Categories
ZAB

ZAB 31

Addu’ar Dogara ga Allah

1 Na zo gare ka, ya Ubangiji, domin ka kiyaye ni.

Kada ka bari a yi nasara da ni.

Kai Allah mai adalci ne,

Ka cece ni, ina roƙonka!

2 Ka ji ni! Ka cece ni yanzu!

Ka zama mafakata, don ka kiyaye ni,

Ka zama mai kāre ni, don ka cece ni.

3 Kai ne mafakata da kariyata,

Ka bi da ni yadda ka alkawarta.

4 Ka kiyaye ni daga tarkon da aka kafa domina,

Kai ne inuwata.

5 Ina ba da kaina gare ka domin ka kiyaye ni.

Za ka fanshe ni, ya Ubangiji,

Kai Allah mai aminci ne.

6 Kana ƙin waɗanda suke yi wa gumaka sujada,

Amma ni na dogara gare ka.

7 Zan yi murna da farin ciki,

Saboda madawwamiyar ƙaunarka.

Ka ga wahalata,

Ka kuwa san damuwata.

8 Ba ka bar magabtana su kama ni ba,

Ka kiyaye ni.

9 Ka yi mini jinƙai, ya Ubangiji,

Gama ina shan wahala,

Idanuna sun gaji saboda yawan kuka,

Na kuwa tafke ƙwarai!

10 Baƙin ciki ya gajerta kwanakina,

Kuka kuma ya rage shekaruna.

Na raunana saboda yawan wahalata,

Har ƙasusuwana suna zozayewa!

11 Magabtana duka suna mini ba’a,

Maƙwabtana sun raina ni,

Waɗanda suka san ni kuwa suna jin tsorona,

Sa’ad da suka gan ni a kan titi sukan guje mini.

12 Duk an manta da ni kamar matacce,

Na zama kamar abin da aka jefar.

13 Na ji magabtana da yawa suna raɗa,

Razana ta kewaye ni!

Suna ƙulla maƙarƙashiya don su kashe ni.

14 Amma a gare ka na dogara, ya Ubangiji,

Kai ne Allahna.

15 Kana lura da ni kullum,

Ka cece ni daga magabtana,

Daga waɗanda suke tsananta mini.

16 Ni, bawanka ne,

Ka dube ni da alherinka,

Ka cece ni saboda madawwamiyar ƙaunarka!

17 Ina kira gare ka, ya Ubangiji,

Kada ka bari a ci nasara a kaina!

Ka sa a ci nasara a kan mugaye,

Ka sa su yi shiru a lahira.

18 Ka rufe bakin maƙaryatan can

Dukan masu girmankai da masu fāriya,

Waɗanda suke wa adalai maganar raini!

19 Abin al’ajabi ne irin tanadin da ka yi wa masu tsoronka!

Abin da kake aikatawa a gaban kowa kuma,

Yana da banmamaki.

Kana kiyaye waɗanda suke amincewa da kai.

20 Ka ɓoye su a wurinka lafiya daga makircin mutane,

A inuwa mai lafiya ka ɓoye su daga zargin magabtansu.

21 Yabo ya tabbata ga Ubangiji!

Gama ya nuna mini ƙaunarsa mai ban al’ajabi,

Sa’ad da aka kewaye ni, aka fāɗa mini!

22 Na ji tsoro, na zaci ka jefar da ni ne daga gabanka.

Amma ka ji kukana sa’ad da na yi kira gare ka neman taimako.

23 Ku ƙaunaci Ubangiji, ku amintattun jama’arsa duka!

Ubangiji yana kiyaye masu aminci,

Amma yakan hukunta masu girmankai da tsanani.

24 Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali,

Dukanku da kuke sa zuciya ga Ubangiji!

Categories
ZAB

ZAB 32

Albarkar Gafarar Zunubi

1 Mai farin ciki ne mutumin da aka gafarta masa zunubansa,

Mai farin ciki ne kuma wanda aka gafarta masa laifofinsa.

