Categories
1 TAR

1 TAR 23

1 Sa’ad da Dawuda ya tsufa, yana da shekaru da yawa, sai ya naɗa ɗansa Sulemanu ya zama Sarkin Isra’ila.

Ayyukan Lawiyawa

2 Dawuda kuwa ya tattara dukan shugabannin Isra’ila, da firistoci, da Lawiyawa.

3 Aka ƙidaya Lawiyawa maza tun daga mai shekara talatin har sama, jimillarsu dubu talatin da dubu takwas (38,000).

4 Sai Dawuda ya ce dubu ashirin da dubu huɗu (24,000) daga cikinsu za su yi hidimar Haikalin Ubangiji, dubu shida (6,000) kuma su zama manyan ma’aikata da alƙalai,

5 dubu huɗu (4,000) su zama matsaran ƙofofi, dubu huɗu (4,000) kuma za su zama masu raira yabbai ga Ubangiji da kayayyakin bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe waɗanda ya yi.

6 Dawuda kuwa ya kasa su kashi kashi bisa ga ‘ya’yan Lawi maza, wato Gershon, da Kohat, da Merari.

7 ‘Ya’yan Gershon maza, su ne Libni da Shimai.

8 ‘Ya’yan Libni, maza, su ne Yehiyel, shi ne babba, da Zetam, da Yowel, su uku.

9 ‘Ya’yan Shimai, maza kuwa, su ne Shelomit, da Heziyel, da Haran, su uku. Waɗannan su ne shugabannin gidajen kakanninsu, Libni.

10 ‘Ya’yan Shimai, maza, su ne Yahat, da Zaina, da Yewush, da Beriya. ‘Ya’yan Shimai, maza, ke nan, su huɗu.

11 Yahat shi ne babba, Zaina shi ne na biyu, amma Yewush, da Beriya ba su da ‘ya’ya da yawa, saboda haka ana lasafta su a haɗe gida ɗaya.

12 ‘Ya’yan Kohat, maza, su ne Amram, da Izhara, da Hebron, da Uzziyel, su huɗu ke nan.

13 ‘Ya’yan Amram, maza, su ne Haruna, da Musa. Aka keɓe Haruna domin ya tsarkake abubuwa mafi tsarki, domin shi da ‘ya’yansa za su ƙone turare a gaban Ubangiji, su yi masa hidima, su riƙa sa albarka da sunansa har abada.

14 Amma ‘ya’yan Musa mutumin Allah, an lasafta su tare da kabilar Lawi.

15 ‘Ya’yan Musa, maza, ke nan, Gershom da Eliyezer.

16 Ɗan Gershom babba shi ne Shebuwel.

17 Ɗan Eliyezer shi ne Rehabiya, shugaba, shi Eliyezer ba shi da waɗansu ‘ya’ya, amma Rehabiya yana da ‘ya’ya da yawa.

18 Ɗan Izhara shi ne Shelomit, shugaba.

19 ‘Ya’yan Hebron, maza, su ne Yeriya, shi ne babba, da Amariya na biyu, da Yahaziyel na uku, da kuma Yekameyam na huɗu.

20 ‘Ya’yan Uzziyel, maza, su ne Mika, da Isshiya.

21 ‘Ya’yan Merari, su ne Mali da Mushi. ‘Ya’yan Mali su ne Ele’azara da Kish.

22 Ele’azara kuwa ya rasu ba shi da ‘ya’ya maza, sai ‘yan mata kaɗai, sai ‘yan’uwansu, ‘ya’yan Kish, maza, suka aure su.

23 ‘Ya’yan Mushi, maza, su uku ne, wato Mali, da Eder, da Yerimot.

24 Waɗannan su ne ‘ya’yan Lawi, maza, bisa ga gidajen kakanninsu, wato su ne shugabannin da aka rubuta sunayensu ɗaya ɗaya daga mai shekara ashirin da haihuwa zuwa sama. Su ne za su yi hidima a cikin Haikalin Ubangiji.

25 Gama Dawuda ya ce, “Ubangiji Allah na Isra’ila ya hutar da jama’arsa, yana kuwa zama a Urushalima har abada.

26 Yanzu Lawiyawa ba za su riƙa ɗaukar alfarwar sujada tare da kayayyakin yin aiki a cikinta ba.”

27 Bisa ga maganar Dawuda ta ƙarshe aka ƙidaya ‘ya’yan Lawiyawa, maza, daga mai shekara ashirin zuwa sama.

28 Aikinsu shi ne su taimaki ‘ya’yan Haruna, maza, gudanar da aiki cikin Haikalin Ubangiji, wato lura da farfajiyoyi da ɗakuna, da tsabtace tsarkakan abubuwa, da yin taimako cikin kowace hidimar Haikalin Ubangiji.

29 Za su kuma taimaka wajen gurasar ajiyewa, da lallausan gari na hadaya ta gari, da waina marar yisti, da abin da akan toya, da abin da akan kwaɓa, da ma’aunan nauyi da na girma.

30 Za su kuma riƙa tsayawa kowace safiya su yi godiya, su kuma yabi Ubangiji. Haka kuma za su riƙa yi da maraice,

31 da kuma lokacin miƙa wa Ubangiji hadayun ƙonawa a ranakun Asabar, da lokacin tsayawar amaryar wata, da lokacin ƙayyadaddun idodi, za su tsaya a gaban Ubangiji bisa ga yawansu da ake bukata.

32 Su ne za su riƙa lura da alfarwa ta sujada, da Wuri Mai Tsarki, za su kuma taimaki ‘ya’yan Haruna, maza, ‘yan’uwansu, da yin hidimar Haikalin Ubangiji.

Categories
1 TAR

1 TAR 24

Ayyukan da aka Raba wa Firistoci

1 Ga yadda ‘ya’yan Haruna, maza, suka karkasu. ‘Ya’yan Haruna, maza, su ne Nadab, da Abihu, da Ele’azara, da Itamar.

2 Amma Nadab da Abihu sun riga mahaifinsu mutuwa, ba su kuma da ‘ya’ya. Saboda haka Ele’azara da Itamar suka shiga aikin firistoci.

