Categories
AYU

AYU 35

1 Elihu kuwa ya yi magana.

2 “Ayuba, ba daidai ba ne, ka ce,

Ba ka yi laifi a gaban Allah ba,

3 Ka kuwa ce, ‘Wace riba na ci?

Wane fifiko nake da shi fiye da idan na yi zunubi?’

4 Zan ba ka amsa, kai da abokanka.

5 Ka duba sama,

Ka dubi gizagizai waɗanda suke can sama da kai.

6 Idan ka yi zunubi, da me ka cuci Allah?

Idan ka aikata laifofi da yawa, wace cuta ka yi masa?

7 Idan kai adali ne da me ka ƙara masa,

Ko kuwa me ya samu daga gare ka?

8 Muguntarka ta shafi mutum ne kamarka,

Haka kuma adalcinka ya shafi ɗan adam ne kawai.

9 “Saboda yawan zalunci, jama’a sukan yi kuka,

Suka nemi taimako, saboda matsin masu ƙarfi.

10 Amma ba su juyo wurin Allah Mahaliccinsu ba,

Wanda yakan sa a raira waƙa da dare,

11 Wanda yake koya mana fiye da namomin jeji da suke a duniya,

Wanda ya sa muka fi tsuntsayen sama hikima.

12 Suka yi kira don taimako, amma Allah bai amsa ba,

Saboda suna da girmankan mugaye.

13 Hakika Allah bai ji holoƙon kukansu ba,

Allah Mai Iko Dukka kuwa bai kula da shi ba.

14 “Ayuba, kai wane ne da za ka ce ba ka gan shi ba?

Da kake cewa ƙararka tana gabansa,

Jiransa kake yi?

15 Yanzu fa saboda bai yi hukunci da fushinsa ba,

Kamar kuma bai kula da laifi ba,

16 Ayuba, maganarka marar ma’ana ce,

Ka yi ta maganganu marasa hikima.”

Categories
AYU

AYU 36

Elihu Ya Ɗaukaka Girman Allah

1 Elihu ya ci gaba da magana.

2 “Ka yi mini haƙuri kaɗan, ni kuwa zan nuna maka,

Gama har yanzu ina da abin da zan faɗa in kāre Allah.

3 Zan tattaro ilimina daga nesa,

In bayyana adalcin Mahaliccina.

4 Gaskiya nake faɗa ba ƙarya ba,

Wanda yake da cikakken sani yana tare da kai.

5 “Ga shi kuwa, Allah Mai Girma, ba ya raina kowa,

Shi mai girma ne, mai cikakkiyar basira.

6 Ba ya rayar da masu laifi,

Amma yakan ba waɗanda ake tsananta wa halaliyarsu.

7 Yakan kiyaye waɗanda suke aikata gaskiya,

Yakan kafa su har abada tare da sarakuna,

A gadon sarauta, ya ɗaukaka su.

8 Amma idan aka ɗaure su da sarƙoƙi,

Da kuma igiyar wahala,

9 Sa’an nan yakan sanar da su aikinsu

Da laifofin da suke yi na ganganci.

10 Yakan sa su saurari koyarwa,

Da umarnai, cewa su juya, su bar mugunta.

11 Idan suka kasa kunne suka bauta masa,

Za su cika kwanakinsu da wadata,

Shekarunsu kuma da jin daɗi.

12 Amma idan ba su kasa kunne ba,

Za a hallaka su da takobi,

Su mutu jahilai.

13 “Waɗanda ba su da tsoron Allah a zuciyarsu,

Suna tanada wa kansu fushi,

Ba su neman taimako sa’ad da ya ɗaure su.

14 Sukan yi mutuwar ƙuruciya,

Sukan ƙare kwanakinsu da kunya.

15 Zai kuɓutar da waɗanda suke shan tsanani,

Ta wurin tsananin da suke sha,

Yakan buɗe kunnuwansu ta wurin shan wahala.

