Categories
ZAB

ZAB 43

Addu’ar Wanda Aka Kai Baƙuwar Ƙasa ala Tilas

1 Ya Allah, ka kuɓutar da ni,

Ka kiyaye al’amarina daga marasa tsoronka,

Ka cece ni daga ƙaryar mugaye!

2 Ya Allah, kai ne kake kāre ni,

Me ya sa ka yashe ni?

Me ya sa nake ta shan wahala saboda muguntar maƙiyana?

3 Ka aiko da haskenka, da gaskiyarka,

Bari su bishe ni,

Su kawo ni Sihiyona, tsattsarkan tudunka,

Su kawo ni Haikalinka, inda zatinka yake!

4 Sa’an nan zan tafi wurin bagadenka, ya Allah,

Zuwa gare ka, kai wanda kake sa ni in yi murna da farin ciki,

In raira waƙar yabo a gare ka da garayata,

Ya Allah, Allahna!

5 Me ya sa nake baƙin ciki?

Me ya sa nake damuwa?

Zan dogara ga Allah,

Zan ƙara yabonsa,

Mai Cetona, Allahna.

Categories
ZAB

ZAB 44

Addu’ar Neman Ceto

1 Da kunnuwanmu muka ji, ya Allah,

Kakanninmu suka faɗa mana,

Manya manyan abubuwa da ka aikata a lokacinsu,

A zamanin dā,

2 Yadda kai da kanka ka kori arna,

Ka dasa jama’arka a ƙasarsu,

Yadda ka hori sauran al’umma,

Amma ka sa jama’arka su wadata.

3 Ba da takubansu suka ci ƙasar ba,

Ba kuwa da ikonsu suka rinjayi ƙasar ba,

Amma da ikonka ne da kuma ƙarfinka,

Ta wurin tabbatar musu kana tare da su,

Kana nuna musu kana ƙaunarsu.

4 “Ya Allah, kai ne Sarkina,

Ka ba jama’arka nasara.

5 Da ikonka muka kori abokan gābanmu,

Saboda kasancewarka tare da mu

Muka rinjayi magabtanmu.

6 Ban dogara ga bakana ba,

Takobina kuwa ba zai cece ni ba.

7 Amma ka cece mu daga abokan gābanmu,

Ka kori waɗanda suke ƙinmu.

8 Za mu yabe ka kullum,

Mu yi maka godiya har abada.”

9 Amma yanzu, ya Allah, ka yashe mu,

Ka bari aka kore mu,

Ba ka ƙara fita ka yi tafiya tare da sojojinmu ba.

10 Ka sa muka gudu daga gaban abokan gābanmu,

Suka ƙwace abin da muke da shi.

11 Ka bari aka yanyanka mu kamar tumaki,

Ka warwatsar da mu a baƙuwar ƙasa.

12 Ka sayar da jama’arka

A bakin ‘yan kuɗi ƙalilan,

Ba ka ci ribar cinikin ba.

13 Maƙwabtanmu suna yi mana dariya saboda kai,

Suna yi mana ba’a, sun maishe mu abin wasa.

14 Ka maishe mu abin raini a wurin arna,

Suna kaɗa mana kai, suna raina mu.

15 Kullum a cikin kunya nake,

Kunya ta lulluɓe ni ɗungum,

16 Saboda dukan wulakanci,

Da zagin da nake sha daga maƙiyana da abokan gābana.

17 Dukan wannan ya same mu,

Ko da yake ba mu manta da kai ba,

Ba mu kuma ta da alkawarin da ka yi da mu ba.

18 Ba mu ci amanarka ba,

Ba mu ƙi yin biyayya da umarnanka ba.

19 Duk da haka ka ƙi taimakonmu da namomin jejin nan,

Ka bar mu a cikin duhu baƙi ƙirin.

20 Da a ce mun daina yin sujada ga Allahnmu,

Muka yi addu’a ga gumaka,

21 Hakika ka gane,

Domin ka san asirin tunanin mutane.

22 Ya Allah, saboda kai ne ake karkashe mu a kowane lokaci,

Ake kuma maishe mu kamar tumakin da za a yanyanka.

23 Ka tashi, ya Ubangiji! Me ya sa kake zama kamar mai barci?

Ka tashi! Kada ka yashe mu har abada!

24 Me ya sa ka ɓuya mana?

Kada ka manta da ƙuncinmu da wahalarmu!

