Categories
YAH

YAH 1

Kalman Ya Zama Mutum

1 Tun fil’azal akwai Kalma, Kalman nan kuwa tare da Allah yake, Kalman nan kuwa Allah ne.

2 Shi ne tun fil’azal yake tare da Allah.

3 Dukan abubuwa sun kasance ta gare shi ne, ba kuma abin da ya kasance na abubuwan da suka kasance, sai ta game da shi.

4 Shi ne tushen rai, wannan rai kuwa shi ne hasken mutane.

5 Haske na haskakawa cikin duhu, duhun kuwa bai rinjaye shi ba.

6 Akwai wani mutum da Allah ya aiko, mai suna Yahaya.

7 Shi fa ya zo shaida ne, domin ya shaidi hasken, kowa yă ba da gaskiya ta hanyarsa.

8 Ba shi ne hasken ba, ya zo ne domin ya shaidi hasken.

9 Akwai hakikanin haske mai shigowa duniya da yake haskaka kowane mutum.

10 Dā yana duniya, duniyar ta wurinsa ta kasance, duk da haka duniya ba ta san shi ba.

11 Ya zo ga abin mulkinsa ne, jama’a tasa kuwa ba ta karɓe shi ba.

12 Amma duk iyakar waɗanda suka karɓe shi, wato, masu gaskatawa da sunansa, ya ba su ikon zama ‘ya’yan Allah,

13 wato, waɗanda aka haifa ba daga jini ba, ba daga nufin jiki ko nufin mutum ba, amma daga wurin Allah.

14 Kalman nan kuwa ya zama mutum, ya zauna a cikinmu, yana mai matuƙar alheri da gaskiya. Mun kuma dubi ɗaukakarsa, ɗaukaka ce ta makaɗaicin Ɗa daga wurin Ubansa.

15 Yahaya ya shaida shi, ya ɗaga murya ya ce, “Wannan shi ne wanda na ce, ‘Mai zuwa bayana ya zama shugabana, domin dā ma yana nan tun ba ni.’ ”

16 Dukanmu kuwa daga falala tasa muka samu, alheri kan alheri.

17 Domin Shari’a, ta hannun Musa aka ba da ita, alheri da gaskiya kuwa ta wurin Yesu Almasihu suka kasance.

18 Ba mutumin da ya taɓa ganin Allah daɗai. Makaɗaicin Ɗa, wanda yake yadda Allah yake, wanda kuma yake a wurin Uba, shi ne ya bayyana shi.

Shaidar Yahaya Maibaftisma

19 Wannan kuwa ita ce shaidar Yahaya, wato, sa’ad da Yahudawa suka aiki firistoci da Lawiyawa daga Urushalima su tambaye shi, ko shi wane ne.

20 Sai ya faɗi gaskiya, bai yi musu ba, gaskiya ya faɗa ya ce, “Ba ni ne Almasihu ba.”

21 Sai suka tambaye shi, “To, yaya, Iliya ne kai?” Ya ce, “A’a, ba shi ba ne.” Suka ce, “Kai ne annabin nan?” Ya ce, “A’a.”

22 Sai suka ce masa, “To, wane ne kai, domin mu sami amsar da za mu mayar wa waɗanda suka aiko mu? Me kake ce da kanka?”

23 Ya ce, “Ni murya ce ta mai kira a jeji, mai cewa, ‘Ku miƙe wa Ubangiji tafarki,’ yadda Annabi Ishaya ya faɗa.”

24 Su kuwa, Farisiyawa ne suka aiko su.

25 Sai suka tambaye shi suka ce, “To, don me kake yin baftisma in kai ba Almasihu ba ne, ba kuwa Iliya ba, ba kuma annabin nan ba?”

26 Sai Yahaya ya amsa musu ya ce, “Ni kam, da ruwa nake baftisma, amma da wani nan tsaye a cikinku wanda ba ku sani ba,

27 shi ne mai zuwa bayana, wanda ko maɓallin takalminsa ma, ban isa in ɓalle ba.”

28 An yi wannan a Betanya ne, a hayin Kogin Urdun, inda Yahaya yake yin baftisma.

“Ga Ɗan Rago na Allah”

29 Kashegari Yahaya ya tsinkayo Yesu na nufo shi, sai ya ce, “Kun ga, ga Ɗan Rago na Allah, wanda zai ɗauke zunubin duniya!

30 Wannan shi ne wanda na ce, ‘Wani yana zuwa bayana, wanda ya zama shugabana, domin dā ma yana nan tun ba ni.’

31 Dā kam, ban san shi ba, sai domin a bayyana shi ga Isra’ila na zo, nake baftisma da ruwa.”

32 Yahaya ya yi shaida ya ce, “Na ga Ruhu na saukowa kamar kurciya daga sama, ya kuma zauna a kansa.

33 Dā kam, ban san shi ba, sai dai wanda ya aiko ni in yi baftisma da ruwa, shi ne ya ce mini, ‘Wanda ka ga Ruhun na sauko masa, yana kuma kasance a kansa, shi ne mai yin baftisma da Ruhu Mai Tsarki.’

34 Na kuwa gani, na kuma yi shaida, cewa wannan Ɗan Allah ne.”

Almajiran Yesu na Farko

35 Kashegari kuma Yahaya na tsaye da almajiransa biyu.

36 Yana duban Yesu na tafiya, sai ya ce, “Kun ga, ga Ɗan Rago na Allah!”

37 Almajiran nan biyu suka ji ya faɗi haka, sai suka bi Yesu.

38 Yesu ya waiwaya ya ga suna biye da shi, sai ya ce musu, “Me kuke nema?” Suka ce masa, “Ya Rabbi, wato Malam ke nan, ina kake da zama?”

39 Sai ya ce musu, “Ku zo ku gani.” Sai suka je suka ga inda yake da zama, suka kuwa yini tare da shi. Wajen ƙarfe huɗu na yamma ne kuwa.

40 Ɗaya daga cikin biyun nan da suka ji maganar Yahaya suka kuma bi Yesu, Andarawas ne, ɗan’uwan Bitrus.

41 Sai ya fara samo ɗan’uwansa Bitrus, ya ce masa, “Mun sami Almasihu,” wato shafaffe.

42 Sai ya kai shi wurin Yesu. Yesu ya dube shi, ya ce, “Wato kai ne Saminu ɗan Yahaya? Za a kira ka Kefas,” wato Bitrus.

Yesu Ya Kira Filibus da Nata’ala

43 Kashegari Yesu ya yi niyyar zuwa ƙasar Galili. Sai ya sami Filibus, ya ce masa, “Bi ni.”

44 Filibus kuwa mutumin Betsaida ne, garin su Andarawas da Bitrus.

45 Filibus ya sami Nata’ala, ya ce masa, “Mun sami wanda Musa ya rubuta labarinsa a Attaura, annabawa kuma suka rubuta labarinsa, wato Yesu Banazare, ɗan Yusufu.”

46 Nata’ala ya ce masa, “A iya samun wani abin kirki a Nazarat kuwa?” Sai Filibus ya ce masa, “Taho dai, ka gani.”

47 Yesu ya ga Nata’ala na nufo shi, sai ya yi zancensa ya ce, “Kun ga, ga Ba’isra’ile na gaske wanda ba shi da ha’inci!”

48 Nata’ala ya ce masa, “A ina ka san ni?” Yesu ya amsa masa ya ce, “Tun kafin Filibus ya kira ka, sa’ad da kake gindin ɓaure, na gan ka.”

49 Sai Nata’ala ya amsa masa ya ce, “Ya Shugaba, kai Ɗan Allah ne! Kai Sarkin Isra’ila ne!”

50 Yesu ya amsa ya ce, “Wato, domin na ce maka na gan ka a gindin ɓaure ne kake ba da gaskiya? Ai, za ka ga al’amuran da suka fi haka ma.”

51 Yesu kuma ya ce masa, “Lalle hakika, ina gaya muku, za ku ga sama ta dāre, mala’ikun Allah suna hawa da sauka ga Ɗan Mutum.”

Categories
YAH

YAH 2

Biki a Kana ta Galili

1 A rana ta uku sai aka yi bikin aure a Kana ta ƙasar Galili. Uwar Yesu kuwa tana nan,

2 aka kuma gayyaci Yesu da almajiransa.

3 Da ruwan inabi ya gaza, uwar Yesu ta ce masa, “Ba su da sauran ruwan inabi.”

4 Yesu ya ce mata, “Iya, ai, wannan magana ba taki ba ce. Lokacina bai yi ba tukuna.”

5 Sai uwa tasa ta ce wa barorin, “Duk abin da ya ce ku yi, sai ku yi.”

6 A wurin kuwa akwai randuna shida na dutse a ajijjiye, bisa ga al’adar Yahudawa ta tsarkakewa, kowacce na cin wajen tulu shida shida.

7 Sai Yesu ya ce musu, “Ku cika randunan nan da ruwa.” Suka ciccika su fal.

8 Sa’an nan ya ce musu, “To, yanzu ku ɗiba, ku kai wa uban bikin.” Sai suka kai.

9 Da uban bikin ya kurɓi ruwan da yanzu aka mayar ruwan inabi, bai kuwa san inda aka samo shi ba (amma barorin da suka ɗebo ruwan sun sani), ya yi magana da ango,

10 ya ce, “Kowa, ai, kyakkyawan ruwan inabi yakan fara bayarwa, bayan mutane sun shassha, sa’an nan kuma ya kawo wanda ya gaza na farin kyau. Amma kai ka ɓoye kyakkyawan ruwan inabin sai yanzu!”

