.

15 Domin in an sulhunta duniya ga Allah, saboda yar da su da aka yi, to, in an karɓe su fa, ba sai rai daga matattu ba?

16 In curin farko tsattsarka ne, haka sauran gurasar ma. In kuma saiwa tsattsarka ce, haka rassan ma.

17 Amma in an sassare waɗansu rassan zaitun na gida, kai kuma da kake zaitun na jeji aka ɗaura aure da kai a gurbinsu, kana kuma shan ni’imar saiwar zaitun ɗin nan tare da sauran rassan,

18 kada ka yi wa sauran rassan alwashi. In kuwa ka yi, ka tuna fa, ba kai kake ɗauke da saiwar ba, saiwar ce take ɗauke da kai.

19 Kila za ka ce, “Ai, an sare rassan nan ne, don a ɗaura aure da ni.”

20 Hakika haka ne, amma saboda rashin bangaskiyarsu ne aka sare su, kai kuwa saboda bangaskiyarka ne kake kafe. Kada fa ka nuna alfarma, sai dai ka ji tsoron Allah.

21 Da yake Allah bai bar rassan asalin ba, kai ma ba zai bar ka ba.

22 Dubi fa alherin Allah da kuma tsananinsa, wato, tsanani ga waɗanda suka fāɗi, alherinsa kuwa a gare ka, muddin ka ɗore a cikin alherin. In ba haka ba, kai ma sai a datse ka.

23 Ko su ma, in dai ba su nace wa rashin bangaskiyarsu ba, sai a ɗaura aure da su, domin Allah yana da ikon sāke mai da su.

24 Kai ma da aka saro daga zaitun ɗin da asalinsa yake na jeji, aka ɗaura aure da kai a jikin zaitun ɗin na gida, saɓanin yadda aka saba, balle waɗannan rassa na asali, da za a ɗaura aure da su a jikin zaitun ɗin nan nasu na asali?

Komar da Isra’ila ga Matsayinsa

25 ‘Yan’uwa, ga wata asirtacciyar gaskiya da nake so ku sani, domin kada ku zaci ku masu hikima ne, taurarewar nan–wadda ba mai tabbata ba ce–ta sami Isra’ilawa ne, har adadin al’ummai masu ɗungumawa zuwa ga Allah ya cika.

26 Ta haka nan ne Isra’ila duka za su sami ceto, kamar yadda yake a rubuce cewa,

“Mai Ceto zai zo daga Sihiyona,

Zai kuma kawar da rashin bin Allah daga zuriyar Yakubu,”

27 “Cikar alkawarina a gare su ke nan,

Sa’ad da na ɗauke musu zunubansu.”

28 A game da bishara kuma, maƙiyan Allah ne su, domin amfaninku ne kuwa. Amma a game da zaɓen Allah, su ƙaunatattunsa ne, albarkacin kakannin kakanninsu.

29 Domin baiwar Allah da kiransa ba sa tashi.

30 Kamar yadda kuka ƙi bin Allah a dā, amma a yanzu aka yi muku jinƙai saboda rashin biyayyarsu,

31 haka su ma da suke marasa biyayya a yanzu, yanzu a yi musu jinƙai kamar yadda aka yi muku.

32 Don Allah ya kulle kowa a cikin rashin biyayya, domin ya nuna jinƙai ga kowa.

33 Zurfin hikimar Allah da na saninsa da rashin iyaka suke! Hukunce-hukuncensa sun fi gaban bincikewa, hanyoyinsa kuma sun fi gaban bin diddigi!

34 “Wa ya taɓa sanin zuciyar Ubangiji?

Ko kuwa wa ya taɓa ba shi wata shawara?”

35 “Wa kyauta ta shiga tsakaninsu da Allah, ya fara bayarwa,

Har da za a sāka masa?”

36 Ai, daga gare shi ne, ta wurinsa kuma, dukkan abubuwa suke, shi ne kuma makomarsu. Ɗaukaka tă tabbata a gare shi har abada. Amin.

Categories
ROM

ROM 12

Hadaya Mai Rai

1 Don haka ina roƙonku ‘yan’uwa, saboda yawan jinƙai na Allah, ku miƙa jikinku hadaya rayayyiya, tsattsarka, abar karɓa ga Allah. Domin wannan ita ce ibadarku ta ainihi.

