Categories
AYU

AYU 5

1 “Ka yi kira, ya Ayuba, ka gani, ko wani zai amsa!

Akwai wani mala’ika da za ka juya zuwa gare shi?

2 Ba shi da amfani ka dami kanka

Har ka mutu, saboda tsarguwa, gama wannan wawanci ne,

Da aikin rashin hankali.

3 Na ga waɗansu wawaye waɗanda ake gani kamar suna zaune lafiya,

Amma nan da nan sai na la’anci gidajensu.

4 Ko kaɗan, ‘ya’yansu maza ba za su taɓa zama lafiya ba.

Ba wanda zai tsaya musu a ɗakin shari’a.

5 Mayunwata za su ci amfanin gonar wawa,

Har da hatsin da yake girma cikin ƙayayuwa,

Waɗanda suke jin ƙishirwa za su ji ƙyashin dukiyarsa.

6 Zunubi ba ya tsirowa daga ƙasa,

Haka ma wahala ba ta tsirowa daga ƙasa.

7 Ai, an haifi mutum domin wahala ne,

Tabbatacce ne kamar yadda tartsatsin wuta suke tashi.

8 “In da ni ne kai, da sai in juya wurin Allah,

In kai ƙarata a wurinsa.

9 Ba za mu iya fahimtar manyan abubuwa da yake yi ba,

Al’ajabansa kuwa ba su da iyaka.

10 Yakan aiko da ruwan sama,

Ya shayar da gonaki.

11 I, Allah ne yake ɗaukaka masu tawali’u,

Shi yake kuɓutar da dukan waɗanda suke makoki.

12 Yakan birkitar da shirye-shiryen masu wayo.

13 Yakan sa wa masu wayo tarko cikin dabarunsu,

Har ba za su yi nasara a dukan abin da suke yi ba.

14 Da rana sukan yi karo da duhu,

Ko da tsakar rana ma lalube suke kamar ana duhu.

15 Amma Allah yakan ceci matalauta daga mutuwa,

Yakan kuma ceci masu bukata daga zalunci.

16 Yakan sa matalauta su sa zuciya,

Ya sa mugaye su yi shiru.

17 “Mai farin ciki ne mutumin da Allah ya hora,

Kada ka tsargu sa’ad da ya tsauta maka.

18 Allah yakan yi maganin raunin da ya yi maka,

Ciwon da ya ji maka da hannunsa,

Da hannunsa yakan warkar.

19 Yakan tsare ka daga cuta sau shida har sau bakwai,

Ba muguntar da za ta taɓa ka.

20 Yakan kiyaye ka da rai a lokacin yunwa,

A yaƙi kuma yakan tsare ka daga mutuwa.

21 Allah yakan kuɓutar da kai daga ƙarairayi da ɓata suna,

Yakan cece ka daga hallaka.

22 Aikin kama-karya da yunwa za su zama abin dariya a gare ka,

Ba kuwa za ka ji tsoron namomin jeji ba.

23 Ba za a sami duwatsu a gonakin da kake nomawa ba,

Mugayen namomin jeji ba za su far maka ba.

24 Sa’an nan za ka zauna lafiya a alfarwanka,

A sa’ad da ka dubi tumakinka, za ka tarar suna nan lafiya.

25 ‘Ya’yanka za su yi yawa kamar ciyawa,

Kamar yadda alkama take a lokacin kakarta.

26 Haka kai ma za ka rayu, har ka tsufa da kyakkyawan tsufa.

27 Kai, Ayuba, mun koyi wannan don mun daɗe muna nazari,

Gaskiya ce, don haka ka yarda da wannan.”

Categories
AYU

AYU 6

Ayuba Ya Zargi Abokansa

1 Ayuba ya amsa.

2 “In da za a auna wahalata da ɓacin raina da ma’auni,

3 Da sun fi yashin teku nauyi.

Kada ka yi mamaki da maganganun da nake yi.

4 Allah Maɗaukaki ya harbe ni da kibau,

Dafinsu kuwa ya ratsa jikina.

Allah ya jera mini abubuwa masu banrazana.

5 “Idan jaki ya sami ciyawar ci, muradinsa ya biya,

In ka ji saniya ta yi shiru, tana cin ingirici ne.