2 Mai farin ciki ne wanda Ubangiji bai zarge shi a kan wani laifi ba,

Wanda ba algus ko kaɗan a cikinsa.

3 Sa’ad da ban hurta zunubaina ba,

Na gajiyar da kaina da yawan kuka dukan yini.

4 Ka hukunta ni dare da rana, ya Ubangiji,

Ƙarfina duka ya ƙare sarai,

Kamar yadda laima yake bushewa,

Saboda zafin bazara.

5 Sa’an nan na hurta zunubaina gare ka,

Ban ɓoye laifofina ba.

Na ƙudurta in hurta su gare ka,

Ka kuwa gafarta dukan laifofina.

6 Saboda haka dukan jama’arka masu biyayya,

Za su yi addu’a gare ka, lokacin bukata.

Sa’ad da babbar rigyawa ta malalo,

Ba za ta kai wurinsu ba.

7 Kai ne maɓoyata,

Za ka cece ni daga wahala.

Ina raira waƙa da ƙarfi saboda cetonka,

Domin ka kiyaye ni.

8 Ubangiji ya ce, “Zan koya maka hanyar da za ka bi,

Zan koya maka, in kuma ba ka shawara.

9 Kada ka zama wawa kamar doki ko alfadari,

Wanda dole sai da linzami, da ragama za a sarrafa shi,

Sa’an nan yă yi maka biyayya.”

10 Tilas ne mugu yă sha wahala,

Amma masu dogara ga Ubangiji,

Madawwamiyar ƙaunarsa tana kiyaye su.

11 Dukanku adalai, ku yi murna,

Ku yi farin ciki,

Saboda abin da Ubangiji ya yi!

Dukanku da kuke yi masa biyayya,

Ku yi sowa ta farin ciki!

Categories
ZAB

ZAB 33

Waƙar Yabo

1 Dukanku adalai ku yi murna,

A kan abin da Ubangiji ya yi,

Ku yabe shi, ku da kuke masa biyayya!

2 Ku kaɗa garaya, kuna yi wa Ubangiji godiya.

Ku raira masa waƙa, da kayan kaɗe-kaɗe masu tsarkiya.

3 Ku raira masa sabuwar waƙa,

Ku kaɗa garaya da gwaninta,

Ku kuma raira waƙa da ƙarfi!

4 Kalmomin Ubangiji gaskiya ne,

Ayyukansa duka kuwa abin dogara ne.

5 Ubangiji yana ƙaunar abin da yake na adalci da gaskiya,

Madawwamiyar ƙaunarsa ta cika duniya.

6 Ubangiji ya halicci duniya da umarninsa,

Rana, da wata, da taurari kuma bisa ga maganarsa.

7 Ya tattara tekuna wuri ɗaya.

Ya rurrufe zurfafan teku a ɗakunan ajiya.

8 Bari duk duniya ta ji tsoron Ubangiji!

Ku ji tsoronsa ku mutanen duniya!

9 Da magana ya halicci duniya,

Ta wurin umarninsa kowane abu ya bayyana.

10 Ubangiji yakan sassoke manufofin sauran al’umma,

Yakan hana su aikata shirye-shiryensu.

11 Amma shirye-shiryensa sukan tabbata har abada.

Nufe-nufensa kuma dawwamammu ne har abada.

12 Mai farin ciki ce al’ummar da Ubangiji yake Allahnta,

Masu farin ciki ne jama’ar da Ubangiji ya zaɓo wa kansa!

13 Daga Sama Ubangiji ya dubo dukan ‘yan adam.

14 Daga inda yake mulki, yakan dubo dukan mazaunan duniya.

15 Shi ya siffata tunaninsu, yana sane da dukan abin da suke yi.

16 Ba saboda ƙarfin mayaƙa sarki yakan ci nasara ba,

Mayaƙi ba yakan yi rinjaye saboda ƙarfinsa ba.