25 Mun fāɗi, an turmushe mu a ƙasa,

An bar mu kwance cikin ƙura.

26 Ka tashi ka taimake mu!

Ka fanshe mu saboda madawwamiyar ƙaunarka!

Categories
ZAB

ZAB 45

Waƙar Ɗaurin Auren Sarki

1 Kwanyata ta cika da kyawawan kalmomi,

Lokacin da nake tsara waƙar sarki,

Harshena kuwa kamar alkalami ne na ƙwararren marubuci.

2 Kai ne mafi kyau a cikin dukan mutane,

Kai mai kyakkyawan lafazi ne,

Kullum Allah yakan sa maka albarka!

3 Ka sha ɗamara da takobinka, ya Maɗaukakin Sarki,

Kai mai iko ne, Maɗaukaki!

4 Ka yi hawan ɗaukaka zuwa nasara,

Domin ka tsare gaskiya da adalci.

Saboda ikonka za ka yi babban rinjaye.

5 Kibanka suna da tsini,

Suna huda zuciyar abokan gābanka,

Al’ummai suna fāɗuwa ƙasa a ƙafafunka.

6 Kursiyinka, ya Allah, zai dawwama har abada abadin!

Kana mulkin mallakarka da adalci.

7 Kana ƙaunar abin da yake daidai,

Kana ƙin abin da yake mugu.

Saboda haka Allah, Allahnka, ya zaɓe ka,

Ya kuwa kwararo maka farin ciki mai yawa fiye da kowa.

8 Tufafinka suna ƙanshin turaren mur, da na aloyes, da na kashiya,

A kowace fādar hauren giwa, mawaƙa suna yi maka waƙar.

9 Daga cikin matan da suke fadarka, har da ‘ya’yan sarakuna.

A daman kursiyinka kuwa ga sarauniya a tsaye.

Tana saye da kayan ado na zinariya mafi kyau duka.

10 Ki ji abin da zan faɗa, ya ke amaryar sarki,

Ki manta da mutanenki da danginki.

11 Saboda ke kyakkyawa ce sarki zai so ki,

Shi ne maigidanki, sai ki yi masa biyayya.

12 Mutanen Taya za su kawo miki kyautai,

Attajirai za su zo su sami farin jini a gare ki.

13 Gimbiya tana fāda, kyakkyawa ce ainun,

Da zaren zinariya aka saƙa rigarta,

14 Aka kai ta wurin sarki tana saye da riga mai ado.

Ga ‘yan matanta a biye,

Aka kawo su wurin sarki.

15 Da farin ciki da murna suka zo,

Suka shiga fādar sarki.

16 Za ka haifi ‘ya’ya maza da yawa,

Waɗanda za su maye matsayin kakanninka,

Za ka sa su zama masu mulkin duniya duka.

17 Waƙata za ta sa a yi ta tunawa da sunanka har abada,

Dukan jama’a za su yabe ka a dukan zamanai masu zuwa.

Categories
ZAB

ZAB 46

Allah ne Mafakarmu da Ƙarfinmu

1 Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu,

Kullum a shirye yake yă yi taimako a lokacin wahala.

2 Saboda haka ba za mu ji tsoro ba,

Ko da duniya za ta girgiza,

Duwatsu kuma su fāɗa cikin zurfafan teku,

3 Ko da a ce tekuna za su yi ruri su tumbatsa,

Tuddai kuma su girgiza saboda tangaɗin tekun.

4 Akwai kogin da yake kawo farin ciki a birnin Allah,

Da cikin tsattsarkan Haikali na Maɗaukaki.

5 Allah yana zaune cikin birnin,

Ba kuwa za a hallaka birnin ba, faufau.

Da asuba Allah zai kawo musu gudunmawa.

6 An kaɓantar da sauran al’umma, mulkoki suka girgiza,

Allah ya yi tsawa, duniya kuwa ta narke.

7 Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu,

Allah na Yakubu shi ne mafakarmu!

8 Zo ku ga abin da Ubangiji ya yi!

Dubi irin ayyukan al’ajabi da ya yi a duniya!

9 Ya hana yaƙoƙi ko’ina a duniya,

Yana karya bakkuna, yana lalatar da māsu,

Yana ƙone karusai da wuta.

10 Ya ce, “Ku yi shiru, ku sani ni ne Allah,

Maɗaukaki ne cikin sauran al’umma,

Maɗaukaki kuma a duniya!”

