Categories
IRM

IRM 26

Maƙarƙashiya a Kashe Irmiya

1 A farkon sarautar Yehoyakim ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, Ubangiji ya yi magana da Irmiya ya ce,

2 “Ka tsaya a filin Haikalin Ubangiji, ka yi wa dukan biranen Yahuza magana, su waɗanda suka zo Haikalin Ubangiji domin su yi sujada. Ka faɗa musu dukan maganar da na umarce ka, kada ka rage ko ɗaya.

3 Mai yiwuwa ne su ji, har kowa ya juyo ya bar muguwar hanyarsa. Ni ma sai in janye masifar da na yi niyyar aukar musu da ita, saboda mugayen ayyukansu.”

4 Ubangiji ya faɗa wa Irmiya ya ce wa jama’a, “Haka Ubangiji ya ce, idan ba za ku kasa kunne gare ni ba, ku yi tafiya a dokata wadda na sa a gabanku ba,

5 ku kuma kula da zantuttukan bayina, annabawa, waɗanda na yi ta aiko muku, to, amma ba ku kula ba.

6 Saboda haka zan mai da wannan Haikali kamar Shilo, in mai da wannan birni ya zama abin la’ana ga dukan al’umman duniya.”

7 Firistoci, da annabawa, da dukan jama’a sun ji dukan maganan nan da Irmiya ya faɗa a cikin Haikalin Ubangiji.

8 Sa’ad da Irmiya ya gama faɗar dukan abin da Ubangiji ya umarce shi ya faɗa wa dukan jama’a, sai firistoci, da annabawa, da dukan jama’a suka kama shi, suna cewa, “Mutuwa za ka yi!

9 Don me ka yi annabci da sunan Ubangiji, ka ce wannan Haikali zai zama kamar Shilo, wannan birni kuma zai zama kufai, ba mazauna a ciki?” Sai jama’a duk suka taru, suka kewaye Irmiya cikin Haikalin Ubangiji.

10 Sa’ad da sarakunan Yahuza suka ji waɗannan al’amura, sai suka fito daga gidan sarki zuwa Haikalin Ubangiji, suka zauna a bakin Sabuwar Ƙofa ta Haikalin Ubangiji.

11 Sai firistoci da annabawa suka faɗa wa sarakunan nan da jama’a duka, suka ce, “Mutumin nan ya cancanci hukuncin kisa, gama ya yi annabci gāba da wannan birni kamar yadda kuka ji da kunnuwanku.”

12 Sa’an nan sai Irmiya ya yi magana da dukan sarakuna da dukan jama’a, ya ce, “Ubangiji ne ya aiko ni in yi annabci gāba da wannan Haikali da wannan birni, da irin maganar da kuka ji.

13 Saboda haka yanzu sai ku gyara al’amuranku da ayyukanku, ku yi biyayya kuma da muryar Ubangiji Allahnku. Ubangiji kuwa zai janye masifar da ya hurta gāba da ku.

14 Amma ni kaina kuwa a hannunku nake, sai ku yi mini yadda kuka ga ya yi kyau, ya kuma dace a gare ku.

15 Ku tabbata dai, idan kuka kashe ni, za ku jawo hakkin jinin marar laifi a kanku da a kan wannan birni da mazauna a cikinsa, gama a gaskiya Ubangiji ne ya aiko ni wurinku domin in faɗa muku dukan maganan nan a kunnuwanku.”

16 Sarakuna kuwa da dukan jama’a suka ce wa firistoci da annabawa, “Wannan mutum bai yi abin da ya isa hukuncin kisa ba, gama ya yi magana da sunan Ubangiji Allahnmu.”

17 Sai waɗansu daga cikin dattawan ƙasar suka miƙe tsaye, suka ce wa dukan taron jama’a,

18 “Mika kuwa, mutumin Moreshet, ya yi annabci a kwanakin Hezekiya, Sarkin Yahuza, ya faɗa wa dukan mutanen Yahuza cewa,

‘Ga abin da Ubangiji Mai Runduna

ya ce,

Za a nome Sihiyona kamar gona,

Urushalima kuwa za ta zama tsibin

juji,

Ƙwanƙolin dutsen Haikalin zai zama

kurmi.’

19 Ashe, Hezekiya Sarkin Yahuza da dukan Yahuza sun kashe shi ne? Ashe, Hezekiya bai ji tsoron Ubangiji, ya roƙi alherinsa ba? Ashe, Ubangiji bai janye masifar da ya hurta a kansu ba? Yanzu fa gab muke da mu jawo wa kanmu babbar masifa.”

20 Akwai wani mutum kuma wanda ya yi annabci da sunan Ubangiji. Sunansa Uriya ɗan Shemaiya mutumin Kiriyat-yeyarim. Ya yi annabci gāba da birnin nan da ƙasan nan da magana irin ta Irmiya.

21 Sa’ad da sarki Yehoyakim, da dukan jarumawansa, da dukan sarakunansa suka ji maganarsa, sai sarki yana so ya kashe shi, amma sa’ad da Uriya ya ji, sai ya ji tsoro, ya gudu ya tsere zuwa Masar.

22 Sa’an nan sai sarki Yehoyakim ya aiki waɗansu mutane zuwa Masar, wato Elnatan ɗan Akbor da waɗansu tare da shi.

23 Suka kamo Uriya daga Masar suka kawo shi wurin sarki Yehoyakim, sai ya sa aka kashe shi da takobi, aka binne gawarsa a makabartar talakawa.

24 Amma Ahikam ɗan Shafan yana tare da Irmiya, saboda haka ba a bashe shi ga mutane don su kashe shi ba.

Categories
IRM

IRM 27

Irmiya Ya Ɗaura Karkiyar Shanu a Wuyansa

1 A farkon sarautar Zadakiya ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, Ubangiji ya yi wa Irmiya magana.

2 Ya ce ya yi wa kansa karkiyar itace da maɗaurai na fata ya ɗaura su a wuyansa,

3 ya aika da magana zuwa ga Sarkin Edom, da Sarkin Mowab, da Sarkin Ammon, da Sarkin Taya, da Sarkin Sidon ta hannun manzannin da suka zo Urushalima wurin Zadakiya Sarkin Yahuza.

4 Ubangiji ya ce wa Irmiya ya umarce su, su tafi, su faɗa wa iyayengijinsu cewa, “In ji Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila, ga abin da za ku faɗa wa iyayengijinku,

5 ‘Ni ne da ikona da ƙarfina na yi duniya, da mutane, da dabbobi waɗanda suke cikinta. Nakan ba da ita ga wanda na ga dama.

6 Yanzu fa na ba bawana Nebukadnezzar, Sarkin Babila, dukan ƙasashen nan, na kuma ba shi namomin jeji su bauta masa.

7 Dukan ƙasashe za su bauta masa, da shi da ɗansa, da jikansa, har lokacin da na sa ƙasar ta fāɗi, sa’an nan al’ummai masu yawa da manyan sarakuna za su bautar da shi.

8 “ ‘Amma idan wata al’umma ko wani mulki bai yarda ya bauta wa Nebukadnezzar, Sarkin Babila ba, bai kuma ɗaura karkiyar Sarkin Babila a wuyansa ba, zan hukunta wa wannan al’umma da takobi, da yunwa, da annoba, har in hallaka ta, ta hannun Nebukadnezzar, ni Ubangiji na faɗa.

