Categories
ZAB

ZAB 11

Mafakar Adalai

1 Na dogara ga Ubangiji domin zaman lafiya,

Wauta ce idan kun ce mini,

“Ka yi firiya kamar tsuntsu zuwa duwatsu,

2 Domin mugaye sun ja bakkunansu,

Sun kuma ɗana kibansu

Domin su harbi mutanen kirki a duhu.

3 Ba abin da mutumin kirki zai iya yi

Sa’ad da kome ya lalace.”

4 Ubangiji yana cikin tsattsarkan Haikalinsa,

Yana da kursiyinsa a Sama.

Yana kallon dukan mutane

Yana sane da abin da suke yi.

5 Yana auna masu kirki da mugaye dukka,

Yana ƙin marar bin doka gaba ɗaya.

6 Yakan aukar da garwashin wuta

Da kibritu mai cin wuta a kan mugaye,

Yakan hukunta su da harshen wuta mai ƙuna.

7 Ubangiji mai adalci ne, yana ƙaunar kyawawan ayyuka,

Masu yi masa biyayya za su zauna a gabansa.

Categories
ZAB

ZAB 12

Addu’ar Neman Taimako

1 Ka cece ni, ya Ubangiji,

Ba sauran mutanen kirki,

Ba kuma za a sami amintattun mutane ba.

2 Dukan mutane suna yi wa juna ƙarya,

Suna ruɗin junansu da yaudara.

3 Ka sa harsunan nan masu yaudara su yi shiru,

Ya Ubangiji, ka rufe bakunan nan masu fāriya!

4 Sukan ce, “Za mu yi magana yadda muka ga dama,

Ba kuwa wanda zai hana mu.

Wane ne yake da ikon faɗa mana abin da za mu faɗa?”

5 Ubangiji ya ce, “Amma zan zo yanzu,

Domin ana zaluntar masu bukata,

Waɗanda aka tsananta musu kuma, suna nishi don zafi.

Zan ba su zaman lafiya da suke nema!”

6 Alkawaran Ubangiji abin dogara ne,

Alkawarai ne na ainihi kamar azurfa

Da aka tace har sau bakwai cikin matoya.

7 Ka kiyaye lafiyarmu, ya Ubangiji,

Ka kiyaye mu daga irin waɗannan mutane.

8 Akwai mugaye ko’ina, suna ta yanga,

Suna ta yabon abin da yake mugunta.

Categories
ZAB

ZAB 13

Addu’ar Neman Taimako daga Wahala

1 Har yaushe za ka manta da ni, ya Ubangiji?

Har abada ne?

Har yaushe za ka ɓoye mini fuskarka?

2 Har yaushe raina zai jure da shan wahala?

Har yaushe zan yi ta ɓacin rai dare da rana?

Har yaushe maƙiyana za su riƙa cin nasara a kaina?

3 Ka dube ni, ya Ubangiji Allahna, ka amsa mini,

Ka mayar mini da ƙarfina, don kada in mutu.

4 Sa’an nan maƙiyana ba za su ce, “Ai, mun yi nasara da shi” ba!

Ba za su iya yin murna saboda fāɗuwata ba.

5 Amma ina dogara ga madawwamiyar ƙaunarka,

Zan yi murna gama za ka cece ni.

6 Zan raira waƙa ga Ubangiji,

Gama ya kyautata mini.

Categories
ZAB

ZAB 14

Muguntar ‘Yan Adam da Wautarsu

1 Wawaye sukan ce wa kansu, “Ba Allah!”

Dukansu sun lalace, sun aikata mugayen al’amura,

Ba wanda yake aikata abin da yake daidai.

2 Daga Sama Ubangiji ya dubi mutane,

Yă ga ko da akwai masu hikima

Waɗanda suke yi masa sujada.

3 Amma dukansu sun koma baya,

Su duka mugaye ne,

Ba wanda yake aikata abin da yake daidai,

Babu ko ɗaya.

4 Ubangiji ya ce, “Ba su sani ba?

Duk waɗannan masu aikin mugunta jahilai ne?

