Categories
ESTA

ESTA 5

Esta Ta Yi wa Sarki da Haman Liyafa

1 A kan rana ta uku sai Esta ta sa rigunan sarautarta, ta tafi, ta tsaya a shirayi na ciki na fādar sarki, kusa da ɗakin sarki. Sarki kuwa yana zaune a gadon sarautarsa, a gidan sarautarsa, daura da ƙofar shiga fāda.

2 Sa’ad da ya ga Esta tana tsaye a shirayin, sai ya miƙa mata sandan zinariya na sarauta, gama ta sami kwarjini a wurinsa. Sai Esta ta matsa kusa ta taɓa kan sandan.

3 Sarki ya ce mata, “Mene ne, sarauniya Esta? Me kike so? Za a ba ki, ko rabin mulkina ma.”

4 Sai Esta ta ce, “Idan sarki ya yarda, bari sarki ya zo tare da Haman yau wurin liyafa da na shirya wa sarki.”

5 Sarki kuwa ya ce, “A zo da Haman maza, mu yi abin da Esta take so.” Sai sarki da Haman suka tafi liyafar da Esta ta shirya.

6 Sa’ad da suke shan ruwan inabi, sai sarki ya tambayi Esta, “Mece ce bukatarki? Za a biya miki ko da rabin mulkina ne.”

7 Sai Esta ta ce, “Bukatata, da roƙona ke nan,

8 idan na sami tagomashi a wurin sarki, idan kuma sarki ya yarda ya biya bukatata da roƙona, to, bari sarki da Haman su zo liyafar da zan yi musu, gobe kuwa zan yi abin da sarki ya faɗa.”

Haman Ya Yi Shirin Kashe Mordekai

9 Ran nan Haman ya fita da murna da farin ciki, amma da ya ga Mordekai a ƙofar sarki, Mordekai kuwa bai tashi ba, bai kuma yi rawar jiki a gabansa ba, sai ya husata ƙwarai.

10 Duk da haka Haman ya cije, ya tafi gida. Ya aika a kirawo abokansa da matarsa, Zeresh.

11 Ya faɗa musu darajar wadatarsa, da yawan ‘ya’yansa, da yawan matsayin da sarki ya girmama shi da su, da yadda sarki ya ciyar da shi gaba fiye da sarakuna da barorin sarki.

12 Ya ƙara da cewa, “Har ma sarauniya Esta ma ba ta yarda kowa ya tafi tare da sarki wurin liyafar da ta shirya ba, sai ni. Gobe ma ta gayyace ni tare da sarki.

13 Duk da haka wannan bai yi mini daɗi ba, muddin Mordekai, Bayahuden nan, yana zaune a ƙofar sarki.”

14 Matarsa, Zeresh kuwa, da abokansa duka suka ce, “Ka sa a shirya gungumen itace mai tsayi kamu hamsin, sa’an nan da safe ka faɗa wa sarki a rataye Mordekai a kai, sa’an nan ka tafi wurin liyafar tare da sarki da murna.”

Haman kuwa ya ji daɗin wannan shawara, sai ya sa aka shirya gungumen itacen.

Categories
ESTA

ESTA 6

Haman Ya Girmama Mordekai Tilas

1 A wannan dare kuwa sarki ya kasa yin barci, sai ya umarta a kawo littafin da aka rubuta al’amuran da suke faruwa don tunawa. Aka kuwa kawo, aka karanta wa sarki.

2 Sai aka tarar an rubuta yadda Mordekai ya gano maƙarƙashiyar Bigtana da Teresh, biyu daga cikin bābāni na sarki, masu tsaron ƙofa, waɗanda suka yi niyya su kashe sarki Ahasurus.

3 Sai sarki ya ce, “To, wace irin daraja ko girma aka ba Mordekai saboda wannan?”

Barorin sarki waɗanda suke yi masa hidima suka ce, “Ba a yi masa kome ba.”

4 Sarki kuwa ya ce, “Wane ne yake a shirayi?”

Daidai lokacin ne kuwa Haman ya shigo shirayi na fari na fādar sarki, don ya yi magana da sarki a kan a rataye Mordekai a gungumen itace da ya shirya.