9 Saboda haka kada ku saurari annabawanku, da masu duba, da masu mafarkai, da matsubbata, ko masu sihiri waɗanda suka ce muku ba za ku bauta wa Sarkin Babila ba.

10 Suna yi muku annabcin ƙarya ne, za su kuwa sa a kai ku wata ƙasa nesa da ƙasarku. Zan kore ku, za ku kuwa lalace.

11 Amma duk al’ummar da za ta ɗaura karkiyar Sarkin Babila a wuyanta, ta kuma bauta masa, zan bar ta a ƙasarta, ta yi noman ƙasarta, ta zauna a ciki, ni Ubangiji na faɗa.’ ”

12 Sai na faɗa wa Zadakiya Sarkin Yahuza wannan magana cewa, “Ka ɗaura karkiyar Sarkin Babila a wuyanka, ka bauta masa, shi da mutanensa, don ka rayu!

13 Don me kai da mutanenka za ku mutu ta takobi, da yunwa, da annoba, kamar yadda Ubangiji ya yi magana a kan kowace al’umma da ta ƙi ta bauta wa Sarkin Babila?

14 Kada ka kasa kunne ga maganar annabawan da suke ce maka, ‘Ba za ku bauta wa Sarkin Babila ba.’ Annabcin ƙarya suke yi muku.

15 Gama Ubangiji ya ce shi bai aike su ba, annabcin ƙarya suke yi muku da sunansa, don ya kore ku, ku halaka, ku da annabawan da suke yi muku annabci.”

16 Sa’an nan na faɗa wa firistoci da jama’a cewa, “In ji Ubangiji, kada ku kasa kunne ga abin da annabawanku suke muku annabci cewa, ‘Ba da daɗewa ba za a komo da kayan Haikalin Ubangiji daga Babila.’ Ƙarya ce suke yi muku.

17 Kada ku ji su, amma ku bauta wa Sarkin Babila don ku rayu! Don me birnin nan zai zama kufai?

18 Idan su annabawa ne, idan kuwa Ubangiji yana magana da su, to, bari su roƙi Ubangiji Mai Runduna kada a tafi Babila da kayayyakin da suka ragu a Haikalin Ubangiji, da a fādar Sarkin Yahuza, da a Urushalima.

19 Gama Ubangiji Mai Runduna ya faɗi zancen ginshiƙai, da babbar kwatarniya, da dakalai, da sauran kayayyaki da aka bar su a birnin nan,

20 wato waɗanda Nebukadnezzar, Sarkin Babila bai kwashe ba a lokacin da ya tafi da Yekoniya ɗan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, da dukan dattawan Yahuza da na Urushalima zuwa bauta a Babila.

21 “Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila, ya faɗa a kan kayayyakin da suka ragu a Haikalin Ubangiji, da a fādar Sarkin Yahuza, da a Urushalima,

22 ‘Za a kwashe su a kai Babila, a can za su kasance har lokacin da zan sāke kulawa da su. Sa’an nan ne zan komo da su, in maishe su a wannan wuri.’ ”

Categories
IRM

IRM 28

Annabcin Ƙarya na Hananiya

1 Ya zama fa a wannan shekara, a watan biyar, a shekara ta huɗu ta sarautar Zadakiya Sarkin Yahuza, sai annabi Hananiya ɗan Azzur mutumin Gibeyon, ya yi magana da ni a Haikalin Ubangiji, a gaban firistoci da dukan jama’a, ya ce,

2 “Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila, ya faɗa, ‘Na karya karkiyar Sarkin Babila.

3 Bayan shekara biyu zan komo da kayayyakin Haikalin Ubangiji zuwa wurin nan. Kayayyakin da Nebukadnezzar, Sarkin Babila ya kwashe daga wannan wuri, ya kai Babila.

4 Zan kuma komo da Yekoniya ɗan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, da dukan waɗanda aka kai su zaman talala daga Yahuza, gama zan karya karkiyar Sarkin Babila.’ ”

5 Sa’an nan annabi Irmiya ya yi magana da annabi Hananiya a gaban firistoci da dukan jama’ar da suke tsaye a Haikalin Ubangiji, ya ce,

6 “Amin, amin, Ubangiji ya sa ya zama haka, Ubangiji ya sa annabcin da ka yi ya zama gaskiya, Ubangiji ya komo da kayayyakin Haikalinsa da dukan waɗanda aka kai su zaman talala a Babila.

7 Amma yanzu sai ka ji maganan nan da zan faɗa maka, kai da dukan jama’an nan.

8 Annabawan da suka riga mu, ni da kai a zamanin dā, sun yi wa ƙasashe masu yawa da manyan mulkoki annabcin yaƙi da yunwa, da annoba.

9 Idan maganar wannan annabi kuwa da ya yi annabcin salama ta cika, sa’an nan ne za a sani gaskiya Ubangiji ne ya aiko shi.”

10 Sai annabi Hananiya ya cire karkiyar daga wuyan annabi Irmiya ya karya ta.

11 Sa’an nan Hananiya ya yi magana a gaban dukan jama’a, ya ce, “In ji Ubangiji, haka zan karya karkiyar Nebukadnezzar, Sarkin Babila, daga wuyan dukan al’ummai kafin shekara biyu.” Sai annabi Irmiya ya yi tafiyarsa.

12 Da ɗan daɗewa bayan da annabi Hananiya ya karya karkiyar da take a wuyan annabi Irmiya, sai Ubangiji ya yi magana da Irmiya, ya ce

13 ya tafi ya faɗa wa Hananiya, ya ce, “Haka Ubangiji ya ce, ‘Ka karya karkiya ta itace, amma zan yi karkiya ta ƙarfe a maimakonta.

14 Gama haka, ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila, na faɗa. Na sa wa wuyan dukan waɗannan al’ummai karkiya ta ƙarfe, don su bauta wa Nebukadnezzar, Sarkin Babila, za su kuwa bauta masa, gama na ba shi su, har da namomin jeji.’ ”

15 Sai annabi Irmiya ya ce wa annabi Hananiya, “Ka ji, ya Hananiya, Ubangiji bai aike ka ba, kana sa mutanen nan su dogara ga ƙarya.

16 Saboda haka, in ji Ubangiji, ‘Zan kawar da kai daga duniya. Za ka mutu a wannan shekara domin ka kuta tayarwa ga Ubangiji.’ ”

17 A wannan shekara kuwa, a watan bakwai, sai annabi Hananiya ya mutu.

Categories
IRM

IRM 29

Wasiƙar Irmiya Zuwa ga Yahudawan da suke Babila

1 Ga maganar wasiƙar da annabi Irmiya ya aika daga Urushalima zuwa ga dattawa, da firistoci, da annabawa, da dukan mutanen da Nebukadnezzar ya kwaso daga Urushalima zuwa Babila. (

2 Ya rubuta wannan bayan tashin sarki Yekoniya, da uwa tasa, da bābāni, da sarakunan Yahuza, da na Urushalima, da gwanayen aikin hannu, da maƙera daga Urushalima.)

3 Ya aika da wasiƙar ta hannun Elasa ɗan Shafan, da Gemariya ɗan Hilkiya waɗanda Zadakiya Sarkin Yahuza ya aika zuwa Babila, wurin Nebukadnezzar, Sarkin Babila. Ga abin da wasiƙar ta ce.

