Categories
M. SH

M. SH 8

Ƙasar da za ku Mallaka Mai Albarka Ce

1 “Sai ku lura, ku aikata dukan umarnan da na umarce ku da su don ku rayu, ku riɓaɓɓanya, ku shiga ƙasar da Ubangiji ya rantse zai ba kakanninku.

2 Ku tuna yadda Ubangiji Allahnku ya bishe ku shekarun nan arba’in a jeji don ya koya muku tawali’u. Ya jarraba ku don ya san zuciyarku, ko za ku kiyaye umarnansa ko babu.

3 Ya koya muku tawali’u, ya bar ku da yunwa, ya ciyar da ku da manna wadda ba ku sani ba, kakanninku kuma ba su sani ba, domin ya sa ku sani, ba da abinci kaɗai mutum yake rayuwa ba, amma mutum yana rayuwa da kowane irin abin da yake fitowa daga wurin Ubangiji.

4 A shekarun nan arba’in tufafinku ba su yayyage ba, ƙafafunku kuma ba su kumbura ba.

5 Kun san wannan a zuciyarku, wato kamar yadda mutum yakan yi wa ɗansa tarbiyya, haka kuma Ubangiji Allahnku yake yi muku tarbiyya.

6 Saboda wannan sai ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin hanyoyinsa, ku ji tsoronsa.

7 Ubangiji Allahnku zai kai ku ƙasa mai kyau. Ƙasa mai rafuffukan ruwa da maɓuɓɓugai, da idanun ruwa masu ɓuɓɓugowa daga cikin kwari da tudu.

8 Ƙasa mai alkama, da sha’ir, da inabi, da ɓaure, da rumman. Ƙasa ce mai itatuwan zaitun da zuma.

9 Ƙasa ce inda za ku ci abinci a yalwace, ba za ku rasa kome ba. Ƙasa ce wadda tama ce duwatsunta, ana kuma haƙar tagulla a tuddanta.

10 Sa’ad da kuka ci, kuka ƙoshi, sai ku yabi Ubangiji Allahnku saboda kyakkyawar ƙasa mai albarka da ya ba ku.”

Faɗakarwa Kada a Manta da Ubangiji

11 “Ku kula fa, don kada ku manta da Ubangiji Allahnku, ku ƙi kiyaye umarnansa, da farillansa, da dokokinsa waɗanda na umarce ku da su yau.

12 Sa’ad da kuka ci kuka ƙoshi, kuka gina kyawawan gidaje, kuka zauna ciki,

13 garkunanku na shanu da tumaki suka riɓaɓɓanya, azurfarku, da zinariyarku suka ƙaru, sa’ad da dukan abin da kuke da shi ya haɓaka,

14 to, sai ku lura, kada ku ɗaukaka kanku, har ku manta da Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar, wato inda kuka yi bauta.

15 Ubangiji ya bishe ku cikin babban jejin nan mai bantsoro, ƙasa mai macizai masu zafin dafi, da kunamai, da busasshiyar ƙasa wadda ba ta da ruwa. Ubangiji kuwa ya ba ku ruwa daga dutsen ƙanƙara.

16 Ya ciyar da ku da manna a jeji, abin da kakanninku ba su sani ba, domin ya koya muku tawali’u, ya jarraba ku, don ya yi muku alheri daga baya.

17 Kada ku ce a zuciya, ‘Ai, ikona da ƙarfin hannuwana ne suka kawo mini wannan wadata.’

18 Sai ku tuna da Ubangiji Allahnku, gama shi ne ya ba ku ikon samun wadata domin ya cika alkawarin da ya rantse wa kakanninku kamar yadda yake a yau.

19 Idan kun manta da Ubangiji Allahnku, kuka bi gumaka, kuka bauta musu, kuka yi musu sujada, to, yau ina faɗakar da ku, cewa lalle za ku hallaka

20 kamar al’umman da Ubangiji ya hallakar a gabanku. Haka za ku hallaka domin ba ku kasa kunne ga muryar Ubangiji Allahnku ba.”

Categories
M. SH

M. SH 9

Ubangiji zai Hallaka Al’umman Ƙasar Kan’ana

1 “Ku ji, ya Isra’ilawa, yau kuna kan haye Kogin Urdun, don ku kori al’ummai waɗanda suka fi ku yawa, sun kuwa fi ku ƙarfi. Suna da manyan birane masu dogon garu.

2 Mutane ne ƙarfafa, dogaye, zuriyar Anakawa waɗanda kuka riga kuka ji labarinsu. Ai, kun ji akan ce, ‘Wane ne zai iya tsayayya da ‘ya’yan Anak?’

3 Yau za ku sani Ubangiji Allahnku yake muku ja gaba sa’ad da kuke hayewa. Shi wuta ne mai cinyewa, zai hallaka su, ya rinjayar muku su, domin ku kore su, ku hallaka su nan da nan kamar yadda Ubangiji ya alkawarta muku.

4 “Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya kore su daga gabanku, kada ku ce a ranku, ‘Ai, saboda adalcinmu ne Ubangiji ya kawo mu mu mallaki ƙasar nan.’ Gama saboda muguntar al’umman nan ne Ubangiji ya kore su a gabanku.

5 Ba saboda adalcinku, ko kuma gaskiyarku ne ya sa za ku shiga ƙasar, ku mallake ta ba, amma saboda muguntar waɗannan al’ummai ne, Ubangiji Allahnku ya kore su a gabanku domin kuma ya cika maganar da ya rantse wa kakanninku, wato su Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.

6 Sai ku sani fa, ba saboda adalcinku ne Ubangiji Allahnku yake ba ku kyakkyawar ƙasan nan don ku mallake ta ba, gama ku jama’a ce mai taurinkai.”

Tayarwar Isra’ilawa a Horeb

7 “Tuna fa, kada ku manta da yadda kuka sa Ubangiji Allahnku ya yi fushi a jeji. Tun daga ranar da kuka fita daga Masar har kuka iso wannan wuri kuna ta tayar wa Ubangiji.

