Categories
EZRA

EZRA 8

Waɗanda Suka Komo daga Zaman Talala

1 Waɗannan su ne shugabannin gidajen kakanninsu. Wannan kuwa shi ne lissafin asalin waɗanda suka komo tare da ni daga Babila a zamanin sarautar sarki Artashate.

2-14 Gershom shi ne shugaban iyalin Finehas,

Daniyel shi ne na iyalin Itamar,

Hattush ɗan Shekaniya, shi ne na iyalin Dawuda.

Zakariya shi ne na iyalin Farosh, ya zo da iyalinsa mutum ɗari da hamsin.

Eliyehoyenai ɗan Zarahiya, shi ne na iyalin Fahat-mowab, tare da shi kuma akwai mutum ɗari biyu.

Shekaniya ɗan Yahaziyel, shi ne na iyalin Zattu, tare da shi akwai mutum ɗari uku.

Ebed ɗan Jonatan, shi ne na iyalin Adin, tare da shi akwai mutum hamsin.

Yeshaya ɗan Ataliya, shi ne na iyalin Elam, yana tare da mutum saba’in.

Zabadiya ɗan Maikel, shi ne na iyalin Shefatiya, yana tare da mutum tamanin.

Obadiya ɗan Yehiyel, shi ne na iyalin Yowab, yana tare da mutum ɗari biyu da goma sha takwas.

Shelomit ɗan Yosifiya, shi ne na iyalin Bani, yana tare da mutum ɗari da sittin.

Zakariya ɗan Bebai, shi ne na iyalin Bebai, yana tare da mutum ashirin da takwas.

Yohenan ɗan Hakkatan, shi ne na iyalin Azgad, yana tare da mutum ɗari da goma.

Elifelet, da Yehiyel, da Shemaiya, su ne na iyalin Adonikam (su ne suka zo daga baya), suna tare da mutum sittin.

Utai da Zabbud, su ne na iyalin Bigwai, suna tare da mutum saba’in.

Ezra Ya Sami Lawiyawa domin Haikali

15 Na kuma tara mutanen a bakin rafin da yake gudu zuwa Ahawa. A nan muka yi zango kwana uku. Sa’ad da na duba jama’a, da firistoci, sai na tarar ba ‘ya’yan Lawi.

16 Sai na sa a kirawo Eliyezer, da Ariyel, da Shemaiya, da Elnatan, da Yarib, da Elnatan, da Natan, da Zakariya, da Mehullam waɗanda suke shugabanni, a kuma kirawo Yoyarib da Elnatan masu hikima.

17 Na kuma aike su zuwa wurin Iddo, shugaba a Kasifiya. Na faɗa musu abin da za su faɗa wa Iddo a Kasifiya da ‘yan’uwansa ma’aikatan Haikali, wato ya aiko mana waɗanda za su yi hidima a Haikalin Allahnmu.

18 Da yake Allah yana tare da mu, sai suka kawo mana mutum mai ganewa daga ‘ya’yan Mali ɗan Lawi, ɗan Isra’ila. Sunan mutumin Sherebiya, da ‘ya’yansa da ‘yan’uwansa, su goma sha takwas ne.

19 Suka kuma kawo Hashabiya tare da Yeshaya daga ‘ya’yan Merari. ‘Yan’uwansa da ‘ya’yansu su ashirin ne.

20 Da kuma ma’aikatan Haikali mutum ɗari biyu da ashirin, waɗanda Dawuda da ma’aikatansa suka keɓe domin su taimaki Lawiyawa. Aka ambaci waɗannan da sunayensu.

Ezra Ya Bi da Jama’a da Azumi da Addu’a

21 Na kuma yi shelar azumi a bakin rafin Ahawa don mu ƙasƙantar da kanmu a gaban Allah, mu roƙe shi ya kiyaye mu, da ‘ya’yanmu, da kayanmu a hanya.

22 Gama na ji kunya in roƙi sarki ya ba mu sojojin ƙasa da na doki su kāre mu daga maƙiya a hanya, da yake na riga na faɗa masa cewa, “Allah yana tare da dukan waɗanda suke nemansa, ikonsa da fushinsa mai zafi kuwa yana kan dukan waɗanda suke mantawa da shi.”

23 Don haka muka yi azumi, muka roƙi Allah saboda wannan, shi kuwa ya ji roƙonmu.

Kyautai domin Haikalin

24 Sai na keɓe goma sha biyu daga cikin manyan firistoci, wato Sherebiya, da Hashabiya, da waɗansu goma daga cikin danginsu.

25 Na auna musu azurfa, da zinariya, da kwanoni waɗanda sarki da fādawansa, da manyan mutanensa, da Isra’ilawa duka suka kawo suka miƙa domin Haikalin Allahnmu.

26-27 Ga abin da na auna na ba su,

talanti ɗari shida da hamsin na azurfa

kayan azurfa na talanti ɗari

kayan zinariya na talanti ɗari

kwanonin zinariya guda ashirin na darik dubu (1,000)

kwanoni guda biyu na tatacciyar tagulla, darajarsu daidai da kwanon zinariya.

28 Na ce musu, “Ku tsarkaka ne ga Ubangiji, kayayyakin kuma tsarkaka ne, azurfa da zinariya sadaka ce ta yardar rai ga Ubangiji Allah na kakanninku.

29 Ku riƙe su, ku yi tsaronsu, har lokacin da za ku kai su a gaban manyan firistoci, da Lawiyawa, da shugabannin gidajen kakanninku na Isra’ila a Urushalima, a shirayin Haikalin Ubangiji.”

30 Sai firistoci da Lawiyawa suka ɗauki azurfa, da zinariya, da kwanoni waɗanda aka auna, zuwa Urushalima, zuwa Haikalin Allahnmu.

Komowar Urushalima

31 Muka kuwa tashi daga kogin Ahawa a ran goma sha biyu ga watan ɗaya, don mu tafi Urushalima, Allahnmu kuma yana tare da mu, ya kuwa cece mu daga hannun maƙiyanmu, da mafasa a hanya.

32 Muka iso Urushalima, muka yi kwana uku.

33 A rana ta huɗu, a Haikalin Allah, sai aka ba da azurfa, da zinariya, da kwanoni ga Meremot ɗan Uriya, firist, da Ele’azara ɗan Finehas, da Lawiyawa, wato Yozabad ɗan Yeshuwa, da Nowadiya ɗan Binnuyi.

34 Aka ƙidaya dukan kome aka kuma auna, sa’an nan aka rubuta yawan nauyin.

35 Waɗanda fa suka komo daga zaman talala, suka miƙa wa Allah na Isra’ila hadaya ta ƙonawa, da bijimai goma sha biyu domin dukan Isra’ila,da raguna tasa’in da shida, da ‘yan raguna saba’in da bakwai. Suka kuma miƙa hadaya don zunubi da bunsurai goma sha biyu. Dukan wannan ya zama hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji.