2 Kada ku biye wa zamanin nan, amma ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so, wato nufinsa kyakkyawa, abin karɓa, cikakke kuma.

3 Albarkacin alherin da aka yi mini ina yi wa kowannenku gargaɗi kada ya ɗauki kansa fiye da yadda ya kamata, sai dai ya san kansa, gwargwadon bangaskiyar da Allah ya ba shi.

4 Wato kamar yadda gaɓoɓi da yawa suke harhaɗe a jiki ɗaya, gaɓoɓin nan kuwa ba aiki iri ɗaya suke yi ba,

5 haka mu ma, ko da yake muna da yawa, jiki ɗaya muke haɗe da Almasihu, kowannenmu kuma gaɓar ɗan’uwansa ne.

6 Da yake muna da baiwa iri iri, gwargwadon alherin da aka yi mana, to, sai mu yi amfani da su. In ta annabci ce, sai mu yi amfani da ita gwargwadon bangaskiyarmu,

7 in ta hidima ce, wajen hidimarmu, mai koyar da Maganar Allah kuwa, wajen koyarwarsa,

8 mai ƙarfafa zuciya kuwa, wajen ƙarfafawarsa, mai yin gudunmawa kuwa, yă bayar hannu sake, shugaba yă yi shugabancinsa da himma, mai yin aikin tausayi, yă yi shi da fara’a.

Gargaɗi a kan Zaman Kirista

9 Ƙauna ta kasance sahihiya. Ku yi ƙyamar abin da yake mugu, ku lazamci abin da yake nagari.

10 A game da ƙaunar ‘yan’uwa kuwa, ku ƙaunaci juna gaya. A wajen ba da girma, kowa yă riga ba ɗan’uwansa.

11 Kada ku sassauta a wajen himma, ku himmantu a ruhu, kuna bauta wa Ubangiji.

12 Sa zuciyar nan taku ta sa ku farin ciki, ku jure wa wahala, ku nace wa yin addu’a.

13 Ku agaji tsarkaka, ku himmantu ga yi wa baƙi alheri.

14 Ku sa wa masu tsananta muku albarka. Ku sa musu albarka, kada ku la’ance su.

15 Ku taya masu farin ciki farin ciki, masu kuka kuwa ku taya su kuka.

16 Ku yi zaman lafiya da juna. Kada ku nuna alfarma, sai dai ku miƙa kanku ga aikata ayyukan tawali’u. Kada ku aza kanku masu hikima ne.

17 Kada ku rama muguntar kowa da mugunta. Ku yi ta lura al’amuranku su zama daidai a gaban kowa.

18 In mai yiwuwa ne, a gare ku, ku yi zaman lafiya da kowa.

19 Ya ku ƙaunatattuna, kada ku ku yi ramuwa, sai dai ku bar wa fushin Allah. Domin a rubuce yake cewa, “Ramuwa tawa ce, ni zan saka, in ji Ubangiji.”

20 Har ma “in maƙiyinka yana jin yunwa, sai ka ci da shi. In yana jin ƙishirwa, ka shayar da shi. Don ta haka ne za ka tula garwashin wuta a kansa.”

21 Kada mugunta ta rinjaye ku, amma ku rinjayi mugunta da nagarta.

Categories
ROM

ROM 13

1 Bari kowa yă yi biyayya ga mahukunta. Gama ba wani iko sai da yardar Allah. Mahukuntan da suke nan kuwa naɗin Allah ne.

2 Saboda haka duk wanda ya yi wa mahukunta tsayayya, ya yi wa umarnin Allah ke nan, masu yin tsayayyar nan kuwa za a yi musu hukunci.

3 Don kuwa mahukunta ba abin tsoro ba ne ga masu aiki nagari, sai dai ga masu mugun aiki. Kana so kada ka ji tsoron mahukunci? To, sai ka yi nagarta, sai kuwa ya yaba maka.

4 Domin shi bawan Allah ne, don kyautata zamanka. Amma in kai mai mugun aiki ne, to, ka ji tsoro, don ba a banza yake riƙe da takobi ba. Ai, shi bawa ne na Allah, mai sāka wa mugu da fushi.

