Categories
ZAK

ZAK 1

Ubangiji Ya Kira Mutanensa Su Komo gare Shi

1 A watan takwas a shekara ta biyu ta sarautar Dariyus, Ubangiji ya yi magana da annabi Zakariya, ɗan Berekiya, ɗan Iddo, ya ce,

2 “Ubangiji ya yi fushi da kakanninku.

3 Domin haka sai ka ce musu, Ubangiji Mai Runduna ya ce, ‘Ku komo wurina, ni kuma zan komo wurinku, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.’

4 Kada ku zama kamar kakanninku, waɗanda annabawa na dā suka yi ta yi musu shela suna cewa, ‘Ubangiji Mai Runduna ya ce, ku bar mugayen hanyoyinku da mugayen ayyukanku.’ Amma ba su ji ba, ba su kuwa kula ba, ni Ubangiji na faɗa.

5 To, ina kakannin nan naku suke? Annabawan fa? Suna da rai har wa yau?

6 Amma maganata da dokokina waɗanda na umarta wa bayina annabawa, sun tabbata a kan kakanninku, sai suka tuba, suka ce, ‘Kamar yadda Ubangiji Mai Runduna ya yi niyya ya yi da mu saboda hanyoyinmu da ayyukanmu, haka kuwa ya yi da mu.’ ”

Wahayin Dawakai da Zakariya Ya Gani

7 A rana ta ashirin da huɗu ga watan goma sha ɗaya, wato watan Shebat, a shekara ta biyu ta sarautar Dariyus, Ubangiji ya kuma yi magana da annabi Zakariya, ɗan Berekiya, ɗan Iddo.

8 Da dare, na ga mutum yana kan aharashin doki, yana tsaye a cikin itatuwan ci-zaƙi, a kwari. A bayansa kuma ga wani aharashin doki, da bidi, da kili.

9 Sai na ce, “Mene ne waɗannan, ya Ubangiji?”

Mala’ikan da ya yi magana da ni ya ce, “Zan bayyana maka ma’anarsu.”

10 Sai mutumin da yake tsaye a cikin itatuwan ci-zaƙin ya amsa ya ce, “Waɗannan su ne Ubangiji ya aike su su yi tsaron duniya, suna kai da kawowa.”

11 Sai suka ce wa mala’ikan Ubangiji wanda yake tsaye a cikin itatuwan ci-zaƙin, “Mun yi ta kai da kawowa a duniya, sai muka ga duniya duka tana zaman lafiya.”

12 Sa’an nan mala’ikan Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Mai Runduna, har yaushe za ka ƙi nuna jinƙai ga Urushalima da biranen Yahuza, waɗanda kake jin haushinsu shekara saba’in ke nan?”

13 Sai Ubangiji ya amsa wa mala’ikan da yake magana da ni da magana ta alheri da ta ta’azantarwa.

14 Mala’ikan kuma da yake magana da ni ya ce, in yi shela in ce, “Ubangiji Mai Runduna ya ce yana jin ƙishin Urushalima da Sihiyona ƙwarai.

15 Yana fushi ƙwarai da al’umman duniya da take zaman lafiya, gama ya yi ɗan fushi da mutanena, amma su suka yi musu hukuncin da ya zarce.

16 Saboda haka shi Ubangiji zai koma ya ji juyayin Urushalima. Za a gina Haikalinsa a cikinta, zai kuma auna Urushalima da ma’auni.”

17 Ya ce, in kuma yi shela, in ce, “Ubangiji Mai Runduna ya ce wadata za ta sake bunƙasa cikin biranensa, zai kuma ta’azantar da Sihiyona, ya kuma zaɓi Urushalima.”

Wahayin Ƙahoni da Maƙera da Zakariya Ya Gani

18 Da na ɗaga idona, sai na ga ƙahoni huɗu.

19 Sai na ce wa mala’ikan da ya yi magana da ni, “Mene ne waɗannan?”

Shi kuwa ya ce mini, “Waɗannan su ne ƙahonin da suka warwatsa Yahuza, da Isra’ila, da Urushalima.”

20 Sa’an nan kuma Ubangiji ya nuna mini waɗansu maƙera, su huɗu.

21 Sai na ce, “Me waɗannan suke zuwa su yi?”

Sai ya ce, “Waɗannan su ne ƙahonin da suka warwatsa Yahuza don kada mutum ya ɗaga kansa. Waɗannan kuwa sun zo don su tsorata su, su karya ƙahonin al’umman duniya waɗanda suka ɗaga ƙahoninsu gāba da ƙasar Yahuza don su warwatsa ta.”