6 Amma wane ne zai iya cin abinci ba gishiri?

Akwai daɗin ɗanɗano ga farin ruwan ƙwai?

7 Ba na jin marmarin cin abinci irin haka,

Kowane irin abu da na ci yakan sa mini cuta.

8 “Me ya sa Allah ya ƙi ba ni abin da nake roƙo?

Me ya sa ya ƙi yin abin da nake so?

9 Da ma ya ci gaba kawai ya kashe ni,

Ko ya sake ikonsa ya datse ni!

10 Da na san zai yi haka, da sai in yi tsalle don murna,

Da ba zan kula da tsananin azabar da nake ciki ba.

Ban taɓa yin gāba da umarnan Allah ba.

11 Wane ƙarfi ne nake da shi na rayuwa?

Wane sa zuciya kuma nake da ita,

tun da na tabbata mutuwa zan yi?

12 Da dutse aka yi ni?

Ko da tagulla aka yi jikina?

13 Ba ni da sauran ƙarfi da zan ceci kaina,

Ba inda zan juya in nemi taimako.

14 “A cikin irin wannan wahala

Ina bukatar amintattun abokai,

Ko da na rabu da Allah, ko ina tare da shi.

15 Amma ku abokaina,kun ruɗe ni,

Kamar rafi wanda yakan ƙafe da rani.

16-17 Rafin yana cike da iska mai laima da ƙanƙara,

Amma lokacin zafi sai su ɓace,

Kwacciyar rafin, sai ta bushe ba kome.

18 Ayari sukan ɓata garin neman ruwa,

Su yi ta gilo, har su marmace a hamada.

19 Ayari daga Sheba da Tema suka yi ta nema,

20 Amma sa zuciyarsu ta ƙare a gefen busassun rafuffuka,

21 Kamar rafuffukan nan kuke a gare ni,

Kun ga abin da ya same ni, kun gigita.

22 Na roƙe ku ku ba ni kyauta ne?

Ko kuwa na roƙe ku ku ba wani rashawa domina?

23 Ko kuma na roƙe ku ku cece ni daga maƙiyi ko azzalumi ne?

24 “To, sai ku koya mini, ku bayyana mini laifofina,

Zan yi shiru in kasa kunne gare ku.

25 Kila muhawara mai ma’ana ta rinjaye ni,

Amma yanzu duk maganar shirme kuke yi.

26 Kuna so ku amsa maganganuna?

Don me?

Mutumin da yake cikin halin ƙaƙa naka yi,

Ba wata maganar da zai yi in ba shirme ba.

27 Kukan jefa wa bayi da marayu kuri’a,

Kukan arzuta kanku daga abokanku na kurkusa.

28 Ku dubi fuskata,

Lalle ba zan faɗi ƙarya ba.

29 Kai, kun zaƙe, ku daina aikata rashin adalci,

Kada ku sa mini laifi, nake da gaskiya.

30 Amma duk da haka kuna tsammani ƙarya nake yi.

Kuna tsammani ba zan iya rarrabe tsakanin gaskiya da ƙarya ba.”

Categories
AYU

AYU 7

Ayuba Ya Damu da Abin da Allah Ya Yi

1 “Kamar kamen soja na tilas,

Haka zaman ‘yan adam take,

Kamar zaman mai aikin bauta.

2 Kamar bawa ne wanda yake sa zuciya ga inuwa mai sanyi,

Kamar ma’aikaci wanda yake sa zuciya ga lokacin biya.

3 Wata da watanni ina ta aikin banza,

Kowane dare ɓacin rai yake kawo mini.

4 Sa’ad da na kwanta barci, sai daren ya daɗa tsawo

In yi ta jujjuyawa duk dare, in ƙosa gari ya waye.

5 Jikina cike yake da tsutsotsi,

Ƙuraje duka sun rufe shi,

Daga miyakuna mugunya tana ta zuba.

6 Kwanakina sun wuce ba sa zuciya,

Sun wuce da sauri kamar ƙoshiyar saƙa.

7 “Ka tuna, ya Ubangiji, raina iska ne kawai,

Farin cikina ya riga ya ƙare.

