Categories
ZAB

ZAB 21

Yabo saboda Nasara

1 Sarki yana murna, ya Ubangiji,

Domin ka ba shi ƙarfi,

Yana cike da farin ciki,

Don ka sa ya ci nasara.

2 Ka biya masa bukatarsa,

Ka amsa roƙonsa.

3 Ka zo gare shi da albarka mai yawa,

Ka sa kambin zinariya a kansa.

4 Ya roƙi rai, ka kuwa ba shi mai tsawo,

Da yawan kwanaki.

5 Darajarsa tana da girma saboda taimakonka,

Ka sa ya yi suna da martaba.

6 Albarkarka tana a kansa har abada,

Kasancewarka tare da shi, takan cika shi da murna.

7 Sarki yana dogara ga Maɗaukaki,

Saboda madawwamiyar ƙaunar Ubangiji

Zai zama sarki har abada.

8 Sarki zai kakkama dukan magabtansa,

Zai kakkama duk waɗanda suke ƙinsa.

9 Ubangiji zai hallaka su kamar harshen wuta, sa’ad da ya bayyana.

Ubangiji zai cinye su a cikin fushinsa,

Wuta kuma za ta cinye su ƙurmus.

10 Sarki zai karkashe ‘ya’yansu duka,

Zai yanyanke dukan zuriyarsu.

11 Sun ƙulla mugayen dabaru, suna fakonsa,

Amma ba za su yi nasara ba.

12 Zai harba kibansa a kansu,

Ya sa su juya su gudu.

13 Ya Ubangiji, ka zo da ƙarfinka!

Za mu raira waƙa mu yabi ikonka.

Categories
ZAB

ZAB 22

Kukan Azaba da Waƙar Yabo

1 Ya Allahna, ya Allahna,

Don me ka yashe ni?

Na yi kuka mai tsanani, ina neman taimako,

Amma har yanzu ba ka zo ba!

2 Da rana na yi kira a gare ka, ya Allahna,

Amma ba ka amsa ba.

Da dare kuma na yi kira,

Duk da haka ban sami hutawa ba.

3 Amma an naɗa ka Mai Tsarki,

Wanda Isra’ila suke yabonsa.

4 Kakanninmu suka dogara gare ka,

Sun dogara gare ka, ka kuwa cece su.

5 Suka yi kira gare ka, suka tsira daga hatsari,

Suka dogara gare ka, ba su kuwa kunyata ba.

6 A yanzu dai ni ba mutum ba ne, tsutsa ne kawai,

Rainanne, abin ba’a ga kowa da kowa!

7 Duk wanda ya gan ni

Sai yă maishe ni abin dariya,

Suna zunɗena da harshensu suna kaɗa kai.

8 Suka ce, “Ka dogara ga Ubangiji,

Me ya sa bai cece ka ba?

Idan Ubangiji na sonka,

Don me bai taimake ka ba?”

9 Kai ne ka fito da ni lafiya a lokacin da aka haife ni,

A lokacin da nake jariri ka kiyaye ni.

10 Tun daga lokacin da aka haife ni nake dogara gare ka,

Kai ne Allahna tun daga ran da aka haife ni.

11 Kada ka yi nisa da ni!

Wahala ta gabato,

Ba kuwa mai taimako.

12 Magabta da yawa sun kewaye ni kamar bijimai,

Dukansu suna kewaye da ni,

Kamar bijimai masu faɗa na ƙasar Bashan.

13 Sun buɗe bakinsu kamar zakoki,

Suna ruri, suna ta bina a guje.

14 Ƙarfina ya ƙare,

Ya rabu da ni kamar ruwan da ya zube ƙasa.

Dukan gaɓoɓina sun guggulle,

Zuciyata ta narke kamar narkakken kakin zuma.

15 Maƙogwarona ya bushe kamar ƙura,

Harshena kuma na liƙe wa dasashina na sama.

Ka bar ni matacce cikin ƙura.

16 Ƙungiyar mugaye na kewaye da ni,

Suka taso mini kamar garken karnuka,

Suka soke hannuwana da ƙafafuna.

