Categories
M. SH

M. SH 18

Gādon Firistoci da Lawiyawa

1 “Lawiyawa da firistoci, wato dukan kabilar Lawi, ba su da rabo ko gādo tare da mutanen Isra’ila. Hadayun Ubangiji da dukan abin da ake kawo masa, su ne za su zama abincinsu.

2 Ba za su sami gādo tare da ‘yan’uwansu ba, Ubangiji ne gādonsu kamar yadda ya alkawarta musu.

3 “To, ga rabon da jama’a za su ba firistoci daga hadayun da suka miƙa, ko sā ne ko tunkiya ce, sai su ba firistoci kafaɗar, da kumatun, da tumbin.

4 Sai kuma ku ba su nunan fari na hatsinku, da ruwan inabinku, da manku, da kuma gashin tumakinku wanda kuka fara sausaya.

5 Gama Ubangiji Allahnku ya zaɓe su, su da ‘ya’yansu, daga dukan kabilanku don su yi aiki da sunan Ubangiji har abada.

6 “Balawe yana da dama ya tashi daga kowane gari na Isra’ila inda yake zaune ya je wurin da Ubangiji ya zaɓa.

7 Idan ya zo, sai ya yi aiki saboda sunan Ubangiji Allahnku kamar sauran ‘yan’uwansa Lawiyawa waɗanda suke aiki a gaban Ubangiji a can.

8 Zai sami rabon abincinsa daidai da saura, har da abin da yake na kakanninsa wanda ya sayar.”

Faɗakarwa a kan Ayyukan Arna

9 “Sa’ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, to, kada ku shiga kwaikwayon ayyuka na banƙyama na waɗannan al’ummai.

10 Kada a tarar da wani daga cikinku wanda zai sa ‘yarsu ko ɗansu ya wuce ta tsakiyar wuta, ko mai duba, ko mai maita, ko mai bayyana gaibi, ko mai sihiri,

11 ko boka, ko mabiya, ko maye, ko mai sha’ani da matattu.

12 Ubangiji yana ƙyamar mai yin waɗannan abubuwa. Saboda waɗannan ayyuka masu banƙyama shi ya sa Ubangiji Allahnku yake korar waɗannan al’ummai a gabanku.

13 Sai ku zama marasa aibu a gaban Ubangiji Allahnku.

Allah ya yi Alkawari zai Ta da wani Annabi kamar Musa

14 “Gama waɗannan al’ummai da za ku kora suna kasa kunne ga masu maita da masu duba, amma ku, Ubangiji Allahnku bai yarda muku ku yi haka ba.

15 “Ubangiji Allahnku zai tayar muku da wani annabi kamata daga cikin jama’arku, sai ku saurare shi.

16 “Wannan shi ne abin da kuka roƙa a wurin Ubangiji Allahnku a Horeb, a ranar taron, gama kun ce, ‘Kada ka bar mu mu ƙara jin muryar Ubangiji Allahnmu, ko mu ƙara ganin wannan babbar wuta, don kada mu mutu,’

17 Ubangiji kuwa ya ce mini, ‘Abin da suka faɗa daidai ne.

18 Zan tayar musu da wani annabi kamarka daga cikin ‘yan’uwansu. Zan sa magana a bakinsa, zai faɗa musu duk abin da na umarce shi.

19 Duk wanda bai saurari maganata wadda zai faɗa da sunana ba, ni da kaina zan nemi hakkinta a gare shi.

20 Amma duk wani annabin da ya yi izgili yana magana da sunana, ni kuwa ban umarce shi ba, ko kuwa yana magana da sunan gumaka, wannan annabi zai mutu.’

21 “Ya yiwu ku ce a zuciyarku, ‘Ƙaƙa za mu san maganar da Ubangiji bai faɗa ba?’

22 Sa’ad da annabi ya yi magana da sunan Ubangiji, idan abin da ya faɗa bai faru ba, bai zama gaskiya ba, to, wannan magana ba Ubangiji ne ya faɗa ba. Wannan annabi ya yi izgili ne kawai, kada ku ji tsoronsa.”

Categories
M. SH

M. SH 19

Biranen Mafaka, Iyakoki na Dā

1 “Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya hallaka al’ummai waɗanda zai ba ku ƙasarsu, sa’ad da kuka kore su, kuka zauna cikin garuruwansu da gidajensu,

2 sai ku keɓe garuruwa uku a ƙasar da Ubangiji Allahnku ya ba ku, ku mallaka.

3 Sai ku shirya hanyoyi, ku kuma raba yankin ƙasa wanda Ubangiji Allahnku zai ba ku ku mallaka kashi uku, domin wanda ya yi kisankai ya gudu zuwa can.

4 Wannan shi ne tanadi domin wanda ya yi kisankai, wato wanda zai gudu zuwa can don ya tsira. Idan ya kashe abokinsa ba da niyya ba, ba kuma ƙiyayya a tsakaninsu a dā,

5 misali, idan mutum ya tafi jeji, shi da abokinsa don su saro itace. Da ya ɗaga gatari don ya sari itace, sai ruwan gatarin ya kwaɓe daga ƙotar, ya sari abokinsa har ya mutu. Irin wannan mai kisankai zai gudu zuwa ɗaya daga cikin biranen don ya tsira,

6 don kada mai bin hakkin jini ya bi shi da zafin fushinsa, ya cim masa, saboda nisan hanyar, har ya kashe shi, ko da yake bai cancanci mutuwa ba, tun da ya ke ba ƙiyayya tsakaninsa da abokinsa a dā.