8 Kuna ganina yanzu, amma ba za ku sāke ganina ba.

Idan kuka neme ni, za ku tarar ba na nan.

9 Kamar girgijen da yake bajewa ya tafi,

Haka nan mutum yake mutuwa.

10 Ba kuwa zai ƙara komowa ba,

Mutanen da suka san shi, duka za su manta da shi.

11 A’a, ko kaɗan ba zan yi shiru ba!

Haushi nake ji, zuciyata ta ɓaci,

Dole ne in yi magana.

12 “Ya Ubangiji, don me ka sa ni a waƙafi?

Kana tsammani ni dodon ruwa ne?

13 Na kwanta ina ƙoƙari in huta,

Ina neman taimako don azabar da nake sha.

14 Amma kai kana firgita ni da mafarkai,

Kana aiko mini da wahayi da ganegane,

15 Har nakan fi so a rataye ni,

Gara in mutu da in rayu a wannan hali.

16 Na fid da zuciya. Na gaji da rayuwa.

Ku rabu da ni. Rayuwa ba ta da wata ma’ana.

17 “Ya Ubangiji, me ya sa mutum yake da daraja haka a gare ka?

Me ya sa kake lura da abin da yake yi?

18 Kakan dube shi kowace safiya.

Kana jarraba shi a kowane daƙiƙa.

19 Ba za ka ko ɗan kawar da kai ba,

Don in samu in haɗiye yau?

20 Ko na yi zunubi ina ruwanka,

Kai mai ɗaure mutane?

Me ya sa ka maishe ni abin bārata?

Ni wani babban kaya mai nauyi ne a gare ka?

21 Ba za ka iya gafarta mini zunubina ba?

Ba za ka kawar da kai ga muguntar da na aikata ba?

Ba da daɗewa ba zan rasu in koma a ƙura,

Lokacin da ka neme ni ba za ka same ni ba.”

Categories
AYU

AYU 8

Bildad Ya Ƙarfafa Hukuncin Allah Daidai Ne

1 Sai Bildad ya yi magana.

2 “Ka gama maganganunka marasa kan gado duka?

3 Allah bai taɓa yin danniya ba,

Bai kuma taɓa fāsa aikata abin da yake daidai ba.

4 Lalle ‘ya’yanka sun yi wa Allah zunubi,

Don haka ya hukunta su yadda ya cancanta.

5 Amma sai ka juyo ka yi roƙo ga Allah Maɗaukaki.

6 Idan kana da tsarki da aminci, Allah zai taimake ka,

Ya maido da iyalin gidanka, ya yi maka sakayya.

7 Duk hasarar dukiyan nan da ka yi, ba kome ba ne

In aka gwada da abin da Allah zai ba ka nan gaba.

8 “Ka tsai da zuciyarka a kan hikima irin ta zamanin dā.

Ka kuma yi ta yin tunani a kan gaskiyar da kakanninmu suka koya.

9 Kwanakinmu ‘yan kaɗan ne kawai,

Ba mu san kome ba,

Mu inuwa ne kawai a fuskar duniya.

10 Amma ka yarda masu hikima na zamanin dā su koya maka,

Ka kasa kunne ga abin da za su faɗa.

11 “Iwa ba ta tsirowa inda ba ruwa,

Ba a taɓa samunta a ko’ina ba sai a fadama.

12 In ruwan ta ƙafe, ita ce za ta fara bushewa,

Tun tana ƙanƙana ba ta isa a yanke a yi amfani da ita ba.

13 Marasa tsoron Allah kamar iwan nan suke,

Ba su da sa zuciya muddin sun rabu da Allah.

14 Suna dogara ga silin zare, murjin gizo-gizo.

15 Idan suka jingina ga saƙar gizo-gizo, za ta iya tokare su?

Idan sun kama ta, za ta taimake su tsayawa?

16 “Mugaye sukan tsiro kamar ciyayi a hasken rana,

Ciyayin da sukan yaɗu su cinye gona duka.

17 Saiwoyinsu sukan nannaɗe duwatsu,

Su riƙe kowane dutse da ƙarfi.

