Categories
1 YAH

1 YAH 5

Bangaskiya ta Yi Nasara da Duniya

1 Kowa da yake gaskata Yesu shi ne Almasihu, haifaffen Allah ne. Kowa yake ƙaunar mahaifi kuwa, yana ƙaunar ɗa kuma.

2 Ta haka muku sani muna ƙaunar ‘ya’yan Allah, wato, in muna ƙaunar Allah, muna kuma bin umarninsa.

3 Domin ƙaunar Allah ita ce mu bi umarninsa, umarninsa kuwa ba matsananta ba ne.

4 Domin duk wanda yake haifaffen Allah yana nasara da duniya. Bangaskiyarmu kuwa ita ce ta sa muka yi nasara da duniya.

5 Wane ne yake nasara da duniya, in ba wanda ya gaskata Yesu Ɗan Allah ba ne?

Shaida a kan Ɗansa

6 Shi ne wanda ya bayyana ta wurin ruwa da jini, Yesu Almasihu, ba fa ta wurin ruwa kaɗai ba, amma ta wurin ruwa da jini.

7 Ruhu kuma shi ne mai ba da shaida, domin Ruhun shi ne gaskiya.

8 Akwai shaidu uku, wato Ruhun, da ruwa, da kuma jini, waɗannan uku kuwa manufarsu ɗaya ce.

9 Tun da yake muna yarda da shaida mutane, ai, shaidar Allah ta fi ƙarfi. Wannan ita ce shaidar Allah, wato, ya shaidi Ɗansa.

10 Kowa ya gaskata da Ɗan Allah, shaidar tana nan gare shi. Wanda bai gaskata Allah ba, ya ƙaryata shi ke nan, domin bai gaskata shaidar da Allah ya yi Ɗansa ba.

11 Wannan kuma ita ce shaidar, cewa Allah yā ba mu rai madawwami, wannan rai kuwa yana cikin Ɗansa.

12 Duk wanda yake da Ɗan, yana da rai. Wanda ba shi da Ɗan Allah kuwa, ba shi da rai.

Tabbatar Samun Rai Madawwami

13 Na rubuto muku wannan ne, ku da kuka gaskata da sunan Ɗan Allah, domin ku tabbata kuna da rai madawwami.

14 Wannan ita ce amincewarmu a gabansa, wato, in mun roƙi kome bisa ga nufinsa, sai ya saurare mu.

15 In kuwa muka san kome muka roƙa yana sauraronmu, mun tabbata mun sami abin da muka roƙa a gare shi ke nan.

16 Kowa ya ga ɗan’uwansa yana yin zunubin da bai kai ga mutuwa ba, sai ya yi masa addu’a. Saboda mai addu’ar nan kuwa, Allah zai ba da rai ga waɗanda suka yi zunubin da bai kai ga mutuwa ba. Akwai zunubin da yake na mutuwa. Ban ce a yi addu’a domin wannan ba.

17 Duk rashin adalci zunubi ne. Akwai kuma zunubin da ba na mutuwa ba.

18 Mun sani kowane haifaffen Allah ba ya yin zunubi, kasancewarsa haifaffen Allah ita takan kare shi. Mugun nan kuwa ba ta taɓa shi.

19 Mun sani mu na Allah ne, duniya duka kuwa tana hannun Mugun.

20 Mun kuma sani Ɗan Allah ya zo, ya yi mana baiwar fahimta domin mu san shi wanda yake na gaskiya. Mu kuwa muna a cikinsa, shi da yake na gaskiya, wato Ɗansa Yesu Almasihu. Shi ne Allah na gasikya da kuma rai madawwami.

21 Ya ku ‘ya’yana ƙanana, ku yi nesa da gumaka.

Categories
2 YAH

2 YAH 1

Gaisuwa

1 Daga dattijon nan na ikkilisiya zuwa ga uwargida zaɓaɓɓiya, da ‘ya’yanta waɗanda nake ƙauna da gaske, ba kuwa ni kaɗai ba, har ma dukan waɗanda suka san gaskiya,

2 wato, muna ƙaunarku saboda gaskiyar da take a dawwame a cikinmu, za ta kuwa kasance tare da mu har abada.

3 Alheri, da jinƙai, da salama na Allah Uban, da kuma na Yesu Almasihu Ɗan Uban, za su tabbata a gare mu, da gaskiya da ƙauna.

Ku Zauna Cikin Koyarwar Almasihu

4 Na yi farin ciki ƙwarai da samun waɗansu ‘ya’yanki suna bin gaskiya, kamar yadda Uba ya ba mu umarni.

5 Yanzu kuma ina roƙonki, uwargida, ba cewa wani sabon umarni nake rubuto miki ba, sai dai wanda muke da shi tun farko ne, cewa mu ƙaunaci juna.