4 “Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila ya ce wa dukan waɗanda aka kai bauta, wato waɗanda ya aika da su bauta daga Urushalima zuwa Babila.

5 ‘Ku gina gidaje, ku zauna a ciki, ku dasa gonaki, ku ci amfaninsu.

6 Ku auri mata, ku haifi ‘ya’ya mata da maza. Ku auro wa ‘ya’yanku mata, ku aurar da ‘ya’yanku mata, domin su haifi ‘ya’ya mata da maza, ku riɓaɓɓanya a can, kada ku ragu.

7 Amma ku nemi zaman lafiyar birni inda na sa aka kai ku zaman talala, ku yi addu’a ga Ubangiji saboda birnin, gama zaman lafiyar birnin shi ne naku zaman lafiyar.’

8 Gama haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila ya faɗa. ‘Kada ku yarda annabawanku da malamanku na duba waɗanda suke tare da ku su ruɗe ku, kada ku kasa kunne ga mafarkansu.

9 Gama annabcin da suke yi muku da sunana, ƙarya ne, ni ban aike su ba.’

10 “Ubangiji ya ce, ‘Sa’ad da kuka cika shekara saba’in a Babila, zan ziyarce ku, zan kuwa cika muku alkawarina. Zan komo da ku zuwa wannan wuri.

11 Gama na san irin shirin da na yi muku, ni Ubangiji na faɗa. Shirin alheri, ba na mugunta ba. Zan ba ku gabata da sa zuciya.

12 Sa’an nan za ku yi kira a gare ni, ku yi addu’a a wurina, zan kuwa ji ku.

13 Za ku neme ni ku same ni, idan kun neme ni da zuciya ɗaya.

14 Za ku same ni, ni Ubangiji na faɗa, zan mayar muku da arzikinku, in tattaro ku daga cikin dukan al’ummai da dukan wurare inda na kora ku, ni Ubangiji na faɗa, zan komo da ku a wurin da na sa a kwashe ku a kai ku zaman talala.’

15 “Domin kun ce, Ubangiji ya ba ku annabawa a Babila,

16 ku ji abin da Ubangiji ya faɗa a kan sarkin da ya hau gadon sarautar Dawuda, da a kan dukan jama’ar da suke zaune a wannan birni, wato a kan danginku waɗanda ba a kwashe su zuwa zaman talala ba.

17 Haka Ubangiji Mai Runduna ya ce, ‘Ga shi, zan aiko musu da takobi, da yunwa, da masifa, zan maishe su kamar ruɓaɓɓen ɓaure waɗanda suka lalace ƙwarai, har ba su ciwuwa.

18 Zan fafare su da takobi, da yunwa, da masifa. Zan maishe su abin ƙyama ga dukan mulkokin duniya. Za su zama abin la’ana, da abin razana, da abin raini, da abin zargi, ga dukan al’ummai, inda na kora su.

19 Domin ba su ji maganata wadda ni Ubangiji na faɗa ba, na yi ta aika muku da ita ta wurin bayina annabawa, amma kuka ƙi, ni Ubangiji na faɗa.

20 Ku ji maganar Ubangiji, dukanku da aka kai ku zaman talala waɗanda na kora daga cikin Urushalima zuwa Babila.’

21 “Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila ya ce a kan Ahab ɗan Kolaya, da Zadakiya ɗan Ma’aseya, waɗanda suke yi muku annabcin ƙarya da sunana. ‘Ga shi, zan bashe su a hannun Nebukadnezzar, Sarkin Babila, zai kashe su a kan idonku.

22 Saboda su duka waɗanda aka kai bautar talala daga Yahuza zuwa Babila, za su mori kalman nan suna yin la’ana cewa, “Ubangiji ya maishe ka kamar Zadakiya da Ahab, waɗanda Sarkin Babila ya gasa da wuta!”

23 Gama sun yi wauta a Isra’ila, sun yi zina da matan maƙwabtansu, sun yi ƙarya da sunana, ni kuwa ban umarce su ba. Ni na sani, ni ne kuma shaida, ni Ubangiji na faɗa.

Saƙo ga Shemaiya

24 “Zancen Shemaiya mutumin Nehelam,

25 haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila ya faɗa. Ga shi, ka aika da wasiƙu da sunanka zuwa ga dukan jama’ar da suke a Urushalima, da zuwa ga Zafaniya ɗan Ma’aseya, firist, da kuma ga dukan firistoci, cewa

26 Ubangiji ya naɗa ka firist a madadin Yehoyada firist, ka lura da Haikalin Ubangiji, ka sa kowane mahaukacin da zai yi annabci a turu, ka sa masa ƙangi.

27 To, me ya sa ba ka tsauta wa Irmiya, mutumin Anatot, wanda yake yin maka annabci ba?

28 Gama ya aiko mana a Babila, cewa za mu daɗe a zaman talala, mu gina wa kanmu gidaje, mu zauna a ciki, mu dasa gonaki mu ci amfaninsu.”

29 Sai Zafaniya firist, ya karanta wasiƙan nan a gaban annabi Irmiya.

30 Ubangiji kuwa ya yi magana da Irmiya, ya ce,

31 ya aika wa dukan waɗanda suke zaman talala ya ce, “Haka Ubangiji ya ce a kan Shemaiya mutumin Nehelam, ‘Saboda Shemaiya ya yi muku annabci, alhali ni ban aike shi ba, ya sa ku dogara ga ƙarya,’

32 saboda haka Ubangiji ya ce, ‘ga shi, zan hukunta Shemaiya, mutumin Nehelam, shi da zuriyarsa ba za a bar masa mai rai ko ɗaya a wannan jama’a ba, wanda zai ga irin alherin da zan yi wa jama’ata, gama ya kuta tayarwa ga Ubangiji,’ ” in ji Ubangiji.

Categories
IRM

IRM 30

Tabbatarwar Komowa daga Zaman Talala

1 Ubangiji ya yi magana da Irmiya, ya ce,

2 “Ni Ubangiji Allah na Isra’ila na ce, ‘Ka rubuta dukan maganar da na faɗa maka a littafi.

3 Gama kwanaki suna zuwa sa’ad da zan komo da mutanena, wato Isra’ila da Yahuza. Zan komo da su zuwa ƙasar da na ba kakanninsu, za su kuwa mallake ta,’ ni Ubangiji na faɗa.”

4 Waɗannan ne maganar da Ubangiji ya faɗa a kan Isra’ila da Yahuza.

5 “Ni Ubangiji na ce,

Mun ji kukan gigitacce,

Kukan firgita ba kuma salama.

6 Yanzu ku tambaya, ku ji,

Namiji ya taɓa haihuwa?

To, me ya sa nake ganin kowane

namiji yana riƙe da kwankwaso,

Kamar mace mai naƙuda,

Fuskar kowa kuma ta yi yaushi?

7 Kaito, gama wannan babbar rana ce,

Ba kuma kamarta,

Lokaci ne na wahala ga Yakubu,

Duk da haka za a cece shi daga

cikinta.”

8 Ubangiji Mai Runduna ya ce, “A wannan rana zan karya karkiya da take a wuyansu, in cire musu ƙangi, ba kuma za su ƙara zama bayin baƙi ba.

