Categories
2 TAR

2 TAR 34

Sarki Yosiya na Yahuza

1 Yosiya yana da shekara takwas sa’ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki shekara talatin da ɗaya a Urushalima.

2 Ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji, yana bin al’amuran da kakansa Dawuda ya yi, bai kauce dama ko hagu ba.

Yosiya Yana Gāba da Arnanci

3 A shekara ta takwas ta mulkinsa, a lokacin yana yaro, sai ya fara neman Allah na kakansa Dawuda. A shekara ta goma, sha biyu, sai ya fara tsarkake Yahuza da Urushalima daga masujadai, da Ashtarot, da sassaƙaƙƙun siffofi, da siffofi na zubi.

4 Sai suka farfashe bagadai na Ba’al a gabansa, ya kuma tumɓuke bagadan ƙona turare waɗanda suke a bisansu. Ya ragargaza Ashtarot, da sassaƙaƙƙun siffofi, da na zubi, ya maishe su ƙura. Ya barbaɗa su a kan kaburbura waɗanda suka miƙa hadayu a kansu.

5 Ya kuma ƙone ƙasusuwan firistoci a bisa bagadansu, ya tsarkake Yahuza da Urushalima.

6 A biranen Manassa, da na Ifraimu, da na Saminu, har zuwa Naftali, a kangwayensu kewaye da su,

7 ya farfashe bagadai, ya buge Ashtarot da siffofi, ya maishe su gari, ya tumɓuke dukan bagadan ƙona turare a dukan ƙasar Isra’ila, sa’an nan ya koma Urushalima.

An Gano Littafin Shari’a

8 A shekara ta goma sha takwas ta mulkinsa, bayan da ya gama tsarkake ƙasar, da Haikalin, sai ya aiki Shafan ɗan Azaliya, da Ma’aseya mai mulkin birnin, da Yowa ɗan Yowahaz, wanda suke magatakarda domin su gyara Haikalin Ubangiji Allahnsa.

9 Sai suka zo wurin Hilkiya babban firist, suka ba shi kuɗin da aka kawo a Haikalin Allah, wanda Lawiyawa, masu tsaron ƙofa, suka tattara daga mutanen Manassa da na Ifraimu, daga sauran Isra’ila, da kuma na dukan Yahuza da Biliyaminu, tare da na mazaunan Urushalima.

10 Sai suka ba da kuɗin ga ma’aikata masu lura da Haikalin Ubangiji, da ma’aikatan da suke aiki a Haikalin Ubangiji, don gyare-gyare, su maishe shi kamar yadda yake dā,

11 sai suka ba masassaƙa da magina kuɗin, don su sayi sassaƙaƙƙun duwatsu, da katako, don yin tsaiko da tankar gine-ginen da sarakunan Yahuza suka bari, har suka lalace.

12 Mutanen fa suka yi aiki mai aminci tare da waɗanda suke lura da su domin su gabatar da aiki, wato Yahat da Obadiya, Lawiyawa, ‘ya’yan Merari, maza, da Zakariya da Meshullam na wajen ‘ya’yan Kohatawa, da waɗansu Lawiyawa da suke da gwanintar bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe.

13 Su ne shugabannin masu ɗaukar kaya, suke kuma nuna wa kowane ma’aikaci irin aikin da zai yi, waɗansu daga cikin Lawiyawa, magatakarda ne, da ma’aikatan hukuma, da masu tsaron ƙofofi.

14 Sa’ad da suke fitowa da kuɗin da aka kawo a Haikalin Ubangiji, sai Hilkiya firist ya gāno littafin Shari’ar Ubangiji wanda aka bayar ta hannun Musa.

15 Sai Hilkiya ya ce wa magatakarda Shafan, “Na gāno Littafin Shari’a a Haikalin Ubangiji.” Sai Hilkiya ya ba Shafan littafin.

16 Shafan kuma ya kai wa sarki littafin, sa’an nan ya faɗa wa sarki cewa, “Dukan abin da aka sa barorinka su yi suna yi.

17 Sai suka juye kuɗin da aka samu don Haikalin Ubangiji, suka miƙa wa masu lura da aikin, da ma’aikatan.”

18 Magatakarda Shafan kuwa ya faɗa wa sarki, ya ce, “Hilkiya firist ya ba ni wani littafi.” Sai Shafan ya karanta wa sarki littafin.

19 Da sarki ya ji irin maganganun da littafin ya faɗa, sai ya yayyage tufafinsa.

20 Sa’an nan sarki ya umarci Hilkiya, da Ahikan ɗan Shafan, da Akbor ɗan Mika, da magatakarda Shafan, da Asaya baran sarki, ya ce,

21 “Ku tafi ku yi tambaya a wurin Ubangiji domina, da kuma domin sauran waɗanda suka ragu a Isra’ila da Yahuza, a kan abin da littafin da aka gāno ya faɗa, gama Ubangiji ya yi fushi da mu da hasala mai tsanani saboda kakanninmu ba su kiyaye maganar Ubangiji, su aikata bisa ga dukan abin da aka faɗa a wannan littafi ba.”

22 Hilkiya kuwa tare da waɗanda sarki ya aika suka tafi wurin annabiya Hulda, matar Shallum ɗan Tikwa, ɗan Harhas, mai lura da wurin ajiyar tufafi, tana zaune a Urushalima, a unguwa ta biyu. Suka faɗa mata saƙon sarki,

23 sai ta ce musu, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya ce in faɗa wa mutumin da ya aiko gare shi,

24 ‘Ni Ubangiji, na ce zan kawo masifa a kan wannan wuri da a kan mazaunan wurin, wato dukan la’anar da aka rubuta a littafin da aka karanta a gaban Sarkin Yahuza.

25 Da yake sun bar bina suka ƙona turare ga gumaka domin su sa ni in yi fushi da dukan ayyukan hannuwansu, saboda haka zan yi fushi da wannan wuri, ba kuwa zan huce ba.’

26 Amma a kan Sarkin Yahuza wanda ya aike ku ku tambayi Ubangiji, ga abin da za ku faɗa masa, ‘Ni Ubangiji, Allah na Isra’ila na ce, a kan maganar da ka ji,

27 da yake zuciyarka mai tuba ce, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gaban Allah, sa’ad da ka ji maganarsa a kan wurin nan da mazaunan wurin, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gabana, ka yayyage tufafinka ka yi kuka a gabana, ni kuma na ji ka.

28 Ga shi, zan kai ka wurin da kakanninka suke, a kabarinka a binne ka da salama, ba za ka ga dukan masifun da zan kawo wa wurin nan da mazaunansa ba.’ ”

Sai suka isar da amsa wurin sarki.

Yosiya Ya Kawar da Arnanci

29 Sarki ya aika a kirawo dukan dattawan Yahuza da na Urushalima.

30 Sai sarki ya haura zuwa Haikalin Ubangiji tare da dukan mutanen Yahuza, da mazaunan Urushalima, da firistoci, da Lawiyawa, da dukan jama’a, babba da yaro. Sai ya karanta dukan maganar da take a littafin alkawari wanda aka gāno a Haikalin Ubangiji, a kunnen dukansu.