36 Suka faɗa wa wakilan sarki da masu mulkin Yammacin Kogin Yufiretis umarnan sarki. Su kuwa suka taimaki mutane, da kuma Haikalin Allah.

Categories
EZRA

EZRA 9

Addu’ar Ezra da Faɗar Laifi

1 Bayan da aka gama waɗannan abubuwa, sai shugabanni suka zo wurina, suka ce, “Mutanen Isra’ila, da firistoci, da Lawiyawa ba su keɓe kansu daga ƙazantar mutanen ƙasar ba, wato su Kan’aniyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Yebusiyawa, da Ammonawa, da Mowabawa, da Masarawa, da Amoriyawa.

2 Gama sun auro wa kansu da ‘ya’yansu ‘yan matan mutanen nan. Yanzu tsattsarkar zuriya ta cuɗanya da mutanen ƙasashe. Shugabanni da magabata sun fi kowa laifi kan wannan rashin gaskiya.”

3 Sa’ad da na ji wannan, sai na yayyage rigata da alkyabbata, na tsittsiga gashin kaina da na gemuna, na zauna a ruɗe.

4 Sa’an nan dukan waɗanda suka yi rawar jiki saboda maganar Allah na Isra’ila, saboda rashin aminci na waɗanda suka komo daga zaman talala, suka taru, suka kewaye ni sa’ad da nake zaune a ruɗe, har lokacin yin sadakar yamma.

5 A lokacin sadakar yamma ɗin, sai na tashi daga yin azumi, da rigata da alkyabbata yagaggu. Na rusuna a gwiwoyina, na ɗaga hannuwana zuwa ga Ubangiji Allahna.

6 Na ce, “Ya Allahna, kunya ta rufe fuskata, ban iya in ko ɗaga idanuna wajenka ba, gama muguntarmu ta sha kanmu, tsibin zunubanmu kuma ya kai har sammai.

7 Tun daga zamanin kakanninmu muna da babban laifi. Saboda zunubanmu, mu da sarakunanmu, da firistocinmu, aka bashe mu a hannun sarakunan waɗansu ƙasashe, aka bashe mu ga takobi, aka kai mu bauta, aka washe mu, aka kunyatar da mu kamar yadda yake a yau.

8 Amma a yanzu a wannan ɗan lokaci Ubangiji Allahnmu ya yi mana alheri da ya bar mana ringi, ya kuma ba mu wuri a wurinsa mai tsarki, inda za mu zauna lafiya domin Allahnmu ya waye mana ido, ya kuma ba mu ‘yar wartsakewa daga bautarmu.

9 Gama mu bayi ne, duk da haka Allahnmu bai manta da mu a bautarmu ba, amma ya sa muka sami tagomashi a wurin sarakunan Farisa, suka iza mu domin mu gina Haikalin Allahnmu, mu sāke gyaransa, mu kuma gina garu a Yahuza da Urushalima.

10 “Yanzu, me za mu ce bayan wannan, ya Allahnmu, gama mun manta da umarnanka.

11 Umarnan da ka umarta ta bakin bayinka annabawa cewa, ‘Ƙasar da kuke shiga don ku mallake ta, ta ƙazantu da ƙazantar al’umman da take cikinta. Ƙazantarsu ta cika dukan ƙasar.

12 Domin haka kada ku aurar musu da ‘ya’yanku mata, kada kuma ku auro wa ‘ya’yanku ‘yan matansu, kada kuma ku nemi zaman arziki da su. Idan kun yi biyayya za ku yi ƙarfi, ku ci albarkar ƙasar, har ku bar ta gādo ga ‘ya’yanku har abada.’

13 Bayan wannan dukan abubuwan nan suka same mu saboda mugayen ayyukanmu da zunubanmu masu yawa. Ya Allahnmu, ga shi ma, ka hukunta mu kaɗan bisa ga yawan zunubanmu, ka kuma bar mana wannan ringi.

14 Za mu sake ƙetare umarninka, mu yi aurayya da mutanen da suke yin waɗannan ƙazanta? Ba za ka yi fushi da mu, ka ƙone mu da fushinka har babu ringi ba?

15 Ya Ubangiji Allah na Isra’ila, kai mai adalci ne, gama ka bar mana ringin da ya tsira kamar yadda yake a yau. Ga mu nan gabanka da zunubinmu, gama ba wanda zai iya tsayawa a gabanka saboda wannan.”

Categories
EZRA

EZRA 10

An Shirya yadda Za a Rabu da Aurayya da Arna

1 Sa’ad da Ezra yake yin addu’a, yana hurta laifi, yana kuka, yana a durƙushe gaban Haikalin Allah, sai babban taron jama’a, mata, da maza, da yara daga Isra’ila suka taru wurinsa. Mutane suka yi kuka mai zafi.

2 Sai Shekaniya ɗan Yehiyel, daga zuriyar Elam, ya yi wa Ezra magana, ya ce, “Mun yi wa Allahnmu rashin aminci, gama mun auri mata baƙi daga mutanen ƙasar, amma duk da haka akwai sauran bege ga Isra’ila.

3 Bari mu yi alkawari da Allahnmu, mu kori dukan waɗannan mata da ‘ya’yansu, bisa ga shawarar shugabanni da waɗanda suke rawar jiki saboda umarnin Allah. Bari mu yi alkawari bisa ga doka.

4 Sai ka tashi, gama wannan hakkinka ne, mu kuwa muna tare da kai. Sai dai ka yi ƙarfin hali, ka yi shi.”

5 Ezra kuwa ya tashi, ya sa firistoci da suke shugabanni, da Lawiyawa, da dukan mutanen Isra’ila su rantse, cewa za su yi abin da aka ce. Sai suka yi rantsuwar.

6 Sa’an nan Ezra ya tashi daga Haikalin Allah, ya tafi gidan Yohenan ɗan Eliyashib, amma ko da ya tafi can bai ci abinci ba, bai kuma sha ruwa ba, gama yana baƙin ciki saboda rashin aminci na waɗanda suka dawo daga zaman talala.

7 Sai aka yi shela a dukan Yahuza da Urushalima, cewa dukan waɗanda suka komo daga zaman talala, su hallara a Urushalima.

8 Duk wanda bai zo a cikin kwana uku ba, za a washe shi, a kuma ware shi daga jama’ar da suka dawo daga zaman talala. Haka shugabanni da dattawa suka umarta.

9 Sai dukan mutanen Yahuza da na Biliyaminu, suka hallara a Urushalima kafin kwana uku, a ran ashirin ga watan tara. Mutanen suka zauna a dandalin Haikali, suna rawar jiki saboda al’amarin, da kuma saboda babban ruwan sama.

