Categories
FAR

FAR 31

Yakubu ya Gudu daga wurin Laban

1 Yakubu ya ji ‘ya’yan Laban suna cewa, “Yakubu ya kwashe dukan abin da yake na mahaifinmu, daga cikin dukan abin da yake na mahaifinmu kuma ya sami dukiyarsa.”

2 Yakubu kuma ya ga ba shi da farin jini a wurin Laban kamar dā.

3 Ubangiji ya ce wa Yakubu, “Ka koma ƙasar kakanninka da danginka, ni kuwa ina tare da kai.”

4 Saboda haka Yakubu ya aika a kirawo Rahila da Lai’atu zuwa cikin saura inda garkensa yake,

5 ya ce musu, “Na ga ba ni da sauran farin jini wurin mahaifinku kamar dā. Amma Allah na mahaifina yana tare da ni.

6 Kun sani na yi wa mahaifinku barantaka da dukan ƙarfina,

7 duk da haka mahaifinku ya cuce ni, ya yi ta sassauya ladana har sau goma, amma Allah bai ba shi ikon zambatata ba.

8 In ya ce, ‘Dabbare-dabbare, su ne ladanka,’ duk garken sai ya haifi dabbare-dabbare, in kuma ya ce ‘masu sofane ne ladanka,’ sai garken duka ya haifi masu sofane.

9 Ta haka Allah ya kwashe dukiyar mahaifinku ya ba ni.

10 “A lokacin ɗaukar cikin garke, cikin mafarki na ta da idanuna, na kuwa gani cikin mafarkin, bunsuran da suke hawan garken, masu sofane, da dabbare-dabbare da roɗi-roɗi ne.

11 Sai mala’ikan Allah ya ce mini a cikin mafarki, ‘Yakubu,’ sai na ce, ‘Ga ni.’

12 Ya kuwa ce, ‘Ta da idanunka ka gani, dukan bunsuran da suke hawan awaki masu sofane ne, dabbare-dabbare da roɗi-roɗi, gama na ga dukan abin da Laban yake yi maka.

13 Ni ne Allah na Betel, inda ka zuba wa dutsen mai, ka kafa shi al’amudi, ka kuma rantse mini. Yanzu fa tashi ka fita daga cikin ƙasan nan, ka koma ƙasar haihuwarka.’ ”

14 Rahila da Lai’atu suka amsa masa, “Akwai wani rabo, ko gādon da ya rage mana a cikin gidan mahaifinmu?

15 Ba ga shi ma, sai kamar baƙi yake ɗaukarmu ba? Gama ya sayar da mu, yana kuwa morar kuɗin da aka bayar dominmu.

16 Dukan dukiyar da Allah ya kwashe daga wurin mahaifinmu, tamu ce da ‘ya’yanmu, yanzu fa, kome Allah ya faɗa maka, sai ka yi.”

17 Sai Yakubu ya tashi, ya ɗauki ‘ya’yansa, da matansa a bisa raƙumansa,

18 ya kora shanunsa duka, da dukan bisashen da ya samu, da shanu da suke nasa, waɗanda ya samu a Fadan-aram a ƙasar Mesofotamiya, zuwa ƙasar Kan’ana wurin mahaifinsa Ishaku.

19 Amma a sa’an nan Laban ya riga ya tafi ya yi wa tumakinsa sausaya, sai Rahila ta sace gumakan gidan mahaifinta.

20 Yakubu kuwa ya yaudari Laban Ba’aramiye da bai sanar da shi zai gudu ba.

21 Ya gudu da dukan abin da yake da shi, ya tashi ya haye Yufiretis, ya miƙe zuwa ƙasar Gileyad ta tuddai.

Laban ya Bi Sawun Yakubu

22 Sa’ad da aka sanar da Laban, cewa Yakubu ya gudu da kwana uku,

23 sai ya ɗauki danginsa tare da shi, ya bi sawunsa har kwana bakwai, yana biye da shi kurkusa har zuwa ƙasar Gileyad ta tuddai.

24 Amma Allah ya zo wurin Laban Ba’aramiye cikin mafarki da dad dare, ya ce masa, “Ka kula fa, kada ka ce wa Yakubu kome, ko nagari ko mugu.”

25 Sai Laban ya ci wa Yakubu. A yanzu Yakubu ya riga ya kafa alfarwarsa a ƙasa ta tuddai, Laban da danginsa kuma suka yi zango a ƙasar Gileyad ta tuddai.

26 Laban ya ce wa Yakubu, “Me ka yi ke nan, da ka cuce ni, ka gudu da ‘ya’yan matana kamar kwason yaƙi?

27 Me ya sa ka gudu a ɓoye? Ka cuce ni, ba ka kuwa faɗa mini ba, ai, da na sallame ka da farin ciki, da waƙe-waƙe, da kiɗa, da garaya.

28 Don me ba ka bari na sumbaci ‘ya’yana mata da maza na yi bankwana da su ba? Kai! Ka yi aikin wauta.

29 Ina da iko in yi maka lahani, amma Allah na mahaifinka, ya yi magana da ni a daren jiya, yana cewa, ‘Ka kula fa kada ka ce wa Yakubu kome, ko nagari ko mugu.’

30 Amma yanzu, ka gudu domin kana kewar gidan mahaifinka ƙwarai, amma don me ka sace mini gumakana?”

31 Yakubu ya amsa wa Laban, ya ce, “Domin na ji tsoro ne gama na yi zaton za ka ƙwace ‘ya’yanka mata ƙarfi da yaji.

32 Ga duk wanda ka iske gumaka a wurinsa, a kashe shi. Yanzu a nan gaban danginmu, ka nuna abin da nake da shi wanda yake naka, ka ɗauka.” Ashe, Yakubu bai sani Rahila ce ta sace su ba.

33 Laban ya shiga alfarwar Yakubu, da ta Lai’atu, da na kuyangin nan biyu, amma bai same su ba. Sai ya fita daga alfarwar Lai’atu, ya shiga ta Rahila.

34 Ashe, Rahila ta kwashe gumakan ta zuba su cikin sirdin raƙumi, ta zauna a kansu. Laban ya wawaka alfarwar duka, amma bai same su ba.

35 Sai ta ce wa mahaifinta, “Kada ubangijina ya yi fushi da ban iya tashi ba, don ina al’adar mata ne.” Ya kuwa bincike, amma bai sami gumakan ba.

36 Yakubu ya husata, ya yi wa Laban faɗa, ya ce wa Laban, “Wane laifi na yi, mene ne zunubina da ka tsananta bina?

37 Ko da yake ka wawaka dukan kayayyakina, me ka samu na gumakanka a ciki? A tabbatar a nan yau a gaban dangina da danginka, su yanke shari’a tsakanina da kai.

38 Waɗannan shekaru ashirin da na yi tare da kai, tumakinka da awakinka ba su yi ɓari ba, ban kuwa ci ragunan garkenka ba.

39 Wanda namomin jeji suka yayyaga ban kawo maka ba, ni da kaina na ɗauki hasararsu. Ka kuma nemi abin da aka sace da rana ko da dare daga hannuna.

40 Abin da na zama ke nan, da rana na sha zafin rana, da dare kuwa na sha sanyi, ga rashin barci.

41 A waɗannan shekaru ashirin da nake cikin gidanka, na yi maka barantaka shekara goma sha huɗu domin ‘ya’yanka mata biyu, shekara shida kuma domin garkenka, ka kuwa sauya ladana har sau goma.