11 Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu,

Allah na Yakubu shi ne mafakarmu!

Categories
ZAB

ZAB 47

Allah ne Mai Mulkin Duka

1 Ku yi tāfi saboda farin ciki,

Ya ku jama’a duka!

Ku raira waƙoƙi da karfi, ku yabi Allah!

2 A ji tsoron Ubangiji Mai Iko Dukka,

Shi babban Sarki ne, ya mallaki dukan duniya.

3 Ya ba mu nasara a bisa jama’o’i,

Ya sa muka yi mulkin al’ummai,

4 Ya zaɓar mana ƙasar da muke zaune,

Wadda take mallaka ce ta fāriya, ta jama’arsa

Wadda yake ƙauna.

5 Allah ya hau kan kursiyinsa!

Aka yi ta sowa ta murna, ana ta busa ƙahoni,

Lokacin da Ubangiji yake hawa!

6 Ku raira yabbai ga Allah,

Ku raira yabbai ga sarkinmu!

7 Allah sarki ne na duniya duka,

Ku yabe shi da waƙoƙi!

8 Allah yana zaune kan kursiyinsa mai tsarki,

Yana mulkin al’ummai,

9 Masu mulkin al’ummai suka tattaru

Tare da jama’ar Allah na Ibrahim.

Allah shi ne garkuwar jarumawa,

Yana mulkin duka!

Categories
ZAB

ZAB 48

Sihiyona Mai Daraja, Birnin Allah

1 Ubangiji mai girma ne,

Dole kuwa a yabe shi da girmamawa a birnin Allahnmu,

A kan tsattsarkan dutsensa.

2 Dutsen Sihiyona, dutse mai tsawo,

Mai kyan gani ne na Allah,

Birnin babban Sarki.

Yakan kawo farin ciki ga dukan duniya!

3 Allah ya nuna akwai zaman lafiya a wurinsa,

A kagarar birnin.

4 Sarakuna suka tattaru,

Suka zo Dutsen Sihiyona,

5 Da suka gan shi sai suka yi mamaki,

Suka tsorata suka gudu.

6 Tsoro ya kama su suka razana,

Kamar mace wadda take gab da haihuwa.

7 Allah yakan hallaka manyan jiragen ruwa da iskar gabas.

8 Mun ji labarin waɗannan al’amura,

Yanzu kuwa mun gan su

A birnin Allahnmu, Mai Runduna,

Zai kiyaye birnin lafiya har abada.

9 A cikin Haikalinka, ya Allah,

Muna tunanin madawwamiyar ƙaunarka.

10 A ko’ina jama’a suna yabonka,

Sunanka ya game duniya duka.

Kana mulki da adalci.

11 Bari jama’ar Sihiyona su yi murna!

Gama kana shari’a ta gaskiya,

Bari biranen Yahuza su yi farin ciki.

12 Ku tafi ku kewaye Dutsen Sihiyona,

Ku ƙirga yawan hasumiyarsa.

13 Ku lura da garukanta, ku bincike kagaranta,

Saboda ku iya faɗa wa tsara mai zuwa,

14 Cewa wannan Allah shi ne Allahnmu har abada abadin,

Shi ne zai bishe mu a dukan zamanai masu zuwa.

Categories
ZAB

ZAB 49

Dogara ga Dukiya Wauta Ce

1 Ku ji wannan, ko wannenku,

Ku saurara jama’a duka na ko’ina,

2 Da manya da ƙanana duka ɗaya,

Da attajirai da matalauta baki ɗaya.

3 Zan yi magana da hikima,

Zan yi tunani mai ma’ana.

4 Zan mai da hankalina ga ka-cici-ka-cici,

In bayyana ma’anarsa sa’ad da nake kaɗa molo.

5 Don me zan ji tsoro a lokacin hatsari,

Sa’ad da mugaye suka kewaye ni,

6 Mutanen da suke dogara ga dukiyarsu,

Waɗanda suke fariya saboda yawan wadatarsu?

7 Har abada mutum ba zai iya fansar wani ba,

Ba kuwa zai iya biyan kuɗin ransa ga Allah ba.

8 Gama kuɗin biyan ran mutum ba shi da iyaka.

Abin da zai iya biya, sam ba zai isa ba,

9 Ba kuwa zai rayar da shi,

Ko ya hana shi mutuwa har abada ba.

10 Yakan sa masu hikima su ma su mutu,

Haka nan ma wawaye da mutanen banza,

Za su mutu su bar dukiyarsu ga zuriyarsu.