11 Wannan ce mu’ujizar farko da Yesu ya yi, ya kuwa yi ta ne a Kana ta ƙasar Galili, ya bayyana ɗaukakarsa. Almajiransa kuma suka gaskata da shi.

12 Bayan haka sai ya tafi Kafarnahum, da shi da uwa tasa, da ‘yan’uwansa, da kuma almajiransa, suka zauna a can ‘yan kwanaki.

Yesu Ya Tsabtace Haikali

13 Idin Ƙetarewa na Yahudawa ya matso, sai Yesu ya tafi Urushalima.

14 A cikin Haikali ya sami waɗansu dillalan shanu, da na tumaki, da na tattabarai, da kuma ‘yan canjin kuɗi zaune wurin aikinsu.

15 Sai ya tuka bulala mai harsuna ta igiya, ya kore su duka daga Haikalin, har da tumakin da shanun, ya kuma watsar da kuɗin ‘yan canjin, ya birkice teburorinsu.

16 Ya ce da dillalan tattabarai, “Ku kwashe waɗannan daga nan, kada ku mai da Haikalin Ubana kasuwa.”

17 Sai almajiransa suka tuna a rubuce yake cewa, “Kishin Haikalinka ya ci raina matuƙa.”

18 Sai Yahudawa suka amsa masa suka ce, “Wace mu’ujiza za ka nuna mana da kake haka?”

19 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku rushe Haikalin nan, ni kuwa in ta da shi a cikin kwana uku.”

20 Yahudawa suka ce, “Sai fa da aka shekara arba’in da shida ana ginin Haikalin nan, kai kuwa a cikin kwana uku za ka ta da shi?”

21 Amma haikalin da Yesu ya ambata jikinsa ne.

22 Saboda haka bayan an tashe shi daga matattu, almajiransa suka tuna ya faɗi haka, suka kuma gaskata Nassi da maganar da Yesu ya faɗa.

Yesu Ya San Zuciyar Kowa

23 To, sa’ad da yake Urushalima lokacin Idin Ƙetarewa, mutane da yawa suka gaskata da sunansa, saboda ganin mu’ujizan da ya yi.

24 Amma Yesu bai amince da su ba,

25 domin ya san zuciyar kowa, ba kuma sai wani ya shaidi mutum a wurinsa ba, domin shi kansa ya san abin da yake zuciyar ɗan adam.

Categories
YAH

YAH 3

Yesu da Nikodimu

1 To, akwai wani Bafarisiye, sunansa Nikodimu, wani shugaban Yahudawa.

2 Wannan mutum ya zo wurin Yesu da dad dare, ya ce masa, “Ya Shugaba, mun sani kai malami ne da ka zo daga wurin Allah, domin ba mai iya yin waɗannan mu’ujizan da kake yi, sai ko Allah yana tare da shi.”

3 Yesu ya amsa masa ya ce, “Lalle hakika, ina gaya maka, in ba a sāke haifar mutum ba, ba zai iya ganin Mulkin Allah ba.”

4 Nikodimu ya ce masa, “Ƙaƙa za a haifi mutum bayan ya tsufa? Wato, ya iya komawa a cikin uwa tasa ta sāke haifo shi?”

5 Yesu ya amsa masa ya ce, “Lalle hakika, ina gaya maka, in ba an haifi mutum ta ruwa da kuma Ruhu ba, ba zai iya shiga Mulkin Allah ba.

6 Abin da mutum ya haifa mutum ne, abin kuma da Ruhu ya haifa ruhu ne.

7 Kada ka yi mamaki domin na ce maka, ‘Dole a sāke haifarku.’

8 Iska tana busawa inda ta ga dama. Kakan ji motsinta, amma ba ka san inda ta fito da inda za ta. Haka fa yake ga duk wanda Ruhu ya haifa.”

9 Sai Nikodimu ya amsa masa ya ce, “Ƙaƙa wannan zai yiwu?”

10 Yesu ya amsa masa ya ce, “Ashe, kai ma da kake malamin Isra’ila, ba ka fahimci waɗannan al’amura ba?

11 Lalle hakika, ina gaya maka, abin da muka sani shi muke faɗa, muna kuma shaidar da abin da muka gani, amma kun ƙi yarda da shaidarmu.

12 In na yi muku zancen al’amuran duniya ba ku gaskata ba, yaya za ku gaskata in na yi muku zancen al’amuran sama?

13 Ba wanda ya taɓa hawa cikin Sama sai shi wanda ya sauko daga Sama, wato, Ɗan Mutum da yake Sama.

14 Kamar yadda Musa ya ɗaga macijin nan a jeji, haka kuma dole ne a ɗaga Ɗan Mutum,

15 domin duk wanda ya gaskata da shi, ya sami rai madawwami.

16 “Saboda ƙaunar da Allah ya yi wa duniya har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin duk wanda ya gaskata da shi kada ya hallaka, sai dai ya sami rai madawwami.

17 Gama Allah bai aiko Ɗansa duniya domin yă yanke mata hukunci ba, sai dai domin duniya ta sami ceto ta wurinsa.

18 Duk wanda ya gaskata da shi, ba za a yi masa hukunci ba. Wanda kuwa bai ba da gaskiya ba, an riga an yi masa hukunci, domin bai gaskata da sunan makaɗaicin Ɗan Allah ba.

19 Hukuncin kuwa shi ne, haske ya shigo duniya, amma mutane suka fi ƙaunar duhu da hasken, don ayyukansu mugaye ne.

20 Duk mai yin rashin gaskiya yakan ƙi hasken, ba ya kuma zuwa wajen hasken, don kada ayyukansa su tonu.

21 Mai aikata gaskiya kuwa yakan zo wajen hasken, domin a bayyana ayyukansa, cewa, da taimakon Allah ne aka yi su.”

Shi Lalle Ya Riƙa Ƙaruwa, Ni kuwa Raguwa

22 Bayan haka, Yesu da almajiransa suka tafi ƙasar Yahudiya. A nan ya jima da su, yana yin baftisma.

23 Yahaya kuma yana yin baftisma a Ainon kusa da Salima, domin da ruwa da yawa a can. Mutane kuwa suka yi ta zuwa ana yi musu baftisma.

24 Domin a sa’an nan ba a sa Yahaya a kurkuku ba tukuna.

25 Sai fa almajiran Yahaya suka tasar wa wani Bayahude da muhawara a kan maganar tsarkakewa.

26 Suka kuma zo wurin Yahaya, suka ce masa, “Ya shugaba, wanda dā kuke tare a hayin Kogin Urdun, wanda kai kanka ma ka shaida shi, to, ga shi, yana yin baftisma, har kowa da kowa yana zuwa wurinsa.”

27 Sai Yahaya ya amsa ya ce, “Ba mai iya samun kome sai ko an ba shi daga Sama.

28 Ku kanku ma shaiduna ne a kan na ce ba ni ne Almasihu ba, amma an aiko ni ne ni riga shi gaba.

29 Mai amarya shi ne ango. Abokin ango kuwa da yake tsaye, yake kuma sauraron magana tasa, yakan yi farin ciki ƙwarai da jin muryar angon. Saboda haka farin cikin nan nawa ya cika.

30 Shi kam, lalle ne ya riƙa ƙaruwa, ni kuwa in riƙa raguwa.

Wanda Ya Zo daga Sama

31 “Mai zuwa daga Sama yana Sama da kowa. Wanda yake na ƙasa asalinsa kuwa na ƙasa ne, maganar ƙasa kuma yake yi. Mai zuwan nan daga Sama yana Sama da kowa.

32 Abin da ya ji, ya kuma gani, shi yake shaidarwa, duk da haka ba wanda yake yarda da shaidarsa.

33 Duk wanda ya yarda da shaidarsa, ya haƙƙaƙe, cewa, Allah mai gaskiya ne.

34 Domin wanda Allah ya aiko, zantuttukan Allah yake faɗa, gama Allah yana ba da Ruhu ba da iyakancewa ba.

35 Uban yana ƙaunar Ɗan, ya kuma sa kome a hannunsa.

36 Wanda ya gaskata da Ɗan, yana da rai madawwami. Wanda ya ƙi bin Ɗan kuwa, ba zai sami rai ba, sai dai fushin Allah ya tabbata a gare shi.”

Categories
YAH

YAH 4

Yesu da Wata Basamariya

1 To, da Ubangiji Yesu ya sani dai Farisiyawa sun ji labari yana samun almajirai, yana kuma yi musu baftisma fiye da Yahaya

2 (ko da yake dai ba Yesu kansa yake yin baftisma ba, almajiransa ne),

3 sai ya bar ƙasar Yahudiya, ya koma ƙasar Galili.