42 Da ba domin Allah na mahaifina da Ibrahim, da martabar Ishaku na wajena ba, hakika da yanzu ka sallame ni hannu wofi. Allah ya ga wahalata da aikin hannuwana, ya kuwa tsauta maka a daren jiya.”

Yarjejeniya Tsakanin Yakubu da Laban

43 Sa’an nan Laban ya amsa ya ce wa Yakubu, “’Ya’ya mata, ‘ya’yana ne, ‘ya’yansu kuma nawa ne, garkunan, garkunana ne, dukan abin da kake gani nawa ne. Amma me zan yi a wannan rana ta yau ga waɗannan ‘ya’ya mata nawa, ko kuma ga ‘ya’yan da suka haifa?

44 Zo mana mu ƙulla alkawari, da ni da kai, bari ya zama shaida tsakanina da kai.”

45 Saboda haka Yakubu ya ɗauki dutse ya kafa shi al’amudi.

46 Yakubu ya ce wa iyalinsa, “Ku tattara duwatsu.” Sai suka ɗauki duwatsu, suka tsiba, suka kuwa ci abinci kusa da tsibin.

47 Laban ya sa masa suna Yegar-sahaduta, amma Yakubu ya kira shi Galeyed.

48 Laban ya ce, “Wannan tsibi shaida ce tsakanina da kai yau.” Saboda haka ya sa wa wurin suna Galeyed.

49 Laban kuma ya kira wurin Mizfa, gama ya ce, “Ubangiji ya kiyaye tsakanina da kai sa’ad da muka rabu da juna.

50 Idan ka wulakanta ‘ya’yana mata, ko kuma ka auri wata mata banda ‘ya’yana mata, ko da yake babu kowa tare da mu, ka tuna, Allah shi ne mashaidi tsakanina da kai.”

51 Sai Laban ya ce wa Yakubu, “Dubi wannan tsibi da al’amudi, wanda na kafa tsakanina da kai.

52 Wannan tsibi, shaida ce, al’amudin kuma shaida ce ba zan zarce wannan tsibi zuwa wurinka ba, kai kuma ba za ka zarce wannan tsibi da wannan al’amudi zuwa wurina don cutarwa ba.

53 Allah na Ibrahim da Nahor, Allah na mahaifinsu, ya shara’anta tsakaninmu.” Saboda haka Yakubu ya rantse da martabar mahaifinsa Ishaku.

54 Yakubu kuwa ya miƙa hadaya a bisa dutsen, ya kirawo iyalinsa su ci abinci, suka kuwa ci abinci suka zauna dukan dare a bisa dutsen.

55 Da sassafe, Laban ya tashi ya sumbaci jikokinsa, da ‘ya’yansa mata, ya sa musu albarka. Sa’an nan ya tashi ya koma gida.

Categories
FAR

FAR 32

Yakubu Ya Yi Shirin Saduwa da Isuwa

1 Yakubu ya yi tafiyarsa, mala’ikun Allah kuma suka gamu da shi.

2 Sa’ad da Yakubu ya gan su ya ce, “Waɗannan rundunar Allah ce!” Saboda haka ya sa wa wannan wuri suna Mahanayim.

3 Yakubu kuwa ya aiki jakadu a gabansa zuwa wurin Isuwa ɗan’uwansa a cikin ƙasar Seyir a karkarar Edom,

4 yana umartarsu da cewa, “Haka za ku faɗa wa shugabana Isuwa, ‘Ga abin da baranka Yakubu ya ce, “Na yi baƙunta a ƙasar Laban, na zauna har wa yau.

5 Ina da takarkarai, da jakai, da garkuna, da barori mata da maza, na kuwa aika a faɗa wa shugabana domin in sami tagomashi a idonka.” ’ ”

6 Jakadun kuwa suka komo wurin Yakubu, suka ce, “Mun je wurin ɗan’uwanka Isuwa, yana kuwa zuwa ya tarye ka da mutum arbaminya tare da shi.”

7 Yakubu fa ya tsorata ƙwarai, ya damu, sai ya karkasa mutanen da suke tare da shi, da garkunan tumaki da awaki, da na shanu, da raƙuma cikin ƙungiya biyu,

8 yana tunani cewa, “In Isuwa ya zo ya hallaka ƙungiya guda, ƙungiyar da ta ragu sai ta tsira.”

9 Sai Yakubu ya ce, “Ya Allah na kakana Ibrahim, da mahaifina Ishaku, Ubangiji, wanda ka ce mini, ‘Koma ƙasarka zuwa wurin danginka, zan kuwa yi maka alheri,’

10 ban cancanci ayyukanka na ƙauna da irin amincin da ka gwada wa baranka ba, gama da sandana kaɗai na haye Kogin Urdun, ga shi yanzu kuwa na zama ƙungiya biyu.

11 Ka cece ni ina roƙonka daga hannun ɗan’uwana, wato daga hannun Isuwa, gama ina jin tsoronsa, kada ya zo ya karkashe mu duka, ‘ya’ya da iyaye.

12 Gama ka riga ka ce, ‘Zan yi maka alheri, in kuma sa zuriyarka su yi yawa kamar yashin teku, waɗanda ba su lasaftuwa saboda yawansu.’ ”

13 Ya yi zango a nan a wannan dare, ya kuwa bai wa ɗan’uwansa Isuwa kyauta daga cikin abin da yake da shi,

14 awakai metan da bunsurai ashirin, tumaki metan da raguna ashirin,

15 raƙuman tatsa talatin tare da ‘yan taguwoyi, shanu arba’in da bijimai goma, jakai mata ashirin da jakai maza goma.

16 Waɗannan ya sa su a hannun barorinsa ƙungiya ƙungiya, ya ce wa barorinsa, “Ku yi gaba, ku ba da rata tsakanin ƙungiya da ƙungiya.”

17 Ya umarci na kan gaba, ya ce, “Sa’ad da Isuwa ɗan’uwana ya gamu da ku, ya tambaye ku cewa, ‘Ku mutanen wane ne? Ina za ku? Waɗannan da suke gabanku na wane ne?’

18 Sa’an nan sai ku ce, ‘Na Yakubu baranka ne, kyauta ce zuwa ga shugabana Isuwa, ga shi nan ma biye da mu.’ ”

19 Da haka nan ya umarci na biyu da na uku da dukan waɗanda suke korar garkunan, ya ce, “Sai ku faɗa wa Isuwa daidai haka nan.

20 Ku kuma ce, ‘Ga shi ma, Yakubu ɗan’uwanka yana biye da mu.’ ” Gama, cikin tunaninsa ya ce, “Ya yiwu in gamshe shi da kyautar da ta riga ni gaba, daga baya in ga fuskarsa, watakila ya karɓe ni.”

21 Saboda haka kyautar ta yi gaba, shi kansa kuwa a daren, ya sauka a zango.

Yakubu Ya Yi Kokawa a Feniyel

22 A wannan dare kuwa ya tashi ya ɗauki matansa biyu, da kuyanginsa biyu da ‘ya’yansa goma sha ɗaya ya haye mashigin Jabbok.

23 Ya ɗauke su ya haye da su rafi, haka kuma ya yi da dukan abin da yake da shi.

24 Aka bar Yakubu shi kaɗai.

Sai wani mutum ya kama shi da kokawa har wayewar gari.