9 Amma za su bauta mini, ni Ubangiji Allahnsu, da Dawuda sarkinsu, wanda zan tayar musu da shi.”

10 Ubangiji ya ce,

“Kada ka ji tsoro, ya barana

Yakubu,

Kada kuma ka yi fargaba, ya

Isra’ila,

Gama zan cece ka daga ƙasa mai

nisa,

Zan kuma ceci zuriyarka daga ƙasar

bautarsu.

Yakubu zai komo, ya yi zamansa rai

a kwance,

Ba kuwa za a tsoratar da shi ba.

11 Gama ina tare da kai don in cece ka,

Zan hallaka dukan al’ummai sarai,

Inda na warwatsa ku.

Amma ku ba zan hallaka ku ba,

Zan hore ku da adalci,

Ba yadda za a yi in ƙyale ku ba

hukunci,

Ni Ubangiji na faɗa.”

12 Ubangiji ya ce,

“Rauninku ba ya warkuwa,

Mikinku kuwa mai tsanani ne

ƙwarai.

13 Ba wanda zai kula da maganarku,

Ba magani domin mikinku,

Ba za ku warke ba.

14 Dukan masu ƙaunarku sun manta

da ku,

Ba su ƙara kulawa da ku,

Domin na yi muku bugu irin na

maƙiyi.

Na yi muku horo irin na maƙiyi

marar tausayi,

Domin laifofinku masu girma ne,

Domin zunubanku da yawa suke.

15 Don me kuke kuka a kan

rauninku?

Ciwonku ba zai warke ba.

Saboda laifofinku masu girma ne,

Domin zunubanku da yawa suke,

Shi ya sa na yi muku waɗannan

abubuwa.

16 Domin haka dukan waɗanda suka

cinye ku, za a cinye su,

Dukan maƙiyanku, kowane ɗayansu

zai tafi bauta,

Waɗanda suka washe ku, za a washe

su.

Dukan waɗanda suka kwashe ku

ganima, su ma za a kwashe su

ganima.

17 Zan mayar muku da lafiyarku,

Zan kuma warkar da raunukanku,

Ko da yake maƙiyanku suna

kiranku yasassu,

Suna cewa, ‘Ai, Sihiyona ce, ba

wanda ya kula da ita.’

Ni Ubangiji na faɗa.”

18 Ubangiji ya ce,

“Ga shi, zan komar wa alfarwar

Yakubu arzikinta,

Zan kuma nuna wa wuraren zamansa

jinƙai,

Za a sāke gina birnin a kufansa,

Fādar kuma za ta kasance a inda

take a dā.

19 Daga cikinsu za a ji waƙoƙin godiya.

Da muryoyin masu murna.

Zai riɓaɓɓanya su, ba za su zama

kaɗan ba,

Zan kuwa ɗaukaka su, ba za a

ƙasƙantar da su ba.

20 ‘Ya’yansu za su zama kamar dā,

Jama’arsu kuma za su kahu a

gabana,

Zan hukunta dukan waɗanda suka

zalunce su.

21 Sarkinsu zai zama ɗaya daga

cikinsu,

Mai mulkinsu kuma zai fito daga

cikinsu.

Zan kawo shi kusa, zai kuwa kusace

ni,

Gama wane ne zai yi ƙarfin hali ya

kusace ni? Ni Ubangiji na faɗa.

22 Za ku zama mutanena,

Ni kuwa zan zama Allahnku.”

23 Ga hadirin hasalar Ubangiji ya taso,

wato iskar guguwa,

Zai huce a kan mugaye.

24 Zafin fushin Ubangiji ba zai huce ba,

Sai ya aikata, ya kammala abubuwan

da ya yi niyya a tunaninsa.

A nan gaba mutanensa za su fahimci

wannan.

Categories
IRM

IRM 31

1 Ubangiji ya ce, “Lokaci yana zuwa da zan zama Allah na dukan iyalan Isra’ila, za su kuwa zama jama’ata.”

2 Haka Ubangiji ya ce, “Jama’ar da

suka tsere wa takobi,

Sun sami alheri a cikin jeji,

A sa’ad da Isra’ila suka nemi

hutawa.”

3-4 Ubangiji ya bayyana gare ni tun

daga nesa cewa,

“Ya Isra’ila, budurwa!

Na kusace ki da madawwamiyar

ƙaunata,

Ba zan fasa amintacciyar ƙaunata a

gare ki ba.

Zan sāke gina ki,

Za ki kuwa ginu,

Za ki ɗauki kayan kaɗe-kaɗe,

Za ki shiga rawar masu murna.

5 Za ki sāke dasa gonar inabi

A kan duwatsun Samariya,

Masu dashe za su dasa,

Za su mori ‘ya’yan.

6 Gama rana tana zuwa sa’ad da mai

tsaro zai yi kira

A ƙasar tudu ta Ifraimu, ya ce,

‘Ku tashi mu haura zuwa Sihiyona

Zuwa wurin Ubangiji Allahnmu.’ ”

7 Ga abin da Ubangiji ya ce,

“Raira wa Yakubu waƙar farin ciki

da ƙarfi,

Ku ta da murya saboda shugaban

al’ummai,

Ku yi shela, ku yi yabo, ku ce,

‘Ya Ubangiji ka ceci jama’arka,

Wato ringin mutanen Isra’ila,’

8 Ga shi, zan fito da su daga ƙasar

arewa,

Zan tattaro su daga manisantan

wurare na duniya,

Tare da su makafi da guragu,

Da mace mai goyo da mai naƙuda,

Za su komo nan a babbar ƙungiya.

9 Da kuka za su komo.

Da ta’aziyya zan bishe su, in komar

da su,

Zan sa su yi tafiya a gefen rafuffukan

ruwa,

A kan miƙaƙƙiyar hanya, inda ba

za su yi tuntuɓe ba.

Gama ni uba ne ga Isra’ila,

Ifraimu kuwa ɗan farina ne.”

10 “Ku ji maganar Ubangiji,

Ya ku al’ummai,

Ku yi shelarsa har a ƙasashen da suke

nesa, na gāɓar teku.

Ku ce, ‘Shi wanda ya warwatsa

Isra’ila zai tattaro ta,

Zai kiyaye ta kamar yadda makiyayi

yakan kiyaye garkensa.’

11 Gama Ubangiji ya fanshi Yakubu.

Ya fanshe shi daga hannuwan

waɗanda suka fi ƙarfinsa.

12 Za su zo su raira waƙa da ƙarfi,

A bisa ƙwanƙolin Sihiyona,

Za su yi annuri saboda alherin

Ubangiji,

Saboda hatsi, da ruwan inabi, da

mai,

Saboda ‘ya’yan tumaki da na shanu.

Rayuwarsu za ta zama kamar

lambu,

Ba za su ƙara yin yaushi ba.

13 Sa’an nan ‘yan mata za su yi rawa

da farin ciki,

Samari da tsofaffi za su yi murna.

Zan mai da makokinsu ya zama

murna,

Zan ta’azantar da su, in ba su farin

ciki maimakon baƙin ciki.

14 Zan yi wa ran firistoci biki da

wadata,

Jama’ata za su ƙoshi da alherina,

Ni Ubangiji na faɗa.”

15 Ga abin da Ubangiji ya ce,

“An ji murya daga Rama,

Muryar baƙin ciki da kuka mai zafi,

Rahila tana kuka saboda ‘ya’yanta,

ba su.

16 Ki yi shiru, ki daina kuka,

Ki shafe hawaye daga idanunki.