5 Saboda haka wajibi ne ka yi biyayya, ba domin gudun fushi kaɗai ba, amma domin lamiri kuma.

6 Shi ne ma ya sa kuke biyan haraji, don su mahukunta ma’aikata ne na Allah, suna kuma yin wannan aiki a koyaushe.

7 Ku ba kowa hakkinsa, masu haraji, harajinsu, masu kuɗin fito, kuɗinsu na fito, waɗanda suka cancanci ladabi, ladabi, waɗanda suka cancanci girmamawa, girmamawa.

8 Kada hakkin kowa ya zauna a kanku, sai dai na ƙaunar juna, don mai ƙaunar maƙwabcinsa ya cika Shari’a ke nan.

9 Umarnan nan cewa, “kada ka yi zina, kada ka yi kisankai, kada ka yi sata, kada ka yi ƙyashi,” da dai duk sauran umarnai an ƙunshe su ne a wannan kalma cewa, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”

10 Ƙauna ba ta cutar maƙwabci saboda haka ƙauna cika Shari’a ce.

11 Ga shi kuma, kun dai san irin zamanin da muke a ciki, ai, lokaci ya riga ya yi da za ku farka daga barci. Gama yanzu mun fi kusa da ceton nan namu a kan sa’ad da muka fara ba da gaskiya.

12 Dare fa ya ƙure, gari ya kusa wayewa. Sai mu watsar da ayyukan duhu, mu yi ɗamara da kayan ɗamara na haske.

13 Mu tafiyar da al’amuranmu yadda ya dace a yi da rana, ba a cikin shashanci da buguwa, ko fasikanci da fajirci, ko jayayya da kishi ba.

14 Amma ku ɗauki halin Ubangiji Yesu Almasihu, kada kuwa ku tanadi halin mutuntaka, don biye wa muguwar sha’awarsa.

Categories
ROM

ROM 14

Kada Ka Ɗora wa Ɗan’uwanka Laifi

1 A game da wanda bangaskiya tasa rarrauna ce kuwa, ku karɓe shi hannu biyu biyu, amma ba a game da sukan ra’ayinsa ba.

2 Ga wani, bangaskiyarsa ta yardar masa cin kome, wanda bangaskiyarsa rarrauna ce kuwa, sai kayan gona kawai yake ci.

3 To, kada fa mai cin kome ɗin nan yă raina wanda ya ƙi ci, kada kuma wanda ya ƙi cin nan, yă ga laifin mai ci, domin Allah ya riga ya karɓe shi hannu biyu biyu.

4 Kai wane ne har da za ka ga laifin baran wani? Ko dai ya tsaya, ko ya faɗi, ai, ruwan maigidansa ne. Za a ma tsai da shi, domin Ubangiji yana da ikon tsai da shi.

5 Wani yakan ɗaukaka wata rana fiye da sauran ranaku, wani kuwa duk ɗaya ne a wurinsa. Kowa dai yă zauna a cikin haƙƙaƙewa, a kan ra’ayinsa.

6 Mai kiyaye wata rana musamman, yana kiyaye ta ne saboda Ubangiji. Mai cin nan kuma, yana ci ne saboda Ubangiji, da yake yana gode wa Allah. Marar cin nan kuma yana ƙin ci ne saboda Ubangiji, shi ma kuwa yana gode wa Allah.

7 Duk a cikinmu ba wanda ya isar wa kansa a sha’anin rayuwarsa ko mutuwarsa.

8 Ko muna a raye, zaman Ubangiji muke yi, ko mun mutu ma, zaman Ubangiji muke yi. Ashe, ko muna a raye, ko kuma a mace, na Ubangiji ne mu.

9 Saboda haka ne musamman Almasihu ya mutu, ya sāke rayuwa, wato, domin ya zama shi ne Ubangijin matattu da na rayayyu duka.

10 To, kai, me ya sa kake ganin laifin ɗan’uwanka? Kai kuma, me ya sa kake raina ɗan’uwanka? Ai, dukkanmu za mu tsaya a gaban kursiyin shari’ar Allah.

11 Domin a rubuce yake,

“Na rantse da zatina, in ji Ubangiji, kowace gwiwa sai ta rusuna mini,

Kowane harshe kuwa sai ya yabi Allah.”