17 Dawakan yaƙi ba su da amfani don cin nasara,

Ƙarfin nan nasu ba zai iya ceto ba.

18 Ubangiji yana kiyaye masu tsoronsa,

Waɗanda suke dogara ga madawwamiyar ƙaunarsa.

19 Yakan cece su daga mutuwa,

Yakan rayar da su a lokacin yunwa.

20 Ga Ubangiji muke sa zuciya,

Shi mai taimakonmu ne, mai kiyaye mu.

21 Saboda da shi muke murna,

Muna dogara ga sunansa mai tsarki.

22 Ka sa madawwamiyar ƙaunarka ta kasance tare da mu, ya Ubangiji,

Da yake a gare ka muke sa zuciya.

Categories
ZAB

ZAB 34

Yabo domin Kuɓuta

1 Zan yi godiya ga Ubangiji kullayaumin,

Faufau ba zan taɓa fasa yabonsa ba.

2 Zan yabe shi saboda abin da ya yi,

Da ma dukan waɗanda suke da tawali’u su kasa kunne, su yi murna!

3 Ku yi shelar girman Ubangiji tare da ni,

Mu yabi sunansa tare!

4 Na yi addu’a ga Ubangiji, ya kuwa amsa mini,

Ya kuɓutar da ni daga dukan tsorona.

5 Waɗanda ake zalunta suka dube shi suka yi murna,

Ba za su ƙara ɓacin rai ba.

6 Marasa galihu suka yi kira gare shi, ya kuwa amsa.

Ya cece su daga dukan wahalarsu.

7 Mala’ikansa yana tsaron waɗanda suke tsoron Ubangiji,

Ya cece su daga hatsari.

8 Ku gane da kanku yadda Ubangiji yake da alheri!

Mai farin ciki ne mutumin da ya sami kwanciyar rai a wurinsa!

9 Ku yi tsoron Ubangiji ku jama’arsa duka,

Masu tsoronsa suna da dukan abin da suke bukata.

10 Har zakoki sukan rasa abinci su ji yunwa,

Amma masu biyayya ga Ubangiji,

Ba abu mai kyau da sukan rasa.

11 Ku zo, ku abokaina, ku kasa kunne gare ni,

Zan koya muku ku ji tsoron Ubangiji.

12 Kuna so ku ji daɗin rai?

Kuna son tsawon rai da farin ciki?

13 To, ku yi nisa da mugun baki,

Da faɗar ƙarairayi.

14 Ku rabu da mugunta, ku aikata alheri,

Ku yi marmarin salama, ku yi ƙoƙarin samunta.

15 Ubangiji yana lura da adalai,

Yana kasa kunne ga koke-kokensu,

16 Amma yana ƙin masu aikata mugunta,

Saboda haka har mutanensu sukan manta da su.

17 Adalai sukan yi kira ga Ubangiji, yakan kuwa kasa kunne,

Yakan cece su daga dukan wahalarsu.

18 Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai,

Yakan ceci waɗanda suka fid da zuciya.

19 Mutumin kirki yakan sha wahala da yawa,

Amma Ubangiji yakan cece shi daga cikinsu duka.

20 Ubangiji yakan kiyaye shi sosai,

Ba ko ɗaya daga cikin ƙasusuwansa da zai karye ba.

21 Mugunta za ta kashe mugu,

Waɗanda suke ƙin adalai za a hukunta su.

22 Ubangiji zai fanshi bayinsa,

Waɗanda suka tafi wurinsa neman mafaka

Za a bar su da rai.

Categories
ZAB

ZAB 35

Addu’ar Kuɓuta daga Maƙiya

1 Ka yi hamayya da masu hamayya da ni, ya Ubangiji,

Ka yi faɗa da masu faɗa da ni!

