Categories
K. MAG

K. MAG 13

1 Ɗa mai hikima yakan mai da hankali sa’ad da mahaifinsa yake kwaɓarsa, amma mutum mai girmankai ba ya yarda da kuskurensa.

2 Mutanen kirki za a sāka musu da alheri a kan abin da suke faɗa, amma mayaudara sukan ƙosa su ta da zaune tsaye.

3 Ka lura da irin abin da kake faɗa don ka kiyaye ranka. Mutumin da bai kula da maganarsa ba, yakan hallakar da kansa.

4 Rago yakan ƙosa ya sami wani abu ainun, amma sam, ba zai samu ba. Mai mai da hankali ga aikinsa zai sami kowane abu da yake bukata.

5 Masu aminci suna ƙin ƙarairayi, amma maganganun mugun abin kunya ne da ƙasƙanci.

6 Adalci yakan kiyaye marasa laifi, amma mugunta ita ce fāɗuwar masu zunubi.

7 Waɗansu mutane sukan nuna su attajirai ne, alhali kuwa ba su da kome. Waɗansu kuma sukan nuna su matalauta ne, alhali kuwa suna da dukiya.

8 Kuɗin attajiri suna iya ceton ransa, bai kyautu ba a razana matalauci.

9 Adalai suna kama da haske mai haskakawa ƙwarai, mugaye kuwa suna kamar fitilar da take mutuwa.

10 Fāriya ba ta kawo kome sai wahala. Hikima ce a nemi shawara.

11 Dukiyar da aka same ta a sawwaƙe, za ka rasa ta da sauri, amma wanda ya same ta da wahala, za ta yi ta ƙaruwa.

12 Idan ba bege, sai zuciya ta karai, amma muradin da ya tabbata zai cika ka da sa zuciya.

13 Idan ka ƙi shawara mai kyau wahala kake nemar wa kanka, idan ka bi ta kuwa za ka zauna lafiya.

14 Koyarwar masu hikima maɓuɓɓugar rai ce, za ta taimake ka ka kuɓuta sa’ad da ranka yake cikin hatsari.

15 Basira takan sa a girmama ka, amma mutanen da ba za a iya amincewa da su ba, a kan hanyar hallaka suke.

16 Mutum mai hankali a ko yaushe yakan yi tunani kafin ya aikata, amma wawa yakan tallata jahilcinsa.

17 Manzanni marasa aminci sukan haddasa wahala, amma waɗanda suke amintattu sukan kawo salama.

18 Mutumin da ba zai koya ba, zai talauce ya sha kunya, amma wanda ya kasa kunne ga tsautawa za a girmama shi.

19 Abu mai kyau ne mutum ya sami biyan bukatarsa! Wawaye sukan ƙi barin mugunta.

20 Ka koya daga wurin masu hikima, za ka zama mai hikima. Yi abuta da wawaye, za ka kuwa lalace.

21 Wahala tana bin masu zunubi ko’ina, amma za a sāka wa adalai da kyawawan abubuwa.

22 Mutumin kirki zai sami dukiya, har ya bar wa jikokinsa, amma dukiyar masu zunubi za ta zama ta adalai.

23 Saurukan da ba a aikatawa, za su ba da isasshen abinci ga matalauci, amma mutane marasa gaskiya sukan hana albarka.

24 Idan ba ka horon ɗanka, ba ka ƙaunarsa ke nan, amma idan kana ƙaunarsa za ka riƙa kwaɓarsa.

25 Adalai suna da isasshen abinci, amma mugaye fama suke da yunwa ko yaushe.

Categories
K. MAG

K. MAG 14

1 Hikimar mata takan gina gidaje, amma wauta takan rushe su.

2 Ka yi gaskiya, za ka nuna girmamawarka ga Ubangiji, amma idan ka yi rashin gaskiya, ka nuna rashin girmamawa ke nan ga Ubangiji.

3 Kalmomin mai hikima za su kiyaye shi, amma maganganun wawa za su jawo masa hukunci.

4 Idan ba ka da shanun noma ba za ka sami hatsi mai yawa ba, amma idan kana da su za ka sami hatsi mai yawan gaske.

5 Amintaccen mashaidi a ko yaushe yana faɗar gaskiya, amma marar aminci ba ya faɗar kome, sai ƙarairayi.

6 Mutum mai fāriya ba zai taɓa zama mai hikima ba sam, amma mutum mai basira yakan koya a sawwaƙe.

7 Ka nisanci wawaye, gama ba su da abin da za su koya maka.

8 Me ya sa haziƙi yake da hikima? Domin ya san abin da zai yi. Me ya sa dakiki yake wauta? Domin yana ganin kansa masani ne.

9 Idan wawaye sun yi zunubi ba sukan kula ba, amma mutanen kirki sukan nemi gafara.

10 Ɓacin ranka naka ne, murnarka kuwa ba za ka raba da wani ba.