16 Allah ya tsamo ka daga cikin wahala,

Ya kawo ka yalwataccen wuri inda ba matsi,

Abincin da aka yi na addaras aka jera maka a kan tebur.

17 “Ka damu ƙwarai don ka ga an hukunta mugaye,

Amma hukunci da adalci sun kama ka.

18 Ka lura kada ka bar hasalarka ta sa ka raina Allah,

Kada kuma ka bar wahalar da kake sha ta sa ka ɓata da mai fansarka.

19 Kukanka ya iya raba ka da wahala,

Ko kuwa dukan ƙarfin da kake da shi?

20 Kada ka ƙosa dare ya yi,

Domin a lokacin nan ne mutane sukan watse,

Kowa ya kama gabansa.

21 Ka lura kada ka rinjayu a kan aikata mugunta,

Gama saboda haka kake shan wannan tsanani,

Don a tsare ka daga aikata mugunta.

22 “Duba, Allah Maɗaukaki ne cikin ikonsa,

Wa ya iya koyarwa kamarsa?

23 Ba wanda zai iya tsara wa Allah abin da zai yi,

Wa ya isa ya ce masa ya yi kuskure?

24 “Ka tuna ka girmama aikinsa,

Wanda mutane suke yabo.

25 Dukan mutane sun ga ayyukansa,

Sun hango shi daga nesa.

26 Ga shi kuwa, Allah Maɗaukaki ne,

Ba mu kuwa san iyakar ɗaukakarsa ba,

Yawan shekarunsa ba su bincikuwa.

27 “Allah yakan sa ruwa ya zama tururi,

Ya maishe shi ruwan sama,

28 Wanda yakan kwararo daga sama,

Ya zubo wa ɗan adam a yalwace.

29 Wa zai iya gane yadda gizagizai suke shimfiɗe a sararin sama,

Da tsawar da ake yi a cikinsu?

30 Ga shi, yakan baza waƙiya kewaye da shi,

Yakan rufe ƙwanƙolin duwatsu.

Zurfin teku yana nan da duhunsa.

31 Gama ta haka yakan shara’anta mutane,

Yakan ba da abinci a yalwace.

32 Ya cika hannunsa da walƙiya,

Yakan sa ta faɗa a kan abin da ya bārata.

33 Tsawarta tana nuna kasancewar Allah,

Ko shanu sun san da zuwan hadiri.”

Categories
AYU

AYU 37

1 “Saboda wannan zuciyata takan kaɗu,

Kamar ta yi tsalle daga inda take.

2 Ku kasa kunne ga tsawar muryarsa,

Ku saurara ga maganarsa mai ƙarfi.

3 Yakan sako ta a ƙarƙashin samaniya duka,

Walƙiyarsa takan zagaya dukan kusurwoyin duniya.

4 Bayan walƙiyar akan ji rugugin muryarsa,

Ya yi tsawa da muryarsa ta ɗaukaka,

Ko da yake an ji muryarsa bai dakatar da tsawar ba.

5 Muryar tsawar Allah mai banmamaki ce,

Yana aikata manyan abubuwa da suka fi ƙarfin ganewarmu.

6 Yakan umarci dusar ƙanƙara ta fāɗo bisa duniya,

Yayyafi da ruwan sama kuwa su yi ƙarfi.

7 Yakan tsai da kowane mutum daga aikinsa,

Domin dukan mutane su san aikinsa.

8 Namomin jeji sukan shiga wurin kwanciyarsu,

Su yi zamansu a ciki.

9 Guguwa takan taso daga inda take,

Sanyi kuma daga cikin iska mai hurawa.

10 Numfashin Allah yakan sa ƙanƙara,

Yakan sa manyan ruwaye su daskare farat ɗaya.

11 Yakan cika girgije mai duhu da ruwa,

Gizagizai sukan baza walƙiyarsa.

12 Sukan yi ta kewayawa ta yadda ya bishe su,

Don su cika dukan abin da ya umarce su a duniya da ake zaune a ciki.