7 Domin haka na umarce ku, ku keɓe wa kanku garuruwa uku.

8 “Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya fāɗaɗa ƙasarku kamar yadda ya alkawarta wa kakanninku, har ya ba ku dukan ƙasar da ya alkawarta zai ba kakanninku,

9 in dai kun lura, kun kiyaye umarnin da nake umartarku da shi yau, ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin tafarkunsa kullum, sa’an nan sai ku ƙara garuruwa uku a kan waɗannan uku ɗin kuma,

10 don kada a zubar da jinin marar laifi a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo, domin kada alhakin jini ya kama ku.

11 “Amma idan wani mutum yana ƙin wani ya kuwa tafi ya yi fakonsa, ya tasar masa, ya yi masa rauni har ya mutu, sa’an nan ya gudu zuwa ɗaya daga cikin garuruwan nan,

12 sai dattawan garinsu su aiko, a kamo shi daga can, sa’an nan su bashe shi ga mai bin hakkin jini don a kashe shi.

13 Kada ku ji tausayinsa. Ta haka za ku hana zub da jinin marar laifi cikin Isra’ila, don ku sami zaman lafiya.

14 “A cikin gādon da za ku samu a ƙasar da Ubangiji Allah yake ba ku ku mallaka, kada ku ci iyakar maƙwabcinku, wanda kakan kakanni suka riga suka kafa.”

Doka a kan Ba da Shaida

15 “Shaidar mutum ɗaya ba za ta isa a tabbatar, cewa mutum ya yi laifi ba, sai a ji shaidar mutum biyu ko uku, kafin a tabbatar da laifin mutum.

16 Idan ɗan sharri ya ba da shaidar zur a kan wani,

17 sai su biyu ɗin su zo a gaban Ubangiji, su tsaya a gaban firistoci da alƙalai waɗanda suke aiki a lokacin.

18 Sai alƙalan su yi bincike sosai. Idan ɗan sharrin ya ba da shaidar zur a kan ɗaya mutumin,

19 to, sai ku yi masa kamar yadda ya so a yi wa wancan mutumin. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikinku.

20 Sauranku za su ji, su ji tsoro, ba za a ƙara aikata irin wannan mugunta ba.

21 Kada ku ji tausayi, zai zama rai maimakon rai, ido maimakon ido, haƙori maimakon haƙori, hannu maimakon hannu, ƙafa maimakon ƙafa.”

Categories
M. SH

M. SH 20

Dokoki a kan Yaƙi

1 “Sa’ad da kuka tafi yaƙi da magabtanku, idan kun ga dawakai, da karusai, da sojoji da yawa fiye da naku, kada ku ji tsoronsu. Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar yana tare da ku.

2 Sa’ad da kuke gab da kama yaƙi, sai firist ya zo gaba, ya yi magana da jama’a,

3 ya ce musu, ‘Ku ji, ya ku Isra’ilawa, yau kuna gab da kama yaƙi da magabtanku, kada ku karai, ko ku ji tsoro, ko ku yi rawar jiki, ko ku firgita saboda su.

4 Ubangiji Allahnku yana tafe tare da ku, zai yaƙi magabtanku dominku, ya ba ku nasara.’

5 “Sa’an nan shugabanni za su yi magana da jama’a, su ce, ‘Ko akwai wani mutum a nan wanda ya gina gidan da bai buɗe shi ba tukuna? Sai ya koma gidansa, kada ya mutu a yaƙi, wani dabam ya yi bikin buɗewar.

6 Ko akwai wani mutum wanda ya dasa gonar inabi da bai ci amfaninta ba? Sai ya koma gidansa, kada ya mutu a yaƙi, wani wani dabam ya ci amfaninta.

7 Ko akwai wani mutum wanda yake tashin yarinya, amma bai aure ta ba tukuna? Sai ya koma gidansa, kada ya mutu a yaƙi, wani ya aure ta.’

8 “Shugabannin yaƙi za su ci gaba da yi wa jama’a magana, su ce, ‘Ko akwai wani mutum a nan wanda yake jin tsoro, wanda zuciyarsa ta karai? Sai ya koma gidansa don kada ya sa zuciyar sauran ‘yan’uwansa kuma su karai.’

9 Sa’ad da shugabannin yaƙi suka daina yi wa jama’a jawabi, sai a zaɓi jarumawan sojoji don su shugabanci mutane.

10 “Sa’ad da kuka kusaci gari don ku yi yaƙi, sai ku fara neman garin da salama.

11 In ya yarda da salamar, har ya buɗe muku ƙofofinsa, sai dukan mutanen da suke cikinsa su yi muku aikin gandu, su bauta muku.

12 Amma idan ya ƙi yin salama da ku, amma ya yi yaƙi da ku, sai ku kewaye shi da yaƙi.

13 Idan Ubangiji Allahnku ya bashe shi a hannunku, sai ku karkashe dukan mazaje da takobi.

14 Amma mata, da yara, da dabbobi, da dukan abin da yake cikin garin, da dukan ganimarsa, sai ku kwashe su ganima, ku mori ganimar magabtanku, wadda Ubangiji Allahnku ya ba ku.

15 Haka za ku yi da dukan garuruwan da suke nesa da ku, wato garuruwan da ba na al’umman da suke kusa da ku ba.

16 “Amma kada ku bar kome da rai a garuruwan mutanen nan da Ubangiji Allahnku yake ba ku su gādo.