8 A Horeb kuka tsokani Ubangiji, Ubangiji kuwa ya yi fushi, har yana so ya hallaka ku.

9 Sa’ad da na hau kan dutsen domin in karɓo allunan dutse, wato allunan alkawarin da Ubangiji ya yi da ku, na zauna a kan dutsen dare arba’in da yini arba’in ban ci ba, ban sha ba.

10 Ubangiji kuwa ya ba ni allunan nan biyu na dutse da shi kansa ya rubuta. A kansu aka rubuta maganar da Ubangiji ya yi muku daga bisa dutsen a tsakiyar wuta a ranar taron.

11 Bayan dare arba’in da yini arba’in ɗin, Ubangiji ya ba ni alluna biyu na dutse, wato alluna na alkawarin.

12 “Sa’an nan ya ce mini, ‘Tashi, ka gangara da sauri, gama jama’arka wadda ka fito da ita daga Masar ta aikata mugunta, ta kauce da sauri daga hanyar da na umarce ta ta bi. Ta yi wa kanta gunki na zubi.’

13 “Ubangiji kuma ya ce mini, ‘Na ga mutanen nan suna da taurinkai.

14 Bari in hallaka su, in shafe sunansu daga duniya, sa’an nan in maishe ka wata al’umma wadda ta fi su iko da kuma yawa.’

15 “Sai na juya, na gangaro daga dutsen da allunan nan biyu na alkawari a hannuwana, dutsen kuma na cin wuta.

16 Da na duba, sai na ga kun yi wa Ubangiji Allahnku zunubi, kun yi wa kanku maraƙi na zubi. Kun kauce da sauri daga hanyar da Ubangiji ya umarce ku ku bi.

17 Sai na ɗauki allunan nan biyu, na jefar da su ƙasa da hannuna, na farfashe su a idonku.

18 Sai na fāɗi ƙasa, na kwanta a gaban Ubangiji dare arba’in da yini arba’in, ban ci ba, ban sha ba, kamar yadda na yi a dā, saboda dukan zunubin da kuka aikata, kuka yi abin da yake mugu ga Ubangiji, kuka tsokane shi.

19 Gama na ji tsoron zafin fushin Ubangiji da ya yi da ku, har ya so ya hallaka ku. Amma Ubangiji ya ji addu’ata a wannan lokaci.

20 Ubangiji kuma ya husata da Haruna, har ya so ya kashe shi, amma na yi roƙo dominsa a lokacin.

21 Sa’an nan na ɗauki abin zunubin nan, wato siffar maraƙin da kuka yi, na ƙone, na farfashe, na niƙe shi lilis, ya zama kamar ƙura mai laushi, na zubar da garin a rafi wanda yake gangarowa daga dutsen.

22 “Kun kuma tsokano Ubangiji ya husata a Tabera, da a Masaha, da a Kibrot-hata’awa.

23 Sa’ad da Ubangiji ya aike ku daga Kadesh-barneya, ya ce, ‘Ku hau ku mallaki ƙasar da nake ba ku,’ sai kuka tayar wa umarnin Ubangiji Allahnku, ba ku gaskata shi ba, ba ku kuwa yi biyayya da muryarsa ba.

24 Tun ran da na san ku, ku masu tayar wa Ubangiji ne.

25 “Sai na fāɗi na kwanta a gaban Ubangiji dare arba’in da yini arba’in saboda Ubangiji ya ce zai hallaka ku.

26 Na roƙi Ubangiji, na ce, ‘Ya Ubangiji Allah, kada ka hallaka jama’arka, abar gādonka wadda ka fanshe ta ta wurin girmanka, waɗanda kuma ka fito da su daga Masar da ikon dantsenka.

27 Ka tuna da bayinka, su Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, kada ka kula da taurinkan jama’ar nan, ko muguntarsu, ko zunubansu

28 Don kada mutanen ƙasar da ka fito da mu su ce, “Ai, saboda Ubangiji ya kāsa ya kai su ƙasar da ya alkawarta musu, saboda kuma ba ya ƙaunarsu, shi ya sa ya fito da su don ya kashe su a jeji.”

29 Amma su mutanenka ne, abin gādonka, waɗanda ka fito da su da ikonka mai girma da dantsenka mai iko.’ ”

Categories
M. SH

M. SH 10

Allunan Dutse na Biyu

1 “A lokacin nan kuwa Ubangiji ya ce mini, ‘Ka sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na farko, ka hau zuwa wurina a bisa dutsen, ka kuma yi akwati na itace.

2 Ni kuma zan rubuta a allunan maganar da take kan alluna na farko waɗanda ka farfashe. Za ka ajiye su cikin akwatin.’

3 “Sai na yi akwati da itacen ƙirya, na kuma sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na farko. Sai na hau dutsen da alluna biyu a hannuna.

4 Ubangiji kuwa ya sāke rubuta dokoki goma a allunan kamar na farko, wato dokoki goma ɗin nan da Ubangiji ya faɗa muku a dutse ta tsakiyar wuta a ranar taron. Sai Ubangiji ya ba ni su.

5 Na sauko daga dutsen, na ajiye allunan cikin akwatin da na yi, a nan suke kamar yadda Ubangiji ya umarce ni.”

6 (Isra’ilawa suka kama tafiya daga rijiyoyin Bene-ya’akan suka zo Mosera. Nan ne Haruna ya rasu, aka binne shi. Sai ɗansa Ele’azara, ya gāje shi a matsayinsa na firist.

7 Daga nan suka tafi Gudgoda, daga Gudgoda kuma suka tafi Yotbata, ƙasa mai rafuffukan ruwa.

8 A wannan lokaci ne Ubangiji ya keɓe kabilar Lawi domin su riƙa ɗaukar akwatin alkawari na Ubangiji, su kuma tsaya a gaban Ubangiji, su riƙa yi masa aiki, su kuma sa albarka da sunan Ubangiji kamar yadda yake a yau.