5 Barorin sarki suka ce, “Ai, Haman ne yake tsaye a shirayi.”

Sai sarki ya ce ya shigo.

6 Da shigowar Haman, sai sarki ya ce masa, “Me za a yi wa mutumin da sarki yake so ya ɗaukaka?”

Haman ya yi tunani ya ce a ransa, “Wane ne sarki yake so ya ɗaukaka, in banda ni?”

7 Sai Haman ya ce wa sarki, “Abin da za a yi wa wanda sarki yake so ya ɗaukaka ke nan.

8 Bari a kawo rigunan sarautar da sarki ya taɓa sawa, da dokin da sarki ya taɓa hawa, a kuma sa kambin sarauta a kansa.

9 Sa’an nan a ba ɗaya daga cikin manyan sarakunanka rigunan ya sa wa wanda kake so ka ɗaukaka, ya kuma hawa da shi kan dokin, sa’an nan ya zagaya da shi a dandalin birni, yana shelar a gabansa yana cewa, ‘Haka za a yi wa wanda sarki yake so ya ɗaukaka.’ ”

10 Sai sarki ya ce wa Haman, “Yi maza, ka ɗauki rigunan da dokin, ka tafi wurin Mordekai, Bayahuden nan, wanda yakan zauna a ƙofar sarki ka yi masa kamar yadda ka faɗa. Kada ka kasa yin kome daga cikin abin da ka faɗa.”

11 Haman kuwa ya ɗauki rigunan da dokin. Ya sa wa Mordekai riguna, ya hawar da shi kan dokin, ya zagaya da shi a dandalin birnin, yana cewa, “Haka za a yi wa wanda sarki yake so ya ɗaukaka.”

12 Sa’an nan Mordekai ya koma ƙofar sarki, Haman kuwa ya gaggauta zuwa gidansa, yana baƙin ciki, kunya ta rufe shi.

13 Da ya koma gida, sai ya faɗa wa Zeresh, matarsa, da dukan abokansa, duk abin da ya same shi. Sai mutanensa masu hikima da Zeresh, matarsa, suka ce masa, “Idan Mordekai, wanda ka fara faɗuwa a gabansa, in dai daga zuriyar Yahudawa yake, to, ba za ka yi nasara a kansa ba, amma hakika za ka fāɗi a gabansa.”

14 Suna magana ke nan, sai bābānin sarki suka iso, suka tafi da Haman a gaggauce zuwa wurin liyafar da Esta ta shirya.

Categories
ESTA

ESTA 7

Haman Ya Fāɗa a Ramin da Ya Haƙa

1 Sarki da Haman kuwa suka tafi wurin Esta, gun liyafa.

2 A rana ta biyu, sa’ad da suke shan ruwan inabi, sai sarki ya sāke ce wa Esta, “Mece ce bukatarki, sarauniya Esta? Za a yi miki. Mene ne roƙonki? Za a ba ki, ko da rabin mulkina ne.”

3 Sai Esta ta ce, “Ya sarki, idan na sami tagomashi a wurinka, idan kuma sarki ya yarda, bukatata ita ce a bar ni da raina, roƙona kuma shi ne a bar mutanena.

4 Gama an sayar da mu, ni da mutanena, don a hallaka mu, a karkashe, a ƙarasa mu. Da a ce an sayar da mu mu zama bayi, mata da maza, da na yi shiru, gama ba za a kwatanta wahalarmu da hasarar da sarki zai sha ba.”

5 Sarki Ahasurus ya ce wa sarauniya Esta, “Wane ne shi, ina yake, wanda zai yi karambanin yin wannan?”

6 Esta ta ce, “Haman ne, magabci, maƙiyi, mugu!”

Sai tsoro ya kama Haman a gaban sarki da sarauniya.

7 Sarki kuwa ya tashi da fushi, ya tafi lambun fāda. Amma Haman ya tsaya don ya roƙi sarauniya Esta ta ceci ransa, gama ya ga sarki yana niyyar hukunta shi.

8 Da sarki ya koma daga lambun fāda zuwa inda suke shan ruwan inabi, sai ga Haman ya fāɗi a kan shimfiɗar da Esta take zaune. Sai sarki ya ce, “Har ma zai ci mutuncin sarauniya a gabana, a gidana?”