11 Gidan mutumin kirki ba zai rushe ba bayan da an lalatar da gidan mugun mutum.

12 Hanyar da kake tsammani ita ce daidai, za ta kai ka ga hallaka.

13 Dariyar mutum takan ɓoye baƙin cikinsa. Sa’ad da murna ta tafi, ko yaushe baƙin ciki yana nan.

14 Mugu zai sami abin da ya cancance shi, mutumin kirki kuma zai sami sakayyar ayyukansa.

15 Wawa yakan gaskata kowane abu, amma mai la’akari yana lura da takawarsa.

16 Mutum mai hankali yana lura don ya kauce wa wahala, amma wawa rashin kula gare shi, yakan aikata kome da gaggawa.

17 Mutum mai zafin rai yakan yi aikin wauta, mai mugayen dabaru kuma abin ƙi ne.

18 Jahilai sukan sami abin da ya cancanci wautarsu, amma ilimi shi ne sakamakon masu azanci.

19 Tilas mugaye su rusuna wa adalai, su roƙe su tagomashi da tawali’u.

20 Ba wanda yake son matalauci, amma attajiri yana da abokai da yawa.

21 Idan kana so ka zama mai farin ciki, sai ka nuna alheri ga matalauci. Zunubi ne ka raina kowane mutum.

22 Waɗansu za su amince da kai, su girmama ka, idan ka aikata nagarta, idan kuwa ka aikata mugunta, to, ka yi babban kuskure.

23 Idan ka yi aiki za ka sami abin masarufi, idan kuwa ka zauna kana ta surutu kawai za ka zama matalauci.

24 Mutane masu hikima za a sāka musu da wadata, amma za a san wawa ta wurin wautarsa.

25 Sa’ad da mashaidi ya faɗi gaskiya zai ceci rayuka, amma maƙaryacin mashaidi yakan ci amanar mutane sa’ad da ya faɗi ƙarairayi.