13 Allah yakan aiko da ruwan sama ya shayar da duniya,

Saboda tsautawa, ko saboda ƙasa, ko saboda ƙauna.

14 “Ka ji wannan, ya Ayuba,

Tsaya ka tuna da ayyukan Allah masu banmamaki.

15 Koka san yadda Allah yakan ba su umarni,

Ya sa walƙiyar girgijensa ta haskaka?

16 Ko kuma ka san yadda gizagizai suke tsaye daram a sararin sama?

Ayyukan banmamaki na Allah, cikakken masani!

17 Ko ka san abin da yake sa ka jin gumi

Sa’ad da iskar kudu take hurowa?

18 Ka iya yin yadda ya yi,

Kamar yadda ya shimfiɗa sararin sama daram,

Kamar narkakken madubi?

19 Ka koya mana abin da za mu faɗa masa,

Ba za mu iya gabatar da ƙararrakinmu ba, gama mu dolaye ne.

20 A iya faɗa masa, cewa zan yi magana?

Mutum ya taɓa so a haɗiye shi da rai?

21 “A yanzu dai mutane ba su iya duban haske,

Sa’ad da yake haskakawa a sararin sama,

Bayan da iska ta hura ta share gizagizai sarai.

22 Daga arewa wani haske kamar na zinariya ya fito mai banmamaki,

Allah yana saye da ɗaukaka mai bantsoro.

23 Mai Iko Dukka, ya fi ƙarfin ganewarmu,

Shi mai girma ne, da iko, da gaskiya,

Da yalwataccen adalci,

Ba ya garari.

24 Saboda haka mutane suke tsoronsa,

Bai kula da waɗanda suke ɗaukar kansu su masu hikima ba ne.”

Categories
AYU

AYU 38

Ubangiji Ya Tabbatar da Jahilcin Ayuba

1 Ubangiji ya yi magana da Ayuba ta cikin guguwa.

2 “Wane ne wannan da yake ɓāta shawara

Da maganganu marasa ma’ana?

3 Ka tashi tsaye ka sha ɗamara kamar namiji,

Zan yi maka tambaya, kai kuwa ka ba ni amsa.

4 A ina kake sa’ad da na aza harsashin gina duniya?

Faɗa mini idan ka sani.

5 Wane ne ya zayyana kusurwoyinta?

Hakika ka sani.

Wane ne kuma ya auna ta?

6 A kan me aka kafa tushenta?

Wa ya aza dutsen kan kusurwarta?

7 Sa’ad da taurarin asuba suka raira waƙa tare,

Sai mala’iku duka suka yi sowa saboda murna.

8 “Wa ya yi wa teku iyaka

Sa’ad da ta tumbatso daga zurfafa?

9 Sa’ad da na suturta ta da gizagizai,

Na yi mata maɗauri da duhu ƙirin.

10 Na sa mata iyakoki,

Na sa mata ƙyamare da ƙofofi,

11 Na ce mata, ‘Iyakar inda za ki tsaya ke nan,

Ba za ki wuce ba.

Nan raƙuman ruwanki masu tumbatsa za su tsaya.’

12 “Ayuba, a dukan kwanakinka

Ka taɓa umartar wayewar gari,

Ko ka sa alfijir ya keto?

13 Da gari ya waye,

Ka kawar da muguntar da ake yi da dare?

14 Yakan sāke kamar lakar da take ƙarƙashin hatimi,

Yakan rine kamar riga.

15 Akan hana wa mugaye haske,

Sa’ad da sukan ɗaga hannuwansu sama akan kakkarya su.

16 “Ko ka taɓa shiga cikin maɓuɓɓugan teku?

Ka taɓa yin tafiya a cikin zurfin lallokin teku?

17 An taɓa nuna maka ƙofofin mutuwa?

Ko kuwa ka taɓa ganin ƙofofin duhu ƙirin?

18 Ko ka san iyakar fāɗin duniya?

Ka amsa mini in ka san dukan waɗannan.

19 “Ina hanya zuwa wurin da haske yake?

