Categories
ZAB

ZAB 91

Zama a Inuwar Mai Iko Dukka

1 Duk wanda ya je wurin Maɗaukaki

Zai zauna lafiya,

Duk wanda yake zaune a inuwar Mai Iko Dukka,

2 Ya iya ce wa Ubangiji,

“Kai ne kāriyata, da mai kiyaye ni!

Kai ne Allahna, a gare ka nake dogara!”

3 Hakika zai kiyaye ka

Daga dukan hatsarorin da ka ɓoye,

Daga kuma dukan mugayen cuce-cuce.

4 Zai rufe ka da fikafikansa,

Za ka zauna lafiya a ƙarƙashinsu.

Amincinsa zai tsare ka, ya kiyaye ka.

5 Ba za ka ji tsoron hatsarori da dare ba,

Ko fāɗawar da za a yi maka da rana,

6 Ko annobar da take aukowa da dare,

Ko mugayen da suke kisa da tsakar rana.

7 Mutum dubu za su fāɗi daura da kai,

Dubu goma kuma za su fāɗi dama da kai,

Amma kai, ba za a cuce ka ba.

8 Da idonka za ka duba, Ka ga yadda ake hukunta wa mugaye.

9 Domin ka ɗauka Ubangiji yake kiyaye ka,

Maɗaukaki ne yake tsaronka,

10 To, ba bala’in da zai same ka,

Ba za a yi wa gidanka aikin ƙarfi da yaji ba.

11 Allah zai sa mala’ikunsa su lura da kai,

Za su kiyaye ka duk inda za ka tafi.

12 Za su ɗauke ka a hannuwansu,

Don kada ka buga ƙafarka a dutse.

13 Za ka tattake zakoki da macizai,

Za ka tattake zakoki masu zafin rai

Da macizai masu dafi.

14 Allah ya ce, “Zan ceci waɗanda suke ƙaunata,

Zan kiyaye waɗanda suka san ni.

15 Sa’ad da suka kira gare ni, zan amsa musu,

Zan kasance tare da su sa’ad da suke shan wahala,

Zan cece su in girmama su.

16 Zan ba su tsawon rai lada,

Hakika kuwa zan cece su.”

Categories
ZAB

ZAB 92

Waƙar Yabo

1 Abu mai kyau ne a yi wa Ubangiji godiya,

A raira waƙa don girmansa, Allah mafi ɗaukaka,

2 A yi shelar madawwamiyar ƙaunarka kowace safiya,

Amincinka kuma kowane maraice,

3 Da abubuwan kaɗe-kaɗe masu tsarkiya,

Da amon garaya mai daɗi.

4 Ya Ubangiji,

Ayyukanka masu iko suna sa ni murna,

Saboda abin da ka aikata

Ina raira waƙa domin farin ciki.

5 Ayyukanka da girma suke, ya Ubangiji!

Tunaninka da zurfi suke!

6 Ga wani abin da wawa ba zai iya sani ba,

Dakiki kuma ba zai iya ganewa ba,

7 Shi ne mai yiwuwa ne mugu ya yi girma kamar tsire-tsire,

Masu aikata mugayen ayyuka kuma su arzuta,

Duk da haka za a hallaka su ɗungum.

8 Gama kai, ya Ubangiji,

Maɗaukaki ne har abada.

9 Mun sani maƙiyanka za su mutu,

Dukan mugaye kuwa za a yi nasara da su.

10 Ka sa ni na yi ƙarfi kamar bijimi mai faɗa,

Ka sa mini albarka da farin ciki.

11 Na ga fāɗuwar maƙiyana,

Na ji kukan mugaye.

12 Adalai za su yi yabanya

Kamar itatuwan giginya,

Za su yi girma kamar itatuwan al’ul na Lebanon.

13 Za su zama kamar itatuwan da aka daddasa a Haikalin Ubangiji,

Suna ta yabanya a Haikalin Allahnmu.

14 Waɗanda suke yin ‘ya’ya da tsufansu,

A kullum kuwa kore shar suke,

Suna da ƙarfinsu kuma.

15 Wannan ya nuna Ubangiji adali ne,

Shi wanda yake kāre ni,

Ba kuskure a gare shi.

Categories
ZAB

ZAB 93

Allah Sarki Ne

1 Ubangiji sarki ne!

Yana saye da ɗaukaka, suturarsa ƙarfi ne.