4 Lalle ne kuwa yă ratsa ƙasar Samariya.

5 Sai ya zo wani gari na ƙasar Samariya, wanda ake kira Saikar, kusa da yankin ƙasar da Yakubu ya ba ɗansa Yusufu.

6 Rijiyar Yakubu kuwa a nan take. Saboda gajiyar tafiya fa, sai Yesu ya zauna haka nan a bakin rijiyar. Wajen tsakar rana ce kuwa.

7 Sai ga wata Basamariya ta zo ɗiban ruwa. Yesu ya ce mata, “Sa mini ruwa in sha.”

8 Almajiransa kuwa sun shiga gari sayen abinci.

9 Sai Basamariyar ta ce masa, “Ƙaƙa kai Bayahude za ka roƙe ni ruwan sha, ni da nake Basamariya?” (Don Yahudawa ba sa cuɗanya da Samariyawa).

10 Yesu ya amsa mata ya ce, “Da kin san kyautar Allah, da kuma wanda ya ce miki, ‘Sa mini ruwa in sha,’ ai, da kin roƙe shi, shi kuwa zai ba ki ruwan rai.”

11 Sai matar ta ce masa, “Ya Shugaba, ai, ba ka da guga, rijiyar kuwa da zurfi. To, ina ka sami ruwan nan na rai?

12 Ashe, ka fi ubanmu Yakubu ne, wanda ya bar mana rijiyar, har shi da kansa, da ‘yayansa, da dabbobinsa, suka sha ruwanta?”

13 Yesu ya amsa mata ya ce, “Duk mai shan ruwan nan zai sāke jin ƙishirwa.

14 Amma duk wanda ya sha ruwan da zan ba shi, ba zai ƙara jin ƙishirwa ba har abada. Ruwan da zan ba shi kuwa zai zama maɓuɓɓuga a gare shi, yana ɓuɓɓugowa har ya zuwa rai madawwami.”

15 Matar ta ce masa, “Ya Shugaba, ka ba ni ruwan nan, don kada in ƙara jin ƙishirwa, kada kuma in riƙa zuwa har nan in ɗiba.”

16 Sai Yesu ya ce mata, “Je ki, ku zo da mijinki.”

17 Sai matar ta amsa ta ce, “Ai, ba ni da miji.” Yesu ya ce mata, “Gaskiyarki da kika ce ba ki da miji,

18 don kin auri maza biyar, wanda kuke tare yanzu kuwa ba mijinki ba ne. A nan kam kin yi gaskiya.”

19 Matar ta ce masa, “Ya Shugaba, na dai gane kai annabi ne.

20 Kakanninmu sun yi sujada a dutsen nan. Ku kuwa kun ce a Urushalima ne wurin da ya wajaba a yi sujada yake.”

21 Sai Yesu ya ce mata, “Uwargida, ki gaskata ni, lokaci na zuwa da ba za ku yi wa Uba sujada ba, ko a kan dutsen nan, ko a Urushalima,

22 Ku kuna yi wa abin da ba ku sani ba sujada, mu kuwa muna yi wa abin da muka sani sujada, domin ceto ta hanyar Yahudawa yake.

23 Amma lokaci na zuwa, har ma ya yi, da masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada a ruhu, da gaskiya kuma. Lalle kuwa irin waɗannan masu sujada ne Uba yake nema.

24 Allah Ruhu ne, masu yi masa sujada kuwa lalle su yi masa sujada a ruhu, da gaskiya kuma.”

25 Sai matar ta ce masa, “Na san Masihi yana zuwa, wanda ake kira Almasihu. Sa’ad da ya zo kuwa, zai sanar da mu kome.”

26 Yesu ya ce mata, “Ni ne, ni mai maganan nan da yake.”

27 Nan take almajiransa suka dawo. Suka yi mamakin ganin yana magana da mace. Amma kuwa ba wanda ya ce, “Me kike bukata?” ko, “Don me kake magana da ita?”

28 Sai matar ta bar tulunta, ta koma gari, ta ce wa mutane,

29 “Ku zo, ku ga mutumin da ya gaya mini duk abin da na taɓa yi! Shin, ko wannan shi ne Almasihu?”

30 Sai suka fito daga garin suka nufo shi.

31 Ana cikin haka sai almajiran suka roƙe shi suka ce, “Ya shugaba, ci abinci.”

32 Amma ya ce musu, “Ina da abincin da ba ku sani ba.”

33 Almajiran suka ce wa juna, “Shin, wani ya kawo masa abinci ne?”

34 Sai Yesu ya ce musu, “Abincina shi ne in aikata nufin wanda ya aiko ni, in kuma cika aikinsa.

35 Ba kuna cewa, kaka saura wata huɗu ba? Ina gaya muku fa, ku duba gonaki, ku gani, sun nuna sun isa girbi.

36 Mai girbi na samun lada, yana kuma tara amfani zuwa rai madawwami, domin mai shuka da mai girbi su yi farin ciki tare.

37 A nan kam, wannan karin maganar gaskiya ne cewa, ‘Wani da shuka, wani da girbi.’

38 Na aike ku girbin abin da ba ku yi wahalarsa ba. Waɗansu sun yi wahala, ku kuwa kun mori wahalarsu.”

39 Samariyawa da yawa na wannan gari suka gaskata da shi saboda maganar matan nan da ta ce, “Ya gaya mini duk abin da na taɓa yi.”

40 Da Samariyawa suka iso wurinsa, suka roƙe shi ya sauka a wurinsu. Ya kuwa kwana biyu a nan.

41 Waɗansu kumma da yawa fiye da na dā suka ba da gaskiya saboda magana tasa.

42 Sa’an nan suka ce wa macen, “Yanzu kam, mun ba da gaskiya, ba don abin da kika faɗa kawai ba, domin mu ma mun ji da kanmu, mun kuma tabbata lalle wannan shi ne Mai Ceton duniya.”

Yesu Ya Warkar da Ɗan Bafada

43 Bayan kwana biyun nan sai ya tashi daga nan ya tafi ƙasar Galili.

44 Domin Yesu kansa ya yi shaida cewa annabi ba shi da girma a ƙasarsu.

45 Da ya isa ƙasar Galili, sai Galilawa suka yi na’am da shi, domin sun ga duk abin da ya yi a Urushalima a lokacin idi, domin su ma sun je idin.

46 Sai ya sāke zuwa Kana ta ƙasar Galili, inda ya mai da ruwa ruwan inabi. A Kafarnahum kuwa akwai wani bafada wanda ɗansa ba shi da lafiya.

47 Da jin cewa Yesu ya fito ƙasar Yahudiya ya komo ƙasar Galili, sai ya tafi wurinsa, ya roƙe shi ya je ya warkar da ɗansa, don yana bakin mutuwa.

48 Yesu ya ce masa, “In ba mu’ujizai da abubuwan al’ajabi kuka gani ba, ba yadda za a yi ku ba da gaskiya.”

49 Sai bafadan nan ya ce masa, “Ya Shugaba, ka zo tun ƙaramin ɗana bai mutu ba.”

50 Yesu ya ce masa, “Yi tafiyarka, ɗanka a raye yake.” Mutumin kuwa ya gaskata maganar da Yesu ya faɗa masa, ya yi tafiyarsa.

51 Yana cikin tafiya sai ga barorinsa sun taryo shi, suka ce masa, “Ɗanka a raya yake.”

52 Sai ya tambaye su ainihin lokacin da ya fara samun sauƙi. Suka ce masa, “Jiya da ƙarfe ɗaya na rana zazzaɓin ya sake shi.”

53 Sai uban ya gane, daidai lokacin nan ne, Yesu ya ce masa, “Ɗanka a raye yake.” Shi da kansa kuwa ya ba da gaskiya, da jama’ar gidansa duka.

54 Wannan kuwa ita ce mu’ujiza ta biyu da Yesu ya yi, bayan Komowarsa ƙasar Galili daga ƙasar Yahudiya.

Categories
YAH

YAH 5

Warkarwa a Tafkin Betasda

1 Bayan haka aka yi wani idi na Yahudawa, Yesu kuwa ya tafi Urushalima.

2 A Urushalima, kusa da Ƙofar Tumaki, akwai wani ruwa da ake ce da shi Betasda da Yahudanci, an kuwa kewaye shi da shirayi biyar.

3 A shirayin nan kuwa marasa lafiya da yawa sun saba kwanciya, makafi, da guragu, da shanyayyu. [Suna jira a motsa ruwan.

4 Don lokaci lokaci wani mala’ika yakan sauko cikin ruwan ya motsa shi. Duk kuwa wanda ya fara shiga bayan an motsa ruwan, sai ya warke daga duk irin cutar da yake da ita.]

5 A nan kuwa akwai wani mutum da ya shekara talatin da takwas da rashin lafiya.

6 Da Yesu ya gan shi kwance, ya kuma sani ya daɗe da wannan hali, sai ya ce masa, “Kana so a warkar da kai?”

7 Marar lafiyar ya amsa masa ya ce, “Ya Shugaba, ai, ba ni da wanda zai angaza ni cikin ruwan lokacin da aka motsa shi. Lokacin da na doshi ruwan kuma sai wani ya riga ni shiga.”

8 Sai Yesu ya ce masa, “Tashi, ka ɗauki shimfiɗarka, ka yi tafiya!”

9 Nan take mutumin ya warke, ya ɗauki shimfiɗarsa ya yi tafiya tasa.

Ran nan kuwa Asabar ce.