26 Tsoron Ubangiji yakan ba da tabbatarwa, da zaman lafiya ga mutum da iyalinsa.

27 Kana so ka kauce wa mutuwa? To, tsoron Ubangiji shi ne maɓuɓɓugar rai.

28 Darajar sarki ta dogara ga irin yawan mutane da ya mallaka, idan ba su, shi ba kome ba ne.

29 Mutum mai kamewa yana da hikima, amma mai zafin rai yana bayyana wautarsa a fili.

30 Kwanciyar rai lafiya ce ga jiki, amma kishi yana kama da ciwon da yake cin ƙashi.

31 Wanda ya zalunci matalauci ya zargi Mahaliccinsa ke nan, amma nuna alheri ga matalauci yin sujada ne.

32 Muguntar mugun takan kawo hallakarsa, amma adalin mutum, an kiyaye shi ta wurin dattakonsa.

33 Hikima tana cikin kowane tunani na haziƙi, wawa bai san kome game da hikima ba.

34 Adalci yakan ɗaukaka al’umma, amma zunubi yakan kunyatar da al’umma.

35 Sarakuna suna jin daɗin ƙwararrun ‘yan majalisarsu, amma sukan hukunta waɗanda suka ba su kunya.

Categories
K. MAG

K. MAG 15

1 Amsa magana da tattausan harshe takan kwantar da hasala, amma magana da kakkausan harshe takan kuta fushi.

2 Sa’ad da mai hikima ya yi magana yakan sa ilimi ya yi bansha’awa, amma wawaye sukan yi ta sheƙa rashin hankali.

3 Ubangiji yana ganin abin da yake faruwa a ko’ina, yana lura da mu, ko muna aikata alheri ko mugunta.

4 Kalmomin alheri suna kawo rai, amma maganganun ƙiyayya suna karya zuciyar mutum.

5 Wauta ce mutum ya ƙi kulawa da abin da mahaifinsa ya koya masa, amma hikima ce idan ka karɓi tsautawarsa.

6 Adalai suna adana dukiyarsu, amma mugaye sukan rasa tasu dukiya sa’ad da wahala ta zo.

7 Mutane masu hikima suke yaɗa ilimi, amma banda wawaye.

8 Ubangiji yana murna sa’ad da adalai suke yin addu’a, amma yana ƙin hadayun da mugaye suke miƙa masa.

9 Ubangiji yana ƙin hanyoyin mugaye, amma yana ƙaunar mutumin da yake yin abin da yake daidai.

10 Idan ka yi abin da ba daidai ba, za ka sha hukunci sosai, za ka mutu idan ka ƙi yarda da tsautawa.

11 Ko lahira ba za ta hana Ubangiji ya san abin da yake can ba. Ƙaƙa fa mutum zai iya ɓoye wa Allah tunaninsa?

12 Mai girmankai ba ya so a tsauta masa. Faufau ba zai nemi shawara a wurin masu hikima ba.

13 Sa’ad da mutum yake murna yakan yi murmushi, amma sa’ad da yake baƙin ciki yakan yi nadama.

14 Mutum mai basira yana neman ilimi, amma dakikai, jahilcinsu ya wadace su.

15 Wahaltaccen mutum a ko yaushe, fama yake yi a zamansa, amma masu farin ciki suna zama da daɗin rai.

16 Gara a zauna da talauci da tsoron Ubangiji, da a sami dukiya game da wahala.

17 Gara cin mabunƙusa tare da waɗanda kake ƙauna, da ka ci abinci mai romo a inda ƙiyayya take.

18 Zafin rai yakan kawo jayayya, amma haƙuri yana kawo salama.

19 Idan kai rago ne za ka gamu da wahala a ko’ina, amma idan kai amintacce ne, ba za ka sha wahala ba.

20 Ɗa mai hikima yana faranta zuciyar mahaifinsa, amma wawa yana raina mahaifiyarsa.

21 Dakikai suna murna da wautarsu, amma mai hikima zai aikata abin da yake daidai.

22 Ka nemi dukan shawarwarin da ka iya ka samu, za ka yi nasara, idan ba tare da shawara ba, za ka fāɗi.

23 Me ya fi wannan zama abin murna? Mutum ya sami maganar da take daidai a lokacin da ya dace!

24 Mutum mai hikima yakan kama hanya ya haura zuwa rai, ba ya bin hanyar da ta gangara zuwa mutuwa.

25 Ubangiji zai rushe gidajen masu girmankai, amma zai kiyaye dukiyar gwauruwa, wato mata wadda mijinta ya mutu.

26 Ubangiji yana ƙin tunanin mugaye, amma yana murna da kalmomi masu daɗi.

27 Mai ƙoƙarin cin ƙazamar riba yana jefa iyalinsa a wahala ke nan. Kada ka karɓi hanci, za ka yi tsawon rai.

28 Mutanen kirki sukan yi tunani kafin su ba da amsa. Mugaye suna da saurin ba da amsa, amma takan jawo wahala.

29 Sa’ad da mutanen kirki sukan yi addu’a, Ubangiji yakan kasa kunne, amma ba ya kulawa da mugaye.

30 Fuska mai fara’a takan sa ka yi murna, labari mai daɗi kuma yakan sa ka ji daɗi.

31 Idan ka mai da hakali sa’ad da ake tsauta maka kai mai hikima ne.

32 Idan ka ƙi koyo kana cutar kanka, idan ka karɓi tsautawa za ka zama mai hikima.

33 Tsoron Ubangiji koyarwa ce domin samun hikima. Sai ka zama mai tawali’u kafin ka sami girmamawa.

Categories
K. MAG

K. MAG 16

Karin Magana Zancen Zaman Mutum

1 Mutane sun iya yin shirye-shiryensu, amma cikawa ta Ubangiji ce.

2 Za ka yi tsammani kowane abu da ka yi daidai ne, amma Ubangiji yana auna manufarka.

3 Ka roƙi Ubangiji, ya sa albarka ga shirye-shiryenka, za ka kuwa yi nasara cikin aikata su.

4 Kowane abu da Ubangiji ya yi yana da makoma, makomar mugun kuwa hallaka ce.

5 Ubangiji yana ƙin kowane mutum da yake fariya. Irin wannan mutum ba zai kuɓuta daga hukunci ba.

6 Ka zama mai biyayya da aminci, Allah kuwa zai gafarta maka zunubinka. Ka dogara ga Ubangiji, ba wani mugun abu da zai same ka.

7 Lokacin da ka yi abin da Ubangiji yake so, ka iya mai da maƙiyanka su zama abokai.

8 Gara ka sami kaɗan ta hanyar gaskiya, da ka tara abu mai yawa ta hanyar zamba.

9 Kana iya yin shirye-shiryenka, amma Allah ne yake bi da kai cikin ayyukanka.

10 Sarkin da yakan yi magana ta wurin ikon Allah, a ko yaushe yakan yanke shawarar da yake daidai.

11 Ubangiji yana son ma’aunai su zama na gaskiya, kowane abin sayarwa kuma ya zama daidai.

12 Sarakuna ba za su iya jurewa da mugunta ba, gama adalci yake sa hukuma ta yi ƙarfi.

13 Sarki yana so ya ji gaskiya, zai kuwa ƙaunaci mutanen da suke faɗar gaskiya.

14 Mutum mai hikima yakan yi ƙoƙari ya faranta zuciyar sarki. Idan kuwa sarki ya hasala mai yiwuwa ne a kashe wani.

15 Alherin sarki kamar gizagizai ne masu kawo ruwan sama a lokacin bazara, akwai rai a ciki.

16 Yana da kyau, ya kuma fi kyau a sami hikima da ilimi fiye da zinariya da azurfa.

17 Mutumin kirki yana tafiya a hanyar da ta kauce wa mugunta, saboda haka ka kula da inda kake tafiya, za ta ceci ranka.

18 Girmankai jagora ne zuwa ga hallaka, fāriya kuwa zuwa ga fāɗuwa.

19 Gara ka zama ɗaya daga cikin matalauta masu tawali’u, da ka zama ɗaya daga cikin masu girmankai, har da za ka sami rabo daga cikin ganimarsu.

