Categories
ZAB

ZAB 131

Addu’ar Tawali’u

1 ‘Ya Ubangiji, na rabu da girmankai,

Na bar yin fariya,

Ba ruwana da manyan al’amura,

Ba ruwana kuma da zantuttukan da suka fi ƙarfina.

2 Amma na haƙura, raina a kwance,

Kamar jinjirin da yake kwance jalisan a hannun mahaifiyarsa,

Haka zuciyata take kwance.

3 Ya Isra’ila, ka dogara ga Ubangiji,

Daga yanzu har abada!

Categories
ZAB

ZAB 132

Yabo saboda Tsattsarkan Wuri

1 Ya Ubangiji, kada ka manta da Dawuda

Da dukan irin aikin da ya yi.

2 Ka tuna, ya Ubangiji, da alkawarin da ya yi,

Da rantsuwar da ya yi maka, ya Maɗaukaki, Allah na Isra’ila,

3 “Ba zan tafi gida ko in kwanta ba,

4 Ba zan huta, ko in yi barci ba,

5 Sai sa’ad da na shirya wa Ubangiji wuri,

Wato Haikali domin Maɗaukaki, Allah na Isra’ila.”

6 Mun ji labari akwatin alkawari yana Baitalami,

Amma muka same shi a kurmi.

7 Muka ce, “Bari mu tafi Haikalin Ubangiji,

Mu yi sujada a gaban kursiyinsa!”

8 Ka zo wurin hutawarka, ya Ubangiji,

Tare da akwatin alkawari,

Alama ce ta ikonka.

9 Ka suturta firistoci da adalci,

Ka sa dukan jama’arka su yi sowa ta farin ciki!

10 Ka yi wa bawanka Dawuda alkawari,

Kada ka rabu da zaɓaɓɓen sarkinka, ya Ubangiji!

11 Ka yi wa Dawuda muhimmin alkawari,

Ba kuwa za ka ta da alkawarin ba.

Ka ce, “Za naɗa ɗaya daga cikin ‘ya’yanka maza yă zama sarki,

Zai yi mulki a bayanka.

12 Idan ‘ya’yanka maza za su amince da alkawarina,

Da umarnan da na yi musu,

‘Ya’yansu maza kuma za su bi bayanka su zama sarakuna,

A dukan lokaci.”

13 Ubangiji ya yaɓi Sihiyona,

A can yake so ya gina Haikalinsa, ya ce,

14 “A nan zan zauna har abada.

A nan kuma nake so in yi mulki.

15 Zan tanada wa Sihiyona dukan abin da take bukata a yalwace,

Zan ƙosar da matalautanta da abinci.

16 Zan sa firistocinta su yi shela,

Cewa ina yin ceto,

Jama’ata kuma za su raira waƙa,

Suna sowa don farin ciki.

17 A nan ne zan naɗa ɗaya daga cikin zuriyar Dawuda

Yake zama babban sarki,

A nan ne kuma zan wanzar da

Mulkin zaɓaɓɓen sarkina.

18 Zan sa maƙiyansa su sha kunya,

Amma mulkinsa zai arzuta.

Ya kuma kahu.”

Categories
ZAB

ZAB 133

Yaba Ƙaunar ‘Yan’uwanci

1 Abu mai kyau ne, mai daɗi kuma,

Ga jama’ar Allah su zauna tare kamar ‘yan’uwa!

2 Yana kama da man zaitun mai daraja,

Wanda yake naso daga bisa kan Haruna zuwa gemunsa,

Har zuwa wuyan riganunsa.

3 Kamar raɓa a bisa Dutsen Harmon,

Wadda take zubowa a bisa tuddan Sihiyona.

A can ne Ubangiji ya alkawarta albarkarsa,

Rai na har abada.

Categories
ZAB

ZAB 134

Kira a Yabi Allah

1 Ku zo mu yabi Ubangiji,

Dukanku bayinsa,

Dukanku waɗanda kuke yi masa hidima,

A cikin Haikalinsa da dare.

2 Ku ɗaga hannuwanku sama, ku yi addu’a a Haikali,

Ku yabi Ubangiji!

3 Ubangiji wanda ya yi sama da duniya,

Ya sa muku albarka daga Sihiyona.

