Categories
2 SAM

2 SAM 4

An Kashe Ish-boshet

1 Da Ish-boshet, ɗan Saul, ya ji labari Abner ya mutu a Hebron, sai gabansa ya faɗi. Dukan mutanen Isra’ila kuma suka tsorata.

2 Shi ɗan nan na Saul yana da shugabanni biyu na ‘yan hari, su ne Ba’ana da Rekab, ‘ya’yan Rimmon na ƙasar Biliyaminu daga Biyerot, (gama an lasafta Biyerot cikin yankin ƙasar Biliyaminu.

3 Mutanen Biyerot sun gudu zuwa Gittayim inda suke zaman baƙunci har wa yau.)

4 Jonatan, ɗan Saul kuwa, yana da ɗa, sunansa Mefiboshet, amma gurgu ne. Yana da shekara biyar sa’ad da aka kawo labarin mutuwar Saul da Jonatan daga Yezreyel. Sai mai renonsa ta ɗauke shi, ta sheƙa a guje. A sa’ad da take gudu sai ya faɗo, sanadin gurguntakar ke nan.

5 Rekab da Ba’ana ‘ya’yan Rimmon suka tafi gidan Ish-boshet da tsakar rana, a lokacin da yake shaƙatawa.

6 Rekab da Ba’ana kuwa, suka laɓaɓa, suka shiga kamar suna neman alkama.

7 Da suka shiga gidan, sai suka iske shi yana kwance a ɗakin kwanansa. Suka buge shi, suka kashe shi, suka datse kansa. Suka ɗauki kansa suka bi ta hanyar Araba, suka yi tafiya dare farai.

8 Suka kai wa Dawuda kan Ish-boshet a Hebron. Suka ce wa sarki Dawuda, “Ga kan Ish-boshet ɗan maƙiyinka, Saul, wanda ya nemi ranka. Ubangiji ya rama wa sarki a kan Saul da zuriyarsa yau.”

9 Amma Dawuda ya ce wa Rekab da Ba’ana, ‘ya’yan Rimmon, mutumin Biyerot, “Na rantse da Ubangiji wanda ya fanshe ni daga kowace masifa,

10 sa’ad da wani ya kawo mini labari cewa, ‘Saul ya mutu,’ mutumin ya yi tsammani albishir ne ya kawo mini, sai na kama shi na kashe shi a Ziklag. Ladan da na ba shi ke nan saboda labarinsa.

11 Balle fa ku da kuke mugayen mutane, da kuka kashe adali a gadonsa, a cikin gidansa, ba sai in nemi hakkin jininsa a hannunku ba, in kawar da ku daga duniya?”

12 Sai Dawuda ya umarci samarinsa su kashe su. Suka datsa hannunsu da ƙafafunsu, suka rataye su a gefen tafkin Hebron. Amma suka ɗauki kan Ish-boshet suka binne a cikin kabarin Abner a Hebron.

Categories
2 SAM

2 SAM 5

Dawuda Ya Zama Sarkin Isra’ilawa da Yahudawa

1 Dukan kabilan Isra’ila kuwa suka zo wurin Dawuda a Hebron, suka ce, “Ga shi, mu ‘yan’uwanka ne.

2 A dā sa’ad da Saul yake sarautarmu, kai kake bi da Isra’ilawa zuwa yaƙi, kai kake komo da su. Ubangiji kuma ya ce maka, ‘Kai za ka lura da jama’ata Isra’ila, za ka zama sarkinsu.’ ”

3 Sai dukan dattawan Isra’ila suka tafi wurin sarki Dawuda a Hebron, shi kuwa ya yi alkawari da su a gaban Ubangiji. Su kuwa suka naɗa shi Sarkin Isra’ila duka.

4 Dawuda ya ci sarauta yana da shekara talatin. Ya yi shekara arba’in yana sarauta.

5 Ya yi sarautar jama’ar Yahuza shekara bakwai da wata shida a Hebron. Ya kuma yi sarautar jama’ar Isra’ila duk da Yahuza shekara talatin da uku a Urushalima.

Dawuda Ya Ci Sihiyona

6 Sarki Dawuda da mutanensa suka tafi Urushalima su yaƙi Yebusiyawa mazaunan ƙasar. Su kuwa suka ce wa Dawuda, “Ba za ka iya zuwa nan ba, makafi kawai da guragu za su kore ka.” A zatonsu Dawuda ba zai iya zuwa can ba.

7 Duk da haka Dawuda ya ci kagarar Sihiyona, wato birnin Dawuda.

8 A ran nan Dawuda ya ce, “Duk wanda zai kashe Yebusiyawa, to, sai kuma ya haura zuwa wuriyar ruwa ya fāɗa wa guragu da makafi waɗanda ran Dawuda yake ƙi.” Don haka a kan ce, “Makafi da guragu ba za su shiga Haikali ba.”

9 Dawuda ya zauna a kagara. Ya ba ta suna Birnin Dawuda. Ya kuma yi gine-gine kewaye da wurin. Ya fara daga Millo zuwa ciki.

10 Dawuda kuwa ya ƙasaita, gama Ubangiji Allah Mai Runduna yana tare da shi.

Hiram Sarkin Taya Ya Yarda da Dawuda

11 Hiram Sarkin Taya ya aiki jakadu zuwa wurin Dawuda. Ya kuma aika masa da katakan itacen al’ul, da kafintoci, da masu yin gini da duwatsu, suka kuwa gina wa Dawuda gida.

12 Dawuda kuwa ya gane lalle Ubangiji ya tabbatar da shi sarki bisa jama’ar Isra’ila, ya kuma ɗaukaka mulkinsa saboda mutanensa, Isra’ila.

‘Ya’yan da aka Haifa wa Dawuda a Urushalima

13 Bayan zuwan Dawuda Urushalima daga Hebron, sai ya ɗauki waɗansu ƙwaraƙwarai, ya kuma auri waɗansu mata. Aka kuma haifa masa waɗansu ‘ya’ya mata da maza.

14 Sunayen ‘ya’yan da aka haifa masa a Urushalima ke nan, Shimeya, da Shobab, da Natan, da Sulemanu,

15 da Ibhar, da Elishuwa, da Nefeg, da Yafiya,

16 da Elishama, da Eliyada, da Elifelet.

