Categories
TIT

TIT 2

Koyar da Kyakkyawar Koyarwa

1 Amma kai kam, sai ka faɗi abin da ya dace da sahihiyar koyarwa.

2 Dattawa su kasance masu kamunkai, natsattsu, mahankalta, masu sahihiyar bangaskiya, da ƙauna, da kuma jimiri.

3 Haka kuma, manyan mata su kasance masu keɓaɓɓen hali, ba masu yanke, ko masu jarabar giya ba, su zamana masu koyar da kyakkyawan abu,

4 ta haka su koya wa mata masu ƙuruciya su so mazansu da ‘ya’yansu,

5 su kuma kasance natsattsu, masu tsarkin rai, masu kula da gida, masu alheri, masu biyayya ga mazansu, don kada a kushe Maganar Allah.

6 Haka kuma, ka gargaɗi samari su yi kamunkai.

7 Kai ma sai ka zama gurbi na aiki nagari ta kowace hanya, da koyarwarka kana nuna rashin jirkituwa, da natsuwa,

8 da kuma sahihiyar maganar da ba za a kushe mata ba, don a kunyata abokan hamayya, su rasa hanyar zarginmu.

9 Bayi su yi biyayya ga iyayengijinsu, su kuma gamsar da su ta kowane hali. Kada su yi tsayayya,

10 ko taɓe-taɓe, sai dai su riƙi amana sosai, don su ƙawatar da koyarwar Allah Mai Cetonmu ta kowane hali.

11 Alherin Allah ya bayyana saboda ceton dukkan mutane,

12 yana koya mana mu ƙi rashin bin Allah da mugayen sha’awace-sha’awacen duniya, mu kuma yi zamanmu a duniyar nan da natsuwa, da adalci, da kuma bin Allah,

13 muna sauraron cikar begen nan mai albarka, wato bayyanar ɗaukakar Allahnmu Mai Girma, Mai Cetonmu Yesu Almasihu,

14 wanda ya ba da kansa dominmu, domin ya fanso mu daga dukan mugun aiki, ya kuma tsarkake jama’a su zama abin mulkinsa, masu himmar yin kyakkyawan aiki.

15 Ka yi ta sanar da waɗannan abubuwa, kana gargaɗar da su, kana tsawatarwa da ƙaƙƙarfan umarni. Kada ka yarda kowa yă raina ka.

Categories
TIT

TIT 3

Himmantuwa ga Aiki Nagari

1 Ka riƙa tuna musu su yi wa mahukunta da shugabanni ladabi, suna yi musu biyayya, suna kuma zaune da shirinsu na yin kowane irin kyakkyawan aiki.

2 Kada su ci naman kowa, kada su yi husuma, sai dai su zama salihai, suna yi wa dukan mutane matuƙar tawali’u.

3 Mu kanmu ma dā can mun yi wauta, mun kangare, an ɓad da mu, mun jarabta da muguwar sha’awa da nishaɗi iri iri, mun yi zaman ƙeta da hassada, mun zama abin ƙi, mu kuma mun ƙi waɗansu.

4 Amma sa’ad da alherin Allah Mai Cetonmu da ƙaunarsa ga ‘yan adam suka bayyana,

5 sai ya cece mu, ba don wani aikin adalci da mu muka yi ba, a’a, sai dai domin jinƙan nan nasa, albarkacin wankan nan na sāke haihuwa, da kuma sabuntawar nan ta Ruhu Mai Tsarki,

6 wanda ya zubo mana a yalwace ta wurin Yesu Almasihu Mai Cetonmu.

7 Wannan kuwa domin a kuɓutar da mu bisa ga alherinsa ne, mu kuma zama magāda masu bege ga rai madawwami.

8 Maganar nan tabbatacciya ce.

Ina so ka ƙarfafa waɗannan abubuwa ƙwarai, don waɗanda suka ba da gaskiya ga Allah su himmantu ga aiki nagari, waɗannan abubuwa kuwa masu kyau ne, masu amfani kuma ga mutane.

9 Amma ka yi nesa da gardandamin banza, da ƙididdigar asali, da husuma, da jayayya a kan Shari’a, domin ba su da wata riba, aikin banza ne kuma.

10 Mutumin da yake sa tsattsaguwa kuwa, in ya ƙi kula da gargaɗinka na farko da na biyu, to, sai ka fita sha’aninsa.

11 Ka dai sani irinsa ɓatacce ne, mai yin zunubi, shi kansa ma ya sani haka yake.

Waɗansu Umarnai

12 Sa’ad da na aiko Artimas ko Tikikus zuwa wurinka, sai ka yi matuƙar, ƙoƙari ka zo wurina a Nikafolis, don na yi niyyar cin damuna a can.