2 Ɗauki garkuwa da makamanka, ka zo ka taimake ni.

3 Ka daga mashin yaƙinka sama, da gatarinka,

Ka yi gaba da masu fafarata.

Ka faɗa mini kai ne Mai Cetona!

4 Ka sa a kori waɗanda suke ƙoƙari su kashe ni, a kunyatar da su!

Ka sa waɗanda suke mini maƙarƙashiya su juya da baya, su ruɗe!

5 Ka sa su zama kamar tattakar da iska take kwashewa,

Kamar waɗanda mala’ikan Ubangiji yake korarsu!

6 Ka sa hanyarsu ta duhunta, ta yi santsi,

A sa’ad da mala’ikan Ubangiji yake fyaɗe su ƙasa!

7 Suka kafa mini tarko ba dalili,

Sun kuma haƙa rami mai zurfi don in faɗa ciki.

8 Amma kafin su farga, hallaka za ta kama su.

Tarkunan da suka kafa za su kama su,

Su kuma fāɗa cikin ramin da suka haƙa!

9 Sa’an nan zan yi murna saboda Ubangiji,

Zan yi murna, gama ya cece ni.

10 Da zuciya ɗaya zan ce wa Ubangiji,

“Ba wani kamarka!

Kakan kāre marasa ƙarfi daga masu ƙarfi,

Talaka da matalauci kuma daga azzalumai!”

11 Mugaye suna ba da muguwar shaida a kaina,

Suna kai ƙarata a kan laifofin da ban san kome a kansa ba.

12 Sun sāka mini alheri da mugunta,

Cike nake da nadama.

13 Amma sa’ad da suke ciwo, nakan sa tufafin makoki,

Na ƙi cin abinci,

Na yi addu’a da kaina a sunkuye,

14 Kamar yadda zan yi wa aboki ko ɗan’uwa addu’a.

Ina tafe a takure saboda makoki,

Kamar wanda yake makoki domin mahaifiyarsa.

15 Sa’ad da nake shan wahala,

Murna suke yi duka,

Sun kewaye ni, suna ta yi mini dariya,

Baƙi sun duke ni, suna ta buguna.

16 Suka wahalshe ni, suka yi mini dariya,

Suna hararata da ƙiyayya.

17 Sai yaushe, za ka duba, ya Ubangiji?

Ka kuɓutar da ni daga farmakinsu,

Ka ceci raina daga waɗannan zakoki!

18 Sa’an nan zan yi maka godiya a gaban babban taron jama’a.

Zan yabe ka a gaban babban taro.

19 Kada ka bar maƙiyana, maƙaryatan nan, su ga fāɗuwata!

Kada ka bar waɗanda suke ƙina ba dalili,

Su ƙyaface ni, su yi murna saboda baƙin cikina!

20 Ba su yin maganar zumunci,

A maimakon haka sukan ƙaga ƙarairayi a kan masu ƙaunar limana.

21 Sukan zarge ni da kakkausan harshe,

Su ce, “Mun ga abin da ka yi!”

22 Amma kai, ya Ubangiji ka ga wannan.

Saboda haka kada ka ƙyale su, ya Ubangiji,

Kada ka yi nisa!

23 Ka tashi, ya Ubangiji, ka kāre ni.

Ya Allah ka tashi, ka bi mini hakkina.

24 Kai mai adalci ne, ya Ubangiji, ka shaida rashin laifina,

Kada ka bar maƙiyana su ƙyaface ni, ya Allahna!

25 Kada ka bar su su ce wa kansu,

“Madalla! Da ma abin da muke so ke nan!”

Kada ka bar su su ce,

“Mun rinjaye shi!”

26 Ka sa waɗanda suka ƙyaface ni a wahalata,

A rinjaye su, su ruɗe.

Ka sa waɗanda suke ɗaukar kansu sun fi ni,

Su sha kunya da wulakanci!