3 Sai Dawuda da Zadok daga zuriyar Ele’azara, da Ahimelek daga zuriyar Itamar suka karkasa su bisa ga ƙayyadaddun lokatansu na yin aiki.

4 Tun da yake akwai manyan mutane da yawa a zuriyar Ele’azara fiye da zuriyar Itamar, sai suka karkasa su haka, shugabannin gidajen kakannin zuriyar Ele’azara mutum goma sha shida, na zuriyar Itamar kuwa su takwas, bisa ga gidajen kakanninsu.

5 Da haka aka karkasa su ta hanyar kuri’a gama akwai ma’aikatan Wuri Mai Tsarki da kuma ma’aikata na Allah daga zuriyar Ele’azara da zuriyar Itamar.

6 Shemaiya, ɗan Netanel marubuci, Balawe, ya rubuta su a gaban sarki da shugabanni, da Zadok firist, da Ahimelek ɗan Abiyata, da shugabannin gidajen kakannin firistoci, da Lawiyawa. Aka ɗauki gida guda daga gidajen kakannin Ele’azara, aka kuma ɗauki ɗaya daga gidajen kakannin Itamar.

7-18 Ga yadda aka shirya ƙungiyoyin iyali ashirin da huɗu su sami aikinsu, 1) Yehoyarib, 2) Yedaiya, 3) Harim, 4) Seyorim, 5) Malkiya, 6) Mijamin, 7) Hakkoz, 8) Abaija, 9) Yeshuwa, 10) Shekaniya, 11) Eliyashib, 12) Yakim, 13) Huffa, 14) Yeshebeyab, 15) Bilga, 16) Immer, 17) Hezir, 18) Haffizzez, 19) Fetahiya, 20) Yehezkel, 21) Yakin, 22) Gamul, 23) Delaiya, 24) Ma’aziya.

19 Waɗannan suna da aikin da aka ba su na hidimar Haikalin Ubangiji bisa ga ka’idar da kakansu Haruna ya kafa musu, kamar yadda Ubangiji Allah na Isra’ila ya umarce shi.

20 Sauran ‘ya’yan Lawi, maza, na wajen Amram, shi ne Shebuwel.

Na wajen Shebuwel, shi ne Yedaiya.

21 Na wajen Rehabiya, shi ne Isshiya,

22 Na wajen Izhara, shi ne Shelomit, na wajen Shelomit, shi ne Yahat.

23 Na wajen Hebron, su ne Yeriya na fari, da Amariya, da Yahaziyel, da Yekameyam.

24 Na wajen Uzziyel, shi ne Mika, na wajen Mika, shi ne Shamir.

25 Ɗan’uwan Mika, shi ne Isshiya. Na wajen Isshiya, shi ne Zakariya.

26 Na wajen Merari, Mali da Mushi, da Yayaziya. Na wajen Yayaziya, shi ne Beno.

27 Na wajen Merari, wato na wajen Yayaziya, su ne Beno, da Shoham, da Zakkur, da Ibri.

28 Na wajen Mali, shi ne Ele’azara wanda ba shi da ‘ya’ya maza.

29 Na wajen Kish, ɗan Kish, shi ne Yerameyel.

30 ‘Ya’yan Mushi, maza, su ne Mali, da Eder, da Yerimot.

Waɗannan su ne ‘ya’yan Lawiyawa, maza, bisa ga gidajen kakanninsu.

31 Su ma suka jefa kuri’a kamar yadda ‘yan’uwansu, ‘ya’yan Haruna, maza, suka yi a gaban sarki Dawuda, da Zadok, da Ahimelek, da shugabannin gidajen kakanni na firistoci da na Lawiyawa. Shugaban gidan kakanni ya jefa kuri’a daidai da ƙanensa.

Categories
1 TAR

1 TAR 25

Ƙungiyoyin Mawaƙa

1 Dawuda fa da shugabannin Lawiyawa suka zaɓi waɗansu daga cikin ‘ya’yan Asaf, maza, da na Heman, da na Yedutun domin su raira waƙa da garayu, da molaye, da kuge. Ga waɗanda suka yi wannan hidima.

2 Daga cikin ‘ya’yan Asaf, maza, Zakkur, da Yusufu, da Netaniya, da Asharela, Asaf mahaifinsu ne yake bi da su, shi ne kuma mawaƙin sarki.

3 Na wajen Yedutun, su ne ‘ya’yan Yedutun, maza, wato Gedaliya, da Zeri, da Yeshaya, da Shimai, da Hashabiya, da Mattitiya, su shida ne. Mahaifinsu Yedutun shi ne yake bi da su, shi ne kuma mai raira waƙoƙi da garaya domin godiya da yabon Ubangiji.

4 Na wajen Heman, su ne ‘ya’yan Heman, maza, wato Bukkiya, da Mattaniya, da Uzziyel, da Shebuwel, da Yerimot, da Hananiya, da Hanani, da Eliyata, da Giddalti, da Romamti-yezer, da Yoshbekasha, da Malloti, da Hotir, da Mahaziyot.

5 Allah ya ba Heman, wato annabin sarki, ‘ya’ya maza su goma sha huɗu, da ‘ya’ya mata su uku, kamar yadda ya yi alkawari, domin ya ba Heman iko.

6 Dukansu tsohonsu ne yake bi da su da raira waƙoƙi, da kaɗa kuge, da molaye da garayu, cikin Haikalin Ubangiji, domin yin sujada. Asaf, da Yedutun, da Heman suna ƙarƙashin umarnin sarki.

7 Jimillar horarrun mawaƙa don raira waƙa ga Ubangiji, su da ‘yan’uwansu, duka waɗanda suke ƙwararru, su ɗari biyu da tamanin da takwas ne.