25 Sa’ad da mutumin ya ga bai rinjayi Yakubu ba sai ya taɓa kwarin kwatangwalonsa, sai gaɓar kwatangwalon Yakubu ta gulle a lokacin da yake kokawa da shi.

26 Sa’an nan sai mutumin ya ce, “Ka bar ni in tafi, gama gari na wayewa.”

Amma Yakubu ya ce, “Ba zan bar ka ka tafi ba, sai ka sa mini albarka.”

27 Sai ya ce masa, “Yaya sunanka?”

Ya ce, “Yakubu.”

28 Sai ya ce, “Ba za a ƙara kiranka da suna Yakubu ba, amma za a kira ka Isra’ila, gama ka yi kokawa da Allah da mutane, ka kuwa yi rinjaye.”

29 Sa’an nan Yakubu ya tambaye shi, “Ina roƙonka, faɗa mini sunanka.”

Amma ya ce, “Don me kake tambayar sunana?” A nan mutumin ya sa masa albarka.

30 Saboda haka Yakubu ya sa wa wurin suna Feniyel, yana cewa, “Gama na ga Allah fuska da fuska, duk da haka ban mutu ba.”

31 Rana ta yi sama a sa’ad da Yakubu ya wuce Feniyel domin yana ɗingishi saboda kwatangwalonsa.

32 Saboda haka, har wa yau, Isra’ilawa ba sā cin jijiyar kwatangwalo wadda take a kwarin kwatangwalo, domin an taɓi kwarin kwatangwalon Yakubu ta jijiyar kwatangwalo.

Categories
FAR

FAR 33

Yakubu ya Sadu da Isuwa

1 Yakubu ya ɗaga ido ya duba ke nan, sai ga Isuwa na zuwa da mutum arbaminya tare da shi. Sai ya raba wa Lai’atu da Rahila ‘ya’yan, tare da kuyangin nan biyu.

2 Ya sa kuyangin da ‘ya’yansu a gaba, sa’an nan Lai’atu sa’an nan Rahila da Yusufu a ƙarshen duka.

3 Shi kansa ya wuce gabansu, ya yi ta sunkuyar da kansa ƙasa sau bakwai, har sa’ad da ya kai kusa da ɗan’uwansa.

4 Amma Isuwa ya sheƙa ya tarye shi, ya rungume shi, ya faɗa a wuyansa, ya sumbace shi, suka kuwa yi kuka.

5 Sa’ad da Isuwa ya ta da idonsa ya ga mata da ‘ya’ya, ya ce, “Su wane ne waɗannan tare da kai?”

Yakubu ya ce, “Su ne ‘ya’ya waɗanda Allah cikin alherinsa ya ba baranka.”

6 Sai kuyangin suka matso kusa, su da ‘ya’yansu, suka sunkuya ƙasa.

7 Haka nan kuma Lai’atu da ‘ya’yanta suka matso, suka sunkuya ƙasa, a ƙarewa Yusufu da Rahila suka matso kusa, su kuma suka sunkuya ƙasa.

8 Isuwa kuwa ya ce, “Ina manufarka da duk waɗannan ƙungiyoyi da na gamu da su?”

Yakubu ya amsa, ya ce, “Ina neman tagomashi ne a idon shugabana.”

9 Amma Isuwa ya ce, “Ina da abin da ya ishe ni, ɗan’uwana, riƙe abin da kake da shi don kanka.”

10 Yakubu ya ce, “A’a, ina roƙonka, in dai na sami tagomashi a idonka, to, sai ka karɓi kyautar da yake hannuna, gama hakika ganin fuskarka, kamar ganin fuskar Allah ne, bisa ga yadda ka karɓe ni.

11 Ina roƙonka, ka karɓi kyautar da na kawo maka, gama Allah ya yi mini alheri matuƙa, gama ina da abin da ya ishe ni.” Da haka Yakubu ya i masa, Isuwa kuwa ya karɓa.

12 Sa’an nan Isuwa ya ce, “Bari mu ci gaba da tafiyarmu, ni kuwa in wuce gabanka.”

13 Amma Yakubu ya ce masa, “Shugabana, ai, ka sani ‘ya’yan ba su da ƙarfi, ga kuma bisashe da shanun tatsa, ina jin tausayinsu ƙwarai da gaske. Idan kuwa aka tsananta korarsu kwana ɗaya, garkunan za su mutu duka.

14 Bari shugabana ya wuce gaban baransa, ni zan biyo a hankali bisa ga saurin shanun da yake gabana, da kuma bisa ga saurin yaran, har in isa wurin shugaba a Seyir.”

15 Sai Isuwa ya ce, “Bari in bar waɗansu daga cikin mutanen da suke tare da ni, a wurinka.”

Amma Yakubu ya ce, “Ka kyauta ƙwarai, amma ba na bukatar haka, ya shugaba.”

16 A ran nan Isuwa ya koma a kan hanyarsa zuwa Seyir.

17 Yakubu ya kama hanya zuwa Sukkot, ya kuwa gina wa kansa gida, ya yi wa shanunsa garke. Saboda haka aka sa wa wurin suna Sukkot.

18 Yakubu kuwa ya kai birnin Shalem wanda yake ƙasar Kan’ana lafiya, a kan hanyarsa daga Fadan-aram, ya kuwa yi zango a ƙofar birnin.

19 Ya kuma sayi yankin saura inda ya kafa alfarwarsa daga ‘ya’yan Hamor, mahaifin Shekem, a bakin azurfa ɗari.

20 A wurin ya gina bagade ya sa masa suna El-Elohe-Isra-el.

Categories
FAR

FAR 34

An Yi wa Dinatu Faɗe

1 Yanzu fa Dinatu ‘yar Lai’atu, wadda ta haifa wa Yakubu, ta fita ta ziyarci waɗansu matan ƙasar,

2 sai Shekem, ɗan Hamor Bahiwiye, yariman ƙasar, da ya gan ta, ya kama ta, ya kwana da ita, ya ɓata ta.

3 Ransa kuwa ya zaƙu da son Dinatu ‘yar Yakubu. Ya ƙaunaci budurwar, ya kalallame ta da maganganu masu daɗi.

4 Sai Shekem ya yi magana da mahaifinsa, Hamor, ya ce, “Ka auro mini wannan budurwa ta zama matata.”

5 Yakubu kuwa ya ji an ɓata ‘yarsa, Dinatu, amma ‘ya’yansa maza suna tare da garken cikin saura, saboda haka Yakubu ya yi shiru har kafin su komo.

6 Sai Hamor mahaifin Shekem ya fita ya je wurin Yakubu, ya yi magana da shi.

7 ‘Ya’yan Yakubu, maza, kuwa sa’ad da suka komo daga saura, da suka ji yadda aka yi, sai suka hasala, abin ya ba su haushi ƙwarai, don Shekem ya yi aikin wauta ga Isra’ila da ya kwana da ‘yar Yakubu. Gama irin wannan abu, bai kamata a yi shi ba.

8 Amma Hamor ya yi magana da su, ya ce, “Zuciyar ɗana Shekem tana begen ‘yarku, ina roƙonku, ku ba shi ita aure.

9 Ku yi aurayya da mu. Ku ba mu ‘yan matanku, ku kuma ku auri ‘yan matanmu.

10 Sai ku zauna tare da mu, ƙasar kuma tana gabanku. Ku zauna a cikinta ku yi sana’a, ku sami dukiya.”

11 Shekem kuma ya ce wa mahaifin Dinatu da ‘yan’uwanta, “Bari in sami tagomashi a idanunku, dukan abin da kuka ce kuwa, sai in yi.