27 Ka sa waɗanda suke murna da kuɓutata

Su yi ta sowa ta murna, suna cewa,

“Ubangiji mai girma ne!

Yana murna da cin nasarar bawansa!”

28 Sa’an nan zan yi shelar adalcinka,

Dukan yini kuwa zan yi ta yabonka.

Categories
ZAB

ZAB 36

Madawwamiyar Ƙaunar Allah

1 Zunubi yakan yi magana da mugun daga can gindin zuciyarsa,

Yakan ƙi Allah, ba ya jin tsoronsa.

2 Domin yana ganin kansa shi wani abu ne,

A tsammaninsa Allah ba zai tona asirinsa ba,

Ya hukunta zunubinsa.

3 Maganarsa mugunta ce cike da ƙarairayi,

Ba shi da sauran isasshiyar hikima da zai aikata nagarta.

4 Yana ƙulla mugunta lokacin da yake kwance a gadonsa,

Halinsa ba shi da kyau,

Ba ya ƙin abin da yake mugu.

5 Madawwamiyar ƙaunarka, ya Ubangiji,

Ta kai har sammai,

Amincinka ya kai sararin sammai.

6 Adalcinka kafaffe ne,

Kamar manyan duwatsu.

Hukuntanka kamar teku mai zurfi suke.

Ya Ubangiji, kai kake lura da mutane da dabbobi.

7 Ina misalin darajar madawwamiyar ƙaunarka, ya Ubangiji!

Mutane sukan sami mafaka a ƙarƙashin fikafikanka.

8 Sukan yi biki da yalwataccen abincin da yake Haikalinka,

Kakan shayar da su daga koginka na alheri.

9 Kai ne mafarin dukan rai,

Saboda haskenka ne kuma, muke ganin haske,

10 Ka yi ta ƙaunar waɗanda suka san ka,

Ka yi wa adalai alheri.

11 Kada ka bar masu girmankai su fāɗa mini,

Kada ka bar mugaye su kore ni.

12 Dubi inda mugaye suka fāɗi!

Can suka kwanta, ba su iya tashi.

Categories
ZAB

ZAB 37

Makomar Mugaye da ta Nagargaru

1 Kada ka damu saboda mugaye,

Kada ka yi ƙyashin masu aikata abin da ba daidai ba.

2 Za su shuɗe kamar busasshiyar ciyawa,

Za su mutu kamar yadda tsire-tsire suke bushewa.

3 Ka dogara ga Ubangiji ka aikata nagarta,

Ka zauna a ƙasar, ka sami lafiya.

4 Ka nemi farin cikinka a wurin Ubangiji,

Zai kuwa biya maka bukatarka.

5 Ka miƙa kanka ga Ubangiji,

Ka dogara gare shi, zai kuwa taimake ka.

6 Zai sa nagartarka ta haskaka kamar haske,

Adalcinka kuma yă haskaka kamar tsakar rana.

7 Ka natsu a gaban Ubangiji,

Ka yi haƙuri, ka jira shi,

Kada ka damu da waɗanda suke da dukiya,

Ko su da suka yi nasara da aikata mugayen shirye-shiryensu.

8 Kada ka yi fushi, kada ka hasala!

Kada ka damu! Gama ba zai yi maka amfanin kome ba.

9 Waɗanda suka dogara ga Ubangiji,

Za su yi zamansu lafiya a ƙasar,

Amma za a kori mugaye.

10 A ɗan ƙanƙanen lokaci mugaye za su shuɗe,

Za ka neme su, amma ba za a same su ba,

11 Amma masu ladabi za su zauna lafiya a ƙasar,

Su ji daɗin cikakkiyar salama.

12 Mugu yakan yi wa mutumin kirki makarƙashiya,

Yana harararsa da ƙiyayya.

13 Ubangiji yana yi wa mugu dariya,

Domin Ubangiji ya sani ba da daɗewa ba mugun zai hallaka.