Dawuda Ya Ci Nasara a kan Filistiyawa

17 Sa’ad da Filistiyawa suka ji an naɗa Dawuda ya zama Sarkin Isra’ila, sai dukansu suka haura zuwa neman ran Dawuda. Da Dawuda ya ji Filistiyawa suna nemansa, sai ya gangara zuwa kagara.

18 Filistiyawa kuwa suka zo suka bazu a kwarin Refayawa.

19 Dawuda kuwa ya yi roƙo ga Ubangiji, ya ce, “Ko in tafi in yi yaƙi da Filistiyawa? Za ka bashe su a hannuna?”

Ubangiji kuwa ya ce masa, “Ka haura, gama hakika, zan ba da Filistiyawa a hannunka.”

20 Sai Dawuda ya zo Ba’al-ferazim, ya ci Filistiyawa a wurin. Sa’an nan ya ce, “Ubangiji ya huda abokan gabana a idona kamar rigyawa.” Saboda haka aka sa wa wurin suna, “Ubangiji Mai Hudawa.”

21 Filistiyawa suka gudu, suka bar gumakansu a nan, Dawuda da mutanensa suka kwashe su.

22 Filistiyawa suka sāke haurawa, suka bazu a kwarin Refayawa.

23 Dawuda ya kuma roƙi Ubangiji. Ubangiji kuwa ya ce masa, “Kada ka haura zuwa wurinsu gaba da gaba, amma ka bi ta bayansu, ka ɓullo musu daura da itatuwan doka.

24 Sa’ad da ka ji motsin rausayawar rassan itatuwan doka, sai ka yi maza, ka faɗa musu, gama Ubangiji zai wuce gaba domin ya bugi rundunar Filistiyawa.”

25 Sai Dawuda ya yi yadda Ubangiji ya umarce shi. Ya yi ta bugun Filistiyawa tun daga Geba har zuwa Gezer.

Categories
2 SAM

2 SAM 6

Dawuda Ya Kawo Akwatin Alkawari a Urushalima

1 Dawuda kuma ya tattara zaɓaɓɓun mutane dubu talatin (30,000) na Isra’ila.

2 Sai ya tafi tare da su duka zuwa Kiriyat-yeyarim domin ya kawo akwatin Alkawarin Allah, wanda ake kira da sunan Ubangiji Mai Runduna wanda yake zaune a tsakanin kerubobin.

3-4 Suka ɗauko akwatin alkawarin Allah daga gidan Abinadab, wanda yake bisa tudu. Suka sa akwatin alkawari a sabuwar karusa. Uzza da Ahiyo, ‘ya’yan Abinadeb, maza, suka bi da karusar da akwatin alkawarin Allah yake ciki. Ahiyo ne yake tafiya a gaban akwatin alkawarin.

5 Sai Dawuda da Isra’ilawa duka suka yi rawa sosai don farin ciki a gaban Ubangiji. Aka yi ta raira waƙoƙi, ana kaɗa molaye, da garayu, da goge, da kacakaura, da kuge.

6 Da suka zo masussukar Kidon, sai Uzza ya miƙa hannunsa ya riƙa akwatin alkawarin Allah, gama takarkaran sun yi kwarangyasa.

7 Ubangiji ya husata da Uzza, ya buge shi, ya mutu nan take kusa da akwatin alkawarin Allah, saboda ya taɓa akwatin alkawari.

8 Sai Dawuda ya ji haushi domin Ubangiji ya fashe haushinsa a kan Uzza. Aka sa wa wurin suna Feresauzza har wa yau.

9 Dawuda kuwa ya ji tsoron Ubangiji a ran nan, ya ce, “Ƙaƙa zan ajiye akwatin alkawarin Ubangiji a wurina?”

10 Domin haka Dawuda bai yarda ya kai akwatin alkawarin Ubangiji cikin Birnin Dawuda ba, sai ya kai shi gidan Obed-edom Bagitte.

11 Akwatin alkawarin Ubangiji yana a gidan Obed-edom Bagitte har wata uku. Ubangiji kuwa ya sa wa Obed-edom da dukan iyalinsa albarka.

An Iso da Akwatin Alkawari a cikin Urushalima

12 Aka faɗa wa Dawuda sarki, cewa, Ubangiji ya sa wa gidan Obed-edom albarka, da dukan abin da yake da shi saboda akwatin alkawarin Allah. Sai Dawuda ya tafi da murna ya kawo akwatin alkawarin Allah daga gidan Obed-edom zuwa Birnin Dawuda.

13 Sa’ad da masu ɗaukar akwatin alkawarin Ubangiji suka yi tafiya taki shida, sai Dawuda ya yi hadaya da sa, da keɓaɓɓiyar tunkiya.

14 Dawuda ya sa falmaran ta lilin. Ya kuwa yi rawa da dukan ƙarfinsa a gaban Ubangiji.

15 Shi da mutanen Isra’ila duka suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji da sowa da busar ƙaho.

16 Sa’ad da akwatin alkawarin Ubangiji ya shiga Birnin Dawuda, sai Mikal, ‘yar Saul, ta leƙa ta taga, ta ga sarki Dawuda yana tsalle, yana rawa a gaban Ubangiji, sai ta raina shi a zuci.

17 Suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji, suka ajiye shi a wurinsa a cikin alfarwar da Dawuda ya kafa dominsa. Dawuda ya miƙa hadayun ƙonawa da na salama a gaban Ubangiji.

18 Sa’ad da ya gama miƙa hadayun ƙonawa da na salama, sai ya sa wa mutanen albarka da sunan Ubangiji Mai Runduna.

19 Ya kuma rarraba wa dukan taron jama’ar Isra’ila, mata da maza, ƙosai, da nama, da zabibi, sa’an nan dukan mutane suka watse, kowa ya tafi gidansa.

20 Da Dawuda ya komo gida domin ya sa wa iyalinsa albarka, Mikal, ‘yar Saul, ta fito domin ta tarye shi, ta ce masa, “Ƙaƙa Sarkin Isra’ila ya ɗauki kansa yau? Ya kware darajarsa a gaban barorinsa mata kamar yadda shakiyyai suke yi.”