10 Ezra firist kuwa ya miƙe tsaye ya ce wa jama’a, “Kun yi rashin aminci, kun auri mata baƙi, ta haka kuka ƙara zunubin Isra’ila.

11 Yanzu sai ku hurta wa Ubangiji Allah na kakanninku, laifinku, ku kuma aikata nufinsa. Ku ware kanku daga mutanen ƙasar da mata baƙi.”

12 Dukan taron jama’a suka amsa da babbar murya, suka ce, “Haka nan ne, haka nan ne, dole ne mu yi yadda ka faɗa.

13 Amma mutane suna da yawa, a lokacin kuwa ana marka, ba za mu iya tsayawa a fili ba, aikin nan kuma ba na kwana ɗaya, ko biyu ba ne, gama mun yi laifi sosai wajen wannan al’amari.

14 Bari shugabanninmu su wakilci dukan taron jama’a, bari kuma dukan waɗanda suke garuruwanmu da suka auri mata baƙi su zo a ƙayyadadden lokaci tare da dattawa da alƙalan garuruwansu, har lokacin da Allah ya huce daga fushinsa a kanmu saboda al’amarin nan.”

15 Jonatan ɗan Asahel da Yazeya ɗan Tikwa ne kaɗai ba su yarda da wannan ba, Meshullam da Shabbetai suka goyi bayansu.

16 Waɗanda suka komo daga zaman talala kuwa suka yi haka. Sai Ezra firist ya zaɓi mutanen da suke shugabannin gidajen kakanninsu. Aka rubuta sunan kowa. Sai suka taru ran ɗaya ga watan goma, don su bincika al’amarin.

17 Suka gama binciken dukan mutanen da suka auri mata baƙi ran ɗaya ga watan fari.

Mazajen da Suke da Mata Baƙi

18 Ma’aseya, da Eliyezer, da Yarib, da Gedaliya iyalin Yeshuwa ɗan Yehozadak, su ne firistocin da suka auri mata baƙi.

19 Sai suka yi alkawari, cewa za su saki matansu. Suka ba da rago don yin hadaya saboda laifinsu.

20-24 Na iyalin Immer, Hanani, da Zabadiya

Na iyalin Harim, Ma’aseya, da Iliya, da Shemaiya, da Yehiyel, da Uzziya

Na iyalin Fashur, Eliyehoyenai, da Ma’aseya, da Isma’ilu, da Netanel, da Yozabad, da Elasa

Na Lawiyawa, Yozabad, da Shimai, da Kelaya, wato Kelita, da Fetahiya, da Yahuza, da Eliyezer

Na mawaƙa, Eliyashib

Na masu tsaron ƙofa, Shallum, da Telem, da Uri

25-33 Akwai kuma waɗansu na Isra’ila.

Na iyalin Farosh, Ramiya, da Izziya, da Malkiya, da Miyamin, da Ele’azara, da Malkiya, da Benaiya

Na iyalin Elam, Mattaniya, da Zakariya, da Yehiyel, da Abdi, da Yeremot, da Iliya

Na iyalin Zattu, Eliyehoyenai, da Eliyashib, da Mattaniya, da Yeremot, da Zabad, da Aziza

Na iyalin Bebai, Yehohanan,da Hananiya, da Zabbai, da Atlai

Na iyalin Bani, Meshullam, da Malluki, da Adaya, da Yashub, da Sheyal, da Yeremot

Na iyalin Fahat-mowab, Adana, da Kelal, da Benaiya, da Ma’aseya, da Mattaniya, da Bezalel, da Binnuyi, da Manassa

Na iyalin Harim, Eliyezer, da Isshiya, da Malkiya, da Shemaiya, da Shimeyon, da Biliyaminu, da Malluki, da Shemariya

Na iyalin Hashum, Mattenai, da Mattatta, da Zabad, da Elifelet, da Yeremai, da Manassa, da Shimai

34-37 Na iyalin Bani, Mayadi, da Amram, da Yuwel, da Benaiya, da Bedeya, da Keluhi, da Waniya, da Meremot, da Eliyashib, da Mattaniya, da Mattenai, da Yawasu

38-42 Na iyalin Binnuyi, Shimai, da Shelemiya, da Natan, da Adaya, da Maknadebai, da Shashai, Sharai, da Azarel, da Shelemiya, da Shemariya, da Shallum, da Amariya, da Yusufu

43 Na iyalin Nebo, Yehiyel, da Mattitiya, da Zabad, da Zebina, da Yaddai, da Yowel, da Benaiya

44 Waɗannan duk sun auro mata baƙi. Sai suka sake su da ‘ya’yansu.

Categories
NEH

NEH 1

Addu’ar Nehemiya domin Urushalima

1 Labarin Nehemiya ɗan Hakaliya ke nan. Ya zama fa a watan Kisle a shekara ta ashirin, sa’ad da ni Nehemiya nake a fādar Shushan, wato alkarya,

2 sai Hanani, ɗaya daga cikin ‘yan’uwana, ya zo tare da waɗansu mutanen Yahuza. Na kuwa tambaye shi labarin Yahudawan da suka tsira, suka koma daga zaman talala, da labarin Urushalima.

3 Sai suka ce mini, “Waɗanda suka tsira, suka koma daga zaman talala, da suke can lardin, suna cikin wahala ƙwarai, suna kuma shan kunya. Garun Urushalima kuma ya rushe, ƙofofi sun ƙone.”

4 Da na ji wannan labari, sai na zauna, na yi kuka. Na yi kwanaki ina baƙin ciki, na yi ta azumi da addu’a a gaban Allah na Sama.

5 Na ce, “Ya Ubangiji Allah na Sama, Allah mai girma, mai banrazana, mai cika alkawari, mai nuna madawwamiyar ƙauna ga waɗanda suke ƙaunarka, wato masu kiyaye umarnanka,

6 ina roƙonka ka kasa kunne, ka kuma buɗe idanunka, ka ji addu’ar bawanka, wadda nake yi a gabanka dare da rana saboda bayinka, mutanen Isra’ila. Ina hurta zunubanmu, mu mutanen Isra’ila, da muka yi maka. Ni da gidan ubana mun yi zunubi.

7 Mun kangare maka, ba mu kiyaye umarnai, da dokoki, da ka’idodi waɗanda ka ba bawanka Musa ba.

8 Ka tuna da maganar da ka umarci bawanka Musa cewa, ‘Idan kun yi rashin aminci, zan warwatsa ku cikin al’ummai.

9 Amma idan kun juyo wurina, kun kiyaye umarnaina, kun aikata su, ko da yake an warsatsar da ku can nesa, zan tattaro ku, in kawo ku wurin da na zaɓa domin in sa sunana ya kahu a wurin.’

