Categories
1 SAM

1 SAM 25

Rasuwar Sama’ila

1 Sama’ila kuwa ya rasu. Dukan Isra’ilawa suka taru suka yi makoki dominsa. Suka binne shi a gidansa a Rama.

Dawuda da Abigail

Sai Dawuda ya tashi ya tafi jejin Faran.

2 Akwai wani mutumin Mawon wanda yake da harka a Karmel. Mutumin mai dukiya ne ƙwarai, yana da tumaki dubu uku (3,000) da awaki dubu (1,000). Yana yi wa tumakinsa sausaya a Karmel.

3 Sunan mutumin kuwa Nabal, sunan matarsa kuma Abigail, ita haziƙa ce, kyakkyawa, amma mijinta miskili ne, marar mutunci. Shi daga zuriyar Kalibu ne.

4 Daga cikin jeji, Dawuda ya ji, wai Nabal yana yi wa tumakinsa sausaya,

5 sai ya aiki samari goma, ya ce musu, “Ku tafi Karmel wurin Nabal, ku ce ina gaishe shi.

6 Gaisuwar da za ku yi masa ke nan, ku ce, ‘Salama gare ka, salama ga gidanka, salama kuma ga dukan abin da kake da shi.

7 Na ji kana da masu sausaya. Lokacin da makiyayanka suke tare da mu, ba mu cuce su ba, ba abin da ya ɓace musu dukan lokacin da suke a Karmel.

8 Tambayi samarinka, za su faɗa maka. Saboda haka ka yarda samarina su sami tagomashi a wurinka, gama yau ranar biki ce. Muna roƙonka ka ba barorinka, da ɗanka, Dawuda abin da za ka iya ba mu.’ ”

9 Sa’ad da samarin Dawuda suka zo, suka faɗa wa Nabal dukan abin da Dawuda ya ce musu, sai suka dakata.

10 Nabal ya amsa wa barorin Dawuda, ya ce, “Wane ne Dawuda? Wane ne ɗan Yesse? A kwanakin nan akwai barori da yawa waɗanda suka tayar wa iyayengijinsu.

11 Zan ɗauki abincina, da ruwana, da namana wanda na yanka wa masu yi mini sausaya in ba mutanen da ban san inda suka fito ba?”

12 Barorin Dawuda suka koma suka faɗa wa Dawuda abin da Nabal ya ce.

13 Sai Dawuda ya ce wa mutanensa, “Kowa ya rataya takobinsa.” Ko wannensu kuwa ya rataya takobi. Dawuda kuma ya rataya nasa takobi. Mutum wajen arbaminya suka tafi tare da shi. Mutum metan kuwa suka zauna a wurin kayayyakinsu.

14 Sai ɗaya daga cikin samarin Nabal ya faɗa wa Abigail, wato matar Nabal cewa, “Dawuda ya aiko manzanninsa daga jeji su gai da maigida, amma maigida ya zazzage su.

15 Ga shi, mutanen kuwa sun yi mana kirki, ba mu sha wata wahala ba, ba abin da ya ɓace mana dukan lokacin da muke tare da su a jeji.

16 Sun zama mana ganuwa dare da rana dukan lokacin da muke tare da su a wurin kiwon tumaki.

17 Yanzu sai ki yi tunani, ki san abin da ya kamata ki yi, gama ana niyyar yi wa maigida da dukan gidansa ɓarna. Ga shi, maigida yana da mugun hali, ba zai ji kowa ba!”

18 Sai Abigail ta yi sauri, ta ɗauki malmalar abinci guda metan, da salkar ruwan inabi biyu, da tumaki biyar da aka gyara, da soyayyen hatsi mudu uku, da nonnan ‘ya’yan inabi guda ɗari, da kauɗar ɓaure guda metan, ta labta wa jakai.

19 Ta ce wa samarin, “Ku yi gaba, ga ni nan tafe bayanku.” Amma ba ta faɗa wa Nabal, mijinta ba.

20 Tana tafiya a kan jaki, ta kai gindin wani dutse ke nan, sai ga Dawuda da mutanensa tafe. Ta tafi, ta sadu da su.

21 Dawuda ya ce a ransa, “Ashe, a banza ne na yi ta lura da dukan abin da yake na mutumin nan a jeji, har ba abin da yake nasa da ya ɓace. Ga shi, ya rama mini alheri da mugunta.

22 Allah ya buge ni in mutu, idan na bar masa wani mutum da rai kafin gobe da safe.”

23 Da Abigail ta ga Dawuda, sai ta yi sauri ta sauka daga kan jakin, ta durƙusa gabansa har ƙasa.

24 Ta faɗi a ƙafafunsa, ta ce, “Ya shugabana, bari laifin ya zama nawa. Ina roƙonka ka bar baiwarka ta yi magana, ka kuma yarda ka ji maganar baiwarka.

25 Kada maigidana ya kula da Nabal, gama wawa ne, kamar yadda sunansa yake, wato wawa. Ni dai ban ga samarin da ubangijina ya aika ba.

26 Yanzu, ya maigida, na rantse da ran Ubangiji da kuma ranka, ka ga Ubangiji ya hana ka zubar da jini, da ɗaukar wa kanka fansa, sai ka bar maƙiyanka da waɗanda suke nema su cuce ka su zama kamar Nabal.

27 Idan ka yarda ka karɓi kyautan nan da baiwarka ta kawo maka domin a ba samarin da suke tare da kai.

28 Ina roƙonka ka gafarta mini laifina. Ubangiji zai sa ka zama sarki, kai da zuriyarka, kana yin yaƙi na Ubangiji. Ba kuwa za ka aikata wani mugun abu ba a dukan kwanakinka.

29 Idan wani ya tashi tsaye don ya bi sawunka, ya kuma nemi ranka, Ubangiji zai kiyaye ranka, amma rayukan maƙiyanka za a wurga su kamar dutsen majajjawa.

30 Sa’ad da Ubangiji ya cika maka dukan alherin da ya yi maka alkawari, ya kuma naɗa ka Sarkin Isra’ila,

31 ba kuwa za ka sami dalilin baƙin ciki ba, ko damuwar lamiri domin ba ka da alhakin jini, ba ka kuma ɗaukar wa kanka fansa. Sa’ad da Ubangiji ya nuna maka alheri, sai ka tuna da ni, baiwarka.”

32 Sa’an nan Dawuda ya ce wa Abigail, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah na Isra’ila, wanda ya aike ki ki tarye ni.

