Categories
W. YAH

W. YAH 7

Adadin Waɗanda aka Buga wa Hatimin, 144,400 na Isra’ila

1 Bayan wannan na ga mala’iku huɗu, a tsaye a kusurwa huɗu ta duniya, suna tsare da iskokin nan huɗu na duniya, don kada wata iska ta busa a kan ƙasa, ko a kan teku, ko a kan wani itace.

2 Sai na ga wani mala’ika yana hawa daga mafitar rana, riƙe da hatimin Allah Rayayye. Sai ya yi wa mala’ikun nan huɗu magana da murya mai ƙarfi, waɗanda aka bai wa ikon azabtar da ƙasa da teku,

3 yana cewa, “Kada ku azabtar da ƙasa, ko teku, ko itatuwa, sai mun buga wa bayin Allahnmu hatimi a goshinsu tukuna.”

4 Sai na ji adadin waɗanda aka buga wa hatimin, dubu ɗari da arba’in da huɗu ne, daga kowace kabilar Isra’ila,

5 wato, an yi wa dubu goma sha biyu hatimi daga kabilar Yahuza, dubu goma sha biyu daga kabilar Ra’ubainu, dubu goma sha biyu daga kabilar Gad,

6 dubu goma sha biyu daga kabilar Ashiru, dubu goma sha biyu daga kabilar Naftali, dubu goma sha biyu daga kabilar Manassa,

7 dubu goma sha biyu daga kabilar Saminu, dubu goma sha biyu daga kabilar Lawi, dubu goma sha biyu daga kabilar Issaka,

8 dubu goma sha biyu daga kabilar Zabaluna, dubu goma sha biyu daga kabilar Yusufu, dubu goma sha biyu kuma daga kabilar Biliyaminu.

Ƙasaitaccen Taro daga Kowace Al’umma

9 Bayan wannan na duba, ga wani ƙasaitaccen taro, wanda ya fi gaban ƙirge, daga kowace al’umma, da kabila, da jama’a, da harshe, suna a tsaitsaye a gaban kursiyin, a gaban Ɗan Ragon kuma, a saye da fararen riguna, da gazarin dabino a hannunsu,

10 suna ta da murya da ƙarfi suna cewa, “Yin ceto ya tabbata ga Allahnmu wanda yake a zaune a kan kursiyin, da kuma Ɗan Rago!”

11 Dukan mala’iku kuwa suna tsaitsaye a kewaye da kursiyin, da dattawan nan, da kuma rayayyun halittan nan guda huɗu, suka fāɗi a gaban kursiyin suka yi wa Allah sujada,

12 suna cewa, “Hakika! Yabo, da ɗaukaka, da hikima, da godiya, da girma, da iko, da ƙarfi su tabbata ga Allahnmu har abada abadin! Amin! Amin!”

13 Sai ɗaya daga cikin dattawan nan ya yi mini magana, ya ce, “Su wane ne waɗannan da suke a saye da fararen riguna, daga ina kuma suke?”

14 Sai na ce masa, “Ya shugaba, ai, ka sani.” Sai ya ce mini, “Su ne waɗanda suka fito daga matsananciyar wahala, sun wanke rigunansu, suka mai da su farare da jinin Ɗan Ragon nan.

15 Saboda haka ne suke a gaban kursiyin Allah, suna bauta masa dare da rana a Haikalinsa. Na zaune a kan kursiyin nan kuwa, zai kare su da Zatinsa,

16 ba za su ƙara jin yunwa ba, ba kuma za su ƙara jin ƙishirwa ba, ba za su ƙara jin zafin rana ko ƙuna ba sam,

17 domin Ɗan Ragon nan da yake a tsakiyar kursiyin, shi zai zama makiyayinsu, zai kuwa kai su maɓuɓɓugar ruwan rai. Allah kuma zai share musu dukan hawaye.”

Categories
W. YAH

W. YAH 8

Hatimi na Bakwai da Tasar Zinariya

1 Sa’ad da Ɗan Ragon ya ɓamɓare hatimi na bakwai, aka yi shiru a Sama kamar na rabin sa’a.

2 Sa’an nan na ga mala’ikun nan bakwai da suke a tsaye a gaban Allah, an ba su ƙaho bakwai.

3 Ga kuma wani mala’ika ya zo ya tsaya a gaban bagadin ƙona turare, riƙe da tasar zinariya ta turaren ƙonawa. Sai aka ba shi turare mai yawa, domin ya haɗa da addu’o’in tsarkaka duka a kan bagadin ƙona turare na zinariya a gaban kursiyin.