17 Za ku hallaka su ƙaƙaf, wato su Hittiyawa, da Amoriyawa, da Kan’aniyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa kamar yadda Ubangiji Allahnku ya umarce ku,

18 don kada su koya muku yin abubuwa masu banƙyama waɗanda suka yi wa gumakansu, har ku yi wa Ubangiji Allahnku zunubi.

19 “Sa’ad da kuka kewaye gari da yaƙi, kuka daɗe kuna yaƙi da shi don ku ci shi, kada ku sassare itatuwansa da gatari har ku lalata su, gama za ku ci amfaninsu. Kada ku sassare su, gama itatuwan da yake cikin saura ba mutane ba ne, da za ku kewaye su da yaƙi.

20 Sai dai itatuwan da kuka sani ba su ba da ‘ya’ya, su ne za ku sassare, ku yi kagara da su saboda garin da kuke yaƙi da shi har ku ci garin.”

Categories
M. SH

M. SH 21

Yadda za a yi da Laifin Kisankai da ba a San wanda ya yi Ba

1 “Idan aka iske gawar mutum wanda wani ya kashe a fili a ƙasar da Ubangiji Allahnku ya ba ku, ku mallaka, ba a kuwa san wanda ya kashe shi ba,

2 sai dattawanku da alƙalanku su fito su auna nisan wurin daga gawar zuwa garuruwan da yake kewaye da gawar.

3 Dattawan garin da ya fi kusa da gawar za su ɗauki karsana wadda ba a taɓa aiki da ita ba, ba a kuma taɓa sa mata karkiya ba.

4 Sai dattawan garin nan su kai karsanar kwari inda ruwa yake gudu, inda ba a taɓa noma ko shuka ba. A can cikin kwarin za a karya wuyan karsanar.

5 Sa’an nan sai firistoci, ‘ya’yan Lawiyawa, su fito gaba, gama su ne Ubangiji Allahnku ya zaɓa don su yi masa aiki, su sa albarka da sunansa, su ne kuma masu daidaita kowace gardama da cin mutunci.

6 Sai dukan dattawan garin da ya fi kusa da gawar su wanke hannuwansu a bisa karsanar da aka karya wuyanta a kwarin.

7 Sa’an nan su ce, ‘Hannuwanmu ba su zub da wannan jini ba, idanunmu kuma ba su ga wanda ya zubar da shi ba.

8 Ya Ubangiji, ka kuɓutar da jama’arka, Isra’ila, wadda ka fansa, kada ka bar alhakin jinin marar laifin nan ya kama jama’arka, Isra’ila. Ka gafarta musu alhakin wannan jini.’

9 Ta haka za ku kawar da alhakin jinin marar laifi daga cikinku, sa’ad da kuka yi abin da yake daidai a wurin Ubangiji.”

Yadda Za a Yi da Matan da Aka Kama Wurin Yaƙi

10 “Sa’ad da kuka tafi yaƙi da magabtanku, Ubangiji Allahnku kuwa ya bashe su a hannunku, kun kuwa kama su bayi,

11 in a cikinsu ka ga wata kyakkyawar mace wadda ka yi sha’awarta, to, ka iya aurenta.

12 Sai ka kawo ta gidanka, ta aske kanta, ta yanke farcenta,

13 ta tuɓe tufafin bauta. Sa’an nan sai ta zauna a gida tana makokin mahaifinta da mahaifiyarta har wata ɗaya cif. Bayan haka ka iya shiga wurinta, ka zama mijinta, ita kuma ta zama matarka.

14 In ka ji ba ka bukatarta, sai ka sake ta ta tafi inda take so, amma kada ka sayar da ita, kada kuma ka wahalshe ta, tun da yake ka riga ka ƙasƙantar da ita.”

Ka’ida a kan Gādon Ɗan Fari

15 “Idan mutum yana da mata biyu, amma ya fi ƙaunar ɗayar, idan kuwa dukansu biyu, wato mowar da borar, suka haifi ‘ya’ya, idan bora ce ta haifi ɗan fari,

16 to, a ranar da zai yi wa ‘ya’yansa wasiyya a kan gādon da zai bar musu, kada ya sa ɗan mowa ya zama kamar shi ne ɗan fari, a maimakon ɗan borar wanda shi ne ɗan farin,

17 Amma sai ya yarda ya ba ɗan farin, wato ɗan borar, za a ba shi riɓi biyu na dukan abin da yake da shi gama shi ne mafarin ƙarfinsa, yana da hakkin ɗan fari.”

Gagararren Ɗa

18 “Idan mutum yana da gagararren ɗa wanda ba ya jin maganar mahaifinsa da ta mahaifiyarsa, sun kuma hore shi, duk da haka bai ji ba,

19 sai mahaifinsa da mahaifiyarsa su kama shi, su kawo shi wurin dattawan garin a dandalin ƙofar gari.

20 Sai su faɗa wa dattawan garinsu, su ce, ‘Wannan ɗanmu ne, gagararre, ba ya yi mana biyayya. Shi mai zari ne, mashayi!’

21 Sa’an nan, sai mutanen garin su jajjefe shi da duwatsu har ya mutu. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikinku. Dukan Isra’ilawa za su ji, su ji tsoro.”