8 Sai suka jefa kuri’a domin su ba kowa aikin da zai yi, yaro da babba, malami da almajiri.

9-31 Waɗannan su ne shugabannin ƙungiyoyi ashirin da huɗu, na goma sha biyu biyu, bisa ga yadda aka tsara su ga aikin. 1) Yusufu daga iyalin Asaf, 2) Gedaliya, 3) Zakkur, 4) Zeri, 5) Netaniya, 6) Bukkiya, 7) Asharela, 8) Yeshaya, 9) Mattaniya, 10) Shimai, 11) Uzziyel, 12) Hashabiya, 13) Shebuwel, 14) Mattitiya, 15) Yeremot, 16) Hananiya, 17) Yoshbekasha, 18) Hanani, 19) Malloti, 20) Eliyata, 21) Hotir, 22) Giddalti, 23) Mahaziyot, 24) Romamtiyezer.

Categories
1 TAR

1 TAR 26

Masu Tsaron Haikali da Shugabanni

1 Ƙungiyoyin masu tsaron ƙofofi ke nan. Na wajen Kora shi ne Shallum ɗan Kore, daga cikin iyalin Ebiyasaf.

2 Shallum kuwa yana da ‘ya’ya maza, su ne Zakariya, da Yediyayel, da Zabadiya, da Yatniyel,

3 da Elam, da Yehohanan, da Eliyehoyenai, su bakwai ke nan.

4 Obed-edom kuma Allah ya ba shi ‘ya’ya maza, su ne Shemaiya, da Yehozabad, da Yowa, da Sakar, da Netanel,

5 da Ammiyel, da Issaka, da Fauletai, da su Allah ya sa masa albarka.

6 Ɗan farin Obed-edom, wato Shemaiya ya haifi ‘ya’ya maza waɗanda suka yi shugabanci a gidan kakansu, gama su jarumawa ne.

7 ‘Ya’yan Shemaiya, su ne Otni, da Refayel, da Obida, da Elzabad, waɗanda ‘yan’uwansu, Elihu, da Semakiya jarumawa ne.

8 Waɗannan duka iyalin Obed-edom ne. Su da ‘ya’yansu maza da ‘yan’uwansu suna da ƙarfi da gwaninta na yin aiki. Su sittin da biyu ne daga wajen Obed-edom.

9 Shallum yana da ‘ya’ya maza da ‘yan’uwa, su goma sha takwas jarumawa.

10 Hosa kuma na wajen ‘ya’yan Merari, maza, yana da ‘ya’ya maza, Shimri shi ne babba, ko da yake ba shi ne ɗan fari ba, duk da haka mahaifinsa ya maishe shi babba.

11 Hilkiya shi ne na biyu, da Tebaliya na uku, da Zakariya na huɗu. Dukan ‘ya’yan Hosa, maza, da ‘yan’uwansa, su goma sha uku ne.

12 Aka rarraba masu tsaron Haikali ƙungiya ƙungiya, bisa ga iyali, aka raba musu ayyuka a Haikali kamar dai sauran Lawiyawa.

13 Sai suka jefa kuri’a bisa ga gidajen kakanninsu, ba a damu da yawan jama’a a iyali ba, a kan kowace ƙofar.

14 Kuri’a ta ƙofar gabas ta faɗo a kan Shallum. Sai aka jefa kuri’a don ɗansa Zakariya, mai ba da shawara mai ma’ana, sai kuri’a ta ƙofar arewa ta faɗo a kansa.

15 Kuri’a ta ƙofar kudu ta faɗo a kan Obed-edom. Aka sa ‘ya’yansa maza su lura da ɗakunan ajiya.

16 Kuri’a ta ƙofar yamma kusa da Ƙofar Shalleket, a kan hanyar da ta haura, ta faɗo a kan Shuffim da Hosa. Aka raba aikin tsaro bisa ga lokatan da aka tsara bi da bi.

17 A kowace rana Lawiyawa shida suke tsaron ƙofar gabas, huɗu a ƙofar kudu, huɗu kuma a ƙofar arewa, biyu biyu suke tsaron ɗakunan ajiya.

18 A ɗan ɗakin da take wajen yamma, akwai masu tsaro huɗu a hanyar, biyu kuma a ɗan ɗakin.

19 Waɗannan su ne ƙungiyoyin masu tsaron ƙofofi daga zuriyar Kora da ta Merari.

Sauran Ayyukan Haikali

20 Sauran Lawiyawa, ‘yan’uwansu kuwa, suke lura da baitulmalin Haikalin Allah, da ɗakin ajiyar kayan da aka keɓe ga Allah.

21 Libni daga cikin iyalin Gershon, shi ne kakan ƙungiyoyin iyali da dama, iyalin Yehiyel ne ɗaya daga cikinsu.

22 Biyu daga cikin wannan iyali, wato Zetam da Yowel, suke lura da baitulmalin Haikali da ɗakin ajiyar kaya.

23 Aka raba aiki kuma ga zuriyar Amram, da ta Izhara, da ta Hebron, da kuma ta Uzziyel.

24 Shebuwel ɗan Gershom, daga zuriyar Musa, shi ne babban jami’in baitulmalin.

25 Ta wurin ɗan’uwan Gershom, wato Eliyezer ya sami dangantaka da Shelomit. Eliyezer shi ne mahaifin Rehabiya, wanda ya haifi Yeshaya, uban Yoram, da Zikri, da Shelomit.

26 Shi wannan Shelomit da ‘yan’uwansa suke lura da kyautai waɗanda sarki Dawuda, da shugabannin, gidajen kakanni, da shugabannin dubu dubu, da na ɗari ɗari, da shugabannin sojoji suka keɓe ga Allah.

27 Daga cikin ganimar yaƙi suka keɓe wani sashi domin gyaran Haikalin Ubangiji.

28 Dukan kuma abin da Sama’ila annabi, da Saul ɗan Kish, da Abner ɗan Ner, da Yowab ɗan Zeruya, suka keɓe an sa su a hannun Shelomit da ‘yan’uwansa.

Ayyukan Sauran Lawiyawa

29 Kenaniya da ‘ya’yansa maza na wajen Izhara su ne aka danƙa wa al’amuran sasantawa na Isra’ilawa, wato sun zama shugabanni da alƙalai.

30 Hashabiya da ‘yan’uwansu, su dubu da ɗari bakwai (1,700), gwanaye ne, daga zuriyar Hebron, su ne suke lura da Isra’ilawan yamma da Urdun a kan aikin Ubangiji da na sarki.