17 Ana iya ganin ƙasusuwana duka.

Magabtana suka dube ni, suka zura mini ido.

18 Suka rarraba tufafina a tsakaninsu,

Suka jefa kuri’a a kan babbar rigata.

19 Kada ka yi nisa da ni, ya Ubangiji!

Ka gaggauta ka cece ni, ya Mai Cetona!

20 Ka cece ni daga takobi,

Ka ceci raina daga waɗannan karnuka.

21 Ka kuɓutar da ni daga waɗancan zakoki,

Ba ni da mataimaki a gaban bijimai masu mugun hali.

22 Zan faɗa wa mutanena abin da ka yi,

Zan yabe ka cikin taronsu.

23 “Ku yabe shi, ku bayin Ubangiji!

Ku girmama shi, ku zuriyar Yakubu!

Ku yi masa sujada, ku jama’ar Isra’ila!

24 Ba ya ƙyale matalauta,

Ko ya ƙi kulawa da wahalarsu,

Ba ya rabuwa da su,

Amma yakan amsa lokacin da suka nemi taimako.”

25 Zan yabe ka a gaban babban taron jama’a

Saboda abin da ka yi,

A gaban dukan masu yi maka biyayya,

Zan miƙa sadakokin da na alkawarta.

26 Matalauta za su ci yadda suke so,

Masu zuwa wurin Ubangiji za su yabe shi,

Su arzuta har abada!

27 Dukan al’ummai za su tuna da Ubangiji,

Za su zo gare shi daga ko’ina a duniya,

Dukan kabilai za su yi masa sujada.

28 Ubangiji Sarki ne,

Yana mulki a kan al’ummai.

29 Masu girmankai duka za su rusuna masa,

‘Yan adam duka za su rusuna masa,

Dukan waɗanda aka ƙaddara musu mutuwa.

30 Zuriya masu zuwa za su bauta masa,

Mutane za su ambaci Ubangiji ga zuriya mai zuwa.

31 Mutanen da ba a haifa ba tukuna, za a faɗa musu,

“Ubangiji ya ceci jama’arsa!”

Categories
ZAB

ZAB 23

Ubangiji Makiyayina Ne

1 Ubangiji makiyayina ne,

Ba zan rasa kome ba.

2 Yana sa ni in huta a saura mai ɗanyar ciyawa,

Yana bi da ni a tafkuna masu daɗin ruwa, suna kwance lif.

3 Yana ba ni sabon ƙarfi.

Yana bi da ni a hanyar da suke daidai kamar yadda ya alkawarta.

4 Ko da hanyan nan ta bi ta tsakiyar duhu na mutuwa,

Ba zan ji tsoro ba, ya Ubangiji,

Gama kana tare da ni!

Sandanka na makiyayi da kerenka

Suna kiyaye lafiyata.

5 Ka shirya mini liyafa

Inda maƙiyana duk za su iya ganina,

Ka marabce ni, ka shafe kaina da mai,

Ka cika tanduna fal da mai.

6 Hakika, alherinka da ƙaunarka

Za su kasance tare da ni muddin raina.

Haikalinka zai zama gidana har abada.

Categories
ZAB

ZAB 24

Sarkin Ɗaukaka

1 Duniya da dukan abin da yake cikinta na Ubangiji ne,

Duniya da dukan mazaunanta nasa ne.

2 Ya gina ta a bisa ruwa mai zurfi na ƙarƙashin ƙasa,

Ya kuma kafa harsashinta a zurfin teku.

3 Wa yake da iko yă hau tudun Ubangiji?

Wa yake da iko ya shiga Haikalinsa tsattsarka?

4 Sai wanda yake da tsarki cikin aiki, da tunani,

Wanda ba ya yi wa gumaka sujada,

Ko kuma yă yi alkawarin ƙarya.

5 Ubangiji zai sa masa albarka,

Allah Mai Cetonsa zai kuɓutar da shi.

6 Su ne irin mutanen da suke zuwa wurin Allah,

Waɗanda suke zuwa a gaban Allah na Yakubu.

7 A buɗe ƙofofi sosai,

A buɗe daɗaɗɗun ƙofofi,

Babban Sarki kuwa zai shigo!