Waɗansu Dokoki

22 “Idan mutum ya yi laifin da ya isa mutuwa, aka rataye shi a itace har ya mutu,

23 kada a bar gawarsa ta kwana a kan itacen. Sai ku binne shi a ranar da aka rataye shi, gama wanda aka rataye shi la’ananne ne ga Ubangiji. Ku binne shi don kada ku ƙazantar da ƙasar da Ubangiji Allah yake ba ku, ku gāda.”

Categories
M. SH

M. SH 22

1 “Idan kun ga ɓataccen san wani, ko tunkiyarsa, to, kada ku ƙyale shi, amma lalle sai ku komar da shi ga mai shi.

2 Idan mutumin ba kusa da ku yake zaune ba, ko kuma ba ku san shi ba, to, sai ku kawo dabbar a gidanku, ta zauna a wurinku, har lokacin da mutumin ya zo ya shaida ta, sa’an nan ku ba shi.

3 Haka nan kuma za ku yi da jakinsa, da riga, da kowane abin wani da ya ɓace, ku kuwa kuka tsinta. Faufau, kada ku ƙyale su.

4 “Idan kun ga jakin wani ko sansa ya faɗi a hanya, kada ku ƙyale shi, sai ku taimake shi ku tashe shi.

5 “Kada mace ta sa suturar maza, kada kuma namiji ya sa suturar mata. Duk mai yin haka, abin ƙyama ne ga Ubangiji Allahnku.

6 “Idan kuna tafiya a hanya, kun ga sheƙar tsuntsu a itace, ko a ƙasa, da ‘ya’yanta, ko da ƙwayaye a ciki, uwar kuma tana kwance bisa ‘ya’yan ko ƙwayayen, kada ku kama uwar duk da ‘ya’yan.

7 Sai ku bar uwar ta tafi, amma kun iya kwashe ‘ya’yan. Yin haka zai sa ku sami zaman lafiya da tsawon rai.

8 “Sa’ad da kuka gina sabon gida, sai ku ja masa rawani don kada ku jawo wa gidanku alhakin jini idan wani ya fāɗi daga bisa.

9 “Kada ku shuka iri biyu a gonar inabinku don kada abin da kuka shuka da amfanin gonar inabinku su zama haramiyarku.

10 “Kada ku haɗa sa da jaki su yi huɗa tare.

11 “Kada ku sa rigar da aka saƙa da ulu garwaye da lilin.

12 “Sai ku yi wa rigar da kukan sa tuntu huɗu, tuntu ɗaya a kowace kusurwa.

Dokoki a kan Hana Lalata

13 “Idan mutum ya auri mace, ya shiga wurinta, sa’an nan ya ƙi ta,

14 yana zarginta da cewa ta yi abin kunya, yana ɓata mata suna a fili, yana cewa, ‘Na auri wannan mata, amma sa’ad da na kusace ta, sai na iske ita ba budurwa ba ce,’

15 sai mahaifinta da mahaifiyarta su kawo shaidar budurcin yarinyar a gaban dattawan garin a dandalin ƙofar garin.

16 Sai mahaifinta ya ce wa dattawan, ‘Na ba wannan mutum ‘yata aure, amma ya ƙi ta.

17 Yana zarginta da aikata abin kunya, ya ce, bai iske ‘yarmu budurwa ba. Amma ga shaidar budurcin ‘yata.’ Sai su shimfiɗa tsalala a gaban dattawan.

18 Sai dattawan garin su kama mutumin su yi masa bulala,

19 su ci shi tara shekel ɗari na azurfa, su ba mahaifin yarinyar, gama a fili mutumin ya ɓata sunan budurwar cikin Isra’ila. Za ta zama matarsa, ba shi da iko ya sake ta muddin ransa.

20 “Idan aka tabbatar zargin gaskiya ne, ba a kuma ga shaidar budurcinta ba,

21 sai a kai yarinyar a ƙofar gidan mahaifinta, sa’an nan mutanen garin su jajjefe ta da duwatsu har ta mutu, don ta yi aikin wauta cikin Isra’ila, gama ta yi karuwanci a gidan mahaifinta. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikinku.

22 “Idan aka iske wani yana kwance da matar wani, sai a kashe dukansu biyu, wato mutumin da matar. Haka za ku kawar da mugunta daga Isra’ila.

23 “Idan a cikin gari wani ya iske budurwar da ake tashinta, ya kwana da ita,

24 sai a kawo su, su biyu ɗin, a dandalin ƙofar gari, ku jajjefe su da duwatsu har su mutu, don yarinyar tana cikin gari, amma ba ta yi kururuwa a taimake ta ba, don kuma mutumin ya ɓata budurwar maƙwabcinsa. Da haka za ku kawar da mugunta daga cikinku.

25 “Amma idan a saura wani ya fāɗa wa yarinyar da ake tashinta, har ya kwana da ita ƙarfi da yaji, sai a kashe wannan mutum.

26 Amma ita yarinyar ba za a yi mata kome ba, domin ba ta yi laifin da ya isa mutuwa ba, gama wannan shari’a daidai take da ta mutumin da ya faɗa wa maƙwabcinsa ya kashe shi.

27 Gama sa’ad da ya same ta a saura, ita wadda ake tashinta ta yi kururuwa, amma ba wanda zai cece ta.

28 “Idan wani ya iske yarinyar da ba a tashinta, ya kama ta, ya kwana da ita, aka kuwa same su,

29 to, sai wanda ya kwana da ita ya ba mahaifinta shekel hamsin na azurfa, ita kuwa za ta zama matarsa, gama ya ci mutuncinta. Ba zai sake ta ba muddin ransa.