18 Amma idan aka tumɓuke su,

Ba wanda zai taɓa cewa sun kasance a wurin.

19 Hakika matuƙar murnar da mugaye suke da ita ke nan,

Yanzu waɗansu ne za su zo su gāje wurarensu.

20 “Amma daɗai Allah ba zai rabu da amintattu ba,

Ba kuwa zai taɓa taimakon mugun mutum ba.

21 Zai sāke barinka ka yi dariya ka ƙyalƙyata kamar dā,

Ka kuma yi sowa da murna matuƙa.

22 Amma zai sa maƙiyanka su sha kunya,

Za a shafe gidajen mugaye.”

Categories
AYU

AYU 9

Ayuba Ya Kasa Amsa wa Allah

1 Ayuba ya amsa.

2 “Ai, na taɓa jin waɗannan duka,

Amma ta ƙaƙa mutum zai yi jayayya da Allah har ya yi nasara?

3 Ta ƙaƙa za ka iya jayayya da shi?

Yana yiwuwa ya yi maka tambayoyi guda dubu

Waɗanda ba wanda zai iya ba da amsarsu.

4 Allah mai hikima ne, mai iko,

Ba wanda zai iya ja in ja da shi.

5 Yakan kawar da manyan duwatsu farat ɗaya,

Ya hallaka su da fushinsa,

6 Allah yakan aiko da girgizar ƙasa, ya girgiza duniya,

Yakan jijjiga ginshiƙan da duniya take zaune a kansu.

7 Allah yana da iko ya hana rana fitowa,

Ko kuma ya hana taurari haskakawa da dare.

8 Ba wanda ya taimaki Allah shimfiɗa sammai,

Wanda yake taka raƙuman ruwan teku, ya kuma kwantar da su.

9 Allah ya rataye taurari a sararin sama,

Wato su mafarauci da kare da zomo,

Da kaza da ‘ya’yanta da taurarin kudu.

10 Ba shi yiwuwa mu gane manyan abubuwa da yake yi.

Ayyukan al’ajabansa ba su da iyaka.

11 “Allah yana wucewa kusa da ni,

Amma ba na ganinsa.

12 Yakan ɗauki abin da yake so, ba wanda yake hana shi,

Ba wanda yake tambayarsa cewa,

‘Me kake yi?’

13 “Allah ba zai huce fushinsa ba.

Ya murƙushe maƙiyansa waɗanda suka taimaki dodon ruwan nan da ake kira Rahab, wanda ya tayar masa.

14 To, ƙaƙa zan yi in samo kalmomin da zan amsa wa Allah?

15 Ko da yake ba ni da laifi,

Duk da haka iyakar abin da zan iya yi ke nan,

In roƙi Allah ya yi mini jinƙai,

Shi da yake alƙalina.

16 Amma duk da haka ko ya yardar mini in yi magana ma,

Ban yi tsammani zai saurare ni ba.

17 Shi ya aiko da hadura, suka yi kacakaca da ni,

Suka ƙuƙƙuje ni, ga shi kuwa, ba wani dalilin da ya sa ya yi mini rauni.

18 Ya hana ni in ko shaƙata,

Ina jin haushin dukan abin da yake yi mini.

19 In gwada ƙarfi ne?

To, a iya gwada wa Allah ƙarfi?

In kai shi ƙara ne?

Wa zai sa shi ya je?

20 Ni ba ni da laifin kome, amintacce ne ni,

A kunne sai a ji kalmomina kamar na marar gaskiya ne.

Kowane abu da na fāɗa, kā da ni yake yi.

21 Ba ni da laifin kome, amma ba na ƙara damuwa.

Na gaji da rayuwa.

22 Don haka ban damu da kome ba.

Da marar laifin da mai laifin duk, Allah zai hallaka mu.

23 Sa’ad da marar laifi ya mutu farat ɗaya,

Allah yakan yi dariya.

24 Allah ya ba da duniya ga mugaye,

Ya makantar da dukan alƙalai,

Idan ba Allah ne ya yi haka nan ba, to, wa ya yi?

25 “Kwanakina suna shuɗewa da sauri, ba mai kyau ko ɗaya.