12 Don haka kowannenmu zai faɗi abin da shi da kansa ya yi, a gaban Allah.

Kada Ka Sa Ɗan’uwanka Yin Tuntuɓe

13 Saboda haka kada mu ƙara ganin laifin juna, gara mu ƙudura, don kada kowannenmu yă zama sanadin tuntuɓe ko faɗuwa ga ɗan’uwansa,

14 Na sani, na kuma tabbata, a tsakani na da Ubangiji Yesu, ba abin da yake marar tsarki ga asalinsa, sai dai ga wanda ya ɗauke shi marar tsarki ne yake marar tsarki.

15 In kuwa cimarka tana cutar ɗan’uwanka, ashe, ba zaman ƙauna kake yi ba. Kada fa cimarka ta hallaka wannan da Almasihu ya mutu dominsa.

16 Saboda haka kada abin da ka ɗauka kyakkyawa ya zama abin zargi ga waɗansu.

17 Ai, Mulkin Allah ba ga al’amarin ci da sha yake ba, sai dai ga adalci, da salama da farin ciki ta wurin Ruhu Mai Tsarki.

18 Wanda duk yake bauta wa Almasihu ta haka, abin karɓa ne ga Allah, yardajje ne kuma ga mutane.

19 Don haka sai mu himmantu ga yin abubuwan da suke kawo salama, suke kuma kawo inganta juna.

20 Kada ka rushe aikin Allah saboda abinci kawai. Hakika dukan abu mai tsarki ne, amma mugun abu ne mutum yă zama sanadin tuntuɓe ga wani, ta wurin abin da yake ci.

21 Ya kyautu kada ma ka ci nama, ko ka sha ruwan inabi, ko kuwa ka yi kowane irin abu, wanda zai sa ɗan’uwanku yin tuntuɓe.

22 Kana da bangaskiya? To, ka riƙe ta tsakaninka da Allah. Albarka tā tabbata ga wanda zuciyarsa ba ta ba shi laifi ba, a game da abin da hankalinsa ya ga daidai ne.

23 Wanda yake shakka, amma kuwa ya ci, ya sani ya yi laifi ke nan, domin ba da bangaskiya ya ci ba. Duk abin da ba na bangaskiya ba ne, zunubi ne.

Categories
ROM

ROM 15

Faranta wa Ɗan’uwanka Rai, ba kanka Ba

1 To, mu da muke ƙarfafa, ya kamata mu ɗauki nauyin raunana, kada mu yi sonkai.

2 Kowannenmu yă faranta wa maƙwabcinsa rai, don kyautata zamansa da kuma inganta shi.

3 Gama ko Almasihu ma bai yi sonkai ba, amma kamar yadda yake a rubuce cewa, “Zagin da waɗansu suka yi maka duk yā komo kaina.”

4 Ai, duk abin da aka rubuta tun dā, an rubuta shi ne domin a koya mana, domin mu ɗore a cikin sa zuciyar nan tamu ta wurin haƙuri da ta’aziyyar da Littattafai suke yi mana.

5 Allah mai ba da haƙuri da ta’aziyya, yă ba ku zaman lafiya da juna bisa halin Almasihu Yesu,

6 domin ku ɗaukaka Allah, Ubangijinmu Yesu Almasihu, da kuma Ubansa, nufinku ɗaya, bakinku ɗaya.

Bishara ga Al’ummai

7 Saboda haka ku karɓi juna da hannu biyu biyu, kamar yadda Almasihu ya karɓe ku hannu biyu biyu, domin a ɗaukaka Allah.

8 Ina dai gaya muku, Almasihu ya zama bara ga Isra’ila, domin nuna gaskiyar Allah, domin kuma tabbatar da alkawaran nan, da Allah ya yi wa kakannin kakanninmu,

9 al’ummai kuma su ɗaukaka Allah saboda jinƙansa. Yadda yake a rubuce,

“Domin haka zan yabe ka a cikin al’ummai,

In kuma yi waƙar yabon sunanka.”

10 Har wa yau kuma an ce,

“Ya ku al’ummai, ku yi ta farin ciki tare da jama’arsa.”

11 Da kuma,

“Ku yabi Ubangiji, ya ku al’ummai duka,

Dukkan kabilai kuma su yabe shi.”