Categories
ZAK

ZAK 2

Wahayin Mutum da Igiyar Awo da Zakariya Ya Gani

1 Da na ɗaga idona, sai ga wani mutum yana riƙe da igiyar awo.

2 Sai na ce, “Ina za ka?”

Ya ce mini, “Zan tafi in auna Urushalima don in san fāɗinta da tsawonta.”

3 Sai ga mala’ikan da yake magana da ni, ya fita, sai wani mala’ika kuma ya zo ya sadu da shi.

4 Ya ce masa, “Ka yi gudu, ka faɗa wa saurayin can, cewa za a zauna a Urushalima kamar a ƙauyuka marasa garu, saboda yawan mutane da dabbobi da suke cikinta.

5 Gama zan zama mata garu na wuta kewaye da ita, zan zama daraja a tsakiyarta, in ji Ubangiji.”

An Kirawo ‘Yan Bautar Talala

6 Ubangiji ya ce, “Yanzu ku gudu daga ƙasar arewa, gama na warwatsa ku a waje kamar iska ta kusurwoyi huɗu na duniya!

7 Ya ke Sihiyona, ku tsere, ku waɗanda kuke zaune a Babila.”

8 Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Bayan ɗaukaka ya aike ni zuwa wurin al’umman duniyan nan da suka washe ku, gama wanda ya taɓe ku, ya taɓi ƙwayar idona.

9 Ga shi, zan nuna ikona a kansu, za su kuwa zama abin waso ga waɗanda suka bauta musu. Sa’an nan za ku sani Ubangiji Mai Runduna ya aike ni.

10 “Ki raira waƙa, ki yi farin ciki, ya Sihiyona, gama ina zuwa, in zauna a tsakiyarki! Ni Ubangiji na faɗa.

11 “A wannan rana al’umman duniya da yawa za su haɗa kai da Ubangiji, za su kuwa zama jama’ata, ni kuma zan zauna a tsakiyarki. Za ki sani Ubangiji Mai Runduna ya aike ni gare ki.

12 Yahuza za ta zama abin mallakar Ubangiji a cikin tsattsarkar ƙasar. Zai kuma zaɓi Urushalima.”

13 Bari dukan ‘yan adam su yi tsit a gaban Ubangiji, gama ya taso daga wurin zamansa mai tsarki.

Categories
ZAK

ZAK 3

Wahayin Yoshuwa Babban Firist da Zakariya Ya Gani

1 Ubangiji ya nuna mini Yoshuwa, babban firist, yana tsaye a gaban mala’ikan Ubangiji. Shaiɗan kuma yana tsaye dama da mala’ikan, yana saran Yoshuwa.

2 Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Ubangiji ya tsauta maka, kai Shaiɗan! Ubangiji wanda ya zaɓi Urushalima ya tsauta maka. Ai, wannan mutum kamar itace ne wanda aka fizge daga cikin wuta.”

3 Yoshuwa dai yana tsaye a gaban mala’ikan saye da riguna masu dauɗa.

4 Mala’ikan kuwa ya ce wa waɗanda suke tsaye a gabansa, “Ku tuɓe masa rigunan nan masu dauɗa.” Sa’an nan ya ce wa Yoshuwa, “Ga shi, na kawar maka da laifinka, zan sa maka riguna masu daraja.”

5 Sai ni kuma na ce, “Bari kuma su naɗa masa rawani mai tsabta.” Suka kuwa naɗa masa rawani mai tsabta, suka kuma sa masa riguna sa’ad da mala’ikan Ubangiji yana nan a tsaye.

6 Sa’an nan mala’ikan Ubangiji ya gargaɗi Yoshuwa, ya ce,

7 “Ubangiji Mai Runduna ya ce, ‘Idan ka yi tafiya a hanyata, ka kuma kiyaye umarnina, zan sa ka zama shugaban Haikalina, ka lura da shirayina, zan kuma sa ka sami damar zuwa wurin waɗannan da yake tsaye.

8 Ka ji, ya Yoshuwa, babban firist, kai da abokanka da suke zaune gabanka, ku alama ce mai kyau. Ga shi, zan kawo bawana mai suna Reshe.