20 Ka mai da hankali ga abin da aka koya maka, za ka yi nasara. Ka dogara ga Ubangiji, za ka yi farin ciki.

21 Mutum mai hikima, wanda ya isa mutum, akan san shi ta wurin haziƙancinsa, kamar yadda kalmominsa suke da daɗi, haka ma rinjayarsa take.

22 Hikima maɓuɓɓugar rai ce ga mai hikima, amma ɓata lokaci ne a yi ƙoƙarin koya wa dakikai.

23 Mai hikima yakan yi tunani kafin ya yi magana, abin da ya faɗa yakan yi rinjaye ƙwarai.

24 Kalmomi masu daɗi suna kama da zuma, suna da daɗin ɗanɗana, suna kuma da amfani domin lafiyarka.

25 Hanyar da kake tsammani ita ce daidai, za ta kai ka ga hallaka.

26 Marmarin cin abinci yakan sa ɗan ƙodago ya yi aiki da ƙwazo, domin yana so ya ci ya ƙoshi.

27 Mutumin da yake jin daɗin yin mugunta yakan tafi yawon nemanta, mugayen maganganunsa ƙuna suke kamar wuta.

28 Mugaye sukan baza jita-jita, suna zuga tashin hankali, suna raba aminai.

29 Mutum mai ta da zaune tsaye yakan ruɗi abokansa, ya kai su ga bala’i.

30 Ka kula da mutane masu murguɗa baki suna kaɗa gira a kanka, sun yi tunanin wani mugun abu ke nan.

31 Furfurar tsufa rawanin daraja ce, sakamako ne ga ran mai adalci.

32 Ya fi kyau ka zama mai haƙuri da ka zama mai ƙarfi. Ya fi kyau ka iya mallakar kanka fiye da mallakar birane.

33 Mutane sukan jefa kuri’a don su san nufin Allah, amma Allah da kansa ne yake ba da amsa.

Categories
K. MAG

K. MAG 17

1 Gara a ci ƙanzo da rai a kwance, da gida cike da liyafa, amma cike da tashin hankali.

2 Bara mai wayo yakan sami iko a kan shashashan ɗan maigidansa, har ya sami rabo a cikin gādon.

3 Zinariya da azurfa da wuta ake gwada su, zuciyar ɗan adam kuwa Ubangiji ne yake gwada ta.

4 Mugaye sukan kasa kunne ga mugayen dabaru, maƙaryata kuma sukan kasa kunne ga ƙarairayi.

5 Wanda ya yi wa matalauci ba’a, Mahaliccinsa yake yi wa zargi. Idan kana murna da hasarar wani, za a hukunta ka.

6 Tsofaffi suna fāriya da jikokinsu, kamar yadda samari suke alfarma da iyayensu maza.

7 Mutumin da yake kamili ba ya faɗar ƙarya, haka ma wawa ba zai faɗi wani abin kirki ba.

8 Waɗansu mutane suna tsammani cin rashawa yakan yi aiki kamar sihiri, sun gaskata zai iya yin kome.

9 Idan kana so mutane su so ka, ka riƙa yafe musu sa’ad da suka yi maka laifi. Mita takan raba abuta.

10 Mutum mai fasaha yakan koyi abu da yawa daga tsautawa ɗaya, fiye da abin da wawa zai koya ko da an dūke shi sau ɗari.

11 Mutuwa za ta zo wa mugaye kamar mugun manzo wanda a ko yaushe yana so ya kuta tashin hankali.

12 Gara mutum ya gamu da beyar ta mata wadda aka kwashe mata kwiyakwiyanta, da ka gamu da waɗansu wawaye suna aikin dakikancinsu.

13 Idan ka sāka alheri da mugunta, ba za ka iya raba gidanka da mugunta ba, faufau.

14 Mafarin jayayya kamar ɓarkewa madatsar ruwa ne, sai a tsai da ita tun ba ta haɓaka ba.

15 Da wanda ya baratar da mugun da wanda ya kā da adali, duk abin ƙi suke ga Ubangiji.

16 Kashe kuɗi saboda ilimi ba shi da amfanin kome ga wawa, domin ba shi da tunani.

17 A ko yaushe abokai sukan nuna ƙaunarsu, ‘yan’uwa kuma, ai, don su ɗauki nawayar juna suke.

18 Sai mutum marar tunani ne kaɗai zai ɗauki lamunin basusuwan maƙwabcinsa.

19 Shi wanda yake son zunubi, yana son wahala ke nan, wanda kuma yake yin fāriya a dukan lokaci yana neman tashin hankali ke nan.