12 Ku faɗa mini ko nawa ne dukiyar auren da sadakin, zan kuwa bayar bisa ga yadda kuka faɗa mini, in dai kawai ku ba ni budurwar ta zama matata.”

13 ‘Ya’yan Yakubu, maza, suka amsa wa Shekem da mahaifinsa Hamor a ha’ince, domin ya ɓata ‘yar’uwarsu Dinatu.

14 Suka ce musu, “Ba za mu iya yin wannan abu ba, mu aurar da ‘yar’uwarmu ga marasa kaciya, gama wannan abin kunya ne a gare mu.

15 Ta wannan hali ne kaɗai za mu yarda, wato idan za ku zama kamarmu, ku yi wa dukan mazajenku kaciya.

16 Sa’an nan za mu ba ku auren ‘ya’yanmu mata, mu kuma mu auro wa kanmu ‘ya’yanku mata. Sai kuwa mu zauna tare da ku, mu zama jama’a ɗaya.

17 Amma idan ba ku saurare mu kun yi kaciya ba, sai mu ɗauki ‘yarmu, mu kama hanyarmu.”

18 Hamor da ɗansa Shekem suka yi na’am da sharuɗan.

19 Saurayin kuwa bai yi jinkirin aikata batun ba, gama yana jin daɗin ‘yar Yakubu. Shekem kuwa shi ne aka fi darajantawa a cikin gidan.

20 Hamor kuwa da ɗansa Shekem, suka je dandali a bakin ƙofar birni, suka yi wa mutanen birninsu magana, suka ce,

21 “Waɗannan mutane suna abuta da mu, ai, sai su zauna a ƙasar a sake, gama ga shi akwai isasshen fili a ƙasar dominsu. Bari mu auri ‘ya’yansu mata, mu kuma mu aurar musu da ‘ya’yanmu mata.

22 Ga sharaɗin da mutanen za su yarda su zauna tare da mu, mu zama jama’a ɗaya, wato kowane namiji a cikinmu ya yi kaciya kamar yadda su suke da kaciya.

23 Da shanunsu, da dukiyarsu da dukan dabbobinsu, ashe, ba za su zama namu ba? Bari dai kurum mu yarda da su, su zauna tare da mu.”

24 Duk jama’ar birnin suka yarda da maganar Hamor da ɗansa Shekem. Aka kuwa yi wa kowane namiji kaciya.

25 A rana ta uku, sa’ad da jikunansu suka yi tsami, biyu daga cikin ‘ya’yan Yakubu, Saminu da Lawi, ‘yan’uwan Dinatu, suka ɗauki takubansu suka fāɗa wa birnin ba labari, suka karkashe mazajen duka.

26 Suka kashe Hamor da ɗansa Shekem da takobi, suka ɗauko Dinatu daga gidan Shekem suka yi tafiyarsu.

27 ‘Ya’yan Yakubu kuwa suka tarar da kisassun, suka washe birnin, saboda sun ɓata ‘yar’uwarsu.

28 Suka kwashe garkunan awaki da tumaki, da garkunan shanu da jakunansu da dukan abin da yake cikin birnin da na cikin saura,

29 dukan dukiyarsu, da ‘yan ƙananansu, da matansu, wato dukan abin da yake cikin gidajen, suka kwashe.

30 Sai Yakubu ya ce wa Saminu da Lawi, “Kun jawo mini wahala. Kun sa na zama abin ƙi ga Kan’aniyawa da Ferizziyawa mazaunan ƙasar. Mutanena kima ne, in suka haɗa kai suka fāɗa mini, za su hallaka ni, da ni da gidana.”

31 Amma ‘ya’yansa suka ce, “Zai mai da ƙanwarmu kamar karuwa?”

Categories
FAR

FAR 35

Allah ya Sa wa Yakubu Albarka a Betel

1 Allah ya ce wa Yakubu, “Tashi, ka hau zuwa Betel, ka zauna can. Can za ka gina bagade ga Allah wanda ya bayyana gare ka sa’ad da kake guje wa ɗan’uwanka Isuwa.”

2 Sai Yakubu ya ce wa iyalin gidansa da dukan waɗanda suke tare da shi, “Ku kawar da gumakan da suke wurinku, ku tsarkake kanku, ku sāke rigunanku,

3 sa’an nan mu tashi mu haura zuwa Betel, domin in kafa bagade ga Allah wanda ya taimake ni a kwanakin ƙuncina, wanda kuwa yake tare da ni duk inda na tafi.”

4 Saboda haka, suka bai wa Yakubu dukan gumakan da suke da su, da zobban kunnuwansu. Sai Yakubu ya ɓoye su a ƙarƙashin itacen oak wanda suke kusa da Shekem.

5 Da suna cikin tafiya, razana daga Allah ta fāɗa wa biranen da suke kewaye da su, har ba wanda ya iya bin ‘ya’yan Yakubu.

6 Sai Yakubu ya zo Luz, wato Betel, wadda take cikin Kan’ana, shi da dukan mutanen da suke tare da shi.

7 A nan ya gina bagade, ya sa wa wurin suna El-betel, domin a nan Allah ya bayyana kansa gare shi sa’ad da yake guje wa ɗan’uwansa.

8 Can Debora, ungozomar Rifkatu ta rasu, aka kuwa binne ta a gangaren Betel, a ƙarƙashin itacen oak, don haka ana kiran wurin, Allon-bakut.

9 Allah kuma ya sāke bayyana ga Yakubu a lokacin da ya komo daga Fadan-aram, ya sa masa albarka.

10 Allah kuwa ya ce masa, “Sunanka Yakubu ne, amma nan gaba ba za a ƙara kiran sunanka Yakubu ba, sai Isra’ila.” Don haka aka kira sunansa Isra’ila.

11 Allah ya ce masa, “Ni ne Allah Maɗaukaki, ka hayayyafa ka riɓaɓɓanya, al’umma da tattaruwar al’ummai za su bumbunto daga gare ka, sarakuna kuma za su fito daga cikinka.

12 Na ba ka ƙasar da na ba Ibrahim da Ishaku, zan kuma ba da ita ga zuriyarka a bayanka.”

13 Sa’an nan Allah ya tashi Sama ya bar shi a wurin da ya yi masa magana.

14 Sai Yakubu ya kafa al’amudin dutse a inda Allah ya yi masa magana, ya zuba masa sadaka ta sha, ya kuma zuba mai a bisansa.

15 Yakubu ya kira sunan wurin da Allah ya yi magana da shi, Betel.

Rasuwar Rahila

16 Da suka tashi daga Betel, tun suna da ‘yar rata da Efrata, sai lokaci ya yi da Rahila za ta haihu, amma ta sha wahala kafin ta haihu.

17 Sa’ad da take cikin naƙudarta, sai ungozoma ta ce mata, “Kada ki ji tsoro, gama yanzu kin sami wani ɗa.”

18 Da tana suma, sai ta sa masa suna Ben-oni, amma mahaifinsa ya sa masa suna Biliyaminu.

19 Ta haka fa Rahila ta rasu, aka kuwa binne ta a bakin hanya zuwa Efrata, wato Baitalami.

20 Yakubu ya kafa al’amudi bisa kabarinta, al’amudin kabarin Rahila ke nan, wanda yake can har wa yau.

21 Isra’ila ya ci gaba da tafiyarsa, ya kuwa kafa alfarwarsa daura da hasumiyar Eder.

‘Ya’yan Yakubu Maza

22 A lokacin da Isra’ila yake zaune a ƙasar, Ra’ubainu ya je ya kwana da Bilha kwarkwarar mahaifinsa, Isra’ila kuwa ya sami labari.