Categories
ZAB

ZAB 135

Waƙar Yabon Girman Ubangiji

1 Ku yabi Ubangiji!

Ku yabi sunansa, ku bayin Ubangiji,

2 Ku da kuke tsaye a Haikalin Ubangiji,

A wuri mai tsarki na Allahnmu.

3 Ku yabi Ubangiji, domin nagari ne shi,

Ku raira yabbai ga sunansa, domin shi mai alheri ne.

4 Ya zaɓar wa kansa Yakubu,

Jama’ar Isra’ila kuwa tasa ce.

5 Na sani Ubangijinmu mai girma ne,

Ya fi dukan alloli girma.

6 Yana aikata dukan abin da ya ga dama a Sama ko a duniya,

A tekuna, da kuma zurfafan da suke ƙarƙas.

7 Yakan kawo gizagizan hadiri daga bangayen duniya,

Yakan yi walƙiya domin hadura,

Yakan fito da iska daga cikin taskarsa.

8 A Masar ne ya karkashe ‘ya’yan fari na mutane da na dabbobi.

9 A can ne ya aikata mu’ujizai da al’ajabai,

Domin ya hukunta Fir’auna da dukan hukumar ƙasarsa.

10 Ya hallakar da sauran al’umma masu yawa,

Ya karkashe sarakuna masu iko, wato

11 Sihon, Sarkin Amoriyawa, da Og, Sarkin Bashan,

Da dukan sarakunan Kan’ana.

12 Ya ba da ƙasarsu ga jama’arsa,

Ya ba da ita ga Isra’ila.

13 Ya Ubangiji, kullayaumi mutane za su sani kai ne Allah,

Dukan tsararraki za su tuna da kai.

14 Ubangiji zai ji juyayin mutanensa,

Zai ‘yantar da bayinsa.

15 Gumakan al’ummai, da azurfa da zinariya aka yi su,

Hannuwan mutane ne suka siffata su.

16 Suna da bakuna, amma ba sa magana,

Da idanu, amma ba sa gani.

17 Suna da kunnuwa, amma ba sa ji,

Ba kuma numfashi a bakinsu.

18 Ka sa su waɗanda suka yi su,

Da dukan waɗanda suke dogara gare su,

Su zama kamar gumakan da suka yi!

19 Ku yabi Ubangiji, ya jama’ar Isra’ila,

Ku yabe shi, ya ku firistocin Allah!

20 Ku yabi Ubangiji, ya ku Lawiyawa,

Ku yabe shi, dukanku da kuke tsoronsa!

21 Ku yabi Ubangiji a Sihiyona da a Urushalima, wato a Haikalinsa.

Ku yabi Ubangiji!

Categories
ZAB

ZAB 136

Waƙar Godiyar Ƙaunar Allah

1 Ku gode wa Ubangiji domin shi mai alheri ne,

Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

2 Ku gode wa Allahn da ya fi dukan alloli girma,

Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

3 Ku gode wa Ubangijin dukan iyayengiji,

Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

4 Shi kaɗai ne yake aikata mu’ujizai masu girma,

Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

5 Ta wurin hikimarsa ya halicci sammai,

Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

6 Ya kafa duniya a bisa kan ruwa mai zurfi,

Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

7 Shi ne ya halicci rana da wata,

Gama ƙaunarsa madawwamiya ce,

8 Rana don ta yi mulkin yini,

Gama ƙaunarsa madawwamiya ce,

9 Wata da taurari kuwa don su yi mulkin dare,

Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

10 Shi ya karkashe ‘ya’yan fari maza, na Masarawa,

Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

11 Shi ya fito da jama’ar Isra’ila daga cikin Masar,

Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

12 Da ƙarfinsa da ikonsa ya fito da su,

Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

13 Shi ne ya keta Bahar Maliya biyu,

Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

14 Shi ya bi da jama’arsa ta cikin tekun,

Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

15 Shi ne ya sa ruwa ya ci Fir’auna da rundunarsa,

Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

16 Ya bi da jama’arsa cikin hamada,

Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

17 Ya karkashe sarakuna masu iko,

Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

18 Ya karkashe shahararrun sarakuna,

Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

19 Ya kashe Sihon, Sarkin Amoriyawa,

Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

20 Ya kashe Og, Sarkin Bashan,

Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

21 Ya ba da ƙasarsu ga jama’arsa,

Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

22 Ya ba da ita ga bawansa Isra’ila,

Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

23 Bai manta da mu sa’ad da aka yi nasara da mu ba,

Gama ƙaunarsa madawwamiyar ce.