9 Domin haka kabilar Lawi ba su da rabo ko gādo tare da ‘yan’uwansu, Ubangiji shi ne gādonsu kamar yadda Ubangiji Allahnku ya faɗa musu.)

10 “Na sāke yin dare arba’in da yini arba’in a kan dutsen kamar dā. Ubangiji kuwa ya amsa addu’ata a lokacin kuma, ya janye hallaka ku.

11 Sai Ubangiji ya ce mini, ‘Tashi, ka tafi, ka kama tafiyarka a gaban jama’an nan domin su je, su shiga, su mallaki ƙasar da na rantse wa kakanninsu, zan ba su.’ ”

Abin da Ubangiji Yake So

12 “Yanzu fa, ya Isra’ilawa ga abin da Ubangiji Allahnku yake so a gare ku. Sai ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin hanyoyinsa, ku ƙaunace shi, ku bauta wa Ubangiji Allahnku da zuciya ɗaya da dukan ranku.

13 Ku kiyaye umarnan Ubangiji da dokokinsa waɗanda nake umurtarku da su yau don amfanin kanku.

14 Duba, saman sammai, da duniya, da dukan abin da yake cikinta na Ubangiji Allahnku ne.

15 Duk da haka Ubangiji ya ƙaunaci kakanninku ya zaɓi zuriyarsu a bayansu daga cikin dukan sauran al’umma, kamar yadda yake a yau.

16 Saboda haka sai ku kame zukatanku, kada ku ƙara yin taurinkai.

17 Gama Ubangiji Allahnku, Allahn alloli ne, da Ubangijin iyayengiji. Shi Allah mai girma ne, mai iko, mai bantsoro, wanda ba ya son zuciya, ba ya karɓar hanci.

18 Yakan yi wa marayu da gwauraye na gaske shari’a da adalci. Yana ƙaunar baƙo, yakan ba shi abinci da sutura.

19 Sai ku ƙaunaci baƙo, gama dā ku baƙi ne a ƙasar Masar.

20 Sai kuma ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku bauta masa. Ku manne masa, ku yi rantsuwa da sunansa.

21 Shi ne abin yabonku, shi ne Allahnku, wanda ya yi muku waɗannan al’amura masu girma, masu bantsoro waɗanda kuka gani da idanunku.

22 Kakanninku saba’in ne suka gangara zuwa Masar, amma yanzu Ubangiji Allahnku ya riɓaɓɓanya ku, kuka yi yawa kamar taurarin sama.”

Categories
M. SH

M. SH 11

Girman Ubangiji

1 “Sai ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku kiyaye faɗarsa, da dokokinsa da farillansa, da umarnansa kullum.

2 Yau fa ku sani ba da ‘ya’yanku nake magana ba, waɗanda ba su sani ba, ba su kuma ga hukuncin Ubangiji Allahnku ba, da girmansa, da ƙarfin ikon dantsensa,

3 da alamunsa, da ayyukan da ya yi a kan Fir’auna Sarkin Masar, da dukan ƙasar,

4 da irin abin da ya yi wa sojojin Masar, da dawakansu, da karusansu, da yadda ya sa ruwan Bahar Maliya ya haɗiye su, a sa’ad da suke bin sawunku, da yadda Ubangiji ya hallaka su ƙaƙaf,

5 da abin da ya yi muku a jeji kafin ku iso wannan wuri,

6 da abin da ya yi wa Datan, da Abiram, ‘ya’yan Eliyab, ɗan Ra’ubainu, yadda ƙasa ta buɗe a tsakiyar Isra’ilawa ta haɗiye su da dukan ‘ya’yansu, da alfarwansu, da dukan abu mai rai wanda yake tare da su.

7 Amma idanunku sun ga manyan ayyukan nan da Ubangiji ya aikata.”

Albarkun Ƙasar Alkawari

8 “Don haka fa, sai ku kiyaye dukan umarnan da na umarce ku da su yau domin ku sami ƙarfin da za ku haye, ku shiga, ku ci ƙasar da za ku mallaka,

9 domin kuma ku yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji ya rantse zai ba kakanninku da zuriyarsu, ƙasar da yake da yalwar abinci.

10 Gama ƙasar da za ku shiga garin ku mallake ta, ba kamar ƙasar Masar take ba inda kuka fito, inda kukan shuka iri sa’an nan ku yi ta zuwa kuna banruwa kamar lambu.

11 Amma ƙasar da za ku haye ku mallaka, ƙasa ce ta tuddai da kwaruruka wadda ruwan sama yake shayar da ita.

12 Ƙasa ce kuma wadda Ubangiji Allahnku yake lura da ita, Ubangiji Allahnku yana dubanta kullum, tun daga farkon shekara har zuwa ƙarshenta.

13 “Idan kun yi biyayya da umarnansa waɗanda ya umarce ku da su yau, kun ƙaunaci Ubangiji Allahnku, kun bauta masa da zuciya ɗaya da dukan ranku,

14 zai shayar da ƙasarku da ruwa a kan kari, da ruwan bazara da na kaka. Za ku tattara sabon hatsinku da sabon ruwan inabinku, da manku.

15 Zai sa ciyawa ta tsiro a saurukanku domin dabbobinku. Za ku ci ku ƙoshi.

16 Ku lura fa, kada zuciya ta ruɗe ku, har ku kauce, ku bauta wa waɗansu alloli, ku yi musu sujada,

17 don kada Ubangiji ya yi fushi da ku, ya rufe sammai, ku rasa ruwa, ƙasa kuma ta kāsa ba da amfaninta, da haka za ku murmutu nan da nan a kyakkyawar ƙasar da Ubangiji yake ba ku.

18 “Sai ku riƙe zantuttukan nan nawa a zuciyarku da ranku. Za ku ɗaura su alama a hannuwanku, da goshinku.

19 Za ku koya wa ‘ya’yanku su, ku yi ta haddace su, sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya, da sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi.