10 “Su bayinka ne, mutanenka ne kuma, waɗanda ka fansa da ikonka.

11 Ya Ubangiji, ka kasa kunne ga addu’ar bawanka, da addu’o’in bayinka, waɗanda suke jin daɗin girmama sunanka. Ka ba bawanka nasara yau ka sa ya sami tagomashi a gaban mutumin nan.”

Categories
NEH

NEH 2

An Aika da Nehemiya Ya Tafi Urushalima

1 Ni kuwa ina riƙe da finjalin sarki. Wata rana a watan Nisan, a shekara ta ashirin ta sarautar sarki Artashate, sa’ad da na kai masa ruwan inabi, sai na ɗauki ruwan inabin, na ba shi. Ni ban taɓa ɓata fuskata a gabansa a dā ba, sai wannan karo.

2 Sai sarki ya tambaye ni, ya ce, “Me ya sa fuskarka ta ɓaci, ga shi, ba ciwo kake yi ba. Ba abin da ya kawo wannan, sai lalle kana baƙin ciki.”

Sai na tsorata ƙwarai,

3 na ce wa sarki, “Ranka ya daɗe, me zai hana fuskata ta ɓaci, da yake birni inda makabartar kakannina take ya zama kango, an kuma ƙone ƙofofinsa da wuta?”

4 Sa’an nan sarki ya ce mini, “To, me kake so?”

Sai na yi addu’a ga Allah na Sama,

5 sa’an nan na ce wa sarki, “Idan ka yarda, idan kuma na sami tagomashi a wurinka, ya sarki, ka yardar mini in tafi Yahuza, birnin kakannina, inda makabartarsu take domin in sāke gina shi.”

6 Sarki kuwa, a sa’an nan sarauniya tana zaune kusa da shi, ya ce mini, “Kwana nawa za ka yi, yaushe kuma za ka dawo?” Sai na faɗa masa, ya kuwa yardar mini in tafi, ni kuwa na yanka masa kwanakin da zan yi.

7 Sa’an nan na ce wa sarki, “Idan sarki ya yarda, sai a ba ni takarda zuwa ga masu mulki da suke a lardin Yammacin Kogin Yufiretis domin su yardar mini in wuce zuwa Yahuza.

8 A kuma ba ni takarda zuwa ga Asaf, sarkin daji, domin ya ba ni katakan da zan yi jigajigan ƙofofin kagarar Haikali, da na garun birnin, da na gidan da zan zauna.” Sarki kuwa ya ba ni abin da na roƙa, gama Allah yana tare da ni.

9 Da na zo wurin masu mulkin Yammacin Kogin Yufiretis, sai na miƙa musu takardar sarki. Sarki ya haɗa ni da sarkin yaƙi da mahayan dawakai.

10 Amma Sanballat Bahorone, da Tobiya, Ba’ammone, bawa, ba su ji daɗi ba ko kaɗan sa’ad da suka ji labari, cewa wani ya zo domin ya inganta zaman lafiyar mutanen Isra’ila.

Nehemiya Ya Ƙarfafa Maginan Garu

11 Da na iso Urushalima na yi kwana uku,

12 sai na fita da dare tare da waɗansu mutane kima,ban faɗa wa kowa abin da Allahna ya sa a zuciyata in yi wa Urushalima ba. Ba waɗansu dabbobi kuma tare da ni, sai dai dabbar da na hau.

13 Da na fita, sai na bi ta Ƙofar Kwari zuwa Rijiyar Dila da Ƙofar Juji, na dudduba garun Urushalima, wanda aka rushe, da ƙofofinsa da wuta ta cinye.

14 Na yi gaba zuwa Ƙofar Maɓuɓɓuga da Tafkin Sarki, amma dabbar da na hau ba ta sami wurin wucewa ba.

15 Haka kuwa na fita da dare ta hanyar kwari na dudduba garun, sa’an nan na koma ta Ƙofar Kwari.

16 Shugabanni ba su san inda na tafi, ko abin da na yi ba, gama ban riga na faɗa wa Yahudawa, da firistoci, da manyan gari, da shugabanni, da sauran waɗanda za su yi aikin ba.

17 Sa’an nan na ce musu, “Kun ga irin wahalar da muke ciki, yadda Urushalima ta zama kango, an kuma ƙone ƙofofinta. Ku zo, mu sāke gina garun Urushalima don mu fita kunya.”

18 Na kuma faɗa musu yadda Allah yana tare da ni, ya kuma taimake ni, da maganar da sarki ya faɗa mini.

Sai suka ce, “Mu tashi, mu kama gini.” Suka himmatu su yi wannan aiki nagari.

19 Amma sa’ad da Sanballat Bahorone, da Tobiya Ba’ammone, bawa, da Geshem Balarabe, suka ji labari, sai suka yi mana ba’a, suka raina mu, suka ce, “Me kuke yi? Kuna yi wa sarki tayarwa ne?”

20 Ni kuwa sai na amsa musu, na ce, “Allah na Sama zai ba mu nasara, saboda haka mu mutanensa za mu tashe, mu kama gini, amma ba ruwanku, ba hakkinku, ba ku da wani abin tunawa a Urushalima.”

Categories
NEH

NEH 3

An Raba wa Mutane Wuraren da Za su Gina

1 Eliyashib, babban firist kuwa, tare da ‘yan’uwansa firistoci, suka tashi suka gina Ƙofar Tumaki. Suka tsarkake ta, suka sa mata ƙyamarenta. Suka tsarkake garun zuwa Hasumiyar Ɗari da Hasumiyar Hananel.

2 Mutanen Yariko suka kama gini kusa da shi.

Sai kuma Zakkur ɗan Imri ya kama gini kusa da na mutanen Yariko.

3 Iyalin Hassenaya suka gina Ƙofar Kifi, suka kafa katakanta, suka sa ƙyamarenta, da sandunan ƙarfe na kulle ƙofofinta.

4 Kusa da su kuma, sai Meremot ɗan Uriya, wato jīkan Hakkoz ya yi gyare-gyare.

Kusa da shi kuma sai Meshullam ɗan Berikiya jikan Meshezabel ya yi gyare-gyare.

Kusa da shi kuma sai Zadok ɗan Ba’ana ya yi gyare-gyare.

5 Kusa da Zadok kuwa mutanen Tekowa suka yi nasu gyare-gyare, amma manyansu ba su sa hannu ga aikin shugabanninsu ba.

6 Yoyada ɗan Faseya, da Meshullam ɗan Besodeya, suka gyara Tsohuwar Ƙofa, suka kafa katakanta, suka sa ƙyamarenta, da sandunan ƙarfe na kulle ƙofofinta.