‘Ya’yan Isra’ila, maza, su goma sha biyu ne.

23 ‘Ya’yan Lai’atu, su ne Ra’ubainu ɗan farin Yakubu, da Saminu, da Lawi, da Yahuza, da Issaka, da Zabaluna.

24 ‘Ya’yan Rahila, su ne Yusufu da Biliyaminu.

25 ‘Ya’yan Bilha, kuyangar Rahila, su ne Dan da Naftali.

26 ‘Ya’yan Zilfa, kuyangar Lai’atu, su ne Gad da Ashiru. Waɗannan su ne ‘ya’yan Yakubu da aka haifa masa a Fadan-aram.

Rasuwar Ishaku

27 Yakubu kuma ya zo wurin mahaifinsa a Mamre, a Kiriyat-arba, wato Hebron ke nan, inda Ibrahim da Ishaku suka yi baƙunci.

28 Yanzu kuwa kwanakin Ishaku shekara ce ɗari da tamanin.

29 Sai Ishaku ya ja numfashinsa na ƙarshe, ya rasu, aka kuwa kai shi ga jama’arsa waɗanda suka riga shi, da kyakkyawan tsufa cike da kwanaki, ‘ya’yansa Isuwa da Yakubu suka binne shi.

Categories
FAR

FAR 36

Zuriyar Isuwa

1 Waɗannan su ne zuriyar Isuwa, wato Edom.

2 Isuwa ya auri matansa daga cikin Kan’aniyawa, wato Ada ‘yar Elon Bahitte, da Oholibama ‘yar Ana ɗan Zibeyon Bahiwiye,

3 da Basemat, ‘yar Isma’ilu, ‘yar’uwar Nebayot.

4 Ada ta haifa wa Isuwa, Elifaz, Basemat kuma ta haifi Reyuwel.

5 Oholibama ta haifi Yewush, da Yalam, da Kora. Waɗannan su ne ‘ya’yan Isuwa waɗanda aka haifa masa a ƙasar Kan’ana.

6 Isuwa ya kwashi matansa, da ‘ya’yansa mata da maza, da dukan jama’ar gidansa, da shanunsa, da dabbobinsa duka, da dukan dukiyarsa da ya samu a ƙasar Kan’ana, ya kuwa tafi wata ƙasa nesa da ɗan’uwansa Yakubu.

7 Gama abin mallakarsu ya yi yawa har ba zai yiwu su zama tare ba, ƙasar baƙuntarsu kuwa ba ta wadace su ba saboda yawan dabbobinsu.

8 Saboda haka Isuwa ya zauna a ƙasar Seyir ta tuddai. Isuwa shi ne Edom.

9 Waɗannan su ne zuriyar Isuwa, kakan Edomawa, a ƙasar Seyir ta tuddai.

10 Waɗannan su ne sunayen ‘ya’yan Isuwa, maza, wato Elifaz ɗan Ada matar Isuwa, Reyuwel ɗan Basemat matar Isuwa.

11 ‘Ya’yan Elifaz su ne Teman, da Omar, da Zeho, da Gatam, da Kenaz.

12 Timna kuwa ƙwarƙwarar Elifaz ɗan Isuwa ce, ta haifa wa Elifaz Amalek. Waɗannan su ne ‘ya’ya maza na Ada, matar Isuwa.

13 Waɗannan su ne ‘ya’yan Reyuwel, maza, Nahat, da Zera, da Shamma, da Mizza. Waɗannan su ne ‘ya’ya maza na Basemat, matar Isuwa.

14 Waɗannan su ne ‘ya’yan Oholibama matar Isuwa ‘yar Ana ɗan Zibeyon. Ta haifi wa Isuwa Yewush, da Yalam, da Kora.

15 Waɗannan su ne shugabanni na zuriyar Isuwa. Ga ‘ya’yan Elifaz, maza, ɗan farin Isuwa, shugaba Teman, da Omar, da Zeho, da Kenaz,

16 da Kora, da Gatam, da Amalek, su ne shugabannin Elifaz cikin ƙasar Edom, su ne ‘ya’yan Ada.

17 Waɗannan su ne ‘ya’yan Reyuwel, maza, ɗan Isuwa. Shugaba Nahat, da Zera, da Shamma, da Mizza, waɗannan su ne shugabannin Reyuwel na cikin ƙasar Edom, su ne ‘ya’ya maza na Basemat, matar Isuwa.

18 Waɗannan su ne ‘ya’ya maza na Oholibama matar Isuwa, shugaba Yewush, da Yalam, da Kora, waɗannan su ne shugabanni waɗanda Oholibama matar Isuwa, ‘yar Ana ta haifa.

19 Waɗannan su ne ‘ya’yan Isuwa, maza, wato Edom, da shugabanninsu.

Zuriyar Seyir

20 Waɗannan su ne ‘ya’ya maza na Seyir Bahore, mazaunan ƙasar Lotan, da Shobal, da Zibeyon, da Ana,

21 da Dishon, da Ezer, da Dishan. Waɗannan su ne shugabannin Horiyawa, ‘ya’yan Seyir, maza, a ƙasar Edom.

22 ‘Ya’yan Lotan, maza, su ne Hori da Hemam, ‘yar’uwarsa Timna ce.

23 Waɗannan su ne ‘ya’yan Shobal, maza, Alwan, da Manahat, da Ebal, da Sheho, da Onam.

24 Waɗannan su ne ‘ya’yan Zibeyon, maza, Aiya da Ana. Shi ne Ana wanda ya sami maɓuɓɓugan ruwan zafi a cikin jeji, a sa’ad da yake kiwon jakunan mahaifinsa Zibeyon.

25 Waɗannan su ne ‘ya’yan Ana, Dishon da Oholibama ‘yar Ana.

26 Waɗannan su ne ‘ya’yan Dishon, maza, Hemdan da Eshban, da Yitran, da Keran.

27 Waɗannan su ne ‘ya’yan Ezer, maza, Bilhan, da Zayawan, da Akan.

28 Waɗannan su ne ‘ya’yan Dishan, maza, Uz da Aran.

29 Waɗannan su ne shugabannin Horiyawa, shugaba Lotan, da Shobal, da Zibeyon, da Ana,

30 da Dishon, da Ezer, da Dishan, waɗannan su ne shugabannin Horiyawa bisa ga shugabancinsu a ƙasar Seyir.

Sarakunan Edom

31 Waɗannan su ne sarakunan da suka yi sarauta a ƙasar Edom, kafin wani sarki ya taɓa yin mulkin Isra’ilawa.

32 Bela ɗan Beyor ya yi sarautar Edom, sunan birninsa kuwa Dinhaba.

33 Bela ya rasu, sai Yobab ɗan Zera daga Bozara ya ci sarauta a bayansa.

34 Ɗan Yobab ya rasu, sai Husham na ƙasar Temanawa ya ci sarauta a bayansa.

35 Da Husham ya rasu, sai Hadad ɗan Bedad wanda ya ci Madayana a ƙasar Mowab, ya ci sarauta a bayansa, sunan birninsa kuwa Awit ne.