33 Basirarki mai albarka ce, ke kuma mai albarka ce, gama kin hana ni zubar da jini da ɗaukar wa kaina fansa yau.

34 Hakika, Ubangiji Allah na Isra’ila ya hana in yi miki ɓarna. Da ba domin kin yi hanzari, kin zo, kin tarye ni ba, da ba wani mutumin Nabal da zai ragu kafin gobe da safe.”

35 Sai Dawuda ya karɓi abin da ta kawo masa. Ya ce mata, “Ki koma gida kada ki damu. Zan yi abin da kike bukata.”

36 Abigail ta koma wurin Nabal, ta iske shi yana biki irin na sarakuna a gidansa. Ya yi ta nishaɗi, ya bugu sosai, don haka ba ta ce masa kome ba sai da safe.

37 Da safe, sa’ad da ruwan inabi ya sake shi, sai Abigail ta faɗa masa abin da ya faru. Zuciyarsa kuwa ta tsinke gaba ɗaya.

38 Bayan kwana goma sai Ubangiji ya bugi Nabal, ya mutu.

39 Sa’ad da Dawuda ya ji Nabal ya mutu, sai ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji wanda ya sāka mini a kan irin rainin da Nabal ya yi mini. Ya kuma hana ni aikata mugunta. Ya ɗora wa Nabal muguntarsa a kansa.”

Sa’an nan Dawuda ya aika, ya nemi Abigail ta zama matarsa.

40 Da barorin Dawuda suka zo wurin Abigail a Karmel, suka ce mata, “Dawuda ne ya aiko mu wurinki domin mu kai ki wurinsa, ki zama matarsa.”

41 Sai ta rusuna har ƙasa, ta ce, “Ni baranyarsa ce, ina a shirye in wanke ƙafafun barorinsa.”

42 Sai ta yi hanzari ta hau jaki, ta ɗauki kuyanginta, su biyar, ta tafi tare da manzannin Dawuda, ta zama matarsa.

43 Dawuda kuma ya auro Ahinowam Bayezreyeliya, dukansu biyu kuwa suka zama matansa.

44 Amma Saul ya aurar da Mikal, ‘yarsa, matar Dawuda, ga Falti ɗan Layish wanda yake a Gallim.

Categories
1 SAM

1 SAM 26

Dawuda Ya Bar Saul da Rai a Zif

1 Zifawa suka zo wurin Saul a Gibeya suka ce, “Ba ga Dawuda yana ɓuya a kan tudun Hakila wanda yake gaban Yeshimon ba?”

2 Saul kuwa ya tashi ya tafi jejin Zif tare da zaɓaɓɓu dubu uku (3,000) na Isra’ila don ya nemi Dawuda.

3 Ya kafa sansaninsa a kan tudun Hakila wanda yake gefen hanya, a gaban Yeshimon. Amma Dawuda ya yi zamansa a jeji. Da ya ga Saul ya bi shi cikin jejin,

4 sai ya aiki magewaya, suka tabbata lalle Saul ya zo.

5 Dawuda kuwa ya tashi ya tafi wurin da Saul ya kafa sansani. Ya kuwa ga inda Saul yake kwance, da kuma Abner ɗan Ner, sarkin yaƙin Saul. Saul ya kwanta a sansanin, sojojin suna kewaye da shi.

6 Dawuda ya ce wa Ahimelek Bahitte, da Abishai, ɗan Zeruya, ɗan’uwan Yowab, “Wa zai tafi tare da ni zuwa sansanin Saul?”

Abishai ya ce, “Zan tafi tare da kai.”

7 Sai Dawuda da Abishai, suka tafi sansanin Saul da dare. Suka tarar da Saul yana barci cikin sansani da mashinsa a kafe a ƙasa, wajen kansa. Abner kuwa da sauran sojoji suna kwance kewaye da shi.

8 Sa’an nan Abishai ya ce wa Dawuda, “Yau Ubangiji ya ba da maƙiyinka a hannunka, ka bar ni in nashe shi da mashi sau ɗaya kaɗai, in sha zararsa, in haɗa shi da ƙasa!”

9 Amma Dawuda ya ce wa Abishai, “Kada ka hallaka shi, gama wa zai taɓa wanda Ubangiji ya keɓe, ya rasa yin laifi?

10 Hakika Ubangiji zai buge shi, ko ajalinsa ya auka, ko kuwa ya hallaka a wurin yaƙi.

11 Ubangiji ya sawwaƙa in miƙa hannuna in taɓa wanda Ubangiji ya keɓe. Sai dai ka ɗauki mashin da butar ruwan da yake wajen kansa, mu tafi.”

12 Da haka Dawuda ya ɗauki mashi da butar ruwan da yake wajen kan Saul, suka tafi. Ba wanda ya gansu, ba wanda ya sani, ba kuwa wanda ya farka, gama dukansu suna barci, domin Ubangiji ne ya sa barci mai nauyi ya share su.

13 Sa’an nan Dawuda ya haye zuwa wancan gefe, ya tsaya can nesa bisa dutsen, da ɗan nisa tsakaninsu.

14 Sai Dawuda ya kira sojojin sansanin, da kuma Abner ɗan Ner, ya ce, “Ba za ka amsa mini ba, Abner?”

Sai Abner ya ce, “Wa yake kiran sarki?”

15 Dawuda ya ce wa Abner, “Kai ba namiji bane? Wa yake kama da kai cikin Isra’ila? Me ya sa ba ka lura da mai girma, sarki ba? Wani mutum ya zo don ya hallaka mai girma sarki.

16 Abin da ka yi ba shi da kyau. Ka isa a kashe ka, da yake ba ka lura da mai girma ba, wanda Ubangiji ya keɓe. Ka duba, ina mashin sarki da butar ruwan da yake wajen kansa suke?”

17 Saul ya gane da muryar Dawuda, ya ce, “Muryarka ke nan ɗana, Dawuda?”

Dawuda ya amsa, “I, muryata ce, ya mai girma sarki.”

18 Sai ya ƙara da cewa, “Me ya sa mai girma yake bin sawun baransa? Me na yi? Mene ne laifina?

19 Bari sarki ya kasa kunne ga maganar baransa. Idan Ubangiji ne ya kuta ka ka yi gāba da ni, to, bari ya karɓi hadaya, amma idan mutane ne, to, bari su zama la’anannu, gama sun kore ni don kada in sami rabo cikin gādon Ubangiji, suna cewa, ‘Tafi ka bauta wa alloli.’

20 Kada ka kashe ni a baƙuwar ƙasa nesa da Ubangiji. Don me Sarkin Isra’ila yake so ya kashe ni, ni da nake kamar tunkuyau? Don me zai farauce ni kamar tsuntsun jeji?”