13 Ka yi himmar taimakon Zinas, masanin shari’a, da Afolos, su kamo hanya, ka kuma tabbata ba abin da ya gaza musu.

14 Jama’armu su koyi himmantuwa ga aikin kirki don biyan bukatun matsattsu, kada su zama marasa amfani.

Sa Albarka

15 Duk waɗanda suke tare da ni suna gaishe ka. Ka gayar mini da masoyanmu, masu bangaskiya.

Alheri yă tabbata a gare ku, ku duka.

Categories
FIL

FIL 1

Gaisuwa

1 Daga Bulus, ɗan sarƙa saboda Almasihu Yesu, da kuma Timoti ɗan’uwanmu, zuwa ga Filiman ƙaunataccen abokin aikinmu,

2 da Aufiya ‘yar’uwarmu, da Arkibus abokin famanmu, da kuma ikkilisiyar da take taruwa a gidanka.

3 Alheri da salama na Allah Ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.

Ƙaunar Filiman da Bangaskiyarsa

4 A kullum ina gode wa Allahna duk sa’ad da nake yi maka addu’a,

5 saboda nakan ji labarin ƙauna da bangaskiya da kake yi wa Ubangiji Yesu da dukkan tsarkaka.

6 Ina addu’a bangaskiyar nan da ta haɗa ku, tă kasance mai ƙwazo a wajen ciyar da sanin dukkan kyawawan abubuwan da suke namu, saboda Almasihu.

7 Na yi farin ciki ƙwarai, zuciyata kuma ta ƙarfafa saboda ƙaunar da kake yi, yă kai ‘dan’uwana, domin zukatan tsarkaka sun wartsake ta dalilinka.

Bulus Ya Yi Roƙo domin Unisimas

8 Saboda haka, ko da yake saboda Almasihu ina iya umartarka gabagaɗi, ka yi abin da ya wajaba,

9 duk da haka saboda ƙauna, na fi so in roƙe ka, ni Bulus tsoho, a yanzu kuma ga ni ɗan sarƙa saboda Almasihu Yesu,

10 ina roƙonka saboda ɗana Unisimas, wanda na zama ubansa ina ɗaure.

11 Dā kam, ba shi da wani amfani a wurinka, amma a yanzu, hakika yana da amfani a gare mu, ni da kai.

12 Ga shi nan, na komo maka da shi kamar gudan zuciyata.

13 Dā kam sona in riƙe shi a wurina, yă riƙa yi mini hidima a madadinka, muddin ina ɗaure saboda bishara.

14 Amma ba na so in yi kome ba tare da yardarka ba, don kada alherinka yă zamana na tilas ne, ba na ganin dama ba.

15 Watakila shi ya sa kuka ɗan rabu, don kă same shi har abada,

16 ba kuma a kan bawa ba, sai dai a kan abin da ya fi bawa, wato ‘dan’uwa abin ƙauna, tun ba ma a gare ni ba, balle fa a gare ka, ta wajen al’amarin jiki da kuma wajen al’amarin Ubangiji.

17 Saboda haka in ka ɗauke ni a kan abokin tarayya, to, sai ka karɓe shi kamar yadda za ka karɓe ni.

18 Ko ma ya yi maka wani laifi, ko kuwa kana binsa wani abu, sai ka mai da shi a kaina.

19 Ni Bulus, ni nake rubuto wannan da hannuna, ni kuwa zan biya, kada ma a yi zancen ranka da na fanso maka!

20 Ya ɗan’uwana, ka yarda in sami wata fa’ida a gare ka saboda Ubangiji! Ka sanyaya mini zuciya saboda Almasihu.

21 Don na tabbatar da biyayyarka, shi ya sa na rubuto maka, don na sani za ka yi, har fiye da abin da na faɗa.

22 Har wa yau kuma, ka shirya mini masauki, domin ina sa zuciya a ba ni yarjin zuwa gare ku albarkacin addu’arku.

Gaisuwa

23 Abafaras, abokin ɗaurina saboda Almasihu Yesu, yana gaishe ka,

24 haka kuma Markus, da Aristarkus, da Dimas, da Luka, abokan aikina, suna gaishe ka.

25 Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu yă tabbata a zukatanku.

Categories
YAK

YAK 1

Gaisuwa

1 Daga Yakubu, bawan Allah, da kuma na Ubangiji Yesu Almasihu, zuwa ga kabilan nan goma sha biyu da suke a warwatse a duniya. Gaisuwa mai yawa.