20 Za ku rubuta su a madogaran ƙofofin gidajenku, da bisa ƙofofinku,

21 don kwanakinku da kwanakin ‘ya’yanku su yi tsawo a ƙasar da Ubangiji ya rantse wa kakanninku zai ba su muddin samaniya tana bisa duniya.

22 “Idan dai za ku lura, ku kiyaye dukan umarnan nan waɗanda nake umartarku ku kiyaye, ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya a dukan hanyoyinsa, ku manne masa,

23 sa’an nan Ubangiji zai kori al’umman nan duka a gabanku. Za ku kori al’umman da suka fi ku yawa da ƙarfi.

24 Duk inda tafin ƙafarku ya taka kuma zai zama naku. Iyakarku za ta kama daga jeji zuwa Lebanon da kuma daga Kogin Yufiretis zuwa Bahar Rum.

25 Ba mutumin da zai iya tsayayya da ku. Ubangiji Allahnku zai sa ƙasar ta firgita, ta ji tsoronku a duk inda kuka sa ƙafa, kamar yadda ya faɗa muku.

26 “Ga shi, yau, na sa albarka da la’ana a gabanku.

27 Za ku sami albarka idan kun yi biyayya da umarnan Ubangiji Allahnku waɗanda nake umartarku da su yau.

28 Za ku zama la’anannu idan ba ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku ba, amma kuka kauce daga hanyar da nake umartarku da ita yau, har ku bi waɗansu alloli waɗanda ba ku san su ba.

29 Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya kai ku cikin ƙasar da za ku shiga ku mallake ta, sai ku ɗibiya albarkar a Dutsen Gerizim, ku ɗibiya la’anar kuma a Dutsen Ebal.

30 Duka biyunsu suna hayin Urdun ne, yamma da hanya a ƙasar Kan’aniyawa, mazaunan Araba, kusa da Gilgal, wajen itacen oak na More.

31 Gama za ku haye Urdun, ku shiga ƙasar da za ku mallaka, wadda Ubangiji Allahnku yake ba ku. Sa’ad da kuka mallake ta, kuka zauna a ciki,

32 sai ku lura, ku aikata dukan dokoki da farillai waɗanda nake sawa a gabanku yau.”

Categories
M. SH

M. SH 12

A Wuri Ɗaya Kaɗai za a Yi Sujada

1 “Waɗannan su ne dokoki da farillai da za ku lura ku aikata a ƙasar da Ubangiji Allah na kakanninku ya ba ku, ku mallaka dukan kwanakinku a duniya.

2 Sai ku hallaka dukan wuraren da al’umman da za ku kora sukan bauta wa gumakansu, a bisa duwatsu masu tsawo, da bisa tuddai, da ƙarƙashin kowane itace mai duhu.

3 Sai ku rurrushe bagadansu, ku ragargaje al’amudansu, ku ƙone ginshiƙansu na tsafi, ku kuma sassare siffofin gumakansu, ku shafe sunayensu daga wuraren nan.

4 “Ba haka za ku yi wa Ubangiji Allahnku ba.

5 Amma sai ku nemi wurin da Ubangiji Allahnku zai zaɓa daga cikin kabilanku duka, inda zai sa sunansa, ya mai da shi wurin zamansa.

6 A can ne za ku tafi, a can ne kuma za ku kai hadayunku na ƙonawa, da sadakokinku, da zakarku, da hadayunku na ɗagawa, da hadayunku na wa’adi, da hadayunku na yardar rai, da ‘ya’yan farin garkenku na shanu, da na tumaki, da na awaki.

7 A nan, wato a gaban Ubangiji Allahnku, za ku ci, ku yi murna, ku da iyalanku, a kan dukan abin da Ubangiji Allahnku ya sa muku albarka da shi.

8 “Kada ku yi kamar yadda muke yi a nan yau, yadda kowa yake yin abin da ya ga dama.

9 Gama ba ku kai wurin hutawa wanda Ubangiji Allahnku zai ba ku gādo ba tukuna.

10 Amma sa’ad da kuka haye Urdun, kuka zauna a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ita gādo, sa’ad da kuma ya ba ku hutawa daga maƙiyanku waɗanda suke kewaye da ku, kuka sami zaman lafiya,

11 sai ku kai dukan abin da na umarce ku ku kai, wato hadayu na ƙonawa, da sadakokinku, da zakarku, da hadayunku na ɗagawa, da hadayunku na wa’adi da kuka yi wa Ubangiji a wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa ya sa sunansa.

12 Ku yi murna a gaban Ubangiji Allahnku, ku da ‘ya’yanku mata da maza, da barorinku mata da maza tare da Lawiyawa waɗanda suke zaune cikinku tun da yake ba su da rabo ko gādo tare da ku.

13 Ku lura, kada ku miƙa hadayunku na ƙonawa ko’ina,

14 amma sai a wurin nan ɗaya wanda Ubangiji zai zaɓa daga cikin kabilanku, nan za ku miƙa hadayunku na ƙonawa, nan ne kuma za ku yi dukan abin da na umarce ku.

15 “Amma kwā iya yanka nama ku ci a garuruwanku duk lokacin da ranku yake so, bisa ga albarkar da Ubangiji yake sa muku. Mai tsarki da marar sarki za su ci abin da aka yanka kamar barewa da mariri.

16 Amma ba za ku ci jinin ba, sai ku zubar da shi a ƙasa kamar ruwa.

17 Kada ku ci waɗannan a garuruwanku, zakar hatsinku, ko ta inabinku, ko ta manku, ko ta ‘ya’yan fari na shanunku da tumakinku, ko hadayunku na wa’adi, da hadayunku na yardar rai, ko hadayarku ta ɗagawa.

18 Amma sai ku ci su a inda Ubangiji Allahnku zai zaɓa, ku da ‘ya’yanku mata da maza, da barorinku mata da maza, da Lawiyawa da suke a cikin garuruwanku. Sai ku yi murna a gaban Ubangiji Allah saboda duk abin da kuke yi.