10 Saboda haka Yahudawa suka ce da wanda aka warkar ɗin, “Ai, Asabar ce, bai kuwa halatta ka ɗauki shimfiɗarka ba.”

11 Sai ya amsa musu ya ce, “Ai, wanda ya warkar da ni, shi ne ya ce in ɗauki shimfiɗata, in tafi.”

12 Suka tambaye shi, “Wane mutum ne ya ce maka ka ɗauki shimfiɗarka ka tafi?”

13 Wanda aka warkar ɗin kuwa bai san ko wane ne ba, domin Yesu ya riga ya tashi saboda taron da yake wurin.

14 Bayan haka Yesu ya same shi a Haikali, ya ce masa, “Ka ga fa, ka warke! To, ka daina yin zunubi, don kada wani abu da ya fi wannan muni ya same ka.”

15 Sai mutumin ya tafi ya gaya wa Yahudawa, Yesu ne ya warkar da shi.

16 Saboda haka, Yahudawa suka fara tsananta wa Yesu, don yana yin irin waɗannan abubuwa ran Asabar.

17 Yesu kuwa ya amsa musu ya ce, “Ubana yana aiki har yanzu, ni ma ina yi.”

18 Don haka, Yahudawa suka ƙara nema su kashe shi, ba don ya keta Asabar kaɗai ba, har ma domin ya ce Allah Ubansa ne, wato, yana daidaita kansa da Allah.

Ikon Ɗan

19 Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku, Ɗan ba ya yin kome shi kaɗai, sai abin da ya ga Uba yana yi. Domin duk abin da Uban yake yi, haka shi Ɗan ma yake yi.

20 Domin Uban na ƙaunar Ɗan, yana kuma nuna masa duk abin da shi kansa yake yi, har ma zai nuna masa ayyukan da suka fi waɗannan, domin ku yi al’ajabi.

21 Yadda Uba yake ta da matattu ya kuma raya su, haka Ɗan ma yake rayar da wanda ya nufa.

22 Uba ba ya hukunta kowa, sai dai yā danƙa dukkan hukunci ga Ɗan,

23 domin kowa yă girmama Ɗan, kamar yadda ake girmama Uban. Wanda ba ya girmama Ɗan, ba ya girmama Uban da ya aiko shi ke nan.

24 Lalle hakika, ina gaya muku, duk mai jin maganata, yake kuma gaskata wanda ya aiko ni, yana da rai madawwami. Ba za a yi masa hukunci ba, domin ya riga ya tsere wa mutuwa, ya kai ga rai.

25 “Lalle hakika, ina gaya muku, lokaci na zuwa, har ma ya yi, da matattu za su ji muryar Ɗan Allah, masu ji kuwa su rayu.

26 Yadda Uba kansa yake tushen rai, haka ya sa Ɗan ya zama tushen rai.

27 Ya kuma ba shi ikon zartar da hukunci, saboda shi Ɗan Mutum ne.

28 Kada ku yi mamakin wannan, domin lokaci na zuwa da duk waɗanda suke kaburbura za su ji murya tasa,

29 su kuma fito, waɗanda suka aikata nagarta su tashi, tashin rai, waɗanda suka yi rashin gaskiya kuwa su tashi, tashin hukunci.

Shaidun Yesu

30 “Ba na iya yin kome ni kaɗai. Yadda nake ji, haka nake yin hukunci. Hukuncina kuwa na adalci ne, domin ba nufin kaina nake bi ba, sai dai nufin wanda ya aiko ni.

31 In na shaida kaina, shaidata ba tabbatacciya ba ce.

32 Akwai wani mashaidina dabam, na kuwa san shaidar da yake yi mini tabbatacciya ce.

33 Kun aika wajen Yahaya, shi kuma ya shaidi gaskiya.

34 Duk da haka shaidar da na dogara da ita ba ta mutum ba ce. Na dai faɗi haka ne domin ku sami ceto.

35 Yahaya fitila ne mai ci, mai haske kuma, kun kuwa yarda ku yi farin ciki matuƙa da haskensa ɗan lokaci kaɗan.

36 Amma shaidar da ni nake da ita ta fi ta Yahaya ƙarfi. Domin ayyukan da Uba ya ba ni in gama, su ainihin ayyukan nan da nake yi, ai, su ne shaidata a kan cewa, Uba ne ya aiko ni.

37 Uban kuma da ya aiko ni, shi kansa ya shaide ni. Ba ku taɓa jin muryarsa ba, ko ganin kama tasa.

38 Maganarsa kuwa ba ta zauna a zuciyarku ba, domin ba ku gaskata wanda ya aiko ni ba.

39 Kuna ta nazarin Littattafai, don a tsammaninku a cikinsu za ku sami rai madawwami, alhali kuwa su ne suke shaidata.

40 Duk da haka, kun ƙi zuwa wurina ku sami rai.

41 Ba na karɓar girma wurin mutane.

42 Amma fa na san ku, ba ku da ƙaunar Allah a zuci.

43 Ni na zo ne da sunan Ubana, ga shi, ba ku karɓe ni ba. In da wani zai zo da sunan kansa, shi za ku karɓa.

44 Ta yaya za ku ba da gaskiya, ku da kuke karɓar girma a junanku, girman da yake daga Allah Makaɗaici kuwa, ba kwa nemansa?

45 Kada ku zaci zan yi ƙararku wurin Uba. Akwai mai yin ƙararku, shi ne Musa, wanda kuke dogara da shi.

46 Da dai kun gaskata Musa, da kun gaskata ni, domin labarina ya rubuta.

47 In kuwa ba ku gaskata abin da ya rubuta ba, ta yaya za ku gaskata maganata?”

Categories
YAH

YAH 6

Ciyar da Mutum Dubu Biyar

1 Bayan haka Yesu ya haye Tekun Galili, wato Tekun Tibariya.

2 Sai taro mai yawa suka bi shi, don sun ga mu’ujizan da yake yi ga marasa lafiya.

3 Sai Yesu ya hau dutse ya zauna a can tare da almajiransa.

4 To, Idin Ƙetarewa, wato idin Yahudawa, ya gabato.

5 Da Yesu ya ɗaga kai ya hango babban taro yana doso shi, sai ya ce wa Filibus, “Ina za mu sayo gurasar da mutanen nan za su ci?”

6 Ya faɗi haka ne fa domin ya gwada shi, saboda shi kansa ya san abin da zai yi.

7 Filibus ya amsa ya ce, “Ai, ko gurasar dinari metan ma ba ta isa ko wannensu ya sami kaɗan ba.”

8 Sai Andarawas ɗan’uwan Bitrus ɗaya daga cikin almajiransa, ya ce masa,

9 “Ga wani ɗan yaro nan da gurasa biyar na sha’ir, da kuma kifi biyu. Amma me waɗannan za su yi wa mutane masu yawa haka?”

10 Yesu ya ce, “Ku ce wa mutane su zauna.” Wuri ne kuwa mai ciyawa. Sai mazaje suka zazzaune, su wajen dubu biyar.

11 Yesu ya ɗauki gurasar, bayan ya yi godiya ga Allah kuma, sai ya rarraba wa waɗanda suke zazzaune. Haka kuma ya yi da kifin, gwargwadon abin da ya ishe su.

12 Da suka ci suka ƙoshi, sai ya ce wa almajiransa, “Ku tattara gutsattsarin da suka saura, kada kome ya ɓata.”

13 Sai suka tattara gutsattsarin gurasar nan biyar na sha’ir da suka saura bayan kowa ya ci, suka cika kwando goma sha biyu.

14 Da jama’a suka ga mu’ujizar da ya yi, suka ce, “Lalle, wannan shi ne annabin nan mai zuwa duniya.!”

15 Da Yesu ya gane suna shirin zuwa su ɗauke shi ƙarfi da yaji su naɗa shi sarki, sai ya sāke komawa kan dutsen shi kaɗai.

Yesu na Tafiya a kan Ruwan Teku

16 Da magariba ta yi, sai almajiransa suka gangara teku.

17 Suka shiga jirgi suka tasar wa haye tekun zuwa Kafarnahun. A sa’an nan duhu ya yi, Yesu kuwa bai zo wurinsu ba tukuna.

18 Sai tekun ta fara hauka saboda wata riƙaƙƙiyar iska da take busowa.

19 Bayan sun yi tuƙi wajen mil uku ko huɗu, sai suka hango Yesu yana tafiya a kan ruwan, ya kusato jirgin. Sai suka firgita.

20 Amma ya ce musu, “Ni ne, kada ku ji tsoro.”

21 Sa’an nan suka yarda suka karɓe shi a cikin jirgin. Nan da nan sai ga jirgin a gāɓar da za su.

Taro sun Nemi Yesu

22 Kashegari sauran taron da suka tsaya a hayin tekun suka lura ba wani jirgi a wurin, sai wani ɗan ƙarami, suka kuma lura Yesu bai shiga cikinsa tare da almajiransa ba, sai almajiran ne kaɗai suka tafi.

23 Akwai kuwa waɗansu ƙananan jirage daga Tibariya da suka iso kusa da wurin nan da taron suka ci gurasa bayan Ubangiji ya yi godiya.