4 Sai hayaƙin turaren ya tashi daga hannun mala’ikan tare da addu’o’in tsarkaka, ya isa a gaban Allah.

5 Sai mala’ikan ya ɗauki tasar nan ta turaren ƙonawa, ya cika ta da wuta daga bagadin ƙona turare, ya watsa a kan duniya, sai aka yi ta aradu, da ƙararraki masu tsanani, da walƙiya, da kuma rawar ƙasa.

Ƙahonin

6 Sa’an nan mala’ikun nan bakwai masu ƙaho bakwai ɗin nan, suka yi shirin busa su.

7 Mala’ikan farko ya busa ƙahonsa, sai ga ƙanƙara da wuta, gauraye da jini. Aka zuba su a duniya, sai sulusin duniya ya ƙone, sulusin itatuwa suka ƙone, dukkan ɗanyar ciyawa kuma ta ƙone.

8 Mala’ika na biyu ya busa ƙahonsa, sai aka jefa wani abu a teku kamar babban dutse mai tsawo, mai cin wuta. Sulusin teku ya zama jini,

9 sulusin halittar da suke a ruwa suka mutu, sulusin jiragen ruwa kuma suka hallaka.

10 Mala’ika na uku ya busa ƙahonsa, sai wani babban tauraro ya faɗo daga sama, yana cin wuta kamar cukwima. Ya faɗa a sulusin koguna da maɓuɓɓugan ruwa.

11 Sunan tauraron kuwa Ɗaci. Sulusin ruwa ya zama mai ɗaci, sai mutane da yawa suka mutu saboda shan ruwan, don ɗacinsa.

12 Mala’ika na huɗu ya busa ƙahonsa, sai aka bugi sulusin rana, da sulusin wata, da kuma sulusin taurari, har sulusin haskensu ya zama duhu, wato ba haske a sulusin yini, haka kuma a sulusin dare.

13 Sa’an nan da na duba, na ji wani juhurma mai jewa a tsakiyar sararin sama, yana kuka da ƙarfi, yana cewa, “Kaito! Kaito! Kaitonku, ku mazaunan duniya, in an yi busan sauran ƙahonin da mala’ikun nan uku suke shirin busawa!”

Categories
W. YAH

W. YAH 9

1 Mala’ika na biyar ya busa ƙahonsa, sai na ga wani tauraron da ya faɗa a kan duniya daga sama, aka ba shi mabuɗin ramin mahallaka.

2 Ya kuwa buɗe ramin mahallakar, sai wani hayaƙi kamar na babbar matoya ya taso, har hayaƙin ramin nan ya duhunta rana da sararin sama.

3 Fāri suka fito zuwa cikin duniya daga cikin hayaƙin nan, aka ba su ikon harbi, irin na kunamin duniya.

4 Aka kuwa hana su cutar ciyayin duniya, ko tsiro, ko kowane itace, sai dai mutanen da ba su da hatimin Allah a goshinsu.

5 Aka kuwa yardar musu su yi musu azaba har wata biyar, amma kada su kashe su, azabarsu kuwa, kamar ta kunama take, in ta harbi mutum.

6 A waɗannan kwanaki kuwa mutane za su nemi mutuwa, amma ba za su same ta ba, za su ƙagauta su mutu, mutuwa kuwa sai ta guje musu.

7 Kamannin fārin nan kuwa kamar dawakai ne da suka ja dāgar yaƙi, a kansu kuma da wani abu kamar kambin zinariya, fuskarsu kuwa kamar ta mutum,

8 gashinsu kamar na mace, haƙorinsu kuma kamar na zaki.

9 Suna saye da sulkuna kamar na ƙarfe, dirin fikafikansu kuwa kamar dirin kekunan doki masu yawa ne suna rugawa fagyan yaƙi,

10 wutsiyarsu kamar ta kunama, ga kuma ƙari, ikonsu yana ji wa mutane ciwo har wata biyar kuwa a wutsiyarsu yake.

11 Sarkinsu kuwa da yake iko da su shi ne mala’ikan mahallaka, sunansa da Yahudanci Abadan, da Helenanci kuwa Afoliyon.

12 Bala’in farko ya wuce, ga kuma bala’i na biyu a nan a tafe.

13 Sa’an nan mala’ika na shida ya busa ƙahonsa, sai na ji wata murya daga zankayen nan huɗu na bagadin ƙona turare na zinariya a gaban Allah,

14 tana ce wa mala’ikan nan na shida mai ƙaho, “Ka saki mala’iku huɗun nan da suke a ɗaure a gabar babban kogin nan Yufiretis.”