31 Sai sarkin ya miƙe tsaye a inda yake, ya yi alkawari a gaban Ubangiji, cewa zai bi Ubangiji, ya kiyaye umarnansa, da farillansa, da dokokinsa da zuciya ɗaya, da dukan ransa. Zai yi aiki da alkawarin da yake rubuce a wannan littafi.

32 Ya kuma sa dukan waɗanda suke a Urushalima da na Biliyaminu, su tsaya a kan wannan magana. Mazaunan Urushalima kuwa suka yi yadda alkawarin Allah ya ce, wato Allah na kakanninsu.

33 Yosiya kuwa ya kawar da dukan abubuwan banƙyama daga dukan ƙasar da jama’ar Isra’ila suke da ita. Ya sa dukan waɗanda suke a Isra’ila su bauta wa Ubangiji Allahnsu. A dukan kwanakin ransa, ba su kauce daga bin Ubangiji Allah na kakanninsu ba.

Categories
2 TAR

2 TAR 35

Yosiya Ya Yi Idin Ƙetarewa

1 Yosiya kuwa ya yi Idin Ƙetarewa ga Ubangiji a Urushalima. A rana ta goma sha huɗu ga wata na fari suka yanka ragon Idin Ƙetarewa.

2 Ya sa firistoci a matsayinsu, ya ƙarfafa su a hidimar Haikalin Ubangiji.

3 Ya kuma faɗa wa Lawiyawa, tsarkakakku na Ubangiji, waɗanda suke koya wa dukan Isra’ila, ya ce, “Ku sa tsattsarkan akwatin alkawari a Haikalin da Sulemanu ɗan Dawuda, Sarkin Isra’ila, ya gina. Ba za ku sāke ɗaukarsa bisa kafaɗunku ba. Yanzu fa sai ku kama hidimar Ubangiji Allahnku da jama’arsa Isra’ila.

4 Ku karkasa kanku bisa ga gidajen kakanninku ƙungiya ƙungiya, ku bi bayanin Dawuda, Sarkin Isra’ila, da na ɗansa Sulemanu.

5 Ku tsaya a Wuri Mai Tsarki, bisa ga ƙungiyoyin gidajen kakannin ‘yan’uwanku, waɗanda su ba firistoci ba ne. Kowanne ya sami kashi daga cikin gidan Lawiyawa.

6 Ku yanka abin Idin Ƙetarewa, ku tsarkake kanku, ku shirya wa ‘yan’uwanku su yi bisa ga maganar Ubangiji ta hannun Musa.”

7 Sarki Yosiya fa ya ba da gudunmawar abin yin hadaya ga waɗanda ba firistoci ba, waɗanda suke wurin, raguna da ‘yan awaki daga cikin garken tumaki da na awaki, yawansu ya kai dubu talatin (30,000) da kuma bijimai dubu uku (3,000). Waɗannan duk daga mallakar sarki ne.

8 Da yardar rai manyan ma’aikatansa, sarakunansa, suka ba da gudunmawa ga jama’ar, da firistoci, da Lawiyawa. Hilkiya, da Zakariya, da Yehiyel, manyan ma’aikatan Haikalin Allah, suka ba firistoci abin yin hadaya don Idin Ƙetarewa, tumaki da awaki dubu biyu da ɗari shida (2,600), da bijimai ɗari uku.

9 Konaniya kuma tare da Shemaiya da Netanel, ‘yan’uwansa, da Hashabiya, da Yehiyel, da Yozabad, shugabannin Lawiyawa, su suka ba Lawiyawa abin yin hadayar Idin Ƙetarewa, raguna da ‘yan awaki dubu biyar (5,000), da bijimai ɗari biyar.

10 Sa’ad da aka shirya yin hidimar, firistoci suka tsaya a wurinsu, Lawiyawa kuwa suka tsaya bisa ga ƙungiyoyinsu, yadda sarki ya umarta.

11 Sai suka yanka ragon Idin Ƙetarewar. Sa’an nan firistoci suka karɓi jinin daga gare su, suka yayyafa, Lawiyawa kuma suka yi ta fiɗa.

12 Sa’an nan suka keɓe hadayu na ƙonawa domin su rarraba bisa ga ƙungiyoyin gidajen kakanni waɗanda su ba firistoci ba ne, don su miƙa wa Ubangiji kamar yadda aka rubuta a littafin Musa. Haka nan kuma suka yi da bijiman.

13 Suka gasa ragon hadayar Idin Ƙetarewa bisa ga ka’idar, sai suka dafa tsarkakan hadayu a tukwane, da manyan tukwane, da kwanoni, nan da nan suka kai wa waɗanda ba firistoci ba.

14 Daga baya kuma suka shirya wa kansu da firistoci, saboda firistoci, ‘ya’yan Haruna, maza, suna ta hidimar miƙa hadayu na ƙonawa, da kuma na kitse, har dare. Don haka Lawiyawa suka shirya wa kansu abinci, suka kuma shirya wa firistoci, ‘ya’yan Haruna, maza.

15 Mawaƙa, ‘ya’yan Asaf, maza, suna wurinsu bisa ga umarnin Dawuda, da Asaf, da Heman, da kuma Yedutun maigani na sarki, matsaran ƙofofi kuma suna a kowace ƙofa, ba lalle sai su bar wurin hidimarsu gama ‘yan’uwansu Lawiyawa sun shirya musu nasu.

16 Haka fa aka shirya dukan hidimar Ubangiji a wannan rana, domin su kiyaye Idin Ƙetarewa, domin kuma su miƙa hadayu na ƙonawa a bisa bagaden Ubangiji, yadda Yosiya sarki ya umarta.

17 Jama’ar Isra’ila waɗanda suke wurin, suka kiyaye Idin Ƙetarewa, da kuma idin abinci marar yisti har kwana bakwai.

18 Ba a taɓa yin Idin Ƙetarewa irin wannan ba tun kwanakin annabi Sama’ila, ba wani kuma daga cikin sarakunan Isra’ila da ya kiyaye Idin Ƙetarewa kamar yadda Yosiya ya kiyaye shi tare da firistoci, da Lawiyawa, da dukan mutanen Yahuza da na Isra’ila, waɗanda suke a wurin, da kuma mazaunan Urushalima.

19 A shekara ta goma sha takwas ta mulkin Yosiya aka yi Idin Ƙetarewa.

Rasuwar Yosiya

20 Bayan wannan duka, sa’ad da Yosiya ya shirya Haikali, sai Neko Sarkin Masar, ya zo don ya yi yaƙi a Karkemish wadda take a Yufiretis, sai Yosiya ya fito don ya kara da shi.