24 Ya ‘yantar da mu daga abokan gābanmu,

Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

25 Yana ba da abinci ga dukan mutane da dabbobi,

Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

26 Ku yi wa Allah sa Sama godiya,

Gama ƙaunarsa madawwamiyar ce.

Categories
ZAB

ZAB 137

Kukan Isra’ilawa a Baƙuwar Ƙasa

1 A bakin kogunan Babila

Muka zauna muka yi ta kuka,

Sa’ad da muka tuna da Sihiyona.

2 A rassan itatuwan wardi da suke kusa da mu

Muka rataye garayunmu.

3 Waɗanda suka kama mu suka sa mu mu yi waƙa,

Suka ce mana, “Ku yi mana shagali

Da waƙar da aka raira wa Sihiyona!”

4 Kaƙa za mu raira waƙar Ubangiji

A baƙuwar ƙasa?

5 Da ma kada in ƙara iya kaɗa garaya,

Idan na manta da ke, Urushalima!

6 Da ma kada in ƙara iya raira waƙa,

Idan na manta da ke,

Idan ban tuna ke ce

Babbar abar farin ciki ba!

7 Ka tuna, ya Ubangiji, da abin da Edomawa suka yi,

A ranar da aka ci Urushalima.

Ka tuna da yadda suka ce,

“A ragargaza ta har ƙasa!”

8 Babila, za a hallaka ki!

Mai farin ciki ne shi wanda ya sāka miki

Bisa ga abin da kika yi mana.

9 Mai farin ciki ne shi wanda zai kwashi jariranki

Yă fyaɗa su a kan duwatsu!

Categories
ZAB

ZAB 138

Godiya domin Alherin Ubangiji

1 Da zuciya ɗaya nake gode maka, ya Ubangiji,

Ina raira waƙar yabonka a gaban alloli.

2 Na durƙusa a gaban tsattsarkan Haikalinka

Ina yabon sunanka.

Sabili da madawwamiyar ƙaunarka da amincinka,

Saboda ka nuna ɗaukakarka da umarnanka.

3 Ka amsa mini sa’ad da na yi kira gare ka,

Da ƙarfinka ka ƙarfafa ni.

4 Dukan sarakunan duniyar nan za su yabe ka, ya Ubangiji,

Gama sun riga sun ji alkawaranka.

5 Za su raira waƙa a kan abin da Ubangiji ya yi,

Za su raira waƙa kuma a kan ɗaukakarsa mai girma.

6 Ko da yake Ubangiji yana can Sama,

Duk da haka yana kulawa da masu kaɗaici.

Masu girmankai kuwa ba za su iya ɓoye kansu daga gare shi ba.

7 Ko lokacin da nake tsakiyar wahala,

Za ka kiyaye ni lafiya,

Ka yi gāba da abokan gābana, waɗanda suka husata,

Za ka kuwa cece ni da ikonka.

8 Za ka aikata kowane abu da ka alkawarta mini,

Ya Ubangiji, ƙaunarka madawwamiya ce har abada.

Ka cikasa aikin da ka fara.

Categories
ZAB

ZAB 139

Cikakken Sanin Allah da Kulawarsa

1 Ya Ubangiji, ka jarraba ni, ka san ni.

2 Ka sa dukan abin da nake yi,

Tun daga can nesa ka gane dukan tunanina.

3 Kana ganina, ko ina aiki, ko ina hutawa,

Ka san dukan ayyukana.

4 Tun kafin in yi magana

Ka riga ka san abin da zan faɗa.

5 Kana kewaye da ni a kowane sashe,

Ka kiyaye ni da ikonka.

6 Yadda ka san ni ya fi ƙarfin magana,

Ya yi mini zurfi, ya fi ƙarfin ganewata.

7 Ina zan tafi in tsere wa Ruhunka?

Ina zan gudu in tsere maka?