31 Yeriya shi ne shugaban zuriyar Hebron bisa ga asalinsu. A shekara ta arba’in ta sarautar Dawuda, sai aka bincika, aka tarar akwai ƙarfafan mutane, jarumawa a cikinsu, a Yazar ta Gileyad.

32 Sarki Dawuda ya sa shi, shi da ‘yan’uwansu su dubu biyu da ɗari bakwai (2,700) gwanaye, waɗanda suke shugabancin gidajen kakanni, su lura da kabilar Ra’ubainu, da ta Gad, da rabin kabilar Manassa a kan dukan ayyukan Allah da na sarki.

Categories
1 TAR

1 TAR 27

Manyan Ma’aikatan Mulki

1 Ga lissafin kawunan iyalin Isra’ilawa, da shugabannin dangi, da jama’a masu gudanar da ayyukan mulki. A kowane wata akan sauya aikin ƙungiyar mutum dubu ashirin da dubu huɗu (24,000), a ƙarƙashin shugaban aiki na wannan wata. Kowane wata akan sauya, wata ƙungiya ta kama aiki.

2-15 Waɗannan su ne shugabanni don kowane wata.

Wata na 1, Yashobeyam, ɗan Zabdiyel. (Shi daga dangin Feresa na kabilar Yahuza ne.)

Wata na 2, Dodai, ɗan Ahowa. (Miklot yake bi masa a shugabancin.)

Wata na 3, Benaiya, ɗan Yehoyada firist. Shugaba ne daga cikin sanannun nan “talatin.” (Ɗansa Ammizzabad ya gāje shi a shugabancin ƙungiya.)

Wata na 4, Asahel, ƙanen Yowab. (Ɗansa Zabadiya ya gāje shi.)

Wata na 5, Shimeya, daga zuriyar Izhara.

Wata na 6, Aira, ɗan Ikkesha, daga Tekowa.

Wata na 7, Helez, mutumin Ifraimu, daga Felet.

Wata na 8, Sibbekai, daga garin Husha. (Shi daga dangin Zera ne, na kabilar Yahuza.)

Wata na 9, Abiyezer, daga Anatot na kabilar Biliyaminu.

Wata na 10, Maharai, daga Netofa. (Shi ma daga dangin Zera ya fito.)

Wata na 11, Benaiya, daga Firaton na kabilar Ifraimu.

Wata na 12, Heled, daga Netofa. (Shi daga zuriyar Otniyel ne.)

Aikin Mulkin Kabilan Isra’ila

16-22 Ga jerin sunayen masu mulkin kabilan Isra’ila.

Ra’ubainu: Eliyezer ɗan Zikri,
Saminu: Shefatiya ɗan Ma’aka,
Lawi: Hashabiya ɗan Kemuwel,
Haruna: Zadok,
Yahuza: Eliyab ɗaya daga cikin ‘yan’uwan sarki Dawuda,
Issaka: Omri ɗan Maikel,
Zabaluna: Ishmaiya ɗan Obadiya,
Naftali: Yerimot ɗan Azriyel,
Ifraimu: Hosheya ɗan Azaziya,
Manassa ta Yamma: Yowel ɗan Fedaiya,
Manassa ta Gabas: Iddo ɗan Zakariya,
Biliyaminu: Yawasiyel ɗan Abner,
Dan: Azarel ɗan Yeroham.

Waɗannan su ne shugabannin kabilai.

23 Sarki Dawuda bai ƙidaya waɗanda shekarunsu suka kasa ashirin ba, gama Ubangiji ya yi alkawari zai sa mutanen Isra’ila su yi yawa kamar taurari a sararin sama.

24 Yowab ɗan Zeruya ne ya fara ƙidayar, amma bai gama ba. Allah ya hukunta wa Isra’ila saboda wannan ƙidaya, saboda haka ba za a taɓa samun cikakken adadi a lissafin da suke a ajiye na fādawan sarki Dawuda ba.

Masu Lura da Dukiyar Sarki

25-30 Ga lissafin masu sarrafa dukiyar sarki.

Ɗakin ajiya na sarki: Azmawet ɗan Adiyel,

Ƙaramin ɗakin ajiya: Jonatan ɗan Uzziya,

Aikin gona: Ezri ɗan Kabilu,

Kurangar Inabi: Shimai daga Rama,

Ɗakin ajiyar Inabi: Zabdi daga Shefam,

Itatuwan zaitun da na ɓaure (a gindin tsaunukan yamma): Ba’al-hanan daga Geder,

Ajiyar man zaitun: Yowash,

Garken shanu na filin Sharon: Shirtai daga Sharon,

Garken shanu na cikin kwari: Shafat ɗan Adlai,

Raƙuma: Obil Ba’isma’ile,

Jakuna: Yedaiya daga Meronot,

Tumaki: Yaziz Bahagire.

31 Dukan waɗannan su ne masu lura da dukiyar sarki Dawuda.

Ƙwararrun Mashawartan Dawuda

32 Jonatan, kawun Dawuda, shi ne mai ba da shawara, yana da ganewa, shi kuma magatakarda ne. Shi da Yehiyel ɗan Hakmoni su ne masu koya wa ‘ya’yan sarki, maza.

33 Ahitofel shi abokin shawarar sarki ne. Hushai Ba’arkite kuwa shi ne abokin sarki.

34 Sai Yehoyada ɗan Benaiya, da Abiyata suka gāji matsayin Ahitofel. Yowab shi ne babban shugaban sojojin sarki.

Categories
1 TAR

1 TAR 28

Dawuda Ya Danƙa Ginin Haikali ga Sulemanu

1 Dawuda ya yi umarni a tara dukan shugabannin Isra’ila, da shugabannin kabilai, da shugabannin ƙungiyoyin da suke bauta wa sarki, da shugabannin dubu dubu, da na ɗari ɗari, da masu lura da dukan dukiya da dabbobin sarki, da na ‘ya’yansa, da fādawa, da manyan sojoji, da jarumawa, a Urushalima.