21 Sai Dawuda ya ce wa Mikal, “Ai, na yi wannan a gaban Ubangiji wanda ya zaɓe ni a madadin mahaifinki da iyalinsa, ya naɗa ni in zama Sarkin Isra’ila, wato jama’ar Ubangiji. Lalle zan yi rawar farin ciki a gaban Ubangiji.

22 Zan mai da kaina abin raini fiye da haka, zan kuma zama abin raini gare ki, amma barori mata da kika ambata, za su girmama ni.”

23 Mikal, ‘yar Saul fa, ba ta haihu ba har ta rasu.

Categories
2 SAM

2 SAM 7

Alkawarin Allah da Dawuda

1 Sa’ad da sarki yake zaune a gidansa, Ubangiji kuma ya hutasshe shi daga fitinar abokan gābansa da suke kewaye da shi,

2 sai sarki ya ce wa annabi Natan, “Duba, ga shi, ina zaune a gidan katakon al’ul, amma akwatin alkawarin Ubangiji yana a alfarwa.”

3 Natan kuwa ya ce wa sarki, “Sai ka yi abin da yake a zuciyarka, gama Ubangiji yana tare da kai.”

4 Amma a daren nan Ubangiji ya yi magana da Natan.

5 Ya ce, “Tafi, ka faɗa wa bawana Dawuda, ka ce, in ji Ubangiji, ‘Ɗakin zama za ka gina mini?

6 Har wa yau ban taɓa zama a ɗaki ba, tun lokacin da na fito da Isra’ilawa daga Masar, amma a alfarwa nake kai da kawowa daga wannan wuri zuwa wancan.

7 A cikin kai da kawowata tare da dukan jama’ar Isra’ila ban taɓa ce wa wani daga cikin shugabannin Isra’ila waɗanda na sa su lura da jama’ata Isra’ila, ya gina mini ɗaki na katakon al’ul ba.’

8 Abin da za ka faɗa wa bawana Dawuda ke nan, in ji Ubangiji Mai Runduna, ‘Na ɗauko ka daga makiyaya inda kake kiwon tumaki domin ka zama sarkin jama’ata Isra’ila.

9 Ban kuwa rabu da kai ba duk inda ka tafi, na kuma kawar da abokan gābanka duka. Zan sa ka shahara kamar shahararrun mutane na duniya.

10-11 Zan nuna wa jama’ata Isra’ila wuri na kansu inda zan kafa su su zauna. Ba wanda zai sāke damunsu. Mugayen mutane kuma ba za su ƙara wahalshe su kamar dā ba, tun lokacin da na naɗa wa jama’ata Isra’ila mahukunta. Zan hutar da kai daga fitinar abokan gābanka duka. Banda wannan kuma ina shaida maka, cewa, zan sa gidanka ya kahu.

12 Sa’ad da kwanakinka suka ƙare, za ka rasu tare da kakanninka. A bayanka, zan ta da ɗanka, na cikinka. Zan sa mulkinsa ya kahu.

13 Shi ne zai gina mini ɗaki. Ni kuwa zan tabbatar da kursiyin sarautarsa har abada.

14 Zan zama uba gare shi, zai kuma zama ɗa a gare ni. Sa’ad da ya yi laifi zan hukunta shi da sanda kamar yadda mutane suke yi. Zan yi masa bulala kamar yadda ‘yan adam suke yi.

15 Amma ba zan daina nuna masa madawwamiyar ƙaunata ba, kamar yadda na yi wa Saul wanda na kawar daga fuskata.

16 Gidanka kuwa da mulkinka za su dawwama a gabana har abada. Gadon sarautarka kuma zai kahu har abada.’ ”

17 Haka kuwa Natan ya faɗa wa Dawuda dukan abin da Allah ya bayyana masa.

Addu’ar Dawuda ta Godiya

18 Sarki Dawuda ya tafi ya zauna a gaban Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Allah, ko ni ko iyalina ba mu cancanci dukan abin da ka yi mana ba.

19 Ga shi, ka ƙara fiye da haka, ya Ubangiji Allah, gama ka yi magana, cewa, gidan bawanka zai kai kwanaki masu tsawo. Wannan ka’ida ce ta ‘yan adam!

20 Me kuma zan ƙara ce maka, gama ka san bawanka, ya Ubangiji Allah.

21 Bisa ga alkawarinka da yardar zuciyarka ne ka aikata waɗannan manyan al’amura domin ka sa in san su.

22 Bisa ga dukan abin da muka ji, kai mai girma ne, ya Ubangiji Allah. Ba kamarka, in banda kai kuma babu wani Allah.

23 Ba wata al’umma kuma a duniya wadda take kama da jama’arka Isra’ila, wadda kai Allah ka fansa ta zama jama’arka. Ka mai da kanka sananne. Ka yi wa jama’arka manyan abubuwa masu banmamaki. Ka kori al’ummai da gumakansu a gaban jama’arka, waɗanda ka fansa daga Masar.

24 Ka zaɓar wa kanka jama’ar Isra’ila su zama mutanenka har abada. Kai kuma, ya Ubangiji, ka zama Allahnsu.

25 “Ya Ubangiji Allah, yanzu ka tabbatar da maganar da ka yi da bawanka da gidansa har abada. Ka aikata bisa ga faɗarka.

26 Za a kuwa ɗaukaka sunanka da cewa, ‘Ubangiji Mai Runduna shi ne Allah na Isra’ila har abada.’ Gidan bawanka Dawuda kuma zai kahu a gabanka.

27 Gama kai, ya Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila, kai ne ka sanar wa ni bawanka, cewa, za ka sa gidana ya kahu, saboda haka ni bawanka na sami ƙarfin halin yin wannan addu’a a gare ka.

28 “Yanzu kuwa, ya Ubangiji Allah, kai ne Allah, kana cika alkawarinka ko yaushe. Ka kuwa yi wa bawanka alkawari mai girma.

29 Ka yarda da farin ciki ka sa wa gidan bawanka albarka domin gidansa ya dawwama a gabanka har abada, gama kai ne ka faɗa, ya Ubangiji Allah. Ka sa albarkarka ta tabbata a gidan bawanka har abada.”