36 Da Hadad ya rasu, sai Samla na Masreka ya ci sarauta a bayansa.

37 Da Samla ya rasu, sai Shawul na Rehobot ta Yufiretis ya ci sarauta a bayansa.

38 Da Shawul ya rasu, sai Ba’al-hanan ɗan Akbor ya ci sarauta a bayansa.

39 Da Ba’al-hanan ɗan Akbor ya rasu, sai Hadad ya ci sarauta a bayansa, sunan birninsa Fau, sunan matarsa kuwa Mehetabel ‘yar Matred, ‘yar Mezahab.

40 Waɗannan su ne sunayen sarakunan Isuwa bisa ga dangoginsu da bisa ga wurin zamansu. Ga sunayensu, sarki Timna, da Alwa, da Yetet,

41 da Oholibama, da Ila, da Finon,

42 da Kenaz, da Teman, da Mibzar,

43 da Magdiyel, da Iram. Waɗannan su ne sarakunan Edom, (wato Isuwa ne kakan Edomawa) bisa ga wuraren zamansu a ƙasar mallakarsu.

Categories
FAR

FAR 37

1 Yakubu ya zauna a ƙasar Kan’ana inda mahaifinsa ya yi baƙunci.

2 Wannan shi ne tarihin zuriyar Yakubu.

Yusufu da ‘Yan’uwansa

Yusufu yana da shekara goma sha bakwai sa’ad da ya zama makiyayin garke tare da ‘yan’uwansa, ɗan ƙanƙanen yaro ne a tsakanin ‘ya’ya maza na Bilha da Zilfa matan mahaifinsa. Sai Yusufu ya kawo labarin munanan abubuwa da ‘yan’uwansa suke yi a wurin mahaifinsa,

3 Isra’ila kuwa ya fi ƙaunar Yusufu da kowannensu, domin shi ɗan tsufansa ne. Sai ya yi masa riga mai ado.

4 Amma sa’ad da ‘yan’uwansa suka gane mahaifinsu yana ƙaunarsa fiye da dukansu, suka ƙi jininsa, ba su iya maganar alheri da shi.

5 Yusufu ya yi mafarki. Sa’ad da ya faɗa wa ‘yan’uwansa, suka ƙara ƙin jininsa.

6 Ya ce musu, “Ku ji irin mafarkin da na yi.

7 Ga shi, muna ɗaurin dammuna cikin gona, ga kuwa damina ya tashi tsaye kyam, ga kuma dammunanku suka taru kewaye da shi, suka sunkuya wa damina.”

8 ‘Yan’uwansa suka ce masa, “Ashe, lalle ne kai za ka sarauce mu? Ko kuwa, ashe lalle ne kai za ka mallake mu?” Sai suka daɗa ƙin jininsa domin mafarkansa da maganganunsa.

9 Shi kuwa sai ya sāke yin wani mafarki, ya faɗa wa ‘yan’uwansa, ya ce, “Ga shi kuma na sāke yin wani mafarki, na ga rana, da wata, da taurari goma sha ɗaya suna sunkuya mini.”

10 Amma sa’ad da ya faɗa wa mahaifinsa da ‘yan’uwansa, sai mahaifinsa ya tsauta masa, ya ce, “Wane irin mafarki ne wannan da ka yi? Lalle ne, da ni da mahaifiyarka da ‘yan’uwanka za mu sunkuya a gabanka har ƙasa?”

11 ‘Yan’uwansa suka ji kishinsa, amma mahaifinsa ya riƙe al’amarin cikin zuciyarsa.

An Sayar da Yusufu zuwa Masar

12 Wata rana, da ‘yan’uwansa suka tafi kiwon garken mahaifinsu a Shekem,

13 Isra’ila ya ce wa Yusufu, “Ashe, ba ‘yan’uwanka suna kiwon garken a Shekem ba? Zo in aike ka wurinsu.”

Sai ya ce masa, “Ga ni.”

14 Mahaifinsa ya ce, “Tafi yanzu, ka dubo lafiyar ‘yan’uwanka da ta garken, ka kawo mini labarinsu.” Saboda haka, ya aike shi daga kwarin Hebron.

Da Yusufu ya isa Shekem,

15 wani mutum ya same shi yana hange-hange cikin karkara. Sai mutumin ya tambaye shi ya ce, “Me kake nema?”

16 Yusufu ya ce, “Ina neman ‘yan’uwana ne. Ina roƙonka ka faɗa mini idan ka san inda suke kiwon garkuna.”

17 Mutumin ya ce, “Sun riga sun tashi daga nan, gama na ji sun ce, ‘Bari mu tafi Dotan.’ ” Saboda haka, Yusufu ya bi sawun ‘yan’uwansa, ya kuwa same su a Dotan.

18 Da suka hango shi daga nesa, kafin ya zo kusa da su, sai suka ƙulla su kashe shi.

19 Suka ce wa juna, “Ga mai mafarkin nan can yana zuwa.

20 Ku zo mu kashe shi yanzu, mu jefa shi cikin ɗaya daga cikin rijiyoyin nan, sa’an nan mu ce, wata muguwar dabbar jeji ce ta kashe shi, sa’an nan mu ga yadda mafarkinsa zai zama.”

21 Amma sa’ad da Ra’ubainu ya ji, ya yi ƙoƙari ya cece shi daga hannunsu, yana cewa, “Kada mu raba shi da ransa.

22 Kada mu kashe shi, mu dai jefa shi cikin rijiyan nan a jeji, amma kada mu yi masa lahani.” Ya yi haka da nufin ya cece shi daga hannunsu, ya mayar da shi ga mahaifinsu.

23 Don haka, sa’ad da Yusufu ya zo wurin ‘yan’uwansa, suka tuɓe masa rigarsa, rigan nan mai ado wadda take wuyansa.

24 Suka ɗauke shi suka jefa shi cikin rijiyar. Rijiyar kuwa wofi ce, ba ruwa a ciki.

25 Suka zauna su ci abinci, da suka ɗaga ido suka duba, sai ga ayarin Isma’ilawa suna zuwa daga Gileyad, da raƙumansu ɗauke da ƙāro, da man ƙanshi na wartsakewa, da mur, suna gangarawa kan hanyarsu zuwa Masar.

26 Yahuza ya ce wa ‘yan’uwansa, “Wace riba ke nan, in mun kashe ɗan’uwanmu, muka ɓoye jininsa?

27 Ku zo mu sayar da shi ga Isma’ilawa, kada mu bar hannunmu ya taɓa shi, gama shi ɗan’uwanmu ne, shi kuma jikinmu ne.” ‘Yan’uwansa suka yarda da shi.

28 Da Madayanawa, fatake, suna wucewa, sai suka jawo Yusufu suka fitar da shi daga cikin rijiyar suka sayar wa Isma’ilawa a bakin azurfa ashirin, aka kuwa tafi da Yusufu zuwa Masar.

29 Sa’ad da Ra’ubainu ya koma a wajen rijiya, da bai ga Yusufu a cikin rijiyar ba, sai ya kyakkece tufafinsa,

30 ya koma wurin ‘yan’uwansa, ya ce, “Saurayin ba ya nan, ni kuwa, ina zan sa kaina?”

31 Suka ɗauki rigar Yusufu, suka yanka akuya, suka tsoma rigar cikin jinin.

32 Suka kuma ɗauki rigan nan mai ado, suka kawo ta ga mahaifinsu, suka ce, “Ga abar da muka samu, duba ka gani, ta ɗanka ce, ko kuwa?”