2 Sarki Dawuda fa ya miƙe tsaye, ya ce, “Ku saurare ni, ku ‘yan’uwana, da jama’ata. Na yi niyya a zuciyata in gina wa akwatin alkawari na Ubangiji wurin hutawa, da wurin zaman zatin Allah. Na riga na yi shiri domin ginin,

3 amma Allah bai yardar mini in yi da kaina ba, domin ni mayaƙi ne, na kuwa zubar da jini.

4 Duk da haka Ubangiji Allah na Isra’ila ya zaɓe ni da zuriyata daga cikin gidan mahaifina, in zama Sarkin Isra’ilawa har abada. Gama shi ya zaɓi Yahuza ya zama shugaba. Daga cikin gidan Yahuza kakana, da kuma daga cikin ‘ya’yan mahaifina, maza, ya ji daɗina har ya naɗa ni sarkin dukan Isra’ila.

5 Daga cikin dukan ‘ya’yana maza, (gama Ubangiji ya ba ni ‘ya’ya maza da yawa), ya zaɓi ɗana Sulemanu ya hau gadon sarautar Isra’ila, abin mulkin Ubangiji.

6 “Ya ce mini, ‘Ɗanka Sulemanu ne zai gina Haikalina da shirayuna, gama na zaɓe shi ya zama ɗa a gare ni, ni kuwa in zama uba a gare shi.

7 Zan tabbatar da mulkinsa har abada idan ya bi umarnaina da ka’idodina da himma kamar yadda ake yi a yau.’

8 “Saboda haka a gaban dukan Isra’ila, wato taron jama’ar Ubangiji, da kuma gaban Allahnmu, sai ku kiyaye, ku bi dukan umarnan Ubangiji Allahnku don ku mallaki ƙasan nan mai kyau, ku kuma bar wa ‘ya’yanku ita gādo har abada.

9 “Kai kuwa ɗana Sulemanu, sai ka san Allah na tsohonka, ka bauta masa da zuciya ɗaya, da kuma yardar rai, gama Ubangiji mai binciken dukan zukata ne, ya kuma san kowane irin nufi da tunani. Idan ka neme shi, za ka same shi, in kuwa ka rabu da shi, shi ma zai yi watsi da kai har abada.

10 Ka lura, gama Ubangiji ya zaɓe ka domin ka gina Haikali, wato Wuri Mai Tsarki. Ka yi ƙarfi, ka kama aiki.”

11 Sa’an nan Dawuda ya ba ɗansa Sulemanu tsarin shirayin Haikalin, da ɗakunansa, da ɗakunan ajiya, da benaye, da Wuri Mafi Tsarki, inda ake gafarta zunubi.

12 Ya kuma ba shi tsarin dukan abin da ya yi nufin yi, na filayen Haikalin Ubangiji da dukan ɗakuna na kewaye, da ɗakunan ajiya na Haikalin Allah, da ɗakunan ajiye kyautan da aka keɓe ga Ubangiji.

13 Ya kuma ba shi tsarin ƙungiyoyin firistoci da na Lawiyawa, da na dukan hidimar da za a yi a Haikalin Ubangiji, da aikin lura da kayayyakin aiki na cikin Haikalin Ubangiji.

14 Ya kuma faɗa wa Sulemanu yawan zinariya da za a yi kwanoni da ita don yin aiki, da yawan azurfa da za a yi kwanoni da ita don yin aiki,

15 da yawan zinariya da za a yi alkukan fitilu, da kuma fitilun, da yawan zinariya da za a yi kowane alkuki da fitilunsa, da yawan azurfa da za a yi alkuki bisa ga yadda za a yi amfani da kowane alkuki,

16 da yawan zinariya da za a yi teburorin gurasar ajiyewa, da azurfar da za a yi teburorin azurfa,

17 da yawan zinariya tsantsa wadda za a yi cokula masu yatsotsi, da daruna, da finjalai, da kwanoni da ita, da yawan azurfa da za a yi kwanoni da ita,

18 da yawan zinariya tsantsa wadda za a yi bagaden ƙona turare da ita. Ya kuma ba shi tsarin zinariya ta kerubobin da za su miƙe fikafikansu su rufe akwatin alkawari na Ubangiji.

19 Sarki Dawuda ya ce, “Dukan wannan rubutacce ne daga wurin Ubangiji zuwa gare ni domin in fahimci fasalin aikin filla filla.”

20 Sarki Dawuda kuma ya ce wa ɗansa Sulemanu, “Ka yi ƙarfin hali, ka dāge sosai, ka kama aikin, kada ka ji tsoro, kada kuwa ka karai, gama Ubangiji Allah, wato Allahna, yana tare da kai. Ba zai bari ka ji kunya ba, ba kuwa zai rabu da kai ba, har ka gama dukan aikin Haikalin.

21 Ga dai ƙungiyoyin firistoci da na Lawiyawa, suna nan domin yin hidima a Haikalin Allah, ga kuma gwanaye na kowace irin sana’a suna tare da kai don yin kowane irin aiki. Shugabanni da dukan jama’a suna ƙarƙashinka duka.”

Categories
1 TAR

1 TAR 29

Ba Da Kyautai domin Gina Haikali

1 Sarki Dawuda fa ya yi magana da dukan taron, ya ce, “Ga shi, ɗana Sulemanu, wanda Allah ya zaɓa, shi dai saurayi ne tukuna, bai gogu da duniya ba tukuna, aikin kuwa babba ne, gama Haikali ba na mutum ba ne, amma na Ubangiji Allah ne.

2 A halin yanzu dai na riga na yi iyakacin ƙoƙarina, har na tanada waɗannan abubuwa saboda Haikalin Allahna, wato zinariya saboda kayayyakin zinariya, azurfa saboda kayayyakin azurfa, tagulla saboda kayayyakin tagulla, baƙin ƙarfe saboda kayayyakin baƙin ƙarfe, itace kuwa saboda kayayyakin itace, da duwatsu da yawa masu daraja, da masu launi iri iri.

3 Saboda kuma ƙaunar Haikalin Allahna da nake yi, shi ya sa na ba da zinariyata da azurfata domin Haikalin Allahna, banda wanda na riga na tanada saboda Haikali mai tsarki.