Da dai sarki ya faɗi haka, sai bābāni suka cafe Haman.

9 Sa’an nan Harbona, ɗaya daga cikin bābānin da yake yi wa sarki hidima ya ce, “Ga shi ma, Haman ya riga ya shirya gungumen itace a gidansa, mai tsayi kamu hamsin, inda zai rataye Mordekai wanda ya ceci sarki ta wurin maganarsa.”

Sai sarki ya ce, “A rataye Haman a gungumen.”

10 Aka kuwa rataye Haman a gungumen itace da ya shirya zai rataye Mordekai. Sa’an nan sarki ya huce.

Categories
ESTA

ESTA 8

An Ba Yahudawa Izini Kada Su Miƙa Wuya

1 A wannan rana sai sarki Ahasurus ya ba Esta gidan Haman, maƙiyin Yahudawa, da duk dukiyar Haman. Mordekai kuwa ya zo gaban sarki, gama Esta ta bayyana yadda yake a gare ta.

2 Sa’an nan sarki ya ɗauki zobensa na hatimi, wanda ya karɓe a wurin Haman, ya ba Mordekai. Esta kuma ta ba Mordekai gidan Haman.

3 Sa’an nan kuma Esta ta faɗi a wajen ƙafafun sarki, ta roƙe shi da hawaye ya kawar da mugun shirin da Haman Ba’agage ya shirya wa Yahudawa.

4 Sai sarki ya miƙo wa Esta sandan sarauta na zinariya.

5 Esta kuwa ta miƙe tsaye a gaban sarki, ta ce, “Idan sarki ya yarda, idan kuma na sami tagomashi a wurinka, idan ya yi wa sarki kyau, idan kuma sarki yana jin daɗina, bari a yi rubutu a soke wasiƙun da Haman Ba’agage ɗan Hammedata ya rubuta don a hallaka Yahudawan da suke cikin dukan lardunan sarki.

6 Gama ƙaƙa zan iya daurewa da ganin masifa da hallaka na mutanena da dangina?”

7 Sai sarki Ahasurus ya ce wa sarauniya da Mordekai, Bayahude, “Ga shi, na riga na ba Esta gidan Haman, an kuma riga an rataye shi a bisa gungume domin ya so ya taɓa Yahudawa.

8 Sai ku rubuta doka yadda kuke so da sunan sarki zuwa ga Yahudawa. Ku hatimce ta da hatimin zoben sarki, gama dokar da aka rubuta da sunan sarki, aka kuma hatimce ta da hatimin zoben sarki, ba za a iya a soke ta ba.”

9 A wannan lokaci aka kirawo magatakardun sarki ran ashirin da uku ga watan uku, wato watan Siwan. Bisa ga umarnin Mordekai aka rubuta doka zuwa ga Yahudawa, da shugabannin mahukunta, da masu mulki, da shugabannin larduna, tun daga Hindu har zuwa Habasha, wato lardi ɗari da ashirin da bakwai. Aka rubuta wa kowane lardi da irin rubutunsa, kowaɗanne mutane kuma da irin harshensu, zuwa ga Yahudawa kuma da irin rubutunsu da harshensu.

10 An yi rubutu da sunan sarki Ahasurus, aka kuma hatimce shi da hatimin zoben sarki. Aka aika da wasiƙun ta hannun ‘yan-kada-ta-kwana, waɗanda suka hau dawakai masu zafin gudu da akan mora a aikin sarki.

11 A wasiƙun, sarki ya yardar wa Yahudawan da suke a kowane birni su taru, su kāre rayukansu, su kuma hallaka kowace rundunar mutane da kowane lardi da zai tasar musu, da ‘ya’yansu, da matansu, su karkashe su, su rurrushe su, su kuma washe dukiyarsu.

12 Za a yi wannan a dukan lardunan sarki Ahasurus ran goma sha uku ga watan goma sha biyu, wato watan Adar.

13 Sai a ba kowane lardi fassarar dokar, don a yi shelarta ga dukan mutane, Yahudawa kuwa su yi shiri saboda wannan rana, domin su ɗau fansa a kan maƙiyansu.

14 Sai ‘yan-kada-ta-kwana suka hau dawakai masu zafin gudu waɗanda akan mora a aikin sarki, suka tafi da gaggawa don su iyar da dokar sarki. Aka yi shelar dokar a Shushan, masarauta.