Ta wurin yi wa jama’ata fashi suke zaman gari,

Ba su yin addu’a gare ni.”

5 Amma za su razana,

Gama Allah yana tare da masu yi masa biyayya.

6 Suna yi wa shirye-shiryen kāsasshe dariya,

Saboda yana dogara ga Ubangiji.

7 Ina addu’a matuƙa domin ceto ya zo ga Isra’ila daga Sihiyona!

Sa’ad da Ubangiji ya sāke arzuta jama’arsa,

Zuriyar Yakubu za su yi farin ciki,

Jama’ar Isra’ila za su yi murna.

Categories
ZAB

ZAB 15

Mazauna a Tudun Allah Mai Tsarki

1 Wane ne zai iya zama cikin Haikalinka?

Wa zai iya tsayawa a Sihiyona, wato tudunka tsattsarka?

2 Sai dai mutumin da yake biyayya ga Allah da kowane abu,

Yana kuwa aikata abin da yake daidai,

Wanda yake faɗar gaskiya da zuciya ɗaya,

3 Wanda kuma ba ya ɓāta sunan waɗansu.

Ba ya zargin abokansa,

Ba ya kuwa baza jita-jita a kan maƙwabtansa.

4 Yakan raina waɗanda Allah ya ƙi su,

Amma yana girmama waɗanda suke yi wa Ubangiji biyayya,

Kullum yana cika alkawaran da ya yi ko ta halin ƙaƙa,

5 Yana ba da rance ba ruwa,

Ba ya karɓar hanci don ya yi shaidar zur a kan marar laifi.

Wanda ya aikata waɗannan abubuwa ba zai taɓa fāɗuwa ba.

Categories
ZAB

ZAB 16

Gādon Alheri

1 Ya Allah, ka kiyaye ni, gama na zo gare ka neman mafaka.

2 Na ce wa Ubangiji, “Kai ne Ubangijina,

Dukan kyawawan abubuwan da nake da su

Daga gare ka suke.”

3 Dubi irin martabar da amintattun jama’ar Ubangiji suke da ita!

Ba abin da raina ya fi so,

Sai in zauna tare da su.

4 Waɗanda suke hanzari zuwa ga gumaka,

Za su jawo wa kansu wahala.

Ba zan yi tarayya da su da hadayarsu ba.

Ba zan yi sujada ga gumakansu ba.

5 Kai ne kaɗai, nake da shi, ya Ubangiji,

Kai ne kake biyan dukan bukatata,

Raina yana hannunka.

6 Kyautanka zuwa gare ni da bansha’awa suke,

Kyawawa ne kuwa ƙwarai!

7 Na yabi Ubangiji saboda yana bi da ni,

Da dare kuma lamirina yana yi mini fadaka.

8 A kullum ina jin Ubangiji yana tare da ni,

Yana nan kusa, ba abin da zai girgiza ni.

9 Don haka cike nake da murna da farin ciki,

Kullum kuwa ina jin kome lafiya yake,

10 Saboda ba za ka yarda in shiga lahira ba,

Ba za ka bar wanda kake ƙauna a zurfafa daga ƙarƙas ba.

11 Za ka nuna mini hanyar rai,

Kasancewarka takan sa in cika da farin ciki,

Taimakonka kuwa yana kawo jin daɗi har abada.

Categories
ZAB

ZAB 17

Addu’ar Neman Tsari daga Azzalumai

1 Ka kasa kunne ga roƙona, ni adalin mutum,

Ka lura da kukana na neman taimako!

Ka kasa kunne ga addu’ata,

Gama ni ba mayaudari ba ne.

2 Za ka shara’anta shari’ar da za ta gamshe ni,

Saboda ka san abin da yake daidai.

3 Ka san zuciyata,

Kakan zo gare ni da dare,

Ka riga ka jarraba ni sarai,

Ba ka kuwa sami mugun nufi a cikina ba.

Na ƙudurta kuma bakina ba zai yi saɓo ba.

4 Zancen aikin sauran mutane,

Na yi biyayya ga umarninka

Ban bi hanyar rashin hankali ba.