21 Amma Neko ya aika ‘yan saƙo su faɗa masa su ce, “Me ya gama mu da juna, ya Sarkin Yahuza? Ban zo in yi yaƙi da kai ba. Na zo ne in yi yaƙi da Sarkin Assuriya! Ka ƙyale ni! Allah ne ya riga ya faɗa mini in hanzarta. Kada ka yi gāba da Allah, wanda yake tare da ni, don kada ya hallaka ka.”

22 Duk da haka Yosiya bai yarda ya koma ba, sai ya ɓad da kama don ya yi yaƙi da shi. Bai yarda da magana wadda Allah ya faɗa wa Neko ba, sai suka kama yaƙi a filin Magiddo.

23 Maharba suka harbi sarki Yosiya, sai ya ce wa barorinsa, “Ku ɗauke ni ku tafi da ni, gama an yi mini mummunan rauni.”

24 Barorinsa kuwa suka ɗauke shi daga cikin karusa, suka sa shi a karusa ta biyu, suka kawo shi Urushalima, sai ya rasu. Aka binne shi a hurumin kakanninsa. Yahuza da Urushalima fa suka yi makoki domin Yosiya.

25 Irmiya kuma ya hurta makoki domin Yosiya. Haka nan kuma dukan mawaƙa mata da maza, suka ambaci Yosiya cikin makokinsu har yau. Suka sa waɗannan su zama farali a Isra’ila, ga shi kuma, an rubuta su a Littafin Makoki.

26 Sauran ayyukan Yosiya, da kyawawan ayyukansa, waɗanda ya yi bisa ga abin da aka rubuta a Shari’ar Ubangiji,

27 ayyukansa na fari da na ƙarshe, an rubuta su a littafin sarakunan Isra’ila da na Yahuza.

Categories
2 TAR

2 TAR 36

Sarki Yehowahaz na Yahuza

1 Jama’ar ƙasa kuwa suka ɗauki Yehowahaz ɗan Yosiya suka naɗa shi sarki. Ya gaji tsohonsa a Urushalima.

2 Yehowahaz yana da shekara ashirin da uku sa’ad da ya ci sarauta, ya kuwa yi mulki a Urushalima wata uku.

3 Sai Sarkin Masar ya tuɓe shi daga sarautarsa ta Urushalima, ya sa su biya gandu, su ba da azurfa talanti ɗari, da zinariya talanti guda.

4 Sarkin Masar ya naɗa Eliyakim, ɗan’uwansa, sarki a Yahuza da Urushalima. Ya sa masa sabon suna Yehoyakim. Amma Neko ya ɗauko Yehowahaz ɗan’uwan Eliyakim ya kai shi Masar.

Sarki Yehoyakim na Yahuza

5 Yehoyakim yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya ci sarauta. Ya yi shekara goma sha ɗaya yana sarauta a Urushalima. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji Allahnsa.

6 Sai Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya hauro ya kara da shi. Ya kama shi, ya ɗaure shi da sarƙoƙi, ya kai shi Babila.

7 Nebukadnezzar kuma ya kwaso waɗansu tasoshi da tukwane na Haikalin Ubangiji, ya kai Babila, ya ajiye su a fādar Babila.

8 Sauran ayyukan Yehoyakim da irin abubuwan da ya yi na banƙyama, da irin laifofinsa, suna nan, an rubuta su a littafin sarakunan Isra’ila da na Yahuza. Ɗansa Yekoniya kuwa ya gāji gadon sarautarsa.

An Kama Sarki Yekoniya

9 Yekoniya yana da shekara takwas sa’ad da ya ci sarauta, ya yi sarauta a Urushalima wata uku da kwana goma. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji.

10 Da bazara sai sarki Nebukadnezzar ya aika aka kawo shi Babila tare da kayayyaki masu daraja na Haikalin Ubangiji. Ya kuma naɗa Zadakiya ɗan’uwan Yekoniya ya zama Sarkin Yahuza da Urushalima.

Sarki Zadakiya na Yahuza

11 Zadakiya yana da shekara ashirin da ɗaya sa’ad da ya ci sarauta, ya yi shekara goma sha ɗaya yana sarautar Urushalima.

12 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji Allahnsa. Bai nuna ladabi a gaban annabi Irmiya ba, wanda ya faɗa masa abin da Ubangiji ya ce.

Fāɗuwar Urushalima

13 Ya kuwa tayar wa sarki Nebukadnezzar wanda ya rantsar da shi da Allah. Amma ya ƙi kula, ya taurare zuciyarsa gāba da Ubangiji, Allah na Isra’ila.

14 Dukan manyan firistoci da sauran jama’a gaba ɗaya, sun zama marasa aminci ƙwarai suna aikata dukan abubuwan banƙyama da al’ummai suke yi. Suka ƙazantar da Haikalin Ubangiji wanda ya tsarkake a Urushalima.

15 Sai Ubangiji, Allah na kakanninsu, ya yi ta aika musu da manzanni saboda yana juyayin jama’arsa da wurin zaman zatinsa.

16 Sai suka yi ta yi wa manzannin Allah ba’a, suka raina maganarsa, suka yi wa annabawansa ba’a, sai Ubangiji ya husata da jama’arsa don abin ya kai intaha.

An Kai Yahuza Bautar Talala

17 Don haka Ubangiji ya bashe su ga Sarkin Kaldiyawa wanda ya karkashe samarinsu da takobi a Haikali, bai yi juyayin saurayi, ko budurwa, ko tsoho, ko gajiyayye ba. Allah ya bashe su duka a hannunsa.

18 Ya kwaso dukan kayayyakin da suke a Haikalin Allah, manya da ƙanana, da dukiyar da take a Haikalin Allah, da ta sarki, da ta sarakunansa ya kai su Babila.

19 Suka ƙone Haikalin Allah suke rushe garun Urushalima, suka ƙone dukan fādodinta, suka lalatar da dukan kayanta masu daraja.

20 Waɗanda ba a kashe ba kuwa ya kwashe su, ya kai Babila, suka zama bayinsa da na ‘ya’yansa maza har zuwa kahuwar mulkin Farisa,

21 don maganar ta cika wadda Ubangiji ya faɗa ta bakin Irmiya, har lokacin da ƙasar take shan hutawar asabatanta na zamanta kango har shekara saba’in, ta kiyaye asabatai.

22 Ubangiji kuwa ya iza Sairus Sarkin Farisa a shekarar da ya ci sarauta, domin a cika maganar da Ubangiji ya faɗa wa Irmiya. Sai ya yi shela a dukan ƙasar mulkinsa, aka kuma rubuta shelar.

23 Ga shelar, “In ji Sairus Sarkin Farisa, Ubangiji, Allah na samaniya ya ba ni sarautar dukan duniya, ya kuma umarce ni in gina masa Haikali a Urushalima, ta ƙasar Yahuza. Duk wanda yake na mutanensa da suke nan, Ubangiji Allahnsa ya kasance tare da shi, bari ya haura zuwa can Urushalima.”