26 Raina na wucewa kamar jirgin ruwa mafi sauri,

Da sauri ƙwarai kamar juhurma ya kai wa zomo sura.

27 Idan an yi murmushi,

Ina ƙoƙari in manta da azabata,

28 Sai dukan wahalar da nake sha ta yi ta firgita ni,

Na sani Allah ya ɗauke ni mai laifi.

29 Tun da yake Allah ya ɗauka, ni mai laifi ne,

To, me zai sa in damu?

30 Ba sabulun da zai iya wanke zunubaina.

31 Allah ya jefa ni a kwatami,

Har tufafina ma suna jin kunyata.

32 Da a ce Allah mutum ne,

Da sai in mayar masa da magana,

Da sai mun je ɗakin shari’a a yanka mana shari’a.

33 Amma ga shi, ba wanda zai shiga tsakaninmu,

Ba wanda zai shara’anta tsakanina da Allah.

34 Ka daina hukunta ni, ya Allah!

Ka daina razanar da ni.

35 Ba na jin tsoro,

Zan yi magana, domin na san zuciyata.”

Categories
AYU

AYU 10

Ayuba Ya Yi Kukan Matsayin da Yake Ciki

1 “Na gaji da rayuwa,

Ku ji ina fama da baƙin ciki.

2 Kada ka hukunta ni, ya Allah.

Ka faɗa mini laifin da kake tuhumata da shi.

3 Daidai ne a gare ka ka yi mugunta?

Ka wulakanta abin da kai da kanka ka yi?

Sa’an nan ka yi murmushi saboda dabarun mugaye?

4 Yadda mutane suke duban abu, haka kake duba?

5 Kai ma ranka gajere ne kamar namu?

6 In haka ne, me ya sa kake bin diddigin dukan laifofina,

Kana farautar dukan abin da na yi?

7 Ka sani, ba ni da laifi,

Ka kuma sani, ba wanda zai cece ni daga gare ka.

8 “Da ikonka ne ka yi ni, ka siffata ni,

Yanzu kuma da ikon nan naka ne za ka hallaka ni.

9 Ka tuna, ya Allah, kai ka halicce ni, da yumɓu kuwa ka yi ni.

Za ka murtsuke ni ne, in kuma koma ƙura?

10 Kai ne ka ba mahaifina ƙarfin da zai haife ni,

Kai ne ka sa na yi girma a cikin cikin mahaifiyata.

11 Kai ne ka siffata jikina da ƙasusuwa da jijiyoyi,

Ka rufe ƙasusuwan da nama, naman kuma ka rufe da fata.

12 Kai ne ka ba ni rai da madawwamiyar ƙauna,

Kulawarka ce ta sa ni rayuwa.

13 Amma yanzu na sani,

Dukan lokacin nan kana da wani nufi a ɓoye game da ni.

14 Jira kake ka ga ko zan yi zunubi,

Don ka ƙi gafarta mini.

15 Da cewa na yi zunubi, na shiga uku ke nan a wurinka.

Amma sa’ad da na yi abin kirki ba na samun yabo.

Ina baƙin ciki ƙwarai, kunya ta rufe ni.

16 Da zan ci nasara a kan kowane abu,

Da sai ka yi ta farautata kamar zaki,

Kana aikata al’ajabai don ka cuce ni.

17 A koyaushe kakan karɓi shaida gāba da ni,

Fushinka sai gaba gaba yake yi a kaina,

Kakan yi mini farmaki a koyaushe.

18 “Ya Allah, me ya sa ka bari aka haife ni?

Da ma na mutu tun kafin wani ya gan ni!

19 Da a ce daga cikin cikin mahaifiyata an wuce da ni zuwa kabari

Da ya fi mini kyau bisa ga kasancewata.

20 Raina bai kusa ƙarewa ba? A bar ni kawai!

Bari in ci moriyar lokacin da ya rage mini.

21 An jima kaɗan zan tafi, ba kuwa zan komo ba faufau,

Zan tafi ƙasa mai duhu, inda ba haske,

22 Ƙasa mai duhu, da inuwoyi da ɗimuwa

Inda ko haske ma kansa duhu ne.”