15 Mordekai kuwa ya fita a gaban sarki da rigunan sarauta, masu launin shuɗi, da fari, da babban kambi na zinariya, da alkyabba ta lilin mai launin shunayya. Aka yi sowa don murna a birnin Shushan.

16 Yahudawa suka sami haske, da farin ciki, da murna, da daraja.

17 A kowane lardi da birni inda maganar sarki da dokarsa suka kai, Yahudawa suka yi farin ciki da murna, suka yi biki, suka yi hutu. Mutane da yawa daga cikin mutanen ƙasar suka zama Yahudawa, gama tsoron Yahudawa ya kama su.

Categories
ESTA

ESTA 9

Yahudawa Sun Hallaka Maƙiyansu

1 A kan rana ta goma sha uku ga watan sha biyu, wato watan Adar, a ranar da za a aikata maganar sarki da dokarsa, wato a ranar da maƙiyan Yahudawa za su fāɗa musu, sai ranar ta zama ranar da Yahudawa ne za su tasar wa maƙiyansu.

2 Sai Yahudawa suka taru a biranensu a dukan lardunan sarki Ahasurus, don su tasar wa waɗanda suke so su yi musu ɓarna. Ba wanda ya tasar musu gama tsoronsu ya kama mutane.

3 Dukan sarakunan larduna, da hakimai, da masu mulki, da ma’aikatan sarki, suka taimaki Yahudawa, gama tsoron Mordekai ya kama su.

4 Gama Mordekai ya zama babban mutum a gidan sarki, ya kuma yi suna a dukan larduna, gama ya yi ta ƙasaita gaba gaba.

5 Yahudawa kuwa suka kashe dukan maƙiyansu da takobi. Suka hallaka maƙiyansu yadda suke so.

6 A Shushan, masarauta kanta, Yahudawa suka hallaka mutum ɗari biyar.

7 Suka kuma kashe Farshandata, da Dalfon, da Asfata,

8 da Forata, da Adaliya, da Aridata,

9 da Farmashta, da Arisai, da Aridai, da Waizata.

10 Su ne ‘ya’ya goma na Haman, ɗan Hammedata, maƙiyin Yahudawa, amma ba su washe dukiyarsu ba.

11 A ranar ce aka faɗa wa sarki yawan mutanen da aka kashe a Shushan, masarauta.

12 Sai sarki ya ce wa sarauniya Esta, “A Shushan, masarauta, Yahudawa sun kashe mutum ɗari biyar da kuma ‘ya’yan Haman guda goma. Mene ne suka yi a sauran lardunan sarki? Mece ce kuma bukatarki? Za a yi miki. Mene ne kuma roƙonki? Za a ba ki.”

13 Esta ta ce, “Idan sarki ya yarda, bari a yardar wa Yahudawan da suke Shushan su yi haka gobe, kamar yadda suka yi yau. Bari a rataye gawawwakin ‘ya’yan Haman guda goma a bisa gumagumai.”

14 Sarki kuwa ya ce a yi haka ɗin. Sai aka yi doka a Shushan, aka kuwa rataye gawawwakin ‘ya’yan Haman guda goma.

15 Yahudawan da suke Shushan kuwa suka taru a rana ta goma sha huɗu ga watan Adar, suka kashe mutum ɗari uku a Shushan, amma ba su washe dukiyarsu ba.

Bikin Furim

16 Yahudawan da suke cikin lardunan sarki kuma suka taru, suka kare rayukansu, suka ƙwaci kansu daga maƙiyansu. Suka kashe mutum dubu saba’in da dubu biyar (75,000) daga cikin maƙiyansu, amma ba su washe dukiyarsu ba.

17 A rana ta goma sha uku ga watan Adar ne suka aikata wannan abu. A rana ta goma sha huɗu suka huta, suka mai da ranar ta zama ta biki, da farin ciki.

18 Amma Yahudawan da suke a Shushan suka taru a rana ta goma sha uku, da rana ta goma sha huɗu, suka huta ran goma sha biyar, suna biki da murna.