15 Sai aka saki mala’ikun nan huɗu, waɗanda aka tanada saboda wannan sa’a, da wannan rana, da wannan wata, da wannan shekara, su kashe sulusin ‘yan adam.

16 Yawan rundunonin sojan doki kuwa, na ji adadinsu zambar dubu metan ne.

17 Ga kuwa yadda na ga dawakan a wahayin da aka yi mini, mahayansu suna saye da sulkuna, launinsu ja kamar wuta, da shuɗi, da kuma rawaya kamar farar wuta, kawunan dawakan kuma kamar na zaki, wuta kuma da hayaƙi da farar wuta suna fita daga bakinsu.

18 Da waɗannan bala’i uku aka kashe sulusin ‘yan adam, wato, da wuta, da hayaƙi, da farar wuta da suke fita daga bakinsu.

19 Domin ikon dawakan nan na a bakinsu da a wutsiyarsu, wutsiyoyinsu kamar macizai suke, har da kawuna, da su ne suke azabtarwa.

20 Sauran ‘yan adam waɗanda bala’in nan bai kashe ba kuwa, ba su tuba sun rabu da abubuwan da suka yi da hannunsu ba, ba su kuma daina yin sujada ga aljannu, da gumakan zinariya, da na azurfa, da na tagulla, da na dutse, da na itace ba, waɗanda ba su iya gani, ko ji, ko tafiya,

21 ba su kuma tuba da kashe-kashenkai da suka yi ba, ko sihirinsu, ko fasikancinsu, ko kuma sace-sacensu.

Categories
W. YAH

W. YAH 10

Mala’ika da Ƙaramin Littafi

1 Sa’an nan na ga wani ƙaƙƙarfan mala’ika yana saukowa daga sama, lulluɓe da gajimare, da bakan gizo a bisa kansa, fuskarsa kamar rana, ƙafafunsa kuma kamar ginshiƙan wuta.

2 Ga wani ƙaramin littafi a buɗe a hannunsa. Sai ya tsai da ƙafarsa ta dama a kan teku, ƙafarsa ta hagu kuwa a kan ƙasa,

3 ya yi kira da murya mai ƙarfi, kamar zaki yana ruri. Da ya yi kiran, sai aradun nan bakwai suka yi tsawa.

4 Sa’ad da kuwa aradun nan bakwai suka yi tsawa, kamar zan rubuta, sai na ji wata murya daga sama tana cewa, “Rufe abin da aradun nan bakwai suka faɗa, kada ka rubuta.”

5 Sai mala’ikan nan da na gani a tsaye a teku da ƙasa ya ɗaga hannunsa na dama sama,

6 ya rantse da wanda yake a raye har abada abadin, wanda ya halicci sama da abin da take a cikinta, da ƙasa da abin da take a cikinta, da kuma teku da abin da take a cikinta, cewa ba sauran wani jinkiri kuma,

7 sai dai a lokacin busa ƙahon da mala’ika na bakwai zai busa ne, za a cika asirtaccen nufin nan na Allah, bisa ga bisharar da ya yi wa bayinsa annabawa.

8 Sa’an nan muryar nan da na ji daga sama ta sāke yi mini magana, ta ce, “Je ka, ka ɗauki littafin nan da yake a buɗe a hannun mala’ikan da yake a tsaye a bisa teku da ƙasa.”

9 Sai na je wurin mala’ikan, na ce masa, ya ba ni ƙaramin littafin. Sai ya ce mini, “Karɓi ka cinye, zai yi maka ɗaci a ciki, amma a baka kamar zuma yake don zaƙi.”

10 Sai na karɓi ƙaramin littafin daga hannun mala’ikan, na cinye. Sai ya yi zaƙi kamar zuma a bakina, amma da na cinye, cikina ya ɗau ɗaci.

11 Sai kuma aka ce mini, “Lalle ne ka sāke yin annabci a game da jama’a iri iri, da al’ummai, da harsuna, da kuma sarakuna da yawa.”