Categories
2 SAM

2 SAM 8

Yaƙe-Yaƙen Dawuda

1 Bayan haka kuma sai Dawuda ya ci Filistiyawa da yaƙi, ya kawo ƙarshen mulkinsu a ƙasar.

2 Sa’an nan ya ci Mowabawa da yaƙi. Ya sa su su kwanta a ƙasa sa’an nan ya riƙa auna su da igiya, kowane awo biyu ya sa a kashe su, awo na uku kuwa sai ya sa a bar su da rai. Mowabawa suka zama talakawansa, suka riƙa kawo haraji.

3 Dawuda kuma ya ci Hadadezer ɗan Rehob, Sarkin Zoba, da yaƙi lokacin da shi Hadadezer yake kan tafiya zuwa Kogin Yufiretis don ya tabbatar da ikonsa a wurin.

4 Dawuda ya ƙwace masa mahayan dawakai dubu ɗaya da ɗari bakwai (1,700), da sojojin ƙafa dubu ashirin (20,000). Dawuda ya yanyanke agarar dawakan, sai dai doki ɗari ne ya bari.

5 Suriyawan Dimashƙu kuwa, suka zo don su taimaki Hadadezer, Sarkin Zoba, Dawuda kuwa ya kashe Suriyawa dubu ashirin da dubu biyu (22,000).

6 Sa’an nan ya ajiye ƙungiyoyin sojojinsa a Suriya ta Dimashƙu. Suriyawa suka zama talakawan Dawuda, suka riƙa kawo masa haraji. Duk inda Dawuda ya tafi, Ubangiji yakan taimake shi.

7 Dawuda ya kwashe garkuwoyi na zinariya waɗanda shugabannin sojojin Hadadezer suka riƙe, ya kawo su Urushalima.

8 Ya kuma kwashe tagulla da yawa daga Beta da Berotayi biranen Hadadezer.

9 Sa’ad da Toyi Sarkin Hamat ya ji labari Dawuda ya ci dukan rundunar Hadadezer da yaƙi,

10 sai ya aiki Adoniram ɗansa wurin sarki Dawuda don ya gaishe shi, ya kuma yaba masa saboda ya ci Hadadezer da yaƙi, gama Hadadezer yakan yi yaƙi da Toyi kullum. Adoniram kuwa ya kawo wa Dawuda kyautar kayan azurfa, da na zinariya, da na tagulla.

11 Dawuda ya keɓe wa Ubangiji kayayyakin nan tare da azurfa da zinariya da ya karɓe daga dukan al’umman da ya mallaka,

12 wato azurfa da zinariya na Edomawa, da na Mowabawa, da na Ammonawa, da na Filistiyawa, da na Amalekawa, da ganimar Hadadezer ɗan Rehob, Sarkin Zoba.

13 Dawuda kuwa ya yi suna. Ya kashe Edomawa dubu goma sha takwas (18,000) a kwarin Gishiri sa’ad da yake komowa.

14 Sai ya sa ƙungiyoyin sojoji a ƙasar Edom duka. Edomawa suka zama talakawan Dawuda. Ubangiji ya ba Dawuda nasara duk inda ya tafi.

Sarakunan Yaƙi na Dawuda

15 Dawuda ya mallaki Isra’ila duka. Ya yi wa dukan jama’arsa shari’ar gaskiya da adalci.

16 Yowab ɗan Zeruya, shi ne shugaban sojojin. Yehoshafat ɗan Ahilud, shi ne marubuci.

17 Zadok ɗan Ahitub, da Ahimelek ɗan Abiyata, su ne firistoci. Seraiya shi ne magatakarda.

18 Benaiya ɗan Yehoyada, shi ne shugaban Keretiyawa da Feletiyawa, wato matsara. ‘Yan’yan Dawuda, maza, suka zama mataimakansa.

Categories
2 SAM

2 SAM 9

Dawuda ya Nuna wa Mefiboshet Alheri

1 Dawuda ya yi tambaya, ko akwai wani da ya ragu daga gidan Saul, wanda zai nuna wa alheri saboda Jonatan.

2 Akwai wani bara na gidan Saul, sunansa Ziba. Sai aka kirawo shi wurin sarki Dawuda. Sarki ya tambaye shi, “Kai ne Ziba?”

Sai ya amsa, “Ranka ya daɗe, ni ne.”

3 Sa’an nan sarki ya tambaye shi ko akwai wani wanda ya ragu daga gidan Saul, wanda zai nuna masa alherin Allah.

Ziba ya ce wa sarki, “Akwai ɗan Jonatan, gurgu ne kuwa.”

4 Sai sarki ya tambaye shi, “Ina yake?”

Ziba ya ce, “Yana gidan Makir, ɗan Ammiyel a Lodebar.”

5 Sarki kuwa ya aika aka zo da shi daga gidan Makir, ɗan Ammiyel, daga Lodebar.

6 Da aka zo da Mefiboshet, ɗan Jonatan, wato jikan Saul, sai ya rusuna har ƙasa, ya yi gaisuwa. Dawuda ya ce, “Mefiboshet!”

Ya amsa, “Ranka ya daɗe, ga baranka.”

7 Dawuda ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, gama zan yi maka alheri ne saboda mahaifinka, Jonatan. Zan mayar maka da dukan gonakin kakanka, Saul. Kullum kuma za ka riƙa cin abinci a teburina.”

8 Mefiboshet kuwa ya rusuna, ya ce, “Ni wane ne har da za ka kula da ni, ni da ban fi mataccen kare daraja ba?”

9 Sa’an nan sarki ya kira Ziba, baran Saul, ya ce masa, “Dukan abin da yake na Saul, da dukan abin da yake na iyalinsa, na ba ɗan maigidanka.

10 Kai, da ‘ya’yanka maza, da barorinka za ku riƙa yi wa iyalin Saul noma, ku kawo musu amfanin domin su sami abinci, amma Mefiboshet kansa, zai riƙa cin abinci a teburina kullum.” (Ziba kuwa yana da ‘ya’ya maza goma sha biyar, da barori ashirin.)

11 Ziba ya amsa wa sarki, ya ce, “Baranka zai yi dukan abin da sarki ya umarta.”

Mefiboshet kuwa ya riƙa cin abinci a teburin sarki kamar ɗaya daga cikin ‘ya’yan sarkin.