19 Ku lura, kada ku manta da Lawiyawa muddin kuna zaune a ƙasarku.

20 “Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya fāɗaɗa ƙasarku kamar yadda ya alkawarta muku, sa’an nan ku ce, ‘Ina so in ci nama,’ saboda kuna jin ƙawar nama, to, kuna iya cin nama yadda kuke so.

21 Idan wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa don ya sa sunansa ya yi muku nisa ƙwarai, to, sai ku yanka daga cikin garken shanunku, ko daga tumaki da awaki, waɗanda Ubangiji ya ba ku, kamar yadda na umarce ku. Za ku iya ci yadda kuke bukata a garuruwanku.

22 Kamar yadda akan ci barewa ko mariri haka za ku ci. Marar tsarki da mai tsarki za su iya cin naman.

23 Sai dai ku lura, kada ku ci jinin, gama jinin shi ne rai, kada ku ci ran tare da naman.

24 Kada ku ci jinin, sai ku zubar a ƙasa kamar ruwa.

25 Kada ku ci shi domin ku sami zaman lafiya, ku da zuriyarku a bayanku, gama za ku riƙa aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji.

26 Amma tsarkakakkun abubuwan da suke wajibanku da hadayunku na wa’adi, su ne za ku ɗauka ku kai wurin da Ubangiji ya zaɓa.

27 Sai ku miƙa nama da jinin hadayunku na ƙonawa a bisa bagaden Ubangiji Allahnku. Za ku zuba jinin sadakokinku a bisa bagaden Ubangiji Allahnku, amma za ku ci naman.

28 Ku lura, ku kasa kunne ga dukan umarnan da nake umartarku da su, don ku sami zaman lafiya, ku da zuriyarku a bayanku har abada, idan kun aikata abin da yake da kyau, daidai ne kuma a gaban Ubangiji Allahnku.”

Faɗakarwa a kan Gumaka

29 “Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya kawar muku da al’umman nan waɗanda za ku shiga ƙasarsu don ku kore su, sa’ad da kuka kore su, kun zauna a ƙasarsu,

30 to, sai ku lura, kada ku jarabtu ku kwaikwaye su bayan da an riga an shafe su daga gabanku! Kada ku tambayi labarin kome na gumakansu, ku ce, ‘Ƙaƙa waɗannan al’ummai suka bauta wa gumakansu? Mu ma za mu yi kamar yadda suka yi.’

31 Kada ku yi wa Ubangiji Allahnku haka, gama sun yi wa gumakansu dukan abar ƙyamar da Ubangiji yake ƙi, har sun ƙona wa gumakansu ‘ya’yansu mata da maza.

32 “Ku lura, ku aikata dukan abin da na umarce ku da shi, kada ku ƙara, kada ku rage daga cikinsa.

Categories
M. SH

M. SH 13

1 “Idan wani annabi, ko mai mafarki ya fito a cikinku, ya yi muku shelar wata alama ko mu’ujiza,

2 idan alamar ko mu’ujizar ta auku, idan kuma ya ce, ‘Bari mu bi gumaka, mu bauta musu, gumakan da ba ku san su ba,

3 kada ku saurari maganar annabin nan ko mai mafarkin nan, gama Ubangiji Allahnku yana jarraba ku ne, ya gani, ko kuna ƙaunarsa da zuciya ɗaya da dukan ranku.

4 Sai ku bi Ubangiji Allahnku, ku yi tsoronsa, ku kiyaye umarnansa, ku kasa kunne ga muryarsa, shi ne za ku bauta masa, ku manne masa kuma.

5 Sai a kashe annabin nan, ko mai mafarkin don ya koyar a tayar wa Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar, wato inda kuka yi bauta, gama ya yi ƙoƙari ya sa ku ku kauce daga hanyar da Ubangiji Allahnku ya umarce ku ku bi. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikinku.

6 “Idan ɗan’uwanka, wato ɗan mahaifiyarka, ko ɗanka, ko ‘yarka, ko ƙaunatacciyar matarka, ko amininka ya rarrashe ka a asirce, yana cewa, ‘Bari mu tafi mu bauta wa gumaka waɗanda ku da ubanninku ba ku san su ba,’

7 wato gumakan al’umman da suke kewaye da ku, ko suna kusa da ku, ko suna nesa da ku, daga wannan bangon duniya zuwa wancan,

8 kada ku yarda, kada ku saurare shi. Kada kuma ku ji tausayinsa, kada ku haƙura da shi ko ku ɓoye shi.

9 Hannunku ne zai fara jifansa, sa’an nan sauran jama’a su jajjefe shi, har ya mutu.

10 Ku jajjefe shi da duwatsu har ya mutu, saboda ya yi niyyar janye ku daga bin Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar, wato inda kuka yi bauta.

11 Da haka nan dukan Isra’ilawa za su ji, su ji tsoro, har da ba za su ƙara aikata mugun abu irin wannan a cikinku ba.

12-13 “Idan kuka ji akwai ‘yan ashararu a wani gari wanda Ubangiji Allahnku ya ba ku ku zauna a ciki, sun fito daga cikinku, suka rikitar da mazaunan garin suna cewa, ‘Ku zo mu bauta wa gumaka,’ waɗanda ba ku san su ba,

14 to, sai ku bincike labarin sosai a hankali. Idan hakika gaskiya ne, mugun abu haka ya faru a cikinku,

15 sai ku karkashe dukan mazaunan garin da takobi, ku kuma karkashe dabbobin da suke cikinsa. Za ku hallaka garin ƙaƙaf.

16 Ku tattara dukan ganimar garin a dandali, ku ƙone garin da dukan ganimar, hadaya ta ƙonawa ce ga Ubangiji Allahnku. Garin zai zama kufai har abada, ba za a ƙara gina shi ba.