Categories
EZRA

EZRA 1

Umarnin Sarki Sairus Yahudawa su Koma

1 Ubangiji kuwa ya iza Sairus Sarkin Farisa a shekarar da ya ci sarauta, domin a cika maganar da Ubangiji ya faɗa wa Irmiya. Sai ya yi shela a dukan ƙasar mulkinsa, aka kuma rubuta shelar.

2 Ga shelar, “In ji Sairus Sarkin Farisa, Ubangiji, Allah na samaniya ya ba ni sarautar dukan duniya, ya kuma umarce ni in gina masa Haikali a Urushalima, ta ƙasar Yahuza.

3 Duk wanda yake na mutanensa da yake nan Ubangiji Allahnsa ya kasance tare da shi, bari ya haura zuwa can Urushalima ta ƙasar Yahuza don ya sāke gina Haikalin Ubangiji, Allah na Isra’ila, shi ne Allah wanda ake masa sujada a Urushalima.

4 A duk inda akwai wani Bayahude, sai mutanen wurin su taimake shi da azurfa, da zinariya, da kaya, da dabbobi, tare da waɗansu kyautai na yardar rai saboda Haikalin Ubangiji wanda yake a Urushalima.”

Komowar Kamammu zuwa Urushalima

5 Shugabannin gidajen kakanni na Yahuza kuwa, da na Biliyaminu, da firistoci, da Lawiyawa, da duk wanda Ubangiji ya taɓa shi, suka tashi don su tafi su sāke gina Haikalin Ubangiji wanda yake a Urushalima.

6 Dukan waɗanda suke kewaye da su, suka taimake su da azurfa, da zinariya, da kayayyaki, da dabbobi, da abubuwa masu daraja, da kyautai na yardar rai.

7 Sarki Sairus kuma ya fito da kayayyakin Haikalin Ubangiji, waɗanda Nebukadnezzar ya kwashe daga Urushalima ya ajiye su a haikalin gumakansa.

8 Sairus Sarkin Farisa ya sa ma’aji, Mitredat, ya fito da kayayyakin, ya ƙidaya wa Sheshbazzar, shugaban Yahuza.

9 Yawan kayayyakin ke nan, kwanonin zinariya guda talatin, da kwanonin azurfa guda dubu (1,000), da wuƙaƙe guda ashirin da tara,

10 da finjalai na zinariya guda talatin, da tasoshi na azurfa ɗari huɗu da goma, da waɗansu kayayyaki guda dubu (1,000).

11 Jimillar kayayyakin duka, na zinariya da na azurfa, dubu biyar da arbaminya (5,400). Sheshbazzar ya tafi da waɗannan kayayyaki duka tare da kamammun da suka komo daga Babila.

Categories
EZRA

EZRA 2

Yawan Kamammu da suka Komo.

1 Waɗannan su ne mutanen da suka bar lardin Babila suka komo Urushalima da Yahuza daga bautar talala da Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya kai su Babila. Kowa ya koma garinsu.

2 Sun komo tare da Zarubabel, da Yeshuwa, da Nehemiya, da Seriya, da Re’elaya, da Mordekai, da Bilshan, Misfar, da Bigwai, da Rehun, da Ba’ana.

Ga jerin iyalan Isra’ila, da yawan waɗanda suka komo na kowane iyali daga zaman talala.

3-20 Zuriyar Farosh, mutum dubu biyu da ɗari da saba’in da biyu (2,172)

Zuriyar Shefatiya, mutum ɗari uku da saba’in da biyu

Zuriyar Ara,mutum ɗari bakwai da saba’in da biyar

Zuriyar Fahat-mowab na zuriyar Yeshuwa da Yowab, mutum dubu biyu da ɗari takwas da goma sha biyu (2,812)

Zuriyar Elam, mutum dubu da ɗari biyu da hamsin da huɗu (1,254)

Zuriyar Zattu, mutum ɗari tara da arba’in da biyar

Zuriyar Zakkai, mutum ɗari bakwai da sittin

Zuriyar Bani, mutum ɗari shida da arba’in da biyu

Zuriyar Bebai, mutum ɗari shida da ashirin da uku

Zuriyar Azgad, mutum dubu da ɗari biyu da ashirin da biyu (1,222)

Zuriyar Adonikam, mutum ɗari shida da sittin da shida

Zuriyar Bigwai, mutum dubu biyu da hamsin da shida (2,056)

Zuriyar Adin, mutum ɗari huɗu da hamsin da huɗu

Zuriyar Ater na Hezekiya, mutum tasa’in da takwas

Zuriyar Bezai, mutum ɗari uku da ashirin da uku

Zuriyar Yora, mutum ɗari da goma sha biyu

Zuriyar Hashum, mutum ɗari biyu da ashirin da uku

Zuriyar Gibeyon, mutum tasa’in da biyar

21-35 Mutanen da suke a garuruwan nan, su ma suka komo.

Mutanen Baitalami, mutum ɗari da ashirin da uku

Mutanen Netofa, mutum hamsin da shida

Mutanen Anatot, mutum ɗari da ashirin da takwas

Zuriyar Azmawet, mutum arba’in da biyu

Zuriyar Kiriyat-yeyarim, da Kefira, da Biyerot, mutum ɗari bakwai da arba’in da uku

Zuriyar Rama da Geba, mutum ɗari shida da ashirin da ɗaya

Mutanen Mikmash, mutum ɗari da ashirin da biyu

Mutanen Betel da Ai, mutum ɗari biyu da ashirin da uku

Zuriyar Nebo, mutum hamsin da biyu

Zuriyar Magbish, mutum ɗari da hamsin da shida

Zuriyar wancan Elam, mutum dubu da ɗari biyu da hamsin da huɗu (1,254)

Zuriyar Harim, mutum ɗari uku da ashirin

Zuriyar Lod, da Hadid, da Ono, mutum ɗari bakwai da ashirin da biyar

Mutanen Yariko, mutum ɗari uku da arba’in da biyar

Zuriyar Senaya, mutum dubu uku da ɗari shida da talatin (3,630)

36-39 Ga kuma lissafin iyalan firistocin da suka komo,

Zuriyar Yedaiya na gidan Yeshuwa, mutum ɗari da saba’in da uku

Zuriyar Immer, mutum dubu da hamsin da biyu (1,052)

Zuriyar Fashur,mutum dubu da ɗari biyu da arba’in da bakwai (1,247)

Zuriyar Harim, mutum dubu da goma sha bakwai (1,017)

40 Lawiyawa na zuriyar Yeshuwa da Kadmiyel na Hodawiya mutum saba’in da huɗu.

41 Mawaƙa na zuriyar Asaf, mutum ɗari da ashirin da takwas.

42 Zuriyar Shallum, da ta Ater, da ta Talmon, da ta Akkub, da ta Hatita, da ta Shobai, su ne zuriyar matsaran ƙofa, yawan mutanensu duka ɗari da talatin da tara.