24 Sa’ad da kuwa taron suka ga ba Yesu, ba almajiransa a nan, su ma suka shiga ƙananan jiragen, suka tafi Kafarnahum neman Yesu.

Yesu Gurasar Rai

25 Da suka same shi a hayin tekun, suka ce masa, “Ya Shugaba, yaushe ka zo nan?”

26 Yesu ya amsa musu ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku, kuna nemana ne ba don kun ga mu’ujizai ba, sai don kun ci gurasar nan kun ƙoshi.

27 Kada ku yi wahala a kan neman abinci mai lalacewa, sai dai a kan abinci mai dawwama har ya zuwa rai madawwami, wanda Ɗan Mutum zai ba ku. Domin shi ne wanda Uba, wato Allah, ya tabbatar wa da ikon yin haka.”

28 Sai suka ce masa, “Me za mu yi mu aikata ayyukan da Allah yake so?”

29 Yesu ya amsa musu ya ce, “Wannan shi ne aikin da Allah yake so, wato ku gaskata da wanda ya aiko.”

30 Sai suka ce masa, “To, wace mu’ujiza za ka yi mu gani mu gaskata ka? Me za ka yi?

31 Kakannin kakanninmu sun ci manna a jeji, yadda yake a rubuce cewa, ‘Ya ba su gurasa daga Sama su ci.’ ”

32 Sa’an nan Yesu ya ce musu, “Lalle hakika, ina gaya muku, ba Musa ne ya ba ku gurasar nan daga Sama ba, Ubana ne yake ba ku hakikanin Gurasa daga Sama.

33 Ai, Gurasan Allah shi ne mai saukowa daga Sama, mai ba duniya rai.”

34 Sai suka ce masa, “Ya Ubangiji, ka riƙa ba mu irin wannan gurasa kullum!”

35 Yesu ya ce musu, “Ni ne gurasa mai ba da rai. Wanda ya zo gare ni ba zai ji yunwa ba har abada, wanda kuma ya gaskata da ni ba zai ƙara jin ƙishirwa ba har abada.

36 Na dai gaya muku, kun gan ni, duk da haka ba ku ba da gaskiya ba.

37 Duk wanda Uba ya ba ni zai zo gare ni, wanda kuwa ya zo gare ni ba zan kore shi ba ko kaɗan.

38 Domin na sauko daga Sama, ba domin in bi nufin kaina ba, sai dai nufin wanda ya aiko ni.

39 Nufin wanda ya aiko ni kuwa, shi ne kada in yar da kowa daga cikin dukkan waɗanda ya ba ni, sai dai in tashe su a ranar ƙarshe.

40 Gama nufin Ubana, shi ne duk wanda yake duban Ɗan, yake kuma gaskatawa da shi, yă sami rai madawwani, ni kuma zan tashe shi a ranar ƙarshe.”

41 Sai fa Yahudawa suka yi masa gunaguni, domin ya ce, “Ni ne Gurasan da ya sauko daga Sama.”

42 Suka ce, “Ashe, wannan ba Yesu ba ne, ɗan Yusufu, wanda uwa tasa da ubansa duk mun san su? To, yaya yanzu zai ce, ‘Na sauko ne daga sama’?”

43 Yesu ya amsa musu ya ce, “Kada ku yi gunaguni a junanku.

44 Ba mai iya zuwa wurina, sai dai in Uba wanda ya aiko ni ne ya jawo shi, ni kuwa zan tashe shi a ranar ƙarshe.

45 A rubuce yake cikin littattafan annabawa cewa, ‘Dukkansu Allah ne zai koya musu.’ To, duk wanda ya ji, ya kuma koya wurin Uba, zai zo gare ni.

46 Ba wai don wani ya taɓa ganin Uban, sai shi wanda yake daga wurin Allah, shi ne ya ga Uban.

47 Lalle hakika ina gaya muku, wanda ya ba da gaskiya, yana da rai madawwami.

48 Ni ne Gurasa mai ba da rai.

49 Kakannin kakanninku sun ci manna a jeji, amma kuwa sun mutu.

50 Ga Gurasa mai saukowa daga Sama, domin kowa yă ci, kada ya mutu.

51 Ni ne Gurasan rai da ya sauko daga Sama. Kowa ya ci Gurasan nan, zai rayu har abada. Har ma gurasar da zan bayar naman jikina ne, domin duniya ta rayu.”

52 Sai Yahudawa suka ta da husuma a junansu, suna cewa, “Yaya mutumin nan zai iya ba mu naman jikinsa mu ci?”

53 Sai Yesu ya ce musu, “Lalle hakika, ina gaya muku, in ba ku ci naman jikin Ɗan Mutum ba, kuka kuma sha jininsa, ba rai a gare ku.

54 Duk wanda suke cin naman jikina, yake kuma shan jinina, yana da rai madawwami, ni kuwa zan tashe shi a ranar ƙarshe.

55 Domin naman jikina abinci ne na hakika, jinina kuma abin sha ne na hakika.

56 Duk wanda suke cin naman jikina, yake shan jinina, a cikina yake zaune, ni kuma a cikinsa.

57 Kamar yadda rayayyen Uba ya aiko ni, nake kuma rayuwa saboda Uban, haka ma wanda yake ni ne abincinsa zai rayu saboda ni.

58 Wannan shi ne Gurasan da ya sauko daga Sama, ba irin wadda kakannin kakanninku suka ci ba, duk da haka suka mutu. Duk mai cin Gurasan nan zai rayu har abada.”

59 Wannan kuwa a majami’a ya faɗa, sa’ad da yake koyarwa a Kafarnahum.

Kalmomin Rai

60 Da jin haka, da yawa daga cikin almajiransa suka ce, “Wannan magana mai wuya ce, wa zai iya jinta?”

61 Yesu kuwa, da yake ya sani a ransa almajiransa suna gunagunin wannan, sai ya ce musu, “Wato, wannan ne ya zamar muku abin tuntuɓe?

62 Yaya ke nan in kuka ga Ɗan Mutum yana hawa inda yake dā?

63 Ai, Ruhu shi ne mai rayarwa, jiki kam ba ya amfana kome. Kalmomin da na faɗa muku ruhu ne, da kuma rai.

64 Amma fa akwai waɗansunku da ba su ba da gaskiya ba.” Domin tun farko Yesu ya san waɗanda ba su ba da gaskiya ba, da kuma wanda zai bāshe shi.

65 Sai ya ƙara da cewa, “Shi ya sa na gaya muku, ba mai iya zuwa gare ni, sai ko Uba ya yardar masa.”

66 Kan wannan da yawa daga cikin almajiransa suka koma da baya, ba su ƙara tafiya tare da shi ba.

67 Sai Yesu ya ce wa goma sha biyun, “Ku ma kuna so ku tafi ne?”

68 Bitrus ya amsa masa ya ce, “Ya Ubangiji, gun wa za mu je? Kai kake da maganar rai madawwami.

69 Mu kuwa mun gaskata, mun kuma tabbata kai ne Mai Tsarkin nan na Allah.”

70 Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Ba ni na zaɓe ku, ku goma sha biyu ba? To, ɗayanku Iblis ne.”

71 Wato, yana nufin Yahuza, ɗan Saminu Iskariyoti, don shi ne zai bāshe shi, ko da yake ɗaya daga cikin goma sha biyun nan ne.

Categories
YAH

YAH 7

‘Yan’uwan Yesu Ba Su Gaskata da Shi Ba

1 Bayan haka, Yesu ya riƙa zagawa a Ƙasar Galili, bai yarda ya zaga ta Yahudiya ba, don Yahudawa suna neman kashe shi.

2 Idin Bukkoki na Yahudawa kuwa ya gabato.

3 Sai ‘yan’uwansa suka ce masa, “Tashi daga nan mana ka tafi ƙasar Yahudiya, almajiranka su ma su ga ayyukan da kake yi.

4 Ai, ba mai aiki a ɓoye in yana so ya shahara. Tun da yake kana yin waɗannan al’amura, to, sai ka bayyana kanka ga duniya.”

5 Domin ko dā ma ‘yan’uwansa ba su gaskata da shi ba.

6 Sai Yesu ya ce musu, “Lokacina bai yi ba tukuna, amma ku, koyaushe lokacinku ne.

7 Ba dama duniya ta ƙi ku, amma ni take ƙi, don na shaide ta a kan ayyukanta mugaye ne.

8 Ku dai ku tafi idin. Ni ba za ni ba yanzu, don lokacina bai yi sosai ba tukuna.”

9 Da ya faɗa musu haka, ya dakata a ƙasar Galili.

Yesu a Idin Bukkoki

10 Bayan ‘yan’uwansa sun tafi idin kuwa, shi ma ya tafi, amma a ɓoye, ba a fili ba.

11 Yahudawa suna ta nemansa a wurin idin suna cewa, “Ina yake ne?”

12 Taro kuma suka riƙa maganarsa a raɗe, waɗansu na cewa, “Mutum ne nagari.” Waɗansu kuma na cewa, “A’a, ai, ɓad da jama’a yake.”

13 Amma ba wanda ya yi magana tasa a fili don tsoron Yahudawa.

14 Wajen tsakiyar idin sai Yesu ya shiga Haikali ya koyar.

15 Yahudawa suka yi mamakin abin, suka ce, “Yaya mutumin nan yake da karatu haka, ga shi kuwa, bai taɓa koyo ba?”

16 Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Koyarwata ba tawa ba ce, ta wanda ya aiko ni ce.