Hakika duniya ta kahu sosai a inda take,

Ba kuwa za ta jijjigu ba.

2 Kursiyinka, ya Ubangiji, ya kahu tun daga farko,

Kana nan tun fil azal.

3 Ya Ubangiji, zurfafan teku suna ta da muryarsu,

Suna ta da muryarsu da ruri.

4 Ubangiji yana mulki cikin Sama,

Mulkinsa mafifici ne,

Fiye da rurin teku,

Fiye da ikon raƙuman ruwan teku.

5 Dokokinka dawwamammu ne, ya Ubangiji,

Haikalinka kuwa tsattsarka ne ƙwarai,

Har abada abadin.

Categories
ZAB

ZAB 94

Addu’ar Neman Sakayya

1 Ya Ubangiji, kai Allah ne wanda yake yin hukunci,

Ka bayyana fushinka!

2 Kai ne mai yi wa dukan mutane shari’a,

Ka tashi, ka sāka wa masu girmankai

Abin da ya dace da su!

3 Har yaushe mugaye za su yi ta murna?

Har yaushe ne, ya Ubangiji?

4 Har yaushe za su yi shakiyanci,

Su yi ta ɗaga kai?

Har yaushe, ya Ubangiji?

5 Suna ragargaza jama’arka, ya Ubangiji,

Suna zaluntar waɗanda suke naka.

6 Suna karkashe gwauraye, wato matan da mazansu suka mutu, da marayu,

Da kuma baƙin da suke zaune a ƙasarmu.

7 Suna cewa, “Ai, Ubangiji ba ya ganinmu,

Allah na Isra’ila ba ya lura da abin da yake faruwa!”

8 Ya jama’ata, ƙaƙa kuka zama dakikai, wawaye haka?

Sai yaushe za ku koya?

9 Allah ya yi mana kunnuwa, shi ba zai ji ba?

Allah ya yi mana idanu, shi ba zai gani ba?

10 Shi ne yake shugabancin sauran al’umma, ba zai hukunta su ba?

Shi ne yake koya wa dukan mutane, shi ba shi da sani ne?

11 Ubangiji ya san tunaninsu,

Ya san kuma hujjojinsu na rashin hankali.

12 Ya Ubangiji, mai farin ciki ne mutumin da kake koya wa,

Mutumin da kake koya masa shari’arka.

13 Don ka ba shi hutawa a kwanakin wahala,

Kafin a haƙa wa mugaye kabari.

14 Ubangiji ba zai rabu da jama’arsa ba,

Ba zai rabu da waɗanda suke nasa ba.

15 Adalci kuma zai sāke dawowa cikin majalisun alƙalai,

Dukan adalai kuwa za su yi na’am da shi.

16 Wa zai tsaya mini gāba da mugaye?

Wa zai goyi bayana gāba da masu aikata mugunta?

17 Da ba domin Ubangiji ya taimake ni ba,

Ai, da tuni na kai ƙasar da ba a motsi.

18 Na ce, “Ina kan fāɗuwa,”

Amma, ya Ubangiji, madawwamiyar ƙaunarka ta riƙe ni.

19 Sa’ad da nake alhini, ina cikin damuwa,

Ka ta’azantar da ni, ka sa in yi murna.

20 Ba ruwanka da alƙalai azzalumai, marasa gaskiya,

Waɗanda suka mai da rashin gaskiya ita ce gaskiyarsu,

21 Sukan shirya wa mutanen kirki maƙarƙashiya,

Sukan yanke wa marar laifi hukuncin kisa.

22 Amma Ubangiji yakan kāre ni,

Allahna yakan kiyaye ni.

23 Shi zai hukunta su saboda muguntarsu,

Ya hallaka su saboda zunubansu.

Ubangiji Allahnmu zai hallaka su.

Categories
ZAB

ZAB 95

Waƙar Yabo da Sujada

1 Ku zo mu yabi Ubangiji!

Mu raira waƙa domin farin ciki ga mai kiyaye mu,

Da Mai Cetonmu!

2 Mu zo gabansa da godiya,

Mu raira waƙoƙin farin ciki na yabo!

3 Gama Ubangiji Allah ne mai iko,

Shi yake mulki bisa sauran alloli duka.

4 Yana mulki bisa dukan duniya,

Daga zurfafan kogwannin duwatsu zuwa tuddai mafiya tsayi.