7 Kusa da su kuma sai Melatiya Bagibeyone, da Yadon Bameronote, da mutanen Gibeyon, da na Mizfa waɗanda suke a ƙarƙashin mulkin Yammacin Kogin Yufiretis suka yi gyare-gyare.

8 Kusa da su kuma sai Uzziyel ɗan Harhaya, maƙerin zinariya, ya yi gyare-gyare.

Kusa da Uzziyel kuma sai Hananiya, ɗaya daga cikin masu yin turare, ya yi gyare-gyare. Suka gyare Urushalima har zuwa Garu Mai Faɗi.

9 Kusa da su kuma sai Refaya ɗan Hur, mai mulkin rabin yankin Urushalima, ya yi gyare-gyare.

10 Kusa da Refaya kuma, sai Yedaiya ɗan Harumaf ya yi gyare-gyare daura da gidansa.

Kusa da Yedaiya sai Hattush ɗan Hashabnaiya ya yi gyare-gyare.

11 Malkiya ɗan Harim, da Hasshub ɗan Fahat-mowab suka gyara wani sashi da kuma Hasumiyar Tanderu.

12 Kusa da su kuma, sai Shallum ɗan Hallohesh mai mulkin rabin yankin Urushalima ya yi gyare-gyare tare da ‘ya’yansa mata.

13 Hanun da mazaunan Zanowa suka gyara Ƙofar Kwari. Sun gina ta, suka sa ƙyamarenta, da sandunan ƙarfe na kulle ƙofofinta, da ƙyamarenta, suka gyara garun kamu dubu, har zuwa Ƙofar Juji.

14 Malkiya ɗan Rekab, mai mulkin yankin Bet-akkerem, ya gyara Ƙofar Juji. Ya gina ta, ya sa ƙyamarenta da sandunan ƙarfe na kulle ƙofofinta.

15 Sai Shallum ɗan Kolhoze, mai mulkin yankin Mizfa ya gyara Ƙofar Maɓuɓɓuga, ya gina ta, ya rufe ta, ya sa ƙyamarenta, da sandunan ƙarfe na kulle ƙofofinta. Ya kuma gina garun Tafkin Siluwam na gonar sarki, har zuwa matakan da suka gangaro daga Birnin Dawuda.

16 Bayansa kuma Nehemiya, ɗan Azbuk, mai mulkin yankin Bet-zur ya yi gyare-gyare, har zuwa wani wuri daura da kabarin Dawuda, har zuwa haƙaƙƙen tafki da gidan masu tsaro.

Lawiyawan da Suka Yi Aikin Garu

17 Waɗannan Lawiyawa sun yi gyare-gyare a ƙarƙashin shugabancin Rehum ɗan Bani.

Kusa da su kuma, sai Hashabiya mai mulkin rabin yankin Kaila, ya yi gyare-gyare domin yankinsa.

18 Bayansa kuma, sai ‘yan’uwansu suka yi gyare-gyare a ƙarƙashin shugabancin Bawwai ɗan Henadad, mai mulkin rabin yankin Kaila.

19 Kusa da su kuma sai Ezer ɗan Yeshuwa, mai mulkin Mizfa, ya gyara wani sashi a gaban gidan makamai a wajen kusurwa.

20 Bayansa kuma, Baruk ɗan Zabbai, ya gyara wani sashi daga wajen kusurwar, har ya zuwa ƙofar gidan Eliyashib babban firist.

21 Bayansa kuma Meremot ɗan Uriya, ɗan Hakkoz, ya gyara wani sashi daga ƙofar gidan Eliyashib, zuwa ƙarshen gidan.

Firistocin da Suka Yi Aikin Garu

22 Bayansa kuma sai firistoci, mutanen filin kwari, suka yi gyare-gyare.

23 Bayansu kuma Biliyaminu da Hasshub suka yi gyara daura da gidansu. Bayansu kuma Azariya, ɗan Ma’aseya, wato jikan Ananiya, ya yi gyara kusa da gidansa.

24 Bayansa kuma Binnuyi, ɗan Henadad, ya gyara wani sashi daga gidan Azariya zuwa kusurwar garun.

25 Falal ɗan Uzai, ya gyara wani sashi daga kusurwar da hasumiyar benen gidan sarki a wajen shirayin matsara.

Bayansa kuma sai Fedaiya ɗan Farosh ya yi gyare-gyare.

26 Ma’aikatan Haikali da suke zaune a Ofel suka yi gyare-gyare zuwa wani wuri daura da Ƙofar Ruwa wajen gabas, har zuwa wata doguwar hasumiya.

Sauran Masu Gini

27 Bayansu kuma mutanen Tekowa suka gyara wani sashi daura da babbar doguwar hasumiya, har zuwa garun Ofel.

28 Daga Ƙofar Dawaki, firistoci suka yi gyare-gyare, kowa ya yi gyara daura da gidansa.

29 Bayansu kuma Zadok, ɗan Immer, ya gyara wani sashi daura da gidansa.

Bayansa kuma Shemaiya, ɗan Shekaniya, mai tsaron Ƙofar Gabas ya yi gyare-gyare.

30 Bayansa kuma Hananiya ɗan Shelemiya, da Hanun, ɗa na shida na Zalaf, suka gyara wani sashi, kashi na biyu.

Bayansu kuma Meshullam, ɗan Berikiya, ya gyara wani sashi daura da gidansa.

31 Bayansa kuma, Malkiya, ɗaya daga cikin maƙeran zinariya ya yi gyare-gyare, har zuwa gidan ma’aikatan Haikali da na ‘yan kasuwa, daura da Ƙofar Taruwa, har zuwa soron bene a wajen kusurwa.

32 Maƙeran zinariya da ‘yan kasuwa suka gyara wani sashi tsakanin soron bene daga kusurwa da Ƙofar Tumaki.

Categories
NEH

NEH 4

Ma’aikata sun Tsare Kansu

1 Sa’ad da Sanballat ya ji muna ginin garun, sai ya husata ƙwarai, ya yi wa Yahudawa ba’a.

2 Ya yi magana a gaban ‘yan’uwansa da sojojin Samariya ya ce, “Mene ne waɗannan Yahudawa kumamai suke yi? Za su mai da abubuwa yadda suka a dā ne? Za su miƙa hadayu ne? Za su gama ginin a rana ɗaya ne? Za su iya samun duwatsun gini daga tsibin matattun duwatsu?”

3 Tobiya Ba’ammone yana kusa da shi, ya ce, “Ai, garun da suke ginawa da duwatsu, ko dila ya hau, sai ya rushe shi!”

4 Sai ni, Nehemiya, na yi addu’a, na ce, “Ka ji, ya Allahnmu, gama ana raina mu, ka sa ba’arsu ta koma kansu, ka sa a washe su a kai su ƙasar bauta.