21 Sa’an nan Saul ya ce, “Na yi laifi, ka komo, ɗana Dawuda, ba zan yi maka kome ba, gama raina ya zama da daraja a gare ka kyau. Na yi aikin wauta, na yi laifi da yawa.”

22 Sai Dawuda ya ce, “Ga mashinka! Ka aiko wani saurayi ya zo ya karɓa.

23 Ubangiji dai zai sāka wa kowa bisa ga adalcinsa da amincinsa. Ubangiji ya bashe ka a hannuna yau, amma na ƙi in kashe wanda Ubangiji ya keɓe.

24 Kamar yadda ranka ya zama da daraja a gare ni yau, bari raina kuma ya zama da daraja a gaban Ubangiji, ya cece ni daga dukan wahala.”

25 Sai Saul ya ce wa Dawuda, “Ubangiji ya sa maka albarka, ɗana Dawuda, za ka yi manyan abubuwa, ka kuwa yi nasara!”

Dawuda dai ya yi tafiyarsa, Saul kuma ya koma gidansa.

Categories
1 SAM

1 SAM 27

Zaman Dawuda tare da Filistiyawa

1 Dawuda ya yi tunani a ransa, ya ce, “Wata rana Saul zai kashi ni, don haka ba abin da ya fi mini, sai in tsere zuwa ƙasar Filistiyawa. Sa’an nan Saul zai fid da zuciya ga nemana a ƙasar Isra’ila. Zan kuwa tsira daga hannunsa.”

2 Dawuda ya tashi tare da mutum ɗari shida da suke tare da shi zuwa wurin Akish, ɗan Mawok, Sarkin Gat.

3 Dawuda da mutanensa da iyalansu suka zauna tare da Akish a Gat. Dawuda yana tare da matansa biyu, Ahinowam Bayezreyeliya, da Abigail Bakarmeliya, wadda Nabal mijinta ya mutu.

4 Da Saul ya ga Dawuda ya tsere zuwa Gat, bai ƙara fita nemansa ba.

5 Dawuda ya ce wa Akish, “Idan na sami tagomashi a wurinka, ka ba ni wurin zama daga cikin garuruwanka na karkara domin in zauna a can. Gama me zai sa baranka ya zauna tare da kai cikin birni sarauta?”

6 Sai Akish ya ba shi Ziklag a wannan rana, saboda haka Ziklag ta zama ta sarakunan Yahuza har wa yau.

7 Dawuda ya yi shekara guda da wata huɗu a ƙasar Filistiyawa.

8 Dawuda yakan fita da mutanensa su kai wa Geshurawa, da Girziyawa, da Amalekawa hari. Waɗannan su ne mazaunan ƙasar a dā, tun daga Shur har zuwa ƙasar Masar.

9 Dawuda yakan fāɗa wa ƙasar, ya hallaka ta, ba zai bar mace ko namiji da rai ba. Ya kuma kwashe tumaki, da shanu, da jakai, da raƙuma, da tufafi, ya komo zuwa wurin Akish.

10 Idan Akish ya tambayi Dawuda, “A ina ka kai hari yau?” Sai ya ce, “Na kai hari a Negeb ta Yahuza, ko Negeb ta Yerameyel, ko Negeb ta Ƙan’aniyawa.”

11 Dawuda bai bar mace ko namiji da rai ba, wato da zai kawo labari, a Gat, domin yana gudun kada su faɗi abin da yake yi, su ce, “Ga abin da Dawuda ya yi.” Abin da Dawuda ya yi ta yi ke nan a lokacin da yake zaune a ƙasar Filistiyawa.

12 Akish kuwa ya amince da Dawuda, yana cewa, “Ya mai da kansa abin ƙi ga mutanensa Isra’ilawa, zai zama barana muddin ransa.”

Categories
1 SAM

1 SAM 28

1 A kwanakin nan Filistiyawa suka tattara sojojinsu don su yi yaƙi da Isra’ilawa. Akish kuwa ya ce wa Dawuda, “Sai ka sani fa, kai da mutanenka za ku tafi tare da ni da sojojina.”

2 Sai Dawuda ya ce, “Za ka ga abin da baranka zai yi.”

Akish ya ce wa Dawuda, “Da kyau, zan sa ka cikin zaunannun jarumawan da suke kāre ni.”

Saul Ya Tafi wurin Mai Duba

3 Sama’ila ya riga ya rasu, dukan Isra’ilawa kuwa suka yi makoki dominsa, suka binne shi a garinsu, wato Rama. Saul kuma ya riga ya kori masu duba da masu maita daga ƙasar.

4 Filistiyawa suka kafa sansaninsu a Shunem. Saul ya tattara Isra’ilawa, su ma suka kafa sansaninsu a Gilbowa.

5 Da Saul ya ga rundunar yaƙin Filistiyawa, sai ya tsorata, ya yi rawar jiki ƙwarai.

6 Saul kuwa ya yi tambaya ga Ubangiji, Ubangiji bai amsa masa ba, ko ta mafarkai, ko ta Urim, ko ta annabawa.

7 Sai ya ce wa barorinsa, “Ku nemo mini wata mace mai duba domin in tafi wurinta in yi tambaya.”

Barorinsa suka ce masa, “Ai, akwai wata mai duba a Endor.”

8 Sai Saul ya ɓad da kama, ya sa waɗansu tufafi. Shi da waɗansu mutum biyu suka tafi wurin matar da dare. Ya ce mata, “Ina roƙonki ki duba mini ta hanyar sihiri. Ki hawar mini da duk wanda zan faɗa miki.”

9 Matar ta ce masa, “Hakika ka san abin da sarki Saul ya yi, yadda ya karkashe masu duba da masu maita a ƙasar. Me ya sa kake ƙoƙarin kafa mini tarko, don ka sa a kashe ni?”

10 Saul ya rantse mata da Ubangiji, ya ce, “Hakika, ba za a hukunta ki saboda wannan ba.”

11 Sai matar ta ce, “Wa kake so in hawar maka?”

Ya ce, “Ki hawar mini da Sama’ila.”

12 Da matar ta ga Sama’ila, sai ta fasa ƙara, ta ce wa Saul, “Don me ka ruɗe ni, ashe, kai ne sarki Saul?”

13 Sarki kuwa ya ce mata, “Kada ki ji tsoro, me kike gani?”

Ta ce masa, “Na ga wani allah yana fitowa daga ƙasa.”

14 Ya ce mata, “Yaya kamanninsa yake?”

Ta ce, “Wani tsoho ne yake hawowa, yana naɗe da alkyabba.”

Saul ya gane Sama’ila ne, sai ya sunkuyar da kai, ya durƙusa har ƙasa da bangirma.