14 Mugaye sun zare takuba,

Sun tanƙware bakkunansu

Don su kashe matalauta da masu bukata,

Su karkashe mutanen kirki.

15 Amma takubansu za su sassoke su,

Za a kakkarya bakkunansu.

16 Ƙanƙanen abin da mutumin kirki yake da shi,

Ya fi dukan dukiyar mugaye amfani,

17 Gama Ubangiji zai raba mugaye da ƙarfinsu,

Amma zai kiyaye mutanen kirki.

18 Ubangiji yana kula da masu yi masa biyayya,

Ƙasar kuwa za ta zama tasu har abada.

19 Ba za su sha wahala a lokacin tsanani ba,

Za su sami yalwa a lokacin yunwa.

20 Amma mugaye za su mutu,

Magabtan Ubangiji kuwa za su shuɗe kamar furen jeji,

Za su ɓace kamar hayaƙi.

21 Mugu yakan ci bashi, yă ƙi biya,

Amma mutumin kirki mai alheri ne,

Mai bayarwa hannu sake.

22 Waɗanda Ubangiji ya sa wa albarka,

Za su zauna lafiya lau a ƙasar,

Amma waɗanda ya la’anta

Za a kore su su fita.

23 Ubangiji yakan bi da mutum lafiya

A hanyar da ya kamata yă bi,

Yakan ji daɗin halinsa,

24 In ya fāɗi, ba zai yi warwar ba,

Gama Ubangiji zai taimake shi

Yă tashi tsaye.

25 Yanzu dai na tsufa, ni ba yaro ba ne,

Amma ban taɓa ganin Ubangiji ya yar da mutumin kirki ba,

Ko kuma a ga ‘ya’yansa suna barar abinci.

26 A koyaushe yakan bayar a sake,

Yana ba da rance ga waɗansu,

‘Ya’yansa kuwa dalilin albarka ne.

27 Ka rabu da mugunta ka aikata nagarta,

Za ka kuwa zauna a ƙasar har abada,

28 Gama Ubangiji yana ƙaunar abin da yake daidai,

Ba ya rabuwa da amintattun jama’arsa,

Yana kiyaye su koyaushe,

Amma za a kori zuriyar mugaye.

29 Adalai za su yi zamansu lafiya a ƙasar,

Su gāje ta har abada.

30 Kalmomin mutumin kirki suna da hikima,

Yana faɗar abin da yake daidai.

31 Yakan riƙe dokar Allahnsa a zuciyarsa, Ba ya kauce mata, faufau.

32 Mugu yakan yi fakon mutumin kirki,

Yă yi ƙoƙari yă kashe shi,

33 Amma Ubangiji ba zai bar shi a hannun magabtansa ba,

Ko kuwa yă bari a kāshe shi

Sa’ad da ake masa shari’a.

34 Ka sa zuciyarka ga Ubangiji

Ka kiyaye dokokinsa,

Shi zai ba ka ƙarfin da za ka mallaki ƙasar,

Za ka kuwa ga an kori mugaye.

35 Na ga wani mugu, azzalumi,

Ya fi kowa tsayi,

Kamar itacen al’ul na Lebanon,

36 Amma bayan ƙanƙanen lokaci,

Da na zaga, ban gan shi ba,

Na neme shi, amma ban same shi ba.

37 Dubi mutumin kirki, ka lura da adali,

Mutumin salama yakan sami zuriya,

38 Amma za a hallaka masu zunubi ƙaƙaf,

Za a kuma shafe zuriyarsu.

39 Ubangiji yakan ceci adalai,

Ya kiyaye su a lokatan wahala.

40 Yakan taimake su, yă kuɓutar da su,

Yakan cece su daga mugaye,

Gama sukan zo wurinsa don yă kāre su.