A ina kuma duhu yake?

20 Ka san iyakarsa ko mafarinsa?

21 Ka sani, gama a lokacin nan an haife ka,

Shekarunka kuwa suna da yawa.

22 “Ka taɓa shiga rumbunan dusar ƙanƙara?

Ko kuwa ka taɓa shiga rumbunan ajiyar ƙanƙara?

23 Na adana su ne don lokacin wahala,

Domin ranar faɗa da ta yaƙi.

24 Ina hanya zuwa inda rana take fitowa,

Ko kuma ta inda iskar gabas take hurowa ta māmaye ko’ina?

25 “Wa ya haƙa hanyar da ruwan sama mai kwararowa zai bi?

Da kuma hanyar da gatarin aradu zai bi?

26 Wa ya kuma kawo ruwan sama a ƙasar da ba mutane,

Da a cikin hamada inda ba kowa,

27 Don a shayar da zozayar ƙasa inda ba kowa,

Har ta tsiro da ciyayi?

28 “Ruwan sama yana da mahaifi?

Wa ya haifi ɗiɗɗigar raɓa?

29 Wace ce mahaifiyar ƙanƙara?

Wace ce kuma ta haifi jaura?

30 Ruwa ya daskare ya yi ƙarfi kamar dutse,

Teku ta daskare.

31 “Za ka iya ɗaure sarƙoƙin kaza-da-‘ya’yanta?

Ko ka iya kwance igiyoyin mafarauci-da-kare-da-zomo?

32 Za ka iya bi da yaneyanen sararin sama bisa ga fasalinsu?

33 Ka san ka’idodin sammai?

Ko ka iya faɗar yadda suka danganta da duniya?

34 “Kana iya yi wa gizagizai tsawa,

Don su kwararo ruwan sama, ya rufe ka?

35 Ka iya aikar walƙiyoyi su tafi,

Sa’an nan su ce maka, ‘Ga mu mun zo?’

36 Wa ya sa hikima a gizagizai,

Ko kuma wa ya ba da ganewa ga kāsashi?

37 Akwai mai hikimar da zai iya ƙidaya gizagizai?

Ko kuwa wa zai iya karkato da salkunan ruwan sammai,

38 Sa’ad da ƙura ta murtuke ta taru jingim, ta game kam?

39 “Ka iya farauto wa zakoki abinci?

Ko ka ƙosar da yunwar sagarun zakoki,

40 Sa’ad da suke fako a kogwanninsu,

Ko suna kwance suna jira a maɓoyarsu?

41 Wa yake tanada wa hankaka abincinsa,

Sa’ad da ‘ya’yansa suke kuka ga Allah,

Suna kai da kawowa saboda rashin abinci?”

Categories
AYU

AYU 39

1 “Ka san lokacin da awakan dutse suke haihuwa?

Ka taɓa lura da yadda batsiya take haihuwa?

2 Ka san ko watanni nawa suke yi kafin su haihu?

Ka san lokacin haihuwarsu?

3 Ka san lokacin naƙudarsu, sa’ad da suke haihuwar ‘ya’yansu,

Lokacin da ‘ya’yansu suke fita cikinsu?

4 ‘Ya’yansu sukan yi ƙarfi su girma a fili cikin saura,

Sukan yi tafiyarsu ba su komawa wurin iyayensu.

5 “Wa ya bar jakin jeji ya yi yadda yake so?

Wa ya ɓalle dabaibayin jaki mai sauri,

6 Wanda na ba fili fetal ya zama gidansa,

Da ƙasa mai gishiri a wurin zamansa?

7 Yakan yi wa hayaniyar birane ba’a,

Ba ruwansa da tsawar masu kora.

8 Tsaunukan duwatsu ne wurin kiwonsa,

A can yake neman kowane ɗanyen abu.

9 “Kutunkun ɓauna zai yarda ya yi maka aiki?

Zai yarda ya kwana ɗaya a dangwalinka?