43-54 Ga lissafin ma’aikatan Haikali da suka komo.

Zuriyar Ziha, da zuriyar Hasufa, da zuriyar Tabbawot

Zuriyar Keros, da zuriyar Siyaha, da zuriyar Fadon

Zuriyar Lebana, da zuriyar Hagaba, da zuriyar Akkub

Zuriyar Hagab, da zuriyar Shamlai, da zuriyar Hanan

Zuriyar Giddel, da zuriyar Gahar, da zuriyar Rewaiya

Zuriyar Rezin,da zuriyar Nekoda, da zuriyar Gazam

Zuriyar Ussa, da zuriyar Faseya, da zuriyar Besai

Zuriyar Asna, da Me’uniyawa, da Nefushiyawa

Zuriyar Bakbuk, da zuriyar Hakufa da zuriyar Harhur

Zuriyar Bazlut, da zuriyar Mehida, da zuriyar Harsha

Zuriyar Barkos, da zuriyar Sisera, da zuriyar Tema

Zuriyar Neziya, da zuriyar Hatifa

55-57 Zuriyar barorin Sulemanu, su ne

Zuriyar Sotai, da zuriyar Hassoferet, da zuriyar Feruda

Zuriyar Yawala, da zuriyar Darkon, da zuriyar Giddel

Zuriyar Shefatiya, da zuriyar Hattil, da zuriyar Fokeret-hazzebayim, da zuriyar Ami

58 Dukan zuriyar ma’aikatan Haikali da zuriyar barorin Sulemanu su ɗari uku da tasa’in da biyu ne.

59 Waɗannan su ne waɗanda suka zo daga Tel-mela, da Tel-harsha, da Kerub, da Addan, da Immer, amma ba su iya tabbatar da gidajen kakanninsu da asalinsu ba, ko su na Isra’ila ne.

60 Su ne zuriyar Delaiya, da zuriyar Tobiya, da zuriyar Nekoda. Su ɗari shida da hamsin da biyu ne.

61 Sai kuma zuriyar firistoci, wato zuriyar Habaya, da zuriyar Hakkoz, da zuriyar Barzillai, wanda ya auri mata daga cikin ‘ya’yan Barzillai, mata, mutumin Gileyad, aka kira shi da sunnansu,

62 suka bincika littafin asalin kakanninsu, amma suka ga ba su a ciki. Don haka aka mai da su ƙazantattu, ba a yarda musu su yi aikin firist ba.

63 Sai mai mulki ya ce ba za su ci abinci mafi tsarki ba, sai firist ya shawarci Urim da Tummim tukuna, wato kamar kuri’a ke nan.

64-67 Yawan taron jama’a su dubu arba’in da biyu da ɗari uku da sittin (42,360).

Barorinsu maza da mata, dubu bakwai da ɗari uku da talatin da bakwai (7,337)

Mawaƙa ɗari biyu mata da maza

Dawakansu ɗari bakwai da talatin da shida

Alfadaransu ɗari biyu da arba’in da biyar

Raƙumansu kuma ɗari huɗu da talatin da biyar ne

Jakunansu kuwa dubu shida da ɗari bakwai da ashirin (6,720)

68 Waɗansu shugabannin gidajen kakanninsu, sa’ad da suka isa Haikalin Ubangiji a Urushalima, sai suka bayar da kyautai da yardar rai don a sāke gina Haikalin Ubangiji a wurin da yake dā.

69 Gwargwadon arzikinsu suka ba da darik dubu sittin da dubu ɗaya (61,000) na zinariya, da maina dubu biyar (5,000) na azurfa, da tufafin firistoci guda ɗari.

70 Firistoci, da Lawiyawa, da waɗansu mutanen da suke zaune a Urushalima da kewayenta, da mawaƙa, da masu tsaron ƙofofi, da ma’aikatan Haikalin, da dukan mutanen Isra’ila suka zauna a garuruwansu.

Categories
EZRA

EZRA 3

An Komo da Yin Sujada

1 Da tsayawar watan bakwai, sai mutanen Isra’ila waɗanda suka riga suka koma garuruwansu, suka taru gaba ɗaya a Urushalima.

2 Sai Yeshuwa ɗan Yehozadak tare da ‘yan’uwansa, firistoci, da Zarubabel ɗan Sheyaltiyel tare da ‘yan’uwansu, suka tashi suka gina bagaden Allah na Isra’ila domin a miƙa hadayu na ƙonawa kamar yadda aka rubuta a dokokin Musa, mutumin Allah.

3 Suka ta da bagaden a wurinsa domin suna jin tsoron mutanen ƙasar. Suka miƙa wa Ubangiji hadayu na ƙonawa safe da yamma.

4 Suka kuma kiyaye Idin Bukkoki kamar yadda aka rubuta, suna miƙa hadayu na ƙonawa kowace rana bisa ga yawan adadin hadayun da ake bukata.

5 Daga baya kuma suka miƙa hadayun ƙonawa na yau da kullum, da hadayu na amaryar wata, da ƙayyadaddun hadayu na idodin Ubangiji, da hadayu na amaryar wata, da ƙayyadaddun Ubangiji.

6 Tun daga rana ta fari ga watan bakwai, suka fara miƙa wa Ubangiji hadayu na ƙonawa, amma ba a riga an aza harsashin Haikalin Ubangiji ba.

An Fara Gina Haikali

7 Sai suka ba magina da masassaƙa kuɗin, suka kuma ba Sidoniyawa da mutanen Taya abinci, da abin sha, da mai don su kawo itacen al’ul daga Lebanon zuwa teku a Yafa bisa ga izinin da suka samu daga wurin sarki Sairus.

8 A watan biyu na shekararsu ta biyu da suka komo wurin Haikalin Allah a Urushalima, sai Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, da Yeshuwa ɗan Yehozadak, da sauran ‘yan’uwansu firistoci, da Lawiyawa da dukan waɗanda suka komo Urushalima daga bauta suka fara aikin ginin. Suka sa Lawiyawa ‘yan shekara ashirin zuwa gaba su yi shugabancin aikin ginin Haikalin Ubangiji.

9 Sai Yeshuwa da ‘ya’yansa da danginsa, da Kadmiyel da ‘ya’yansa, da ‘ya’yan Hodawiya, da ‘ya’yan Henadad, duk Lawiyawa ne, suka yi shugabancin aikin ginin Haikalin Allah.

10 Sa’ad da maginan suka aza harsashin ginin Haikalin Ubangiji, firistoci suna nan tsaye saye da rigunansu, suna riƙe da ƙahoni, Lawiyawa kuma ‘ya’yan Asaf, suna riƙe da kuge domin su yabi Ubangiji, bisa ga umarnin Dawuda, Sarkin Isra’ila.

11 Da bangirma suka raira waƙa ta yabo da godiya ga ubangiji, suna cewa,

“Ubangiji nagari ne,

Gama ƙaunarsa marar matuƙa ce,

Ta tabbata har abada ga Isra’ila.”