Categories
ZAB

ZAB 38

Addu’ar Mai Shan Wuya

1 Kada ka yi fushi har ka tsauta mini, ya Ubangiji!

Kada ka hukunta ni da fushinka!

2 Ka hukunta ni, ka kuwa yi mini rauni,

Ka kuma buge ni har ƙasa.

3 Saboda fushinka ina ciwo mai tsanani,

Duk jikina ya kamu da ciwo saboda zunubina.

4 Ina nutsewa cikin ambaliyar zunubaina,

Ina jin nauyinsu, sun danne ni ƙasa.

5 Saboda wawancina, miyakuna sun ruɓe, suna wari,

6 An tanƙware ni, an ragargaza ni,

Ina ta kuka dukan yini.

7 Ina fama da zazzaɓi,

Ina rashin lafiya ƙwarai.

8 An ragargaza ni sarai, an kuwa ci nasara a kaina,

Na damu a zuciyata, ina nishi don zafi.

9 Ka san bukatata, ya Ubangiji,

Kana jin dukan nishe-nishena.

10 Zuciyata tana ɗar, ƙarfina ya ƙāre,

Idanuna sun dushe.

11 Abokaina da maƙwabtana ba su ko zuwa kusa da ni, saboda miyakuna,

Har iyalina ma sun guje mini.

12 Masu son kashe ni, sun haƙa mini tarkuna,

Masu so su cuce ni, suna barazanar lalatar da ni,

Yini sukutum suna ƙulla mini maƙarƙashiya.

13 Kamar kurma nake, ba na iya ji,

Kamar kuma bebe, ba na iya magana.

14 Ni kamar mutumin da ba ya iya amsawa nake, don ba na ji.

15 Na dogara gare ka, ya Ubangiji,

Kai za ka amsa mini, ya Ubangiji Allahna.

16 Kada ka bar magabtana su yi murna saboda wahalata.

Kada ka bar su su yi kirari a kan faɗuwata!

17 Ina gab da fāɗuwa,

Ina cikin azaba kullum.

18 Na hurta zunubaina,

Sun cika ni da taraddadi.

19 Magabtana lafiyayyu ne masu ƙarfi.

Waɗanda yake ƙina ba dalili, suna da yawa.

20 Masu rama nagarta da mugunta,

Suna gāba da ni,

Domin ina ƙoƙarin aikata abin da yake daidai.

21 Kada ka yashe ni, ya Ubangiji,

Kada ka rabu da ni, ya Allahna!

22 Sai ka taimake ni yanzu, ya Ubangiji, Mai Cetona!

Categories
ZAB

ZAB 39

Rai Mai Halin Shuɗewa

1 Na ce, “Zan yi hankali da abin da nake yi,

Don kada harshena yă sa ni zunubi,

Ba zan ce kome ba sa’ad da mugaye suke kusa.”

2 Na yi shiru, ban ce kome ba,

Ko a kan abin da suke da kyau!

Amma duk da haka wahalata sai ƙaruwa take yi,

3 Zuciyata kuwa ta cika da taraddadi,

Bisa ga yawan tunanina, haka yawan wahalata zai zama,

Dole ne in yi ta tambaya,

4 “Ya Ubangiji, kwana nawa zan yi a duniya?

Yaushe zan mutu?

Ka koya mini ranar da ajalina zai auko.

5 “Ga shi, ka gajerta yawan kwanakina!

Yawan kwanakina a wurinka kamar ba kome ba ne.

Hakika duk mutum mai rai,

Bai fi shaƙar iska ba.

6 Bai kuma fi inuwa ba!

Duk abin da yake yi banza ne,

Yakan tara dukiya, amma bai san wanda zai more ta ba!

7 “A kan me zan sa zuciya, ya Ubangiji?

A gare ka nake dogara.

8 Ka cece ni daga dukan zunubaina,

Kada ka bar wawaye su yi mini ba’a.

9 Zan yi shiru, ba zan ce kome ba,

Saboda ka sa na sha wahala haka.