17 Kada ku ɗauka daga cikin abin da aka haramta don zafin fushin Ubangiji ya huce, ya yi muku jinƙai, ya ji tausayinku, ya kuma riɓaɓɓanya ku ma kamar yadda ya rantse wa kakanninku,

18 in dai za ku yi wa Ubangiji Allahnku biyayya, ku kiyaye dukan umarnansa waɗanda nake umartarku da su yau, ku kuma ku aikata abin da yake daidai ga Ubangiji Allahnku.”

Categories
M. SH

M. SH 14

Al’adar Makokin da Aka Hana

1 “Ku ‘ya’ya ne ga Ubangiji Allahnku, kada ku yi wa jikinku zāne, kada kuma ku yi wa kanku sanƙo saboda wani wanda ya rasu.

2 Gama ku keɓaɓɓun mutane ne na Ubangiji Allahnku. Ubangiji Allahnku kuwa ya zaɓo ku daga cikin dukan al’umman duniya ku zama mutanensa, wato abin gādonsa.”

Halattattun Dabbobi da Haramtattu

3 “Kada ku ci abin da yake haram.

4 Ga dabbobin da za ku ci, da saniya, da tunkiya, da akuya,

5 da mariri, da barewa, da mariya, da mazo, da makwarna, da gada, da ɓauna, da ragon dutse.

6 Za ku iya cin kowace dabbar da take da rababben kofato, wadda kuma take tuƙa.

7 Amma duk da haka cikin waɗanda suke tuƙa, da waɗanda suke da rababben kofato ba za ku ci raƙumi, da zomo, da rema ba, ko da yake suna tuƙa, amma ba su da rababben kofato. Haram ne su a gare ku.

8 Ba kuma za ku ci alade ba, ko da yake yana da rababben kofato, amma ba ya tuƙa. Haram ne shi a gare ku. Kada ku ci naman irin waɗannan dabbobi, ko ku taɓa mushensu.

9 “Daga dukan irin abin da yake zaune a ruwa za ku iya cin duk abin da yake da ƙege da ɓamɓaroki.

10 Kada ku ci duk irin abin da ba shi da ƙege ko ɓamɓaroki, gama haram yake a gare ku.

11 “Kuna iya cin dukan halattattun tsuntsaye.

12 Amma waɗannan tsuntsaye ne ba za ku ci ba, mikiya, da gaggafa, da ungulun kwakwa,

13 da duki, da buga zabi, da kowace irin shirwa,

14 da kowane irin hankaka,

15 da jimina, da ƙururu, da bubuƙuwa, da kowane irin shaho,

16 da mujiya, da babbar mujiya, da ɗuskwi,

17 da kwasakwasa, da ungulu, da dimilmilo,

18 da zalɓe, da kowane irin jinjimi, da katutu, da yaburbura.

19 “Dukan ‘yan ƙwari masu fikafikai masu rarrafe haram ne a gare ku, kada ku ci su.

20 Za ku iya cin duk abin da yake da fikafikai in dai shi halattacce ne.

21 “Kada ku ci mushe. Amma mai yiwuwa ne ku ba baren da yake zaune a garuruwanku, ko kuma ku sayar wa baƙo. Gama ku jama’a ce keɓaɓɓiya ga Ubangiji Allahnku.

“Kada ku dafa ɗan akuya a madarar uwarsa.”

Dokar Zakar

22 “Ku fitar da zakar dukan amfanin da kuka shuka a gonarku kowace shekara.

23 Ku ci zakar sabon hatsinku, da ruwan inabinku, da manku, da ‘yan fari na shanunku, da tumakinku, a gaban Ubangiji Allahnku, a wurin da zai zaɓa ya tabbatar da sunansa, don ku koyi tsoron Ubangiji Allahnku har abada.

24 Idan ya zamana wurin ya yi muku nisa, har ba za ku iya kai zakar a wurin ba, saboda wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa domin ya tabbatar da sunansa ya yi muku nisa sa’ad da Ubangiji Allahnku ya sa muku albarka,

25 to, sai ku sayar da zakar, ku tafi da kuɗin wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa,

26 ku kashe kuɗin a kan duk abin da kuke so, ko sa ne, ko tunkiya, ko ruwan inabi, ko abin sha mai gafi, ko dai duk irin abin da ranku yake so. Nan za ku yi liyafa a gaban Ubangiji Allahnku, ku yi murna tare da iyalan gidanku.

27 “Amma fa, kada ku manta da Balawen da yake garuruwanku gama ba shi da gādo kamarku.

28 A ƙarshen kowace shekara uku, sai ku kawo dukan zakar abin da kuka girbe a wannan shekara, ku ajiye a ƙofofinku.

29 Sa’an nan sai Balawe, da yake shi ba shi da gādo kamarku, da baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske, waɗanda suke zaune a garuruwanku, su zo, su ci, su ƙoshi, domin Ubangiji Allahnku ya sa muku albarka cikin dukan aikin da hannunku zai yi.”

Categories
M. SH

M. SH 15

Shekarar Yafewa

1 “A ƙarshen kowace shekara bakwai dole ku yafe dukan basusuwan da kuke bi.

2 Ga yadda za ku yafe. Sai kowane mai bin bashi ya yafe wa maƙwabcinsa, kada ya karɓi kome a hannun maƙwabcinsa ko ɗan’uwansa, gama an yi shelar yafewa ta Ubangiji.

3 Kana iya matsa wa baƙo ya biya ka, amma sai ka yafe wa danginka bashin da kake binsa.

4 “Ba za a sami matalauci a cikinku ba, da yake Ubangiji Allahnku zai sa muku albarka a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ita gādo, ku mallaka,

5 muddin kun yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnku, kuna kiyaye wannan umarni da na umarce ku da shi yau.

6 Ubangiji Allahnku zai sa muku albarka kamar yadda ya alkawarta. Za ku ba al’ummai da yawa rance, amma ba za ku bukaci rance don kanku ba. Za ku mallaki al’ummai da yawa, amma su ba za su mallake ku ba.

7 “Idan akwai wani danginku matalauci, a wani gari na cikin garuruwan ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, to, kada ku taurara zuciyarku, ku ƙi sakin hannu ga danginku matalauci.