8 Wane ne wannan babban Sarki?

Ubangiji ne mai ƙarfi mai iko,

Ubangiji mai nasara cikin yaƙi!

9 A buɗe ƙofofi sosai,

A buɗe daɗaɗɗun ƙofofi,

Babban Sarki kuwa zai shigo!

10 Wane ne wannan babban Sarki?

Ubangiji Mai Runduna, shi ne babban Sarki!

Categories
ZAB

ZAB 25

Addu’a domin Biyarwa, da Gafartawa, da Kiyayewa

1 A gare ka nake yin addu’a, ya Ubangiji,

2 A gare ka nake dogara, ya Allah.

Ka cece ni daga shan kunyar fāɗuwa,

Kada ka bar magabtana su yi mini duban wulakanci!

3 Waɗanda suke dogara gare ka,

Ba za su kasa yin nasara ba,

Sai dai waɗanda suke gaggawa su yi maka tayarwa.

4 Ka koya mini al’amuranka, ya Ubangiji,

Ka sa su zama sanannu a gare ni.

5 Ka koya mini in yi zamana bisa ga gaskiyarka,

Gama kai Mai Cetona ne.

Dukan yini ina dogara a gare ka.

6 Ya Ubangiji, ka tuna da alherinka da madawwamiyar ƙaunarka,

Waɗanda ka nuna tun a dā.

7 Ka gafarta zunubaina da kurakuraina masu yawa na ƙuruciyata.

Saboda madawwamiyar ƙaunarka da alherinka,

Ka tuna da ni, ya Ubangiji!

8 Ubangiji mai adalci ne, mai alheri,

Yana koya wa masu zunubi tafarkin da za su bi.

9 Yana bi da masu tawali’u a tafarkin da suke daidai,

Yana koya musu nufinsa.

10 Da ƙauna da aminci yana bi da dukan waɗanda suke biyayya da alkawarinsa da umarnansa.

11 Ka cika alkawarinka, ya Ubangiji, ka gafarta zunubaina, gama suna da yawa.

12 Waɗanda suke biyayya da Ubangiji

Za su koyi hanyar da za su bi daga gare shi.

13 Kullayaumi za su arzuta,

‘Ya’yansu kuma za su zauna lafiya a ƙasar.

14 Ubangiji yakan amince da waɗanda suke biyayya da shi,

Yakan koya musu alkawarinsa.

15 A koyaushe ga Ubangiji nake neman taimako,

Yakan kuɓutar da ni daga hatsari.

16 Ka juyo wajena, ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai,

Gama ina zaman kaɗaici da rashin ƙarfi.

17 Damuwar zuciyata ta yi yawa,

Ka raba ni da dukan damuwa,

Ka cece ni daga dukan wahalata.

18 Ka kula da wahalata da azabata,

Ka gafarta dukan zunubaina.

19 Ka duba yawan magabtan da nake da su,

Dubi irin ƙiyayyar da suke yi mini!

20 Ka yi mini kāriya, ka cece ni,

Gama na zo wurinka neman kāriya.

21 Ka sa nagartata da amincina su kiyaye ni,

Gama na dogara gare ka.

22 Ka fanshi jama’arka daga dukan wahalarsu, ya Allah!

Categories
ZAB

ZAB 26

Addu’ar Neman Tsare Mutunci

1 Ka hurta rashin laifina, ya Ubangiji,

Gama na yi abin da suke daidai,

Na dogara gare ka gaba ɗaya.

2 Ka jarraba ni ka auna ni, ya Ubangiji,

Ka gwada muradina da tunanina.

3 Madawwamiyar ƙaunarka tana bi da ni,

Amincinka yake yi mini jagora kullayaumin.

4 Ba na tarayya da mutanen banza,

Ba abin da ya gama ni da masu riya.

5 Ina ƙin tarayya da masu mugunta,

Nakan kauce wa mugaye.

6 Ya Ubangiji, na wanke hannuwana

Don in nuna ba ni da laifi,

Da ibada nakan taka, ina kewaya bagadenka.

7 Na raira waƙar godiya,

Na faɗi dukan ayyukanka masu banmamaki.