Categories
AYU

AYU 11

Zofar Ya Zargi Ayuba a kan Aikata Laifi

1 Zofar ya amsa.

2 “Ba wanda zai amsa dukan wannan surutu?

Yawan magana yakan sa mutum ya zama daidai?

3 Ayuba,kana tsammani ba za mu iya ba ka amsa ba?

Kana tsammani maganganunka na ba’a

Za su sa mu rasa abin da za mu mayar maka?

4 Ka ɗauka duk abin da kake faɗa gaskiya ne,

Ka kuma mai da kanka kai mai tsarki ne a gaban Allah.

5 Da ma Allah zai amsa maka,

Ya yi magana gāba da kai,

6 Da ya faɗa maka hikima tana da fannoni da yawa.

Akwai abubuwa waɗanda suka fi ƙarfin ganewar ɗan adam.

Duba, Allah ya ƙyale wani ɓangare na laifinka.

7 “Kana iya gane matuƙa da iyakar

Girman Allah da na ikonsa?

8 Sararin sama ba shi ne matuƙa a wurin Allah ba,

Amma ga shi, yana can nesa da kai,

Allah ya san lahira,

Amma kai ba ka sani ba.

9 Fāɗin girman Allah ya fi duniya

Ya kuma fi teku fāɗi.

10 Idan Allah ya kama ka ya gurfanar da kai gaban shari’a,

Wa zai iya hana shi?

11 Allah ya san irin mutanen da ba su da amfani,

Domin yana ganin dukan mugayen ayyukansu.

12 Idan dakikan mutane sa yi hikima,

To, jakunan jeji ma sa yi irin hali na gida.

13 “Ayuba, ka shirya zuciyarka,

Ka ɗaga hannuwanka zuwa wurin Allah.

14 Ka kawar da mugunta da kuskure daga gidanka.

15 Sa’an nan ka sāke shan ɗamarar zaman duniya,

Da ƙarfi da rashin tsoro.

16 Duk wahalarka za ta gushe daga tunaninka,

Kamar yadda rigyawa takan wuce, ba a ƙara tunawa da ita.

17 Ranka zai yi haske fiye da hasken rana da tsakar rana.

Kwanakin ranka mafiya duhu

Za su yi haske kamar ketowar alfijir.

18 Za ka yi zaman lafiya, cike da sa zuciya,

Allah zai kiyaye ka, ya ba ka hutawa.

19 Ba za ka ji tsoron kowane maƙiyi ba,

Mutane da yawa za su nemi taimako daga gare ka.

20 Amma mugaye za su dudduba ko’ina da fid da zuciya,

Ba su da wata hanyar da za su kuɓuta.

Sauraronsu kaɗai shi ne mutuwa.”

Categories
AYU

AYU 12

Ayuba Ya Ƙarfafa Ikon Allah da Hikimar Allah

1 Ayuba ya amsa.

2 “Aha! Ashe, kai ne muryar jama’a,

Idan ka mutu hikima ta mutu ke nan tare da kai.

3 Amma ni ma ina da hankali gwargwado, kamar yadda kake da shi,

Ban ga yadda ka fi ni ba.

Kowa ya san sukan abin da ka faɗa.

4 Har abokaina ma, suna ta yi mini dariya yanzu,

Suna ta dariya ko da yake ni adali ne marar laifi,

Amma akwai lokacin da Allah ya amsa addu’o’ina.

5 Ba ka shan wahalar kome, duk da haka ka maishe ni abin dariya.

Ka bugi mutumin da yake gab da fāɗuwa.

6 Amma ɓarayi da marasa tsoron

Allah suna zaune cikin salama,

Ko da yake ƙarfinsu ne kaɗai allahnsu.

7 “Don haka tsuntsaye da dabbobi sun fi ka sani,

Suna da abu mai yawa da za su koya maka.

8 Ka roƙi talikan da suke a duniya, da cikin teku, hikimar da suke da ita.

9 Dukansu sun sani ikon Ubangiji ne ya yi su.

10 Allah shi ne yake bi da rayukan talikansa.

Numfashin dukan mutane kuwa a ikonsa yake.