9 Ni Ubangiji Mai Runduna na ce, a kan dutsen da na kafa a gaban Yoshuwa, dutse mai ido bakwai zan yi rubutu, zan kawar da laifin al’umman nan rana ɗaya.

10 A wannan rana kowane ɗayanku zai gayyaci maƙwabcinsa zuwa gindin kurangar inabinsa da itacen ɓaurensa.’ ”

Categories
ZAK

ZAK 4

Wahayin Alkuki da Itatuwan Zaitun da Zakariya Ya Gani

1 Mala’ikan da yake Magana da ni ya komo ya farkar da ni kamar yadda akan farkar da mutum daga barci.

2 Sa’an nan ya ce mini, “Me ka gani?”

Sai na ce, “Na ga alkuki wanda aka yi da zinariya tsantsa, da kwano a kansa, da fitilu bakwai a kansa, da butoci bakwai a kan kowace fitilar da yake bisa alkukin.

3 Akwai itatuwan zaitun biyu kusa da alkukin, ɗaya a wajen dama da kwano, ɗaya kuma a wajen hagun.”

4 Sai ni kuma na ce wa mala’ikan da yake magana da ni, “Mene ne waɗannan, ya ubangijina?”

5 Sa’an nan mala’ikan da yake magana da ni ya ce, “Ba ka san abubuwan nan ba?”

Na ce, “A’a, ubangijina.”

6 Sa’an nan ya ce, “Wannan ita ce maganar Ubangiji zuwa ga Zarubabel cewa, ‘Ba da ƙarfi, ko iko ba, amma da Ruhuna,’ in ji Ubangiji Mai Runduna.

7 ‘Mene ne kai, ya babban dutse? Za ka zama fili a gaban Zarubabel, zai kuwa kwaso duwatsun da suke ƙwanƙoli da sowa, yana cewa alheri, alheri ne ya kawo haka.’ ”

8 Ubangiji kuma ya yi magana da ni ya ce,

9 “Zarubabel ne ya ɗora harsashin ginin Haikalin nan da hannunsa, shi ne kuma zai gama ginin da hannunsa. Sa’an nan za ka sani Ubangiji Mai Runduna ya aike ni zuwa gare ka.

10 Gama wane ne ya taɓa raina ranar ƙananan abubuwa? Amma za su yi murna da ganin igiyar awo a hannun Zarubabel. Waɗannan fitilu bakwai su ne alama Ubangiji yana kai da kawowa a duniya.”

11 Na ce masa, “Mece ce ma’anar waɗannan itatuwan zaitun da suke wajen dama da hagun alkukin?”

12 Na kuma sāke tambayarsa na ce, “Mece ce ma’anar waɗannan rassan itatuwan zaitun, waɗanda suke kusa da bututu biyu na zinariya, inda mai yake fitowa?”

13 Sai ya ce mini, “Ba ka san ma’anar waɗannan ba?”

Na ce, “A’a, ubangijina.”

14 Sa’an nan ya ce, “Waɗannan su ne keɓaɓɓu biyu waɗanda yake tsaye kusa da Ubangijin dukan duniya.”

Categories
ZAK

ZAK 5

Wahayin Littafi na Tashi Sama

1 Da na ɗaga idona sama kuma, sai na ga littafi mai tashi a sama.

2 Sai mala’ikan ya tambaye ni ya ce, “Me ka gani?”

Na amsa, “Na ga littafi mai tashi a sama, tsawonsa kamu ashirin ne, fāɗinsa kuma kamu goma.”

3 Sa’an nan ya ce mini, “Wannan la’ana ce wadda take tashi bisa ƙasa duka. Gama za ta datse ɓarawo da mai rantsuwa da ƙarya.

4 Ubangiji Mai Runduna ya ce, ‘Zan aika da littafin a gidan ɓarawo da gidan mai rantsuwa da sunana a kan ƙarya. Littafin zai zauna a gidansa, ya ƙone gidan, da katakan, da duwatsun.’ ”

Wahayin Mace a cikin Kwando

5 Sa’an nan mala’ikan da yake magana da ni ya matso, ya ce mini, “Ka ɗaga idonka, ka ga abin nan da yake fitowa.”

6 Ni kuwa na ce masa, “Mene ne wannan?”

Ya ce, “Wannan babban kwando ne wanda ya fita.” Ya kuma ce, “Wannan mugunta ce a dukan ƙasar.”