20 Mutumin da yakan yi tunanin mugunta, ya kuma hurta ta, kada ya sa zuciya ga samun abin kirki, sai dai bala’i kaɗai.

21 Mahaifi wanda ɗansa yake yin abubuwan wauta, ba shi da kome sai ɓacin rai da baƙin ciki.

22 Kasancewa da murna yakan ba ka lafiya. Zama da baƙin rai dukan lokaci mutuwar tsaye ce.

23 Alƙalai marasa gaskiya suna cin hanci a ɓoye, sa’an nan ba za su aikata adalci ba.

24 Baligi da hikima yake aikinsa, amma wanda bai balaga ba, bai san abin da zai yi ba.

25 Wawan da yakan jawo wa mahaifinsa ɓacin rai, abin baƙin ciki yake ga mahaifiyarsa.

26 Ba daidai ba ne a ci marar laifi tara, yi wa mutumin kirki bulala kuwa rashin adalci ne.

27 Mutumin da ya tabbata yana da gaskiya ba zai cika yawan magana ba, natsattsen mutum yana da basira ƙwarai.

28 Banda haka ma, ko wawa in bai buɗe bakinsa ba, za a zaci shi mai hikima ne, mai basira.

Categories
K. MAG

K. MAG 18

1 Mutumin da ya kula da kansa kaɗai ba ya jituwa da kowa, ko wani ya faɗi maganar da take daidai ba zai yarda ba.

2 Wawa bai kula ba, ko ya fahimci abu, ko bai fahimta ba. Abin da yake so ya yi kaɗai, shi ne ya nuna kuzarinsa.

3 Zunubi da kunya a tattare suke. Idan ka yar da mutuncinka za ka sha ba’a a maimakonsa.

4 Harshen ɗan adam yana iya zama shi ne asalin hikima mai zurfi kamar teku, sabo kamar ruwan rafi mai gudu.

5 Ba daidai ba ne a yi wa mugun mutum alheri, sa’an nan a ƙi yi wa marar laifi adalci.

6 Sa’ad da wawa ya fara jayayya, yana neman dūka ne.

7 Sa’ad da wawa ya yi magana yana lalatar da kansa ne, maganarsa tarko ce, da ita ake kama shi.

8 Ɗanɗanar jita-jita daɗi gare ta, mukan ƙosa mu haɗiye ta.

9 Rago yana daidai da mutumin da yake lalatar da abubuwa.

10 Sunan Ubangiji kamar ƙaƙƙarfar hasumiya ne, inda adali yakan shiga ya zauna lafiya.

11 Attajirai suna zato dukiyarsu ita ce za ta kiyaye su kamar garuka masu tsayi da suke kewaye da birni.

12 Ba wanda za a girmama sai mai tawali’u, mutum mai girmankai kuwa yana kan hanyar hallaka.

13 Ka saurara kafin ka amsa, idan kuwa ba ka yi ba, ka zama dakiki mai bankunya.

14 Sa zuciya ga rai yakan taimaki mutum sa’ad da yake ciwo, amma idan ya karai, to, tasa ta ƙare.

15 Mutane masu basira, a ko yaushe suna da himma, a shirye kuma suke domin su koya.

16 Kana so ka sadu da babban mutum? Ka kai masa kyauta, za ka gan shi a sawwaƙe.

17 Wanda ya fara mai da magana a majalisa yakan zama kamar shi ne mai gaskiya, sai abokin shari’arsa ya mai da tasa maganar tukuna.

18 Idan mutum biyu ƙarfafa suna jayayya da juna a gaban shari’a, kuri’a a asirce kaɗai take iya daidaita tsakaninsu.

19 Ɗan’uwan da ya ji haushinka zai gagare ka, idan ka yi faɗa da shi zai rufe maka ƙofarsa.

20 Bisa ga sakamakon hurcinka haka za ka rayu.

21 Abin da ka faɗa ya iya cetonka ko ya hallaka ka, saboda haka tilas ne ka karɓi sakamakon maganarka.

22 Idan ka sami mace ka sami abu mai kyau, wannan alheri ne wanda Ubangiji ya yi maka.

23 Matalauci yakan yi roƙo da taushi, maganar matalauci rarrashi ne, amma attajiri yakan yi magana garas.

24 Waɗansu abokai ba su sukan ɗore ba, amma waɗansu abokai sun fi ‘yan’uwa aminci.

Categories
K. MAG

K. MAG 19

1 Gara mutum ya zama matalauci amma mai aminci, da a ce ya zama maƙaryaci, wawa.

2 Yin ɗokin da ba ilimi ba shi da amfani, rashin haƙuri kuma zai jawo maka wahala.

3 Waɗansu mutane sukan lalatar da kansu ta wurin ayyukansu na jahilci, sa’an nan su sa wa Ubangiji laifi.

4 Attajirai sukan sami sababbin abokai a ko yaushe, amma matalauta ba zu su iya riƙon ‘yan kaɗan da suke da su ba.

5 Idan ka faɗi ƙarya a majalisa, za a hukunta ka, ba za ka kuɓuta ba.

6 Kowa na ƙoƙari ya sami farin jini wurin manyan mutane, kowa na so a ce shi abokin mutumin nan ne, mai yawan alheri.

7 ‘Yan’uwan matalauci ba su bukatarsa, ba abin mamaki ba ne ya rasa abokai. Kome ƙoƙarin da zai yi ba zai sami ko ɗaya ba.