Bangaskiya da Tawali’u

2 Ya ku ‘yan’uwana, duk sa’ad da gwaje-gwaje iri iri suka same ku, ku mai da su abin farin ciki ƙwarai.

3 Domin kun san jarrabawar bangaskiyarku takan haifi jimiri.

4 Sai kuma jimiri ya yi cikakken aikinsa, domin ku zama kamilai cikakku kuma, ba ku gaza da kome ba.

5 In waninku ya rasa hikima, sai ya roƙi Allah, mai ba kowa hannu sake, ba tare da gori ba, sai kuwa a ba shi.

6 Amma fa sai ya roƙa da bangaskiya, ba tare da shakka ba. Don mai shakka kamar raƙuman ruwan teku yake, waɗanda iska take korawa tana tuttunkuɗawa.

7-8 Kada irin mutumin nan mai zuciya biyu, wanda bai tsai da zuciyarsa a gu ɗaya a dukan al’amuransa ba, ya sa rai da wani abu a gun Ubangiji.

9 Ƙasƙantaccen ɗan’uwa yă yi taƙama da ɗaukakarsa.

10 Mai arziki kuma yă yi alfarma da ƙasƙancinsa, gama zai shuɗe kamar hudar ciyawa.

11 In rana ta tāke da ƙunarta, sai ciyawa ta bushe, hudarta ta kaɗe, kyanta kuma ya gushe. Haka ma mai arziki zai gushe yana a cikin tsakiyar harkarsa.

Gwaji da Jarrabawa

12 Albarka tā tabbata ga mai jimirin gwaji, domin in ya jure gwajin, sai ya sami kambin rai, wanda Ubangiji ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari.

13 Duk wanda ake jarabta, kada ya ce Allah ne yake jarabtarsa, gama ba shi yiwuwa a jarabci Allah da mugunta, shi kansa kuwa ba ya jarabtar kowa.

14 Amma kowane mutum yakan jarabtu in mugun burinsa ya ruɗe shi, ya kuma yaudare shi.

15 Mugun buri kuma in ya yi ciki, yakan haifi zunubi. Zunubi kuma in ya balaga, yakan jawo mutuwa.

16 Kada fa a yaudare ku, ya ‘yan’uwana ƙaunatattu.

17 Kowace kyakkyawar baiwa, da kowace cikakkiyar kyauta, daga Sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.

18 Bisa ga nufinsa ya kawo mu ta maganar gaskiya, domin mu zama kamar nunan fari na halittarsa.

Jin Magana da Aikatawa

19 Ya ‘yan’uwana ƙaunatattu, ku san wannan, wato, kowa yă yi hanzarin kasa kunne, da jinkirin yin magana, da kuma jinkirin yin fushi,

20 don fushin mutum ba ya aikata adalci.

21 Saboda haka, sai ku yar da kowane irin aikin ƙazanta da ƙeta iri iri, maganar nan da aka dasa a zuciyarku, ku yi na’am da ita a cikin halin tawali’u, domin ita ce mai ikon ceton rayukanku.

22 Amma ku zama masu aikata maganar, ba masu ji kawai, kuna yaudarar kanku ba.

23 Don duk wanda yake mai jin maganar ne kawai, ba mai aikatawa ba, kamar mutum yake mai duba fuskarsa a madubi,

24 don yakan dubi fuskarsa ne kawai ya tafi, nan da nan kuwa sai ya mance kamanninsa.

25 Amma duk mai duba cikakkiyar ka’idar nan ta ‘yanci, ya kuma nace a kanta, ya zama ba mai ji ne kawai ya mance ba, sai dai mai aikatawa ne ya zartar, to wannan shi za a yi wa albarka a cikin abin da yake aikatawa.

26 In wani yana zaton shi mai addini ne, amma bai kame bakinsa ba, sai dai ya yaudari kansa, to, addinin mutumin nan na banza ne.

27 Addini sahihi kuma marar aibu a gaban Allah Ubanmu, shi ne a kula da gwauraye mata, da marayu a cikin ƙuntatarsu, a kuma a keɓe kai marar aibi daga duniya.

Categories
YAK

YAK 2

Faɗaka a kan Tara

1 Ya ku ‘yan’uwana, kada ku nuna bambanci muddin kuna riƙe da bangaskiyarku ga Ubangijinmu Yesu Almasihu, Ubangiji Maɗaukaki.

2 Misali, in mutum mai zobban zinariya da tufafi masu ƙawa ya halarci taronku, wani matalauci kuma ya shigo a saye da tsummoki,

3 sa’an nan kuka kula da mai tufafi masu ƙawar nan, har kuka ce masa, “Ga mazauni mai kyau a nan,” matalaucin nan kuwa kuka ce masa, “Tsaya daga can,” ko kuwa, “Zauna a nan ƙasa a gabana,”

4 ashe, ba ku nuna bambanci a tsakaninku ba ke nan, kuna zartar da hukunci da mugayen tunani?

5 Ku saurara, ya ‘yan’uwana ƙaunatattu. Ashe, Allah bai zaɓi matalautan duniyar nan su wadata da bangaskiya, har su sami gado a cikin mulkin nan da ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari ba?