12 Mefiboshet yana da ɗa sunansa Mika. Dukan waɗanda suke zaune a gidan Ziba kuma suka zama barorin Mefiboshet.

13 Mefiboshet kuwa ya zauna a Urushalima ya riƙa cin abinci a teburin sarki kullum. Dukan ƙafafunsa kuwa sun naƙasa.

Categories
2 SAM

2 SAM 10

Dawuda ya ci Ammonawa da Suriyawa

1 Sa’ad da Sarkin Ammonawa, wato Nahash, ya rasu, sai Hanun ɗansa ya gāje shi.

2 Dawuda ya ce, “Zan yi wa Hanun alheri kamar yadda tsohonsa ya yi mini.” Dawuda kuwa ya aiki manzanni su yi masa ta’aziyya.

Amma da suka isa can,

3 sai hakiman Ammonawa suka ce wa Hanun shugabansu, “Kana tsammani Dawuda yana girmama tsohonka ne, da ya aiko manzanninsa su yi maka ta’aziyya? Ai, manzannin nan da ya aiko ‘yan leƙen asirin ƙasa ne. Sun zo ne su bincika don su san yadda za a ci birnin.”

4 Sai Hanun ya sa aka aske wa manzannin nan na Dawuda rabin gyammansu suka kuma yanyanke rigunansu daidai ɗuwawu, sa’an nan suka sallame su.

5 Da aka faɗa wa Dawuda sai ya aika a tarye su, gama mutanen sun sha kunya ƙwarai. Sarki Dawuda ya ce musu su zauna a Yariko har gyammansu su toho, sa’an nan su komo.

6 Da Ammonawa suka ga sun sa Dawuda ya yi gāba da su, suka yi sufurin Suriyawan Bet-rehob da na Zoba, mutum dubu ashirin (20,000), suka kuma yi sufurin Sarkin Ma’aka da mutanensa dubu ɗaya, da mutanen Ish-tobi dubu goma sha biyu (12,000).

7 Da Dawuda ya ji labari, sai ya aiki Yowab da dukan rundunar jarumawan.

8 Ammonawa suka fita suka ja dāgar yaƙi a ƙofar garin, amma Suriyawan Zoba da na Rehob, da mutanen Ish-tobi da na Ma’aka suka ja tasu dāgar a karkara.

9 Da Yowab ya ga an ja masa dāgar yaƙi gaba da baya, sai ya zaɓi waɗansu Isra’ilawa, ya sa su gabza da Suriyawa.

10 Sauran mutane kuwa ya sa su a hannun Abishai, ƙanensa. Ya sa su gabza da Ammonawa.

11 Ya ce musu, “Idan Suriyawa sun fi ƙarfina, ku kawo mini gudunmawa, amma idan Ammonawa sun fi ƙarfinku, sai in kai muku gudunmawa.

12 Mu yi ƙarfin hali, mu yi jaruntaka saboda jama’armu da biranen Allahnmu. Ubangiji ya yi abin da ya gamshe shi.”

13 Sa’an nan Yowab da mutanensa suka matsa, su gabza da Suriyawa. Suriyawa kuwa suka gudu.

14 Da Ammonawa suka ga Suriyawa sun gudu, su ma suka gudu daga gaban Abishai suka shiga birnin. Sa’an nan Yowab ya komo Urushalima daga wurin yaƙi da Ammonawa.

15 Sa’ad da Suriyawa suka ga Isra’ilawa sun ci su, suka tattara kansu.

16 Hadadezer ya aika aka kawo Suriyawan da suke a hayin Kogin Yufiretis. Suka taru a Helam. Shobak shugaban rundunar Hadadezer shi ne ya shugabance su.

17 Sa’ad da Dawuda ya ji labari, ya tara Isra’ilawa duka, ya haye Urdun zuwa Helam. Suriyawa kuwa suka ja dāgar yaƙi, suka yi yaƙi da Dawuda.

18 Amma Suriyawa suka gudu daga gaban Isra’ilawa. Dawuda kuwa ya kashe Suriyawa, mahayan karusai ɗari bakwai, da mahayan dawakai dubu arba’in (40,000). Aka yi wa Shobak shugaban rundunarsu rauni wanda ya zama ajalinsa, a can ya rasu.

19 Sa’ad da dukan hakiman Hadadezer suka ga Isra’ilawa sun ci su, sai suka yi sulhu da Isra’ilawa. Suka zama talakawansu. Wannan ya sa Suriyawa suka ji tsoron ƙara kai wa Ammonawa gudunmawa.

Categories
2 SAM

2 SAM 11

Dawuda da Bat-Sheba

1 Da bazara lokacin da sarakuna sukan fita zuwa yaƙi, Dawuda ya aiki Yowab, da shugabannin sojojinsa, da sojojin Isra’ila duka. Suka tafi suka ragargaza Ammonawa, suka kuma kewaya Rabba da yaƙi. Amma Dawuda ya yi zamansa a Urushalima.

2 Wata rana da yamma Dawuda ya tashi daga shaƙatawa, yana yawo a kan rufin soron fādarsa, can ya hangi wata kyakkyawar mata tana wanka.

3 Sai ya aika a bincika ko wace ce wannan mata, ashe, ‘yar Ammiyel ce, matar Uriya Bahitte.

4 Dawuda kuwa ya aiki waɗansu manzanni suka kawo masa ita, ya kwana da ita. (A lokacin kuwa ta gama wankan haila ke nan.) Sa’an nan ta koma gidanta.

5 Matar kuwa ta yi juna biyu, sai ta aika a faɗa wa Dawuda, cewa, tana da ciki.

6 Dawuda kuwa ya aika wurin Yowab ya ce, “Ka aiko mini da Uriya Bahitte.” Yowab kuwa ya aika da Uriya wurin Dawuda.

7 Da Uriya ya iso, sai Dawuda ya tambaye shi labarin Yowab, da lafiyar jama’ar, da labarin yaƙin.

8 Ya kuma ce masa, “Ka tafi gidanka, ka wanke ƙafafunka.” Da Uriya ya fita daga gidan sarki, sarki ya ba da kyauta a kai masa.