10 Kada ka ƙara hukunta ni!

Na kusa mutuwa saboda bugun da kake yi mini!

11 Kakan hukunta zunuban mutum ta wurin tsautawarka,

Kamar yadda asu yake lalata abu.

Hakika mutum bai fi shaƙar iska ba!

12 “Ka ji addu’ata, ya Ubangiji,

Ka kuma kasa kunne ga roƙona,

Kada ka yi shiru sa’ad da na yi kuka gare ka!

Yadda dukan kakannina suka yi,

Ni baƙonka ne na ɗan lokaci.

13 Ka ƙyale ni ko zan sami kwanciyar rai,

Kafin in tafi, ai, tawa ta ƙāre.”

Categories
ZAB

ZAB 40

Wakar Yabo

1 Na yi ta jiran taimakon Ubangiji,

Sa’an nan ya kasa kunne gare ni, ya ji kukana.

2 Ya fisshe ni daga rami mai hatsari!

Ya aza ni a kan dutse lafiya lau.

Ya kawar mini da tsoro.

3 Ya koya mini raira sabuwar waƙa,

Waƙar yabon Allahnmu.

Da yawa idan suka ga wannan za su tsorata,

Za su kuwa dogara ga Ubangiji.

4 Mai farin ciki ne mutumin da yake dogara ga Ubangiji,

Wanda bai juya ga gumaka ba,

Ko ya haɗa kai da masu sujada ga allolin karya.

5 Ka yi mana abubuwa masu yawa, ya Ubangiji Allahna.

Ba wani kamarka!

Idan na yi ƙoƙari in faɗe su duka,

Sun fi ƙarfin in faɗa.

6 Ba ka bukatar baye-baye da hadayu,

Ba ka so a miƙa maka hadayun ƙonawa

Na dabbobi a bisa bagade ba,

Ko baya-baye don a kawar da zunubai.

A maimakon haka, ka ba ni kunnuwan da zan saurare ka.

7 Sai na amsa, “Ga ni, umarnanka zuwa gare ni

Suna a Littafin Shari’a.

8 Ina ƙaunar in aikata nufinka sosai, ya Allah!

Ina riƙe da koyarwarka a zuciyata.”

9 A taron dukan jama’arka, ya Ubangiji,

Na ba da albishir na cetonka.

Ka sani ba zan fasa hurta shi ba.

10 Ban riƙe labarin cetonka don kaina kaɗai ba,

Nakan yi maganar amincinka, da taimakonka a koyaushe.

Ba na yin shiru a taron dukan jama’arka,

Amma ina ta shaida madawwamiyar ƙaunarka da amincinka.

11 Ya Ubangiji, na sani ba za ka fasa yi mini jinƙai ba!

Ƙaunarka da amincinka za su kiyaye lafiyata kullum.

12 Wahalai iri iri sun kewaye ni, har ba su ƙidayuwa!

Alhakin zunubaina ya tarar da ni,

Har ba na iya gani,

Sun fi gashin kaina yawa, na karaya.

13 Ka cece ni, ya Allah,

Ya Ubangiji, ka yi hanzari ka taimake ni!

14 Ka sa masu so su kashe ni,

A ci nasara a kansu, su ruɗe!

Ka sa waɗanda suke murna saboda wahalaina

Su koma baya, su sha kunya!

15 Ka sa waɗanda suke mini ba’a

Su razana sabili da faɗuwarsu!

16 Ka sa dukan waɗanda suke zuwa gare ka

Su yi murna, su yi farin ciki!

Ka sa waɗanda suke ƙaunar cetonka

Kullayaumi su ce, “Allah da girma yake!”

17 Ba ni da ƙarfi, ba mataimaki,

Ya Allah, ka zo wurina da hanzari.

Kai ne mataimakina da Mai Cetona,

Kada ka yi jinkiri, ya Ubangiji!