30 “Kada mutum ya auri matar mahaifinsa, kada kuma ya kware fatarinta, gama na mahaifinsa ne.”

Categories
M. SH

M. SH 23

Waɗanda Za a Ware daga Cikin Taron Jama’a

1 “Duk wanda aka dandaƙe ko wanda aka yanke gabansa ba zai shiga taron jama’ar Ubangiji ba.

2 “Shege ba zai shiga taron jama’ar Ubangiji ba. Har tsara ta goma zuriyarsa ba za su shiga taron jama’ar Ubangiji ba.

3 “Kada Ba’ammone ko Bamowabe ya shiga taron jama’ar Ubangiji. Har tsara ta goma ta zuriyarsu ba za su shiga taron jama’ar Ubangiji ba.

4 domin ba su zo sun tarye ku, su kawo muku abinci da ruwa ba sa’ad da kuke a hanyarku, lokacin da kuka fito daga Masar. Ga shi kuma, sun yi ijara da Bal’amu ɗan Beyor daga Fetor ta Mesofatamiya ya zo ya la’anta ku.

5 Amma Ubangiji Allahnku ya ƙi saurarar Bal’amu, sai Ubangiji ya juyar da la’anar ta zama muku albarka saboda Ubangiji Allahnku yana ƙaunarku.

6 Har abada kada ku nemar musu zaman lafiya ko wadata.

7 “Kada ku ji ƙyamar Ba’edome gama shi danginku ne. Kada kuma ku ji ƙyamar Bamasare don kun yi baƙunci a ƙasarsa.

8 ‘Ya’yansu tsara ta uku, za su iya shiga taron jama’ar Ubangiji.”

Kiyaye Sansanin Yaƙi da Tsabta

9 “Sa’ad da kuka kafa sansani don ku yi yaƙi da magabtanku, sai ku kiyaye kanku daga kowane mugun abu.

10 Idan wani a cikinku ya ƙazantu saboda ya zubar da maniyyi da dare, to, sai ya fita daga sansanin, kada ya koma sansanin.

11 Amma da maraice, sai ya yi wanka da ruwa, ya koma sansani sa’ad da rana ta faɗi.

12 “Za ku keɓe wani wuri a bayan sansani inda za ku riƙa zagayawa.

13 Sai ku ɗauki abin tona ƙasa tare da makamanku. Lokacin da za ku zagaya garin yin najasa, sai ku tsuguna ku tona rami da abin tona ƙasa sa’an nan ku rufe najasar da kuka yi.

14 Gama Ubangiji Allahnku yakan yi yawo cikin sansaninku don ya cece ku, ya ba da magabtanku cikin hannunku. Saboda haka dole ku tsabtace sansaninku don kada Ubangiji ya iske wata ƙazanta a cikinku, ya rabu da ku.”

Waɗansu Dokoki

15 “Kada ku ba da bawan da ya tsere, ya zo gare ku, ga ubangijinsa.

16 Zai zauna a wurinku. Sai ya zauna tare da ku, a wurin da ya zaɓa cikin garuruwanku inda ya fi so. Kada ku dame shi.

17 “Kada Isra’ilawa mata da maza su shiga ƙungiyar karuwanci na addini.

18 Kada ku kawo kuɗin da aka samu ta wurin karuwanci, ko kuɗin da aka samu ta wurin yin luɗu a Haikalin Ubangiji don biyan wa’adin da kuka riga kuka yi, gama wannan abin ƙyama ne ga Ubangiji Allahnku.

19 “Kada ku ba danginku rance da ruwa, ko rancen kuɗi ne, ko na abinci, ko na kowane irin abu da akan ba da shi da ruwa.

20 Kun iya ba baƙo rance da ruwa, amma kada ku ba danginku rance da ruwa don Ubangiji Allahnku ya sa muku albarka a kan dukan abin da za ku yi a ƙasar da kuke shiga, ku kuma mallake ta.

21 “Idan kun yi wa Ubangiji Allahnku wa’adi, to, kada ku yi jinkirin cikawa, gama Ubangiji Allahnku zai neme shi a gare ku, ba kuwa zai zama zunubi a gare ku ba.

22 Idan kun nisanci yin wa’adi, ba zai zama zunubi gare ku ba.

23 Sai ku cika duk abin da kuka faɗa da bakinku, gama da yardarku ne kuka yi wa Ubangiji Allahnku wa’adi wanda kuka alkawarta.

24 “Sa’ad da kuka shiga gonar inabin maƙwabcinku, kuna iya cin ‘ya’yan inabin, har ku ƙoshi yadda kuke so, amma kada ku sa wani a jakarku.

25 Sa’ad da kuka shiga hatsin maƙwabcinku da yake tsaye, kun iya ku yi murmuren tsabar da hannunku, amma kada ku sa wa hatsin maƙwabcinku lauje.”

Categories
M. SH

M. SH 24

Dokar Kisan Aure

1 “Idan mutum ya sami wata mata ya aura, amma idan ba ta gamshe shi ba saboda ya iske wani abu marar kyau game da ita, har ya ba ta takardar saki a hannunta, ya sallame ta daga gidansa,

2 ta kuwa fita gidansa, idan ta je ta auri wani mutum dabam,

3 idan shi kuma ya ƙi ta, ya ba ta takardar saki a hannunta, ya sallame ta daga gidansa, ko kuma idan ya mutu ne,

4 to, kada mijinta na fari wanda ya sake ta, ya sāke aurenta, tun da yake ta ƙazantu. Gama wannan abar ƙyama ce a wurin Ubangiji. Kada ku jawo alhaki a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ku gāda.