8 Ya Ubangiji, ina ƙaunar Haikali inda zatinka yake,

Inda ɗaukakarka yake zaune.

9 Kada ka hallaka ni tare da masu zunubi,

Ka cece ni daga ƙaddarar masu kisankai,

10 Mutanen da suke aikata mugunta a dukan lokaci,

A koyaushe suna shirye don su ba da rashawa.

11 Amma ni, ina yin abin da yake daidai,

Ka yi mini jinƙai ka fanshe ni!

12 Na kuɓuta daga dukan hatsarori,

A taron sujada na yabi Ubangiji!

Categories
ZAB

ZAB 27

Ubangiji Ne Haskena da Cetona

1 Ubangiji ne haskena da cetona,

Ba zan ji tsoron kowa ba.

Ubangiji yana kiyaye ni daga dukan hatsari,

Ba zan ji tsoro ba.

2 Sa’ad da mugaye suka tasar mini,

Suna ƙoƙari su kashe ni,

Za su yi tuntuɓe su fāɗi.

3 Ko da rundunar mayaƙa ta kewaye ni,

Ba zan ji tsoro ba.

Ko da magabtana sun tasar mini,

Zan dogara ga Allah.

4 Abu guda nake roƙo a wurin Ubangiji,

Abu ɗaya kaɗai nake bukata,

Shi ne in zauna a masujadar Ubangiji,

In yi ta al’ajabin alherinsa

Dukan kwanakin raina,

In roƙi biyarwarsa a can.

5 A lokatan wahala zai kiyaye ni a inuwarsa,

Zai kiyaye ni lafiya a Haikalinsa,

Zai ɗora ni a kan dutse mai tsayi, ya kiyaye ni.

6 Ta haka zan ci nasara a kan magabtana da suke kewaye da ni.

Da sowar farin ciki mai yawa zan miƙa sadakoki a Haikalinsa!

Zan raira waƙa, in yabi Ubangiji!

7 Ka ji ni, ya Ubangiji, sa’ad da na ya yi kira gare ka!

Ka yi mini jinƙai ka amsa mini!

8 Ka ce, “Zo wurina,”

Zan kuwa zo gare ka, ya Ubangiji,

9 Kada ka ɓoye mini fuskarka, ya Ubangiji!

Kada ka yi fushi da ni,

Kada kuwa ka kori bawanka.

Kai ne kake taimakona, tun dā ma,

Kada ka bar ni, kada ka yashe ni,

Ya Allahna, Mai Cetona!

10 Mai yiwuwa ne ubana da uwata su yashe ni,

Amma Ubangiji zai lura da ni.

11 Ka koya mini abin da ya kamata in yi, ya Ubangiji,

Ka bi da ni kan lafiyyiyar hanya,

Domin ina da magabta da yawa.

12 Kada ka bar ni a hannun magabtana,

Waɗanda suke fāɗa mini da ƙarairayi da kurari.

13 Hakika zan rayu domin in ga alherin Ubangiji

Da zai yi wa jama’arsa.

14 Ka dogara ga Ubangiji!

Ka yi imani, kada ka karai.

Ka dogara ga Ubangiji!

Categories
ZAB

ZAB 28

Addu’ar Roƙo da Yabo

1 Ina kira gare ka, ya Ubangiji mai kāre ni,

Ka ji kukana!

In kuwa ba ka amsa mini ba,

Zan zama ɗaya daga cikin waɗanda suka gangara zuwa lahira.

2 Ka ji ni lokacin da na yi kuka gare ka neman taimako,

Ina ɗaga hannuwana wajen tsattsarkan Haikalinka.

3 Kada ka kāshe ni tare da mugaye,

Tare da masu aikata mugunta,

Mutane waɗanda maganarsu kamar ta zumunci ce,

Amma zukatansu cike suke da ƙiyayya.

4 Ka hukunta su saboda abin da suka aikata.

Ka hukunta su saboda dukan ayyukansu,

Ka ba su abin da ya cancance su!

5 Ba su kula da abin da Ubangiji ya yi ba,

Ko kuma abin da ya halitta,

Don haka zai hukunta su, ya hallaka su har abada.