6 Amma, kun wulakanta matalauta! Ashe, ba masu arzikin ne suke matsa muku ba? Ba su ne kuwa suke janku zuwa gaban shari’a ba?

7 Ba kuma su ne kuke saɓon sunan nan mai girma da ake kiranku da shi ba?

8 Idan lalle kun cika muhimmin umarni yadda Nassi ya ce, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka,” to, madalla.

9 Amma in kun nuna bambanci, kun yi zunubi ke nan, Shari’a kuma ta same ku da laifin keta umarni.

10 Duk wanda yake kiyaye dukkan Shari’a, amma ya saɓa a kan abu guda, ya saɓi Shari’a gaba ɗaya ke nan.

11 Domin shi wannan da ya ce, “Kada ka yi zina,” shi ne kuma ya ce, “Kada ka yi kisankai.” To, in ba ka yi zina ba amma ka yi kisankai, ai, ka zama mai keta Shari’a ke nan.

12 Saboda haka, maganarku da aikinku su kasance irin na mutanen da za a yi wa shari’a bisa ga ka’idar ‘yanci.

13 Gama Shari’a marar jinƙai ce ga wanda ba ya nuna jinƙai. Amma jinƙai yana rinjayar hukunci.

Bangaskiya Ba Tare da Ayyuka Ba Banza Ce

14 Ya ku ‘yan’uwana, ina amfani mutum ya ce yana da bangaskiya, alhali kuwa ba ya aikin da zai nuna ta? Anya, bangaskiyar nan tāsa ta iya cetonsa?

15 Misali, in wani ɗan’uwa ko ‘yar’uwa suna zaman huntanci, kullum kuma abinci bai wadace su ba,

16 waninku kuma ya ce musu, “To, ku sauka lafiya, Allah ya ba ci, da sha, da tufatarwa” ba tare da kun biya musu bukata ba, ina amfanin haka?

17 Haka ma, bangaskiya ita kaɗai, ba tare da aikin da ya nuna ta ba, banza ce.

18 To, amma wani zai ce, “Ai, kai kana da bangaskiya, ni kuwa sai aikatawa.” To, nuna mini bangaskiya, taka ba tare da aikatawa ba, ni kuma in nuna maka aikatawata, tabbatar bangaskiyata.

19 Ka gaskata Allah ɗaya ne? To, madalla. Ai, ko aljannu ma sun gaskata, amma suna rawar jiki don tsoro.

20 Kai marar azanci! Wato sai an nuna maka, bangaskiya ba tare da aikatawa ba, wofiya ce?

21 Sa’ad da kakanmu Ibrahim ya miƙa ɗansa Ishaku a bagadin hadaya, ashe, ba ta wurin aikatawa ne ya barata ba?

22 Ka gani, ashe, bangaskiyarsa da aikatawarsa duka yi aiki tare, har ta wurin aikatawar nan bangaskiyarsa ta kammala.

23 Aka kuma cika Nassin nan da ya ce, “Ibrahim ya gaskata Allah, bangaskiyar nan tasa kuma aka lasafta ta adalci ce a gare shi,” aka kuma kira shi aminin Allah.

24 Kun ga, ashe, Allah yana kuɓutar da mutum saboda aikatawarsa ne, ba saboda bangaskiya ita kaɗai ba.

25 Ashe, ba haka kuma Rahab karuwar nan ta sami kuɓuta saboda aikatawarta ba? Wato, sa’ad da ta sauki jakadun nan, ta fitar da su ta wata hanya dabam?

26 To, kamar yadda jiki ba numfashi matacce ne, haka ma bangaskiya ba aikatawa matacciya ce.

Categories
YAK

YAK 3

Ɓarnar Harshe

1 Ya ku ‘yan’uwana, kada yawancinku su zama masu koyarwa, domin kun sani, mu da muke koyarwa za a yi mana shari’a da ƙididdiga mafi tsanani.

2 Domin dukanmu muna yin kuskure da yawa. In kuwa mutum ba ya shirme a maganarsa, to, shi cikakken mutum ne, yana kuwa iya kame duk sauran gaɓoɓinsa ma.

3 Ga misali, idan mun sa linzami a bakin doki, don mu bi da shi, mukan sarrafa dukan jikinsa ma.

4 Ku dubi jiragen ruwa kuma, ko da yake suna da girma haka ƙaƙƙarfar iska kuma tana kora su, duk da haka, da ɗan ƙaramin ƙarfe ne matuƙi yake juya su duk inda ya nufa.

5 Haka ma harshe yake, ga shi, ɗan ƙaramin abu ne, sai manyan fariya! Ku dubi yadda ɗan ƙaramin ƙyastu yake kunna wa babban jeji wuta!