5 “Idan mutum ya yi sabon aure, kada ya tafi yaƙi tare da sojoji, ko kuma a sa shi kowane irin aiki. Sai ya huta a gida har shekara ɗaya saboda gidansa, don ya faranta wa matar da ya auro zuciya.”

Waɗansu Dokoki

6 “Kada mutum ya karɓi jinginar dutsen niƙa ko ɗan dutsen niƙa, gama yin haka karɓar jinginar rai ne.

7 “Idan aka iske mutum yana satar danginsa Ba’isra’ile don ya maishe shi bawansa, ko ya sayar da shi, sai a kashe ɓarawon. Ta haka za ku kawar da mugunta daga tsakiyarku.

8 “Game da ciwon kuturta, sai ku lura ku bi daidai da yadda firistoci na Lawiyawa suka umarce ku, ku yi. Sai ku kiyaye, ku aikata yadda na umarce su.

9 Ku tuna da abin da Ubangiji Allahnku ya yi wa Maryamu a lokacin da kuka fito daga Masar.

10 “Idan kun ba maƙwabcinku rance na kowane iri, kada ku shiga gidansa don ku ɗauki jingina.

11 Sai ku tsaya a waje, mutumin da kuka ba shi rancen zai kawo muku jinginar.

12 Amma kada ku yarda abin da aka jinginar ya kwana a wurinku idan mutumin matalauci ne.

13 Sai ku mayar masa da shi a faɗuwar rana domin ya yi barci yafe da rigarsa ya gode muku. Yin haka zai zama muku adalci a wurin Ubangiji Allahnku.

14 “Kada ku zalunci ɗan ƙodago wanda yake matalauci, ko shi danginku ne, ko kuwa baƙon da yake zaune a garuruwan ƙasarku.

15 Sai ku biya shi hakkinsa a ranar da ya yi aikin, kafin faɗuwar rana, gama shi matalauci ne, zuciyarsa tana kan abin hakkinsa, don kada ya yi wa Ubangiji kuka a kanku, har ya zama laifi a gare ku.

16 “Kada a kashe ubanni maimakon ‘ya’ya, kada kuma a kashe ‘ya’ya maimakon ubanni. Amma za a kashe mutum saboda laifin da ya aikata.

17 “Kada ku karkatar da shari’ar baƙo ko maraya. Kada kuma ku karɓi mayafin matar da mijinta ya rasu abin jingina.

18 Ku tuna, dā ku bayi ne a Masar, Ubangiji Allahnku ya fanshe ku daga can, saboda haka ina umartarku ku yi wannan.

19 “Idan kun manta da wani dami a gona lokacin girbin amfanin gona, kada ku koma ku ɗauko. Ku bar wa baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske, domin Ubangiji Allahnku ya sa muku albarka a kan dukan aikin hannuwanku.

20 Sa’ad da kuka kakkaɓe ‘ya’yan zaitunku, kada ku sāke bin rassan kuna kakkaɓewa, sai ku bar wa baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske.

21 Sa’ad da kuka girbe gonar inabinku kada kuma ku yi kala, sai ku bar wa baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske.

22 Sai ku tuna, dā ku bayi ne a Masar, don haka nake umartarku ku yi wannan.”

Categories
M. SH

M. SH 25

1 “Idan wata gardama ta tashi tsakanin mutane, suka je gaban shari’a, alƙalai kuwa suka yanke musu maganar, suka kuɓutar da marar laifi, suka kā da mai laifin,

2 idan mai laifin ya cancanci bulala, sai alƙali ya sa shi ya kwanta ƙasa, a bulale shi a gabansa daidai yawan bulalar da ta dace da irin laifin da ya yi.

3 Za a iya yi masa bulala arba’in, amma kada ta fi haka, don kada a ci gaba da bugunsa fiye da haka, har ya zama rainanne a idonku.

4 “Kada ku yi wa takarkari takunkumi sa’ad da yake tattaka hatsinku.”

Gādon Aure

5 “Idan ‘yan’uwa suna zaune wuri ɗaya tare, in ɗayansu ya rasu bai haihu ba, to, kada matar marigayin ta auri wani baƙo wanda yake ba a cikin dangin mijin ba. Sai ɗan’uwan mijinta ya zo wurinta, ya aure ta, ya yi mata abin da ya kamaci ɗan’uwan miji ya yi.

6 Ɗan farin da za ta haifa, zai zama magajin marigayin don kada a manta da sunansa cikin Isra’ila.

7 Amma idan mutum ya ƙi ya auri matar ɗan’uwansa, marigayi, sai matar ta tafi wurin dattawa a dandalin ƙofar gari, ta ce, ‘Ɗan’uwan mijina, marigayi, ya ƙi wanzar da sunan ɗan’uwansa cikin Isra’ila, gama ya ƙi yi mini abin da ya kamaci ɗan’uwan marigayi, ya yi.’

8 Sai dattawan garin su kira mutumin, su yi masa magana. Idan ya nace, yana cewa, ‘Ba na so in aure ta,’

9 sai matar ɗan’uwansa, marigayi, ta tafi wurinsa a gaban dattawan, ta kwaɓe takalmin ƙafarsa, ta tofa masa yau a fuskarsa, ta ce, ‘Haka za a yi wa wanda ya ƙi kafa gidan ɗan’uwansa.’