6 Ƙauna kuwa ita ce mu bi umarninsa. Umarnin kuwa, shi ne kamar yadda kuka ji tun farko, cewa ku yi zaman ƙauna.

7 Gama masu ruɗi da yawa sun fito duniya, waɗanda ba sa bayyana yarda, cewa Yesu Almasihu ya bayyana da jiki, irin wannan shi ne mai ruɗi, magabcin Almasihu.

8 Ku kula da kanku don kada ku yar da aikin da muka yi, amma dai ku sami cikakken sakamako.

9 Kowa ya yi ƙari, bai tsaya a kan koyarwar Almasihu ba, Allah ba ya tare da shi ke nan. Wanda kuwa ya tsaya a kan koyarwar nan, yana da uba da Ɗan.

10 Kowa ya zo gare ku, bai kuwa zo da wannan koyarwa ba, kada ku karɓe shi a gidanku, ko maraba ma kada ku yi masa.

11 Don duk wanda ya yi masa maraba, mugun aikinsa, sai yă shafe shi.

Gaisuwa

12 Ko da yake ina da abin da zan faɗa muku da yawa, na gwammace ba a wasiƙa ba, amma na sa zuciya in ziyarce ku, mu yi magana baka da baka. don farin cikinmu ya zama cikakke.

13 ‘Ya’yan ‘yar’uwarki zaɓaɓɓiya suna gaishe ki.

Categories
3 YAH

3 YAH 1

Gaisuwa

1 Daga dattijon nan na ikkilisiya zuwa ga Gayus, ƙaunatacce, wanda nake ƙauna da gaske.

2 Ya ƙaunataccena, ina addu’a kă sami zaman lafiya ta kowace hanya da kuma lafiya jiki, kamar yadda ruhunka yake a zaune lafiya.

3 Na yi farin ciki ƙwarai sa’ad da waɗansu ‘yan’uwa suka zo suka shaida gaskiyarka, yadda hakika kake bin gaskiya.

4 Ba abin da ya fi faranta mini rai kamar in ji ‘ya’yana suna bin gaskiya.

Yaba Kirkin Gayus

5 Ya ƙaunataccena, duk abin da kake yi wa ‘yan’uwa, aikin bangaskiya kake yi, tun ba ma ga baƙi ba.

6 Su ne suka shaida ƙaunarka a gaban ikkilisiya. Zai kyautu ka raka su a guzuri, kamar yadda ya cancanci bautar Allah,

7 domin saboda sunan nan ne suka fito, ba sa kuma karɓar kome daga al’ummai.

8 Domin haka ya kamata mu karɓi irin mutanen nan, mu ɗau nauyinsu, domin mu zama abokan aiki da su a kan gaskiya.

Diyotarifis Mai Ƙin Bin Magana

9 Na yi wa ikkilisiya ‘yar wasiƙa, amma shi Diyotarifis wanda yake so ya fi kowa a cikinsu, ya ƙi bin maganarmu.

10 Saboda haka, in na zo zan tabbatar masa da abin da yake yi, yana surutu game da mu, yana ɓaɓɓata mu. Wannan ma bai ishe shi ba, har ya ƙi yi wa ‘yan’uwa maraba, yana kuma hana masu so su marabce su, yana fitar da su daga ikkilisiya.

Kyakkyawar Shaida kan Dimitiriyas

11 Ya ƙaunataccena, kada ka kwaikwayi mugun aiki, sai dai nagari. Kowa da yake aikin nagari na Allah ne. Mai mugun aiki kuwa bai san Allah ba sam.

12 Dimitiriyas yana da kyakkyawar shaida a gun kowa, har gaskiya kanta ma tana yi masa shaida. Mu ma mun shaide shi, ka kuwa san shaidarmu tabbatacciya ce.

Gaisuwa

13 Dā kam, ina da abin da zan rubuto maka da yawa, amma yanzu na gwammace kada in rubuto a wasiƙa.

14 Ina sa zuciya mu sadu ba da daɗewa ba, sa’an nan ma yi magana baka da baka.

15 Salama tă tabbata gare ku. Aminanmu suna gaishe ka. Ka gai da aminanmu kowa da kowa.

Categories
YAHU

YAHU 1

Gaisuwa

1 Daga Yahuza bawan Yesu Almasihu, ɗan’uwan Yakubu zuwa ga kirayayyu, ƙaunatattun Allah Uba, keɓaɓɓu ga Yesu Almasihu.

2 Jinƙai, da salama, da ƙauna su yawaita a gare ku.

Hukuncin Malaman Ƙarya

3 Ya ku ƙaunatattuna, da yake dā ma ina ɗokin rubuto muku zancen ceton nan namu, mu duka, sai na ga wajibi ne in rubuto muku in gargaɗe ku, ku dage ƙwarai a kan bangaskiyar nan da aka danƙa wa tsarkaka sau ɗaya tak, ba ƙari.