12 Ishaya kuma ya ce,

“Tsatson Yesse zai bayyana,

Wanda zai tashi yă mallaki al’ummai,

A gare shi ne al’ummai za su sa zuciya.”

13 Allah mai kawo sa zuciya, yă cika ku da matuƙar farin ciki da salama saboda bangaskiyarku, domin ku yi matuƙar sa zuciya ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.

14 Ya ‘yan’uwana, ni ma da kaina na amince da ku, cewa ku da kanku masu nagarta ne ƙwarai da gaske, masu cikakken sani, kun kuma isa ku gargaɗi juna.

15 Duk da haka, a kan waɗansu batatuwan da na rubuto muku, na ƙara ƙarfafawa ƙwarai, domin tuni, saboda alherin da Allah ya yi mini

16 da ya sa ni bawan Almasihu Yesu ga al’ummai, ina hidimar bisharar Allah, domin al’ummai su zama hadaya mai karɓuwa a gare shi, tsattsarka ta wurin Ruhu Mai Tsarki.

17 Ashe kuwa, ina da dalilin yin alfarma da Almasihu Yesu a game da al’amarin Allah.

18 Ba zan kuskura in faɗi kome ba, sai abin da Almasihu ya aikata ta wurina, a wajen sa al’ummai biyayya ta wurin maganata da aikina,

19 ta wurin ikon mu’ujizai, da abubuwan al’ajabai, da kuma ta wurin ikon Ruhun, har dai daga Urushalima da kewayenta, har zuwa Ilirikun, na yi bisharar Almasihu a ko’ina.

20 Har ya zama mini abin buri in sanar da bishara, a inda ba a taɓa sanar da sunan Almasihu ba, don kada in ɗora ginina a kan harsashin wani,

21 sai dai kamar yadda yake a rubuce,

“Waɗanda ba a taɓa faɗa wa labarinsa ba, za su gane,

Waɗanda ba su taɓa jin labarinsa ba ma, za su fahimta.”

Bulus Ya Shirya yă Ziyarci Roma

22 Shi ya sa sau da yawa ban sami sukunin zuwa wurinku ba.

23 A yanzu kuwa tun da yake ba sauran wani wuri da ya rage mini a lardin nan, shekaru da yawa kuma ina ɗokin zuwa wurinku,

24 ina sa zuciya in gan ku, in zan wuce zuwa ƙasar Asbaniya, har ma ku raka ni zuwa can, bayan da na ɗan ɗebe kewa da ganinku.

25 Amma a yanzu kam, za ni Urushalima, don in kai wa tsarkaka gudunmawa.

26 Mutanen Makidoniya da na Akaya, sun ji daɗin yin gudunmawar daidai gwargwado ga matalauta, a cikin tsarkakan da suke a Urushalima.

27 Sun kuwa ji daɗin yin haka, domin hakika kamar bashi ne a kansu. Domin tun da yake al’ummai sun yi tarayya da su a kan ni’imarsu ta ruhu, ashe kuwa, ya kamata su ma su taimake su da ni’imarsu ta duniya.

28 In kuwa na gama wannan, na kuma danƙa musu wannan taimako lafiya, sai in bi ta kanku zuwa ƙasar Asbaniya.

29 Na kuma sani, in na zo wurinku, zan zo ne a cikin falalar albarkar Almasihu

30 Amma ina roƙonku ‘yan’uwa, saboda Ubangijinmu Yesu Almasihu, da kuma ƙaunar nan da Ruhu yake bayarwa, ku taya ni yin addu’a da naciya ga Allah saboda kaina,

31 domin in tsira daga maƙiyan bangaskiya a Yahudiya, don kuma gudunmawar da nake kaiwa Urushalima, ta zama abar karɓa ga tsarkaka,

32 har in Allah ya yarda in iso wurinku da farin ciki, mu wartsake tare.

33 Allah mai ba da salama ya kasance tare da ku duka. Amin.

Categories
ROM

ROM 16

Gaisuwa

1 Ga ‘yar’uwarmu Fibi ina sada ku da ita, ita ma kuwa mai hidimar ikilisiya ce a Kankiriya.

2 Ku karɓe ta da hannu biyu biyu saboda Ubangiji, ta halin da ya dace da tsarkaka. Ku kuma taimake ta da duk irin abin da ta nemi taimako a gare ku, domin ita ma tā taimaki mutane da yawa, har ma da ni kaina.