10 Za a kira sunan gidansa cikin Isra’ila, ‘Gidan wanda aka kwaɓe masa takalmi.’ ”

Waɗansu Dokoki

11 “Idan mutane biyu suna faɗa da juna, idan matar mutum ɗaya daga cikinsu ta zo don ta taimaki mijinta, idan ta kama marainan wancan mutum da hannunta,

12 sai ku yanke hannunta, kada ku ji tausayi.

13 “Kada ku riƙe ma’aunin nauyi iri biyu a jakarku, wato babba da ƙarami.

14 Kada kuma ku ajiye mudu iri biyu a gidanku, wato babba da ƙarami.

15 Sai ku kasance da ma’aunin nauyi da mudu masu kyau don ku daɗe a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku.

16 Gama duk wanda yake aikata irin waɗannan abubuwa, da dukan marasa gaskiya, abin ƙyama ne su ga Ubangiji Allahnku.”

A Karkashe dukan Amalekawa

17 “Ku tuna da abin da Amalekawa suka yi muku a hanya, lokacin da kuka fito daga Masar.

18 Yadda suka yi muku kwanto a hanya, suka fāɗa muku ta baya, suka karkashe waɗanda suka gaji tiɓis. Ba su ko ji tsoron Allah ba.

19 Domin haka sa’ad da Ubangiji Allahnku ya ba ku hutawa daga dukan magabtanku da suke kewaye da ku a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ku mallaka, abar gādo, to, sai ku shafe Amalekawa daga duniya, don kada a ƙara tunawa da su. Kada fa ku manta.”

Categories
M. SH

M. SH 26

Abin da Za a Yi da Nunan Fari da Zaka

1 “Sa’ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ku gāda, kuka mallake ta, kuka zauna cikinta,

2 to, sai ku keɓe nunan fari na dukan amfanin ƙasa wanda kuka shuka a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku. Ku sa cikin kwando, ku tafi inda Ubangiji Allahnku zai zaɓa don ya tabbatar da sunansa.

3 Ku je wurin firist wanda yake aiki a lokacin, ku ce, ‘Yau, na sakankance a gaban Ubangiji Allahnka, cewa na shiga ƙasar da Ubangiji ya rantse wa kakanninmu zai ba mu.’

4 “Sa’an nan firist ya karɓi kwandon daga gare ku ya sa shi kusa da bagaden Ubangiji Allahnku.

5 Sa’an nan kuma sai ku hurta waɗannan kalmomi a gaban Ubangiji Allahnku, ku ce, ‘Ubana Ba’aramiye ne, mayawaci a dā. Ya gangara zuwa Masar yana da jama’a kima, ya yi baƙunci a wurin. Amma a can ya zama al’umma mai girma, mai iko, mai yawa.

6 Masarawa suka wulakanta mu, suka tsananta mana, suka bautar da mu.

7 Amma muka yi kuka ga Ubangiji Allah na kakanninmu. Ubangiji kuwa ya ji kukanmu, ya ga azabarmu, da wahalarmu, da zaluncin da ake yi mana.

8 Sai Ubangiji ya fisshe mu daga Masar da dantsensa mai ƙarfi, mai iko, tare da bantsoro, da alamu, da mu’ujizai.

9 Ubangiji ya kawo mu nan, ya ba mu ƙasar nan, ƙasar da take mai yalwar abinci.

10 Ga shi, yanzu mun kawo nunan fari na amfanin ƙasar, da kai, ya Ubangiji, ka ba mu.’

“Sai ku ajiye shi a gaban Ubangiji Allahnku, ku yi sujada a gaban Ubangiji Allahnku.

11 Ku yi murna kuma, ku da Lawiyawa, da baƙin da suke zaune tare da ku, saboda dukan alherin da Ubangiji Allah ya yi muku, ku da gidanku.

12 “Sa’ad da kuka gama fitar da zakarku ta amfanin gona a shekara ta uku, wadda take shekara ta fid da zaka, sai ku ba Balawe, da baƙo, da maraya, da matar da mijinta ya rasu, don su ci, su ƙoshi a cikin garuruwanku.

13 Sa’an nan za ku ce a gaban Ubangiji Allahnku, ‘Na fitar da tsattsarkan kashi daga cikin gidana na ba Balawe, da baƙo, da maraya, da matar da mijinta ya rasu bisa ga umarnin da ka yi mini. Ban karya wani umarninka ba, ban kuwa manta da su ba.

14 Ban ci kome daga cikin zakar sa’ad da nake baƙin ciki ba, ban kuma fitar da kome daga cikinta ba sa’ad da nake da ƙazanta, ban kuma miƙa wa matattu kome daga cikinta ba. Na yi biyayya da muryar Ubangiji Allahna, na aikata dukan abin da ka umarce ni.

15 Ka duba ƙasa daga Sama, daga wurin zamanka mai tsarki, ka sa wa jama’arka, Isra’ila, albarka duk da ƙasar da ka ba mu, ƙasar da take mai yalwar abinci, kamar yadda ka rantse wa kakanninmu.’ ”

Tsattsarkar Jama’a ta Ubangiji

16 “Yau Ubangiji Allahnku yana umartarku ku kiyaye waɗannan dokoki da farillai. Sai ku lura ku aikata su da dukan zuciyarku da dukan ranku.

17 Yau kun shaida, cewa Ubangiji shi ne Allahnku, za ku yi tafiya cikin tafarkunsa, za ku kiyaye dokokinsa, da umarnansa, da farillansa, za ku kuma yi masa biyayya.