15 Sai Sama’ila ya ce wa Saul, “Don me ka dame ni, ka hawar da ni?”

Saul ya ce, “Ina cikin babbar wahala, gama Filistiyawa suna yaƙi da ni, Allah kuma ya rabu da ni, ya ƙi amsa mini ko ta wurin annabawa ko ta mafarkai, saboda haka na kira ka, ka faɗa mini abin da zan yi.”

16 Sai Sama’ila ya ce masa, “Don me za ka tambaye ni, tun da yake Ubangiji ya rabu da kai, ya zama magabcinka?

17 Ai, abin da Ubangiji ya faɗa mini a kanka, shi ne ya cika, gama Ubangiji ya fizge mulki daga hannunka, ya ba maƙwabcinka Dawuda.

18 Domin ba ka bi maganar Ubangiji ba, ba ka zartar da hukuncinsa mai zafi a kan Amalekawa ba, saboda haka Ubangiji ya yi maka haka yau.

19 Banda haka kuma Ubangiji zai ba da Isra’ilawa tare da kai a hannun Filistiyawa. Gobe, da kai da ‘ya’yanka maza za ku kasance tare da ni. Ubangiji zai ba da rundunar yaƙin Isra’ila a hannun Filistiyawa.”

20 Da jin maganar Sama’ila sai Saul ya faɗi ƙasa warwar. Tsoro ya kama shi ƙwarai. Ba shi kuma da ƙarfi domin bai ci kome dukan yini da dukan dare ba.

21 Sai matar ta zo wurin Saul, da ta ga ya tsorata, sai ta ce masa, “Baiwarka ta yi kasai da ranta, ta kuwa kasa kunne gare ka.

22 To, kai ma ka kasa kunne ga baiwarka. Bari in ba ka abinci, ka ci don ka sami ƙarfin tafiya.”

23 Sai ya ƙi, ya ce, “Ba zan ci abinci ba.” Sai da barorinsa da matar suka roƙe shi, sa’an nan ya ji maganarsu, ya tashi daga ƙasa, ya zauna a bakin gado.

24 Matar kuwa ta yi hanzari ta yanka turkakken maraƙinta, ta ɗauki gari ta kwaɓa, ta toya abinci marar yisti da shi.

25 Sa’an nan ta kawo wa Saul da barorinsa, suka ci, sa’an nan suka tashi suka tafi da daren nan.

Categories
1 SAM

1 SAM 29

Filistiyawa Ba Su Amince da Dawuda Ba

1 Filistiyawa suka tattara rundunar yaƙinsu a Afek. Isra’ilawa kuma suka kafa sansaninsu kusa da maɓuɓɓugar da take a Yezreyel.

2 Sa’ad da sarakunan Filistiyawa suke wucewa da rundunarsu na mutum ɗari ɗari da na mutum dubu dubu, Dawuda kuma da mutanensa suna biye a baya tare da Akish.

3 Shugabannin sojojin Filistiyawa suka ce, “Me waɗannan Ibraniyawa suke yi a nan?”

Akish kuwa ya ce wa shugabannin sojojin Filistiyawa, “Ai, wannan Dawuda ne baran Saul, Sarkin Isra’ila, wanda yake tare da ni tun da daɗewa. Tun lokacin da ya zo wurina ban taɓa samunsa da wani laifi ba.”

4 Amma shugabannin sojojin Filistiyawa suka husata da shi, suka ce masa, “Ka sa mutumin nan ya koma wurin da ka zaunar da shi. Ba zai tafi tare da mu zuwa wurin yaƙin ba, don kada ya juya mana gindin baka. Ai, da kawunan mutanenmu ne zai yi sulhu da ubangijinsa.

5 Ko ba Dawuda ɗin nan ne ba, da suka raira masa waƙa cikin raye-rayensu, suna cewa, ‘Saul ya kashe dubbai, Dawuda kuwa ya kashe dubun dubbai’?”

6 Akish kuwa ya kira Dawuda, ya ce masa, “Kai amintacce ne a ganina, daidai ne kuma ka tafi yaƙi tare da ni, gama ban same ka da wani laifi ba tun daga ranar zuwanka wurina har yau, duk da haka sarakunan ba su amince da kai ba.

7 To, sai ka koma ka isa lafiya, don kada ka tā da hankalin sarakunan Filistiyawa.”

8 Dawuda ya ce wa Akish, “Me na yi? Wane laifi ka samu a wurin baranka tun daga ranar da na shiga hidimarka har zuwa yau, da ba zan tafi in yi yaƙi da abokan gāban ubangijina sarki ba?”

9 Akish ya amsa wa Dawuda, ya ce, “A ganina kai marar laifi ne kamar mala’ikan Allah, duk da haka shugabannin sojojin Filistiyawa sun ce, ‘Ba zai tafi yaƙi tare da mu ba.’

10 Ka tashi da sassafe kai da barorin ubangijinka da suka zo tare da kai. Da gari ya waye sai ku kama hanya.”

11 Dawuda kuwa ya tashi da sassafe ya kama hanya tare da mutanensa zuwa ƙasar Filistiyawa, amma Filistiyawa suka haura zuwa Yezreyel.

Categories
1 SAM

1 SAM 30

Dawuda Ya Ci Amalekawa

1 Sa’ad da Dawuda da mutanensa suka koma Ziklag a rana ta uku, sai suka tarar Amalekawa sun riga sun kawo wa Negeb da Ziklag hari. Suka cinye Ziklag, suka ƙone ta.

2 Suka kwashe mata da dukan waɗanda suke ciki manya da ƙanana, suka tafi da su. Ba su kashe kowa ba, amma suka kwashe su, suka tafi.

3 Da Dawuda da mutanensa suka ga an ƙone garin, an kuma kwashe matansu, da ‘ya’yansu mata da maza ganima,

4 sai suka yi ta kuka da ƙarfi, har ƙarfinsu ya ƙare.

5 An kwashe matan Dawuda biyu ganima, wato Ahinowam Bayezreyeliya da Abigail Bakarmeliya, matar Nabal wanda ya mutu.

6 Dawuda kuwa ya damu ƙwarai gama mutane suna niyyar su jajjefe shi da duwatsu, domin ransu ya ɓace saboda ‘ya’yansu mata da maza. Amma Ubangiji Allahnsa ya ƙarfafa shi.

7 Sai ya ce wa Abiyata firist, ɗan Ahimelek, ya kawo masa falmaran. Abiyata kuwa ya kawo masa.

8 Sai Dawuda ya yi tambaya ga Ubangiji ya ce, “In bi sawun ‘yan harin nan? Zan ci musu?”

Ya ce masa, “Bi su, gama za ka ci musu, ka ƙwato abin da suka kwashe.”