10 Ka iya ɗaure shi da igiya a kwarin kunya?

Ko kuwa zai yi maka kaftu a fadamarka?

11 Za ka dogara gare shi saboda tsananin ƙarfinsa?

Za ka kuma bar masa aikinka?

12 Ka gaskata zai komo,

Ya kawo maka hatsi a masussukarka?

13 “Jimina takan karkaɗa fikafikanta da alfarma!

Amma ba su ne gashin fikafikan ƙauna ba.

14 Jimina takan bar wa ƙasa ƙwayayenta,

Ta bar ƙasa ta ɗumama su.

15 Takan manta wani ya iya taka su su fashe,

Ya yiwu kuma wani naman jeji ya tattake su.

16 Takan yi wa ‘ya’yanta mugunta,

Sai ka ce ba nata ba ne,

Ko da yake ta sha wahala a banza,

Duk da haka ba ta damu ba.

17 Gama Allah bai ba ta hikima ba,

Bai kuwa ba ta fahimi ba.

18 Amma sa’ad da ta sheƙa a guje,

Takan yi wa doki maguji da mahayinsa dariya.

19 “Kai ka yi wa doki ƙarfinsa?

Kai ne kuma ka daje wuyansa da geza?

20 Kai ne ka sa shi tsalle kamar ɗango?

Kwarjinin firjinsa yana da bantsoro.

21 Yakan yi nishi a fadama,

Yana murna saboda ƙarfinsa,

A wurin yaƙi ba ya ja da baya, ba ya jin tsoron kibau.

22 Tsoro abin dariya ne a gare shi, bai damu ba.

Ba ya ba da baya ga takobi,

23 Kibau na ta shillo a kansa,

Māsu suna ta gilmawa a gabansa.

24 Da tsananin fushi da hasala yana kartar ƙasa,

Da jin ƙarar ƙaho, sai ya yi ta zabura.

25 Sa’ad da aka busa ƙaho yana ce, ‘Madalla.’

Yakan ji warin yaƙi daga nesa, da hargowar sarakunan yaƙi da ihunsu.

26 “Ta wurin hikimarka ne shirwa take tashi,

Ta buɗe fikafikanta ta nufi kudu?

27 Ta wurin umarninka ne gaggafa take tashi sama

Ta yi sheƙarta can ƙwanƙoli?

28 A kan dutse take zaune, a can take gidanta,

Cikin ruƙuƙin duwatsu.

29 Daga can takan tsinkayi abincinta

Idanunta sukan hango shi tun daga nesa.

30 ‘Yayanta sukan tsotsi jini,

A inda kisassu suke, can take.”

Categories
AYU

AYU 40

1 Ubangiji ya yi wa Ayuba magana.

2 “Mai neman sa wa wani laifi ya jā da Mai Iko Dukka?

Wanda yake gardama da Allah, bari ya ba da amsa.”

3 Ayuba ya amsa wa Ubangiji ya ce,

4 “Ai, ni ba a bakin kome nake ba,

Wace amsa zan ba ka?

Na rufe bakina na yi gam.

5 Ai, na riga na yi magana sau ɗaya, har ma sau biyu,

Ba zan amsa ba, ba zan ƙara cewa kome ba.”

Bayyanuwar Ikon Allah

6 Sa’an nan Ubangiji ya amsa wa Ayuba daga cikin guguwa, ya ce,

7 “Tashi tsaye ka sha ɗamara kamar namiji,

Zan yi maka tambaya, kai kuwa ka ba ni amsa.

8 Kai kanka za ka sa mini laifi?

Za ka kā da ni don kai ka barata?

9 Kana da ƙarfi kamar na Allah?

Kana iya tsawa da murya kamar tasa?

10 “Ka caɓa ado da kwarjini da ɗaukaka,

Ka yafa daraja da maƙami.

11 Ka kwararar da rigyawar fushinka,

Ka dubi dukan wanda yake alfarma, a wulakance.

12 Ka dubi dukan wanda yake alfarma ka ƙasƙantar da shi,

Ka tattake mugaye a inda suke.