9 Amma Uriya bai tafi gidansa ba, sai ya kwana a ƙofar gidan sarki tare da sauran barorin sarki.

10 Da aka faɗa wa Dawuda, cewa, Uriya bai tafi gidansa ba, Dawuda ya kira Uriya ya ce masa, “Ka dawo daga tafiya, me ya sa ba ka tafi gidanka ba?”

11 Uriya ya ce wa Dawuda, “Akwatin alkawari, da mutanen Isra’ila, da na Yahuza, suna zaune a bukkoki. Shuganana Yowab, da barorinsa suna zaune a sansani a karkara, ƙaƙa ni zan tafi gidana in ci in sha, in kwanta da matata? Na rantse da ranka, ba zan yi haka ba.”

12 Dawuda kuma ya ce wa Uriya, “Ka kwana nan kuma yau, gobe in sallame ka.” Sai Uriya ya kwana a Urushalima a ran nan.

13 Kashegari kuma Dawuda ya kira shi liyafa. Ya zo, ya ci ya sha tare da shi, har Dawuda ya sa shi ya bugu. Amma da dare, sai ya tafi ya kwanta a shimfiɗarsa tare da sauran barorin sarki, amma bai tafi gidansa ba.

14 Da safe Dawuda ya rubuta wasiƙa, ya ba Uriya ya kai wa Yowab.

15 A wasiƙar ya ce wa Yowab, “Tura Uriya a gaba a inda yaƙin ya fi zafi, sa’an nan ku ja da baya, ku bar shi don a buge shi a kashe shi.”

16 Sa’ad da Yowab yake kama garin da yaƙi, sai ya sa Uriya a inda ya sani akwai jarumawan gaske.

17 Mutanen garin suka fito suka yi yaƙi da Yowab. Suka kashe waɗansu daga cikin sojojin Dawuda. Uriya Bahitte, shi ma aka kashe shi.

18 Sai Yowab ya aika aka faɗa wa Dawuda labarin yaƙin.

19-20 Ya ce wa manzo, “Bayan da ka gama faɗa wa sarki labarin yaƙin duka, idan sarki ya husata, har ya ce maka, ‘Me ya sa kuka tafi yaƙi kurkusa da garin? Ba ku sani ba za su tsaya a gefen garu daga ciki su yi harbi?

21 Wa ya kashe Abimelek ɗan Yerubba’al? Ba mace ce a TebEze ta jefe shi da ɗan dutsen niƙa ta kan garu daga ciki ta kashe shi ba? Me ya sa kuka tafi kusa da garu?’ Sai ka faɗa masa cewa, ‘Baranka, Uriya Bahitte, shi ma an kashe shi.’ ”

22 Manzon kuwa ya tafi ya faɗa wa Dawuda dukan abin da Yowab ya ce.

23 Ya ce, “Abokan gābanmu sun sami sa’a a kanmu. Sun fito su gabza da mu a karkara, amma muka kore su zuwa cikin ƙofar garin.

24 Sai maharba suka tsaya a kan garu daga ciki suka yi ta harbin barorinka. Waɗansu daga cikin barorin sarki sun mutu. Baranka Uriya Bahitte shi ma ya matu.”

25 Dawuda ya ce wa manzon, “Je ka ka faɗa wa Yowab kada wannan abu ya dame shi, ai, takobi ba ya tarar wanda zai kashe. Ku ƙara matsa wa garin lamba, ku faɗa masa har ku ragargaza shi. Ka ƙarfafa Yowab.”

26 Sa’ad da matar Uriya ta ji labarin mutuwar mijinta, ta yi makoki dominsa.

27 Da kwanakin makokin suka ƙare, sai Dawuda ya aika aka kawo ta gidansa, ta zama matarsa, ta haifa masa ɗa. Amma Ubangiji bai ji daɗin mugun abin nan da Dawuda ya yi ba.

Categories
2 SAM

2 SAM 12

Natan Ya Tsauta wa Dawuda

1 Sai Ubangiji ya aiki Natan wurin Dawuda. Ya je wurinsa ya ce masa, “Akwai waɗansu mutum biyu a cikin wani gari. Ɗayan basarake ne, attajiri, ɗayan kuwa talaka ne, matalauci.

2 Basaraken yana da garkunan tumaki, da na awaki, da na shanu.

3 Amma talakan ba shi da kome sai ‘yar tunkiyar da ya sayo. Ya yi renonta, ta yi girma a wurinsa, tare da ‘ya’yansa. Takan ci daga cikin ɗan abincinsa, ta kuma sha daga cikin abin shansa, ta kwanta a ƙirjinsa. Ta zama kamar ‘ya a gare shi.

4 Wata rana basaraken ya yi baƙo, amma bai yarda ya kamo daga cikin garkensa ya yanka wa baƙon ba, sai ya kamo ‘yar tunkiyar talakan nan, matalauci, ya yanka wa baƙon da ya zo wurinsa.”

5 Dawuda ya husata ƙwarai a kan mutumin, ya ce wa Natan, “Hakika mutumin da ya yi haka ya cancanci mutuwa.

6 Sai kuma ya biya diyyar ‘yar tunkiya riɓi huɗu, domin ya aikata mugun abu na rashin tausayi.”

7 Sai Natan ya ce wa Dawuda, “Kai ne mutumin. In ji Ubangiji Allah na Isra’ila, ‘Na naɗa ka Sarkin Isra’ila, na cece ka daga hannun Saul.

8 Na kuma ba ka gidan ubangidanka da matansa. Banda wannan kuma na ba ka gidan Isra’ila da na Yahuza. Da a ce wannan ya yi maka kaɗan, da na ƙara maka kuma kamar haka.

9 Me ya sa ka raina maganar Ubangiji, har da ka aikata mugun abu haka a gabansa? Ka kashe Uriya Bahitte ta hannun Ammonawa, ka ɗauki matarsa ta zama matarka.

10 Domin haka takobi ba zai rabu da gidanka ba, domin ka raina ni, ka ɗauki matar Uriya Bahitte ta zama matarka.

11 Na rantse zan sa wani daga cikin iyalinka ya far maka da tashin hankali. A idonka zan ba da matanka ga wani mutum. Zai kwana da su da rana katā.