33 Da ya gane ita ce, ya ce, “Rigar ɗana ce, wani mugun naman jeji ne ya cinye shi, ba shakka an yayyage Yusufu.”

34 Sai Yakubu ya kyakkece rigunansa, ya yi ɗamara da majayi, ya yi kukan ɗansa har kwanaki masu yawa.

35 Dukan ‘ya’yansa mata da maza suka tashi domin su ta’azantar da shi, amma ya ƙi ta’azantuwa, yana cewa, “A’a, a Lahira zan tafi wurin ɗana, ina baƙin ciki.” Haka mahaifinsu ya yi kuka dominsa.

36 A lokacin kuwa, ashe, Madayanawa sun riga sun sayar da shi a Masar ga Fotifar, sarkin yaƙin Fir’auna, shugaba na masu tsaron fādar Fir’auna.

Categories
FAR

FAR 38

Yahuza da Tamar

1 Ya zama fa a wannan lokaci, Yahuza ya bar ‘yan’uwansa ya gangara, ya zauna wurin wani Ba’adullame mai suna Hira.

2 A can, sai Yahuza ya ga ‘yar wani Bakan’ane mai suna Shuwa. Ya aure ta, ya shiga wurinta,

3 ta yi ciki, ta haifi ɗa namiji, ya kuwa raɗa masa suna Er.

4 Sai ta sāke yin ciki, ta kuma haifi ɗa, ta raɗa masa suna Onan.

5 Har yanzu kuma ta sāke haihuwar ɗa, ta raɗa masa suna Shela. A Kezib ta haifi Shela.

6 Yahuza kuwa ya auro wa ɗan farinsa, Er, mata, sunanta Tamar.

7 Amma Er, ɗan farin Yahuza mugu ne a gaban Ubangiji. Sai Ubangiji ya kashe shi.

8 Sa’an nan Yahuza ya ce wa, Onan, “Shiga wurin matar ɗan’uwanka, ka yi mata wajibin ɗan’uwan miji, ka samar wa ɗan’uwanka zuriya.”

9 Amma Onan ya sani zuriyar ba za ta zama tasa ba, saboda haka duk lokacin da ya shiga wurin matar ɗan’uwansa, sai ya zubar da maniyyi a ƙasa don kada ya ba ɗan’uwansa zuriya.

10 Amma abin nan da ya yi, mugun abu ne a gaban Ubangiji, shi ma Ubangiji ya kashe shi.

11 Yahuza kuwa ya ce wa Tamar surukarsa, “Yi zaman gwauranci a gidan mahaifinki, har ɗana Shela ya yi girma,” gama yana jin tsoro kada shi kuma ya mutu kamar ‘yan’uwansa. Saboda haka Tamar ta tafi ta zauna a gidan mahaifinta.

12 A kwana a tashi, ga matar Yahuza, ‘yar Shuwa ta rasu. Da Yahuza ya gama karɓar ta’aziyya, sai ya haura Timna wurin masu sausayar tumakinsa, da shi da abokinsa Hira Ba’adullame.

13 Sa’ad da aka faɗa wa Tamar, aka ce, “Surukinki zai haura zuwa Timna ya yi wa tumakinsa sausaya,”

14 sai ta tuɓe tufafinta na takaba, ta yi lulluɓi ta lulluɓe kanta, ta zauna a ƙofar Enayim a hanyar Timna, gama ta ga Shela ya yi girma, amma ba a ba da ita gare shi ba.

15 Da Yahuza ya gan ta, ya yi tsammani wata karuwa ce, gama ta rufe fuskarta.

16 Sai ya je wurinta a gefen hanyar, ya ce, “Zo, mu kwana mana,” gama bai san ita surukarsa ba ce.

Sai ta ce, “Me za ka ba ni, da za ka kwana da ni?”

17 Ya amsa, ya ce, “Zan aiko miki da ɗan akuya daga cikin garken.”

Ta ce, “Ko ka ba ni jingina, kafin ka aiko?”

18 Ya ce, “Wane alkawari zan yi miki?”

Ta amsa, ta ce, “Ba ni hatiminka da ɗamararka da sandan da yake a hannunka.” Ya kuwa ba ta su, ya kwana da ita. Sai ta yi ciki.

19 Ta tashi ta yi tafiyarta. Da ta cire lulluɓinta ta sa tufafinta na takaba.

20 Sa’ad da Yahuza ya aika da ɗan akuya ta hannun abokinsa Ba’adullame don ya karɓi jinginar daga hannun matar, bai same ta ba.

21 Ya tambayi mutanen wurin, ya ce, “Ina karuwan nan wadda take zaune a Enayim a bakin hanya?”

Sai suka ce, “Ba wata karuwar da ta taɓa zama nan.”

22 Ya koma wurin Yahuza ya ce, “Ban same ta ba, mutanen wurin kuma suka ce, ‘Ba wata karuwa da ta zo nan.’ ”

23 Yahuza ya amsa, ya ce, “Bari ta riƙe abubuwan su zama nata, don kada a yi mana dariya, gama ga shi, na aike da ɗan akuya, amma ba ka same ta ba.”

24 Bayan misalin wata uku, aka faɗa wa Yahuza, “Tamar surukarka ta yi lalata, har ma tana da ciki.”

Sai Yahuza ya ce, “A fito da ita, a ƙone ta.”

25 Za a fito da ita ke nan sai ta aika wa surukinta, ta ce, “Wanda yake da waɗannan kaya shi ya yi mini ciki.” Ta kuma ce, “Ka shaida, ina roƙonka, ko na wane ne wannan hatimi, da abin ɗamarar, da sanda.”

26 Sai Yahuza ya shaida su, ya ce, “Ta fi ni gaskiya, tun da yake ban ba da ita ga ɗana Shela ba.” Daga nan bai ƙara kwana da ita ba.

27 Sa’ad da lokaci ya yi da za ta haihu, ashe, cikin tagwaye ne.

28 Da tana cikin naƙuda, sai hannun wani ya fara fitowa, ungozoma kuwa ta ɗauki jan zare ta ɗaura a hannun, tana cewa, “Wannan shi ya fara fitowa.”

29 Amma da ya janye hannunsa, ga ɗan’uwansa ya fito, sai ta ce, “A’a, ta haka za ka keta ka fito!” Saboda haka aka raɗa masa suna Feresa.

30 Daga baya ɗan’uwansa ya fito da jan zare a hannunsa, aka kuwa sa masa suna Zera.

Categories
FAR

FAR 39

Yusufu da Matar Fotifar

1 Aka kuwa gangara da Yusufu zuwa Masar. Sai Fotifar Bamasare sarkin yaƙin Fir’auna, shugaban masu tsaron fāda ya saye shi daga hannun Isma’ilawa, waɗanda suka gangaro da shi zuwa can.

2 Ubangiji yana tare da Yusufu, har ya zama mutum ne mai galaba a gidan maigidansa Fotifar, Bamasaren.

3 Maigidansa kuwa ya ga Ubangiji yana tare da shi, Ubangiji kuma yakan sa albarka ga aikin hannuwansa duka.

4 Don haka Yusufu ya sami tagomashi a wurinsa, ya zama mai yi masa hidima. Fotifar kuma ya shugabantar da shi a bisa gidansa, da bisa dukan abin da yake da shi.