4 Gama waɗansu mutane sun saɗaɗo a cikinku, waɗanda tun zamanin dā aka ƙaddara ga hukuncin nan, marasa bin Allah ne, masu mai da alherin Allah dalilin aikata fajirci, suna kuma ƙin makaɗaicin Ubangijinmu Yesu Almasihu.

5 Sai dai ina so in tuna muku, ko da yake kun riga kun san kome sosai, cewa Ubangiji ya ceci jama’a daga ƙasar Masar, duk da haka daga baya ya hallaka waɗanda ba su ba da gaskiya ba.

6 Har ma mala’ikun da ba su kiyaye girmansu ba, amma suka bar ainihin mazauninsu, ya tsare su cikin sarƙa madawwamiya a baƙin duhu, har ya zuwa shari’ar babbar ranar nan.

7 Haka kuma Saduma da Gwamrata, da birane kewayensu, waɗanda su ma suka dulmuya cikin fasikanci da muguwar sha’awa ta jiki, an nuna su domin ishara, suna shan hukuncin madawwamiyar wuta.

8 Haka kuma masu mafarke-mafarken nan, sukan ƙazantar da jikinsu, su ƙi bin mulki, su kuma yi wa masu ɗaukaka baƙar magana.

9 Amma lokacin da babban mala’ika, Mika’ilu yake fama da Iblis, suna mūsu a kan gawar Musa, shi Mika’ilu bai yi garajen ɗora masa laifi da baƙar magana ba, sai dai ya ce, “Ubangiji yă tsawata maka.”

10 Amma mutanen nan sukan kushe duk abin da ba su fahinta ba, saboda abubuwan da suka sani bisa ga jiki suna kamar dabbobi marasa hankali, su ne kuwa sanadin halakarsu.

11 Kaitonsu! Don sun bi halin Kayinu, sun ɗunguma cikin bauɗewar Bal’amu don kwaɗayi, sun kuma hallaka ta irin tawayen Kora.

12 Waɗannan mutane kamar aibobi ne a taronku na soyayya, suna ta shagulgulan ciye-ciye a cikinku, ba kunya ba tsoro, suna kula da kansu kawai. Su kamar holoƙon hadiri ne, wanda iska take korawa. Su kamar itatuwa ne, marasa ‘ya’ya da kaka, matattu murus, tumɓukakku.

13 Su kamar raƙuman ruwan teku ne masu hauka, suna taƙama da kumfar kunyarsu. Su kamar taurari ne masu kai da kawowa, waɗanda aka tanada wa matsanancin duhu har abada.

14 Anuhu ma wanda yake na bakwai daga Adamu, shi ma ya yi annabci a kan waɗannan mutane cewa, “Ga shi, Ubangiji ya zo da dubban tsarkakansa,

15 don ya zartar da hukunci kan kowa, yă kuma tabbatar wa marasa bin Allah dukan aikinsu na rashin bin Allah, da suka aikata ta hanyar rashin bin Allah, da kuma baƙaƙen maganganu da masu zunubi marasa bin Allah suka yi game da shi.”

16 Waɗannan su ne masu gunaguni, masu ƙunƙuni, masu biye wa muguwar sha’awa, marubata, masu yi wa mutane bambaɗanci don samun wata fa’ida.

Faɗaka da Gargadi

17 Ya ku ƙaunatattuna, lalle ku tuna da maganar da manzannin Ubangijinmu Yesu Almasihu suka faɗa a dā,

18 da suka ce da ku, “A zamanin ƙarshe za a yi waɗansu mutane masu ba’a, masu biye wa muguwar sha’awarsu ta rashin bin Allah.”

19 Waɗannan su ne masu raba tsakani, masu son zuciya, marasa Ruhu.

20 Amma ya ku ƙaunatattuna, ku riƙa inganta kanku ga bangaskiyarku mafi tsarki, kuna addu’a da ikon Ruhu Mai Tsarki.

21 Ku tsaya a kan ƙaunar da Allah yake yi mana, kuna sauraron jinƙan Ubangijinmu Yesu Almasihu mai kaiwa ga rai madawwami.

22 Ku ji tausayin waɗanda suke shakka,

23 kuna ceton waɗansu kuna fizgo su daga wuta. Waɗansu kuma ku ji tausayinsu, amma tare da tsoro kuna ƙyamar ko da tufafin da halinsu na mutuntaka ya ƙazantar.

Sa Albarka

24 Ga wanda yake da iko yă tsare ku daga faɗuwa, yă kuma miƙa ku marasa aibi a gaban ɗaukakarsa da matuƙar farin ciki,

25 ga Allah makaɗaici Mai Cetonmu ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu, ɗaukaka, da fifiko, da mulki, da iko su tabbata gare shi, tun fil’azal, da yanzu, da kuma har abada abadin. Amin, amin.

