Categories
ZAK

ZAK 11

1 Ki buɗe ƙofofinki, ke Lebanon,

Don wuta ta cinye itatuwan al’ul naki.

2 Ka yi kuka, kai itacen kasharina,

Gama itacen al’ul ya riga ya fāɗi,

Itatuwa masu daraja sun lalace,

Ku yi kuka, ku itatuwan oak na Bashan,

Saboda an sassare itatuwan babban kurmi.

3 Ku ji kukan makiyaya,

Gama an ɓata musu darajarsu.

Ji rurin zakoki,

Gama an lalatar da jejin Urdun.

Makiyaya Marasa Amfani

4 Ga abin da Ubangiji Allah ya faɗa, “Ka zama makiyayin garken tumakin da za a yanka.

5 Masu sayensu za su yanyanka su, ba za a kuwa hukunta su ba. Masu sayar da su kuma za su yi hamdala gare ni, su ce sun sami dukiya. Makiyayansu kuwa ba su ji tausayinsu ba.

6 “Gama ba zan ƙara jin tausayin mazaunan ƙasan nan ba, ni Ubangiji na faɗa. Ga shi, zan sa su fāɗa a hannun junansu da a hannun sarkinsu. Za su lalatar da ƙasar, ba kuwa zan cece su daga hannunsu ba.”

7 Sai na zama makiyayi na masu tumakin kore. Na kuwa ɗauko sanda biyu, na ce da ɗaya “Alheri,” ɗaya kuma na ce da shi “Haɗa Kai.” Sai na yi kiwon tumakin.

8 A wata guda na hallaka makiyayan nan uku, gama ban jure da su ba, su ma sun gaji da ni.

9 Sai na ce wa tumakin, ba zan yi kiwonsu ba, “Waɗanda za su mutu sai su mutu, waɗanda kuma za su hallaka, to, sai su hallaka. Sauran da suka ragu kuma, su yi ta cin naman junansu!”

10 Sa’an nan na ɗauki sandana, wato “Alheri,” na karya shi, alama ke nan da ta nuna na keta alkawarin da na yi wa al’ummai duka.

11 Da haka aka karya alkawarina a wannan rana. Masu tumakin kore suna tsaye suna kallon abin da na yi, sai suka gane lalle wannan maganar Ubangiji ce.

12 Sai na ce musu, “Idan kun ga daidai ne sai ku biya ni hakkina, idan kuwa ba haka ba ne, to, ku riƙe abinku!” Sai suka biya ni tsabar azurfa talatin, ladana.

13 Ubangiji kuma ya ce mini, “Ka zuba kuɗin a baitulmalin Haikali.” Sai na ɗauki kuɗin da suka kimanta shi ne tamanina, na zuba su a baitulmalin Haikalin Ubangiji.

14 Sa’an nan kuma na karya sandana na biyun mai suna “Haɗa Kai,” wato alama ke nan da ta nuna na kawar da ‘yan’uwancin da yake tsakanin Yahuza da Isra’ila.

15 Ubangiji kuwa ya ce mini, “Ka sāke ɗaukar kayan aiki na makiyayi marar amfani.

16 Gama ga shi, zan sa wani makiyayi a ƙasan nan, wanda ba zai kula da masu lalacewa ba, ko waɗanda suka warwatse, ko ya warkar da gurgu, ko ya ciyar da waɗanda suka ragu, amma zai ci naman masu ƙiba, ya farfashe kofatonsu.

17 Taka ta ƙare, kai makiyayi marar amfani,

Wanda yakan bar tumakin!

Da ma takobi ya sari dantsensa da idonsa na dama!

Da ma hannunsa ya shanye sarai,

Idonsa na dama kuma ya makance!”

Categories
ZAK

ZAK 12

Za a Ceci Urushalima nan Gaba

1 Ga maganar Ubangiji game da Isra’ila. Ubangiji wanda ya shimfiɗa sammai, ya kirkiro duniya, ya kuma sa rai a cikin mutum, ya ce,

2 “Ga shi, ina gab da sa Urushalima ta zama ƙoƙon sa tangaɗi ga dukan al’ummai da yake kewaye. Yaƙin da zai kewaye Urushalima zai shafi Yahuza ita ma.

3 A ran nan zan sa Urushalima ta zama dutse mai nauyi ga dukan al’ummai. Duk wanda ya ɗaga ta zai ji wa kansa mugun rauni. Dukan al’umman duniya za su taru su kewaye ta.

4 A wannan rana zan firgita kowane doki, in sa mahayinsa ya haukace. Zan lura da mutanen Yahuza, amma zan makantar da dawakan abokan gābansu.