5 Ina tafiya a kan tafarkinka kullum,

Ban kuwa kauce ba.

6 Ina addu’a gare ka, ya Allah,

Domin kakan amsa mini,

Don haka ka juyo wurina ka kasa kunne ga maganata.

7 Ka bayyana ƙaunarka mai banmamaki,

Ya Mai Ceto,

Muddin muna kusa da kai mun tsira daga maƙiyanmu.

8 Ka kiyaye ni kamar yadda ake kiyaye idanu,

Ka ɓoye ni a inuwar fikafikanka,

9 Daga hare-hare na mugaye.

Maƙiyana cike da ƙiyayya sun kewaye ni.

10 Ba su jin tausayi, suna magana da girmankai,

11 Yanzu suna kewaye da ni duk inda na juya,

Suna jira su sami dama su fyaɗa ni ƙasa.

12 Kamar zakoki suke nema su yayyage ni kaca-kaca,

Kamar sagarun zakoki suna fakona a wurin ɓuyarsu.

13 Ka zo, ya Ubangiji,

Ka yi yaƙi da maƙiyana, ka yi nasara da su!

Ka cece ni da takobinka daga mugaye,

14 Ka cece ni daga gare su da ikonka,

Ka cece ni daga waɗanda suke da duk abin da suke so a duniyan nan,

Ka hukunta su da wahalar da ka shirya musu,

Ka sa har ‘ya’yansu, su ma, ta ishe su,

Wahalar da ta ragu kuma, ta sami jikokinsu!

15 Zan gan ka domin ni adali ne,

Sa’ad da na farka, kasancewarka tana cika ni da farin ciki.

Categories
ZAB

ZAB 18

Waƙar Dawuda ta Nasara

1 Ina ƙaunarka ƙwarai, ya Ubangiji!

Kai ne mai kāre ni.

2 Ubangiji ne Mai Cetona,

Shi ne garkuwata mai ƙarfi.

Allahna, shi ne yake kiyaye ni,

Lafiya nake sa’ad da nake tare da shi,

Yana kiyaye ni kamar garkuwa,

Yana kāre ni, ya ba ni lafiya.

3 Na yi kira ga Ubangiji,

Yakan cece ni daga magabtana,

Yabo ya tabbata ga Ubangiji!

4 Mutuwa ta ɗaure ni kam da igiyoyinta,

Halaka ta auko mini a kai a kai.

5 Mutuwa ta ɗaure ni kam da igiyoyinta,

Kabari kuma ya ɗana mini tarko.

6 A shan wahalata na kira ga Ubangiji,

Na yi kira ga Allahna domin neman taimako.

A Haikalinsa ya ji muryata,

Kukana na neman taimako ya kai kunnensa.

7 Sai duniya ta raurawa ta girgiza,

Harsashin duwatsu suka jijjigu, suka girgiza

Saboda Allah ya husata!

8 Hayaƙi ya yi ta tuƙaƙowa daga hancinsa,

Harshen wuta da garwashi suna fitowa daga bakinsa.

9 Ya buɗe sararin sama, ya sauko ƙasa,

Tare da girgije mai duhu a ƙarƙashin ƙafafunsa.

10 Ya sauko ta bisa bayan kerubobi,

Yana tafe da sauri a kan fikafikan iska.

11 Ya rufe kansa da duhu,

Gizagizai masu duhu cike da ruwa, suna kewaye da shi.

12 Ƙanƙara da garwashin wuta suka sauko

Daga cikin walƙiya da take gabansa,

Suka keto ta cikin gizagizai masu duhu.

13 Sa’an nan Ubangiji ya yi tsawa daga sararin sama,

Aka ji muryar Maɗaukaki.

Ƙanƙara da garwashin wuta suka sauko.

14 Ya harba kibansa, ya watsa magabtana,

Da walƙatawar walƙiya ya kore su.

15 Kashiyar teku ta bayyana,

Tussan duniya sun bayyana,

Sa’ad da ka tsauta wa magabtana, ya Ubangiji,

Sa’ad da kuma ka yi musu tsawa da fushi.