7 Da aka ɗaga murfin kwando na darma, sai ga mace tana zaune a cikin kwandon!

8 Sai ya ce, “Wannan mugunta ce.” Sa’an nan ya tura ta cikin kwandon, ya rufe bakin kwandon da murfi na darma mai nauyi.

9 Da na ɗaga idona, sai na ga mata biyu suna matsowa. Iska tana hura fikafikansu, gama suna da fikafikai kamar na shamuwa. Suka ɗaga kwandon sama.

10 Sai na tambayi mala’ikan da yake magana da ni, na ce, “Ina za su kai kwandon?”

11 Ya ce mini, “Za su tafi da shi ƙasar Shinar don su gina masa haikali, sa’ad da suka gama ginin, za su ajiye shi a ciki.”

Categories
ZAK

ZAK 6

Wahayin Karusai Huɗu

1 Na kuma ɗaga idona, sai na ga karusa huɗu suna fitowa daga tsakanin duwatsu biyu. Duwatsun kuwa na tagulla ne.

2 Dawakai aharasai ne suke jan karusa ta fari, ta biyu kuwa akawalai ne suke janta.

3 Na uku kuma dawakai kiliyai ne suke janta, ta huɗu kuwa hurdu ne yake janta.

4 Sa’an nan na ce wa mala’ikan da yake magana da ni, “Mene ne waɗannan, ya ubangijina?”

5 Ya ce mini, “Waɗannan su ne ruhohi huɗu waɗanda suka fito daga sama bayan da sun nuna kansu a gaban Ubangijin duniya duka.

6 Karusar da akawalai suke ja, za ta tafi ƙasar arewa, wadda kuma dawakai kiliyai suke ja, za ta bi su. Wadda kuwa hurde suke ja, za ta tafi ƙasar kudu.”

7 Sa’ad da ingarmun suka fita, sai suka ƙagauta su zagaya duniya don su bincike ta. Ya ce musu kuwa, “Ku tafi, ku bincike duniya, kuna kai da kawowa.” Har kuwa suka yi.

8 Ya kuma kira ni, ya ce, “Duba, waɗanda suka tafi ƙasar arewa sun sa fushin Ubangiji ya huce.”

Kwatancin Naɗawar Yoshuwa

9 Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,

10 “Ka karɓi sadaka daga Heldai, da Tobiya, da Yedaiya waɗanda suka komo daga bautar talala a Babila. A ranar kuma ka tafi gidan Yosiya ɗan Zafaniya.

11 Ka karɓi azurfa da zinariya a wurinsu, ka ƙera kambi, ka sa shi a kan Yoshuwa, ɗan Yehozadak, babban firist.

12 Ka kuwa ce masa, ‘Ubangiji Mai Runduna ya ce, mutumin da sunansa Reshe, zai yi girma a inda yake, zai kuma gina Haikalin Ubangiji.

13 Shi ne zai gina Haikalin Ubangiji, ya kuma sami girma, ya yi mulki kamar sarki, ya kuma zama firist. Kome kuwa zai tafi daidai.’

14 Kambin zai kasance a Haikalin Ubangiji don tunawa da Heldai, da Tobiya, da Yedaiya, da Yosiya ɗan Zafaniya.

15 “Waɗanda yake nesa za su zo su gina Haikalin Ubangiji. Za ku kuwa sani Ubangiji Mai Runduna ya aiko ni wurinku. Wannan zai faru idan kun yi biyayya sosai da muryar Ubangiji Allahnku.”

Categories
ZAK

ZAK 7

An La’anci Azumi na Rashin Gaskiya

1 A rana ta huɗu ga watan tara, wato watan Kisle, a shekara ta huɗu ta sarautar sarki Dariyus, Ubangiji ya yi magana da Zakariya.

2 Sai mutanen Betel suka aiki Sharezer da Regem-melek da mutanensu su nemi tagomashi a wurin Ubangiji,

3 su kuma tambayi firistocin Haikalin Ubangiji da annabawa, cewa ko ya kamata su yi baƙin ciki da azumi a watan biyar kamar yadda suka saba yi a shekarun baya?