11 Amma kamar yadda harsunanku suke jin daɗin ɗanɗanar abinci,

Haka nan kuma kunnuwanku suke jin daɗin sauraren kalmomi.

12-13 “Tsofaffi suna da hikima,

Amma Allah yana da hikima da iko.

Tsofaffi suna da tsinkaya,

Amma Allah yana da tsinkaya da ikon aikatawa.

14 Sa’ad da Allah ya rurrushe, wa zai iya sāke ginawa?

Wa kuma zai iya fitar da mutumin da Allah ya sa a kurkuku?

15 Akan yi fari sa’ad da Allah ya hana ruwan sama,

Rigyawa takan zo sa’ad da ya kwararo ruwa.

16 Allah mai iko ne a kullum kuwa cikin nasara yake

Da macuci, da wanda aka cutar, duk ƙarƙashin ikon Allah suke.

17 Yakan mai da hikimar masu mulki wauta,

Yakan mai da shugabanni marasa tunani.

18 Yakan tuɓe sarakuna ya sa su kurkuku.

19 Yakan ƙasƙantar da firistoci da mutane masu iko.

20 Yakan rufe bakin waɗanda aka amince da su.

Yakan kawar da hikimar tsofaffi.

21 Yakan kunyatar da masu iko,

Ya hana wa masu mulki ƙarfi.

22 Yakan aika da haske a wuraren da suke da duhu kamar mutuwa.

23 Yakan sa sauran al’ummai su yi ƙarfi su ƙasaita,

Sa’an nan ya fatattaka su, ya hallaka su.

24 Yakan sa shugabanninsu su zama wawaye,

Ya bar su su yi ta makuwa, su ruɗe, su ɓata,

25 Su yi ta lalube cikin duhu, su yi ta tangaɗi kamar bugaggu.”

Categories
AYU

AYU 13

Ayuba Ya Kāre Mutuncinsa

1-2 “Duk abin da ka hurta, na taɓa jinsa,

Na gane da shi sarai.

Iyakar abin da kuka sani, ni ma na sani.

Ba ku fi ni da kome ba.

3 Amma da Allah nake jayayya, ba da ku ba,

Ina so in yi muhawara da shi a kan ƙarar da nake da ita.

4 Kun ɓoye jahilcinku da ƙarairayi.

Kun zama kamar likitoci waɗanda ba su iya warkar da kowa ba.

5 Kada ku faɗi kome,

Wani sai ya ce kuna da hikima!

6 “Ku saurara mini, zan faɗi ƙarata.

7 Me ya sa kuke yin ƙarya?

Kuna tsammani ƙarairayinku za su taimaki Allah?

8 Son zuciya kuke yi, ko ba haka ba?

Kuna goyon bayan Allah?

Za ku goyi bayan Allah sa’ad da aka gurfanar da ni gaban shari’a?

9 Da Allah ya bincike ku sosai,

Zai iske wani abin kirki ne a cikinku?

Kuna tsammani za ku ruɗi Allah, kamar yadda kuke ruɗin mutane?

10 Ko da yake kun ɓoye son zuciyarku,

Duk da haka zai tsauta muku,

11 Ikonsa kuwa zai razana ku.

12 Karin maganarku da muhawararku ba su da ƙarfi ƙwarai.

13 “Ku yi shiru ku ba ni zarafi in yi magana.

Duk abin da zai faru, ya faru.

14 A shirye nake in yi kasai da raina.

15 Na fid da zuciya ɗungum.

To, in Allah ya kashe ni, sai me?

Zan faɗa masa ƙarata.

16 Mai yiwuwa ne ƙarfin halina ya cece ni,

Tun da yake ba wani mugun mutumin da zai iya zuwa gaban Allah.

17 Sai a saurari bayanin da zan yi.

18 A shirye nake in faɗi ƙarata,

Domin na sani ina da gaskiya.

19 “Ya Allah, za ka yi ƙarata?

Idan kuwa ka yi, to, a shirye nake in yi shiru in mutu.

20 Ina da abu biyu da zan yi maka roƙo,

Ka yarda da su, sa’an nan ba zan yi ƙoƙari in ɓoye ba.

21 Wato ka daina hukuncin da kake yi mini,

Kada ka sa razanarka ta ragargaza ni.