Categories
W. YAH

W. YAH 11

Shaidu Biyu Ɗin

1 Sa’an nan aka ba ni wata gora kamar sanda, aka kuma ce mini, “Tashi ka auna Haikalin Allah, da bagadin hadaya, da kuma masu sujada a ciki,

2 amma kada ka auna harabar Haikalin, ka ƙyale ta, domin an ba da ita ga al’ummai, za su tattake tsattsarkan birnin nan har wata arba’in da biyu.

3 Zan kuma bai wa mashaidana biyu iko su yi annabci kwana dubu da metan da sittin, suna a saye da tsummoki.”

4 Waɗannan su ne itatuwan zaitun ɗin nan guda biyu, da fitilun nan biyu da suke a tsaye a gaban Ubangijin duniya.

5 In kuwa wani yana da niyyar cutarsu, sai wuta ta huro daga bakinsu, ta lashe maƙiyansu, duk mai niyyar cutarsu kuwa, ta haka ne lalle za a kashe shi.

6 Suna da ikon hana ruwan sama, don kada a yi ruwa a duk kwanakin da suke yin annabci, suna kuma da iko a kan ruwa, su mai da shi jini, su kuma ɗora wa duniya kowane irin bala’i, a duk lokacin da suke so.

7 Bayan da suka ƙare shaidarsu, sai wata dabba mai fitowa daga mahallaka tă yaƙe su, ta cinye su, ta kashe su,

8 a kuma bar gawawwakinsu a kan hanyar babban birnin nan da ake kira Saduma da Masar ga ma’ana ta ruhu, a inda aka gicciye Ubangijinsu.

9 Mutanen dukkan jama’a, da kabila, da harshe, da al’umma za su riƙa kallon gawawwakinsu, har kwana uku da rabi, su kuwa ƙi yarda a binne su.

10 Mazaunan duniya kuma, sai su yi ta alwashi a kansu, suna ta shagali, suna a’aika wa juna da kyauta, domin annabawan nan biyu dā sun azabtar da mazaunan duniya.

11 Amma bayan kwana uku da rabin nan, sai numfashin rai daga wurin Allah ya shiga a cikinsu, suka tashi a tsaye, matsanancin tsoro kuwa ya rufe waɗanda suka gan su.

12 Sai suka ji wata murya mai ƙara daga sama tana ce musu, “Ku hawo nan!” Sai suka tafi sama a cikin gajimare, maƙiyansu suna gani.

13 A nan tāke sai aka yi wata babbar rawar ƙasa, sai ushirin garin ya zube, mutum dubu bakwai aka kashe a rawar ƙasar, sauran kuwa suka tsorata, suka ɗaukaka Allah Mai Sama.

14 Bala’i na biyu ya wuce, ga kuma bala’i na uku yana zuwa nan da nan.

Ƙaho na Bakwai

15 Sa’an nan mala’ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji waɗansu muryoyi masu ƙara a Sama, suna cewa, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Almasihunsa, shi kuma zai yi mulki har abada abadin.”

16 Sai dattawan nan ashirin da huɗu da suke a zaune a kan kursiyansu a gaban Allah suka fādi suka yi wa Allah sujada,

17 Suna cewa,

“Mun gode maka, ya Ubangiji Allah, Maɗaukaki,

Wanda yake a yanzu, shi ne kuma a dā,

Saboda ka ɗauki ikonka mai girma, kana mulki.

18 Al’ummai sun husata, fushinka kuwa ya auko,

Lokaci ya yi da za a yi wa matuttu shari’a,

A kuma yi wa bayinka, annabawa da tsarkaka sakamako,

Da masu jin tsoron sunanka, yaro da babba,

A kuma hallaka masu hallaka duniya.”

19 Sa’an nan aka buɗe Haikalin nan na Allah da yake a Sama, aka kuma ga akwatin alkawarinsa a Haikalinsa. Sai aka yi ta walƙiya da kururuwa, da aradu, da rawar ƙasa, da ƙanƙara manya manya.

Categories
W. YAH

W. YAH 12

Wata Mace da Macijin

1 Aka kuma ga wata babbar alama a sama, wata mace tana a lulluɓe da rana, tana a tsaye a kan wata, da kuma kambi mai taurari goma sha biyu a kanta.

2 Tana da ciki, sai kuma ta yi ta ƙara ta ƙagauta domin ta haihu, saboda azabar naƙuda.

3 Sai kuma aka ga wata alama a sama, ga wani ƙaton jan maciji mai kawuna bakwai, da ƙahoni goma, da kambi bakwai a kawunansa.