5 Ubangiji ya sa wa gidan Bamasaren albarka sabili da Yusufu tun daga lokacin da Fotifar Bamasaren ya shugabatar da shi a bisa gidansa da dukan dukiyarsa. Albarkar Ubangiji na bisa dukan abin da yake da shi, na gida da na jeji.

6 Ya bar dukan abin da yake da shi a hannun Yusufu. Tun da ya same shi, ba ruwansa da kome, sai dai abincin da zai ci.

Yusufu fa kyakkyawa ne mai kyan gani.

7 Ya zamana fa, wata rana, sai matar maigidansa ta sa idonta kan Yusufu, ta ce, “Ka kwana da ni.”

8 Amma ya ƙi, ya kuwa faɗa wa matar maigidansa, ya ce, “Ga shi, tun da maigida ya same ni, maigidana ba ruwansa da kome na cikin gida, ya kuwa riga ya sa dukan abin da yake da shi cikin hannuna.

9 Bai fi ni iko cikin gidan nan ba, ba kuma abin da ya hana mini sai ke kaɗai, domin ke matarsa ce. Ƙaƙa fa zan aikata wannan babbar mugunta, in yi wa Allah zunubi?”

10 Ko da yake ta yi ta yi wa Yusufu magana yau da gobe, amma bai biye mata ya kwana da ita ko su zauna tare ba.

11 Amma wata rana, sa’ad da ya shiga cikin gida ya yi aikinsa, mazajen gidan kuma ba wanda yake gidan,

12 sai ta kama rigarsa, tana cewa, “Ka kwana da ni.” Amma ya bar rigarsa a hannunta ya gudu ya fita.

13 Da ta ga ya bar rigarsa a hannunta ya gudu, ya fita waje,

14 sai ta yi kira ga mutanen gidan, ta ce musu, “Ku duba ku gani, ya kawo mana Ba’ibrane ya ci mutuncinmu. Ya zo wurina don ya kwana da ni, sai na yi ihu da ƙarfi.

15 Da ya ji na ta da murya na yi ihu, ya kuwa gudu ya bar rigarsa, ya fita waje.”

16 Ta ajiye rigar a wurinta har maigidansa ya komo.

17 Sai ta mayar masa da magana, ta ce, “Baran nan, Ba’ibrane wanda ka kawo cikinmu, ya shigo wurina don ya ci mutuncina,

18 amma nan da nan da na ta da murya na yi ihu, sai ya gudu ya bar rigarsa a hannuna, ya gudu zuwa waje.”

19 Sa’ad da maigidan Yusufu ya ji abin da matarsa ta faɗa masa, “Ka ji yadda baranka ya yi da ni ke nan,” sai ya husata.

20 Maigidan Yusufu ya ɗauke shi ya māka shi a kurkuku, inda ‘yan sarƙa na sarki suke tsare, can ya zauna a kurkuku.

21 Amma Ubangiji yana tare da Yusufu, ya kuwa nuna masa madawwamiyar ƙauna, ya sa ya sami farin jini a wurin yarin kurkukun.

22 Yarin kurkuku ya shugabantar da Yusufu bisa dukan ‘yan sarƙa da suke a kurkuku, dukan abin da ake yi a wurin kuma shi yake yi.

23 Yarin kurkukun, ba ruwansa da dukan abin da Yusufu yake kula da shi, domin Ubangiji yana tare da shi, dukan abin da ya yi kuwa Ubangiji yakan sa wa abin albarka.

Categories
FAR

FAR 40

Yusufu Ya Fassara Mafarkan ‘Yan Kurkuku

1 Bayan waɗannan al’amura, sai mai shayarwa da mai tuya na Sarkin Masar suka yi wa maigidansu Sarkin Masar laifi.

2 Fir’auna ya yi fushi da ma’aikatan nan nasa biyu, wato shugaban masu shayarwa da shugaban masu tuya.

3 Ya ba da su a sa su kurkuku, cikin gidan shugaban masu tsaron fāda, wato kurkuku inda Yusufu yake a tsare.

4 Shugaban ‘yan tsaron ya danƙa su ga Yusufu don ya hidimta musu, sun kuwa jima a kurkukun har an daɗe.

5 Suka yi mafarki, su biyu ɗin, a dare ɗaya, da shi mai shayarwar da mai tuyar na gidan Sarkin Masar, waɗanda aka sa a kurkuku, kowanne kuwa da nasa mafarkin da kuma tasa irin fassarar mafarkin.

6 Da Yusufu ya zo wurinsu da safe, ya ga sun damu.

7 Sai ya tambaye su ya ce, “Me ya sa fuskokinku suke a yamutse yau?”

8 Suka ce masa, “Mafarkai muka yi, ba kuma wanda zai fassara mana su.”

Sai Yusufu ya ce musu, “Ashe, ba a wurin Allah fassarori suke ba? Ku faɗa mini su, ina roƙonku.”

9 Saboda haka, shugaban masu shayarwa ya faɗa wa Yusufu mafarkinsa, ya ce masa, “A mafarkina ga kurangar inabi a gabana.

10 A kurangar akwai rassa uku. Sai ta yi toho, ta huda nan da nan, ta kuma yi nonna, har suka nuna suka zama inabi.

11 Finjalin Fir’auna na hannuna, sai na ɗauki ‘ya’yan inabi na matse su cikin finjalin Fir’auna, na sa finjalin a hannun Fir’auna.”

12 Yusufu ya ce masa, “Wannan ita ce fassararsa, rassan nan uku, kwana uku ne,

13 bayan kwana uku Fir’auna zai ɗaukaka ka, ya komar da kai matsayinka, za ka kuma sa finjalin Fir’auna a hannunsa kamar dā lokacin da kake mai hidimar shayarwarsa.

14 Amma ka tuna da ni sa’ad da abin ya tabbata gare ka, sai ka yi mini alheri, ka ambace ni a wurin Fir’auna, har da za a fisshe ni daga wannan gida.

15 Gama ni, hakika sato ni aka yi daga ƙasar Ibraniyawa. A nan kuma ban yi wani abin da zai isa a sa ni a kurkuku ba.”

16 Sa’ad da shugaban masu tuya ya ga fassarar tana da kyau, sai ya ce wa Yusufu, “Ni ma cikin nawa mafarki, na ga kwanduna uku na waina a bisa kaina.

17 A kwandon da yake bisa ɗin akwai toye-toye iri iri domin Fir’auna, amma ga tsuntsaye suna ta ci daga cikin kwandon da yake bisa duka, wato wanda yake bisa kaina ɗin.”

18 Yusufu ya amsa, “Wannan ita ce fassararsa, kwandunan uku, kwana uku ne,

19 bayan kwana uku Fir’auna zai falle kanka ya rataye ka a bisa itace, tsuntsaye kuwa za su ci naman jikinka.”

20 A rana ta uku, wadda take ranar haihuwar Fir’auna, Fir’auna ya yi wa dukan bayinsa biki, sai ya kawo shugaban masu shayarwa da shugaban masu tuya a gaban fādawansa.

21 Ya komar da shugaban masu shayarwa a matsayinsa na shayarwa, ya kuwa miƙa finjali a hannun Fir’auna,

22 amma ya rataye shugaban masu tuya kamar yadda Yusufu ya fassara musu.

23 Duk da haka shugaban masu shayarwar bai tuna da Yusufu ba, amma ya manta da shi.