6 A yabi Ubangiji,

Gama ya ji kukana na neman taimako!

7 Ubangiji yakan kiyaye ni, yă tsare ni.

Na dogara gare shi.

Ya taimake ni, don haka ina murna,

Ina raira masa waƙoƙin yabo.

8 Ubangiji yana kiyaye jama’arsa,

Yakan kiyaye sarkinsa da ya zaɓa, ya kuma cece shi.

9 Ka ceci jama’arka, ya Ubangiji,

Ka sa wa waɗanda suke naka albarka!

Ka zama makiyayinsu,

Ka lura da su har abada.

Categories
ZAB

ZAB 29

Muryar Ubangiji a cikin Hadiri

1 Ku yabi Ubangiji, ku alloli,

Ku yabi ɗaukakarsa da ikonsa.

2 Ku yabi sunan Ubangiji mai daraja,

Ku rusuna a gaban Mai Tsarki sa’ad da ya bayyana.

3 An ji muryar Ubangiji a kan tekuna,

Allah Maɗaukaki ya yi tsawa,

Tsawar muryarsa kuwa ta yi amsa kuwa a bisa teku.

4 An ji muryar Ubangiji

A dukan ikonsa da zatinsa!

5 Muryar Ubangiji takan karya itatuwan al’ul,

Har ma da itatuwan al’ul na Lebanon.

6 Yakan sa duwatsun Lebanon su yi tsalle kamar ‘yan maruƙa,

Ya kuma sa Dutsen Harmon ya yi tsalle kamar ɗan maraƙi.

7 Muryar Ubangiji ta sa walƙiya ta walƙata.

8 Muryarsa ta sa hamada ta girgiza,

Ta girgiza hamadar Kadesh.

9 Muryar Ubangiji ta sa barewa ta haihu,

Ta sa itatuwa su kakkaɓe,

Sa’ad da aka yi sowa a cikin Haikalinsa,

Aka ce, “Daukaka ga Allah!”

10 Ubangiji yana sarautar ruwa mai zurfi,

Yana sarauta kamar sarki har abada.

11 Ubangiji yana ba jama’arsa ƙarfi,

Ya sa musu albarka da salama.

Categories
ZAB

ZAB 30

Addu’ar Godiya domin Kuɓuta daga Mutuwa

1 Ina yabonka, ya Ubangiji saboda ka cece ni,

Ka kuwa hana magabtana su haɗiye ni.

2 Na roƙi taimako a gare ka, ya Ubangiji Allahna,

Ka kuwa warƙar da ni.

3 Ka dawo da ni daga lahira.

Na gangara tare da waɗanda suke gangarawa cikin zurfafa a ƙasa,

Amma ka ceci raina.

4 Ku raira yabo ga Ubangiji,

Ku amintattun jama’arsa!

Ku tuna da abin da Mai Tsarki ya aikata,

Ku yi masa godiya!

5 Fushinsa ba ya daɗewa,

Alherinsa kuwa har matuƙa ne.

Mai yiwuwa ne yă zama ana kuka da dare,

Amma a yi murna da safe.

6 Ina zaune jalisan, na ce wa kaina,

“Faufau ba za a taɓa cin nasara a kaina ba.”

7 Kana yi mini alheri, ya Ubangiji,

Ka kiyaye ni kamar a kagarar dutse.

Amma sa’ad da ka ɓoye mini fuskarka,

Sai in cika da tsoro.

8 Ina kira gare ka, ya Ubangiji,

Ina roƙon taimakonka.

9 Wane amfani za a samu daga mutuwata?

Ina ribar da za a samu daga zuwana kabari?

Ko matattu suna iya yabonka?

Za su iya shelar madawwamin alherinka?

10 Ka ji ni, ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai!

Ka taimake ni, ya Ubangiji!

11 Ka mai da baƙin cikina

Ya zama rawar farin ciki,

Ka tuɓe mini tufafin makoki,

Ka sa mini na farin ciki.

12 Don haka ba zan yi shiru ba,

Zan raira maka yabo,

Ya Ubangiji, kai ne Allahna,

Zan gode maka har abada.