11 Kaburburansu za su zama gidajensu har abada,

Can za su kasance kullum,

Ko da yake a dā suna da ƙasa ta kansu.

12 Girman mutum ba zai hana shi mutuwa ba,

Zai mutu kamar dabba.

13 Dubi abin da zai faru ga waɗanda suke dogara ga kansu,

Da irin ƙaddarar waɗanda dukiya ta ishe su.

14 Za a ƙaddara su ga mutuwa kamar tumaki,

Mutuwa ce za ta yi kiwonsu.

Da safe adalai za su ci nasara a kansu,

Sa’ad da gawawwakinsu suke ruɓewa a ƙasar matattu,

Nesa da gidajensu.

15 Amma Allah zai fanshe ni,

Zai ɗauke ni daga ikon mutuwa.

16 Kada ka damu sa’ad da mutum ya zama attajiri,

Ko kuwa dukiyarsa ta ƙasaita,

17 Domin ba zai ɗauke ta a lokacin mutuwarsa ba,

Dukiyarsa ba za ta shiga kabari tare da shi ba.

18 Ko da a ce mutum ya sami falalar wannan rai,

Ana kuwa ta yabonsa saboda nasarar da ya ci,

19 Duk da haka zai tarar da kakanninsa waɗanda suka mutu,

Inda duhu ya dawwama har abada.

20 Girman mutum ba zai hana shi mutuwa ba,

Zai mutu kamar dabba.

Categories
ZAB

ZAB 50

Allah ne Mai Shari’a

1 Allah Maɗaukaki, Ubangiji, ya yi magana,

Yana kiran dukan duniya, daga gabas zuwa yamma.

2 Allah yana haskakawa daga Sihiyona,

Da cikar jamalin Sihiyona.

3 Allahnmu ya zo, ba a ɓoye yake ba,

Wuta mai cinyewa na tafe a gabansa,

Babban hadiri kuwa na kewaye da shi.

4 Ya kira sammai da duniya su zama shaidu,

Su ga yadda yake shara’anta jama’arsa.

5 Ya ce, “Ku tattaro mini amintattuna,

Waɗanda suka cika alkawarin da yake tsakanina da su,

Ta wurin miƙa hadaya.”

6 Sammai suna shelar adalcin Allah,

Domin shi yake yin shari’a!

7 “Ku ji, ya ku jama’ata, zan kuwa yi magana,

Zan ba da shaida gāba da ku, ya Isra’ila.

Ni ne Allah, Allahnku.

8 Ban tsauta muku saboda hadayunku ba,

Ko saboda hadayu na ƙonawa da kuke ta miƙa mini kullum.

9 Ba na bukatar bijimai daga gonakinku,

Ko awaki daga garkunanku.

10 Gama namomin jeji nawa ne,

Dubban shanu da suke kan tuddai kuma nawa ne.

11 Dukan tsuntsayen da suke tashi a sararin sama nawa ne,

Da dukan masu rai da suke ƙasa.

12 “Da ina jin yunwa ba sai na faɗa muku ba,

Gama da duniya da dukan abin da yake cikinta nawa ne.

13 Nakan ci naman bijimai ne?

Ko nakan sha jinin awaki?

14 Bari ku miƙa wa Allah hadayarku ta godiya,

Ku ba Mai Iko Dukka, dukan hadayun da kuka alkawarta.

15 Ku yi kira gare ni sa’ad da wahala ta zo,

Zan cece ku,

Ku kuwa za ku yabe ni.”

16 Amma Allah ya ce wa mugaye,

“Don me za ku haddace umarnaina?

Don me za ku yi magana a kan alkawaraina?

17 Kun ƙi in tsauta muku,

Kun yi watsi da umarnaina.

18 Sa’ad da kuka ga ɓarawo kukan yi abuta da shi.

Kuna haɗa kai da mazinata.

19 “Kullum a shirye kuke ku hurta mugunta,

Ba ku jin nauyin faɗar ƙarya.

20 A shirye kuke ku sari ‘yan’uwanku,

Ku sa musu laifi.

21 Kun aikata waɗannan duka, ni kuwa ban ce kome ba,

Saboda haka kuka zaci ni kamar ku nake.

Amma yanzu zan tsauta muku,

In bayyana muku al’amarin a fili.