Categories
W. YAH

W. YAH 1

Wahayin Yesu Almasihu

1 Wahayin Yesu Almasihu da Allah ya ba shi ya nuna wa bayinsa abin da lalle ne zai auku ba da daɗewa ba, ya kuwa bayyana shi ta wurin aiko da mala’ikansa zuwa gun bawansa Yahaya,

2 wanda ya shaidi Maganar Allah, da kuma shaidar Yesu Almasihu, har da dukan abin da ya gani.

3 Albarka tā tabbata ga mai karanta maganar nan ta annabci, ta kuma tabbata ga masu ji, waɗanda kuma suke kiyaye abin da yake a rubuce a ciki, domin lokaci ya gabato.

Gaisuwa Zuwa ga Ikilisiyoyi Bakwai

4 Daga Yahaya zuwa ga ikilisiyoyin nan bakwai da suke a ƙasar Asiya.

Alheri da salama su tabbata a gare ku daga wanda yake a yanzu, shi ne a dā, shi ne kuma a nan gaba, da kuma Ruhohin nan bakwai da suke a gaban kursiyinsa,

5 da kuma Yesu Almasihu Amintaccen Mashaidi, na farko a cikin masu tashi daga matattu, mai mulkin sarakunan duniya.

Ɗaukaka da mulki su tabbata har abada abadin ga wanda yake ƙaunarmu, ya kuma ɓalle mana ƙangin zunubanmu ta wurin jininsa,

6 ya mai da mu firistoci, mallakar Allah Ubansa. Amin.

7 Ga shi, zai zo a cikin gajimare, kowa zai gan shi, har da waɗanda suka soke shi, duk kabilan duniya kuma za su yi kuka a kansa. Wannan haka yake. Amin.

8 “Ni ne Alfa. Ni ne Omega,” in ji Ubangiji Allah, wanda yake a yanzu, shi ne a dā, shi ne kuma a nan gaba, Maɗaukaki.

Wahayin Ɗan Mutum

9 Ni ne Yahaya, ɗan’uwanku abokin tarayyarku a cikin tsanani, da mulki, da jimiri da suke a cikin Yesu. Ina a can tsibirin da ake kira Batamusa saboda Maganar Allah da kuma shaidar Yesu.

10 A ranar Ubangiji ya zamana Ruhu ya iza ni, sai na ji wata murya mai ƙara a bayana kamar ta ƙaho,

11 tana cewa, “Rubuta abin da ka gani a littafi, ka aika wa ikilisiyoyin nan bakwai, wato ta Afisa, da ta Simirna, da ta Birgamas, da ta Tayatira, da ta Sardisu, da ta Filadalfiya, da kuma ta Lawudikiya.”

12 Sai na juya in ga wanda yake yi mini magana, da juyawata kuwa, sai na ga fitilu bakwai na zinariya.

13 A tsakiyar fitilun nan kuwa, na ga wani kamar Ɗan Mutum, saye da riga har idon sawu, ƙirjinsa kuma da ɗamarar zinariya.

14 Kansa da gashinsa farare fat ne kamar farin ulu, farare fat kamar alli, idanunsa kamar harshen wuta,

15 ƙafafunsa kamar gogaggiyar tagulla, kamar wadda aka tace a maƙera, muryarsa kuma kamar ƙugin ruwaye masu gudu.

16 Yana riƙe da tauraro bakwai a hannunsa na dama, daga bakinsa kuma takobi mai kaifi biyu yake fitowa. Fuskarsa tana haske kamar rana a tsaka.

17 Da na gan shi, sai na fāɗi a gabansa kamar na mutu. Amma ya ɗora mini hannunsa na dama, ya ce, “Kada ka ji tsoro. Ni ne na Farko. Ni ne na Ƙarshe,

18 ni ne kuma Rayayye. Dā na mutu, amma ga shi a yanzu, ina a raye har abada abadin, ina kuwa da mabuɗan mutuwa da na Hades.

19 To, ka rubuta abubuwan da ka gani, da abubuwan da suke a nan a yanzu, da abubuwan da suke shirin aukuwa bayan wannan.

20 Asirtacciyar ma’anar taurarin nan bakwai da ka gani a hannuna na dama kuwa, da kuma fitilun nan bakwai na zinariya, to, su taurarin nan bakwai, mala’iku ne na ikilisiyoyin nan bakwai, fitilun nan bakwai kuwa, ikkilisiya bakwai ɗin ne.

Categories
W. YAH

W. YAH 2

Saƙo zuwa ga Afisa

1 “Sai ka rubuta wa mala’ikan ikkilisiyar da take a Afisa haka, ‘Ga maganar wadda take riƙe da taurarin nan bakwai a hannunsa na dama, wadda kuma take tafiya a tsakiyar fitilun nan bakwai na zinariya.

2 “ ‘Na san ayyukanka, da famarka, da jimirinka, da yadda ba ka iya haƙurce wa mugaye, ka kuma gwada waɗanda suke ce da kansu manzanni, alhali kuwa ba su ba ne, ka tarar na ƙarya ne.