9-10 Sai Dawuda da mutanensa ɗari shida suka tashi, suka kama hanya, suka kai rafin Besor inda suka bar mutum metan waɗanda suka kāsa. Amma Dawuda da mutum ɗari huɗu suka ci gaba da bin mutanen.

11 Mutanen Dawuda suka sami wani Bamasare a karkara, suka kawo shi wurin Dawuda. Suka ba shi abinci da ruwa, ya ci ya sha.

12 Suka kuma ba shi kauɗar ɓaure da nonnan inabi biyu. Da ya ci sai ya wartsake, gama ya yi yini uku da dare uku ba ci ba sha.

13 Dawuda kuwa ya tambaye shi, “Wane ne ubangidanka? Daga ina ka fito?”

Ya amsa, ya ce, “Ni saurayi ne, Bamasare, baran wani Ba’amaleke. Kwana uku ke nan da ubangidana ya tafi ya bar ni a baya saboda ba ni da lafiya.

14 Mun kai hari a Negeb ta Keretiyawa ta Yahuza, da Negeb ta Kalibu, muka kuma ƙone Ziklag.”

15 Dawuda ya ce masa, “Za ka yarda ka kai ni wurin maharan nan?”

Sai ya ce wa Dawuda, “Idan ka rantse mini da Allah, ba za ka kashe ni ba, ba kuwa za ka mai da ni wurin ubangidana ba, sai in kai ka inda maharan nan suke.”

16 Ya kai Dawuda a wurinsu, sai ga su nan a baje ko’ina a ƙasar, suna ci, suna sha, suna rawa, saboda ganima mai yawa da suka kwashe daga ƙasar Filistiyawa da ƙasar Yahuza.

17 Sai Dawuda ya yi ta karkashe su tun faɗuwar rana har zuwa kashegari da yamma. Ba wanda ya tsira daga cikinsu sai samari ɗari huɗu waɗanda suka tsere a kan raƙuma.

18 Dawuda ya ƙwato dukan abin da Amalekawa suka kwashe, har da matansa biyu.

19 Ba abin da ya ɓace, ƙanƙane ko babba, ko cikin ‘ya’ya mata da maza, ko kuwa wani abu daga cikin ganimar, duk Dawuda ya komar da su.

20 Ya kuma ƙwato garkunan tumaki, da na awaki, da na shanu. Mutanensa suka koro shanun, suka yi gaba, suka ce, “Wannan shi ne ganimar Dawuda.”

21 Da Dawuda ya zo wurin mutum ɗari biyu ɗin nan waɗanda suka tafke, suka kāsa binsa, waɗanda aka bar su a rafin Besor, sai suka tafi su taryi Dawuda da mutanensa da suka tafi tare da shi. Sa’ad da Dawuda ya zo kusa da su ya gaishe su.

22 Sai dukan mugaye da marasa kirki daga cikin mutanen da suka tafi tare da Dawuda suka ce, “Tun da yake ba su tafi tare da mu ba, ba za mu ba su kome daga cikin ganimar da muka ƙwato ba, sai dai kowane mutum ya ɗauki matarsa da ‘ya’yansa ya tafi.”

23 Amma Dawuda ya ce, “’Yan’uwana, ba za ku yi haka da abin da Ubangiji ya ba mu ba. Ubangiji ya kiyaye mu, ya kuma ba da maharan da suka washe mu a hannunmu.

24 Wa zai goyi bayanku a kan wannan al’amari? Wanda ya tafi wurin yaƙi da wanda ya zauna wurin kaya rabonsu zai zama daidai da juna.”

25 Tun daga wannan rana zuwa gaba, wannan ya zama doka da ka’ida ga Isra’ila.

26 Sa’ad da Dawuda ya komo Ziklag, sai ya aika wa abokansa, dattawan Yahuza, da rabo daga cikin ganimar, ya ce, “Ga kyauta dominku, daga cikin ganimar maƙiyan Ubangiji.”

27 Kyautar domin waɗanda suke a Betel, da Ramot ta Negeb, da Yattir,

28 da Arower, da Sifmot, da Eshtemowa,

29 da Rakal, da garuruwa na Yerameyeliyawa, da garuruwa na Ƙan’aniyawa,

30 da Horma, da Ashan, da Atak,

31 da Hebron, da dukan wuraren da Dawuda da mutanensa suka taɓa tafiya.

Categories
1 SAM

1 SAM 31

Rasuwar Saul da ‘Ya’yansa Maza

1 Filistiyawa suka yi yaƙi da Isra’ilawa. Isra’ilawa kuma suka yi gudun Filistiyawa, aka karkashe su a Dutsen Gilbowa.

2 Filistiyawa suka ci Saul da ‘ya’yansa maza. Suka kashe Jonatan, da Abinadab, da Malkishuwa, ‘ya’yan Saul.

3 Yaƙin ya matsa wa Saul. Maharba suka harbe shi, suka yi masa mummunan rauni.

4 Sai ya ce wa mai ɗaukar masa makamai, “Ka zare takobinka ka sha zarata da shi domin kada marasa kaciyan nan su zo su sha zarata, su yi mini ba’a.” Amma mai ɗaukar masa makamai bai yarda ba, domin ya ji tsoro da yawa. Sai Saul ya zare takobinsa, ya faɗa a kansa.

5 Da mai ɗaukar masa makamai ya ga Saul ya rasu, shi ma ya fāɗa a kan nasa takobi ya mutu tare da Saul.

6 Haka Saul, da ‘ya’yansa maza guda uku, da mai ɗaukar masa makamai, da dukan mutanen da suke tare da shi suka mutu a rana ɗaya.

7 Sa’ad da Isra’ilawan da suke a wancan hayi na kwarin da waɗanda suke a wancan hayin Urdun suka ga mayaƙan Isra’ila sun gudu, Saul kuma da ‘ya’yansa sun mutu, sai suka bar garuruwansu, suka gudu. Filistiyawa kuwa suka zo suka zauna a cikinsu.

8 Da Filistiyawa suka zo kashegari don su washe kayan kisassun, sai suka tarar da gawar Saul da gawawwakin ‘ya’yansa uku a kan Dutsen Gilbowa.

9 Suka yanke kansa, suka tuɓe makamansa. Suka aika manzannin a ƙasar Filistiyawa da suke kusa don su kai wannan albishir zuwa ga haikalin gumakansu, da mutanensu.