6 Harshe ma wuta ne fa! A cikin duk gaɓoɓinmu, harshe shi ne tushen kowace irin mugunta, mai ɓata dukan jiki, mai zuga zuciyar mutum ta tafasa, shi kuwa Gidan Wuta ne yake zuga shi.

7 Don kuwa ana iya sarrafa kowace irin dabba, da tsuntsu, da masu jan ciki, da halittar ruwa, ɗan adam har yā sarrafa su ma,

8 amma ba ɗan adam ɗin da zai iya sarrafa harshe, ai, mugunta ne da ba ta hanuwa, a cike yake da dafi mai kashewa.

9 Da shi muke yabon Ubangiji Uba, da shi kuma muke zagin mutane waɗanda aka halitta da kamannin Allah.

10 Da baki ɗaya ake yabo, ake kuma zagi. ‘Yan’uwana, ai, wannan bai kamata ba!

11 Ashe, marmaro ɗaya ya iya ɓuɓɓugowa da ruwan daɗi da na zartsi ta ido guda?

12 Ya ‘yan’uwana, ashe, ɓaure yana iya haifar zaitun? Ko kuwa inabi ya haifi ɓaure? Haka kuma, ba dama a sami ruwan daɗi a idon ruwan zartsi.

Hikima Mai Saukowa daga Sama

13 Ina mai hikima da fahimi a cikinku? To, ta kyakkyawan zamansa sai ya nuna aikinsa da halin tawali’u da hikima suke sawa.

14 Amma in kuna da matsanancin kishi da sonkai a zuciyarku, kada ku yi alwashi da haka, kuna saɓa wa gaskiya.

15 Wannan hikima ba irin wadda take saukowa daga Sama ba ce, ta duniya ce, ta son zuciya , ta Shaiɗan kuma.

16 A duk inda kishi da sonkai suke, a nan hargitsi da kowane irin mugun aiki ma suke.

17 Amma hikimar nan ta Sama, da farko dai tsattsarka ce, mai lumana ce, saliha ce, mai sauƙin kai, mai tsananin jinƙai, mai yawan alheri, mai kaifi ɗaya, sahihiya kuma.

18 Daga irin salama wanda masu sulhuntawa suke shukawa akan girbe adalci.

Categories
YAK

YAK 4

Abuta da Duniya

1 Me yake haddasa gāba da husuma a tsakaninku? Ashe, ba sha’awace-sha’awacenku ne suke yaƙi da juna a zukatanku ba?

2 Kukan yi marmarin abu ku rasa, sai ku yi kisankai. Kukan yi kwaɗayi, ku kasa samu, sai ku yi husuma da faɗa. Kukan rasa don ba kwa addu’a ne.

3 Kukan yi addu’a ku rasa, don kun yi ta da mugun nufi ne, don ku ɓatar a kan nishaɗinku.

4 Maciya amana! Ashe, ba ku sani abuta da duniya gāba ce da Allah ba? Saboda haka, duk mai son abuta da duniya, yā mai da kansa mai gāba da Allah ke nan.

5 Ko kuna tsammani a banza ne Nassi ya ce, “Wannan ruhu da Allah ya sa a cikinmu yana tsaronmu ƙwarai”?

6 Allah shi yake yin mayalwacin alheri. Domin haka Nassi ya ce, “Allah yana gāba da masu girmankai, amma yana yi wa masu tawali’u alheri.”

7 Saboda haka, ku miƙa kanku ga Allah, ku yi tsayayya da Iblis, lalle kuwa zai guje muku.

8 Ku kusaci Allah, shi ma zai kusace ku. Ku tsarkake al’amuranku, ya ku masu zunubi. Ku kuma tsarkake zukattanku, ya ku masu zuciya biyu.

9 Ku yi nadama, ku yi baƙin ciki, ku yi ta kuka. Dariyarku tă zama baƙin ciki, murnarku tă koma ɓacin zuciya.

10 Ku ƙasƙantar da kanku ga Ubangiji, shi kuwa zai ɗaukaka ku.

Ɗora wa Ɗan’uwa Laifi

11 Ya ku ‘yan’uwana, kada ku kushe wa juna. Kowa ya kushe wa ɗan’uwansa, ko ya ɗora masa laifi, ya kushe wa shari’a ke nan, ya kuma ɗora mata laifi. In kuwa ka ɗora wa shari’a laifi, kai ba mai binta ba ne, mai ɗora mata laifi ne.

12 Mai ba da Shari’a ɗaya ne, shi ne kuma mai yinta, shi ne kuwa mai ikon ceto da hallakarwa. To, kai wane ne har da za ka ɗora wa ɗan’uwanka laifi?