4 Sa’an nan Ubangiji Mai Runduna ya yi mini magana, ya ce,

5 in faɗa wa dukan mutanen ƙasar da firistoci, in ce, “Sa’ad da kuka yi azumi da baƙin ciki a watan biyar da na bakwai dukan shekarun nan saba’in, saboda ni ne kuka yi azumin?

6 Sa’ad da kuma kuke ci, kuna sha, ba don kanku ne kuke ci, kuke sha ba?”

7 Maganar ke nan da Ubangiji ya faɗa ta bakin annabawan dā, a lokacin akwai mutane da arziki cikin Urushalima da garuruwa kewaye da ita, a lokacin kuma akwai mutane a Negeb da gindin tuddai.

Rashin Biyayya ne ya Jawo Bautar Talala

8 Ubangiji kuma ya yi magana da Zakariya, ya ce,

9 “Ni Ubangiji Mai Runduna, na ce ku yi shari’ar gaskiya, bari kowa ya nuna alheri da jinƙai ga ɗan’uwansa.

10 Kada kuma ku zalunci gwauruwa, wato wadda mijinta ya rasu, da maraya, da baƙo, da matalauci, kada kuma waninku ya shirya wa ɗan’uwansa mugunta a zuciyarsa.

11 “Amma suka ƙi ji, suka ba da baya, suka toshe kunnuwansu don kada su ji.

12 Suka taurare zuciyarsu kamar dutse don kada su ji dokoki da maganar da ni Ubangiji Mai Runduna na aiko ta wurin Ruhuna zuwa ga annabawa na dā. Domin haka ni Ubangiji Mai Runduna na aukar musu da hasala mai zafi.

13 Kamar yadda na yi kira suka ƙi ji, haka kuma suka yi kira, ni ma na ƙi ji.

14 Na sa guguwa ta warwatsa su a cikin al’ummai da ba su san su ba. Ƙasar da suka bari ta zama kango, ba mai kai da kawowa a cikinta. Ƙasa mai kyau ta zama kango.”

Categories
ZAK

ZAK 8

Ubangiji zai Sāke Rayar da Urushalima

1 Ubangiji Mai Runduna kuma ya yi magana da ni, ya ce,

2 “Ni Ubangiji Mai Runduna ina kishin Sihiyona ƙwarai.

3 Zan koma wurin Sihiyona, in zauna a tsakiyar Urushalima. Za a ce da Urushalima birnin gaskiya, da kuma dutsen Ubangiji Mai Runduna, tsattsarkan dutse.

4 Tsofaffi, mata, da maza, za su zauna a titunan Urushalima, kowa yana tokare da sanda saboda tsufa.

5 Samari da ‘yan mata zan sa su cika titunan Urushalima, suna wasa.

6 “Idan abin nan ya zama mawuyaci ga sauran jama’a a kwanakin nan, zai zama mawuyacin abu ne a gare ni?

7 Ni Ubangiji Mai Runduna na ce, zan ceci mutanena daga ƙasar gabas da ƙasar yamma.

8 Zan kawo su su zauna a Urushalima. Za su zama jama’ata, ni kuma zan zama Allahnsu da gaskiya da adalci.

9 “Ni Ubangiji Mai Runduna na ce, ku himmantu, ku da kuke jin magana ta bakin annabawa a waɗannan kwanaki tun lokacin da aka ɗora harsashin ginin Haikalin Ubangiji Mai Runduna, don a gina Haikalin.

10 Gama kafin waɗannan kwanaki, mutum da dabba ba su da abin yi. Ba kuma zaman lafiya ga mai fita da shiga saboda maƙiya, gama na sa kowane mutum ya ƙi ɗan’uwansa.

11 Amma yanzu ba zan yi da sauran jama’an nan kamar yadda na yi a kwanakin dā ba, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.

12 Gama za a yi shuka da salama. Kurangar inabi za ta yi ‘ya’ya, ƙasa kuma za ta ba da amfani, za a yi isasshen ruwan sama. Ni kuwa zan sa sauran jama’an nan su ci moriyar abubuwan nan duka.

13 Ya jama’ar Yahuza da jama’ar Isra’ila, kamar yadda kuka zama abin la’antarwa a cikin al’ummai, haka kuma zan cece ku, ku zama masu albarka, kada ku ji tsoro, amma ku himmantu.

14 “Ni Ubangiji Mai Runduna, na ce, kamar yadda na ƙudura in aukar muku da masifa, ban kuwa fasa ba, lokacin da kakanninku suka tsokane ni, suka sa na yi fushi.