10 Suka ajiye makaman Saul cikin haikalin gumakan nan Ashtarot. Suka ɗaure gawarsa a kan garun Bet-sheyan.

11 Da mazaunan Yabesh-gileyad suka ji abin da Filistiyawa suka yi wa Saul,

12 sai dukan jarumawa suka tashi, suka yi tafiya dukan dare. Suka ɗauko gawar Saul da gawawwakin ‘ya’yansa daga kan garun Bet-sheyan. Da suka zo Yabesh sai suka ƙone su a can.

13 Suka binne ƙasusuwansu a gindin itacen tsamiya a Yabesh, sa’an nan suka yi azumi kwana bakwai.

Categories
2 SAM

2 SAM 1

Dawuda Ya ji Labarin Rasuwar Saul da Jonatan

1 Bayan rasuwar Saul, sa’ad da Dawuda ya komo daga karkashe Amalekawa, ya yi kwana biyu a Ziklag.

2 Kashegari sai ga wani mutum ya zo daga sansanin Saul, da tufafinsa a yayyage, da ƙura kuma a kansa. Da ya zo wurin Dawuda sai ya fāɗi ƙasa, ya yi gaisuwa.

3 Sai Dawuda ya tambaye shi, ya ce, “Daga ina ka zo?”

Ya ce, “Na tsere ne daga sansanin Isra’ilawa.”

4 Dawuda ya ce masa, “Faɗa mini abin da ya faru.”

Sai ya ce, “Mutane sun gudu daga bakin dāga, an kuma kashe galibin mutanenmu. Saul da ɗansa Jonatan kuma sun mutu.”

5 Dawuda ya ce wa mutumin, “Ta yaya ka sani Saul da ɗansa, Jonatan, sun mutu?”

6 Mutumin kuwa ya amsa ya ce, “Ya zama fa ina kan dutsen Gilbowa, sai ga Saul ya jingina a māshinsa. Karusai da mahayan dawakan abokan gāba sun rutsa shi.

7 Da ya waiga, ya gan ni, sai ya kira ni, ni kuwa na amsa, na ce, ‘Ga ni.’

8 Ya ce mini, ‘Wane ne kai?’ Na ce masa, ‘Ni Ba’amaleke ne.’

9 Sai ya ce mini, ‘Zo ka kashe ni gama ina cikin azaba, amma raina bai fita ba.’

10 Sai na tafi na kashe shi domin na tabbata ba zai yi rai ba bayan ya fāɗi. Na kuma cire kambin da yake kansa da ƙarau da yake a dantsensa. Ga su, na kawo wa ubangijina.”

11 Sai Dawuda ya yayyage tufafinsa. Dukan mutanen da suke tare da shi kuma suka yayyage nasu.

12 Suka yi makoki, da kuka, da azumi har maraice saboda Saul, da Jonatan ɗansa, da mutanen Ubangiji, da gidan Isra’ila domin an Karkashe su a yaƙi.

13 Dawuda ya ce wa mutumin nan da ya kawo labarin, “Daga ina ka zo?”

Sai ya ce masa, “Ai, ni ɗan wani baƙo ne, Ba’amaleke.”

14 Dawuda ya ce, “Me ya sa ba ka ji tsoro ka miƙa hannunka, ka hallaka wanda Ubangiji ya keɓe ba?”

15 Sai Dawuda ya kira ɗaya daga cikin samarin, ya ce masa, “Ka kashe shi.” Ya dai buge shi, ya mutu.

16 Dawuda kuwa ya ce, “Alhakin jininka yana bisa kanka tun da yake da bakinka ka ce, ‘Ni ne na kashe wanda Ubangiji ya keɓe.’ ”

Dawuda Ya Yi Makoki domin Saul da Jonatan

17 Sai Dawuda ya raira waƙar makoki domin Saul da Jonatan, ɗansa.

18 Ya umarta a koya wa mutanen Yahuza wannan waƙa. (An rubuta ta a littafin Yashar.)

19 “An kashe darajarki, ya Isra’ila, a kan tuddanki!

Jarumawan sojojinmu sun fāɗi!

20 Kada a ba da labarin a Gat,

Ko a titin Ashkelon.

Kada ku sa matan Filistiyawa su yi murna,

Kada ku sa ‘yan matan arna su yi farin ciki.

21 “Kada ruwan sama ko raɓa su zubo kan tuddan Gilbowa.

Da ma gonakinta su zama marasa ba da amfani.

Gama a can ne aka zube garkuwoyin jarumawa a wulakance,

Tsatsa ta rufe garkuwar Saul.

22 Bakan Jonatan mai kisa ne,

Takobin Saul ba shi da jinƙai,

Yana kashe masu iko, yana kuma kashe abokan gāba.

23 “Saul da Jonatan ƙaunatattu ne, suna da bansha’awa,

A raye suna tare, haka kuma a mace suna tare.

Sun fi gaggafa sauri,

Sun fi zaki ƙarfi.

24 “Ku ‘yan matan Isra’ila, ku yi makoki domin Saul!

Ya suturta ku da mulufi mai ƙayatarwa,

Ya yi muku adon lu’ulu’u da zinariya.

25 “Jarumawa sun fāɗi,

An kashe su a bakin dāga.

Jonatan na kwance matacce a tuddai.

26 “Na damu ƙwarai saboda kai, ɗan’uwana Jonatan,

Ƙaunatacce kake a gare ni!

Ƙaunarka a gare ni abar al’ajabi ce,

Ta fi ƙaunar mace.

27 “Jarumawa sun fāɗi,

Makamansu ba su da sauran amfani.”

Categories
2 SAM

2 SAM 2

An Naɗa Dawuda Sarkin Yahuza

1 Bayan wannan sai Dawuda ya roƙi Ubangiji, ya ce, “Ko in haura in mallaki ɗaya daga cikin garuruwan Yahuza?”

Ubangiji ya ce masa, “Ka haura.”

Dawuda kuma ya ce, “Zuwa wane gari zan haura?”

Sai Ubangiji ya ce masa, “Zuwa Hebron.”

2 Dawuda kuwa ya haura zuwa can tare da matansa biyu, wato Ahinowam Bayezreyeliya, da Abigail matar marigayi Nabal Bakarmele.

3 Ya kuma tafi tare da mutanen da suke tare da shi, kowa da iyalinsa. Suka zauna a garuruwan Hebron.

4 Mutanen Yahuza kuwa suka zo, suka naɗa Dawuda da man naɗawa domin ya zama Sarkin Yahuza.

Da Dawuda ya ji labari mutanen Yabesh-gileyad, sun binne Saul,

5 sai ya aiki manzanni da saƙo wurin mutanen Yabesh-gileyad ya ce, “Ubangiji ya sa muku albarka da yake kun yi wa Saul, ubangijinku, wannan alheri, har kuka binne shi.