5 Sa’an nan iyalan Yahuza za su ce wa kansu, ‘Ubangiji Allah Maɗaukaki yana ƙarfafa mutanensa waɗanda suke zaune a Urushalima.’

6 “A ranan nan zan sa iyalan Yahuza su zama kamar wuta a kurmi, ko kuwa a gonar da hatsi ya nuna. Za su halaka dukan al’umman da suke kewaye da su. Amma mutanen Urushalima za su yi zamansu lami lafiya.

7 “Ubangiji zai fara ba mutanen Yahuza nasara, domin kada darajar jama’ar Dawuda da ta mazaunan Urushalima ta fi ta mutanen Yahuza.

8 A ranar, Ubangiji zai kiyaye mazaunan Urushalima, har wanda yake marar ƙarfi a cikinsu zai zama mai ƙarfi kamar Dawuda. Jama’ar Dawuda za ta zama kamar Allah, kamar mala’ikan Ubangiji a gabansu.

9 A ranar kuma zan hallaka dukan al’umman da suka zo su yi yaƙi da Urushalima.

10 “Zan cika zuriyar Dawuda da mutanen Urushalima da ruhun tausayi da na addu’a. Za su dubi wanda suka soke shi, har ya mutu. Za su yi makoki dominsa kamar waɗanda aka yi musu rasuwar ɗan farinsu.

11 A ran nan za a yi babban makoki a Urushalima kamar mutane suka yi wa Hadadrimmon a filin Magiddo.

12 Kowane iyali a ƙasar za su yi makokinsu a keɓe, iyalin gidan Dawuda kuma za su yi nasu a keɓe, matansu za su yi nasu a keɓe. Iyalin gidan Natan su ma za su yi nasu makoki a keɓe, matansu kuma a keɓe.

13 Iyalin gidan Lawi za su yi makokinsu a keɓe, matansu kuma a keɓe. Iyalin gidan mutanen Shimai za su yi makokinsu a keɓe, matansu kuma a keɓe.

14 Sauran dukan iyalan da suka ragu za su yi nasu makoki a keɓe, matansu kuma a keɓe.”

Categories
ZAK

ZAK 13

1 “A ran nan za a buɗe maɓuɓɓuga don wanke zuriyar Dawuda da mazaunan Urushalima daga zunubi da rashin tsarki.

2 A wannan rana fa, ni Ubangiji Mai Runduna, zan shafe sunayen gumaka daga ƙasar, har da ba za a ƙara tunawa da su ba. Zan kuma kawar da annabawa da mugayen aljannu.

3 Idan har yanzu wani ya ci gaba da yin annabci, sai mahaifinsa da mahaifiyarsa su ce masa, ‘Ba za ka rayu ba, gama kana faɗar ƙarya da sunan Ubangiji.’ Sa’an nan mahaifinsa da mahaifiyarsa su soke shi sa’ad da yake annabcin.

4 A wannan rana ce kowane annabi zai ji kunyar wahayinsa sa’ad da ya yi annabcin. Ba zai sa rigar gashi don ya ruɗi jama’a ba.

5 Amma zai ce, ‘Ni ba annabi ba ne, ni manomi ne, gama ƙasa abar mallakata ce tun ina yaro.’

6 Idan wani ya tambaye shi cewa, ‘Waɗannan raunukan da suke a hannuwanka fa?’ Zai ce, ‘Ai, raunuka ne da aka yi mini a gidan abokaina.’ ”

Za a Kashe Makiyayi na Ubangiji

7 “Ka farka, ya kai takobi, ka fāɗa wa makiyayina,

Ka fāɗa wa mutumin da yake kusa da ni,

Ka sari makiyayin domin tumakin su watse.

Zan bugi ƙanana da hannuna,

Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.

8 Ni Ubangiji na ce sulusi biyu na ƙasar za su hallaka,

Sulusi ɗaya ne kawai zai ragu.

9 Sulusi ɗayan da ya ragu kuwa zan tura cikin wuta,

Zan tace su da wuta kamar yadda akan tace azurfa,

Zan gwada su kamar yadda akan gwada zinariya.

Za su kira gare ni,

Zan kuwa amsa musu,

Zan ce, ‘Su jama’ata ne,’

Su kuma za su ce, ‘Ubangiji shi ne Allahnmu.’ ”

Categories
ZAK

ZAK 14

Urushalima da Sauran Al’umma

1 Ga ranar Ubangiji tana zuwa sa’ad da za a raba ganimar da aka ƙwace daga gare ku a kan idonku.

2 Gama zan tattara dukan al’ummai su yi yaƙi da Urushalima. Za a ci birnin, a washe gidajen. Za a yi wa mata faɗe. Za a kai rabin mutanen birnin bauta, amma za a bar sauran mutanen a cikin birnin.