22 “Ka fara yin magana, ya Allah, ni kuwa zan amsa.

Ko kuma ka bari in yi magana, sa’an nan ka amsa mini.

23 Kuskure da laifi guda nawa na yi?

Waɗanne irin laifofi ake tuhumata da su?

24 Me ya sa kake guduna?

Me ya sa ka maishe ni kamar maƙiyi?

25 Ƙoƙari kake ka firgita ni?

Ni ba wani abu ba ne, ganye ne kawai,

Ka fāɗa wa tattaka da yaƙi ne kawai.

26 Ka kawo mugayen ƙararraki a kaina,

Har da laifofin da na yi na ƙuruciya.

27 Ka ɗaure ƙafata da sarƙoƙi,

Kakan lura da kowace takawata,

Har kana bin diddigin sawayena.

28 Saboda wannan na zama abin kallo,

ni kuwa kamar ragargazajjen itace ne, ko diddigaggiyar riga.”

Categories
AYU

AYU 14

Ayuba Ya Yi Tunani a kan Rashin Tsawon Rai

1 “Mutum duka kwanakin ransa gajere ne, kwanakin wahala kuwa.

2 Sukan yi girma su bushe nan da nan kamar furanni,

Sukan shuɗe kamar inuwa.

3 Na ma isa ka dube ni ne, ya Allah?

Ko ka gabatar da ni a gabanka,

Ka yi mini shari’a?

4 Ba wani abu tsarkakakke

Da zai fito daga cikin kowane marar tsarki, kamar mutum.

5 Tsawon kwanakin ransa, an ƙayyade su tun can,

An ƙayyade yawan watannin da zai yi,

Ka riga ka yanke haka ya Allah, ba su sākuwa.

6 Ka kawar da fuska daga gare shi, ka rabu da shi,

Ka bar shi ya ji daɗin kwanakinsa na fama da aiki idan zai iya.

7 “Akwai sa zuciya ga itacen da aka sare,

Yana iya sāke rayuwa ya yi toho.

8 Ko da yake saiwoyinsa sun tsufa,

Kututturensa kuma ya ruɓe a ƙasa,

9 In aka zuba ruwa, sai ya toho kamar sabon tsiro.

10 Amma ɗan mutum ya mutu, ƙarshensa ke nan,

Ya mutu, a ina yake a lokacin nan?

11 “Mai yiwuwa ne koguna za su daina gudu,

Har tekuna kuma su ƙafe.

12 Amma matattu ba za su tashi ba daɗai,

Ba za su ƙara tashi ba sam, muddin sararin sama na nan.

Sam, ba za a dame su cikin barcinsu ba.

13 “Ya Allah, da ma a ce ka ɓoye ni a lahira,

Ka bar ni a ɓoye, har fushinka ya huce,

Sa’an nan ka sa lokacin da za ka tuna da ni!

14 Idan mutum ya mutu, zai sāke rayuwa kuma?

Amma zan jira lokaci mafi kyau,

In jira sai lokacin wahala ya wuce.

15 Sa’an nan za ka yi kira, ni kuwa zan amsa,

Za ka yi murna da ni, ni talikinka.

16 Sa’an nan za ka lura da kowace takawata

Amma ba za ka bi diddigin zunubaina ba.

17 Za ka soke zunubaina ka kawar da su,

Za ka shafe dukan kurakuran da na taɓa yi.

18 “Lokaci na zuwa sa’ad da duwatsu za su fāɗi,

Har ma za a kawar da duwatsun bakin teku.

19 Ruwa zai zozaye duwatsu, su ragu,

Ruwan sama mai ƙarfi zai kwashe jigawa,

Kai ma ka bar mutane, ba su da sauran sa zuciya ko kaɗan.

20 Ka fi ƙarfin mutum, ka kore shi har abada,

Fuskarsa ta rikiɗe sa’ad da ya mutu.

21 ‘Ya’yansa maza za su sami girma,

amma sam, ba zai sani ba,

Sam, ba wanda zai faɗa masa sa’ad da aka kunyatar da su.

22 Ciwon jikinsa da ɓacin zuciyarsa kaɗai yake ji.”