Sai mutane duka suka ɗaga murya da ƙarfi suka yabi Ubangiji, saboda an aza harsashin ginin Haikalin Ubangiji.

12 Amma da yawa daga cikin firistoci, da Lawiyawa, da shugabannin gidajen kakanni, wato tsofaffi waɗanda suka ga Haikali na farko, suka yi kuka da babbar murya a sa’ad da suka ga an aza harsashin ginin wannan Haikali. Waɗansu kuwa suka yi sowa don farin ciki.

13 Saboda haka mutane ba su iya rarrabe amon muryar murna da ta kuka ba, gama mutanen suka ɗaga murya da ƙarfi har aka ji su daga nesa.

Categories
EZRA

EZRA 4

Magabta Suna Hana Aiki

1 Sa’ad da abokan gāban Yahuza da Biliyaminu suka ji waɗanda suka komo daga bauta suna gina Haikalin Ubangiji Allah na Isra’ila,

2 sai suka tafi wurin Zarubabel, da shugabannin gidajen kakanni, suka ce musu, “Ku yarda mana mu yi ginin tare, gama muna yi wa Allahnku sujada kamar yadda kuke yi, muna kuma ta miƙa masa sadaka tun kwanakin Esar-haddon, Sarkin Assuriya, wanda ya kawo mu nan.”

3 Amma Zarubabel, da Yeshuwa, da shugabannin gidajen kakannin Isra’ila suka ce musu, “Ba abin da za ku yi tare da mu na ginin Haikalin Allahnmu, amma mu kaɗai za mu yi wa Ubangiji Allah na Isra’ila, gini kamar yadda sarki Sairus, wato Sarkin Farisa, ya umarce mu.”

4 Sai mutanen ƙasar suka shiga karya zuciyar jama’ar Yahuza, su kuwa suka ji tsoron yin gini.

5 Mutanen kuwa suka yi ijara da mashawarta, da za su sa niyyarsu ta shiririce tun daga zamanin Sairus, Sarkin Farisa, har zuwa zamanin Dariyus, Sarkin Farisa.

6 A farkon sarautar Ahasurus, sai suka rubuta takarda ƙara a kan mazaunan Yahuza, da Urushalima.

Takarda Zuwa ga Sarki

7 A zamanin Artashate kuma sai Bishlam, da Mitredat, da Tabeyel, da magoya bayansu suka rubuta wa Artashate Sarkin Farisa takarda da harufan Suriya, aka fassara ta.

8 Rehum shugaban sojoji, da Shimshai magatakarda, suka rubuta takardar ƙara a kan Urushalima zuwa Sarki Artashate.

9 Sa’an nan Rehum shugaban sojoji ya rubuta tare da Shimshai magatakarda,da abokansu, da alƙalai, da masu mulkin larduna, da ma’aikatan hukumomi, wato mutanen Farisa, da na Erek, da na Babila, da na Shusha a ƙasar Elam,

10 da sauran al’ummai, waɗanda mai girma, Asnaffar, ya kwaso, ya zaunar da su a biranen Samariya, da sauran wurare na Yammacin Kogi.

11 Ga abin da suka rubuta.

“Gaisuwa daga talakawanka, mutane na hayin Kogin zuwa ga sarki Artashate.

12 “Muna sanar da sarki, cewa Yahudawan nan waɗanda suka fito daga gare ka suka zo wurinmu, sun tafi Urushalima, suna sāke gina mugun birnin nan na tawaye, sun fara gina garun, ba da jimawa ba za su gama ginin.

13 Sarki ya sani fa, idan an sāke gina birnin, aka kuma gama garun, ba za su biya haraji ko kuɗin shiga da fita na kaya ko kuɗin fito ba, baitulmalin sarki za ta rasa kuɗi ke nan.

14 Da yake muke cin moriyar fāda, ba daidai ba ne mu bari a raina sarki. Saboda haka muke sanar da sarki,

15 domin a bincika a littattafan tarihin kakanninka. Za ka gani a littattafan tarihi, cewa wannan birni na tayarwa ne, mai yin ta’adi ga sarakuna da larduna. A nan ne aka ta da hargitsi a dā. Shi ya sa aka lalatar da shi.

16 Muna sanar da sarki fa, idan aka sāke gina wannan birni da garunsa, ba za ka sami abin mallaka a lardin Yammacin Kogi ba.”

Amsar Sarki

17 Sarki kuma ya aika musu da amsa ya ce, “Gaisuwa zuwa ga Rehum shugaban sojoji, da Shimshai magatakarda, da abokansu waɗanda suke zaune a Samariya da lardin Yammacin Kogi.

18 “An karanta mini wasiƙar da kuka aiko mana, filla filla.

19 Na ba da umarni, aka bincika, aka kuwa tarar, cewa wannan birni ya tayar wa sarakuna a dā, an yi tawaye da hargitsi cikinsa.

20 Manya manyan sarakuna sun yi sarauta a Urushalima, waɗanda suka yi mulki a kan dukan lardin Yammacin Kogi, waɗanda aka biya su haraji, da kuɗin shiga da fita na kaya, da kuɗin fito.

21 Saboda haka sai ka umarci waɗannan mutane su daina gina birnin nan, sai lokacin da na ba da umarni.

22 Ka kula fa, kada ka yi kasala a wannan al’amari, don me ɓarna za ta bunƙasa har ta cuci sarki?”

23 Sa’ad da aka karanta wa Rehum, da Shamshai magatakarda, da abokansu, wasiƙar sarki Artashate, suka hanzarta suka tafi wurin Yahudawa a Urushalima, suka gwada musu iko, suka tilasta musu su daina ginin.

24 An tsai da aikin Haikalin Allah a Urushalima, sai a shekara ta biyu ta sarautar Dariyus Sarkin Farisa.

Categories
EZRA

EZRA 5

An Sāke Kama Aikin Gina Haikali

1 Haggai kuwa, da Zakariya ɗan Iddo, annabawa, suka yi wa Yahudawan da suke a Yahuza da Urushalima wa’azi da sunan Allah na Isra’ila wanda yake iko da su.

2 Sai Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, da Yeshuwa ɗan Yehozodak, suka tashi suka sāke kama aikin gina Haikalin Allah wanda yake a Urushalima. Annabawan Allah suna tare da su, suna taimakonsu.

3 A wannan lokaci kuma, sai Tatenai, mai mulkin lardin Yammacin Kogi, da Shetar-bozenai, da abokansu suka je wurinsu suka yi magana da su, suka ce, “Wa ya ba ku izini ku gina Haikalin nan, har ku gama wannan garu?”

4 Suka kuma tambaye su, “Ina sunayen waɗanda suke yin wannan gini?”

5 Amma ikon Allah yana kan dattawan Yahudawa, saboda haka ba su hana su yin ginin ba, sai sun kai wa Dariyus labari, sun sami amsa a rubuce tukuna.