19 Yahudawan da suke zaune a ƙauyuka, da karkara, suka mai da rana ta goma sha huɗu ga watan Adar, ranar farin ciki, da biki, da hutu, da ranar aika wa juna da abinci.

20 Mordekai kuwa ya rubuta abubuwan nan da suka faru, ya aika da takardun zuwa ga dukan Yahudawa waɗanda suke a dukan lardunan sarki Ahasurus, na kusa da na nesa.

21 Ya yi musu umarni, cewa su kiyaye rana ta goma sha huɗu da ta goma sha biyar na watan Adar a kowace shekara.

22 Su ne ranakun da Yahudawa suka sami kuɓuta daga abokan gābansu. A wannan wata ne kuma baƙin cikinsu ya zama farin ciki, makokinsu kuma ya zama hutawa. Sai su maishe su ranakun biki da farin ciki, da aika wa juna da abinci, da kuma ba da kyautai ga matalauta.

23 Sai Yahudawa suka ɗauka su yi kamar yadda suka fara, da kuma yadda Mordekai ya rubuta musu.

24 Haman Ba’agage, ɗan Hammedata, maƙiyin dukan Yahudawa, ya ƙulla wa Yahudawa makirci don ya hallaka su. Ya jefa Fur, wato kuri’a don ya hallaka su.

25 Amma da Esta ta zo wurin sarki, sai sarki ya ba da umarni a rubuce,cewa mugun makircin nan da Haman ya shirya wa Yahudawa ya koma a kansa. Shi da ‘ya’yansa maza aka rataye su a bisa gumagumai.

26 Saboda haka suka sa wa ranakun nan suna Furim, wanda asalinsu daga Fur ne, wato kuri’a. Domin haka dukan abin da aka rubuta a wannan takarda, da abin da suka gani a wannan al’amari, da abin da ya same su,

27 sai Yahudawa suka ga wajibi ne a gare su, da zuriyarsu, da waɗanda ka tare da su, su kiyaye ranaku biyu ɗin nan ba fashi kowace shekara, bisa ga abin da aka rubuta.

28 Za a tuna da ranakun nan, a kiyaye su a kowane zamani, da kowane iyali, da lardi, da birni. Ranakun Furim ɗin nan, Yahudawa ba za su daina tunawa da su ba, zuriyarsu kuma ba za ta daina tunawa da su ba.

29 Sa’an nan sarauniya Esta ‘yar Abihail, da Mordekai Bayahude, ta ba da cikakken iko a rubuce don ta tabbatar da takardan nan ta biyu game da Furim.

30 Aka aika da takardun zuwa ga dukan Yahudawa da suke a lardi ɗari da ashirin da bakwai na mulkin Ahasurus, da kalmomin salama da na gaskiya,

31 da cewa a kiyaye ranakun Furim a lokacinsu, kamar yadda Mordekai Bayahude, da sarauniya Esta, suka umarci Yahudawa, kamar yadda kuma suka kafa wa kansu da zuriyarsu lokacin tunawa da azuminsu da baƙin cikinsu.

32 Da umarnin Esta aka kafa ka’idodin Furim, aka kuwa rubuta su a littafi.

Categories
ESTA

ESTA 10

Ƙasaitar Mordekai

1 Sarki Ahasurus ya fasa haraji a ƙasar tudu da ta bakin teku.

2 An rubuta a littafin tarihin sarakunan Mediya da na Farisa, dukan ayyukan iko, da isa, da cikakken labarin darajar Mordekai,wadda sarki ya ba shi.

3 Gama sarki Ahasurus kaɗai yake gaba da Mordekai Bayahude, Mordekai kuma yana da girma a wurin Yahudawa, yana kuma da farin jini a wurin taron jama’ar ‘yan’uwansa, gama ya nemi lafiyar jama’arsa, yana kuma maganar alheri ga dukan mutane.

Categories
AYU

AYU 1

Shaiɗan Ya Jarraba Ayuba

1 Akwai wani mutum a ƙasar Uz, mai suna Ayuba, amintacce ne, mai tsoron Allah. Shi mutumin kirki ne, natsattse, yana ƙin aikata kowace irin mugunta.