15 Haka kuma na ƙudura a waɗannan kwanaki in yi wa Urushalima da jama’ar Yahuza alheri. Kada ku ji tsoro!

16 Abubuwan da za ku yi ke nan, ku faɗa wa juna gaskiya, ku yi shari’a ta gaskiya a majalisunku, domin zaman lafiya.

17 Kada ku ƙulla wa junanku sharri, kada kuma ku so yin rantsuwa ta ƙarya, gama ina ƙin waɗannan abubuwa duka, ni Ubangiji na faɗa.”

18 Ubangiji Mai Runduna ya yi magana da ni, ya ce,

19 “Ni Ubangiji Mai Runduna na ce, azumi na watan huɗu, da na watan biyar, da na watan bakwai, da na watan goma, za su zama lokatan murna, da farin ciki, da idodin farin ciki, ga jama’ar Yahuza, saboda haka sai ku ƙaunaci gaskiya da salama.

20 “Mutanen birane da yawa za su hallara.

21 Mutanen wani birni za su tafi wurin mutanen wani birni, su ce musu, ‘Za mu tafi mu roƙi alherin Ubangiji, mu kuma nemi Ubangiji Mai Runduna. Ku zo mu tafi.’

22 Jama’a da yawa da al’ummai masu iko za su zo Urushalima su nemi Ubangiji Mai Runduna, su kuma roƙi alherin Ubangiji.

23 Ni Ubangiji Mai Runduna na ce, a waɗannan kwanaki mutum goma daga kowace al’umma da kowane harshe za su kama kafa wurin Bayahude, su ce, ‘Ka yardar mana mu tafi tare da kai, gama mun ji Allah yana tare da ku.’ ”

Categories
ZAK

ZAK 9

Hukuncin da Za a Yi wa Al’umman da Suke Kewaye

1 Ubangiji ya yi magana gāba da ƙasar Hadrak, da kuma gāba da Dimashƙu. Ubangiji ne yake lura da ‘yan adam duk da kabilan Isra’ila.

2 Ubangiji kuma yana gāba da Hamat wadda yake kan iyaka, yana kuma gāba da Taya da Sidon ko da yake suna da hikima ƙwarai.

3 Taya ta gina wa kanta kagara,

Ta kuma tara azurfa kamar ƙura,

Zinariya kuma kamar sharar titi.

4 Amma Ubangiji zai washe ta,

Ya zubar da dukiyarta a cikin teku,

Wuta kuma za ta cinye ta.

5 Ubangiji ya ce,

“Ashkelon za ta gani ta ji tsoro,

Gaza kuma za ta yi makyarkyata da azaba,

Haka kuma Ekron za ta fid da zuciya,

Sarki zai halaka cikin Gaza,

Ashkelon za ta zama kufai.

6 Tattarmuka za su zauna a Ashdod,

Zan kuma sa alfarmar Filistiya ta ƙare.

7 Zan kawar da jininsu daga bakinsu,

Da kuma haramtattun abubuwa daga haƙoransu.

Sauransu za su zama jama’ar Allahnmu,

Za su zama kamar sarki cikin Yahuza.

Mutanen Ekron za su zama kamar Yebusiyawa.

8 Zan kafa sansani kewaye da Haikalina saboda maƙiya,

Don masu kai da kawowa.

Ba wani azzalumi da zai ci su da yaƙi,

Gama yanzu ni kaina na gani.”

Sarki Mai Zuwa

9 Ki yi murna ƙwarai, ya Sihiyona!

Ta da murya ya Urushalima!

Ga Sarkinki yana zuwa wurinki,

Shi mai adalci ne, mai nasara,

Shi kuma mai tawali’u ne,

Yana bisa kan jaki, a kan aholaki.

10 Ubangiji ya ce,

“Zan datse karusa daga Ifraimu,

In datse ingarman yaƙi a Urushalima,

Zan kuma karya bakan yaƙi.

Sarkinki zai tabbatar wa al’umman duniya da salama,

Mulkinsa zai zama daga teku zuwa teku,

Daga Kogin Yufiretis zuwa matuƙar duniya.”

Za a Rayar da Sihiyona

11 Ubangiji ya ce,

“Ke kuma, saboda jinin alkawarina da yake tsakanina da ke,

Zan ‘yantar da waɗanda suke cikin rami,

Waɗanda aka kama daga cikinki.