12 Kai, a ɓoye ka yi naka zunubi, amma zan sa a yi maka a gaban dukan mutanen Isra’ila da rana katā.’ ”

13 Sai Dawuda ya ce wa Natan, “Na yi wa Ubangiji zunubi.”

Natan ya ce masa, “Ubangiji ya gafarta maka, ba za ka mutu ba.

14 Amma domin ka ba da ƙofa ga magabtan Ubangiji su zarge shi, wato saboda abin da ka aikata, ɗan da za a haifa maka zai mutu.”

15 Sa’an nan Natan ya tafi gida.

Ɗan Dawuda Ya Mutu, aka Haifi Sulemanu

Ubangiji kuwa ya sa ciwo ya kama yaron da matar Uriya ta haifa wa Dawuda.

16 Dawuda kuwa ya roƙi Allah saboda yaron. Ya yi azumi. Ya shiga ya kwanta a ƙasa dukan dare.

17 Sai fādawansa suka zo suka kewaye shi, don su tashe shi daga ƙasa, amma bai yarda ba, bai kuma ci abinci tare da su ba.

18 An kwana bakwai sai yaron ya mutu. Fādawansa suka ji tsoron faɗa masa rasuwar yaron. Suka ce wa junansu, “Ga shi, tun lokacin da yaron yake da rai mun yi masa magana, amma bai kasa kunne gare mu ba, yaya za mu iya faɗa masa rasuwar yaron? Zai yi wa kansa ɓarna.”

19 Da Dawuda ya ga fādawansa suna raɗa da juna, sai ya gane lalle yaron ya rasu. Ya tambaye su, ya ce, “Yaron ya rasu ne?”

Suka amsa cewa, “I, ya rasu.”

20 Sai Dawuda ya tashi daga ƙasa, ya yi wanka, ya shafa mai, ya sake tufafinsa, ya tafi ɗakin sujada, ya yi sujada, sa’an nan ya koma gidansa ya ce a kawo abinci. Suka kawo masa abinci ya ci.

21 Fādawansa suka ce masa, “Me ka yi ke nan? Ka yi azumi, ka yi kuka saboda yaron tun yana da rai, amma da yaron ya rasu ka tashi, ka ci abinci.”

22 Ya ce musu, “Tun yaron yana da rai, na yi azumi da kuka, ina cewa wa ya sani, ko Ubangiji zai yi mini jinƙai, ya bar yaron da rai?

23 Amma yanzu ya rasu, me zai sa kuma in yi azumi? Zan iya koma da shi ne? Ni zan tafi wurinsa, amma shi ba zai komo wurina ba.”

24 Sa’an nan Dawuda ya yi wa Batsheba, matarsa, ta’aziyya. Ya shiga wurinta, ya kwana da ita. Ta haifa masa ɗa. Ya raɗa masa suna Sulemanu. Ubangiji kuwa ya ƙaunace shi,

25 ya kuma umarci annabi Natan ya raɗa wa yaron suna Yedideya, wato ƙaunataccen Ubangiji.

Dawuda ya ci Rabba da Yaƙi

26 Yowab kuwa ya yi yaƙi da Rabba ta Ammonawa, yana kuwa gab da cin birnin.

27 Sai ya aiki manzanni wurin Dawuda ya ce, “Na yaƙi Rabba, na kama hanyar samun ruwansu.

28 Yanzu ka tara sauran sojoji ka fāɗa wa birnin, ka ci shi da kanka. Gama ba na so in yi suna da cin birnin.”

29 Saboda haka sai Dawuda ya tara sauran sojoji duka, ya tafi Rabba, ya yi yaƙi da ita, ya kuwa ci birnin.

30 Sarkinsu, wato Milkom, yana da kambi na zinariya a kansa, nauyinsa ya kai talanti ɗaya na zinariya yana kuma da duwatsu masu daraja cikinsa. Dawuda kuwa ya ɗauke kambin daga kan sarkin ya sa a nasa. Sa’an nan ya kwaso ganima mai ɗumbun yawa daga cikin birnin.

31 Ya kuma kamo mutanen da suke cikin birnin, ya sa su su yi aiki da zartuka, da faretani, da gatura. Ya kuma sa su yi tubula. Haka Dawuda ya yi da dukan biranen Ammonawa. Sa’an nan Dawuda da dukan sojojinsa suka koma Urushalima.

Categories
2 SAM

2 SAM 13

Amnon da Tamar

1 Absalom, ɗan Dawuda, yana da kyakkyawar ƙanwa, sunanta Tamar. Ana nan Amnon ɗaya daga cikin ‘ya’yan Dawuda, ya ƙaunace ta.

2 Amnon ya matsu har ya fara ciwo saboda Tamar ƙanwarsa. Ita kuwa budurwa ce, ba shi yiwuwa Amnon ya yi wani abu da ita.

3 Amma Amnon yana abuta da Yonadab, ɗan Shimeya, ɗan’uwan Dawuda. Yonadab kuwa yana da hila.

4 Sai ya ce masa, “Ya ɗan sarki, me ya sa kake damuwa kowace rana? Ba za ka faɗa mini ba?”

Sai Amnon ya ce masa, “Na jarabtu ne da Tamar ƙanwar ɗan’uwana Absalom.”

5 Yonadab kuwa ya ce masa, “Kwanta a gadonka ka yi kamar kana ciwo, lokacin da mahaifinka ya zo domin ya duba ka, sai ka ce masa, ‘A bar ƙanwata Tamar ta zo ta ba ni abinci, ta riƙa shirya abincin a idona, don in gani in kuma riƙa ci daga hannunta.’ ”

6 Amnon kuwa ya kwanta, ya yi kamar yana ciwo.

Sa’ad da sarki ya zo duba shi, sai Amnon ya ce wa sarki, “Ina roƙo a sa ƙanwata, Tamar, ta zo ta toya mini waina a inda nake, ta riƙa ba ni da hannunta ina ci.”