8 Ka yi wa kanka gatanci, ka koyi dukan abin da kake iyawa, sa’an nan ka tuna da abin da ka koya, za ka arzuta.

9 Ba wanda zai faɗi ƙarya a majalisa ya rasa shan hukunci, maƙaryaci, tasa ta ƙare.

10 Ko kusa wawaye ba za su yi zaman jin daɗi ba, haka nan kuma bayi ba za su yi mulki a kan iyayengijinsu ba.

11 Mutum mai hankali yake danne fushinsa. Lokacin da wani ya cuce ka, abin kirki ne, ka yi kamar ba ka kula da shi ba.

12 Hasalar sarki kamar rurin zaki ne, amma alherinsa kamar saukar ruwan sama ne.

13 Dakikin ɗa yana jawo wa mahaifinsa lalacewa, mace mai mita tana kama da ɗiɗɗigar ruwa.

14 Mutum na iya cin gādon gida da kuɗi daga wurin iyayensa, amma Ubangiji ne kaɗai yake ba shi mace mai hankali.

15 Rago, yi ta ragwancinka ka yi ta sharar barci, amma kai za ka sha yunwa.

16 Ka kiyaye umarnai za ka rayu, in ka ƙi binsu kuwa za ka mutu.

17 Sa’ad da ka bayar ga matalauci kamar ka ba Ubangiji rance ne, gama Ubangiji zai sāka maka.

18 Ka yi wa ‘ya’yanka tarbiyya tun suna ƙanana yadda za su iya koyo. Idan ba ka yi haka ba, ka taimaka wajen lalacewarsu ke nan.

19 Idan mutum mai zafin rai ne, ƙyale shi ya sha sakamakonsa. Idan ka fisshe shi daga cikin wahala sau ɗaya, sai ka sāke yi.

20 Ka saurari shawara, ka yarda ka koya, wata rana za ka zama mai hikima.

21 Mutum ya iya shirya dabaru iri iri, amma sai nufin Ubangiji ne zai tabbata.

22 Abin kunya ne mutum ya zama mai haɗama, matalauci kuma ya fi maƙaryaci.

23 Ka yi tsoron Ubangiji za ka yi tsawon rai, ka kuma sami biyan bukata, ba abin da zai cuce ka.

24 Waɗansu mutane sun cika lalaci, ko abincinsu ba su iya taunawa.

25 Za a hukunta mai fāriya saboda ya zama ishara ga mutanen da ba su san kome ba, mutum mai hikima yakan koya sa’ad da aka tsauta masa.

26 Sai marar kunya, marar mutunci suke wulakanta mahaifinsa, ko ya kori mahaifiyarsa daga gidansa.

27 Ɗana idan ka bar yin nazari za ka manta da abin da ka riga ka koya.

28 Ba gaskiya ga mashaidin da ya yi niyyar cutar wani. Mugaye suna ƙaunar yin mugunta.

29 Wawa mai fāriya hakika zai sha dūka.

Categories
K. MAG

K. MAG 20

1 Ruwan inabi da barasa sukan sa ka ka yi ta tā da murya, ka zama wawa. Wauta ce mutum ya bugu.

2 Ka ji tsoron fushin sarki kamar yadda za ka ji tsoron zaki mai ruri, sa shi ya yi fushi kashe kai ne.

3 Kowane wawa yakan fara yin jayayya, abin da ya fi daraja shi ne ka fita ka ware kanka.

4 Manomin da ya cika lalaci, ya kasa nome gonakinsa a kan kari, a lokacin girbi ba zai sami kome ba.

5 Tunanin mutum kamar ruwa yake a rijiya mai zurfi, sai mai basira ya iya ya jawo shi.

6 Kowa gani yake shi mai biyayya ne, mai aminci. Amma ina? Ko ka yi ƙoƙari ka sami amintacce ɗaya daga cikinsu, ba za ka samu ba.

7 ‘Ya’yan da mahaifinsu amintacce ne, wanda yake aikata abin da yake daidai, sun yi sa’a.