3 Na sani kana haƙuri, kana kuma jimiri saboda sunana, ba ka kuwa gaji ba.

4 Amma ga laifinka, wato, ka yar da ƙaunar da ka yi tun daga farko.

5 Ka tuna da komawa bayan da ka yi fa, ka tuba, ka yi irin aikin da ka yi tun daga farko. In ba haka ba, zan zo a gare ka in kawar da fitilarka daga wurin zamanta, sai ko in ka tuba.

6 Amma a wannan waje kam ka kyauta, kā ƙi ayyukan Nikolatawa, ni ma kuwa na ƙi su.

7 Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi izinin cin ‘ya’yan itacen rai, wanda yake a cikin Firdausin Allah.’ ”

Saƙo Zuwa ga Simirna

8 “Ka kuma rubuta wa mala’ikan ikkilisiyar da take a Simirna haka, ‘Ga maganar wanda yake na Farko da na Ƙarshe, wanda ya mutu, ya kuma sāke rayuwa.

9 “ ‘Na san tsananin da kake sha, da talaucinka (amma bisa ga hakika kai mawadaci ne), na kuma san yanken da waɗansu suke yi maka, masu cewa su Yahudawa ne, alhali kuwa ba su ba ne, jama’ar Shaiɗan ne.

10 Kada ka ji tsoron wuyar da za ka sha. Ga shi, Iblis yana shiri ya jefa waɗansunku a kurkuku don a gwada ku, za ku kuwa sha tsanani har kwana goma. Ka riƙi amana ko da za a kashe ka, ni kuwa zan ba ka kambin rai.

11 Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara, mutuwa ta biyu ba za ta cuce shi ba ko kaɗan.’ ”

Saƙo Zuwa ga Birgamas

12 “Ka kuma rubuta wa mala’ikan ikkilisiyar da take a Birgamas haka, ‘Ga maganar wanda yake da takobi mai kaifi biyu.

13 “ ‘Na san a inda kake da zama, wato, a inda kursiyin Shaiɗan yake. Duk da haka kuwa, ka tsaya a gare ni, ba ka bar yi mini bangaskiya ba, ko a zamanin Antibas amintaccen mashaidina, wanda aka kashe a cikinku, a inda Shaiɗan yake zaune.

14 Amma ga waɗansu laifofinka kaɗan. Akwai waɗansu a cikinku, da suke bin koyarwar Bal’amu, wanda ya koya wa Balak ya sa Isra’ilawa laifi, don su ci abincin da aka yi wa gumaka sadaka, su kuma yi fasikanci.

15 Haka kai ma kake da waɗansu masu bin koyarwar Nikolatawa.

16 Saboda haka, sai ka tuba. In ba haka ba kuwa, zan zo a gare ka da wuri, in yaƙe su da takobin da yake a bakina.

17 Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ɓoyayyiyar manna, zan kuma ba shi wani farin dutse, da sabon suna a rubuce a jikin dutsen, ba kuwa wanda ya san sunan, sai wanda ya karɓe shi.’ ”

Saƙo Zuwa ga Tayatira

18 “Ka kuma rubuta wa mala’ikan ikkilisiyar da take a Tayatira haka, ‘Ga maganar Ɗan Allah, mai idanu kamar harshen wuta, mai ƙafafu kamar gogaggiyar tagulla.

19 “ ‘Na san ayyukanka, da ƙaunarka, da bangaskiyarka, da ibadarka, da jimirinka, ayyukanka kuma na yanzu, sun fi na farkon.

20 Amma ga laifinka, wato, ka haƙurce wa matar nan Yezebel, wadda take ce da kanta annabiya, take kuma koya wa bayina, tana yaudararsu, su yi fasikanci, su kuma ci abincin da aka yi wa gumaka hadaya.

21 Na ba ta damar tuba, amma ta ƙi tuba da fasikancinta.

22 To, ga shi, zan jefa ta a gado, masu yin fasikanci da ita kuma zan ɗora musu matsananciyar wahala, sai ko in sun tuba da irin aikinta.

23 Zan kashe ‘ya’yanta tashi ɗaya, dukan ikilisiyoyi kuma za su sani Ni ne mai fayyace birnin zuciya. Zan kuma saka wa kowannenku gwargwadon aikinsa.

24 Amma a game da sauranku, ku na Tayatira, da ba sa bin wannan koyarwa, ba su kuma koyi abin da waɗansu suke kira zurfafan al’amuran Shaiɗan ba, ina ce muku, ban ɗora muku wani nauyi ba.

25 Sai dai ku riƙi abin da kuke da shi kankan, har in zo.

26 Duk wanda ya ci nasara, yake kuma kiyaye aikina har ƙarshe, shi zan bai wa iko a kan al’ummai,

27 zai kuwa mallake su da sanda ta ƙarfe, ya farfashe su kamar tukwanen yumɓu

28 (kamar yadda Ni ma kaina na sami iko a gun Ubana), zan kuma ba shi gamzaki.