4 Wutsiyarsa ta sharo sulusin taurari, ta zuba su a ƙasa. Sai macijin ya tsaya a gaban matar nan mai naƙuda, don ya lanƙwame ɗan nata in ta haife shi.

5 Ta kuwa haifi ɗa namiji, wanda zai mallaki dukkan al’ummai da sandar ƙarfe, amma aka fyauce ɗan nata, aka kai shi zuwa wurin Allah da kursiyinsa.

6 Matar kuwa, sai ta gudu ta shiga jeji, a inda Allah ya shirya mata wurin da za a cishe ta har kwana dubu da metan da sittin.

7 Sai yaƙi ya tashi a sama, Mika’ilu da mala’ikunsa suna yaƙi da macijin nan, macijin kuma da mala’ikunsa suka yi ta yaƙi,

8 amma aka cinye su, har suka rasa wuri a sama sam.

9 Sai aka jefa ƙaton macijin nan a ƙasa, wato macijin nan na tun dā dā, wanda ake kira Ibilis da Shaiɗan, mayaudarin dukkan duniya, aka jefa shi a duniya, mala’ikunsa ma aka jefa su tare da shi.

10 Sai na ji wata murya mai ƙara a Sama tana cewa, “A yanzu fa, ceto, da ƙarfi, da mulki na Allahnmu, da kuma ikon Almasihunsa sun bayyana, don an jefa mai ƙarar ‘yan’uwanmu a ƙasa, shi da yake ƙararsu dare da rana a gun Allahnmu.

11 Sun kuwa yi nasara da shi albarkacin jinin Ɗan Ragon nan, da kuma albarkacin maganar da suka shaida, domin ba su yi tattalin ransu ba, har abin ya kai su ga kisa.

12 Saboda haka, sai ku yi farin ciki, ya ku sammai, da ku mazauna a ciki. Amma kaitonku, ke ƙasa, da kai teku, don Ibilis ya sauko gare ku da matsanancin fushi, don ya san lokacinsa ya ƙure.”

13 Da macijin nan ya ga an jefa shi a ƙasa, ya fafari matar nan da ta haifi ɗa namiji, da tsanani.

14 Amma aka ba matar fikafikan nan biyu na babban juhurman nan, don ta tashi ta guje wa macijin nan, ta shiga jeji, ta je wurin da za a cishe ta a lokaci ɗaya, da lokatai, da rabin lokaci.

15 Sai macijin ya kwarara ruwa daga bakinsa kamar kogi daga bayan matar, don ya share ta da ambaliya.

16 Amma ƙasa ta taimaki matar, ita ƙasar ta buɗe bakinta ta shanye kogin da macijin nan ya kwararo daga bakinsa.

17 Macijin kuwa ya yi fushi da matar, ya tafi ya ɗaura yaƙi da sauran zuriyarta, wato, waɗanda suke kiyaye umarnin Allah, suke kuma shaidar Yesu. Sai ya tsaya a kan yashin teku.

Categories
W. YAH

W. YAH 13

Dabbobi Biyu Ɗin

1 Na kuma ga wata dabba tana fitowa daga cikin teku, mai ƙaho goma, da kawuna bakwai, da kambi goma a kan ƙahoninta, da kuma wani suna na saɓo a kawunanta.

2 Dabbar da na gani kuwa kamar damisa take, ƙafafunta kamar na beyar, bakinta kuma kamar na zaki. Macijin kuwa ya ba ta ƙarfinsa, da kursiyinsa, da ikonsa mai girma.

3 Ɗaya daga cikin kawunanta, an yi masa rauni kamar na ajali, amma rauninsa mai kamar na ajalin nan ya warke. Sai dabbar ta ɗauke wa duk duniya hankali, suna mamaki,

4 har suka yi wa macijin nan sujada, don shi ne ya bai wa dabbar ikonsa, suka kuma yi wa dabbar sujada, suna cewa, “Wa ya yi kama da dabbar nan? Wa kuma zai iya yaƙi da ita?”

5 An kuwa ba dabbar nan baki, tana fariya da maganganun saɓo, aka kuma yardar mata ta zartar da iko, har wata arba’in da biyu.

6 Sai ta buɗe bakinta don ta saɓi Allah, ta yi ta saɓon sunansa, da wurin zamansa, da waɗanda suke a zaune a Sama.

7 Aka kuma yardar mata ta yaƙi tsarkaka, ta cinye su. Aka kuma ba ta iko a kan kowace kabila, da jama’a, da harshe, da al’umma.