8 Sarkin da yake yin shari’a ta gaskiya, da ganin mugunta ya san ta.

9 Wane ne zai iya cewa lamirinsa garau yake, har da zai ce ya rabu da zunubinsa?

10 Allah yana ƙin masu ma’aunin algus.

11 Ayyukan da saurayi yake yi suke bayyana yadda yake, kana iya sani ko shi amintacce ne, mai nagarta.

12 Ubangiji ya ba mu ido don mu gani, ya ba mu kunne don mu ji.

13 Idan barci ne sana’arka za ka talauce. Ka yi ta aiki za ka sami wadataccen abinci.

14 Mai saye yakan yi kukan tsada a kullum, amma yakan tafi ya yi ta fāriya a kan ya iya ciniki.

15 In ka san abin da kake faɗa, kana da wani abu wanda ya fi zinariya da lu’ulu’ai tamani.

16 Sai wawa kaɗai yake ɗaukar lamunin biyan basusuwan da baƙo ya ci, ya kamata a karɓi dukiyarsa jingina.

17 Abin da ka samu ta hanyar zamba kakan ji daɗinsa kamar abinci mai kyau, amma ko ba jima ko ba daɗe zai zama kamar yashi cike da bakinka.

18 Ka nemi kyakkyawar shawara za ka yi nasara, kada ka jefa kanka cikin yaƙi ba tare da shiri ba.

19 Mai baza jita-jita ba shi da asiri, ka yi nesa da mai yawan surutu.

20 Idan ka zagi iyayenka, za ka mutu kamar fitilar da ta mutu cikin duhu.

21 Dukiyar da aka same ta a sawwaƙe, amfaninta kaɗan ne.

22 Kada ka ɗaukar wa kanka fansa, ka dogara ga Ubangiji shi zai yi sakamako.

23 Ubangiji yana ƙin waɗanda suke awo da ma’aunin algus.

24 Ubangiji ya ƙayyade hanyoyinmu, ta ƙaƙa wani zai ce ya fahimci rai?

25 Ka yi tunani a hankali kafin ka yi wa’adi za ka miƙa wa Allah wani abu, mai yiwuwa ne ka yi da na sani nan gaba.

26 Sarki mai hikima zai bincika ya gane waɗanda suke aikata mugunta, ya hukunta su ba tausayi.

27 Ubangiji ne ya ba mu hankali da lamiri, ba za mu iya ɓoye masa ba.

28 Sarki zai zauna dafa’an cikin mulkinsa muddin yana mulki da aminci, da adalci, da daidaita.

29 Ƙarfin samari abin darajantawa ne, furfurar tsofaffi abar girmamawa ce.

30 Wani lokaci sai mun sha wuya muke sāke hanyoyinmu.

Categories
K. MAG

K. MAG 21

1 Ubangiji ne yake mallakar tunanin sarki a sawwaƙe kamar yadda yake yi da ruwan rafi.

2 Ko da a ce dukan abin da kake yi daidai ne, ka tuna fa Ubangiji ya san manufarka.

3 Ubangiji ya fi so ka yi abin da yake daidai, mai kyau kuma, fiye da ka miƙa masa hadayu.

4 Girmankai da fāriya suke bi da mugaye, wannan kuwa zunubi ne.

5 Yin shiri a tsanaki zai kai ka ga biyan bukatarka, idan kuwa ka cika gaggawa ba za ka sami abin da zai ishe ka ba.

6 Dukiyar da aka tara ta hanyar rashin gaskiya takan ƙare nan da nan, takan kuma kai ga mutuwa.

7 Mugaye, tasu ta ƙare saboda muguntarsu, gama sun ƙi yin abin da yake daidai.

8 Mutane masu laifi sukan bi ta karkatacciyar hanya, marasa laifi kuwa suna aikata abin da yake daidai.

9 Gara zama a saƙo da zama a gida ɗaya tare da mace mai mita.

10 Mugaye sun zaƙu su aikata mugunta, ba su yi wa kowa jinƙai.

11 Sa’ad da aka hukunta mai girmankai, ko marar tunani yakan koyi wani abu, mutum mai hikima yakan koyi abin da ake koya masa.

12 Adali ya san tunanin mugaye, yakan kuwa zama sanadin lalacewarsu.

13 Idan ka ƙi jin kukan matalauci, naka kukan da kake yi na neman taimako, ba za a ji ba.

14 Kyauta a asirce takan kwantar da zuciyar wanda yake fushi da kai.

15 Sa’ad da aka yi adalci mutanen kirki sukan yi murna, amma mugaye sukan yi baƙin ciki.

16 Mutuwa tana jiran wanda ya ƙi bin hanyar hankali.

17 Sa kai cikin nishaɗi, wato shan ruwan inabi, da cin abinci mai tsada, ba zai bar ka ka tara dukiya ba.

18 Wahalar da mugaye suke so su jawo wa mutanen kirki, za ta koma kansu.

19 Gara ka zauna a hamada, da ka zauna tare da mace mai mita, mai yawan kai ƙara.

20 Mutane masu hikima suna zaune da wadata da nishaɗi, amma wawaye da zarar sun sami kuɗi sukan kashe su nan da nan.

21 Ka yi alheri ka yi aminci, za ka yi tsawon rai waɗansu kuma za su girmama ka, su yi maka abin da yake daidai.

22 Sarkin yaƙi mai wayo yakan ci birnin da jarumawa suke tsaro, ya rushe garun da suke taƙama da shi.

23 Idan ba ka so ka shiga wahala, ka lura da abin da kake faɗa.

24 Ba kalmar da ta fi “fāɗin rai” dacewa ga mutum mai girmankai, mai fāriya marar tunani.

25 Malalacin mutumin da ya ƙi yin aiki, kansa yake kashewa.

26 Duk abin da yake tunani dukan yini, shi ne a kan abin da yake so ya samu. Amma adali ko ta ƙaƙa yakan bayar da hannu sake.