13 Dukansu ka binne su a ƙasa,

Ka ɗaure fuskokinsu, ka jefa su a lahira.

14 Sa’an nan ni kaina kuma zan sanar da kai,

Cewa da hannun damanka za ka yi nasara.

15 “Ga dorina wanda ni na halicce ta,

Kamar yadda na halicce ka,

Tana cin ciyawa kamar sa.

16 Ga shi, ƙarfinta yana cikin ƙugunta,

Ikonta yana cikin tsakar cikinta.

17 Na yi mata wutsiya miƙaƙƙiya, mai ƙarfi kamar itacen al’ul,

Jijiyoyin cinyoyinta suna haɗe wuri ɗaya

18 Ƙasusuwanta bututun tagulla ne,

Gaɓoɓinta kamar sandunan ƙarfe ne.

19 “Ita ce ta farko cikin ayyukan Allah,

Sai Mahaliccinta kaɗai yake iya tunkararta da takobi!

20 Gama duwatsu suke ba ta abinci,

A inda dukan namomin jeji suke wasa.

21 Takan kwanta a inuwar ƙaddaji,

Ta ɓuya a cikin iwa, da a fadama.

22 Gama inuwar da take rufe ta ta ƙaddaji ce,

Itatuwan wardi na rafi, sun kewaye ta.

23 Ga shi, ba ta jin tsoron tumbatsar kogi,

A natse take, ko da ta bakinta rigyawar Urdun take wucewa.

24 Akwai wanda zai iya kama ta da ƙugiya,

Ko ya sa mata asirka?”

Categories
AYU

AYU 41

1 “Ka iya kama dodon ruwa da ƙugiyar kama kifi?

Ko kuma ka iya zarge harshensa da igiya?

2 Ka iya sa wa hancinsa asirka?

Ko ka iya huda muƙamuƙinsa da ƙugiya?

3 Zai ta yi maka godo?

Zai yi maka magana da tattausar murya?

4 Zai ƙulla alkawari da kai,

Cewa zai zama baranka har abada?

5 Za ka yi wasa da shi kamar yadda za ka yi da tsuntsu?

Ko za ka ɗaure shi da tsarkiya domin barorinka mata?

6 ‘Yan kasuwa za su saye shi?

Za su karkasa shi ga fatake?

7 Za ka iya huhhuda fatarsa da zaguna?

Ko kuwa kansa da māsu?

8 In ka kama shi, ka daɗe kana tunawa da yaƙin da ba za ka ƙara marmarin yi ba!

9 Ba ma amfani a yi ƙoƙarin kama shi,

Tunanin yin haka ma abin tsoro ne.

10 Ba wani mai zafin hali da zai kuskura ya tsokane shi.

Wane ne wannan da zai iya tsayawa a gabana?

11 Wa ya ba ni har da zan biya shi?

Dukan abin da yake cikin duniyan nan nawa ne.

12 “Ba zan yi shiru a kan zancen gaɓoɓinsa ba,

Ko babban ƙarfinsa, ko kyan ƙirarsa.

13 Wa zai iya yaga babbar rigarsa?

Ko kuwa ya kware sulkensa da aka ninka biyu?

14 Wa zai iya buɗe leɓunansa?

Gama haƙoransa masu bantsoro ne.

15 An yi gadon bayansa da jerin garkuwoyi ne,

An haɗa su daɓa-daɓa kamar an liƙe.

16 Suna haɗe da juna gam,

Ko iska ba ta iya ratsa tsakaninsu.

17 Sun manne da juna har ba su rabuwa.

18 Atishawarsa takan walƙata walƙiya,

Idanunsa kuma kamar ketowar alfijir.

19 Harsunan wuta kamar jiniya suna fitowa daga bakinsa,

Tartsatsin wuta suna ta fitowa.

20 Hayaƙi na fita daga hancinsa

Kamar tururi daga tukunya mai tafasa,

Ko bāgar da ta kama wuta.