6 Wannan ita ce wasiƙar da Tattenai mai mulkin lardin Yammacin Kogi, da Shetar-bozenai, da abokansu ma’aikatan hukuma waɗanda suke Yammacin Kogi, suka aika wa sarki Dariyus.

7 “Zuwa ga sarki Dariyus, salama gare ka.

8 Muna sanar da sarki, cewa mun tafi lardin Yahuza a wurin Haikalin Allah Mai Girma. Ana ginin Haikalin da manyan duwatsu, ana kuma sa katakai a bango. Aikin yana ci gaba sosai a hannunsu.

9 “Mun yi magana da dattawan, muka tambaye su wane ne ya ba su izini su gina wannan Haikali har su gama bangonsa.

10 Mun kuma tambaye su sunayensu don mu rubuta maka sunayen mutanen da suke shugabanninsu.

11 To, sai suka ce mana, ‘Mu bayin Allah ne wanda yake da sama da ƙasa, muna sāke gina Haikalin da wani babban sarki na Isra’ila ya gina tun shekaru da yawa da suka wuce.

12 Amma saboda kakanninmu suka tsokani Allah na Sama, sai ya bashe su a hannun Nebukadnezzar, Sarkin Babila, mutumin Kaldiya. Shi ne ya lalatar da Haikalin nan, ya kuma kwashe jama’a zuwa Babila.

13 Amma a shekara ta fari ta sarautar Sairus, Sarkin Babila, sai ya ba da izini a sāke gina wannan Haikali na Allah.

14 Kwanonin zinariya da na azurfa na Haikalin Allah, waɗanda Nebukadnezzar ya kwashe daga cikin Haikalin da yake Urushalima, zuwa haikalin gumaka na Babila, sarki Sairus ya ɗauke su daga haikalin Babila ya ba wani mai suna Sheshbazzar wanda ya naɗa shi mai mulki.

15 Ya ce masa, ya ɗauki waɗannan kwanoni, ya tafi, ya sa su cikin Haikalin da yake a Urushalima, a sāke gina Haikalin Allah a wurin da yake a dā.’

16 Sheshbazzar kuwa ya zo ya aza harsashin ginin Haikalin Allah wanda yake a Urushalima. Tun daga wannan lokaci, har yanzu ana ta gininsa, har yanzu kuma ba a gama ba.

17 Domin haka in ya gamshi sarki, sai a bincike ɗakin littattafan da yake Babila don a gani ko sarki Sairus ya ba da izini a sāke gina wannan Haikalin Allah a Urushalima. Bari sarki ya aiko mana da abin da ya gani a kan wannan al’amari.”

Categories
EZRA

EZRA 6

An Gano Umarnin Sarki Sairus

1 Sarki Dariyus kuwa ya ba da umarni a bincike ɗakin littattafai na Babila, inda aka ajiye takardun shaida.

2 Sai aka sami takarda a Ekbatana, babban lardin Mediya. A cikin takardar aka iske rubutu don tunawa.

3 “A shekara ta fari ta sarautar sarki Sairus, sai ya ba da izini a sāke gina Haikalin Allah da yake a Urushalima, wurin da za a miƙa sadaka da hadayu na ƙonawa. Sai a aza harsashi da ƙarfi. Tsayinsa zai zama kamu sittin, fāɗinsa kuwa kamu sittin.

4 Za a jera manyan duwatsu jeri uku, da jeri ɗaya na katako, a kuma biya kuɗin aikin daga baitulmalin sarki.

5 A kuma kawo kwanonin nan na zinariya da na azurfa cikin Haikalin Allah, waɗanda Nebukadnezzar ya kwaso daga cikin Haikali a Urushalima ya kawo Babila, a komar da su, a mayar da su a Haikali a Urushalima, a ajiye kowanne a wurinsa a Haikalin Allah.”

Sarki Dariyus Ya Umarta a Ci gaba da Aiki

6 Sarki Dariyus ya ce, “Zuwa ga Tattenai, mai mulkin Yammacin Kogi, da Shetar-bozenai, da abokansu, wato ma’aikatan hukuma na lardin Yammacin Kogi, ku nisance su.

7 “Ku ƙyale aikin Haikalin nan na Allah kawai, ku ƙyale masu mulkin Yahudawa da dattawan Yahudawa, su sāke gina Haikalin Allah a wurin da yake a dā.

8 Ina umartarku ku biya wa dattawan Yahuza kuɗin sāke ginin Haikalin nan na Allah, a biya mutanen nan cikakken kuɗin aiki daga baitulmalin sarki, wanda yake a lardin Yammacin Kogi, ba tare da ɓata lokaci ba.

9 A ba su duk abin da suke bukata, wato kamar ‘yan bijimai, da raguna, da ‘yan tumaki domin yi wa Allah na Sama hadayun ƙonawa, da alkama, da gishiri, da ruwan inabi, da man naɗawa yadda firistoci a Urushalima suke bukata, sai a ba su kowace rana banda fashi,

10 domin su miƙa wa Allah na Sama sadaka mai daɗin ƙanshi, su kuma yi addu’a saboda sarki da ‘ya’yansa.

11 Na kuma umarta, cewa duk wanda ya karya wannan doka, sai a fitar da itace daga cikin gidansa, a fiƙe kan itacen, a tsire mutumin, sa’an nan a mai da gidansa juji.

12 Allah wanda ya sa sunansa ya kasance a Urushalima, ya hamɓarar da kowane sarki, ko al’umma waɗanda za su sāke wannan doka don su lalatar da Haikalin Allah da yake a Urushalima. Ni Dariyus na kafa wannan doka. Lalle ne a kiyaye dokata sarai.”

An Ƙeɓe Haikalin

13 Saboda maganar sarki Dariyus, sai Tattenai mai mulkin lardin Yammacin Kogi, da Shetar-bozenai, da abokansu suka aikata abin da sarki Dariyus ya umarta da aniya.

14 Dattawan Yahuza suka yi nasarar ginin ta wurin wa’azin annabi Haggai da Zakariya ɗan Iddo. Suka gama ginin bisa ga umarnin Allah na Isra’ila, da umarnin Sairus, da Dariyus, da Artashate sarakunan Farisa.

15 An gama ginin Haikali a ran ashirin da uku ga watan Adar, a shekara ta shida ta sarautar sarki Dariyus.

16 Sai mutanen Isra’ila, da firistoci, da Lawiyawa, da sauran waɗanda suka komo daga bauta, suka yi bikin keɓe Haikalin Allah da murna.

17 A bikin keɓe Haikalin Allah, suka miƙa bijimai ɗari, da raguna ɗari biyu,da ‘yan raguna ɗari huɗu. Suka kuma miƙa hadayu don zunubi saboda dukan Isra’ila, bunsurai goma sha biyu, bisa ga yawan kabilan Isra’ila.