2 Yana da ‘ya’ya bakwai maza, uku mata.

3 Yana da tumaki dubu bakwai (7,000), da raƙuma dubu uku (3,000), da shanu dubu guda (1,000), da jakuna ɗari biyar. Yana kuma da barori masu yawan gaske, don haka ya fi kowa a ƙasar gabas arziki nesa.

4 ‘Ya’yansa maza sukan yi liyafa bi da bi a gidajen junansu, inda su duka sukan taru koyaushe, sukan gayyaci ‘yan’uwan nan nasu mata su halarci liyafar.

5 A kowane lokacin da aka gama da liyafar, Ayuba yakan tashi da sassafe, kashegarin liyafar, yă miƙa hadayu don yă tsarkake ‘ya’yansa. Haka yake yi kullum, don yana zaton mai yiwuwa ne ɗaya daga cikin ‘ya’yan ya yi zunubi, ya saɓi Allah a ɓoye.

6 Sa’ad da ranar da talikan sama masu rai sukan hallara gaban Ubangiji ta yi, Shaiɗan ma ya zo tare da su.

7 Sai Ubangiji ya tambaye shi, ya ce, “Kai fa me kake yi?”

Shaiɗan ya amsa, ya ce, “Ina ta kaiwa da kawowa ne, a ko’ina a duniya.”

8 Ubangiji ya ce masa, “Ko ka lura da bawana Ayuba? Ba wani mutumin kirki, mai aminci, kamarsa a duniya. Yana yi mini sujada, natsattse ne, yana ƙin aikata kowace irin mugunta.”

9 Shaiɗan ya amsa, ya ce, “A banza Ayuba yake yi maka sujada?

10 Ai, don ka kiyaye shi ne, shi da iyalinsa, da dukan abin da yake da shi. Ka kuma sa wa duk abin da yake yi albarka, ka kuwa ba shi shanun da suka isa su cika dukan ƙasan nan.

11 Amma da a ce za ka raba shi da dukan abin hannunsa, to, da zai fito fili yă zage ka ƙiri ƙiri.”

12 Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “To, shi ke nan, dukan abin hannunsa yana cikin ikonka, amma shi kansa kada ka cuce shi.” Sai Shaiɗan ya tafi.

An Hallaka ‘Ya’yan Ayuba da Dukiyarsa

13 Wata rana ‘ya’yan Ayuba suna shagali a gidan wansu,

14 sai ga jakada ya zo wurin Ayuba a guje, ya ce, “Muna huɗar gona da shanu, jakuna suna kiwo a makiyayar da suke kusa da wurin,

15 sai Sabiyawa suka auka musu farat ɗaya, suka sace su duka, suka kuma karkashe duk barorinka, sai ni kaɗai na tsira, na zo in faɗa maka.”

16 Kafin yă gama magana, sai wani bara ya zo, ya ce, “Tsawa ta kashe tumaki da makiyayansu duka, ni kaɗai na tsira, na zo in faɗa maka.”

17 Kafin yă gama magana, sai wani bara ya zo, ya ce, “Ƙungiyoyin mahara uku na Kaldiyawa suka auka mana, suka kwashe raƙuma duka, suka kuma karkashe barorinka duka, sai ni kaɗai na tsira, na zo in faɗa maka.”

18 Kafin yă gama magana, sai wani bara ya zo, ya ce, “Sa’ad da ‘ya’yanka suke liyafa a gidan wansu,

19 sai hadiri ya taso daga hamada, ya rushe gidan, ya kashe ‘ya’yanka duka, ni kaɗai na tsira na zo in faɗa maka.”

20 Sai Ayuba ya tashi, ya kyakkece tufafinsa don baƙin ciki. Ya aske kansa, ya fāɗi ƙasa,

21 ya ce, “Ban shigo duniya da kome ba, ba kuma zan fita cikinta da kome ba. Ubangiji ya bayar, shi ne kuma ya karɓe, yabo ya tabbata ga sunansa.”

22 Ko da yake waɗannan al’amura duka sun faru, duk da haka Ayuba bai sa wa Allah laifi ba.

Categories
AYU

AYU 2

Shaiɗan Ya Sāke Jarraba Ayuba

1 Sa’ad da ranar da talikan sama masu rai sukan hallara gaban Ubangiji ta sāke yi, Shaiɗan shi ma ya zo tare da su.

2 Ubangiji ya tambaye shi, ya ce, “Ina ka fito?”

Sai Shaiɗan ya amsa, ya ce, “Ina ta kaiwa da kawowa ne, ko’ina a duniya.”