21 Numfashinsa yakan kunna gawayi,

Harshen wuta yana fita daga bakinsa.

22 A wuyansa ƙarfi yake zaune,

Razana tana rausaya a gabansa.

23 Namansa yana ninke, manne da juna,

Gama ba ya motsi.

24 Zuciyarsa tana da ƙarfi kamar dutse,

Ƙaƙƙarfa kamar dutsen niƙa.

25 Sa’ad da ya miƙe tsaye, ƙarfafa sukan tsorata,

Su yi ta tutturmushe juna.

26 Ko an sare shi da takobi,

Ko an nashe shi da māshi ko hargi, ko an jefe shi,

Ba sa yi masa kome.

27 Kamar ciyawa baƙin ƙarfe yake a gare shi,

Tagulla ma kamar ruɓaɓɓen itace take.

28 Kibiya ba za ta sa ya gudu ba,

Jifar majajjawa a gare shi kamar jifa da tushiyoyi ce.

29 A gare shi kulake kamar tushiyoyi ne,

Kwaranniyar karugga takan ba shi dariya.

30 Kaifin ƙamborin cikinsa kamar tsingaro ne.

Yana jan ciki a cikin laka kamar lular ƙarfe.

31 Yakansa zurfafa su tafasa kamar tukunya,

Teku kuwa kamar kwalabar man shafawarsa.

32 Idan yana wucewa sai a ga hasken dārewar ruwa,

Yakansa zurfafa su yi kumfa.

33 A duniya ba kamarsa,

Taliki ne wanda ba shi da tsoro.

34 Yakan dubi kowane abu da yake mai alfarma,

Shi sarki ne a bisa dukan masu girmankai.”

Categories
AYU

AYU 42

Ayuba Ya Tuba aka kuma Karɓe Shi

1 Ayuba ya amsa wa Ubangiji.

2 “Na sani kai kake da ikon yin dukan abu,

Ba wanda ya isa ya hana ka yin abin da ka nufa.

3 Wane ne wannan marar ilimi da zai ɓoye shawara?

Saboda haka na hurta abin da ban gane ba,

Abubuwa waɗanda ban gane ba suna banmamaki ƙwarai.

4 Ka ce, ‘Kasa kunne, zan yi magana da kai,

Zan yi maka tambaya, ka ba ni amsa.’

5 Dā jin labarinka nake,

Amma yanzu na gan ka ido da ido.

6 Saboda haka na ga ni ba kome ba ne,

Na tuba, ina hurwa da ƙura da toka.”

Ƙarshen Magana

7 Bayan da Ubangiji ya gama faɗa wa Ayuba waɗannan magana, sai ya ce wa Elifaz, mutumin Teman, “Ina fushi da kai da abokan nan naka biyu, gama ba ku faɗi gaskiya game da ni ba, kamar yadda bawana Ayuba ya yi.

8 Yanzu fa, sai ku kama bijimai bakwai da raguna bakwai, ku kai wa Ayuba, ku miƙa su hadaya ta ƙonawa domin kanku. Ayuba zai yi addu’a dominku, ni kuwa zan amsa addu’arsa don kada in sāka muku bisa ga wautarku. Gama ba ku faɗi gaskiya game da ni ba, kamar yadda bawana Ayuba ya yi.”

9 Sai Elifaz mutumin Teman, da Bildad mutumin Shuwa, da Zofar mutumin Na’ama suka tafi suka yi kamar yadda Ubangiji ya faɗa musu, Ubangiji kuwa ya karɓi addu’ar Ayuba.

Allah Ya Mayar wa Ayuba da Wadatarsa

10 Ubangiji kuwa ya mayar wa Ayuba da dukiyarsa, sa’ad da ya yi addu’a domin abokansa, sai Ubangiji ya mayar masa da riɓin abin da yake da shi dā.