Za a sāka miki wahalarki,

Za su komo daga ƙasar abokin gāba,

Ni Ubangiji na faɗa.

17 Akwai sa zuciya dominki a nan

gaba,

Ni Ubangiji na faɗa.

‘Ya’yanki za su komo ƙasarsu.

18 “Na ji Ifraimu yana baƙin ciki, yana

cewa,

‘Ka hore ni, na kuwa horu,

Kamar ɗan maraƙin da ba shi da

horo,

Ka komo da ni don in zama kamar

yadda nake a dā,

Gama kai ne Ubangiji Allahna.

19 Gama na tuba saboda na rabu da

kai,

Bayan da aka ganar da ni, sai na

sunkuyar da kai,

Kunya ta kama ni, na gigice,

Domin ina ɗauke da wulakancin

ƙuruciyata.’

20 Ashe, Ifraimu ba ƙaunataccen

ɗana ba ne?

Ashe, shi ba ɗan gaban goshina ba

ne?

A duk lokacin da na ambace shi a

kan muguntarsa

Nakan tuna da shi da ƙauna.

Saboda na ƙwallafa zuciyata a

kansa,

Hakika zan yi masa jinƙai, ni

Ubangiji na faɗa.”

21 Ki kafa wa kanki alamun hanya,

Ki kafa wa kanki shaidu,

Ki lura da gwadabe da kyau,

Hanyar da kin bi, kin tafi.

Ya budurwa Isra’ila, ki komo,

Komo zuwa biranen nan naki.

22 Har yaushe za ki yi ta shakka,

Ya ke ‘yar marar bangaskiya?

Gama Ubangiji ya halitta sabon abu

a duniya,

Mace ce za ta kāre namiji.”

23 Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila, ya ce, “Nan gaba za su sāke yin magana a ƙasar Yahuza da biranenta a sa’ad da na mayar musu da dukiyarsu.

‘Ubangiji ya sa maka albarka,

Ya wurin zaman adalci,

Ya tsattsarkan tudu!’

24 Yahuza kuwa da dukan biranenta za su zauna tare a can, da manoma, da makiyaya, da garkunansu.

25 Gama zan biya bukatar waɗanda suka gaji, in wartsakar da waɗanda ransu ya yi yaushi.”

26 Irmiya ya farka, ya ce, “Ina kuwa cikin barcina mai daɗi sai na farka na duba.”

Sabon Alkawari

27 “Ni Ubangiji na ce, ga shi, zan sa mutane da dabbobi su cika ƙasashen Isra’ila da na Yahuza.

28 Zai zama kamar yadda na lura da su don a tumɓuke su, a rushe su, a lalatar da su, a kawo musu masifa, haka kuma zan lura da su, a kuma dasa su, ni Ubangiji na faɗa.

29 A waɗannan kwanaki ba za su ƙara cewa,

‘Ubanni suka ci ‘ya’yan inabi masu

tsami,

Haƙoran ‘ya’ya suka mutu’ ba.

30 Amma kowa zai mutu saboda

zunubin kansa,

Wanda ya ci inabi masu tsami,

Shi ne haƙoransa za su mutu.”

31 Ubangiji ya ce, “Ga shi, kwanaki suna zuwa da zan yi sabon alkawari da mutanen Isra’ila da na Yahuza.

32 Ba irin wanda na yi da kakanninsu ba, sa’ad da na fito da su daga ƙasar Masar, alkawarin da suka karya, ko da yake ni Ubangijinsu ne, ni Ubangiji na faɗa.

33 Amma wannan shi ne alkawarin da zan yi da mutanen Isra’ila bayan waɗancan kwanaki, ni Ubangiji na faɗa. Zan sa dokokina a cikinsu, zan rubuta su a zukatansu, zan zama Allahnsu, su kuma za su zama jama’ata.

34 Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabcinsa, ko ɗan’uwansa cewa, ‘Ka san Ubangiji’ ba, gama su duka za su san ni, tun daga ƙarami har zuwa babba. Zan gafarta musu laifofinsu, ba kuwa zan ƙara tunawa da zunubansu ba.”

35 Haka Ubangiji ya ce,

Shi wanda ya ba da rana ta haskaka

yini,

Ya sa wata da taurari su ba da haske

da dare,

Shi ne yakan dama teku, ya sa

raƙumanta su yi ruri,

Sunansa Ubangiji Mai Runduna.

36 “Idan dai wannan kafaffiyar ka’ida

ta daina aiki a gabana,

Ni Ubangiji na faɗa,

To, ashe, zuriyar Isra’ila za ta daina

zama al’umma a gabana ke nan

har abada.

37 Idan a iya auna sammai a kuma iya

bincike tushen duniya a ƙarƙas,

To, ashe, zan watsar da dukan

zuriyar Isra’ila ke nan saboda

dukan abin da suka yi,

Ni Ubangiji na faɗa.

38 “Ga shi, kwanaki suna zuwa da za a sāke gina birnin domin Ubangiji, ni Ubangiji na faɗa, tun daga hasumiyar Hananel zuwa yamma, har zuwa Ƙofar Kan Kusurwa.

39 Sa’an nan ma’aunin zai daɗa gaba, har ya kai tudun Gareb, sa’an nan ya nausa zuwa Gowa.

40 Dukan filin kwarin gawawwaki da toka, da dukan filaye har zuwa rafin Kidron zuwa kan kusurwar Ƙofar Doki wajen gabas, za su zama mai tsarki ga Ubangiji. Ba za a ƙara tumɓuke shi ko a rushe shi ba har abada.”

Categories
IRM

IRM 32

Irmiya Ya Sayi Saura a Anatot

1 Ubangiji ya yi magana da Irmiya a shekara ta goma ta mulkin Zadakiya, Sarkin Yahuza. A lokacin kuwa Nebukadnezzar yana da shekara goma sha takwas da sarauta a Babila.

2 A lokacin nan kuwa sojojin Sarkin Babila sun kewaye Urushalima da yaƙi, annabi Irmiya kuwa yana a tsare a gidan waƙafi, a fādar Sarkin Yahuza.

3 Zadakiya Sarkin Yahuza, ya sa shi a kurkuku, gama ya ce, “Don me kake yin annabci? Ka ce, Ubangiji ya ce, ga shi, zai ba da wannan birni a hannun Sarkin Babila, zai kuwa cinye shi da yaƙi.

4 Zadakiya Sarkin Yahuza kuwa, ba zai tsere wa Kaldiyawa ba, amma za a ba da shi a hannun Sarkin Babila. Zai yi magana da shi fuska da fuska, ya kuma gan shi ido da ido.

5 Sarkin Babila kuwa zai tafi da Zadakiya zuwa Babila. Zai zauna can sai lokacin da na ziyarce shi. Ko da ya yi yaƙi da Kaldiyawa ba zai yi nasara ba.”

6 Irmiya ya ce, “Ubangiji ya yi magana da ni, cewa

7 ga shi, Hanamel, ɗan Shallum kawuna, zai zo wurina ya ce mini, ‘Ka sayi gonata wadda take a Anatot, gama kai ne ka cancanci ka fanshe ta, sai ka saye ta.’ ”

8 Sai Hanamel ɗan kawuna ya zo wurina a gidan waƙafi, bisa ga faɗar Ubangiji, ya ce mini, “Ka sayi gonata wadda take a Anatot a ƙasar Biliyaminu, gama kai ne ka cancanta ka mallake ta, kai ne za ka fanshe ta, sai ka saye ta.” Sa’an nan na sani wannan maganar Ubangiji ce.