6 Ubangiji ya nuna muku ƙaunarsa da amincinsa. Ni kuwa zan yi muku alheri saboda abin da kuka yi.

7 Yanzu sai ku ƙarfafa, ku yi jaruntaka, gama Saul shugabanku ya rasu, mutanen Yahuza kuwa sun naɗa ni sarkinsu.”

Dawuda ya Yaƙi Gidan Saul

8 Abner kuwa ɗan Ner, sarkin yaƙin Saul, ya tsere da Ish-boshet, ɗan Saul, zuwa Mahanayim.

9 Ya naɗa shi Sarkin Gileyad, da Ashiru, da Yezreyel, da Ifraimu, da ƙasar Biliyaminu, da dukan Isra’ila.

10 Ish-boshet, ɗan Saul, yana da shekara arba’in sa’ad da ya ci sarautar Isra’ila, ya yi shekara biyu yana sarauta. Amma mutanen Yahuza suka bi Dawuda.

11 Dawuda ya yi shekara bakwai da rabi yana sarautar Yahuza a Hebron.

12 Abner, ɗan Ner, tare da fādawan Ish-boshet, ɗan Saul, suka tashi daga Mahanayim zuwa Gibeyon.

13 Sai kuma Yowab, ɗan Zeruya, tare da fādawan Dawuda suka fita suka tafi tarye su a tafkin Gibeyon. Suka zauna, waɗannan a wannan gefe, waɗancan a wancan gefe na tafkin.

14 Sai Abner ya ce wa Yowab, “Bari samarin su tashi su yi kokawa a gabanmu.”

Yowab kuwa ya ce, “To, sai su tashi.”

15 Sai suka tashi, suka haye. Mutum goma sha biyu a madadin mutanen Biliyaminu da Ish-boshet, ɗan Saul, mutum goma sha biyu kuma a madadin mutanen Dawuda.

16 Kowa ya kama abokin kokawarsa a kā, suka soki juna a kwiɓi da takuba. Suka faɗi tare. Aka sa wa wurin suna Helkat-hazzurim, wato filin takuba, wurin yana nan a Gibeyon.

17 Yaƙin kuwa ya yi zafi a ranar. Mutanen Dawuda suka ci Abner da mutanen Isra’ila.

18 ‘Ya’yan Zeruya, maza, su uku suna nan, wato Yowab, da Abishai, da Asahel. Asahel maguji ne kamar barewa.

19 Sai ya tasar wa bin Abner haiƙan, bai kauce ba.

20 Da Abner ya waiga, sai ya ce, “Kai ne Asahel?”

Ya amsa, “Ni ne.”

21 Abner ya ce masa, “Ka daina haye mini, ka runtumi ɗaya daga cikin samarin, ka kama shi, ka karɓe masa makaminsa.” Amma Asahel bai daina binsa ba.

22 Abner kuma ya sāke ce masa, “Ka daina bina, kada ka sa in kashe ka fa! Idan na kashe ka kuwa, yaya zan yi ido biyu da dan’uwanka, Yowab?”

23 Amma Asahel bai daina binsa ba, Abner dai ya nashe shi da gindin māshi a ciki, sai mashin ya fita ta bayansa. Ya fāɗi ya mutu nan take. Duk wanda ya zo inda Asahel ya fāɗi ya mutu, sai ya tsaya cik.

24 Amma Yowab da Abishai suka bi Abner, har faɗuwar rana, suka isa tudun Amma, wanda yake gaban Gaiya, a hanya zuwa jejin Gibeyon.

25 Mutanen Biliyaminu kuma suka haɗa kansu, suka goyi bayan Abner, suka zama ƙungiya guda, suka tsaya kan tudu.

26 Abner kuwa ya kira Yowab, ya ce, “Har abada ne takobi zai hallakar? Ba ka sani ba ƙarshen zai yi ɗaci? Sai yaushe za ka umarci mutanenka su daina runtumar ‘yan’uwansu?”

27 Yowab ya ce, “Na rantse da Ubangiji, hakika da ba domin ka yi magana ba, da mutanena ba za su daina runtumarka ba har gobe da safe.”

28 Sa’an nan Yowab ya busa ƙaho, dukan mutanensa kuwa suka tsaya, ba su ƙara runtumar mutanen Isra’ila ba, ba wanda kuma ya yaƙi wani.

29 Abner da mutanensa suka bi dare farai, suka ratsa Araba, suka haye Urdun. Suka yi ta tafiya dukan safiyan nan, suka shige Bitron, har suka kai Mahanayim.

30 Da Yowab ya komo daga runtumar Abner, ya tattara mutanensa duka, sai ya ga an rasa mutum goma sha tara daga cikin mutanen Dawuda, banda Asahel.

31 Amma barorin Dawuda suka kashe mutanen Biliyaminu mutum ɗari uku da sittin daga cikin waɗanda suke tare da Abner.

32 Suka ɗauki Asahel, suka tafi suka binne shi a kabarin mahaifinsa a Baitalami. Yowab kuwa da mutanensa suka bi dare farai, gari ya waye musu a Hebron.

Categories
2 SAM

2 SAM 3

1 Gidan Saul da gidan Dawuda suka daɗe suna yaƙi da juna. Ƙarfin gidan Dawuda ya yi ta ƙaruwa, amma na gidan Saul ya yi ta raguwa.

‘Ya’ya Maza da aka Haifa wa Dawuda a Hebron

2 ‘Ya’ya maza da aka haifa wa Dawuda a Hebron ke nan, Ahinowam Bayezreyeliya ta haifa masa ɗan farinsa, Amnon.

3 Abigail, matar marigayi, Nabal Bakarmele, ta haifa masa ɗansa na biyu, Kileyab. Ma’aka ‘yar Talmai, Sarkin Geshur, ta haifa masa ɗansa na uku, Absalom.

4 Haggit ta haifa masa ɗansa na huɗu, Adonaija. Abital ta haifa masa ɗansa na biyar, Shefatiya.

5 Matarsa Egla ta haifa masa ɗansa na shida, Itireyam. Dukan waɗannan a Hebron ne aka haife su.

Abner ya Bi Dawuda

6 Abner ya ƙasaita sosai a gidan Saul a lokacin da ake yaƙi tsakanin jarumawan Saul da na Dawuda.

7 Saul yana da ƙwarƙwara mai suna Rizfa, ‘yar Aiya. Sai Ish-boshet ya ce wa Abner, “Me ya sa ka kwana da ƙwarƙwarar tsohona?”