Kada a Yi Fariya Saboda Gobe

13 To, ina masu cewa, “Yau ko gobe za mu je gari kaza, mu shekara a can, mu yi ta ciniki, mu ci riba”?

14 Alhali kuwa ba ku san abin da gobe za ta kawo ba. Wane iri ne ranku? Ai, kamar hazo yake, jim kaɗan sai ya ɓace.

15 Sai dai ya kamata ku ce, “In Ubangiji ya nufa, ya kai rai, ma yi kaza da kaza.”

16 Amma ga shi, kuna fariya ta alfarmar banza da kuke yi. Duk irin wannan fariya kuwa muguwar aba ce.

17 Saboda haka, duk wanda ya san abin da ya kamata, ya kuwa kasa yi, ya yi zunubi ke nan.

Categories
YAK

YAK 5

Faɗaka ga Masu Arziki

1 To, ina masu arziki? Ku yi ta kuka da kururuwa saboda baƙin ciki iri iri da za su aukar muku.

2 Arzikinku mushe ne! Tufafinku kuma duk cin asu ne!

3 Zinariyarku da azurfarku sun ɓāci ƙwarai, ɓācin nan nasu kuwa zai zama shaida a kanku, yă ci naman jikinku kamar wuta! Kun dai jibge dukiya a zamanin ƙarshen nan!

4 Ga shi kuwa, zaluncin da kuka yi na hakkin masu girbi a gonakinku yana ta ƙara, kukan masu girbin kuwa ya kai ga kunnen Ubangijin Runduna.

5 Kun yi zaman duniya da annashuwa da almubazzaranci, ashe, kiwata kanku kuka yi saboda ranar yanka!

6 Kun hukunta mai adalci, kun kuma kashe shi, bai kuwa yi muku tsayayya ba.

Haƙuri da Addu’a

7 Domin haka, sai ku yi haƙuri, ‘yan’uwana, har ya zuwa ranar komowar Ubangiji. Ga shi, manomi yana sa rai ga samun amfanin gona mai albarka, yana kuwa haƙuri da samunsa, har a yi ruwan shuka da na kaka.

8 Ku ma sai ku yi haƙuri, ku tsai da zukatanku, domin ranar komowar Ubangiji ta yi kusa.

9 ‘Yan’uwa, kada ku yi wa juna gunaguni, don kada a hukunta ku. Ga mai shari’a a bakin ƙofa!

10 A kan misalin shan wuya da haƙuri kuma, ‘yan’uwa, ku dubi annabawa ma da suka yi magana da sunan Ubangiji.

11 Ga shi, mukan yaba wa waɗanda suka jure. Kun dai ji irin jimirin da Ayuba ya yi, kun kuma ga irin ƙarshen da Ubangiji ya yi masa, yadda Ubangiji yake mai yawan tausayi, mai jinƙai kuma.

12 Amma fiye da kome, ‘yan’uwana, kada ku rantse sam, ko da sama, ko da ƙasa, ko da kowace irin rantsuwa ma. Sai dai in kun ce “I”, ya tsaya a kan “I” ɗin kawai, in kuwa kun ce “A’a”, ya tsaya a kan “A’a” ɗin kawai, don kada a hukunta ku.

13 In waninku yana shan wuya, to, sai ya yi addu’a, in kuma waninku yana murna, to, sai ya yi waƙar yabon Allah.

14 In waninku yana rashin lafiya, to, sai ya kira dattawan ikkilisiya su yi masa addu’a, suna shafa masa mai da sunan Ubangiji.

15 Addu’ar bangaskiya kuwa, za ta warkar da marar lafiya Ubangiji kuma zai tashe shi, in ma ya yi zunubi, za a gafarta masa.

16 Saboda haka, sai ku riƙa bayyana wa juna laifofinku, kuna yi wa juna addu’a, don a warkar da ku. Addu’ar mai adalci tana da ƙarfin aiki ƙwarai da gaske.

17 Iliya ɗan adam ne kamarmu, amma da ya nace da addu’a kada a yi ruwa, sai da aka shekara uku da wata shida ba a yi ruwa a ƙasar ba.

18 Da ya sāke yin addu’a kuwa, sai sama ta sako ruwa, ƙasa kuma ta ba da amfaninta.

19 Ya ku ‘yan’uwana, in waninku ya bauɗe wa gaskiya, wani kuma ya komo da shi,

20 to, yă dai tabbata, kowa ya komo da mai zunubi a hanya daga bauɗewarsa, ya kuɓutar da ran mai zunubin nan ke nan daga mutuwa, ya kuma rufe ɗumbun zunubansa.

Categories
1 BIT

1 BIT 1

Gaisuwa

1 Daga Bitrus, manzon Yesu Almasihu, zuwa ga zaɓaɓɓun Allah da suke bare, a warwatse a Fantas, da Galatiya, da Kafadokiya, da Asiya, da kuma Bitiniya,

2 su da suke zaɓaɓɓu bisa ga rigyasanin Allah Uba, waɗanda Ruhu kuma ya tsarkake, domin su yi wa Yesu Almasihu biyayya, su kuma tsarkaka da jininsa. Alheri da salama su yawaita a gare ku.