17 Duk mai son aikata nufin Allah zai san koyarwan nan ko ta Allah ce, ko domin kaina nake faɗa.

18 Mai magana don kansa, neman ɗaukakar kansa yake yi. Amma mai neman ɗaukakar wanda ya aiko shi, shi ne mai gaskiya, ba kuwa rashin gaskiya a gare shi.

19 Ashe, ba Musa ne ya ba ku Shari’a ba? Duk da haka ba mai kiyaye Shari’ar a cikinku. Don me kuke neman kashe ni?”

20 Taron suka amsa suka ce, “Kana da iska! Wa yake neman kashe ka?”

21 Yesu ya amsa musu ya ce, “Aiki ɗaya kawai na yi, dukanku kuwa kuna mamakinsa.

22 Musa ya bar muku kaciya, (ba ko shi ya fara ba, tun kakannin kakanni ne), ga shi kuma, kukan yi wa mutum kaciya ko a ran Asabar ma.

23 To, in ana yi wa mutum kaciya ran Asabar don gudun keta Shari’ar Musa, kwa yi fushi don na warkar da mutum sarai ran Asabar?

24 Kada ku yi hukunci da zato, amma ku yi hukunci da adalci.”

Wannan Almasihu Ne?

25 Sai waɗansu mutanen Urushalima suka ce, “Ashe, ba wannan ne mutumin da suke nema su kashe ba?

26 Ga shi nan kuwa, yana magana a fili, ba su ce masa kome ba! Ya yiwu kuma shugabanni sun san lalle wannan shi ne Almasihu?

27 Wannan kam, mun san daga inda yake, amma sa’ad da Almasihu ya zo ba wanda zai san daga inda yake.”

28 Yesu yana koyarwa a Haikalin ke nan, sai ya ɗaga murya ya ce, “Kun dai san ni, kun kuma san daga inda nake. Ban fa zo domin kaina ba. Wanda ya aiko ni mai gaskiya ne, shi kuwa ba ku san shi ba.

29 Ni na san shi, domin daga wurinsa na fito, shi ne kuwa ya aiko ni.”

30 Don haka suka nema su kama shi, amma ba wanda ya taɓa shi, domin lokacinsa bai yi ba tukuna.

31 Duk da haka mutane da yawa cikin taron sun gaskata da shi, suna cewa, “Sa’ad da Almasihu ya zo, zai yi mu’ujizai fiye da na mutumin nan?”

An Aiki Dogaran Haikalin Su Kamo Yesu

32 Farisiyawa suka ji taro suna raɗeraɗinsa haka, sai manyan firistoci da Farisiyawa suka aiki dogaran Haikali su kamo shi.

33 Sai Yesu ya ce, “Saurana ɗan lokaci kaɗan tare da ku, sa’an nan zan koma wurin wanda ya aiko ni.

34 Za ku neme ni, amma ba za ku same ni ba. Inda nake kuwa ba za ku iya zuwa ba.”

35 Sai Yahudawa suka ce wa juna, “Ina za shi da har ba za mu same shi ba? Za shi wurin Yahudawan da suka warwatsu a cikin al’ummai ne, ya koya wa al’umman?

36 Me kuma yake nufi da cewa, ‘Za ku neme ni amma ba za ku same ni ba’? da kuma cewa, ‘Inda nake ba za ku iya zuwa ba’?”

Kogunan Ruwan Rai

37 A ranar ƙarshe ta idin, wato babbar ranar, sai Yesu ya tsaya, ya ɗaga murya ya ce, “Duk mai jin ƙishirwa yă zo gare ni yă sha.

38 Duk mai gaskatawa da ni, kamar yadda Nassi ya ce, ‘Daga zuciyarsa ne kogunan ruwan rai za su gudana.’ ”

39 To, wannan shi ne ya faɗa game da Ruhu, wanda masu gaskatawa da shi za su karɓa, domin har yanzu ba a ba da Ruhu ba, saboda ba a ɗaukaka Yesu ba tukuna.

Rabuwa ta Shiga Tsakanin Mutane

40 Da jin maganan nan waɗansu daga cikin taron suka ce, “Hakika wannan annabin nan ne.”

41 Waɗansu kuwa suka ce, “Wannan Almasihu ne.” Amma waɗansu suka ce, “Me? Ashe, Almasihu daga ƙasar Galili zai fito?

42 Nassi ba cewa ya yi Almasihu zuriyar Dawuda ne ba, daga kuma Baitalami yake, ƙauyen da Dawuda ya zauna?”

43 Sai kuma rabuwa ta shiga tsakaninsu a kansa.

44 Waɗansunsu suka so su kama shi, amma ba wanda ya taɓa shi.

Shugabanni Ba Su Gaskata da Yesu Ba

45 Daga nan dogaran Haikali suka koma wurin manyan firistoci da Farisiyawa, su kuwa suka ce musu, “Don me ba ku kawo shi ba?”

46 Sai dogaran suka amsa suka ce, “A’a, ba mutumin da ya taɓa magana kamar wannan!”

47 Sai Farisiyawa suka amsa musu suka ce, “Af! Har ku ma an ɓad da ku ne?

48 Ashe, akwai wani daga cikin shugabanni ko Farisiyawa da ya gaskata da shi?

49 Amma wannan taro da ba su san Attaura ba, ai, la’anannu ne.”

50 Nikodimu kuwa da ya je wurinsa dā, yana kuwa ɗaya daga cikinsu, ya ce musu,

51 “Ashe, shari’armu takan hukunta mutum tun ba a ji daga bakinsa ba, an kuma san abin da yake ciki?”

52 Suka amsa masa suka ce, “Kai ma Bagalile ne? Bincika mana ka gani, ai, ba wani annabi da zai bayyana a ƙasar Galili.”

Matar da aka Kama da Zina

[

53 Sai kowa ya tafi gida.

Categories
YAH

YAH 8

1 Yesu kuwa ya hau Dutsen Zaitun.

2 Da sassafe kuma ya sāke shiga Haikali. Duk mutane suka zo wurinsa, ya kuwa zauna yana koya musu.

3 Sai malaman Attaura da Farisiyawa suka kawo wata mace da aka kama da zina. Da suka tsai da ita a tsaka,

4 suka ce masa, “Malam, matan nan an kama ta ne, suna cikin yin zina.

5 To, a Attaura Musa ya umarce mu mu kashe irin waɗannan da jifa, kai kuwa me ka ce?”

6 Sun faɗi haka ne don su gwada shi, ko sa sami hanyar kai ƙararsa. Amma Yesu ya sunkuya, ya yi ta rubutu a ƙasa da yatsa.

7 Da suka dinga tambayarsa sai ya ɗaga, ya ce musu, “To, marar zunubi a cikinku ya fara jifanta da dutse.”

8 Sai ya sāke sunkuyawa, ya yi ta rubutu a ƙasa.

9 Su kuwa da suka ji haka suka fita da ɗaya ɗaya, tun daga babbansu har ya zuwa ƙaraminsu, aka bar Yesu shi kaɗai, da matar tsaye a tsakiya.

10 Sai Yesu ya ɗaga, ya ce mata, “Uwargida, ina suke? Ba wanda ya hukunta ki?”

11 Ta ce, “Babu, ya Ubangiji.” Sai Yesu ya ce, “Ni ma ban hukunta ki ba. Yi tafiyarki. Daga yau kada ki ƙara yin zunubi.”]

Yesu Hasken Duniya

12 Sai Yesu ya ƙara musu da cewa, “Ni ne Hasken duniya. Wanda yake bi na ba zai yi tafiya a duhu ba, amma zai sami hasken rai,”

13 Saboda haka Farisiyawa suka ce masa, “Kanka kake wa shaida, shaidarka kuwa ba tabbatacciya ba ce.”

14 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ko na shaidi kaina, ai, shaidata tabbatacciya ce, domin na san inda na fito, da kuma inda za ni. Amma ku ba ku san inda na fito ba, ko kuma inda za ni.

15 Ku kuna hukunci irin na duniya ne, ni kuwa ba na hukunta kowa.

16 Amma ko da zan yi hukunci, hukuncina na gaskiya ne, domin ba ni kaɗai nake ba, ni da Uba wanda ya aiko ni ne.

17 A Attaurarku ma a rubuce yake, cewa shaidar mutum biyu tabbatacciya ce.

18 Ni ne nake shaidar kaina, Uba da ya aiko ni kuma yana shaidata.”

19 Saboda haka suka ce masa, “Ina Uban naka yake?” Yesu ya amsa ya ce, “Ko ni ko Ubana, ba wanda kuka sani. Da kun san ni, da kun san Ubana ma.”

20 Ya faɗi wannan magana ne a baitulmalin Haikali, lokacin da yake koyarwa a wurin. Duk da haka ba wanda ya kama shi, don lokacinsa bai yi ba tukuna.

Inda Za Ni Ba Ku Iya Zuwa Ba

21 Sai ya ƙara ce musu, “Zan yi tafiya, za ku kuwa neme ni, amma za ku mutu da zunubinku. Inda za ni kuwa ba za ku iya zuwa ba.”