11 Sa’an nan dukan ‘yan’uwan Ayuba mata da maza da dukan waɗanda suka san shi a dā, suka zo gidansa suka ci abinci tare da shi, suka yi juyayin abin da ya same shi, suka ta’azantar da shi,saboda dukan wahalar da Ubangiji ya aukar masa. Kowannensu ya ba shi ‘yan kuɗi da zoben zinariya.

12 Ubangiji ya sa wa wannan zamani na Ayuba albarka, har fiye da na farko. An ba shi tumaki dubu goma sha huɗu (14,000), da raƙuma dubu shida (6,000), da takarkari dubu biyu (2,000), da jakai mata dubu ɗaya (1,000).

13 Ya kuma haifi ‘ya’ya maza bakwai, mata uku.

14 Ya raɗa wa ta farin suna Yemima, da ta biyun Keziya,da ta ukun Keren-Haffuk.

15 Duk ƙasar ba ‘yan mata kyawawa kamar ‘ya’yan Ayuba. Mahaifinsu kuwa ya ba su gādo tare da ‘yan’uwansu maza.

16 Ayuba ya rayu shekara ɗari da arba’in bayan wannan, ya ga ‘ya’yansa, ya ga jikokin jikokinsa har tsara ta huɗu.

17 Sa’an nan Ayuba ya rasu da kyakkyawan tsufa.

Categories
ZAB

ZAB 1

Farin Ciki na Gaskiya

1 Albarka ta tabbata ga mutumin da

Ba ya karɓar shawarar mugaye,

Wanda ba ya bin al’amuran masu zunubi,

Ko ya haɗa kai da masu wasa da Allah.

2 Maimakon haka, yana jin daɗin karanta shari’ar Allah,

Yana ta nazarinta dare da rana.

3 Yana kama da itacen da yake a gefen ƙorama,

Yakan ba da ‘ya’ya a kan kari,

Ganyayensa ba sa yin yaushi,

Yakan yi nasara a dukan abin da yake yi.

4 Amma mugaye ba haka suke ba,

Su kamar yayi suke wanda iska take kwashewa.

5 Allah kuwa zai hukunta mugaye,

Masu zunubi kuwa za a ware su daga adalai.

6 Gama Ubangiji yana lura da al’amuran adalai,

Amma al’amuran mugaye za su watse.

Categories
ZAB

ZAB 2

Mulkin Sarkin da Ubangiji Ya Zaɓa

1 Don me al’ummai suke shirin tayarwa?

Don me waɗannan mutane suke ƙulla shawarwarin banza?

2 Sarakunan duniya sun yi tayarwa,

Masu mulkinsu suna shirya maƙarƙashiya tare,

Gāba da Ubangiji da zaɓaɓɓen sarkinsa.

3 Suna cewa, “Bari mu ‘yantar da kanmu daga mulkinsu,

Bari mu fice daga ƙarƙashinsu!”

4 Ubangiji ya yi dariya daga kan kursiyinsa can Sama,

Ya mai da su abin dariya.

5 Ya yi musu magana da fushi,

Ya razanar da su da hasalarsa,

6 Ya ce, “A bisa Sihiyona, dutsena tsattsarka,

Na naɗa sarkina.”

7 Sarkin ya ce, “Zan yi shelar abin da Ubangiji ya hurta.

Ubangiji ya ce mini, ‘Kai ɗana ne,

Yau ne na zama mahaifinka.

8 Ka yi roƙo, zan kuwa ba ka dukan al’ummai,

Dukan duniya kuma za ta zama taka.

9 Za ka mallake su da sandan ƙarfe,

Za ka farfashe su kamar tukunyar yumɓu.’ ”

10 Yanzu ku kasa kunne gare ni, ku sarakuna,

Ku mai da hankali, ku mahukunta!

11 Ku bauta wa Ubangiji da tsoro,

Ku yi rawar jiki, ku rusuna masa,

12 Ku yi mubaya’a da Ɗan,

Idan kuwa ba haka ba zai yi fushi da ku, za ku kuwa mutu,

Gama yakan yi fushi da sauri.

Albarka ta tabbata ga dukan masu zuwa gare shi neman mafaka!