27 Ubangiji yana ƙin hadayar da mugaye suka miƙa masa, tun ba wadda suka miƙa ta da mugun nufi ba.

28 Ba a gaskata shaidar maƙaryaci, amma mutumin da yakan yi tunani a kan al’amura, akan karɓi tasa.

29 Adali ya tabbatar da kansa, haka ma mugun mutum yakan yi da’awa, cewa shi ma ya tabbatar da kansa.

30 Hikima, da haziƙanci, da basira, ba kome suke ba gāba da Ubangiji.

31 Kana iya shirya dawakai don zuwa yaƙi, amma nasara ta Ubangiji ce.

Categories
K. MAG

K. MAG 22

1 Idan ya zama dole ne ka zaɓa tsakanin kyakkyawan suna ko dukiya, to, ka zaɓi kyakkyawan suna, tagomashi kuma ya fi azurfa da zinariya.

2 Ba bambanci tsakanin mawadaci da matalauci, gama Ubangiji ne ya halicce su duka.

3 Mutum mai hankali, in ya ga wahala tana zuwa yakan kauce mata, amma shashasha yakan kutsa kai ciki, daga baya ya yi da na sani.

4 Kana da tsoron Ubangiji, ka yi tawali’u, za ka arzuta, ka ɗaukaka, ka sami tsawon rai.

5 Idan kana ƙaunar ranka ka nisanci tarkunan da aka kafa a hanya don su kama mugaye.

6 Ka koya wa yaro yadda zai yi zamansa, zai kuwa tuna da ita dukan kwanakinsa.

7 Matalauta su ne bayin attajirai, bawa ne kai ga wanda ka ci bashi a gare shi.

8 In ka shuka rashin gaskiya masifa ce za ta tsiro, wato hukunci mai tsanani wanda zai hallakar da kai.

9 Ka zama mai hannu sake, ka riƙa ba matalauta abincinka, za a sa maka albarka saboda haka.

10 Ka rabu da mutum mai fāriya, mai gardama, mafaɗaci, hatsaniya za ta ƙare.

11 In ka yi ladabi za ka zama aminin sarki, gama yana ƙaunar amintaccen mutum.

12 Ubangiji yana lura ya ga an riƙe gaskiya sosai ta wurin ƙin yarda da maganganun ƙarya.

13 Malalaci yakan yi zamansa a gida, yakan ce, “Zaki zai kama ni in na fita waje.”

14 Zina tarko ce, takan kama waɗannan waɗanda Ubangiji yake fushi da su.

15 Halin yara ne su yi wauta da waɗansu abubuwa na rashin kula, amma tsumagiya za ta koya musu abin da ya fi kyau.

16 Idan attajirai kake yi wa kyauta, kana kuma zaluntar matalauta don ka arzuta, kai kanka za ka talauce.

Umarnai da Dokoki

17 Ka kasa kunne zan koya maka abin da masu hikima suka faɗa, yi nazari a kan koyarwarsu.

18 Za ka yi murna in ka tuna da su, ka iya faɗarsu.

19 Ina so ka dogara ga Ubangiji, don haka zan faɗa maka su yanzu.

20 Na rubuta maka karin magana, suna ƙunshe da ilimi da kyakkyawar shawara.

21 Zan koya maka ainihin gaskiya, domin sa’ad da aka aike ka ka nemo ta, za ka iya kawo amsa daidai.

22 Kada ka ƙwari matalauci don ka fi shi, kada ka ƙwari wanda ba shi da mai taimako a gaban shari’a.

23 Ubangiji zai yi magana dominsu a kan shari’ar da suke yi, ya nemi ran duk wanda yake neman rayukansu.

24 Kada ka yi abuta da mutane masu zafin fushi, ko masu zafin rai.

25 Mai yiwuwa ne ka koyi irin ɗabi’unsu, har ka kasa sākewa.

26 Kada ka yi alkawarin ɗaukar wa wani lamuni,

27 gama idan ka kāsa biya har gadonka ma za su ɗauke.

28 Kada ka kawar da shidar kan iyaka wadda kakanninka suka kafa.

29 Ka nuna mini mutumin da yake aiki mai kyau, ni kuwa in nuna maka mutumin da ya fi duka, wanda ya cancanci ya zauna tare da sarakuna.