3 Sa’an nan Ubangiji zai tafi ya yi yaƙi da waɗannan al’ummai kamar yadda ya yi a dā.

4 A wannan rana ƙafafunsa za su tsaya a bisa Dutsen Zaitun wanda yake wajen gabas da Urushalima. Dutsen Zaitun zai tsage biyu daga gabas zuwa yamma, ya zama babban kwari. Sashi guda na dutsen zai janye zuwa wajen kudu. Ɗaya sashin kuma zai janye zuwa wajen arewa.

5 Za ku gudu zuwa kwarin duwatsuna, gama kwarin duwatsu zai kai har Azel, kamar yadda kakanninku suka gudu a zamanin Azariya, Sarkin Yahuza, a lokacin da aka yi girgizar ƙasa. Sa’an nan Ubangiji Allahna zai zo tare da dukan tsarkakansa!

6 A wannan rana ba haske. Masu ba da haske za su dushe.

7 Ubangiji ne ya san wannan rana. Ba rana ba dare. Da maraice ma akwai haske.

8 A wannan rana ruwa mai rai zai gudano daga Urushalima. Rabinsa zai nufi tekun Gishiri, rabi kuma zai nufi Bahar Rum. Zai riƙa malalowa rani da damuna.

9 A ranar, Ubangiji zai zama Sarkin Duniya duka, zai kuma zama shi ne Ubangiji shi kaɗai, ba wani suna kuma sai nasa.

10 Ƙasa dukka za ta zama fili, daga Geba zuwa Rimmon a kudancin Urushalima. Amma Urushalima za ta kasance a kan tudu, za ta miƙe daga Ƙofar Biliyaminu, zuwa wurin da ƙofa ta fari take a dā, har zuwa Ƙofar Kusurwa, sa’an nan ta miƙe daga Hasumiyar Hananel zuwa wuraren matsewar ruwan inabin sarki.

11 Za a zauna cikin Urushalima lami lafiya, ba sauran la’ana.

12 Ga annobar da Ubangiji zai bugi dukan al’ummai da ita, wato su da suka tafi su yi yaƙi da Urushalima. Naman jikunansu zai ruɓe lokacin da suke a tsaye. Idanunsu kuma za su ruɓe cikin kwarminsu. Harsunansu za su ruɓe a bakunansu.

13 A wannan rana babbar gigicewa daga wurin Ubangiji za ta faɗo musu, har kowa zai kama hannun ɗan’uwansa, ya kai masa dūka.

14 Mutanen Yahuza za su yi yaƙi don su kāre Urushalima. Za a kuma tattara dukan dukiyar al’umman da suke kewaye, su zinariya, da azurfa, da riguna tuli.

15 Annoba irin wannan kuma za ta faɗo wa dawakai da alfadarai, da raƙuma, da jakuna, da dukan dabbobin da suke cikin sansaninsu.

16 Sa’an nan wanda ya ragu daga cikin dukan al’umman da suka kai wa Urushalima yaƙi zai riƙa haurawa zuwa Urushalima kowace shekara, domin yi wa Ubangiji Maɗaukakin Sarkin sujada a lokacin kiyaye Idin Bukkoki.

17 Idan kuwa wata al’umma a duniya ba ta haura zuwa Urushalima domin ta yi wa Ubangiji Maɗaukakin Sarki sujada ba, ba za a yi mata ruwan sama ba.

18 Idan al’ummar Masar ba ta halarci Idin Bukkoki ba, ba za a yi mata ruwan sama ba. Ubangiji kuma zai kawo mata irin annobar da ya kawo wa al’umman da suka ƙi halartar Idin Bukkoki.

19 Wannan shi ne hukuncin da za a yi wa Masar da dukan al’umman da suka ƙi halartar Idin Bukkoki.

20 A wannan rana za a zāna waɗannan kalmomi, wato “Mai Tsarki ga Ubangiji” a kan ƙararrawar dawakai. Tukwanen da suke Haikalin Ubangiji za su zama kamar kwanonin da suke a gaban bagade.

21 Kowace tukunya da take a Urushalima da Yahuza za ta zama tsattsarka ga Ubangiji Mai Runduna domin dukan masu miƙa hadaya su ɗauka su dafa naman hadaya a cikinsu. A wannan rana ba za a ƙara samun mai ciniki a Haikalin Ubangiji Mai Runduna ba.