22 Saboda haka sai Yahudawa suka ce, “Wato zai kashe kansa ke nan da ya ce, ‘Inda za ni ba za ku iya zuwa ba’?”

23 Sai ya ce musu, “Ku daga ƙasa kuke, ni kuwa daga sama nake. Ku na duniyan nan ne, ni kuwa ba na duniyar nan ba ne.”

24 Shi ya sa na ce muku za ku mutu da zunubanku. Domin in ba ku gaskata ni ne shi ba, za ku mutu da zunubanku.”

25 Sai suka ce masa, “Kai wane ne?” Yesu ya ce musu, “Daidai yadda na gaya muku.

26 Akwai abubuwa da yawa da zan faɗa game da ku, in kuma hukunta. Amma shi wannan da ya aiko ni mai gaskiya ne. Abin da na jiyo daga gare shi kuwa, shi nake shaida wa duniya.”

27 Ba su gane maganar Uba yake yi musu ba.

28 Sai Yesu ya ce, “Sa’ad da kuka ɗaga Ɗan Mutum, a sa’an nan ne za ku gane ni ne shi, ba na yin kome kuma ni kaɗai, sai dai Uba ya koya mini, haka nake faɗa.

29 Wanda kuwa ya aiko ni yana tare da ni, bai bar ni ni kaɗai ba, domin koyaushe ina aikata abin da yake so.”

30 Sa’ad da Yesu yake faɗar haka, mutane da yawa suka gaskata da shi.

Gaskiya Za ta ‘Yanta Ku

31 Sai Yesu ya ce wa Yahudawan nan da suka gaskata shi, “In dai kun zauna kan maganata, hakika ku almajiraina ne.

32 Za ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za ta ‘yanta ku.”

33 Suka amsa masa suka ce, “Ai, mu zuriyar Ibrahim ne, ba mu taɓa bauta wa kowa ba. Yaya kuma za ka ce za a ‘yanta mu?”

34 Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku, duk mai aikata zunubi bawan zunubi ne.

35 Ai, bawa ba ya ɗorewa a gida har abada, ɗa kuwa yana ɗorewa.

36 In kuwa Ɗan ya ‘yanta ku, za ku ‘yantu, ‘yantuwar gaske.

37 Na san dai ku zuriyar Ibrahim ne, amma kuwa kuna neman kashe ni, don maganata ba ta shigarku.

38 Ina faɗar abin da na gani a wurin Ubana, ku kuma kuna yin abin da kuka ji daga wurin naku uba.”

Ubanku Iblis Ne

39 Suka amsa masa suka ce, “Ai, Ibrahim ne ubanmu.” Yesu ya ce musu, “Da ku ‘ya’yan Ibrahim ne, da sai ku yi aikin da Ibrahim ya yi.

40 Ga shi yanzu, kuna neman kashe ni, ni mutumin da na gaya muku gaskiyar da na ji wurin Allah. Ba haka Ibrahim ya yi ba.

41 Ku kuna aikin da ubanku yake yi ne.” Suka ce masa, “Ba a haife mu daga fasikanci ba, ubanmu ɗaya ne, wato Allah.”

42 Yesu ya ce musu, “Da Allah ne Ubanku da kun ƙaunace ni, domin daga wurin Allah na fito, ga ni nan kuwa. Ban zo domin kaina ba, shi ne ya aiko ni.

43 Don me ba kwa gane maganata? Don ba kwa iya jimirin jin maganata ne.

44 Ku na ubanku Iblis ne, niyyarku kuwa ku aikata burin ubanku. Shi dā ma tun farko mai kisankai ne, bai zauna kan gaskiya ba, don ba ruwansa da gaskiya. Duk sa’ad da yake ƙarya, cinikinsa yake yi, don shi maƙaryaci ne, uban ƙarairayi kuma.

45 Amma domin ina faɗar gaskiya, ba kwa gaskata ni.

46 A cikinku wa zai iya haƙƙaƙewa na taɓa yin zunubi? In kuwa gaskiya nake faɗa, to, don me ba kwa gaskata ni?

47 Na Allah yakan saurari Maganar Allah. Abin da ya sa ba kwa sauraronta ke nan, don ku ba na Allah ba ne.”

Kafin Ibrahim, Nake

48 Yahudawa suka amsa masa suka ce, “Ashe, gaskiyarmu da muka ce kai Basamariye ne, kana kuma da iska.”

49 Yesu ya amsa ya ce, “Ni ba mai iska ba ne. Ubana nake girmamawa, ku kuwa wulakanta ni kuke yi.

50 Ba ni nake nemar wa kaina girma ba, akwai mai nemar mini, shi ne kuma mai yin shari’a.

51 Lalle hakika, ina gaya muku, kowa ya kiyaye maganata ba zai mutu ba har abada.”

52 Sai Yahudawa suka ce masa, “To, yanzu kam, mun tabbata kana da iska. Ai, Ibrahim ya mutu, haka ma annabawa, kana kuwa cewa kowa ya kiyaye maganarka ba zai mutu ba har abada.

53 Wato ka fi ubanmu Ibrahim ne, ya kuwa mutu? Annabawa ma sun mutu! Wa ka mai da kanka ne?”

54 Yesu ya amsa ya ce, “In ma na ɗaukaka kaina, ɗaukakata ba a bakin kome take ba. Ubana shi ne mai ɗaukaka ni, wanda kuke cewa, shi ne Allahnku.

55 Ku ba ku san shi ba, amma ni na san shi. Da na ce ban san shi ba, da na zama maƙaryaci kamarku. Amma na san shi, ina kuma kiyaye magana tasa.

56 Ubanku Ibrahim ya yi farin ciki matuƙa ya sami ganin zamanina, ya kuwa gan shi, ya yi murna.”

57 Sai Yahudawa suka ce masa, “Har yanzu ma ba ka kai shekara hamsin ba, wai kuwa har ka ga Ibrahim!”

58 Sai Yesu ya ce musu, “Lalle hakika, ina gaya muku, tun ba a haifi Ibrahim ba, ni ne.”

59 Don haka suka ɗebo duwatsu su jajjefe shi. Yesu kuwa ya ɓuya, ya fita daga Haikalin.

Categories
YAH

YAH 9

Warkar da Wanda aka Haifa Makaho

1 Yesu na wucewa sai ya ga wani mutum da aka haifa makaho.

2 Sai almajiransa suka tambaye shi suka ce, “Ya Shugaba, wa ya yi zunubi da aka haifi mutumin nan makaho, shi, ko iyayensa?”

3 Yesu ya amsa ya ce, “Ba domin mutumin nan ko iyayensa sun yi zunubi ba, sai domin a nuna aikin Allah ne a kansa.

4 Lalle ne mu yi aikin wanda ya aiko ni tun da sauran rana. Ai, dare zai yi sa’ad da ba mai iya aiki.

5 Muddin ina duniya ni ne hasken duniya.”

6 Da ya faɗi haka sai ya tofa yau a ƙasa, ya cuɗa ƙasa, ya shafa a idanun makahon,

7 ya ce masa, “Je ka, ka wanke ido a ruwan Siluwam,” wato aikakke. Shi ke nan sai ya je ya wanke ido, ya komo yana gani.

8 Maƙwabta da waɗanda suka saba ganinsa dā yana bara, suka ce, “Ashe, ba wannan ne yakan zauna yana bara ba?”

9 Waɗansu suka ce, “Shi ne mana.” Waɗansu kuwa suka ce, “A’a, kai dai, sun yi kama.” Shi kuwa ya ce, “Sosai ni ne!”

10 Sai suka ce masa, “To, ƙaƙa aka yi idanunka suka buɗe?”

11 Ya amsa ya ce, “Mutumin nan da ake kira Yesu ne ya cuɗa ƙasa ya shafa mini a idanu, ya ce mini, ‘Je ka Siluwam ka wanke ido.’ Na kuwa je na wanke, sai na sami gani.”

12 Suka ce masa, “Ina yake?” Ya ce, “Ban sani ba.”

Farisiyawa Sun Bincika Labarin Wanda aka Warkar

13 Sai suka kai wa Farisiyawa mutumin da yake makaho a dā.

14 To, ran Asabar ne Yesu ya cuɗa ƙasar ya buɗe masa ido.

15 Farisiyawa ma suka tambaye shi ta yadda aka yi ya sami gani. Ya ce musu, “Cuɗaɗɗiyar ƙasa ya shafa a idona, na wanke, ina gani.”

16 Saboda haka, waɗansu Farisiyawa suka ce, “Mutumin nan ba daga Allah yake ba, don ba ya kiyaye Asabar.” Waɗansu kuwa suka ce, “Yaya mutum mai zunubi zai iya yin mu’ujizai haka?” Sai rabuwa ta shiga tsakaninsu.

17 Sai suka sāke ce wa makahon, “To, kai fa, me ka gani game da shi, da yake kai ya buɗe wa ido?” Ya ce, “Ai, annabi ne.”

18 Yahudawa kam, ba su gaskata shi makaho ne a dā ba, ya kuma sami gani, har suka kira iyayen wanda ya sami ganin,

19 suka tambaye su suka ce, “Wannan ɗanku ne da kuke cewa an haife shi makaho? To, ta yaya yake iya gani yanzu?”