Rayayyiyar Bege

3 Godiya ta tabbata a gare shi, shi wanda yake Allah da Uba na Ubangijinmu Yesu Almasihu, wanda ta wurin tsananin jinƙansa ya sāke haifuwarmu, domin mu yi rayayyen bege, ta wurin albarkacin tashin Yesu Almasihu daga matattu,

4 mu kuma sami gādo marar lalacewa, marar ɓāci, marar ƙarewa kuma, wanda aka keɓe muku a Sama,

5 wato, ku da ikon Allah yake kiyayewa ta wurin bangaskiyarku, domin samun ceton nan da aka shirya a bayyana a ƙarshen zamani.

6 A kan wannan ne kuke da matuƙar farin ciki, ko da yake da ɗan lokaci kwa yi baƙin ciki ta dalilin gwaje-gwaje iri iri.

7 Wannan kuwa domin a tabbatar da sahihancin bangaskiyarku ne (wadda ta fi zinariya daraja nesa, ita zinariya kuwa, ko da yake mai ƙarewa ce, akan jarraba ta da wuta), domin bangaskiyar nan taku tă jawo muku yabo da girma da ɗaukaka a bayyanar Yesu Almasihu.

8 Ko da yake ba ku taɓa ganinsa ba, kuna ƙaunarsa. Ko da yake ba kwa ganinsa a yanzu, duk da haka kuna gaskatawa da shi, kuna farin ciki matuƙa, wanda ya fi gaban ambato,

9 kuna samun ceton rayukanku, ta wurin sakamakon bangaskiyarku.

10 Annabawan da suka yi annabci a kan alherin da zai zama naku, sun tsananta bin diddigi a kan wannan ceto,

11 suna bincike ko wane ne, ko kuma wane lokaci ne, Ruhun Almasihu da yake a zuciyarsu yake ishara, sa’ad da ya yi faɗi a kan wuyar da Almasihu zai sha, da kuma ɗaukakar da take biye.

12 An dai bayyana musu, cewa ba kansu suke bauta wa ba, ku suke bauta wa, a game da abubuwan da masu yi muku bishara, ta ikon Ruhu Mai Tsarki, wanda aka aiko daga sama suka samar da ku a yanzu. Su ne kuwa abubuwan da mala’iku suke ɗokin gani.

Kira a Yi Zaman Tsarki

13 Don haka, sai ku yi ɗamara, ku natsu, ku sa zuciyarku sosai a kan alherin da zai zo muku a bayyanan Yesu Almasihu.

14 Ku yi zaman ‘ya’ya masu biyayya. Kada ku biye wa muguwar sha’awarku ta dā, ta lokacin jahilcinku.

15 Amma da yake wanda ya kira ku mai tsarki ne, ku ma kanku sai ku zama tsarkaka a cikin dukan al’amuranku.

16 Domin a rubuce yake cewa, “Sai ku zama tsarkaka domin ni mai tsarki ne.”

17 Da yake kuna kiransa Uba a wajen addu’a, shi da yake yi wa kowa shari’a gwargwadon aikinsa, ba zaɓe, sai ku ƙarasa lokacin baƙuncinku, kuna tsoronsa.

18 Domin kun sani an fanshe ku ne daga al’adunku na banza da wofi da kuka gāda, ba da abubuwa masu lalacewa kamar azurfa da zinariya ba,

19 sai dai da jinin nan mai daraja na Almasihu, kamar na ɗan rago marar naƙasa, marar tabo.

20 An rigyasaninsa a kan haka, tun ba a halicci duniya ba, amma saboda ku ne aka bayyana shi a zamanin ƙarshe.

21 To gare shi ne kuka gaskata da Allah, wanda ya ta da shi daga matattu, ya kuma ɗaukaka shi, domin bangaskiyarku da begenku su kasance ga Allah.

22 Da yake kun tsarkake ranku kuna yi wa gaskiya biyayya har kuna nuna sahihiyar ƙauna ga ‘yan’uwa, sai ku himmantu ga ƙaunar juna da zuciya ɗaya.

23 Gama sāke haifuwarku aka yi, ba ta iri mai lalacewa ba, sai dai marar lalacewa, wato, ta Maganar Allah rayayyiya dawwamammiya.

24 Domin

“Duk ɗan adam kamar ciyawa yake,

Duk darajarsa kamar furen ciyawa take,

Ciyawar takan bushe, furen yakan kaɗe,

25 Maganar Ubangiji kuwa dawwamammiya ce,”

Ita ce maganar bishara da aka yi muku.