8 Idan na hau cikin samaniya kana can,

In na kwanta a lahira kana can,

9 In na tashi sama, na tafi, na wuce gabas,

Ko kuma na zauna a can yamma da nisa,

10 Kana can domin ka bi da ni,

Kana can domin ka taimake ni.

11 Da na iya roƙon duhu ya ɓoye ni,

Ko haske da yake kewaye da ni

Ya zama dare,

12 Amma har duhun ma, ba duhu ba ne a gare ka,

Dare kuwa haskensa kamar na rana ne.

Duhu da haske, duk ɗaya ne gare ka.

13 Kai ne ka halicci kowace gaɓa ta jikina,

Kai ne ka harhaɗa ni a cikin mahaifiyata.

14 Ina yabonka gama kai abin tsoro ne,

Dukan abin da ka yi sabo ne, mai banmamaki.

Da zuciya ɗaya na san haka ne.

15 Ka ga lokacin da ƙasusuwana suke siffatuwa,

Sa’ad da kuma ake harhaɗa su a hankali

A cikin mahaifiyata,

Lokacin da nake girma a asirce.

16 Ka gan ni kafin a haife ni.

Ka ƙididdige kwanakin da ka ƙaddara mini,

Duka an rubuta su a littafinka,

Tun kafin faruwar kowannensu.

17 Ya Allah, tunaninka suna da wuyar ganewa a gare ni,

Ba su da iyaka!

18 In na ƙirga su, za su fi tsabar yashi,

Sa’ad da na farka, har yanzu ina tare da kai.

19 Ya Allah, da yadda nake so ne, da sai ka karkashe mugaye!

‘Yan ta da zaune tsaye kuma sai su rabu da ni!

20 Suna ambaton mugayen abubuwa a kanka,

Suna faɗar mugayen abubuwa gāba da sunanka.

21 Ya Ubangiji, ga yadda nake ƙin waɗanda suke ƙinka,

Da yadda nake raina waɗanda suke tayar maka!

22 Ƙiyayyar da nake yi musu ta kai intaha,

Na ɗauke su, su abokan gābana ne.

23 Jarraba ni, ya Allah, ka san tunanina,

Gwada ni, ka gane damuwata.

24 Ka bincike, ko akwai wani rashin gaskiya a gare ni,

Ka bi da ni a madawwamiyar hanya.

Categories
ZAB

ZAB 140

Addu’ar Neman Tsari daga Mugaye

1 Ka cece ni daga mugaye, ya Ubangiji,

Ka kiyaye ni daga mutane masu hargitsi.

2 Kullum suna shirya mugunta,

Kullum suna kawo tashin hankali.

3 Harsunansu kamar macizai masu zafin dafi,

Kalmominsu kuwa kamar dafin gamsheƙa ne.

4 Ka tsare ni daga ikon masu mugunta, ya Ubangiji,

Ka kiyaye ni daga masu tashin hankali,

Waɗanda suke shirya fāɗuwata.

5 Masu girmankai sun kafa mini tarko,

Sun shimfiɗa ragar igiya,

Sun kuma kakkafa tarkuna a hanya don su kama ni.

6 Na ce wa Ubangiji, “Kai ne Allahna.

Ka ji kukana na neman taimako, ya Ubangiji!

7 Ya Ubangiji, Allahna, Mai Cetona, mai ƙarfi,

Kā kiyaye ni cikin yaƙi.

8 Ya Ubangiji, kada ka biya wa mugaye burinsu,

Kada ka bar mugayen dabaru su yi nasara!

9 “Kada ka bar maƙiyana su sami nasara,

Ka sa kashedin da suke yi mini yă koma kansu.

10 Ka sa garwashin wuta yă zubo a kansu,

Ka sa a jefa su a rami, kada su ƙara fita.

11 Ka sa waɗanda suke saran waɗansu a ƙaryace,

Kada su yi nasara.

Ka sa mugunta ta hallaka mutumin da yake ta da zaune tsaye.”

12 Na sani kai, ya Ubangiji, kana kāre matsalar talakawa,

Da hakkin matalauta.

13 Hakika adalai za su yabe ka,

Za su zauna a gabanka.