18 Yau kuma Ubangiji ya shaida, cewa ku ne jama’arsa ta musamman, kamar yadda ya alkawarta muku. Ku kuwa za ku kiyaye dukan umarnansa.

19 Shi kuwa zai ɗaukaka ku ku zama abin yabo, masu suna, masu daraja, fiye da dukan al’umman da ya yi. Za ku zama jama’a tsattsarka ta Ubangiji Allahnku kamar yadda ya faɗa.”

Categories
M. SH

M. SH 27

Za a Rubuta Dokoki a Dutsen Ebal

1 Musa da dattawan Isra’ila suka umarci jama’a, suka ce, “Ku kiyaye dukan umarnai waɗanda na umarce ku da su yau.

2 Bayan da kuka haye Urdun, kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, sai ku kakkafa manyan duwatsu, ku yi musu shafe da farar ƙasa.

3 Sai ku rubuta kalmomin wannan shari’a a kansu daidai lokacin da kuka haye ku shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, ƙasar da take mai yalwar abinci, kamar yadda Ubangiji Allahnku ya alkawarta wa kakanninku.

4 Sa’ad da kuka haye Urdun ɗin sai ku kakkafa waɗannan duwatsu a bisa Dutsen Ebal bisa ga umarnin da na yi muku yau. Ku yi musu shafe da farar ƙasa.

5 Can za ku gina wa Ubangiji Allahnku bagade da duwatsun da ba a taɓa sassaƙa su da baƙin ƙarfe ba.

6 Sai ku gina wa Ubangiji Allahnku bagade da duwatsun da ba a sassaƙa ba. A bisa wannan bagade za ku miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji Allahnku.

7 Za ku kuma miƙa hadayu na salama ku ci a wurin, ku yi ta murna a gaban Ubangiji Allahnku.

8 Sai ku rubuta dukan kalmomin waɗannan dokoki su fita sosai bisa duwatsun nan.”

9 Sai Musa da Lawiyawan da suke firistoci, suka ce wa Isra’ilawa, “Ku ji. Yau kun zama jama’ar Ubangiji Allahnku.

10 Sai ku saurari muryar Ubangiji Allahnku, ku kiyaye umarnansa, da dokokinsa waɗanda muke umartarku da su yau.”

La’ana a kan Dutsen Ebal

11 A wannan rana kuma Musa ya umarci jama’a, ya ce,

12 “Sa’ad da kuka haye Urdun, sai waɗannan kabilai su tsaya a bisa Dutsen Gerizim su sa wa jama’a albarka, wato kabilar Saminu, da ta Lawi, da ta Yahuza, da ta Issaka, da ta Yusufu, da ta Biliyaminu.

13 Waɗannan za su tsaya a bisa kan Dutsen Ebal don su la’anta, wato kabilar Ra’ubainu, da ta Gad, da ta Ashiru, da ta Zabaluna, da ta Dan, da ta Naftali.

14 Sa’an nan Lawiyawa za su ta da murya, su ce wa dukan Isra’ilawa:

15 “ ‘La’ananne ne mutumin da ya sassaƙa, ko ya ƙera gumaka, abar ƙyama ce ga Ubangiji, aikin hannun mai sana’a, ya kafa ta a ɓoye.’

“Sai dukan jama’a su amsa, ‘Amin, Amin!’

16 “ ‘La’ananne ne wanda ya raina mahaifinsa ko mahaifiyarsa.’

“Sai dukan jama’a su amsa, ‘Amin, Amin!’

17 “ ‘La’ananne ne wanda ya ci iyakar maƙwabcinsa.’

“Sai dukan jama’a su amsa, ‘Amin, Amin!’

18 “ ‘La’ananne ne wanda ya karkatar da makaho daga hanya.’

“Sai dukan jama’a su amsa, ‘Amin, Amin!’

19 “ ‘La’ananne ne wanda ya yi wa baƙo, ko maraya, ko gwauruwa ta gaske shari’a ta rashin gaskiya.’

“Sai dukan jama’a su amsa, ‘Amin, Amin!’

20 “ ‘La’ananne ne wanda ya kwana da matar mahaifinsa, gama ya buɗe fatarin matar mahaifinsa.’

“Sai dukan jama’a su amsa, ‘Amin, Amin!’

21 “ ‘La’ananne ne wanda ya kwana da dabba.’

“Sai dukan jama’a su amsa, ‘Amin, Amin!’

22 “ ‘La’ananne ne wanda ya kwana da ‘yar’uwarsa, wato ‘yar mahaifinsa, ko ‘yar mahaifiyarsa.’

“Sai dukan jama’a su amsa, ‘Amin, Amin!’

23 “ ‘La’ananne ne wanda ya kwana da surukarsa.’

“Sai dukan jama’a su amsa, ‘Amin, Amin!’

24 “ ‘La’ananne ne wanda ya buge maƙwabcinsa daga ɓoye.’

“Sai dukan jama’a su amsa, ‘Amin, Amin!”

25 “ ‘La’ananne ne wanda aka yi ijara da shi don ya kashe marar laifi.’

“Sai dukan jama’a su amsa, ‘Amin, Amin!’

26 “ ‘La’ananne ne wanda bai yi na’am da kalmomin dokokin nan don ya yi aiki da su ba.’

“Sai dukan jama’a su amsa, ‘Amin, Amin!’ ”