8 Amma ku ba shi hannu sake, ku ranta masa abin da yake so gwargwadon bukatarsa.

9 Amma fa, ku lura, kada ku yi tunanin banza a zuciyarku, kuna cewa, ‘Ai, shekara ta bakwai, shekarar yafewa ta yi kusa,’ har ku ɗaure wa danginku matalauci fuska, ku ƙi ba shi kome. Zai yi kuka ga Ubangiji a kanku, abin kuwa zai zama laifi a kanku.

10 Sai ku ba shi hannu sake, ba da ɓacin zuciya ba. Saboda wannan Ubangiji zai sa muku albarka cikin aikinku duka, da abin da kuke niyyar yi.

11 Gama ba za a rasa matalauta a ƙasar ba, saboda haka nake umartarku, cewa ku zama da hannu sake ga ‘yan’uwanku, da mabukaci, da matalauci.”

Yadda za a Yi da Bayi

12 “Idan aka sayar muku da Ba’ibrane ko mace ko namiji, to, sai ya bauta muku shekara shida, amma a ta bakwai, sai ku ‘yantar da shi.

13 Idan kuma kun ‘yantar da shi, kada ku bar shi ya tafi hannu wofi.

14 Sai ku ba shi hannu sake daga cikin tumakinku, da awakinku, da masussukar hatsinku, da wurin matsewar inabinku. Ku ba shi kamar yadda Ubangiji Allahnku ya sa muku albarka.

15 Ku tuna dā ku bayi ne a ƙasar Masar, amma Ubangiji Allahnku ya ‘yantar da ku, domin haka nake ba ku wannan umarni yau.

16 “Amma idan ya ce muku, ‘Ba na so in rabu da ku,’ saboda yana ƙaunarku da iyalinku, tun da yake yana jin daɗin zama tare da ku,

17 to, sai ku ɗauki basilla ku huda kunnensa har ƙyauren ƙofa, zai zama bawanku har abada. Haka kuma za ku yi da baiwarku.

18 Sa’ad da kuka ‘yantar da shi kada ku damu, gama shekara shida ya yi muku bauta wadda ta ninka ta ɗan ƙodago. Ubangiji Allahnku kuwa zai sa muku albarka cikin dukan abin da kuke yi.”

Keɓewar ‘Ya’yan Fari

19 “Sai ku keɓe wa Ubangiji Allahnku dukan ‘yan fari maza waɗanda aka haifa muku daga cikin garkenku na shanu, da na tumaki, da na awaki. Kada ku yi aiki da ɗan farin shanunku, kada kuma ku sausayi ɗan farin tunkiyarku.

20 Ku da iyalanku za ku ci shi kowace shekara a gaban Ubangiji Allahnku a wurin da Ubangiji zai zaɓa.

21 Idan yana da wani lahani kamar gurguntaka ko makanta, ko kowane irin mugun lahani, to, kada ku miƙa shi hadaya ga Ubangiji Allahnku.

22 Sai ku ci shi a gida. Mai tsarki da marar tsarki a cikinku za su iya ci, kamar barewa ko mariri.

23 Sai dai kada ku ci jinin, amma ku zubar a ƙasa kamar ruwa.”

Categories
M. SH

M. SH 16

Idin Ƙetarewa

1 “Ku kiyaye watan Abib don ku yi Idin Ƙetarewa ga Ubangiji Allahnku, gama a watan Abib ne Ubangiji Allahnku ya fito da ku daga Masar da dad dare.

2 Sai ku miƙa hadayar ƙetarewa daga garkenku na tumaki da na shanu ga Ubangiji Allahnku a wurin da Ubangiji ya zaɓa domin ya tabbatar da sunansa.

3 Kada ku ci abinci mai yisti tare da hadayar. Kwana bakwai za ku riƙa cin abinci marar yisti tare da hadayar, gama abincin wahala ne, gama da gaggawa kuka fita daga ƙasar Masar, don haka za ku tuna da ranar da kuka fito daga ƙasar Masar dukan kwanakinku.

4 Kada a iske yisti a ƙasarku duka har kwana bakwai. Kada kuma ku ajiye naman hadayar da kuka miƙa da yamma a rana ta fari ya kwana har safiya.

5 “Kada ku miƙa hadayar ƙetarewa a kowane garin da Ubangiji Allahnku yake ba ku.

6 Amma ku miƙa ta a wurin da Ubangiji Allahnku zai zaɓa don ya tabbatar da sunansa. Nan za ku miƙa hadayar ƙetarewa da yamma da faɗuwar rana, daidai da lokacin da kuka fito daga Masar.

7 Sai ku dafa shi, ku ci a inda Ubangiji Allahnku zai zaɓa. Da safe sai ku koma alfarwanku.

8 Kwana shida za ku yi kuna cin abinci marar yisti, amma a rana ta bakwai sai ku yi muhimmin taro saboda Ubangiji Allahnku. Kada ku yi aiki a wannan rana.

Idin Makonni

9 “Sai ku ƙirga mako bakwai, wato ku fara ƙirga mako bakwai ɗin daga lokacin da kuka fara sa lauje don ku yanke hatsinku da suke tsaye.

10 Sa’an nan sai ku yi Idin Makonni domin Ubangiji Allahnku. Za ku ba da sadaka ta yardar rai gwargwadon albarkar da Ubangiji Allahnku ya sa muku.

11 Sai ku yi murna a gaban Ubangiji Allahnku a inda Ubangiji Allahnku ya zaɓa don ya tabbatar da sunansa, ku da ‘ya’yanku mata da maza, da barorinku mata da maza, da Balawen da suke zaune a garinku, da baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske, waɗanda suke zaune tare da ku.

12 Ku tuna fa, ku dā bayi ne a Masar, domin haka ku lura, ku kiyaye waɗannan dokoki.

Idin Bukkoki

13 “Za ku yi Idin Bukkoki kwana bakwai bayan da kun gama tattara amfaninku daga masussukanku, da wurin matsewar ruwan inabinku.