8 Duk mazaunan duniya kuma, za su yi mata sujada, wato, duk wanda, tun farkon duniya, ba a rubuta sunansa a Littafin Rai na Ɗan Ragon nan da yake Yankakke ba.

9 Duk mai kunnen ji, yă ji.

10 Kowa aka ƙaddara wa bauta, sai ya je aikin bautar.

Kowa kuwa ya yi kisa da takobi, to, kuwa da takobi za a kashe shi lalle.

Wannan yana nuna jimiri da bangaskiya na tsarkaka.

11 Sa’an nan na ga wata dabba na fitowa daga cikin ƙasa. Tana da ƙaho biyu kamar na ɗan rago, maganarta kuwa kamar ta macijin nan.

12 Tana zartar da duk ikon dabbar nan ta farko, a kan idonta, tana kuma sa duniya da duk mazauna a cikinta, su yi wa dabbar nan ta farko sujada, wadda aka warkar mata da rauninta mai kamar na ajali.

13 Tana yin manyan abubuwan al’ajabi, har ma tana sa wuta ta zuba a ƙasa daga sama, a gaban idon mutane.

14 Tana kuma yaudarar mazaunan duniya, da abubuwan al’ajabin nan da aka yardar mata ta yi a gaban dabbar nan, tana umartarsu, su yi wata siffa saboda dabbar nan wadda aka yi wa rauni da takobi, ta kuwa rayu.

15 An kuma yardar mata ta busa wa siffar dabbar nan rai, har siffar dabbar nan ma ta iya yin magana, ta kuma sa a kashe waɗanda suka ƙi yi wa siffar dabbar nan sujada.

16 Har wa yau, sai ta sa a yi wa kowa alama a hannun dama, ko a goshi, manya da yara duka, mawadata da matalauta, ɗa da bawa,

17 har ba mai iya saye ko sayarwa sai ko yana da alamar nan, wato, sunan dabbar nan, ko kuwa lambar sunanta.

18 Wannan abu sai a game da hikima. Duk mai basira ya ƙididdige lambar dabbar nan, don lamba ce ta wani mutum, lambar kuwa ɗari shida ce da sittin da shida.

Categories
W. YAH

W. YAH 14

Waƙar 144,000 Ɗin

1 Sa’an nan na duba, sai ga Ɗan Ragon nan a tsaye a kan Dutsen Sihiyona, akwai kuma mutum dubu ɗari da dubu arba’in da huɗu tare da shi, waɗanda aka rubuta sunansa, da sunan Ubansa, a goshinsu.

2 Sai na ji wata murya daga Sama kamar ƙugin ruwa mai gudu, kamar aradu mai ƙara, muryar da na ji kuwa, kamar ta masu molo ce na kiɗan molo.

3 Suna raira wata sabuwar waƙa a gaban kursiyin, a gaban rayayyun halittan nan huɗu, da kuma a gaban dattawan nan. Ba mai iya koyon waƙar nan, sai mutum dubu ɗari da dubu arba’in da huɗu ɗin nan, waɗanda aka fanso daga duniya.

4 Waɗannan su ne waɗanda ba su taɓa ƙazantuwa da fasikanci ba, domin su tsarkaka ne. Su ne kuma suke bin Ɗan Ragon a duk inda ya je. Su ne kuma aka fanso daga cikin mutane a kan su ne nunan fari na Allah, da na Ɗan Ragon nan kuma,

5 ba wata ƙarya a bakinsu, domin su marasa aibu ne.

Sanarwar Mala’iku Uku Ɗin

6 Sa’an nan na ga wani mala’ika yana kaɗawa a tsakiyar sararin sama, yana tafe da madawwamiyar bishara, domin ya sanar da ita ga mazaunan duniya, wato, ga kowace al’umma, da kabila, da harshe, da jama’a.

7 Sai ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Ku ji tsoron Allah, ku ɗaukaka shi, domin lokacinsa na yin hukunci ya yi. Ku yi masa sujada, shi da ya halicci sama, da ƙasa, da teku, da kuma maɓuɓɓugan ruwa.”

8 Sai kuma mala’ika na biyu ya biyo, yana cewa, “Ta fāɗi! Babila mai girma ta fāɗi! Ita da ta zuga dukkan al’ummai su yi tsananin jarabar yin fasikanci da ita.”