29 Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikilisiyoyi.’ ”

Categories
W. YAH

W. YAH 3

Saƙo Zuwa ga Sardisu

1 “Ka kuma rubuta wa mala’ikan ikkilisiyar da take a Sardisu haka, ‘Ga maganar mai Ruhohin Allah guda bakwai, da kuma taurarin nan bakwai.

“ ‘Na san ayyukanka, kai rayayye ne, alhali kuwa matacce ne kai.

2 Ka yi zaman tsaro, ka ƙarfafa abin nan da ya saura, yake kuma a bakin mutuwa, don ban ga aikinka cikakke ne ba a gaban Allahna.

3 Don haka, sai ka tuna da abin da ka karɓa ka kuma ji, ka kiyaye shi, sa’an nan ka tuba. In ba za ka yi tsaro ba, zan zo kamar ɓarawo, ba kuwa za ka san a lokacin da zan auko maka ba.

4 Amma dai har yanzu kana da waɗansu kaɗan a Sardisu da ba su ƙazantar da kansu ba, za su kuwa kasance tare da ni da fararen kaya, don sun cancanta.

5 Duk wanda ya ci nasara, za a sa masa fararen tufafi, ba kuwa zan soke sunansa daga Littafin Rai ba, zan ce shi nawa ne a gaban Ubana, da kuma a gaban mala’ikunsa.

6 Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikilisiyoyi.’ ”

Saƙo Zuwa ga Filadalfiya

7 “Ka kuma rubuta wa mala’ikan ikkilisiyar da take a Filadalfiya haka, ‘Ga maganar Mai Tsarkin nan, Mai gaskiya, wanda yake da mabuɗin Dawuda, wanda in ya buɗe, ba mai rufewa, in kuma ya rufe, ba mai buɗewa.

8 “ ‘Na san ayyukanka. Ka ga, na bar maka ƙofa a buɗe, wadda ba mai iya rufewa. Na dai san ƙarfinka kaɗan ne, duk da haka, kā kiyaye maganata, ba ka yi musun sanin sunana ba.

9 To, ga shi, zan sa su waɗanda suke daga jama’ar Shaiɗan, masu cewa su Yahudawa ne, alhali kuwa ba su ba ne, ƙarya suke yi, zan sa su, su zo, su kwanta a gabanka, su sani dai na ƙaunace ka.

10 Tun da yake ka kiyaye maganar da na yi maka ta yin jimiri, Ni ma zan kiyaye ka daga sharrin lokacin nan na gwaji, wanda zai auko wa dukan duniya, don a gwada mazaunan duniya.

11 Ina zuwa da wuri. Ka riƙi abin da kake da shi kankan, kada wani ya karɓe maka kambinka.

12 Duk wanda ya ci nasara, zan mai da shi ginshiƙi a Haikalin Allahna. Ba zai ƙara fita daga ciki ba, zan kuma rubuta sunan Allahna a jikinsa, da sunan Birnin Allahna, wato, Sabuwar Urushalima, mai saukowa daga wurin Allahna daga Sama, da kuma nawa sabon suna.

13 Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikilisiyoyi.’ ”

Saƙo Zuwa ga Lawudikiya

14 “Ka kuma rubuta wa mala’ikan ikkilisiyar da take a Lawudikiya haka, ‘Ga maganar tabbataccen nan, Amintaccen Mashaidi mai gaskiya, wanda ta wurinsa dukkan halittar Allah ta kasance.

15 “ ‘Na san ayyukanka. Ba ka da sanyi, ba ka kuwa da zafi. Da ma a ce kana da sanyi, ko kuwa kana da zafi.

16 To, saboda kai tsakatsaki ne, ba ka da sanyi, ba ka kuwa da zafi, zan tofar da kai daga bakina.

17 Tun da ka ce, kai mai arziki ne, cewa ka wadata ba ka bukatar kome, ba ka sani ba kuwa kai ne matsiyacin, abin yi wa kaito, matalauci, makaho, tsirara kuma.

18 Saboda haka, ina yi maka shawara ka sayi zinariya a guna, wadda aka tace da wuta, don ka arzuta, da kuma fararen tufafi da za ka yi sutura, ka rufe tsiraicinka don kada ka ji kunya, da kuma man shafawa a ido don ka sami gani.

19 Waɗanda nake ƙauna, su nake tsawata wa, nake kuma horo. Saboda haka, sai ka himmantu ka tuba.

20 Ga ni nan a tsaye a bakin ƙofa, ina ƙwanƙwasawa, kowa ya ji muryata ya buɗe ƙofar, sai in shiga wurinsa, in ci abinci tare da shi, shi kuma tare da ni.