16 Ubangiji ya miƙa hannunsa daga samaniya ya ɗauke ni,

Ya tsamo ni daga cikin ruwa mai zurfi.

17 Ya cece ni daga magabtana masu ƙarfi,

Daga kuma dukan masu ƙina,

Gama sun fi ƙarfina!

18 Sa’ad da nake shan wahala suka auka mini,

Amma Ubangiji ya kiyaye ni.

19 Ya fisshe ni daga cikin hatsari,

Ya cece ni, don yana jin daɗina.

20 Ubangiji yakan sāka mini, saboda ni adali ne,

Yakan sa mini albarka, don ni marar laifi ne.

21 Na yi biyayya da umarnan Ubangiji,

Ban yi wa Ubangiji Allahna tawaye ba.

22 Na kiyaye dukan dokokinsa,

Ban yi rashin biyayya da umarnansa ba.

23 Ya sani ba ni da laifi,

Domin na kiyaye kaina daga mugunta.

24 Don haka ya sāka mini, domin ni adali ne,

Gama ya sani ni marar laifi ne.

25 Kai, ya Ubangiji, mai aminci ne ga masu aminci,

Kai nagari ne, cikakke ga kamilai.

26 Kai Mai Tsarki ne ga waɗanda suke tsarkaka,

Amma kana gāba da mugaye.

27 Kakan ceci masu tawali’u,

Amma kakan ƙasƙantar da masu girmankai.

28 Ubangiji yakan ba ni haske,

Allah yakan kawar da duhuna.

29 Yakan ba ni ƙarfin da zan fāɗa wa magabtana,

Da ikon rinjayar kagararsu.

30 Wannan Allah dai! Ayyukansa kamiltattu ne ƙwarai,

Maganarsa abar dogara ce!

Kamar garkuwa yake, ga duk mai neman taimako a wurinsa.

31 Ubangiji shi kaɗai ne Allah,

Allah ne kaɗai kāriyamu.

32 Shi ne Allahn da yake ƙarfafa ni,

Yana kiyaye lafiyata a kan hanya.

33 Yana sa in tabbata lafiya nake tafiya, kamar barewa.

Yana kiyaye ni lafiya a kan duwatsu.

34 Yakan horar da ni don yaƙi,

Domin in iya amfani da baka mafi ƙarfi.

35 Ya Ubangiji ka kiyaye ni, ka cece ni,

Na zama babban mutum saboda kana lura da ni,

Ikonka kuma ya kiyaye lafiyata.

36 Ka tsare ni, ba a kama ni ba,

Ban kuwa taɓa fāɗuwa ba.

37 Na kori magabtana, har na kama su,

Ba zan tsaya ba, sai na yi nasara da su.

38 Zan buge su har ƙasa, ba kuwa za su tashi ba,

Za su fāɗi ƙarƙashin ƙafafuna.

39 Kakan ba ni ƙarfin yin yaƙi,

Kakan ba ni nasara a kan magabtana.

40 Ka kori magabtana daga gare ni,

Zan hallaka waɗanda suke ƙina.

41 Suna kukan neman taimako, amma ba wanda zai iya cetonsu,

Za su yi kira ga Ubangiji, amma ba zai amsa ba.

42 Zan murƙushe su har su zama ƙura

Wadda iska take kwashewa,

Zan tattake su kamar caɓi a titi.

43 Ka cece ni daga mutane masu tawaye,

Ka naɗa ni in yi mulkin sauran al’umma,

Jama’ar da ban san ta ba, ta zama abin mulkina.

44 Za su yi biyayya sa’ad da suka ji ni,

Baƙi za su rusuna mini,

45 Za su karai,

Su fita, suna rawar jiki daga kagaransu.

46 Ubangiji mai rai ne! Yabo ya tabbata ga mai kāre ni!

Allah ne, Mai Cetona! A yi shelar girmansa!

47 Yakan ba ni nasara a kan magabtana,

Yakan sa jama’a a ƙarƙashina,

48 Yakan cece ni daga maƙiyana.

Ka ba ni nasara a kan magabtana, ya Ubangiji,

Ka kiyaye ni daga mutane masu kama-karya,

49 Don haka zan yabe ka a cikin al’ummai,

Zan raira maka yabo.