4 Na ba da zinariya tsantsa, talanti dubu uku (3,000), da azurfa tsantsa, talanti dubu bakwai (7,000), domin yin ado a bangon Haikalin,

5 da kuma dukan kayayyakin da masu sana’a za su yi. Yanzu fa ko akwai mai niyyar ba da sadaka ta yardar rai ga Ubangiji?”

6 Sa’an nan shugabannin gidajen kakanni, da shugabannin kabilai, da shugabanni na dubu dubu, da na ɗari ɗari, da masu lura da aikin sarki, suka bayar da yardar rai.

7 Sun ba da zinariya talanti dubu biyar (5,000), da darik dubu goma (10,000), da azurfa talanti dubu goma (10,000), da tagulla talanti goma sha takwas (18,000), da ƙarfe talanti dubu ɗari (100,000).

8 Dukan waɗanda suke da duwatsu masu daraja suka bayar da su cikin taskar Haikalin Ubangiji, ta hannun Yehiyel Bagershone.

9 Sai jama’a suka yi murna da ganin yadda suka bayar hannu sake, gama sun kawo sadakokinsu a gaban Ubangiji da zuciya ɗaya, shi sarki Dawuda kuma ya yi murna ƙwarai.

Dawuda Ya Yabi Allah

10 Dawuda ya yabi Ubangiji a gaban dukan taron, ya ce, “Ya Ubangiji Allah na kakanmu Yakubu, yabo ya tabbata gare ka har abada abadin!

11 Girma, da iko, da daraja, da nasara, da ɗaukaka duk naka ne, ya Ubangiji, gama dukan abin da yake cikin sammai da duniya naka ne. Mulki kuma naka ne, ya Ubangiji. Kai ne Maɗaukaki duka.

12 Dukan wadata da girma daga gare ka suke, kai kake mulki da dukan iko da ƙarfi. Kai ne kake da iko ka ba mutum iko da ƙarfi.

13 Yanzu ya Allahnmu, muna gode maka muna kuma yabon sunanka mai daraja.

14 “Amma wane ni ko kuma jama’ata, da za mu iya kawo sadaka mai yawa haka? Gama dukan kome daga gare ka yake. Daga cikin abin da muka karɓa daga wurinka muka ba ka.

15 Gama mu kamar baƙi ne, masu yawo a gabanka kamar kakanninmu. Kwanakinmu a duniya kamar inuwa ne, ba za mu tsere wa mutuwa ba.

16 Ya Ubangiji Allahnmu, duk wannan da muka kawo domin mu gina maka Haikali saboda sunanka mai tsarki, daga gare ka ne muka samu, duka naka ne.

17 Da yake na sani, ya Allahna, kakan gwada zuciya, kana ƙaunar gaskiya, bisa ga amincewar zuciyata, da yardar rai, na miƙa maka dukan waɗannan abubuwa. Ina murna da ganin jama’arka waɗanda suke nan a tattare, sun kawo maka sadakokinsu da yardar rai.

18 Ya Ubangiji, Allah na Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, kakanninmu, ka tabbatar da yardar rai ɗin nan a rayukan jama’arka, ka bi da zukatansu zuwa gare ka.

19 Ka kuma ba ɗana Sulemanu cikakkiyar zuciya, har da zai kiyaye umarnanka, da shaidunka, da dokokinka, domin ya aikata su duka, ya kuma gina Haikali wanda na riga na yi tanadi dominsa.”

Sulemanu Ya Gāji Dawuda

20 Sa’an nan Dawuda ya ce wa taro duka, “Sai ku yabi Ubangiji Allahnku yanzu.” Taron jama’a kuwa suka yabi Ubangiji Allah na kakanninsu, suka rusuna har ƙasa, suka yi wa Ubangiji sujada, suka kuma girmama sarki.

21 Kashegari sai suka miƙa wa Ubangiji hadayu, suka kuma miƙa hadayun ƙonawa ga Ubangiji, bijimai dubu ɗaya (1,000), da raguna dubu ɗaya (1,000), da ‘yan raguna dubu ɗaya (1,000), da hadayunsu na sha, da hadayu masu yawa domin Isra’ila duka.

22 Sai suka ci, suka sha, suka yi murna a gaban Ubangiji a wannan rana.

Sai suka sake shelar naɗin Sulemanu ɗan Dawuda sarki, a karo na biyu, suka shafa masa man keɓewa domin ya zama mai mulki na Ubangiji, Zadok kuwa shi ne firist.

23 Sai Sulemanu ya zauna a kan gādon sarauta na Ubangiji maimakon tsohonsa Dawuda. Ya yi nasara a cikin sarautar, Isra’ilawa dukansu suka yi masa biyayya.

24 Dukan ma’aikatan hukuma kuwa, da manyan mutane, da kuma dukan ‘ya’yan sarki Dawuda, suka yi alkawari za su yi wa sarki Sulemanu biyayya.

25 Ubangiji kuwa ya ɗaukaka Sulemanu ƙwarai da gaske a gaban dukan Isra’ilawa, ya ɗaukaka sarautarsa fiye da ta waɗanda suka riga shi sarauta a Isra’ila.

Sarautar Dawuda a Taƙaice

26 Dawuda ɗan Yesse ya yi mulki bisa dukan Isra’ila,

27 har shekara arba’in. Ya yi mulki a Hebron shekara bakwai sa’an nan ya yi mulki shekara talatin da uku a Urushalima.

28 Sa’an nan ya rasu da kyakkyawan tsufa, cike da shekaru, da arziki, da daraja. Ɗansa Sulemanu kuma ya gāji sarautarsa.

29 An fa rubuta ayyukan sarki Dawuda daga farko har ƙarshe a tarihin Sama’ila, annabi, da na annabi Natan, da na annabi Gad.

30 An rubuta labarin mulkinsa, da ikonsa, da al’amuran da suka same shi, da Isra’ilawa, da dukan mulkokin ƙasashe na kewaye.