5 Kada ka shafe laifinsu, kada kuwa ka gafarta musu, gama sun ci mutuncinmu, mu da muke gini.”

6 Muka gina garun, har ya kai rabin tsayinta, domin mutane sun himmatu da aikin.

7 Amma sa’ad da Sanballat, da Tobiya, da Larabawa, da Ammonawa, da mutanen Ashdod, suka ji yadda ginin garun Urushalima yake ci gaba, ana kuma tattoshe tsattsaguwa, sai suka husata.

8 Dukansu suka ƙulla za su zo, su yi yaƙi da Urushalima, su ta da hankali a cikinta.

9 Sai muka yi addu’a ga Allahnmu, muka sa masu tsaro su yi mana tsaro dare da rana saboda su.

10 Mutanen Yahuza kuwa suka ce,

“Ƙarfin ma’aikata yana kāsawa,

Akwai komatsai da yawa da za a kwashe,

Yaya za mu iya gina garun yau?”

11 Abokan gābanmu kuma suka ce, “Ba za su sani ba, ba kuwa za su gan mu ba, sai dai kawai su gan mu a cikinsu, za mu karkashe su, mu tsai da aikin.”

12 Da Yahudawan da suke zaune kusa da su suka zo, suka yi ta nanata mana irin shirin abokan gabanmu, wato za su zo su fāɗa mana.

13 Saboda haka na sa jama’a su ja ɗamara bisa ga iyalinsu a bayan garu, a wuraren da ba a gina ba. Suna riƙe da takuba, da māsu, da bakuna.

14 Da na ga mutane sun damu, sai na tashi na yi magana da shugabanni, da sauran jama’a, na ce, “Kada ku ji tsoro, ku tuna da Ubangiji mai iko, mai banrazana, ku yi yaƙi domin ‘yan’uwanku, da ‘ya’yanku mata da maza, da matanku, da gidajenku.”

15 Da abokan gābanmu suka ji mun san shirinsu, Ubangiji kuwa ya wargaje shirinsu, sai dukanmu muka koma wurin garun, kowa ya kama aikinsa.

16 Daga wannan rana, sai rabin barorina suka yi ta gini, rabi kuwa suna riƙe da māsu, da garkuwoyi, da bakuna, da sulke. Shugabannin kuwa suka goyi bayan dukan Yahudawa sosai.

17 Masu ginin garun da masu ɗaukan kaya suna yi da hannu ɗaya, hannu ɗaya kuma na riƙe da makami.

18 Kowane magini yana rataye da takobinsa sa’ad da yake gini. Mai busa ƙaho yana kusa da ni.

19 Sai na ce wa manya da shugabanni, da sauran jama’a, “Aikin nan babba ne, mai yawa kuma, ga shikuwa, muna rarrabe a kan garun nesa da juna.

20 Duk inda kuka ji an busa ƙaho, sai ku taru a wurin. Allahnmu zai yi yaƙi dominmu.”

21 Haka kuwa muka yi aikin, rabinmu na riƙe da māsu tun daga wayewar gari har zuwa fitowar taurari.

22 A wannan lokaci kuma na ce wa jama’a, kowane mutum tare da baransa ya kwana a Urushalima domin a yi tsaro da dare, da safe kuma a kama aiki.

23 Saboda haka ni, da ‘yan’uwana, da barorina, da matsaran da suke tare da ni, ba wanda ya tuɓe tufafinsa. Kowa yana riƙe da makami.

Categories
NEH

NEH 5

An Hana Ba da Kuɗi da Ruwa

1 Sai mata da maza suka yi ta kuka ƙwarai saboda ‘yan’uwansu Yahudawa.

2 Akwai waɗanda suka ce, “Mu da ‘ya’yanmu mata da maza muna da yawa, sai mu sami hatsi don mu ci mu rayu.”

3 Waɗansu kuma suka ce, “Saboda yunwa mun jinginar da gonakinmu, da gonakin inabinmu, da gidajenmu don mu sami hatsi.”

4 Akwai waɗansu kuma da suka ce, “Mun ci bashin kuɗi don mu biya haraji a kan gonakinmu, da gonakin inabinmu.

5 Ga shi kuwa, mu da su dangin juna ne, ‘ya’yanmu da nasu kuma ɗaya ne, duka da haka muna tilasta wa ‘ya’yanmu mata da maza su zama bayi. Har ma waɗansu daga cikin ‘ya’yanmu mata an riga an bautar da su, amma ba mu da iko mu ce kome, domin gonakinmu da gonakin inabinmu suna a hannun waɗansu mutane.”

6 Ni Nehemiya na husata ƙwarai, sa’ad da na ji kukansu da wannan magana.

7 Sai na yi shawara a zuciyata, na yi wa manya da shugabanni faɗa, na ce musu, “Kuna musguna wa ‘yan’uwanku da yake kuna ba su rance da ruwa.”

Sa’an nan na kira babban taro saboda su.

8 Na ce musu, “Da iyakacin ƙoƙarinmu mun fanshi ‘yan’uwanmu Yahudawa waɗanda aka sayar wa al’ummai, amma ga shi, kuna tilasta wa ‘yan’uwanku su sayar da kansu ga ‘yan’uwansu.” Sai suka yi tsit, suka rasa abin da za su ce.

9 Na kuma ce musu, “Abin da kuke yi ba shi da kyau. Ya kamata ku yi tsoron Allah don ku hana al’ummai, abokan gabanmu, yi mana ba’a.

10 Ni ma da ‘yan’uwana da barorina muna ba da rancen kuɗi da hatsi. Sai mu daina sha’anin ba da rance da ruwa.

11 Yau sai ku mayar musu da gonakinsu, da gonakin inabinsu, da na zaitunsu, da gidajensu, da kashi ɗaya bisa ɗari na kuɗi, da na hatsi, da na ruwan inabi, da na mai, waɗanda kuka karɓa a wurinsu.”

12 Sa’an nan suka ce, “Za mu mayar musu da waɗannan abubuwa, ba kuwa za mu bukaci wani abu a gare su ba. Za mu yi abin da ka faɗa.”

Sai na kira firistoci su rantsar da su, cewa za su yi yadda suka alkawarta.

13 Sai kuma na kakkaɓe hannuna, na ce, “Duk wanda ya karya wannan alkawari, haka Allah zai kakkaɓe shi daga gidansa da aikinsa. Allah zai kakkaɓe shi, ya wofintar da shi.”

Sai dukan taron suka amsa, “Amin, amin.” Suka kuma yabi Ubangiji. Suka kuwa cika alkawarin da suka yi.

Rashin Sonkan Nehemiya

14 Tun kuma lokacin da na yi mulkin ƙasar Yahuza, a shekara ta ashirin zuwa shekara ta talatin da biyu ta sarautar sarki Artashate, shekara goma sha biyu ke nan, ni ko ‘yan’uwana, ba wanda ya karɓi albashin da akan ba mai mulki.