9 Sai na sayi gonar a Anatot daga hannun Hanamel ɗan kawuna, na biya shi shekel goma sha bakwai na azurfa.

10 Na sa hannu a takarda, na buga hatimi na liƙe, na sami shaidu na kuwa auna kuɗin da ma’auni.

11 Na ɗauki takardun ciniki waɗanda aka rubuta sharuɗan a ciki da wadda aka liƙe da wadda ba a liƙe ba,

12 na ba Baruk, ɗan Neriya, ɗan Ma’aseya, a gaban Hanamel, ɗan kawuna, da gaban shaidun da suka sa hannun a takardar shaidar sayen, da gaban dukan Yahudawa waɗanda suke zaune a gidan waƙafi.

13 Sai na umarci Baruk a gabansu cewa,

14 “Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila, ya ce, ‘Ka ɗauki waɗannan takardun shaida, wadda aka liƙe da wadda ba a liƙe ba, ka sa su a cikin tukunyar ƙasa domin kada su lalace.’

15 Gama haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila, ya faɗa, ‘Gidaje, da gonaki, da gonakin inabi, za a sāke sayensu a ƙasan nan.’ ”

Addu’ar Irmiya

16 Bayan da na ba Baruk, ɗan Neriya, takardar sharuɗan ciniki, sai na yi addu’a ga Ubangiji, na ce,

17 “Ya Ubangiji Allah, kai ne ka yi sammai da duniya ta wurin ikonka da ƙarfinka, ba abin da ya fi ƙarfinka.

18 Kakan nuna madawwamiyar ƙauna ga dubbai, amma kakan hukunta wa ‘ya’ya saboda laifin ubanninsu. Ya maigirma Maɗaukaki, Allah, sunanka kuwa Ubangiji Mai Runduna.

19 Kai babban mashawarci ne, mai aikata manyan ayyukanka. Kana ganin dukan ayyukan ‘yan adam. Kakan sāka wa kowa bisa ga halinsa da ayyukansa.

20 Ka aikata alamu da al’ajabai a ƙasar Masar. Har wa yau kuma kana aikata su a Isra’ila da kuma cikin dukan al’ummai, ka yi wa kanka suna kamar yadda yake a yau.

21 Ta wurin alamu da al’ajabai, da iko, da ƙarfi, da banrazana, ka fito da jama’arka Isra’ila daga ƙasar Masar.

22 Ka kuwa ba su wannan ƙasa wadda ka rantse za ka ba kakanninsu. Ƙasar da take cike da yalwar albarka.

23 Amma sa’ad da suka shiga cikinta suka mallake ta, ba su yi biyayya da muryarka ba, ba su kiyaye dokokinka ba, ba su aikata dukan abin da ka umarce su ba, saboda haka ka sa wannan masifa ta auko musu.

24 “Ga shi, Kaldiyawa sun gina mahaurai kewaye da birnin da suka kewaye shi da yaƙi. Saboda takobi, da yunwa, da annoba aka ba da birnin a hannun Kaldiyawa, waɗanda suke yaƙi da birnin. Abin da ka faɗa ya tabbata, ka kuwa gani.

25 Duk da haka ya Ubangiji Allah, ka ce mini, ‘Sayi gonar da kuɗi, a gaban shaidu, ko da yake an ba da birnin a hannun Kaldiyawa.’ ”

26 Ubangiji kuwa ya ce wa Irmiya,

27 “Ni ne Ubangiji Allah na dukan ‘yan adam, ba abin da ya fi ƙarfina.

28 Saboda haka, ni Ubangiji, na ce zan ba da wannan birni a hannun Kaldiyawa da hannun Nebukadnezzar Sarkin Babila, za su ci birnin.

29 Kaldiyawa da suke yaƙi da wannan birni za su zo, za su ƙone wannan birni da wuta ƙurmus, da gidaje waɗanda aka ƙona turare ga Ba’al a kan rufinsu. Aka kuma miƙa hadayu na sha ga gumaka, don su tsokane ni in yi fushi.

30 Gama jama’ar Isra’ila da ta Yahuza, tun daga ƙuruciyarsu, ba su aikata kome a gabana ba sai mugunta, ba abin da jama’ar Isra’ila suka yi, sai tsokanata da gumaka don in yi fushi da ayyukan hannuwansu, ni Ubangiji na faɗa.

31 Wannan birni ya tsokane ni ƙwarai tun lokacin da aka gina shi har zuwa yau, domin haka zan kawar da shi daga gabana.

32 Wannan kuwa saboda muguntar jama’ar Isra’ila ce da ta Yahuza, wadda suka yi don su tsokane ni in yi fushi, su da sarakunansu, da shugabanninsu, da firistocinsu, da annabawansu, da mutanen Yahuza, da mazaunan Urushalima.

33 Sun juya mini baya, ba su fuskance ni ba, ko da yake na yi ta koya musu, amma ba su saurara ga koyarwata ba.

34 Sun kafa gumakansu na banƙyama a cikin Haikalina wanda ake kira da sunana, sun kuwa ƙazantar da shi.

35 Sun gina wa Ba’al masujadai a kwarin ɗan Hinnom don su miƙa ‘ya’yansu mata da maza hadaya ga Molek, ni kuwa ban umarce su ba, ba shi kuwa a tunanina. Ga shi, sun aikata wannan abin banƙyama, don su sa Yahuza ta yi zunubi.”

Alkawari na Sa Zuciya

36 “Domin haka ga abin da ni Ubangiji Allah na Isra’ila na ce a kan wannan birni wanda ka ce, ‘An ba da shi ga Sarkin Babila, da takobi, da yunwa, da annoba.’

37 Ga shi, zan tattaro su daga dukan ƙasashe inda na kora su, da fushina, da hasalata, da haushina. Zan komo da su a wannan wuri, zan sa su su zauna lafiya.

38 Za su zama mutanena, ni kuwa in zama Allahnsu.

39 Zan ba su zuciya ɗaya, da tafarki ɗaya domin su yi tsorona har abada, domin amfanin kansu da na ‘ya’yansu a bayansu.

40 Zan yi madawwamin alkawari da su, ba zan fasa nuna musu alheri ba, zan kuwa sa tsorona a zukatansu domin kada su bar bina.

41 Zan ji daɗin yi musu alheri. Zan dasa su a wannan ƙasa da aminci da zuciya ɗaya.”

42 Gama haka Ubangiji ya faɗa, “Daidai kamar yadda na kawo wannan babbar masifa a kan jama’an nan, haka kuma zan kawo musu dukan waɗannan alherai da na alkawarta musu.

43 Za a sayi gonaki a wannan ƙasa wadda kake cewa ta zama kufai, ba mutum, ba dabba a ciki, wadda aka ba da ita ga Kaldiyawa.

44 Za a sayi gonaki da kuɗi, a sa hannu a kan sharuɗa, a hatimce su a gaban shaidu, a ƙasar Biliyaminu da wuraren da suke kewaye da Urushalima, da cikin garuruwan Yahuza, da na garuruwan ƙasar tudu, da a garuruwan kwaruruka, da a garuruwan Negeb, gama zan komar wa mutane da wadatarsu a ƙasarsu, ni Ubangiji na faɗa.”