Categories
2 TAR

2 TAR 1

Addu’ar Sulemanu ta Neman Hikima

1 Sulemanu ɗan Dawuda ya kahu sosai cikin mulkinsa, gama Ubangiji Allahnsa yana tare da shi, Ubangiji kuwa ya sa shi ya zama mashahuri.

2 Sulemanu ya yi magana da dukan manya, wato shugabannin dubu dubu, da na ɗari ɗari, da alƙalai, da dukan shugabanni na Isra’ila, wato shugabannin gidajen kakanni.

3 Sa’an nan Sulemanu da dukan waɗanda suke tare da shi, suka tafi masujadar da take a Gibeyon, gama alfarwar sujada ta Allah, wadda Musa, bawan Ubangiji ya yi a jeji, tana can.

4 Amma dai Dawuda ya riga ya ɗauko akwatin alkawari na Allah daga Kiriyat-yeyarim, ya kawo shi a wurin da ya shirya, gama ya kafa masa alfarwa a Urushalima.

5 Amma bagaden tagulla wanda Bezalel ɗan Uri daga dangin Hur, ya yi, yana a gaban Wuri Mai Tsarki na Ubangiji, sai Sulemanu da taron jama’a suka yi sujada ga Ubangiji a can.

6 Sulemanu kuwa ya haura, ya tafi wurin da bagaden tagulla yake a gaban Ubangiji, a cikin alfarwa ta sujada, ya miƙa hadayun ƙonawa dubu a kansa.

7 A wannan dare Allah ya bayyana ga Sulemanu, ya ce masa, “Ka roƙe ni abin da kake so in ba ka.”

8 Sai Sulemanu ya ce wa Allah, “Ka nuna wa tsohona Dawuda madawwamiyar ƙaunarka, har ka naɗa ni sarki a matsayinsa.

9 Yanzu fa ya Ubangiji Allah, alkawarin da ka yi wa tsohona ya cika, gama ka naɗa ni sarki a kan jama’a mai yawa kamar turɓaya.

10 Yanzu sai ka ba ni hikima da sani yadda zan iya kai da kawowa a gaban wannan jama’a, gama wa zai iya mulkin wannan jama’a taka mai yawa haka?”

11 Allah kuwa ya amsa wa Sulemanu ya ce, “Tun da kana da irin wannan tunani a zuciyarka, ba ka kuwa roƙi dukiya, ko wadata, ko girma, ko ran maƙiyanka ba, ba ka kuma roƙi tsawon rai ba, amma ka roƙa wa kanka hikima da sani domin ka iya yin mulkin jama’ata wadda na naɗa ka sarki a kanta,

12 to, na ba ka hikima da sani. Zan kuma ba ka dukiya, da wadata, da girma, waɗanda ba wani sarkin da ya taɓa samun irinsu, ba kuma wani sarkin da zai taɓa samun irinsu.”

13 Daga nan sai Sulemanu ya taso daga masujadar da take Gibeyon inda alfarwa ta sujada take, ya zo Urushalima inda ya zauna yana mulkin Isra’ila.

Sulemanu Ya Tara Dawakai da Karusai

14 Sai Sulemanu ya tara karusai da mahayan dawakai. Yana da karusai dubu ɗaya da ɗari huɗu (1,400), da mahayan dawakai dubu goma sha biyu (12,000), sai ya sa su a biranen karusai, waɗansu kuma a Urushalima tare da shi.

15 Sarki ya yawaita azurfa da zinariya har suka zama kamar duwatsu a Urushalima. Haka kuma ya yi da itatuwan al’ul, suka yawaita kamar itatuwan ɓaure a fadama.

16 Wakilan sarki suka ɗauki nauyin shigo da dawakai daga Masar da Kilikiya,

17 suka kuma shigo da karusai daga Masar. Suka riƙa sayar wa sarakunan Hittiyawa da na Suriyawa karusai a kan azurfa ɗari shida shida, kowane doki kuma a kan azurfa ɗari da hamsin.

Categories
2 TAR

2 TAR 2

Shirye-shiryen Ginin Haikali

1 Sai Sulemanu ya yi niyya a ransa zai gina Haikali saboda sunan Ubangiji, ya kuma gina wa kansa fāda.

2 Don haka, sai ya sa mutane dubu saba’in (70,000) don ɗaukar kaya, dubu tamanin (80,000) su haƙo duwatsu a tsaunuka, dubu uku da ɗari shida (3,600) kuma su ne shugabanni.

3 Sulemanu fa ya aika wurin Hiram Sarkin Taya ya ce, “Yadda ka yi wa tsohona Dawuda, wato ka aiko masa da itatuwan al’ul domin ya gina gida inda zai zauna, ni ma ina so ka yi mini haka.

4 Ga shi dai, na yi niyyar gina Haikali saboda sunan Ubangiji Allahna, in kuma keɓe masa shi, domin a riƙa ƙona masa turare mai daɗin ƙanshi, inda kuma za a riƙa ajiye gurasar ajiyewa dukan lokaci, don kuma a riƙa miƙa hadayun ƙonawa safe da yamma, da ranakun Asabar, da na amarya wata, da kuma a lokatan ƙayyadaddun idodin Ubangiji Allahnmu, yadda dai aka faralta a riƙa yi a cikin Isra’ila.

5 Haikalin nan kuwa da nake niyyar ginawa babba ne, gama Allahnmu ya fi dukan alloli.

6 Amma wa ya isa ya gina masa Haikali, shi wanda sama da saman sammai ba su iya ɗaukarsa ba. Ni wane ne da zan gina masa Haikali, sai dai wurin da za a riƙa ƙona turare a gabansa?

7 Saboda haka sai ka aiko mini da mutum wanda ya gwanance a kan aiki da azurfa, da tagulla, da baƙin ƙarfe, da kuma shunayya, da garura, da shuɗɗan zare, da wanda kuma ya gwanance da aikin sassaƙa, domin ya yi aiki tare da gwanayen mutane da nake da su a Yahuza da Urushalima, waɗanda tsohona Dawuda ya kawo.

8 Ka kuma aiko mini da itacen al’ul, da na fir, da katakon algum daga Lebanon, gama na sani barorinka sun san yadda ake yanyanka katakan Lebanon. Barorina za su yi aiki tare da barorinka,

9 domin su shirya mini katako mai yawa. Gama Haikalin da zan gina mai girma ne ƙwarai, mai banmamaki.