22 “Ku ji wannan ku da kuke ƙyale ni,

In ba haka ba zan hallaka ku,

Ba wanda zai cece ku.

23 Wanda yake yin godiya a sa’ad da yake miƙa hadayarsa, yana girmama ni,

Da wanda yake yi mini biyayya kuma, zan nuna masa cetona.”

Categories
ZAB

ZAB 51

Addu’ar Roƙon Gafara

1 Ka yi mini jinƙai, ya Allah,

Sabili da madawwamiyar ƙaunarka.

Ka shafe zunubaina,

Saboda jinƙanka mai girma!

2 Ka wanke muguntata sarai,

Ka tsarkake ni daga zunubina!

3 Na gane laifina,

Kullum ina sane da zunubina.

4 Na yi maka zunubi, kai kaɗai na yi wa,

Na kuwa aikata mugunta a gare ka.

Daidai ne shari’ar da ka yi mini,

Daidai ne ka hukunta ni.

5 Mugu ne ni tun lokacin da aka haife ni,

Mai zunubi ne ni tun daga ranar da aka haife ni.

6 Amintacciyar zuciya ita kake so,

Ka cika tunanina da hikimarka.

7 Ka kawar da zunubina, zan kuwa tsarkaka,

Ka wanke ni, zan kuwa fi auduga fari.

8 Bari in ji sowa ta farin ciki da murna.

Ko da yake ka ragargaza ni,

Ka kakkarya ni, duk da haka zan sāke yin murna.

9 Ka kawar da fuskarka daga zunubaina,

Ka shafe duk muguntata.

10 Ka halitta tsarkakakkiyar zuciya a cikina, ya Allah,

Ka sa sabon halin biyayya a cikina.

11 Kada ka kore ni daga gabanka,

Kada ka ɗauke mini Ruhunka Mai Tsarki.

12 Ka sāke mayar mini da farin ciki na cetonka,

Ka ƙarfafa ni da zuciya ta biyayya.

13 Sa’an nan zan koya wa masu zunubi umarnanka,

Za su kuwa komo wurinka.

14 Ka rayar da raina, ya Allah Mai Cetona,

Zan kuwa yi shelar adalcinka da farin ciki.

15 Ka taimake ni in yi magana, ya Ubangiji,

Zan kuwa yabe ka.

16 Ba ka son sadakoki, ai, da na ba ka,

Ba ka jin daɗin hadayun ƙonawa.

17 Hadayata, ita ce halin ladabi, ya Allah,

Zuciya mai ladabi da biyayya,

Ba za ka ƙi ba, ya Allah.

18 Ya Allah, ka yi wa Sihiyona alheri, ka taimake ta,

Ka sāke gina garun Urushalima.

19 Sa’an nan za ka ji daɗin hadaya ta ainihi,

Da dukan hadayun ƙonawa.

Za a miƙa bijimai hadayu a bisa bagadenka.

Categories
ZAB

ZAB 52

Hukuncin Allah da Alherinsa

1 Me ya sa kake fariya da muguntarka,

Ya kai, babban mutum?

Ƙaunar Allah tana nan a koyaushe.

2 Kana shirya maƙarƙashiya don ka lalatar da waɗansu,

Harshenka kamar aska mai kaifi yake.

Kana ƙirƙiro ƙarairayi kullum.

3 Kana ƙaunar mugunta fiye da nagarta,

Kana kuwa ƙaunar faɗar ƙarya fiye da gaskiya.

4 Kana jin daɗin cutar mutane da maganganunka,

Ya kai, maƙaryaci!

5 Don haka Allah zai ɓata ka har abada,

Zai kama ka, yă jawo ka daga alfarwarka,

Zai kawar da kai daga ƙasar masu rai.

6 Adalai za su ga wannan, su ji tsoro,

Za su yi maka dariya, su ce,

7 “Duba, ga mutumin da bai dogara ga Allah

Don ya sami zaman lafiyarsa ba.

A maimakon haka, sai ya dogara ga wadatarsa.

Yana neman zaman lafiyarsa ta wurin muguntarsa.”

8 Amma ni, kamar itacen zaitun nake, wanda yake girma kusa da Haikalin Allah,

Ina dogara ga madawwamiyar ƙaunarsa har abada abadin.

9 Zan gode maka, ya Ubangiji,

Saboda abin da ka aikata.

Zan dogara gare ka,

Sa’ad da nake sujada tare da jama’arka,

Domin kai mai alheri ne.