12 Ku koma mafakarku, ku ɗaurarru masu sa zuciya.

Gama yanzu zan sāka muku har ninki biyu.

13 Gama na tankwasa Yahuza ta zama bakana,

Na kuma mai da Ifraimu ta zama kibiya,

Zan yi amfani da mutanen Sihiyona kamar takobi,

Su yi yaƙi da mutanen Hellas.”

14 Ubangiji kuwa zai bayyana kansa gare su,

Kibiyarsa za ta fita kamar walƙiya,

Ubangiji Allah zai busa ƙaho,

Zai taho ta cikin guguwa daga kudu.

15 Ubangiji Mai Runduna zai tsare su,

Za su tattake duwatsun majajjawa,

Za su sha jini kamar ruwan inabi,

Za su cika kamar tasar ruwan inabi,

Kamar kuma kusurwoyin bagade.

16 A wannan rana Ubangiji Allahnsu zai cece su,

Gama su jama’arsa ne, garkensa kuma,

Kamar yadda lu’ulu’u yake haske a kambi,

Haka za su yi haske a ƙasarsa.

17 Wane irin kyau da bansha’awa alherinsa yake!

Hatsi zai sa samari su yi murna.

Sabon ruwan inabi kuma zai sa ‘yan mata su yi farin ciki.

Categories
ZAK

ZAK 10

Alkawarin Mai Ceto

1 Ku roƙi ruwan sama daga wurin Ubangiji a lokacin bazara,

Gama Ubangiji ne yake yin gizagizan hadiri,

Shi ne yake bai wa mutane yayyafi.

Shi ne kuma yake ba kowane mutum tsire-tsiren saura.

2 Gama maganar shirme kan gida yake yi,

Masu dūba suna ganin wahayin ƙarya,

Masu mafarkai suna faɗar ƙarya,

Ta’aziyyarsu ta banza ce.

Domin haka mutane suna ta yawo kamar tumaki,

Suna shan wahala saboda rashin makiyayi.

3 Ubangiji ya ce,

“Ina fushi ƙwarai da makiyayan,

Zan kuwa hukunta shugabannin,

Gama ni Ubangiji Mai Runduna zan lura da garkena,

Wato jama’ar Yahuza.

Zan mai da su dawakaina na yaƙi.

4 Daga cikinsu za a sami mafificin dutsen gini,

Daga cikinsu kuma za a sami turken alfarwa,

Daga cikinsu za a sami bakan yaƙi,

Daga cikinsu kuma kowane mai mulki zai fito.

5 Za su zama kamar ƙarfafan mutane cikin yaƙi,

Za su tattaka maƙiyi a cikin taɓon tituna.

Za su yi yaƙi, gama Ubangiji yana tare da su,

Za su kunyatar da sojojin doki.

6 “Zan sa jama’ar Yahuza ta yi ƙarfi,

Zan ceci jama’ar Yusufu.

Zan dawo da su domin ina jin tausayinsu.

Za su zama kamar waɗanda ban taɓa ƙyale su ba,

Gama ni Ubangiji Allahnsu ne,

Zan amsa musu.

7 Sa’an nan mutanen Ifraimu za su zama kamar ƙarfafan jarumawa,

Za su yi farin ciki kamar sun sha ruwan inabi,

‘Ya’yansu za su gani su yi murna,

Zukatansu za su yi murna da Ubangiji.

8 “Zan yafato su in tattaro su,

Gama zan fanshe su,

Zan sa su su yi yawa kamar yadda suke yi a dā.

9 Ko da yake na watsar da su cikin al’ummai,

Duk da haka za su riƙa tunawa da ni daga ƙasashe masu nisa.

Su da ‘ya’yansu za su rayu, su komo.

10 Zan dawo da su gida daga ƙasar Masar,

In tattaro su daga Assuriya,

Zan kawo su a ƙasar Gileyad da ta Lebanon,

Har su cika, ba sauran wuri.

11 Za su bi ta cikin tekun wahala,

Zan kwantar da raƙuman teku,

Kogin Nilu zai ƙafe duk da zurfinsa,

Za a ƙasƙantar da Assuriya,

Sandan sarautar Masar zai rabu da ita.

12 Zan ƙarfafa su,

Za su yi tafiya da sunansa,

Ni Ubangiji na faɗa.”