3 Ubangiji ya tambaye shi, ya ce, “Ko ka lura da bawana Ayuba? Ba wani mutumin kirki, mai aminci, kamarsa a duniya. Yana yi mini sujada, natsattse ne, yana ƙin aikata kowace irin mugunta. Kai ka sa na yardar maka ka far masa, ba tare da wani dalili ba. Amma duk da haka Ayuba yana nan da amincinsa kamar yadda yake.”

4 Shaiɗan ya amsa, ya ce, “Mutum ya iya rabuwa da dukan abin da yake da shi don yă ceci ransa.

5 Amma yanzu da a ce za ka taɓa lafiyar jikinsa, da sai yă fito fili yă zage ka.”

6 Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Shi ke nan, yana cikin ikonka, amma fa, kada ka kashe shi.”

7 Sa’an nan Shaiɗan ya rabu da Ubangiji, ya je ya sa ƙuraje su fito ko’ina a jikin Ayuba.

8 Ayuba ya je ya zauna kusa da juji ya ɗauki tsingaro ya yi ta sosa ƙurajen.

9 Sai matarsa ta ce masa, “Har yanzu kana da amincin nan naka? Don me ba za ka zagi Allah ka mutu ba?”

10 Ayuba ya amsa, ya ce mata, “Wace irin maganar gāɓanci ce haka? Lokacin da Allah ya aiko mana da alheri, mukan yi na’am da shi, to, me zai sa sa’ad da ya aiko mana da wahala za mu yi gunaguni?” Cikin dukan wahalar da Ayuba ya sha, bai sa wa Allah laifi ba.

Abokan Ayuba Sun Zo

11 Sa’ad da uku daga cikin abokan Ayuba, wato Elifaz daga birnin Teman, da Bildad daga ƙasar Shuwa, da Zofar daga ƙasar Na’ama, suka ji labarin irin yawan wahalar da Ayuba yake sha, sai suka kama hanya suka tafi su ziyarce shi, su ta’azantar da shi.

12 Suka hango Ayuba tun daga nesa, amma ba su gane shi ba. Da suka gane shi sai suka fara kuka da murya mai ƙarfi. Suka kyakkece tufafinsu saboda baƙin ciki, suka ɗibi ƙura suka watsa a kawunansu.

13 Sa’an nan suka zauna a ƙasa tare da shi, har kwana bakwai, amma ba wanda ya ce uffan, saboda ganin irin yawan wahalar da yake sha.

Categories
AYU

AYU 3

Ayuba Ya Kai Kuka ga Allah

1 Ayuba ya yi magana ya la’anci ranar da aka haife shi.

2 Ya ce,

“Ya Ubangiji, ka la’anci ranan nan da aka haife ni.

3 Ka la’anci daren nan da aka yi cikina.

4 Ka mai da ranan nan ta zama duhu, ya Allah.

Kada a ƙara tunawa da wannan rana,

Kada haske ya ƙara haskakata.

5 Ka sa ta zama ranar duhu baƙi ƙirin.

Ka rufe ta da gizagizai, kada hasken rana ya haskaka ta.

6 Ka shafe wannan dare daga cikin shekara,

Kada kuma a ƙara lasafta shi.

7 Ka sa daren ya zama marar amfani, daren baƙin ciki.

8 Ka faɗa wa masu sihiri su la’anci wannan rana,

Su waɗanda suke umartar dodon ruwa.

9 Ka hana gamzaki haskakawa,

Kada ka bar daren nan ya sa zuciya ga wayewar gari,

10 Ka la’anci daren nan da aka haife ni,

Da ya jefa ni a baƙin ciki da wahala.

11 “Da ma na mutu tun a cikin cikin uwata,

Ko kuwa da haihuwata in mutu.

12 Me ma ya sa uwata ta rungume ni a ƙirjinta,

Ta shayar da ni kuma da mamanta?