7 Sai Dawuda ya aika gida, wurin Tamar, ya ce, “Tafi gidan Amnon wanki, ki shirya masa abinci.”

8 Tamar kuwa ta tafi gidan wanta Amnon, inda yake kwance. Sai ta ɗauki ƙullu, ta cuɗa, ta toya waina a idonsa.

9 Ta juye wainar daga kaskon yana gani, amma ya ƙi ci. Ya ce wa waɗanda suke cikin ɗakin su fita. Su kuwa suka fita.

10 Sa’an nan Amnon ya ce wa Tamar, “Kawo abincin a cikin ɗakin kwanana, ki riƙe mini in ci.” Sai ta ɗauki wainar da ta yi, ta kai wa Amnon, wanta, a ɗakin kwana.

11 Amma da ta kawo kusa da shi don ya ci, ya kama ta, ya ce, “Zo in kwana da ke ƙanwata.”

12 Ta ce masa, “Haba, wana, kada ka ƙasƙantar da ni, gama ba a yin haka a cikin Isra’ila, kada ka yi halin dabba.

13 Ni kuwa ina zan sa kaina saboda kunya? Kai kuwa za ka zama ɗaya daga cikin riƙaƙƙun sakarkarin mutane na cikin Isra’ila. Ina roƙonka ka yi magana da sarki, gama ba zai hana ka ka aure ni ba.”

14 Amma Amnon bai ji maganarta ba. Da yake ya fi ta ƙarfi, sai ya yi mata faɗe.

15 Bayan haka sai Amnon ya ƙi ta da mummunar ƙiyayya, har ƙiyayyar ta fi yawan ƙaunar da ya yi mata. Ya ce mata, “Tashi, ki fita.”

16 Sai ta ce masa, “A’a wana, muguntar koran nan da kake yi mini, ta fi ta wadda ka riga ka yi mini.”

Amma bai kasa kunne gare ta ba.

17 Sai ya kira baran da yake yi masa hidima, ya ce, “Fitar da matan nan daga gabana, ka rufe ƙofa.”

18 Tamar kuwa tana saye da doguwar riga mai hannuwa, gama haka gimbiyoyi budurwai suke ado. Baran Amnon kuwa ya fitar da ita, ya kulle ƙofar.

19 Tamar ta baɗe kanta da toka, ta keta doguwar rigarta mai hannuwa wadda ta sa, ta rufe fuska da hannu, ta tafi tana ta kuka da ƙarfi.

20 Absalom wanta ya tambaye ta, ya ce, “Ko Amnon wanki ya ɓata ki? To, yi shiru, ƙanwata, shi wanki ne, kada ki damu da yawa.” Tamar kuwa ta zauna a kaɗaice a gidan Absalom wanta.

21 Da Dawuda sarki ya ji wannan, sai ya husata ƙwarai.

22 Amma Absalom bai tanka wa Amnon da wata magana ta alheri ko ta mugunta ba, gama yana ƙin Amnon saboda ya yi wa Tamar ƙanwarsa faɗe.

Absalom Ya Rama Ya Gudu

23 Bayan shekara biyu cif, sai Absalom ya sa a yi masa sausayar tumaki a Ba’al-hazor, wadda take kusa da Ifraimu. Ya kuma gayyaci dukan ‘yan’uwansa, wato ‘yan sarki.

24 Ya kuma tafi wurin sarki, ya ce masa, “Ranka ya daɗe, ga shi, ina sausayar tumakina, ina roƙonka, ka zo, kai da fādawanka tare da ni.”

25 Amma sarki ya ce wa Absalom, “A’a ɗana, ba ma tafi duka ba, don kada mu nawaita maka.” Absalom ya dāge cewa, sai sarki ya je, amma duk da haka sarki bai tafi ba, sai dai ya sa masa albarka.

26 Sa’an nan Absalom ya ce, “Idan ba za ka tafi ba, ina roƙonka ka bar Amnon ɗan’uwana ya tafi tare da mu.”

Sarki ya ce, “Don me zai tafi tare da kai?”

27 Amma Absalom ya dāge har sarki ya yarda. Amnon da dukan ‘ya’yan sarki suka tafi tare da shi.

28 Absalom ya umarci barorinsa, ya ce, “Ku lura sa’ad da Amnon ya bugu da ruwan inabi, in na ce, ‘Bugi Amnon’, sai ku kashe shi. Kada ku ji tsoro, gama ni na umarce ku, sai dai ku yi ƙarfin hali, ku yi jaruntaka.”

29 Haka kuwa barorin Absalom suka kashe Amnon yadda Absalom ya umarta. Sauran ‘ya’yan sarki kuwa suka tashi, kowa ya hau alfadarinsa, ya gudu.

30 Sa’ad da suke kan hanya labari ya kai kunnen Dawuda. Aka ce, “Absalom ya kashe dukan ‘ya’yan sarki, ba wanda ya tsira daga cikinsu.”

31 Sai sarki ya tashi ya keta rigunansa, ya kwanta a ƙasa. Dukan barorinsa kuma da suke tsaye a wurin suka kyakketa rigunansu.

32 Amma Yonadab, ɗan Shimeya, ɗan’uwan Dawuda, ya ce, “Ranka ya daɗe, ba fa dukan ‘ya’yan sarki aka kashe ba. Amnon ne kaɗai aka kashe ta umarnin Absalom, gama ya ƙudura wannan tun daga ranar da Amnon ya yi wa Tamar ƙanwarsa faɗe.

33 Don haka, kada shugabana sarki ya damu, cewa, an kashe dukan ‘ya’yan sarki, gama Amnon ne kaɗai aka kashe.”

34 Absalom kuwa ya gudu.

Sa’an nan sojan da yake tsaro a wannan lokaci ya ga ɗumbun mutane suna tahowa daga hanyar Horonayim, wajen gefen dutse.

35 Sai Yonadab ya ce wa sarki, “Waɗannan ‘ya’yan sarki ne yake zuwa, kamar yadda na faɗa.”

36 Yana gama magana ke nan, sai ga ‘ya’yan sarki sun iso. Suka yi ta kuka da ƙarfi. Sarki kuma da dukan fādawansa suka yi kuka mai tsanani.

37 Amma Absalom ya gudu ya tafi wurin Talmai, ɗan Ammihud, Sarkin Geshur. Dawuda kuwa ya yi makokin Amnon ɗansa kwana da kwanaki.

38 Absalom ya shekara uku a Geshur.

39 Sai zuciyar sarki ta koma kan Absalom, gama ya haƙura a kan Amnon da yake ya riga ya rasu.