14 Sai ku yi murna a cikin idin, ku da ‘ya’yanku mata da maza, da barorinku mata da maza, da Balawe, da baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske, waɗanda suke zaune tare da ku.

15 Za ku kiyaye idin ga Ubangiji Allahnku har kwana bakwai a inda Ubangiji zai zaɓa, gama Ubangiji Allahnku zai yalwata dukan amfanin gonakinku, da dukan ayyukan hannunku don ku cika da murna.

16 “Sau uku a shekara dukan mazajenku za su zo, su hallara a gaban Ubangiji Allahnku a inda zai zaɓa, wato a lokacin idin abinci marar yisti, da lokacin idin makonni, da kuma a lokacin Idin Bukkoki. Kada su hallara a gaban Ubangiji hannu wofi.

17 Kowane mutum zai kawo irin abin da ya iya, gwargwadon albarkar da Ubangiji Allahnku ya sa masa.”

Yin Shari’ar Gaskiya

18 “Sai ku naɗa alƙalai da shugabanni domin garuruwanku waɗanda Ubangiji Allahnku ya ba ku bisa ga kabilanku. Sai su yi wa jama’a shari’a da adalci.

19 Kada ku ɓata shari’a, kada ku yi sonzuciya, kada kuma ku karɓi hanci, gama cin hanci yakan makantar da idanun mai hikima, ya karkatar da maganar adali.

20 Adalci ne kaɗai za ku sa gaba domin ku rayu, ku mallaki ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku.

21 “Kada ku dasa kowane irin itace na tsafi kusa da bagaden Ubangiji Allahnku, wanda za ku gina.

22 Kada kuma ku kafa al’amudi, abin da Ubangiji Allahnku yake ƙi.”

Categories
M. SH

M. SH 17

1 “Kada ku miƙa wa Ubangiji Allahnku hadaya da sa ko da tunkiyar da take da lahani ko naƙasa, gama wannan abar ƙyama ce ga Ubangiji Allahnku.

2 “Idan aka sami wata, ko wani, daga cikin wani gari da Ubangiji Allahnku yake ba ku, yana aikata abin da yake mugu a gaban Ubangiji Allahnku, yana karya alkawarinsa,

3 har ya je, ya bauta wa gumaka, ya yi musu sujada, ko rana, ko wata, ko ɗaya daga cikin rundunar sama, ya yi abin da na hana,

4 idan aka faɗa muku, ko kuwa kun ji labarinsa sai ku yi cikakken bincike. Idan gaskiya ce, aka kuma tabbata an yi wannan mugun abu cikin Isra’ilawa,

5 to, ku kawo macen, ko mutumin, da ya aikata wannan mugun abu a bayan ƙofar garinku, nan za ku jajjefe shi da duwatsu har ya mutu.

6 Bisa ga shaidar mutum biyu ko uku za a kashe shi, amma ba za a kashe mutum a kan shaidar mutum ɗaya ba.

7 Sai shaidun su fara jifansa sa’an nan sauran jama’a su jajjefe shi. Ta haka za a kawar da mugunta daga cikinsu.

8 “Idan aka kawo muku shari’a mai wuyar yankewa a ɗakin shari’arku, ko ta kisankai ce, ko ta jayayya ce, ko ta cin mutunci ce, ko kowace irin shari’a mai wuyar yankewa, sai ku tashi, ku tafi wurin da Ubangiji Allahnku zai zaɓa.

9 Za ku kai maganar wurin Lawiyawan da suke firistoci, ko kuma a wurin alƙalin da yake aiki a lokacin. Za ku tambaye su, za su faɗa muku yadda za a yanke shari’a.

10 Sai ku yanke shari’ar yadda suka faɗa muku daga wurin da Ubangiji ya zaɓa. Ku lura fa, ku yi yadda suka faɗa muku.

11 Dole ne ku yi yadda suka koya muku, da yadda suka yanke shari’ar. Kada ku kauce dama ko hagu daga maganar da suka faɗa muku.

12 Duk wanda ya yi izgili, ya ƙi yin biyayya da firist wanda yake a can, yana yi wa Ubangiji Allahnku hidima, ko kuma ya ƙi yi wa alƙalin biyayya, to, lalle sai a kashe wannan mutum. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikin Isra’ilawa.

13 Sa’an nan duk jama’a za su ji, su kuwa ji tsoro. Ba za su ƙara yin izgilanci ba kuma.”

Ka’idodin Zaman Sarki

14 “Sa’ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku don ku mallake ta, ku zauna a ciki, sa’an nan ku yi tunanin naɗa wa kanku sarki, kamar al’umman da suke kewaye da ku,

15 to, kwā iya naɗa wa kanku sarki wanda Ubangiji Allahnku ya zaɓa. Sai ku naɗa wa kanku sarki daga cikin jama’arku. Kada ku naɗa wa kanku baƙo wanda ba ɗan’uwanku ba.

16 Amma kada sarkin ya tattara wa kansa dawakai, kada kuma ya sa mutane su tafi Masar don su ƙaro masa dawakai, tun da yake Ubangiji ya riga ya yi muku kashedi da cewar, ‘Kada ku sāke komawa can.’

17 Kada kuma ya auri mata da yawa don kada zuciyarsa ta karkace. Kada kuma ya tattara wa kansa kuɗi da yawa.

18 Sa’ad da ya hau gadon sarautar, sai ya sa a rubuta masa dokoki daga cikin littafin dokoki wanda yake wurin Lawiyawan da suke firistoci.

19 Kada ya rabu da littafin, amma ya riƙa karanta shi dukan kwanakinsa domin ya koyi tsoron Ubangiji Allahnsa ta wurin kiyaye dukan dokoki da umarnai,

20 don kada zuciyarsa ta kumbura, har ya ga ya fi ‘yan’uwansa, don kuma kada ya karkace daga bin umarni zuwa dama ko hagu, don shi da ‘ya’yansa su daɗe, suna mulki a Isra’ila.”