Categories
IRM

IRM 33

Komo da Harka a Urushalima

1 Ubangiji ya sāke yin magana da Irmiya sa’ad da yake a kulle a gidan waƙafi.

2 Ubangiji wanda ya halitta duniya, ya siffata ta, ya kafa ta, sunansa Ubangiji, ya ce,

3 “Ka kira ni, ni kuwa zan amsa maka, zan kuwa nuna maka manyan al’amura masu girma da banmamaki, waɗanda ba ka sani ba.”

4 Gama haka Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya ce, a kan gidajen da suke a wannan birni, da gidajen sarakunan Yahuza, waɗanda aka rurrushe domin a yi wa garukan jigo saboda mahaurai da suka kewaye birni, da kuma saboda yaƙi.

5 “Sa’ad da ake zuwa yaƙi da Kaldiyawa gidaje za su cika da gawawwakin mutane waɗanda na kashe da fushina da hasalata, gama na ɓoye wa wannan birni zatina saboda dukan muguntarsu.

6 Ga shi, zan kawo wa birnin lafiya, gama zan warkar da su, in wadata su da salama da gaskiya.

7 Zan kuma mayar wa mutanen Yahuza da mutanen Isra’ila da arzikinsu, in sāke kafa su kamar yadda suke a dā.

8 Zan shafe dukan laifin da suka yi mini, in kuma gafarta musu dukan zunubansu da tayarwar da suka yi mini.

9 Sunan wannan birni zai zama mini abin murna, da abin yabo, da darajantawa ga dukan al’umman duniya waɗanda za su ji dukan alherin da na yi dominsu, za su ji tsoro su yi rawar jiki saboda dukan alheri da dukan wadata da na tanada musu.”

10 Haka Ubangiji ya faɗa, “A wannan wuri da ka ce ya zama kufai, ba mutum ko dabba, wato a biranen Yahuza da titunan Urushalima, inda ba kowa, ba mutum ko dabba a ciki,

11 za a sāke jin muryar murna da ta farin ciki, da muryar ango da ta amarya, da muryoyin mawaƙa, sa’ad da suke kawo hadayun godiya a cikin Haikalin Ubangiji, suna cewa,

‘Ku yi godiya ga Ubangiji Mai

Runduna,

Gama Ubangiji nagari ne,

Gama madawwamiyar ƙaunarsa

tabbatacciya ce.’

Gama zan mayar da arzikin ƙasar kamar yadda yake a dā, ni Ubangiji na faɗa.”

12 Haka Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Wannan wuri wanda yake kufai, inda ba mutum ko dabba, da cikin dukan biranensa, zai sāke zama makiyaya, inda masu kiwo za su zauna da garkunansu.

13 A garuruwan ƙasar tuddai, da na kwaruruka, da na Negeb, da na ƙasar Biliyaminu, da na wuraren da suke kewaye da Urushalima, da na Yahuza, garkuna za su sāke bi ta ƙarƙashin hannun mai ƙidayawa,” in ji Ubangiji.

14 “Ga shi, kwanaki suna zuwa sa’ad da zan cika alkawarin da na yi wa mutanen Isra’ila da na Yahuza.

15 A waɗannan kwanaki da a lokacin nan, zan sa wani reshe mai adalci ya fito daga zuriyar Dawuda, zai aikata gaskiya da adalci a ƙasar.

16 A waɗannan kwanaki za a ceci mutanen Yahuza, mutanen Urushalima kuwa za su zauna lafiya. Sunan da za su sa wa Urushalima birninsu, shi ne, ‘Adalcinmu Ubangiji ne.’

17 Gama ni Ubangiji na ce Dawuda ba zai taɓa rasa mutumin da zai zauna a gadon sarautar Isra’ila ba.

18 Lawiyawa kuma ba za su rasa firistocin da za su tsaya a gabana, suna miƙa hadayun ƙonawa ba, da hadayu na gari na ƙonawa, su kuma miƙa sadaka har abada.”

19 Ubangiji kuma ya yi magana da Irmiya ya ce, “Haka Ubangiji ya faɗa,

20 idan ka iya hana dare da yini su bayyana a ƙayyadaddun lokatansu,

21 to, ashe, alkawarin da na yi wa bawana Dawuda zai tashi ke nan, har ya rasa ɗan da zai yi mulki a gadon sarautarsa, alkawarin kuma da na yi wa firistoci masu yi mini hidima, da ma’aikatana, zai tashi.

22 Kamar yadda ba a iya ƙidaya rundunan sammai ba, ba a iya kuma auna yashin teku ba, haka nan zan yawaita zuriyar bawana Dawuda da Lawiyawa, firistoci, masu yi mini hidima.”

23 Ubangiji kuma ya ce wa Irmiya,

24 “Ba ka ji abin da mutanen nan suke cewa ba? Wai, ‘Ubangiji ya ƙi iyalin nan biyu da ya zaɓa!’ Suka raina jama’ata, ba su kuma maishe ta al’umma ba.

25 Amma ni Ubangiji na ce, idan ban kafa alkawarina game da yini, da kuma game da dare, da ka’idodin da take mulkin sammai da duniya ba,

26 sa’an nan zan ƙi zuriyar Yakubu da bawana Dawuda. Ba kuma zan zaɓi wani daga cikin zuriyarsa ya yi mulkin zuriyar Ibrahim, da ta Ishaku, da ta Yakubu ba. Amma zan mayar musu da arzikinsu, in nuna jinƙai a kansu.”

Categories
IRM

IRM 34

Faɗaka ga Zadakiya

1 Ubangiji ya yi magana da Irmiya sa’ad da Nebukadnezzar, Sarkin Babila, da dukan sojojinsa, da dukan sojojin mulkokin al’umman da suke a ƙarƙashinsa, da dukan mutane suke yaƙi da Urushalima da dukan biranenta.

2 Ubangiji Allah na Isra’ila ya ce wa Irmiya ya tafi, ya faɗa wa Zadakiya Sarkin Yahuza cewa, “Ni Ubangiji, zan ba da wannan birni a hannun Sarkin Babila, zai kuwa ƙone shi da wuta.

3 Ba za ka tsere masa ba, amma lalle za a kama ka, a ba da kai a hannunsa. Za ka ga Sarkin Babila ido da ido, ka kuma yi magana da shi fuska da fuska. Za ka tafi Babila.

4 Ya Zadakiya, Sarkin Yahuza, ka ji maganar da ni Ubangiji na faɗa a kanka, ba za ka mutu ta wurin takobi ba.

5 Za ka mutu da salama. Kamar yadda aka ƙona wa sarakuna marigayanka turare, haka kai ma mutane za su ƙona maka turare, za su yi makoki dominka suna cewa, ‘Kaito, sarki ya rasu.’ Ni Ubangiji na faɗa.”

6 Sai annabi Irmiya ya faɗa wa Zadakiya, Sarkin Yahuza, dukan maganan nan a Urushalima,

7 sa’ad da sojojin Sarkin Babila suke yaƙi da Urushalima da kuma dukan biranen da suka ragu na Yahuza, wato Lakish da Azeka. Waɗannan su kaɗai ne biranen Yahuza masu garu da suka ragu.

Ta da Alkawari game da Bayin Ibraniyawa

8 Ubangiji kuma ya yi magana da Irmiya bayan da Zadakiya ya yi alkawari da dukan mutanen Urushalima don a yi musu shelar ba da ‘yanci,

9 cewa kowa ya saki bayinsa, mata da maza, waɗanda suke Yahudawa. Kada kowa ya riƙe bawa wanda yake Bayahude, ɗan’uwansa.