20 Sai iyayen nasa suka amsa suka ce, “Mun dai san wannan ɗanmu ne, makaho ne aka haife shi.

21 Amma ta yadda aka yi yake gani yanzu ba mu sani ba, ba mu ma san wanda ya buɗe idon ba. Ku tambaye shi, ai, ba yaro ba ne, zai faɗa da bakinsa.”

22 Iyayensa sun faɗi haka ne don tsoron Yahudawa, don dā ma Yahudawa sun ƙulla, cewa kowa ya amsa, cewa shi ne Almasihu, za a fisshe shi daga jama’a.

23 Shi ya sa iyayensa suka ce, “Ai, ba yaro ba ne, ku tambaye shi.”

24 Sai suka sāke kiran mutumin nan da yake makaho a dā, suka ce masa, “Ka tsoraci Allah dai! Mu kam, mun san mutumin nan mai zunubi ne.”

25 Sai ya amsa ya ce, “Ko mai zunubi ne, ni ban sani ba. Abu ɗaya kam, na sani, dā ni makaho ne, yanzu kuwa ina gani.”

26 Sai suka ce masa, “Shin, me ya yi maka? Ta yaya ya buɗe maka ido?”

27 Ya amsa musu ya ce, “Na riga na faɗa muku, ba ku ji ba. Don me kuke so ku sāke ji? Ko ku ma kuna so ku zama almajiransa ne?”

28 Sai suka fāɗa shi da zagi, suna cewa, “Kai ne dai almajirin wannan ɗin, mu kam, almajiran Musa ne.

29 Mun dai sani Allah ya yi magana da Musa, amma wannan ba mu san ta inda ya fito ba.”

30 Sai mutumin ya amsa musu ya ce, “Yau ga abin mamaki! Ashe, ba ku san ta inda ya fito ba, ga shi kuwa, ya buɗe mini ido!

31 Mun sani Allah ba ya sauraron masu zunubi, amma duk wanda yake mai bautar Allah, yake kuma aikata nufinsa, Allah yakan saurare shi.

32 Tun da aka fara duniya ba a taɓa jin wani ya buɗe idon wanda aka haifa makaho ba.

33 Da mutumin nan ba daga Allah ya fito ba, da ba abin da zai iya yi.”

34 Suka amsa masa suka ce, “Kai da aka haifa a baƙin zunubi ne za ka koya mana?” Sai suka kore shi.

Makanta ta Ruhu

35 Yesu ya ji labari sun kore shi. Da ya same shi, ya ce, “Ka gaskata da Ɗan Mutum ko?”

36 Ya amsa ya ce, “Wane ne shi, ya Shugaba, da zan gaskata da shi?”

37 Yesu ya ce masa, “Ai, ka gan shi, shi ne ma mai magana da kai.”

38 Sai ya ce, “Ya Ubangiji, na ba da gaskiya,” ya kuma yi masa sujada.

39 Yesu ya ce, “Na shigo duniyan nan ne don rarrabewa, domin waɗanda ba sa gani su gani, waɗanda suke gani kuma su makance.”

40 Da Farisiyawan nan da suke tare da shi suka ji haka, suka ce masa, “Wato mu ma makafi ne?”

41 Yesu ya ce musu, “Ai, da makafi ne ku, da ba ku da zunubi. Amma da yake kun ce kuna gani, to, zunubinku ya tabbata.

Categories
YAH

YAH 10

Misali na Garken Tumaki

1 “Lalle hakika, ina gaya muku, wanda bai shiga garken tumaki ta ƙofa ba, amma ya haura ta wani gu, to, shi ɓarawo ne, ɗan fashi kuma.

2 Wanda kuwa ya shiga ta ƙofar, makiyayin tumakin ne.

3 Mai tsaron ƙofar yakan buɗe masa, tumakin kuma sukan saurari murya tasa, yakan kama sunan nasa tumaki, ya kai su waje.

4 Bayan ya fitar da dukan nasa waje, sai ya shige gabansu, tumakin na biye da shi, domin sun san murya tasa.

5 Ba za su bi baƙo ba, sai dai su guje shi, don ba su san muryar baƙo ba.”

6 Yesu ya yi musu wannan misali, amma ba su gane abin da ya faɗa musu ba.

Yesu Ne Makiyayi Mai Kyau

7 Don haka Yesu ya sāke ce musu, “Lalle hakika, ina gaya muku, ni ne ƙofar tumakin.

8 Duk waɗanda suka riga ni zuwa cewa, su ne ni, ɓarayi ne, ‘yan fashi kuma, amma tumakin ba su kula da su ba.

9 Ni ne ƙofar. Kowa ya shiga ta wurina zai sami ceto, ya kai ya kawo, ya kuma yi kiwo.

10 Ɓarawo yakan zo ne kawai don sata da kisa da hallakarwa. Ni kuwa na zo ne domin su sami rai, su kuma same shi a yalwace.

11 Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau kuwa shi ne mai ba da ransa domin tumakin.

12 Wanda yake ɗan asako kuwa, ba makiyayin gaske ba, tumakin kuma ba nasa ba, da ganin kyarkeci ya doso, sai ya watsar da tumakin, ya yi ta kansa, kyarkeci kuwa ya sure waɗansu, ya fasa sauran.

13 Ya gudu ne fa, don shi ɗan asako ne, ba abin da ya dame shi da tumakin.

14 Ni ne Makiyayi mai kyau. Na san nawa, nawa kuma sun san ni,

15 kamar yadda Uba ya san ni, ni kuma na san Uban. Ina ba da raina maimakon tumakin.

16 Ina kuma da waɗansu tumaki da ba na wannan garke ba ne. Su ma lalle in kawo su, za su kuwa saurari muryata, su zama garke guda, makiyayi kuma guda.

17 Domin wannan uba yake ƙaunata, domin ina ba da raina in ɗauko shi kuma.

18 Ba mai karɓe mini rai, don kaina nake ba da shi. Ina da ikon ba da shi, ina da ikon ɗauko shi kuma. Na karɓo wannan umarni ne daga wurin Ubana.”

19 Saboda maganan nan fa, sai rabuwa ta sāke shiga tsakanin Yahudawa.

20 Da yawa daga cikinsu suka ce, “Ai, mai iska ne, haukansa kawai yake yi. Don me za ku saurare shi?”

21 Waɗansu kuwa suka ce, “A’a, wannan magana, ai, ba ta mai iska ba ce. Ashe, iska tana iya buɗe wa makaho ido?”

Yahudawa Sun Ƙi Yesu

22 Lokacin idin tsarkakewa ne kuwa a Urushalima,

23 damuna ce kuma, Yesu kuwa na zagawa a Shirayin Sulemanu cikin Haikali,

24 sai Yahudawa suka kewaye shi, suka ce masa, “Har yaushe za ka bar mu da shakka? In dai kai ne Almasihun, ka gaya mana a fili.”

25 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ai, na faɗa muku, ba ku gaskata ba. Ayyukan da nake yi da sunan Ubana, suke shaidata.

26 Amma ku ba ku gaskata ba, domin ba kwa cikin tumakina.

27 Tumakin nan nawa sukan saurari muryata, na san su, suna kuma bi na.

28 Ina ba su rai madawwami, ba kuwa za su halaka ba har abada, ba kuma mai ƙwace su daga hannuna.

29 Ubana, wanda ya ba ni su, ya fi duka girma, ba kuwa mai iya ƙwace su daga ikon Uban.

30 Ni da Uba ɗaya muke.”

31 Sai Yahudawa suka sāke ɗebo duwatsu su jajjefe shi.

32 Yesu ya amsa musu ya ce, “Na nuna muku ayyuka nagari masu yawa daga wurin Uba, a kan wanne a cikinsu za ku jajjefe ni?”

33 Yahudawa suka amsa suka ce, “Ba don wani aiki nagari za mu jajjefe ka ba, sai don sāɓo, don kai, ga ka mutum, amma kana mai da kanka Allah.”

34 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ba a rubuce yake a Shari’arku ba cewa, ‘Na ce ku alloli ne’?

35 To, in waɗanda Maganar Allah ta zo musu ya ce da su alloli (Nassi kuwa ba ya tashi),

36 kwa ce da wanda Uba ya keɓe, ya kuma aiko duniya, ‘Sāɓo kake,’ domin na ce, ‘Ni Ɗan Allah ne’?

37 In ba ayyukan da Ubana yake yi nake yi ba, to, kada ku gaskata ni.

38 Amma in su nake yi, ko ba ku gaskata ni ba, to, ku gaskata ayyukan, don ku sani, ku kuma gane, Uba na cikina, ni kuma ina cikin Uba.”

39 Sai suka sāke ƙoƙarin kama shi, amma ya fita daga hannunsu.

40 Sa’an nan ya sāke komawa hayin Kogin Urdun, wurin da Yahaya ya fara yin baftisma, ya zauna a can,

41 mutane kuwa da yawa suka zo wurinsa, sai suka riƙa cewa, “Hakika, Yahaya bai yi wata mu’ujiza ba, amma duk abin da ya faɗa game da mutumin nan gaskiya ne.”

42 Nan fa mutane da yawa suka gaskata da shi.