9 Sai kuma mala’ika na uku ya biyo, yana ɗaga murya da ƙarfi, yana cewa, “Duk mai yi wa dabbar nan da siffarta sujada, wanda kuma ya yarda a yi masa alama a goshinsa, ko a hannunsa,

10 zai ci karo da azabar Allah tsantsa ta tsananin fushinsa, za a kuwa azabta shi da wuta, da duwatsun wuta, a gaban mala’iku tsarkaka, da kuma Ɗan Ragon.

11 Hayaƙin azabar nan tasu ya dinga tashi har abada abadin, ba su da wani rangwame dare da rana, wato, waɗannan masu yi wa dabbar nan da siffarta sujada, da kuma duk wanda ya yarda aka yi masa alamar sunanta.”

12 Wannan yana nuna jimirin tsarkaka, masu kiyaye umarnin Allah da kuma bangaskiya ga Yesu.

13 Sai kuma na ji wata murya daga Sama tana cewa, “Rubuta wannan. Albarka tā tabbata ga matattu, wato, waɗanda za su mutu a nan gaba a kan su na Ubangiji ne.” Ruhu ya ce, “Hakika, masu albarka ne, domin su huta daga wahalarsu, gama aikinsu yana a biye da su!”

Girbe Duniya

14 Sa’an nan na duba, sai ga wani farin gajimare, da wani kamar Ɗan Mutum a zaune a kan gajimaren, da kambin zinariya a kansa, da kakkaifan lauje a hannunsa.

15 Sai mala’ika ya fito daga Haikalin, yana magana da murya mai ƙarfi da wanda yake a zaune a kan gajimaren, yana cewa, “Ka sa laujenka ka yanke, don lokacin yanka ya yi, amfanin duniya ya nuna sarai.”

16 Sai wanda yake a zaune a kan gajimaren ya wurga laujensa zuwa duniya, aka girbe amfanin duniya.

17 Wani mala’ika kuma ya fito daga Haikali a Sama, shi ma kuwa yana da kakkaifan lauje.

18 Sai kuma wani mala’ika ya fito daga bagadin ƙona turare, wato, mala’ikan da yake da iko da wutar, ya yi magana da murya mai ƙarfi da wannan mai kakkaifan lauje, ya ce, “Ka sa laujenka ka yanke nonnan inabin zuwa duniya, don inabin ya nuna.”

19 Sai mala’ikan ya wurga laujensa duniya, ya tattara inabin duniya, ya zuba a cikin babbar mamatsar inabi ta fushin Allah.

20 Aka tattake mamatsar inabin a bayan gari, jini kuma ya yi ta gudana daga mamatsar inabin, ya kai kamar tsawon linzami a bakin doki, har mil metan.

Categories
W. YAH

W. YAH 15

Mala’iku Masu Bala’i Bakwai

1 Na kuma ga wata alama a Sama, mai girma, mai banmamaki, mala’iku bakwai masu bala’i bakwai, waɗanda suke bala’in ƙarshe, don su ne iyakacin fushin Allah.

2 Sai na ga wani abu kamar bahar na gilas, gauraye da wuta, na kuma ga waɗanda suka yi nasara da dabbar nan, da siffarta, da kuma lambar sunanta, a tsaitsaye a bakin bahar na gilas, da molayen yabon Allah a hannunsu.

3 Suna raira waƙar da Musa bawan Allah ya yi, da kuma wadda ake yi wa Ɗan Ragon nan, suna cewa,

“Ayyukanka manya ne, masu banmamaki,

Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki!

Hanyoyinka na adalci ne, na gaskiya ne kuma,

Ya Sarkin al’ummai.

4 Wane ne ba zai ji tsoronka ba, ya Ubangiji,

Ya kuma ɗaukaka sunanka?

Domin kai kaɗai ne Mai Tsarki.

Dukkan al’ummai za su zo su yi maka sujada,

Don ayyukanka na adalci sun bayyana.”

5 Bayan wannan na duba, ga Wuri Mafi Tsarki a buɗe a Haikali a Sama.

6 Sai mala’ika bakwai ɗin nan masu bala’i bakwai suka fito daga Haikalin, saye da tufafin lilin mai tsabta, mai ɗaukar iko, da ɗamarar zinariya a ƙirjinsu.

7 Sai ɗaya daga cikin rayayyun halittan nan guda huɗu, ta ba mala’ikun nan bakwai tasoshi bakwai na zinariya, a cike da fushin Allah, shi da yake a raye har abada abadin.