10 Zan ba barorinka masu aikin katako misalin mudu dubu ashirin (20,000) ta sussukakkiyar alkama, da mudu dubu ashirin (20,000) ta sha’ir, da misalin garwar ruwan inabi dubu ashirin (20,000), da ta mai dubu ashirin (20,000).”

11 Hiram, Sarkin Taya kuwa, ya ba Sulemanu amsar takardarsa, ya ce, “Saboda Ubangiji yana ƙaunar jama’arsa, ya naɗa ka sarkinsu.”

12 Hiram ya ci gaba da cewa, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda ya yi sama da ƙasa, ya ba sarki Dawuda ɗa mai hikima, mai hankali, mai ganewa, wanda zai gina Haikali dominsa, ya gina fāda kuma domin kansa.

13 Yanzu zan aika maka da Huram mutum mai gwaninta, mai ganewa.

14 Shi ɗan wata mace mutuniyar Dan, mahaifinsa kuwa mutumin Taya ne. Huram ya gwanance a kan aiki da zinariya, da azurfa, da tagulla, da baƙin ƙarfe, da dutse, da itace, da kuma shuɗi, da shunayya, da garura, da lilin mai kyau. Shi kuma zai iya sassaƙa kowane irin abu da aka sa shi ya sassaƙa, tare da gwanayenka, da na tsohonka, ubangidana, wato Dawuda.

15 To, yanzu, sai ka aiko wa barorinka da alkama, da sha’ir, da mai, da ruwan inabi kamar yadda ka alkawarta.

16 Mu kuwa za mu yanko maka dukan katakan da kake bukata a Lebanon, mu kawo maka su a kan gadajen fito ta hanyar teku, zuwa Yafa, domin ka kwashe ka kai Urushalima.”

An Fara Ginin Haikali

17 Sarki Sulemanu ya ƙidaya dukan baƙin da suke a ƙasar Isra’ila, kamar yadda tsohonsa Dawuda ya yi. Yawan baƙin da aka samu sun kai dubu ɗari da dubu hamsin da uku, da ɗari shida (153,600).

18 Sai ya zaɓi mutum dubu saba’in (70,000) daga cikinsu su zama masu ɗaukar kaya, dubu tamanin (80,000) kuma don su riƙa haƙo duwatsu daga tsaunuka, dubu uku da ɗari shida (3,600) kuwa don su zama shugabanni.

Categories
2 TAR

2 TAR 3

Sulemanu Ya Gina Ɗakin Sujada domin Ubangiji

1 Sulemanu kuwa ya fara ginin Haikalin Ubangiji a Urushalima a kan Dutsen Moriya, inda Ubangiji ya taɓa bayyana ga tsohonsa Dawuda, inda kuma Dawuda ya riga ya shirya a daidai masussukar Arauna Bayebuse.

2 Ya fara ginin a ran biyu ga watan biyu a shekara ta huɗu ta sarautarsa.

3 Ga awon harsashin da Sulemanu ya kafa domin ginin Haikalin Ubangiji. Tsawonsa bisa ga tsohon magwajin, kamu sittin ne, fāɗin kuwa kamu ashirin.

4 Tsawon shirayi daga gaban Haikalin ya yi daidai da fāɗin Haikalin, wato kamu ashirin, sa’an nan tsayinsa kamu ɗari da ashirin. Aka shafe ciki da zinariya tsantsa.

5 Ya jera itatuwan fir a cikin babban ɗakin, sa’an nan ya shafe su da zinariya tsantsa, ya kuma zana siffofin itatuwan dabino da na sarƙoƙi.

6 Banda wannan kuma ya ƙawata Haikalin da duwatsu masu daraja da zinariya irin ta Farwayim.

7 Ya kuma shafe Haikalin duk da ginshiƙansa, da bakin ƙofofinsa, da bangayensa, da ƙyamarensa da zinariya, ya kuma zana siffofin kerubobi a jikin bangaye.

8 Sai ya gina Wuri Mafi Tsarki. Tsawonsa daidai da fāɗin Haikalin, wato kamu ashirin, fāɗinsa kuma kamu ashirin. Ya shafe shi da zinariya tsantsa, wadda jimillar nauyinta ta yi talanti ɗari shida.

9 Nauyin ƙusoshin ya kai shekel hamsin na zinariya. Ya kuma shafe benaye da zinariya tsantsa.

10 Ya sassaƙa siffofin kerubobi biyu na itace, a Wuri Mafi Tsarki, ya shafe su da Zinariya.

11 Tsawon fikafikan kerubobin duka kamu ashirin ne, fiffike ɗaya, kamu biyar, ya taɓo bangon ɗakin, ɗaya fiffiken kuma wanda shi ma kamu biyar ne, ya taɓo fiffiken kerub ɗaya ɗin.

12 Guda kerub ɗin kuma, fiffikensa guda ya taɓo bangon ɗakin, ɗaya fiffiken shi ma ya taɓo fiffiken kerub na farko.

13 Tsawon fikafikan kerubobin ya kai kamu ashirin. Su kerubobin a tsaye suke, suna fuskantar babban ɗakin.

14 Sai ya yi labule mai launin shuɗi, da shunayya, da garura, da lilin mai kyau, sa’an nan ya zana siffofin kerubobin a jikin labulen.

Kayan Haikali

15 Ya kuma yi ginshiƙai biyu domin ƙofar Haikalin, tsayinsu kamu talatin da biyar ne, ya yi wa ginshiƙan dajiya, tsayin kowace dajiya kamu biyar ne.

16 Ya yi sarƙoƙi, ya rataya wa ginshiƙan, ya kuma yi siffofin rumman guda ɗari, ya maƙala wa sarƙoƙin.

17 Sai ya kafa ginshiƙin a ƙofar Haikali, ɗaya a wajen kudu, ɗaya kuma a wajen arewa. Ya sa wa na wajen kudu suna Yakin, na wajen arewa kuwa Bo’aza.