13 Da a ce na mutu a lokacin, da yanzu ina huce,

14 Da ina ta barcina kamar sarakuna da masu mulki

Waɗanda suka sāke gina fādodi na dā,

15 Da ina ta sharar barcina kamar shugabanni

Waɗanda suka cika gidajensu da zinariya da azurfa,

16 In yi ta sharar barci kamar jariran da aka haifa matattu.

17 Mugaye za su daina muguntarsu a kabari,

Ma’aikatan da suka gaji da aiki su ma za su huta,

18 Har ‘yan sarƙa ma za su ji daɗin salama,

Su huta daga tsautawa da umarnai masu tsanani.

19 Kowa da kowa yana wurin, babba da ƙarami duk ɗaya ne,

Bayi ma sun sami ‘yanci.

20 “Me ya sa ake barin mutane su yi ta zama cikin damuwa?

Me ya sa ake ba da haske ga waɗanda suke baƙin ciki?

21 Sun jira mutuwa, amma ta ƙi samuwa,

Sun fi son kabari da kowace irin dukiya.

22 Ba su da farin ciki, sai sun mutu an binne su tukuna.

23 Allah ya ɓoye musu sanin abin da zai faru nan gaba,

Ya kalmashe su kowane gefe.

24 A maimakon cin abinci, sai baƙin ciki nake yi,

Ba kuma zan daina yin nishi ba,

25 Dukan abin da nake jin tsoro ko fargaba ya faru.

26 Ba ni da salama, ba ni da hutawa,

Wahala ba za ta taɓa ƙarewa ba.”

Categories
AYU

AYU 4

Elifaz Ya Tsauta wa Ayuba

1 Elifaz ya yi magana.

2 “Ayuba, za ka ji haushi in na yi magana?

Ba zan iya kannewa, in yi shiru ba.

3 Ka koya wa mutane da yawa,

Ka kuma ƙarfafa hannuwan marasa ƙarfi.

4 Idan wani ya yi tuntuɓe,

Ya gaji, ya rasa ƙarfi,

Kalmominka suka ƙarfafa zuciyarsa,

Har ya iya tsayawa kyam.

5 Yanzu naka lokacin wahala ya zo,

Kai kuwa ka rikice, ka kasa ɗaurewa,

6 Kana yi wa Allah sujada,

Ba wani laifi a zamanka,

Ya kamata ka amince ka sa zuciya.

7 “Yanzu fa sai ka yi tunani.

Ka faɗi bala’i ɗaya wanda ya taɓa fāɗa wa adalin mutum.

8 Na taɓa ganin mutane suna huɗe gonar mugunta,

Suna shuka mugunta,

Suka kuwa girbe mugunta.

9 A cikin fushinsa Allah yakan hallaka su kamar hadiri.

10 Mugaye sukan yi ruri suna gurnani kamar zakoki,

Amma Allah yakan sa su yi tsit,

Ya kakkarya haƙoransu.

11 Kamar zakoki da ba su da abin da za su kashe su ci,

Haka nan za su mutu, ‘ya’yansu kuwa su warwatse duka.

12 “Wata rana wani saƙo ya zo a hankali,

Har da ƙyar nake iya ji,

13 Kamar wani irin mafarki mai razanarwa yake,

Wanda ya hana ni jin daɗin barcina.

14 Na yi rawar jiki ina makyarkyata,

Duk jikina yana ta ɓare-ɓare don tsoro.

15 Wata iska marar ƙarfi ta taɓa fuskata,

Sai fatar jikina ta yanƙwane saboda fargaba.

16 Na ga wani abu can yana tsaye,

Na zura ido, amma ban san kowane irin abu ba ne,

Ina cikin wannan hali sai na ji murya,

17 Ta ce, ‘Mutum yana iya zama adali a gaban Allah?

Akwai kuma wanda yake mai tsarki a gaban Mahaliccinsa?

18 Allah ba ya amince wa barorinsa na cikin sammai,

Yakan sami laifi a wurin mala’ikunsa.

19 Ta ƙaƙa zai amince da talikinsa wanda aka yi da ƙasa,

Abin da yake na ƙura, ana kuwa iya murƙushe shi kamar asu.

20 Mai yiwuwa ne mutum yana raye da safe

Amma ya mutu ba a sani ba kafin maraice.

21 Duk abin da ya mallaka an ɗauke,

Duk da haka ya mutu cikin rashin hikima.’ ”