18 Sai suka karkasa firistoci da Lawiyawa ƙungiya domin yin aikin Ubangiji a Urushalima kamar yadda aka rubuta a Attaura ta Musa.

An Yi Idin Ƙetarewa

19 A rana ta goma sha huɗu ga watan fari, sai waɗanda suka komo daga bauta suka kiyaye Idin Ƙetarewa.

20 Gama firistoci da Lawiyawa sun tsarkake kansu, suka kuwa tsarkaka, sai suka yanka ragon Idin Ƙetarewa saboda dukan waɗanda suka komo daga bauta, da kuma saboda ‘yan’uwansu firistoci, da su kansu.

21 Mutanen Isra’ila waɗanda suka komo daga zaman talala suka ci tare da kowane mutumin da ya haɗa kai da su, ya kuma keɓe kansa daga ƙazantar al’umman ƙasar, domin ya bi Ubangiji Allah na Isra’ila.

22 Suka kuma kiyaye idin abinci marar yisti kwana bakwai da murna, gama Ubangiji ya sa su yi murna, ya kuma juyo da zuciyar Sarkin Assuriya wajensu, saboda haka ya taimake su da aikin Haikalin Allah, Allah na Isra’ila.

Categories
EZRA

EZRA 7

Ezra da Ƙungiyarsa Sun Iso Urushalima

1 Bayan wannan a zamanin Artashate Sarkin Farisa, sai Ezra ya gane da asalinsa, wato shi na ɗan Seraiya, da Azariya, da Hilkiya,

2 da Shallum, da Zadok, da Ahitub,

3 da Amariya, da Azariya, da Merayot,

4 da Zarahiya, da Uzzi, da Bukki,

5 da Abishuwa da Finehas, da Ele’azara, da Haruna babban firist.

6 Ezra ɗin ya taho daga Babila. Shi malami ne, masanin shari’ar Musa, wadda Ubangiji Allah na Isra’ila ya bayar. Sarki kuwa ya ba shi dukan abin da ya roƙa, gama Ubangiji Allahnsa yana tare da shi.

7 A shekara ta bakwai kuma ta sarautar sarki Artashate, waɗansu mutanen Isra’ila, da waɗansu firistoci, da Lawiyawa,da mawaƙa, da matsaran ƙofa, da ma’aikatan Haikali, suka taho Urushalima.

8 Ezra kuma tare da su, suka iso Urushalima a watan biyar na shekara ta bakwai ta sarautar sarkin.

9 Suka taso daga Babila a rana ta fari ga watan fari, suka iso Urushalima a rana ta fari ga watan biyar, Allah kuwa yana tare da su.

10 Gama Ezra ya ba da kansa ga yin nazarin dokokin Allah, ya kiyaye su, ya kuma koyar wa Isra’ilawa dokoki da farillan Allah.

Takardar da Sarki Artashate Ya Ba Ezra

11 Wannan ita ce takardar doka da sarki Artashate ya ba Ezra, wanda yake firist da magatakarda, ƙwararre cikin sha’anin dokoki da umarnan Ubangiji a cikin Isra’ilawa.

12 Ta ce, “Daga Artashate, sarkin sarakuna, zuwa ga Ezra firist, masanin shari’ar Allah na Sama.

13 “Yanzu na yi doka, cewa kowane mutum daga cikin mutanen Isra’ila, da firistocinsu, da Lawiyawansu da suke cikin mulkina wanda yake so ya koma Urushalima, sai ya tafi tare da kai.

14 Gama sarki ne da ‘yan majalisarsa guda bakwai suka aike ka don ka san irin zaman mutanen Yahuza da na Urushalima game da dokokin Allahnka, waɗanda suke a hannunka,

15 domin kuma ka ba da azurfa da zinariya waɗanda sarki da ‘yan majalisarsa suka ba Allah na Isra’ila da yardar ransu, wato Allah wanda Haikalinsa yake a Urushalima,

16 da kuma azurfa da zinariya da za ka samu a dukan lardin Babila tare da hadayu na yardar rai daga mutane da firistoci, hadayun da suka yi wa’adi su bayar da yardar ransu domin Haikalin Allahnsu, da yake a Urushalima.

17 “Da wannan kuɗi ne za ka himmatu, ka sayi bijimai, da raguna, da ‘yan raguna, da hadayunsu na gari, da na sha. Za ka miƙa su a bisa bagaden Haikalin Allah da yake a Urushalima.

18 Duk abin da kai da ‘yan’uwanka kuka ga ya dace ku yi, sai ku yi shi da sauran azurfa da zinariya bisa ga nufin Allahnku.

19 Kwanonin da aka ba ka domin hidima a Haikalin Allah, sai ka ajiye su a gaban Allah a Urushalima.

20 Dukan abin da ake bukata domin Haikalin Allah, abin nan kuwa ya kamata a yi shi, sai ka yi shi da kuɗin baitulmalin sarki.

21 “Ni, sarki Artashate, ina umartar kowane ma’aji na Yammacin Kogin Yufiretis, cewa duk abin da Ezra, firist, masanin dokokin Allah na Sama, zai bukata a gare ka, sai ka himmatu ka yi.

22 Sai ku ba shi abin da ya kai talanti ɗari na azurfa, da mudu ɗari na alkama, da garwa ɗari ta ruwan inabi, mai kuma garwa ɗari. Gishiri kuwa a bayar da yawa, kada a iyakance.

23 Dukan abin da Allah na Sama ya umarta, sai a yi shi sosai domin Haikalin Allah na Sama, domin kada ya yi fushi da mulkin sarki da ‘ya’yansa.

24 Muna kuma sanar da ku, cewa ba daidai ba ne ku karɓi haraji, da kuɗin shiga da fita, daga wurin firistoci, da Lawiyawa, da mawaƙa, da matsaran ƙofa, da masu lura da Haikali, da ma’aikatan wannan Haikali na Allah.

25 “Kai kuma, Ezra, bisa ga hikimar da Allahnka ya ba ka, sai ka naɗa mahukunta da alƙalai waɗanda za su yi wa mutanen da suke a lardin Yammacin Kogi shari’a, wato dukan waɗanda suka san shari’a. Waɗanda ba su san shari’a ba kuwa, sai ka koya musu.

26 Duk wanda bai yi biyayya da shari’ar Allahnka ba, ko shari’ar sarki, sai a yi masa hukunci mai tsanani, ko na mutuwa, ko na kora, ko na ƙwace dukiyarsa, ko na kurkuku.”

Ezra Ya Yi Yabon Allah

27 Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na kakanninmu, wanda ya sa a zuciyar sarki ya ƙawata Haikalin Ubangijin da yake a Urushalima.

28 Wanda kuma ya sa na sami tagomashi a wurin sarki, da ‘yan majalisarsa, da manyan ma’aikatansa. Na sami ƙarfin hali, gama Ubangiji Allahna yana tare da ni. Sai na tattara manyan mutane na Isra’ila don mu tafi tare.