5 Yana mulki bisa tekun da ya yi,

Da kuma bisa ƙasar da ya siffata.

6 Ku zo, mu durƙusa, mu yi masa sujada,

Mu durƙusa a gaban Ubangiji, Mahaliccinmu!

7 Shi ne Allahnmu,

Mu ne jama’ar da yake lura da ita,

Mu ne kuma garken da yake ciyarwa.

Yau ku ji abin da yake faɗa.

8 “Kada ku taurare zuciyarku yadda kakanninku suka yi a Meriba,

Kamar yadda suka yi a jeji a Masaha, a wancan rana.

9 A can suka gwada ni suka jarraba ni,

Ko da yake da idanunsu suka ga abin da na yi dominsu.

10 A shekara arba’in ɗin nan,

Jama’ar nan ta zama abar ƙyama gare ni,

‘Su marasa biyayya ne,’ in ji ni,

‘Gama sun ƙi bin umarnaina!’

11 Sai na ji haushi, na yi musu alkawari mai nauyi.

Na ce, ‘Faufau ba za ku shiga ƙasar da zan ba ku hutawa a ciki ba.’ ”

Categories
ZAB

ZAB 96

Allah Maɗaukakin Sarki Ne

1 Ku raira sabuwar waƙa ga Ubangiji!

Ku raira waƙa ga Ubangiji, ya duniya duka!

2 Ku raira waƙa ga Ubangiji, ku yabe shi!

Kowace rana ku ba da labari mai daɗi cewa,

“Ya cece mu!”

3 Ku yi shelar ɗaukakar Ubangiji ga sauran al’umma,

Ku yi shelar ayyukansa masu girma ga dukan kabilai.

4 Ubangiji da girma yake, tilas a ɗaukaka shi,

Tilas a fi jin tsoronsa fiye da dukan alloli.

5 Allolin dukan al’ummai, gumaka ne kawai,

Amma Ubangiji ne ya yi sammai.

6 Daraja da ɗaukaka suna kewaye da shi,

Girma da jamali suna cikin Haikalinsa.

7 Dukan jama’ar da suke bisa duniya su yabi Ubangiji!

Ku yabi ɗaukakarsa da ikonsa!

8 Ku yabi sunan Ubangiji mai ɗaukaka,

Ku kawo sadaka, ku shiga Haikalinsa.

9 Ku durƙusa a gaban Mai Tsarki, sa’ad da ya bayyana,

Ku yi rawar jiki a gabansa, ku duniya duka!

10 A faɗa wa dukan sauran al’umma, “Ubangiji Sarki ne!

Duniya ta kahu da ƙarfi a wurin zamanta,

Ba za a iya kaushe ta ba,

Shi zai shara’anta dukan jama’a da adalci.”

11 Duniya da sararin sama, ku yi murna!

Ki yi ruri, ya ke teku da dukan masu rai da suke cikinki,

12 Ku yi murna ya ku filaye da dukan abubuwan da suke cikinku!

Sa’an nan itatuwan da suke cikin kurama

Za su ta da murya saboda farin ciki

13 A gaban Ubangiji, gama ya zo ne ya mallaki duniya.

Zai mallaki dukan jama’ar duniya

Da adalci da gaskiya.

Categories
ZAB

ZAB 97

Allah Ne Mai Mulkin Dukka

1 Ubangiji Sarki ne! Ki yi murna ke duniya!

Ku yi murna, dukanku tsibiran da suke cikin tekuna!

2 Gajimare da duhu sun kewaye shi.

A kan adalci da gaskiya ya kafa mulkinsa.

3 Wuta tana tafe a gabansa, tana cinye maƙiyansa

Waɗanda suke kewaye da shi.

4 Walƙiyarsa ta haskaka duniya,

Duniya kuwa ta gani ta yi ta rawar jiki.

5 Tuddai sun narke a gaban Ubangiji kamar kākin zuma,

A gaban Ubangijin dukan duniya.

6 Sammai suna shelar adalcinsa,

Dukan kabilai kuwa, sun ga ɗaukakarsa.

7 Dukan waɗanda suke yi wa siffofi sujada za su sha kunya,

Haka kuma waɗanda suke fāriya da gumakansu.

Dukan alloli za su rusuna a gabansa.

8 Jama’ar Sihiyona suna murna,

Garuruwan Yahuza kuma suna farin ciki,

Sabili da irin shari’unka, ya Ubangiji!