15 Waɗanda suka riga ni mulki sun nawaita wa mutane. Sun yi ta karɓar abinci da ruwan inabi daga gare su, banda shekel arba’in kowace rana domin abinci da ruwan inabi. Har ma barorin masu mulki sun nawaya wa mutane. Amma ni ban yi haka ba, saboda ina tsoron Allah.

16 Na mai da hankali ga aikin garu, ban samar wa kaina gonaki ba. Barorina duka suka haɗa kai da ni a kan aikin gini.

17 Duk da haka akwai Yahudawa da shugabanni ɗari da hamsin waɗanda suke cin abinci a teburina, banda waɗanda sukan zo wurinmu daga al’umman da suke kewaye da mu.

18 Ga abincin da ake shiryawa kowace rana, sa ɗaya, da tumaki shida kyawawa, da kuma kaji. A kowace rana ta goma akan kawo salkunan ruwan inabi masu yawa, amma duk da haka ban karɓi albashin da akan ba mai mulki ba, domin wahala ta yi wa mutane yawa.

19 Ya Allahna, ka tuna da alherin da na yi wa mutanen nan.

Categories
NEH

NEH 6

Sharrin ‘Yan Hammayya

1 Sa’ad da fa aka sanar da Sanballat, da Tobiya, da Geshem Balarabe, da sauran abokan gābanmu, cewa na gina garun, har ba sauran tsaguwa da ta ragu, ko da yake a lokacin ban riga na sa wa ƙofofi ƙyamare ba,

2 sai Sanballat da Geshem suka aika wurina cewa, “Ka zo mu sadu a wani ƙauye a filin Ono,” amma da nufin su cuce ni.

3 Sai na aika musu da manzanni, na ce, “Ina fama da babban aiki, ba ni da damar zuwa wurinku. Don me zan bar aiki in gangaro zuwa wurinku?”

4 Suka yi ta aiko mini da wannan saƙo har sau huɗu, ni kuwa na yi ta ba su amsa irin ta dā.

5 A karo na biyar sai Sanballat ya aiko da buɗaɗɗiyar wasiƙa ta hannun baransa, da irin maganar dā.

6 Ga abin da yake cikin wasiƙar, “Geshem ya faɗa mini, ana ta ji jita jita wurin maƙwabta, cewa kai da Yahuduwa kuna niyyar tayarwar, don haka kake ginin garun, kana so kuma ka naɗa kanka sarki.

7 Ga shi, ka sa annabawa su yi shelarka a Urushalima cewa, ‘Akwai sarki a Yahuza.’ To, za a faɗa wa sarki wannan magana, sai ka zo mu yi shawara tare a kan wannan al’amari.”

8 Sai na mayar masa da amsa cewa, “Faufau, ba a yi wani abu haka kamar yadda ka faɗa ba, kai ne ka ƙaga wannan a zuciyarka.”

9 Gama dukansu so suke su tsoratar da mu, suna cewa, “Za su daina aikin.” Amma na yi addu’a, na ce, “Ya Allah, ka ƙarfafa ni.”

10 Sa’ad da na ziyarci Shemaiya ɗan Delaiya, wato jikan wanda aka hana shi fita, sai ya ce mini, “Bari mu tafi cikin Haikalin Allah, mu rufe ƙofofin Haikalin, gama suna zuwa su kashe ka, za su iya zuwa a wani dare su kashe ka.”

11 Sai na ce, “Mutum kamata ne, zai gudu? Mutum irina zai shiga Haikali don ya tsere? To, ba zan tafi ba.”

12 Na gane Allah bai aike shi wurina ba. Ya yi mini wannan magana domin Tobiya da Sanballat sun haɗa baki da shi.

13 Gama da wannan nufi ne suka haɗa baki, don in ji tsoro, in yi yadda suke so, in yi zunubi, da haka za su ba ni mugun suna, su yi mini ba’a.

14 “Ya Allahna, ka tuna da Tobiya da Sanballat bisa ga abubuwan nan da suka yi, da annabiya Nowadiya, da sauran annabawa waɗanda suka so su tsoratar da ni.”

Gamawar Aikin

15 A cikin kwana hamsin da biyu aka gama garun, ran ashirin da biyar ga watan Elul.

16 Sa’ad da abokan gābanmu da dukan al’umman da suke kewaye da mu suka ji, sai suka ji tsoro, gabansu kuma ya faɗi, gama sun gane, da taimakon Allahnmu muka yi wannan aiki.

17 A kwanakin nan kuma shugabannin Yahuza suka yi ta aika wa Tobiya da wasiƙu, shi kuma Tobiya yana ta aika musu da nasa wasiƙu.

18 Mutane da yawa a Yahuza sun rantse za su goyi bayan Tobiya, domin ya auri ‘yar Shekaniya, ɗan Ara. Ɗansa kuma, wato Yohenan, ya auri ‘yar Meshullam, ɗan Berikiya.

19 Mutane suka yi magana a kan ayyukan kirki na Tobiya a gabana. Suka kuma kai maganata a wurinsa, sai Tobiya ya yi ta aika mini da wasiƙu don ya tsoratar da ni.

Categories
NEH

NEH 7

Nehemiya Ya Zaɓi Masarautan Urushalima

1 Sa’ad da aka gina garun, aka sa ƙofofinsa, aka kuma sa matsaran ƙofofi, da mawaƙa, da Lawiyawa,

2 sai na ba ɗan’uwana, Hanani, da Hananiya, shugaban kagara, aikin riƙon Urushalima. Shi Hananiya mai aminci ne, mai tsoron Allah, fiye da sauran mutane.

3 Sa’an nan na ce musu, kada su buɗe ƙofofin Urushalima da sassafe, sai rana ta cira sosai, su kuma kulle ƙofofin da ƙarfe kafin matsara su tashi wajen faɗuwar rana. Su samo matsara daga mazaunan Urushalima, su sa su tsaye a muhimman wurare, waɗansunsu kuma suna zaga gidaje.

Lissafin Mutane

4 Birnin yana da faɗi da girma, amma mutanen da suke ciki kaɗan ne, ba a kuma gina gidaje ba tukuna.

5 Allahna kuwa ya sa a zuciyata in tara manya da shugabanni, da sauran jama’a don a rubuta su bisa ga asalinsu. Na sami littafin asali na waɗanda suka fara komowa. Ga abin da na tarar aka rubuta ciki.

6 Waɗannan su ne mutanen lardin Yahuza, waɗanda suka komo daga zaman talala da Nebukadnezzar Sarkin Babila ya kai mutane. Sun komo Urushalima da Yahuza. Kowa ya tafi garinsu.