21 Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi izinin zama tare da ni a kursiyina. kamar yadda ni ma na ci nasara, na kuma zauna tare da Ubana a kursiyinsa.

22 Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikilisiyoyi.’ ”

Categories
W. YAH

W. YAH 4

Sujada a Samaniya

1 Bayan wannan na duba, sai ga wata ƙofa a buɗe a Sama. Muryar farko da na ji dā, mai kama da ƙaho, ta ce mini, “Hawo nan, zan nuna maka abin da lalle ne ya auku bayan wannan.”

2 Nan da nan kuwa Ruhu ya iza ni, sai ga wani kursiyi a girke a Sama, da wani a zaune a kai.

3 Na zaunen kuwa ya yi kama da yasfa da yakutu. Kewaye da kursiyin kuma akwai wani bakan gizo mai kama da zumurrudu.

4 Kewaye da kursiyin kuwa akwai waɗansu kursiyai ashirin da huɗu, da dattawa ashirin da huɗu a zaune a kai, masu fararen tufafi, da kuma kambin zinariya a kansu.

5 Sai walƙiya take ta fitowa daga kursiyin, da ƙararraki, da kuma aradu. A gaban kursiyin kuma fitilu bakwai suna ci, waɗanda suke Ruhohin nan na Allah guda bakwai.

6 A gaban kursiyin kuwa akwai wani abu kamar bahar na gilas, garau yake kamar ƙarau.

Kewaye da kursiyin kuma, ta kowane gefensa, da waɗansu rayayyun halitta guda huɗu, masu idanu ta ko’ina, gaba da baya.

7 Rayayyiyar halittar farko kamar zaki take, ta biyu kuma kamar ɗan maraƙi, ta uku kuma da fuska kamar ta mutum, ta huɗu kuma kamar juhurma yana jewa.

8 Su rayayyun halittan nan huɗu kuwa, kowaccensu tana da fikafikai shida, jikinsu duk idanu ne ciki da waje, dare da rana kuwa ba sa daina waƙa, suna cewa,

“Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki, Ubangiji Allah Maɗaukaki,

Shi ne a dā, shi ne a yanzu, shi ne kuma a nan gaba!”

9 Duk lokaci kuma da rayayyun halittan nan suka ɗaukaka wanda yake zaune a kan kursiyin, yake kuma raye har abada abadin, suka girmama shi, suka kuma gode masa,

10 sai dattawan nan ashirin da huɗu suka fāɗi a gaban wanda yake a zaune a kan kursiyin, su yi masa sujada, shi da yake a raye har abada abadin, su kuma ajiye kambinsu a gaban kursiyin, suna waƙa, suna cewa,

11 “Macancanci ne kai, ya Ubangiji Allahnmu,

Kă sami ɗaukaka, da girma, da iko,

Domin kai ne ka halicci dukkan abubuwa,

Da nufinka ne suka kasance aka kuma halicce su.”

Categories
W. YAH

W. YAH 5

Yimƙaƙƙen Littafin da Ɗan Ragon

1 A hannun dama na wanda yake zaune a kursiyin kuma, sai na ga wani littafi rubutacce ciki da bai, an yimƙe shi da hatimi bakwai.

2 Na kuma ga wani ƙaƙƙarfan mala’ika, yana shela da murya mai ƙarfi cewa, “Wa ya cancanta ya buɗe littafin nan, ya kuma ɓamɓare hatimansa?”

3 Ba kuwa wani a Sama ko a ƙasa, ko a ƙarƙashin ƙasa, da zai iya buɗe littafin, balle yă duba a cikinsa.

4 Sai na yi ta kuka da ba a sami wanda ya cancanta ya buɗe littafin, ko ya duba a cikinsa ba, ko ɗaya.

5 Sai ɗaya daga cikin dattawan nan ya ce mini, “Kada ka yi kuka. Ga shi, Zakin nan na kabilar Yahuza, Tsatson Dawuda, ya ci nasara har yake da iko yă buɗe littafin nan da hatimansa bakwai.”

6 Sai na ga wani Ɗan Rago yana a tsaye a tsakiyar kursiyin, kewaye da shi kuma ga rayayyun halittan nan huɗu da dattawan, Ɗan Ragon kuwa kamar yankakke ne, yana da ƙaho bakwai da ido bakwai, waɗanda suke Ruhohin Allah guda bakwai, da aka aika a duniya duka.

7 Sai ya je ya ɗauki littafin nan daga hannun dama na wanda yake a zaune a kan kursiyin.

8 Da ya ɗauki littafin, rayayyun halittan nan guda huɗu, da dattawan nan ashirin da huɗu, suka fāɗi gaban Ɗan Ragon, kowannensu yana riƙe da molo, da tasar zinariya a cike da turare, waɗanda suke addu’o’in tsarkaka.