Categories
1 BIT

1 BIT 2

Rayayyen Dutse da Kabila Tsattsarka

1 Saboda haka, sai ku yar da kowace irin ƙeta, da ha’inci, da munafunci, da hassada, da kuma kowane irin kushe.

2 Kamar jariri sabon haihuwa, ku yi marmarin shan madara marar gami mai ruhu, domin ku girma da shi, har ya kai ku ga samun ceto,

3 in dai kun ɗanɗana alherin Ubangiji.

4 Ku zo a gare shi, rayayyen dutsen nan, hakika abin ƙi ne a gun mutane, amma zaɓaɓɓe, ɗaukakakke a gun Allah.

5 Ku kuma, kamar rayayyun duwatsu, bari a gina gida mai ruhu da ku, domin ku zama tsattsarkar ƙungiyar firistoci, da nufin ku miƙa hadayu na ruhu, abin karɓa ga Allah, ta wurin Yesu Almasihu,

6 Domin a tabbace yake a Nassi cewa,

“Ga shi, na sa mafificin dutsen a gini a Sihiyona, zaɓaɓɓe, ɗaukakakke,

Duk mai gaskatawa da shi kuwa, ba zai kunyata ba.”

7 A gare ku, ku da kuka ba da gaskiya kuwa, shi ɗaukakakke ne. Amma ga waɗanda suka ƙi gaskatawa, to,

“Dutsen da magina suka ƙi,

Shi ne ya zama mafificin dutsen gini,”

8 Da kuma,

“Dutsen sa tuntuɓe,

Da fā na sa faɗuwa.”

Sun yi tuntuɓe ne da maganar, don sun ƙi biyayya da ita. Haka kuwa aka ƙaddaro musu.

9 Amma ku kabila ce zaɓaɓɓiya, ƙungiyar firistocin babban Sarki, tsattsarkar al’umma, jama’ar mallakar Allah, domin ku sanar da mafifitan al’amuran wannan da ya kirawo ku daga cikin duhu, kuka shiga maɗaukakin haskensa.

10 Dā ba jama’a ɗaya kuke ba, amma a yanzu, ku jama’ar Allah ce. Dā ba ku sadu da jinƙansa ba, amma a yanzu kun sadu da shi.

Ku yi Zaman Bayin Allah

11 Ya ƙaunatattuna, ina roƙonku don ku baƙi ne, bare kuma, ku guje wa mugayen sha’awace-sha’awace na halin mutuntaka waɗanda suke yaƙi da zuciyarku.

12 Ku yi halin yabo a cikin al’ummai, don duk sa’ad da suke kushenku, cewa ku mugaye ne, sai su ga kyawawan ayyukanku, har su ɗaukaka Allah a ran da alheri ya sauko musu.

13 Ku yi biyayya ga kowace hukumar mutane saboda Ubangiji, ko ga sarki, domin shi ne shugaba,

14 ko kuwa ga mahukunta, domin su ne ya a’aika su hori mugaye, su kuma yabi masu kirki.

15 Domin nufin Allah ne ku toshe jahilcin marasa azanci ta yin aiki nagari.

16 Ku yi zaman ‘yanci, sai dai kada ku fake a bayan ‘yancin nan naku, ku yi mugunta. Amma ku yi zaman bayin Allah.

17 Ku girmama kowa, ku ƙaunaci ‘yan’uwa, ku ji tsoron Allah, ku girmama sarki.

Koyi da Wahalar Almasihu

18 Ku barori, ku bi iyayen gidanku da matuƙar ladabi, ba sai na kirki da masu sanyin hali kaɗai ba, har ma da miskilai.

19 Ai, abin karɓa ne, in saboda mutum yana sane da nufin Allah, ya jure wa wuyar da yake sha, ba da alhakinsa ba.

20 To, ina abin taƙama don kun yi haƙuri in kun sha dūka a kan laifin da kuka yi? Amma, in kun yi aiki nagari kuka sha wuya a kansa, kuka kuma haƙura, to shi ne abin karɓa ga Allah.

21 Domin a kan haka ne musamman aka kira ku. Gama Almasihu ma ya sha wuya dominku, ya bar muku gurbi ku bi hanyarsa.

22 Bai taɓa yin laifi ba faufau, ba a kuwa taɓa jin yaudara a bakinsa ba.

23 Da aka zage shi bai rama ba, da ya sha wuya kuma bai yi kashedi ba, sai dai ya dogara ga mai shari’ar adalci.

24 Shi kansa ya ɗauke zunubanmu a jikinsa a kan gungume, domin mu yi zamanmu matattu ga zunubi, rayayyu kuma ga adalci. Da raunukansa ne aka warkar da ku.

25 A dā kun ɓăce kamar tumaki, amma a yanzu kun dawo ga Makiyayi, wato mai kula da rayukanku.