8 Sai Haikalin ya cika da hayaƙi mai fitowa daga ɗaukakar Allah da ikonsa. Ba mai iya shiga Haikalin nan, sai bayan bala’i bakwai na mala’ikun nan bakwai sun ƙare.

Categories
W. YAH

W. YAH 16

Tasoshin Azaba

1 Sai na ji wata murya mai ƙara daga Haikalin, tana ce wa mala’ikun nan bakwai, “Ku je ku juye tasoshin nan bakwai na fushin Allah a kan duniya.”

2 Daga nan mala’ikan farko ya je ya juye abin da yake a tasarsa a kan duniya, sai kuwa waɗansu mugayen miyaku masu azabtarwa suka fito a jikin mutanen da suke da alamar dabbar nan, suke kuma yi wa siffarta sujada.

3 Mala’ika na biyu ya juye abin da yake a tasarsa a teku, ya zama kamar jinin mataccen mutum, kowane abu mai rai na cikin teku kuma ya mutu.

4 Mala’ika na uku ya juye abin da yake a tasarsa a koguna da maɓuɓɓugan ruwa, sai suka zama jini.

5 Na kuwa ji mala’ikan ruwa yana cewa,

“Kai mai adalci ne a hukuncin nan naka,

Ya kai Mai Tsarki, wanda kake a yanzu, kake kuma a dā.

6 Don mutane sun zub da jinin tsarkaka da na annabawa,

Ga shi kuwa, ka ba su jini su sha.

Sakamakonsu ke nan!”

7 Sai na ji wata murya a bagadin ƙona turare, tana cewa,

“Hakika, ya Ubangiji Allah Maɗaukaki,

Hukuncinka daidai yake, na adalci ne kuma!”

8 Sai mala’ika na huɗu ya juye abin da yake a tasarsa a rana, sai aka yardar mata ta ƙona mutane da wuta.

9 Sai matsanancin zafi ya ƙona mutane, har suka zagi sunan Allah, shi da yake da ikon waɗannan bala’i, ba su kuwa tuba sun ɗaukaka shi ba.

10 Mala’ika na biyar ya juye abin da yake a tasarsa a kursiyin dabbar nan, sai mulkinta ya zama duhu, har mutane suka ciji leɓunansu don azaba,

11 suka zagi Allah Mai Sama saboda azabarsu da miyakunsu, ba su kuma tuba da ayyukansu ba.

12 Mala’ika na shida ya juye abin da yake a tasarsa a babban kogin nan Yufiretis, sai ruwansa ya ƙafe, don a shirya wa sarakuna daga gabas tafarki.

13 Na kuma ga baƙaƙen aljannu masu kama da kwaɗi gudu uku, suna fitowa daga bakin macijin nan, da bakin dabbar nan, da kuma bakin annabin nan na ƙarya,

14 su iskoki ne, aljannu masu yin abubuwan al’ajabi, masu zuwa wurin sarakunan duniya duka, don su tara su saboda yaƙi a babbar ranar nan ta Allah Maɗaukaki.

15 (“Ga ni nan a tafe kamar ɓarawo! Albarka tā tabbata ga wanda yake a zaune a faɗake, yana saye da tufafinsa, don kada ya tafi tsirara, a ga tsiraicinsa.”)

16 Sai suka tattara su a wurin da ake kira Armageddon da Yahudanci.

17 Mala’ika na bakwai ya juye abin da yake a tasarsa a sararin sama, sai aka ji wata murya mai ƙara daga Haikali, wato, daga kursiyin, ta ce, “An gama!”

18 Sai aka yi ta walƙiya, da ƙararraki masu tsanani, da aradu, da wata babbar rawar ƙasa irin wadda ba a taɓa yi ba, tun da ɗan adam yake a duniya, gawurtacciyar rawar ƙasa ƙwarai da gaske.

19 Babban birnin nan kuwa ya rabu gida uku, biranen al’ummai kuma suka fāɗi. Sai Allah ya tuna da Babila mai girma, don ya sa ta, ta sha fushinsa mai tsananin gaske.

20 Kowane tsibiri ya ɓace, manyan duwatsu ma ba a ƙara ganinsu ba.

21 Waɗansu manyan ƙanƙara kuma kamar kayan jaki suka faɗo a kan mutane daga sama, har mutane suka zagi Allah, saboda bala’in ƙanƙarar. Bala’in nan da matuƙar bantsoro yake!