50 Kullayaumi Allah yakan ba sarkin da ya naɗa babbar nasara.

Yakan nuna madawwamiyar ƙauna ga wanda ya zaɓa,

Wato Dawuda da zuriyarsa har abada.

Categories
ZAB

ZAB 19

Ayyukan Allah da Shari’arsa

1 Dubi yadda sararin sama yake bayyana ɗaukakar Allah!

Dubi yadda suke bayyana a fili ayyukansa da ya yi!

2 Kowace rana tana shelar ɗaukakarsa ga ranar da take biye,

Kowane dare yana nanata ɗaukakarsa ga daren da take biye.

3 Ba magana ko kalma da aka hurta,

Ba wani amon da aka ji,

4 Duk da haka muryarsu ta game duniya duka,

Saƙonsu ya kai ko’ina a duniya.

Allah ya kafa wa rana alfarwa a sararin sama,

5 Tana fitowa kamar ango yana taƙama daga gidansa,

Kamar ɗan wasan da ya ƙosa ya yi tsere.

6 Takan fara daga wannan ƙarshen sararin sama, ta kewaye zuwa wancan.

Ba abin da zai iya ɓuya daga zafinta.

7 Dokar Ubangiji cikakkiya ce,

Tana wartsakar da rai.

Umarnan Ubangiji abin dogara ne,

Sukan ba da hikima ga wanda ba shi da ita.

8 Ka’idodin Ubangiji daidai suke,

Waɗanda suke biyayya da su sun ji daɗi.

Umarnan Ubangiji daidai suke,

Sukan ba da fahimi ga zuciya.

9 Daidai ne a bauta wa Ubangiji,

A ci gaba da yi har abada.

Duk abin da Ubangiji ya hukunta daidai ne,

A kullum hukuntan Ubangiji daidai suke.

10 Abin da ake so ne fiye da zinariya,

I, fiye da tatacciyar zinariya ma,

Sun fi zuma zaƙi,

I, fiye da tatacciyar zuma ma.

11 Suna ba ni ilimi, ni baranka,

Ina samun ladan yin biyayya da su.

12 Ba mai iya ganin kuskuren kansa,

Ka cece ni daga ɓoyayyun laifofi!

13 Ka tsare ni kuma daga laifofi na fili,

Kada ka bari su mallake ni.

Sa’an nan zan zama kamili,

In kuɓuta daga mugun zunubi.

14 Ka sa maganata da tunanina su zama abin karɓa a gare ka,

Ya Ubangiji, Mafakata da Mai Fansata!

Categories
ZAB

ZAB 20

Addu’ar Neman Nasara

1 Ubangiji ya amsa maka a ranar wahala!

Allah na Yakubu ya kiyaye ka!

2 Ya aiko maka da taimako daga Haikalinsa,

Ya kawo maka gudunmawa daga Sihiyona.

3 Ya karɓi hadayunka,

Ya kuma ji daɗin dukan sadakokinka.

4 Ya ba ka abin da kake bukata,

Ya sa dukan shirye-shiryenka su yi nasara.

5 Mu kuma, sai mu yi sowa ta farin ciki saboda ka ci nasara,

Mu yi bikin cin nasara da ka yi,

Da yabon Ubangiji Allahnmu.

Allah ya amsa dukan roƙe-roƙenka!

6 Yanzu dai na sani Ubangiji yakan ba da nasara ga zaɓaɓɓen sarkinsa,

Yakan amsa masa daga samaniyarsa mai tsarki,

Da ikonsa mai girma yakan sa shi yă yi nasara.

7 Waɗansu ga karusan yaƙinsu suke dogara,

Waɗansu kuwa ga dawakansu,

Amma mu, ga ikon Ubangiji Allahnmu muke dogara!

8 Za su yi tuntuɓe su fāɗi,

Amma mu za mu tashi mu tsaya daram!

9 Ka ba sarki nasara, ya Ubangiji,

Ubangiji zai amsa mana sa’ad da muka yi kira.