8 Abner ya husata saboda wannan magana, ya ce, “Kana zato ni maci amanar ƙasa ne? Kana tsammani ina wa ƙasar Yahuza aiki ne? Tun da farko ina ta nuna alheri ga gidan Saul, tsohonka, da ‘yan’uwansa, da abokansa, ban kuwa ba da ka a hannun Dawuda ba. Amma ga shi, yau ka zarge ni da laifin kwartanci game da wannan mata.

9 Allah ya la’anta ni, idan ban yi wa Dawuda abin da Ubangiji ya rantse masa ba,

10 wato in mayar wa Dawuda da sarautar gidan Saul. In kafa kursiyin Dawuda a kan Isra’ila da kan Yahuza tun daga Dan har zuwa Biyer-sheba.”

11 Ish-boshet kuwa bai ce wa Abner uffan ba, don yana jin tsoronsa.

12 Sai Abner ya aiki manzanni zuwa wurin Dawuda a Hebron, ya ce, “Ƙasar ta wane ne? Ka yi mini alkawari, ni kuwa zan goyi bayanka, in sa dukkan Isra’ilawa su bi ka.”

13 Dawuda ya ce, “Da kyau, zan yi maka alkawari a kan wannan sharaɗi, ba za ka ga fuskata ba sai ka kawo mini matata, Mikal, ‘yar Saul, sa’ad da za ka zo wurina.”

14 Sa’an nan Dawuda ya aiki manzanni zuwa wurin Ish-boshet, ɗan Saul, ya ce, “Ka ba ni matata, Mikal, wadda na biya sadakinta da loɓa ɗari ta Filistiyawa.”

15 Sai Ish-boshet ya aika aka ƙwato Mikal daga wurin mijinta, Falti, ɗan Layish.

16 Mijinta ya bi ta yana ta kuka har zuwa Bahurim. Sai Abner ya ce masa ya koma, ya kuwa koma.

17 Abner ya shawarci dattawan Isra’ila, ya ce, “Dā ma can kuna so Dawuda ya sarauce ku.

18 To, yanzu sai ku yarda ya sarauce ku, gama Ubangiji ya yi wa Dawuda alkawari ya ce, ‘Ta hannun bawana, Dawuda, zan ceci jama’ar Isra’ila daga hannun Filistiyawa, da na dukan abokan gābansu.’ ”

19 Abner kuma ya yi magana da mutanen Biliyaminu, sa’an nan ya tafi ya faɗa wa Dawuda a Hebron abin da dukan Isra’ilawa da dukan kabilar Biliyaminu suka ga ya yi kyau, su yi.

20 Abner tare da mutum ashirin suka zo wurin Dawuda a Hebron, Dawuda kuwa ya yi musu liyafa.

21 Sai Abner ya ce wa Dawuda, “Zan tashi in tafi in tattara wa ubangijina sarki dukan Isra’ilawa, domin su yi alkawari da kai, kai kuma ka sarauce su yadda kake so.” Dawuda kuwa ya sallami Abner, ya tafi lafiya.

An Kashe Abner

22 Sai ga barorin Dawuda da Yowab sun komo daga hari. Sun kawo ganima mai yawa. Abner kuwa ya riga ya tafi, gama Dawuda ya riga ya sallame shi, ya tafi lafiya.

23 Da Yowab da sojojin da suke tare da shi suka iso, sai aka faɗa masa cewa, “Abner ɗan Ner ya zo wurin sarki, sarki kuwa ya bar shi ya tafi lafiya.”

24 Sai Yowab ya tafi wurin sarki ya ce, “Me ke nan ka yi? Abner ya zo wurinka, me ya sa ka bar shi ya tafi lafiya?

25 Ka sani Abner ɗan Ner ya zo ya ruɗe ka ne, ya san fitarka da shigarka, ya kuma san dukan abin da kake yi.”

26 Da Yowab ya fita daga wurin Dawuda, sai ya aiki manzanni su bi bayan Abner. Suka komo da shi a rijiyar Sira, amma Dawuda bai sani ba.

27 Sa’ad da Abner ya komo Hebron, sai Yowab ya raɓa da shi wajen ƙofar garin kamar zai gana da shi, sai ya soke shi a ruwan ciki, ya fāɗi ya mutu, saboda alhakin jinin ɗan’uwansa, Asahel.

28 Daga baya sa’ad da Dawuda ya ji, sai ya ce, “Ni da mulkina baratattu ne a gaban Ubangiji daga alhakin jinin Abner ɗan Ner har abada.

29 Allah ya sa alhakin jinin ya faɗa kan Yowab da dukan gidan ubansa. Ya sa kada a rasa mai ɗiga, ko kuturu, ko wanda yake dogara sanda, ko wanda aka kashe da takobi, ko wanda ba shi da abinci, a gidan Yowab.”

30 Ta haka Yowab da ɗan’uwansa Abishai suka kashe Abner saboda ya kashe ƙanensu, Asahel, a wurin yaƙi a Gibeyon.

31 Dawuda kuwa ya ce wa Yowab da dukan mutanen da suke tare da shi, “Ku kyakketa tufafinku, ku sa tsummoki, ku yi makoki domin Abner.” Sarki Dawuda kuwa ya bi bayan makara.

32 Suka binne Abner a Hebron. Sarki ya ta da murya ya yi kuka a kabarin Abner. Dukan mutane kuma suka yi kuka.

33 Sarki ya yi wannan makoki domin Abner, ya ce,

“Don me Abner zai mutu kamar wawa?

34 Hannuwansa ba a ɗaure suke ba,

Ƙafafunsa kuma ba a dabaibaye suke ba.

Ya mutu kamar wanda mugayen mutane suka kashe.”

Dukan mutane suka yi kuka kuma saboda shi.

35 Mutane kuwa suka zo su ba Dawuda magana, ko ya ci abinci tun rana ba ta faɗi ba. Amma Dawuda ya rantse ya ce, “Allah ya buge ni in mutu nan, idan na ɗanɗana abinci ko wani abu kafin rana ta faɗi.”

36 Da mutanen suka lura, sai suka yarda da abin da sarki ya yi, suka kuma ji daɗin kowane abu da sarki ya yi.

37 A wannan rana dukan mutanen Dawuda da dukan mutanen Isra’ila suka gane, ashe, ba nufin Dawuda ba ne a kashe Abner ɗan Ner.

38 Sarki ya ce wa fādawansa, “Ba ku sani ba, basarake ne, babban mutum ne kuma ya faɗi a cikin Isra’ila yau?

39 Yau na raunana, ko da yake ni sarki ne naɗaɗɗe. Waɗannan mutane, ‘ya’yan Zeruya, sun fi ƙarfina, Ubangiji ya sāka wa mai aikata mugunta da muguntar da ya aikata.”