9 Ya Ubangiji Mai Iko Dukka, kai kake mulkin dukan duniya,

Ka fi sauran alloli duka girma.

10 Ubangiji yana ƙaunar masu ƙin mugunta.

Yakan kiyaye rayukan jama’arsa,

Yakan cece su daga ikon mugaye.

11 Haske yakan haskaka adalai,

Haka kuma murna ta cika ga masu nagarta.

12 Dukanku adalai ku yi murna,

Saboda abin da Ubangiji ya yi!

Ku tuna da abin da Mai Tsarki ya yi,

Ku yi masa godiya!

Categories
ZAB

ZAB 98

Yabo saboda Adalcin Allah

1 Ku raira sabuwar waƙa ga Ubangiji,

Gama ya aikata ayyuka masu banmamaki!

Ta wurin ikonsa, da ƙarfinsa mai tsarki ya yi nasara.

2 Ubangiji ya bayyana cin nasararsa,

Ya sanar da ikonsa na ceto ga sauran al’umma.

3 Ya cika alkawarinsa wanda ya yi wa jama’ar Isra’ila,

Da tabbatacciyar ƙauna da aminci.

Dukan mutane ko’ina sun ga nasarar Allahnmu!

4 Ku raira waƙa ta farin ciki ga Ubangiji.

Dukanku waɗanda suke a duniya,

Ku yabe shi da waƙoƙi, kuna ta da murya da ƙarfi,

Saboda farin ciki!

5 Ku raira yabbai ga Ubangiji da garayu,

Ku kaɗa garayu!

6 Ku busa kakaki da ƙahoni,

Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, Sarki!

7 Ki yi ruri, ya ke teku,

Ke da dukan masu rai waɗanda suke cikinki,

Ki raira waƙa, ke duniya,

Da dukan waɗanda suke zaune cikinki!

8 Ku yi tāfi, ya ku tekuna,

Ku raira waƙa tare, ya ku tuddai, don farin ciki.

9 A gaban Ubangiji, gama ya zo ne ya yi mulki bisa duniya!

Zai yi mulki bisa dukan jama’ar duniya da adalci da gaskiya.

Categories
ZAB

ZAB 99

Amincin Allah ga Isra’ila

1 Ubangiji Sarki ne,

Mutane suna rawar jiki,

Yana zaune a bisa kursiyinsa a bisa kerubobi,

Duniya ta girgiza.

2 Ubangiji mai iko ne a Sihiyona,

Shi ne yake mulki a bisa dukan sauran al’umma.

3 Kowa da kowa zai yabi sunansa mai girma, Maɗaukaki,

Mai Tsarki ne shi!

4 Maɗaukaki kana ƙaunar abin da yake daidai,

Ka kawo adalci cikin Isra’ila,

Ka kawo adalci da gaskiya.

5 Ku yabi Ubangiji Allahnmu,

Ku yi sujada a gaban kursiyinsa!

Mai Tsarki ne shi!

6 Musa da Haruna firistocinsa ne,

Sama’ila kuma mai yi masa sujada ne.

Suka yi kira ga Ubangiji, ya kuwa amsa musu.

7 Ya yi magana da su daga girgije,

Suka yi biyayya da dokoki da umarnai da ya ba su.

8 Ya Ubangiji Allahnmu, ka amsa wa jama’arka,

Ka nuna musu, kai Allah ne mai yin gafara,

Amma kakan hukunta su saboda zunubansu.

9 Ku yabi Ubangiji Allahnmu,

Ku yi sujada a bisa dutsensa mai tsarki!

Ubangiji Allahnmu Mai Tsarki ne!

Categories
ZAB

ZAB 100

Waƙar Yabo

1 Bari dukan duniya ta raira waƙar farin ciki ga Ubangiji!

2 Ku yi wa Ubangiji sujada da murna,

Ku zo gabansa, kuna raira waƙoƙin farin ciki!

3 Kada fa a manta da cewa, Ubangiji shi ne Allah!

Shi ne ya yi mu, mu kuwa nasa ne,

Mu jama’arsa ne, mu garkensa ne.

4 Ku shiga Haikalinsa da godiya,

Ku shiga wurinsa mai tsarki, ku yabe shi!

Ku gode masa, ku yabe shi!

5 Ubangiji nagari ne,

Ƙaunarsa madawwamiya ce,

Amincinsa kuwa har abada abadin ne.