3 Ku gai da Bilkisu da Akila, abokan aikina a cikin Almasihu Yesu,

4 waɗanda suka kasai da ransu saboda ni, ba kuwa ni kaɗai nake gode musu ba, har ma da dukkan ikilisiyoyin al’ummai.

5 Ku kuma gai da ikilisiyar da take taruwa a gidansu. Ku gai da ƙaunataccena Abainitas, wanda yake shi ne ya fara bin Almasihu a ƙasar Asiya.

6 Ku gai da Maryamu, wadda ta yi muku aiki ƙwarai da gaske.

7 Ku gai da Andaranikas da Yuniyas, ‘yan’uwana, abokan ɗaurina, waɗanda suke shahararru a cikin manzanni, har ma sun riga ni bin Almasihu.

8 Ku gai da Amfiliyas, ƙaunataccena a cikin Ubangiji.

9 Ku gai da Urbanas abokin aikinmu a cikin Almasihu, da kuma ƙaunataccena Istakis.

10 Ku kuma gai da Abalis, amintaccen nan a cikin Almasihu. Ku gai da jama’ar Aristobulus.

11 Ku gai da ‘dan’uwana Hirudiyan. Ku gai da waɗanda suke na Ubangiji a cikin jama’ar Narkisas.

12 Ku gai da Tarafina da Tarafusa, masu aikin Ubangiji. Ku gai da Barsisa, ƙaunatacciya, wadda ta yi aikin Ubangiji ƙwarai da gaske.

13 Ku gai da Rufas, fitaccen mai bin Ubangiji, da kuma mahaifiyarsa, tawa kuma.

14 Ku gai da Asinkiritas, da Filiguna, da Hamisa, da Baturobas, da Hamasa, da kuma ‘yan’uwan da suke tare da su.

15 Ku gai da Filulugusa, da Yuliya, da Niriyas, da ‘yar’uwarsa, da Ulumfas da kuma dukan tsarkakan da suke tare da su.

16 Ku gaggai da juna da tsattsarkar sumba. Dukan ikilisiyoyin Almasihu suna gaishe ku.

17 Ina roƙonku, ‘yan’uwa, ku yi hankali fa da masu raba tsakani, saɓanin koyarwar da kuka koya, suna sa tuntuɓe. Ku yi nesa da su.

18 Ai, irin waɗannan mutane ba sa bauta wa Ubangijinmu Almasihu, sai dai cikinsu. Ta romon kunne da daɗin baki suke yaudarar masu sauƙin kai.

19 Amma ku kam, ai, kowa ya san biyayyarku, shi ya sa nake farin ciki da ku. Sai dai ina so ku gwanance da abin da yake nagari, amma ya zama ba ruwanku da mugunta.

20 Allah mai ba da salama kuwa, zai sa ku tattake Shaiɗan da hanzari. Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu yă tabbata a gare ku.

21 Timoti, abokin aikina, yana gaishe ku, haka kuma Lukiyas da Yason da kuma Susibataras, ‘yan’uwana.

22 Ni Tartiyas, mai rubuta wasiƙar nan, ina gaishe ku saboda Ubangiji.

23 Gayus, mai masaukina, mai kuma saukar da dukan ‘yan ikilisiya, yana gaishe ku. Arastas, ma’ajin gari, da kuma ɗan’uwanmu Kawartas, suna gaishe ku.

24 Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu yă tabbata a gare ku duka. Amin, Amin.

Ƙarasawa da Yabo

25 Ɗaukaka tă tabbata ga mai ikon ƙarfafa ku bisa ga bisharata, bisa ga wa’azin Yesu Almasihu, wadda ta gare ta ne aka bayyana asirin nan da yake ɓoye tun fil’azal.

26 Asirin nan kuwa sanar da shi ga dukan al’ummai, ta wurin littattafan annabawa, bisa ga umarnin Allah Madawwami, domin a jawo su, su gaskata, su yi biyayya.

27 Ɗaukaka tă tabbata har abada ga Allah Makaɗaicin hikima ta wurin Yesu Almasihu! Amin, Amin.