7 Sun komo tare da Zarubabel, da Yeshuwa, da Nehemiya, da Seraiya, da Re’elaya, da Nahamani, da Mordekai, da Bilshan, da Misfar, da Bigwai, da Rehum, da Ba’ana.

8-25 Ga jerin iyalan Isra’ila da adadin waɗanda suka komo daga zaman dole

iyalin Farosh, dubu biyu da ɗari da saba’in da biyu (2,172)

iyalin Shefatiya, ɗari uku da saba’in da biyu

iyalin Ara, ɗari shida da hamsin da biyu

iyalin Fahat-mowab, wato zuriyar Yeshuwa da Yowab, dubu biyu da ɗari takwas da goma sha takwas (2,818)

iyalin Elam, dubu da ɗari biyu da hamsin da huɗu (1,254)

iyalin Zattu, ɗari takwas da arba’in da biyar

iyalin Zakkai, ɗari bakwai da sittin

iyalin Bani, ɗari shida da arba’in da takwas

iyalin Bebai, ɗari shida da ashirin da takwas

iyalin Azgad, dubu biyu da ɗari uku da ashirin da biyu (2,322)

iyalin Adonikam, ɗari shida da sittin da bakwai

iyalin Bigwai, dubu biyu da sittin da bakwai (2,067)

iyalin Adin, ɗari shida da hamsin da biyar

iyalin Ater (na Hezekiya), tasa’in da takwas

iyalin Hashum, ɗari uku da ashirin da takwas

iyalin Bezai, ɗari uku da ashirin da huɗu

iyalin Yora, ɗari da goma sha biyu

iyalin Gibeyon, tasa’in da biyar

26-38 Mutanen da kakanninsu suka zauna a waɗannan garuruwa, su ma sun komo daga zaman talala.

Baitalami da Netofa, ɗari da tamanin da takwas

Anatot, ɗari da ashirin da takwas

Azmawet, arba’in da biyu

Kiriyat-yeyarim da Kefira, da Biyerot, ɗari bakwai da arba’in da uku

Rama da Geba, ɗari shida da ashirin da ɗaya

Mikmash, ɗari da ashirin da biyu

Betel da Ai, ɗari da ashirin da uku

Da wani Nebo, hamsin da biyu

Da wani Elam, dubu da ɗari biyu da hamsin da huɗu (1,254)

Harim, ɗari uku da ashirin

Yariko, ɗari uku da arba’in da biyar

Lod, da Hadid, da Ono, ɗari bakwai da ashirin da ɗaya

Senaya, dubu uku da ɗari tara da talatin (3,930)

39-42 Ga lissafin iyalin firistoci da suka komo daga zaman talala.

Yedaiya, na zuriyar Yeshuwa, ɗari tara da saba’in da uku

Immer, dubu ɗaya da hamsin da biyu (1,052)

Fashur, dubu da ɗari biyu da arba’in da bakwai (1,247)

Harim, dubu ɗaya da goma sha bakwai (1,017)

43 Lawiyawan da suka komo daga zaman talala, Yeshuwa da Kadmiyel na zuriyar Hodawiya, saba’in da huɗu.

44 Mawaƙa, na zuriyar Asaf, ɗari da arba’in da takwas.

45 Masu tsaron Haikali su ne zuriyar Shallum, da Ater, da Talmon, da Akkub, da Hatita, da Shobai, ɗari da talatin da takwas.

46-56 Ma’aikatan Haikali da suka komo daga zaman talala, su ne

Zuriyar Ziha, da Hasufa, da Tabbawot,

Keros, da Siyaha, da Fadon,

Lebana, da Hagaba, da Shamlai,

Hanan, da Giddel, da Gahar,

Rewaiya, da Rezin, da Nekoda,

Gazam, da Uzza, da Faseya,

Besai, da Me’uniyawa, da Nefushiyawa,

Bakbuk, da Hakufa, da Harkur,

Bazlut, da Mehida, da Harsha,

Barkos, da Sisera, da Tema,

Neziya, da Hatifa.

57-59 Iyalan barorin Sulemanu da suka komo daga zaman talala, su ne

na Sotai, da Hassoferet, da Feruda,

Yawala, da Darkon, da Giddel,

Shefatiya, da Hattil, da Fokeret-hazzebayim, da Ami.

60 Jimillar zuriyar ma’aikatan Haikali da na Sulemanu, su ɗari uku da tasa’in da biyu ne.

61-62 Waɗannan su ne daga zuriyar Delaiya, da Tobiya, da Nekoda, waɗanda suka zo daga garuruwan Telmela, da Tel-harsha, da Kerub, da Addan, da Immer, amma ba su iya nuna gidajen kakanninsu, ko zuriyarsu a cikin Isra’ilawa ba, su ɗari shida ne da arba’in da biyu.

63 Na wajen firistoci kuma su ne zuriyar Habaya, da na Hakkoz, da na Barzillai, wanda ya auri ‘yar Barzillai mutumin Gileyad, aka kira shi da sunan zuriyar surukinsa.

64 Waɗannan suka nema a rubuta su tare da waɗanda aka rubuta jerin sunayen asalinsu, amma ba a same su a ciki ba, saboda haka aka hana su shiga cikin firistoci, sun zama kamar marasa tsarki.

65 Sai mai mulki ya faɗa musu kada su ci abinci mafi tsarki, sai an sami firist wanda zai yi tambaya ta wurin Urim da Tummin tukuna.

66-69 Jimillar waɗanda suka komo duka su dubu arba’in da dubu biyu da ɗari uku da sittin ne (42,360)

barorinsu mata da maza, waɗanda yawansu ya kai dubu bakwai da ɗari uku da talatin da bakwai (7,337)

mawaƙa ɗari biyu da arba’in da biyar mata da maza

dawakansu kuma ɗari bakwai da talatin da shida ne

alfadaransu kuma ɗari biyu da arba’in da biyar ne

raƙumansu ɗari huɗu da talatin da biyar ne

jakunansu dubu shida da ɗari bakwai da ashirin (6,720)

70-72 Da yawa daga cikin jama’a suka ba da taimako domin biyan aikin gyaran Haikali.

Mai mulki ya ba da

zinariya darik dubu (1,000)

kwanonin wanke hannu guda hamsin

rigunan firistoci ɗari biyar da talatin

Shugabannin iyali suka ba da

zinariya darik dubu ashirin (20,000)

azurfa maina dubu biyu da ɗari biyu (2,200)

Sauran jama’a suka ba da

zinariya darik dubu ashirin (20,000)

azurfa maina dubu biyu (2,000)

rigunan firistoci guda sittin da bakwai

73 Sa’an nan firistoci, da Lawiyawa, da masu tsaron Haikali, da mawaƙa da waɗansu da dama daga cikin jama’a, da ma’aikatan Haikali, da dukan Isra’ilawa suka zauna a garuruwansu.