10 Sai suka yi biyayya. Dukan sarakuna da dukan jama’a waɗanda suka yi alkawarin, cewa kowa zai ‘yantar da bawansa ko baiwarsa, ba za su ƙara bautar da su ba, suka yi biyayya, suka ‘yantar da su.

11 Daga baya kuwa suka sāke komo da waɗannan bayi, mata da maza waɗanda suka ‘yantar, suka kuma mai da su bayi.

12 Ubangiji ya yi magana da Irmiya, ya ce,

13 “Ni Ubangiji Allah na Isra’ila, na yi alkawari da kakanninku lokacin da na fito da su daga ƙasar Masar daga bauta, na ce,

14 ‘A shekara ta bakwai, dole ne ku ‘yantar da ‘yan’uwanku, Ibraniyawa, waɗanda aka sayar muku, suka kuwa bauta muku shekara shida. Dole ne ku ‘yantar da su daga bautarku.’ Amma kakanninku ba su kasa kunne gare ni ba.

15 A ‘yan kwanakin da suka wuce kuka yi abu mai kyau a gabana da kuka tuba, har kuka yi wa juna shelar ‘yanci. Kuka yi alkawari a gabana a Haikalin da ake kira da sunana.

16 Amma sai kuka sāke tunaninku, kuka ɓata sunana sa’ad da kowannenku ya komo da bayinsa, mata da maza, waɗanda kuka ‘yantar, don su zauna yadda suke so. Ga shi kuma, kun komo da su su zama bayinku.

17 Domin haka ni Ubangiji na ce, ba biyayya kuka yi mini ba, da irin shelar ‘yancin da kowannenku ya yi wa ɗan’uwansa da maƙwabcinsa, saboda haka ni zan yi muku shelar ‘yanci zuwa mutuwa ta takobi, da annoba, da yunwa. Zan sa ku zama abin ƙyama ga dukan mulkokin duniya.

18 Mutanen da suka keta alkawarina, ba su kuma kiyaye maganar alkawarin da suka yi a gabana ba, sa’ad da suka raba ɗan maraƙi kashi biyu, suka bi ta tsakiyarsa,

19 wato manyan fādawan Yahuza, da na Urushalima, da ‘yan majalisa, da firistoci da dukan jama’ar ƙasa, waɗanda suka bi ta tsakanin rababben ɗan maraƙin,

20 zan bashe su a hannun abokan gabansu waɗanda suke neman ransu. Gawawwakinsu za su zama abincin tsuntsaye da namomin jeji.

21 Zadakiya, Sarkin Yahuza kuwa, da sarakunansa, zan bashe su a hannun abokan gābansu waɗanda suke neman ransu, wato sojojin Sarkin Babila, waɗanda suka tashi suka bar ku.

22 Ni Ubangiji zan umarce su su komo zuwa wannan birni don su yi yaƙi da shi, su ci shi, su ƙone shi da wuta. Zan sa biranen Yahuza su zama kufai, ba masu zama a ciki.”

Categories
IRM

IRM 35

Biyayyar Rekabawa

1 A lokacin da Yehoyakim, ɗan Yosiya yake mulkin Yahuza, sai Ubangiji ya ce wa Irmiya,

2 “Ka tafi gidan Rekabawa, ka yi magana da su, ka kawo su a Haikalin Ubangiji, cikin ɗayan ɗakunan, sa’an nan ka ba su ruwan inabi su sha.”

3 Sai na ɗauki Yazaniya ɗan Irmiya, ɗan Habazziniya, da ‘yan’uwansa, da dukan ‘ya’yansa maza da dukan iyalin gidan Rekabawa.

4 Na kawo su cikin Haikalin Ubangiji, a ɗakin ‘ya’yan Hanan da Igdaliya, mutumin Allah. Ɗakin yana kusa da na shugabanni, a kan ɗakin Ma’aseya ɗan Shallum mai tsaron bakin ƙofa.

5 Sa’an nan na sa tuluna cike da ruwan inabi, da ƙoƙuna a gaban Rekabawa, sai na ce musu, “Ku sha ruwan inabi!”

6 Sai suka amsa, suka ce, “Ba za mu sha ruwan inabi ba, gama Yonadab ɗan Rekab, kakanmu, ya umarce mu cewa, ‘Ko ku, ko ‘ya’yanku, ba za ku sha ruwan inabi ba har abada,

7 ba kuma za ku gina ɗaki ba, ba kuwa za ku yi shuka ba, ba za ku yi dashe ba, ba za ku yi gonar inabi ba. Za ku zaune cikin alfarwai dukan kwanakin ranku, domin ku yi tsawon rai a ƙasar baƙuncinku.’

8 Mu kuma muka yi biyayya da umarnin da Yonadab ɗan Rekab, kakanmu, ya yi mana, cewa kada mu sha ruwan inabi, mu da matanmu, da ‘ya’yanmu mata da maza,

9 kada kuma mu gina wa kanmu gidajen zama. Ba mu da gonar inabi, ko gona ko iri.

10 Amma a alfarwai muke zamanmu. Mun yi biyayya da dukan abin da Yonadab kakanmu ya umarce mu.

11 Amma sa’ad da Nebukadnezzar Sarkin Babila ya kawo yaƙi a ƙasar, sai muka ce, ‘Bari mu tafi Urushalima domin muna jin tsoron sojojin Kaldiyawa da Suriyawa.’ Shi ya sa muke zaune a Urushalima.”

12 Sa’an nan Ubangiji ya yi magana da Irmiya ya ce,

13 “Haka ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila, na faɗa, ka tafi ka faɗa wa mutanen Yahuza da mazaunan Urushalima cewa, ‘Ba za ku karɓi umarnina, ku kasa kunne ga maganata ba?’

14 Umarnin da Yonadab ɗan Rekab ya yi wa ‘ya’yansa, kada su sha ruwan inabi, sun kuwa kiyaye shi. Ba su taɓa shan ruwan inabi ba har wa yau, domin suna biyayya da umarnin kakansu. Ni kuwa na yi ta yi muku magana, amma ba ku kasa kunne gare ni ba.

15 Na yi ta aiko muku da bayina annabawa, ina cewa, kowa ya bar muguwar hanyarsa, ya gyara ayyukansa, kada ya bauta wa gumaka. Ta haka za ku zauna a ƙasa wadda na ba ku, ku da kakanninku, amma ba ku kasa kunne, ku ji ni ba.

16 ‘Ya’yan Yonadab ɗan Rekab sun kiyaye umarnin da kakansu ya yi musu. Amma jama’an nan ba su yi mini biyayya ba.

17 Domin haka, ni Ubangiji Allah Mai Runduna, Allah na Isra’ila, na ce zan kawo wa mutanen Yahuza da mazaunan Urushalima masifar da na ce zan kawo musu, domin na yi musu magana, ba su ji ba, na kira su, ba su amsa ba.”

18 Sai Irmiya ya ce wa Rekabawa, “Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Tun da yake kun kiyaye dukan abin da Yonadab kakanku ya umarce ku,

19 saboda haka Yonadab ɗan Rekab ba zai taɓa rasa magaji wanda zai tsaya a gabana ba.’ ”