9 Suna raira sabuwar waƙa, suna cewa,

“Macancanci ne kai ka ɗauki littafin nan, ka ɓamɓare hatimansa,

Domin dā an kashe ka, ka kuma fanso wa Allah mutane ta jininka

Daga kowace kabila, da kowane harshe, da kowace jama’a, da kowace al’umma,

10 Ka mai da su firistoci mallakar Allahnmu, za su kuwa mallaki duniya.”

11 Sa’an nan na duba, sai na ji muryar mala’iku masu yawa, a kewaye da kursiyin, da rayayyun halittan nan, da kuma dattawan nan, yawansu zambar dubu har dubun dubbai,

12 suna cewa da murya mai ƙarfi, “Macancanci ne Ɗan Ragon nan da aka yanka yă sami iko, da wadata, da hikima, da ƙarfi, da girma, da ɗaukaka, da yabo!”

13 Sai na ji kowace halittar da take a Sama, da ƙasa, da ƙarƙashin ƙasa, da bisa teku, da kuma dukkan abin da yake cikinsu, suna cewa, “Yabo, da girma, da ɗaukaka, da mulki sun tabbata ga wanda yake a zaune a kan kursiyin, da Ɗan Ragon nan, har abada abadin!”

14 Sai rayayyun halittan nan huɗu suka ce, “Amin! Amin!” Dattawan nan kuma suka fāɗi suka yi sujada.

Categories
W. YAH

W. YAH 6

Hatiman

1 To, ina gani sa’ad da Ɗan Ragon nan ya ɓamɓare ɗaya daga cikin hatiman nan bakwai, na ji ɗaya daga cikin rayayyun halittan nan huɗu ta yi magana kamar aradu ta ce, “Zo.”

2 Da na duba, ga farin doki, mahayinsa kuma yana da baka, aka ba shi kambi, ya kuwa fita yana mai nasara, domin ya ƙara cin nasara.

3 Da ya ɓamɓare hatimi na biyu, na ji rayayyiyar halittar nan ta biyu ta ce, “Zo.”

4 Sai wani jan doki ya fito, aka kuma ba mahayinsa izini yă ɗauke salama daga duniya, don mutane su kashe juna, aka kuma ba shi babban takobi.

5 Da ya ɓamɓare hatimi na uku, na ji rayayyiyar halittar nan ta uku ta ce, “Zo.” Da na duba, ga baƙin doki, mahayinsa kuwa da mizani a hannunsa.

6 Sai na ji kamar wata murya a tsakiyar rayayyun halittar nan huɗu tana cewa, “Mudun alkama dinari guda, mudu uku na sha’ir dinari guda, sai dai kada ka ɓāta mai da kuma ruwan inabi!”

7 Da ya ɓamɓare hatimi na huɗu, na ji muryar rayayyiyar halittan nan ta huɗu ta ce, “Zo.”

8 Da na duba, ga doki kili, sunan mahayinsa kuwa Mutuwa, Hades kuma tana biye da shi. Sai aka ba su iko a kan rubu’in duniya, su yi kisa da takobi, da yunwa, da annoba, da kuma namomin jeji na duniya.

9 Da ya ɓamɓare hatimi na biyar, na ga rayukan waɗanda aka kashe saboda Maganar Allah, da shaidar da suka yi a ƙarƙashin bagadin ƙona turare.

10 Sai suka ta da murya da ƙarfi suka ce, “Ya Ubangiji Mamallaki, Mai Tsarki, Mai Gaskiya, sai yaushe ne za ka yi hukunci, ka ɗaukar mana fansar jininmu a gun mazaunan duniya?”

11 Sai aka ba kowannensu farar riga, aka ce musu, su dai huta kaɗan, har a cika adadin abokan bautarsu, wato, ‘yan’uwansu, waɗanda za a kashe, kamar yadda su ma aka kashe su.

12 Da ya ɓamɓare hatimi na shida, na duba, sai kuwa aka yi wata babbar rawar ƙasa, rana ta koma baƙa kamar gwado na gashi, gudan wata ya zama kamar jini,

13 taurari kuma suka faɗa a ƙasa kamar yadda ɓaure yake zubar da ɗanyun ‘ya’yansa, in ƙasaitacciyar iska ta kaɗa shi,

14 sararin sama ya dāre ya naɗe kamar tabarma, sai aka kawar da kowane dutse, da kowane tsibiri daga mazauninsa.

15 Sai sarakunan duniya, da manyan mutane, da sarakunan yaƙi, da ma’arzuta, da ƙarfafa, da kuma kowane bawa da ɗa, suka ɓuya a kogwanni, da kuma a cikin duwatsu,

16 suna ce wa duwatsun, “Ku faɗo a kanmu, ku ɓoye mu daga idon wanda yake a zaune a kan kursiyin, da kuma fushin Ɗan Ragon nan,

17 don babbar ranar fushinsu ta zo, wa kuwa zai iya jure mata?”